WAYE ANGON CHAPTER 26 BY MARYAM JAFAR KADUNA
zan fi kowa farin ciki da abin nan.” Na ce,
“Ban da ni ko?”Ya ce, “Ke ce ta farko, ban taba ganin wadanda suka dace da juna ba sai su.
Na jinjina kai alamar gamsuwa, na ce “Wallahi zan yi farin ciki Alhaji.” Ya ce,Kinga yanzu ya rage namu kenan.Na ce, “Tabbas haka ne.
Koda muka tara su muka yi musu maganar, da farin ciki Imran ya ce Tabbas haka ne, na dade da son Mabaruka amman ban taba sanar mata ba. Ko don ina ganin itama haka ne a ranta.
Da sauri ta kalle shi yanayinta ya sauya.
Atakaice dai Mabaruka ta nuna mana ita bata sonshi,kawai dai Allah ne yasa shakuwa tsakaninsu, amman ita Sulaiman take so.
Yanayin da Imran ya shiga hankalinmu ya tashi, duk ya sukurkuce, shi kanshi mahaifinsa bai ji dadin hakanba.Hakan yasa na tursasa mata lallai, sai ta aure shi, don-ina ganin kuruciya a tare da ita, kamar ma bata san meye son ba, zata je ta cuci kanta.Musamman da ta min maganar wai Sulaiman takeSo, Kanin Binta. Na tsorata ainun don nasan sharrinta.Tamkar uwa ce a gidan su Sulaiman din, ita ce mai bada shawara kuma suna jin maganarta. Hakan yasa na tsani aurenta da shi, kar ta shiga halin da na shiga a baya sanadiyyar mahaifinta. Hakan yasa na Kara tsanar auren, saboda zabin Babanta ne kuma ga shi ban gamsu ba.Don haka na nace lallai ba za ta aure shi ba sai Imran,don nasan tana sonshi kuruciya ce kurum ba za ta ganeba. Amman in sun yi auren za ta fahimta, hankalinta zaifi kwanciya a kan Sulaiman din.Hakan shine yasa na sami kanin Babanta na fada masa abin da nake tsoro, shine Baba Haruna, shi ma
yaga gaskiyata ya ce na turo Imran din yaje suka suka gaisa ya gamsu da shi da halayensa ya yaba sosai,don haka ya shige min gaba har ya daura aurensu.Ta dubi Alkali ta ce,
“Wannan shi’ ne dalilin daura aurenta da Imran.”
Nan fa kotu ta hargitse akan wannan hardadden
auren, wasu cewa suke shin me kotu zata yanke? Wa keda mata kenan? Wasu su ce Sulaiman wasu su ce Imran. To ku a ganinku WAYE ANGON a cikinsu?Ita kanta kotu kanta ya dauki zafi a kan wannan al’ama rin, don haka ta daga zaman sai bayan sayi daya.A haka dai aka tashi zaman, ‘yan Jarida suka dinga tururuwar son yin magana da su amman ba su samu dama ba. Ana tashi Imran da Sharifa da Momy suka shige motarsu, Imran ya jawo hannun Mabaruka zai
saka ta motar. Saukar naushi ya ji ta bayanshi, bai san sanda ya duke ba kansa inda ya dake shi yai mai nauyi ya durkushe nan yana kokowa da numfashinsa, karshe dai ya sume a nan.
Sharifa ta rugo da gudu tayo kanshi tana kuka ta-
dinga girgiza shi, amman ina! Momy ma hankalinta a tashi. Shi kanshi Sulaiman din hankalinshi ya tashi, kowa ya yi cak! Yana kallon me zai faru? Dagowar Sharifat sai
dai ya ji saukar wani gigitaccen mari.
Ya dago yana kallonta abin ya ba shi mamaki,
wannan yarinyar ce ta mare shi? Don haka ya fidda hannu ya kai mata wani marin shima kan ka ce me fada ya hargitse tsakaninsu.
A ka shiga raba su, su kansu yan rabon suka kama dambe tsakanin ‘yan adawa, ji ka ke sautin duka na fitowa tif! tif) kau! Waje fa ya hargitse, Allah yasa ‘yan sanda suna kusa suka rufar musu,
A ka kwashi Imran sai asibiti da gaggawa, Sharifa
tana biye da su tana kuka, duk sawun yatsunshi a
fuskarta. Ita kanta wacce ake fadan kanta hankalinta ya tashi ganin Imran kwance ba numfashi, ba ta yi Kasa a gwiwa ba suka bisu asibitin ita da Rafi’atu da magoya bayansu
Yayin da ‘yan sanda suka damke Sulaiman, magoya bayanshi suka nufi ofishin ‘yan sandan suma. A asibiti an ba Imran gado an kuma yi nasarar farfadowarshi, duka ne ya ji shi har da ya dawo jin kansa yake gingiringin wani dum!
An dai masa duk abin da ya kamata, su Momy da
Daddyn Imran din suna gewaye kanshi, yayin da
Sharifa ke saman gadon da yake tana dan jajja masa yatsu.
Mabarukan tana gefe tana kallonsu tamkar bakuwa tazo ganin marar lafiya, su kadai ke nan nan da shi.Rafi’a ma na gefenta.
Hankalinshi ba ya ko ina sai kan matarsa Mabaruka, so yake su hada ido amman ta ki yarda su hadan. Ta turbune fuska kanta na kan window, ya lumshe ido tareda ajiyar zuciya.
Gajiya tayi da tsayuwar, tambayar kanta take to mema nake a nan? In tafiyata mana. Don haka ta dubi Rafi’atu ta ce,Zo mu tafi,”
Rafi’atu ta kalleta da kyau ta ce, Maburuka ba ki da hankali ko? Kina kallon ba shi da lafiya kowa bai bar
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe