YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 10 KARSHE BY ANUP JANYAU (_SPY_🎥)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 10 KARSHE BY ANUP JANYAU

(_SPY_🎥)

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

___________________________

“Wannan wanne irin shirmen banza ne?, taya zaku bari ta shammace ku?, na san halin Fatima kamar yinwar cikina, ga dukkan alama kunyi sakacin da har ta gano kuna bibiyarta saisa ta sanja taku”.

Inji Abba da ke tsaye a tsakiyar palornshi, wayarshi kare a kunne alamar waya ce yake, d’an shiru yayi yana sauraron su Rabson kana yace;

“Zan baku dama ta k’arshe, da zaran kunyi sake da ita shikenan kwangilar ta wuce ku”.

Yana gama fad’in haka ya ciro wayar daga kunnenshi tare da katse kiran.

“Alhaji me kake shirin yi ne?”.

Ammah ta tambaya, don tun d’azun take tsaye a palorn tana sauraren wayar da yake ba tare da ya sani ba. Saurin juyowa yayi ya kalleta, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace;

“Hafsa wannan bai shafe ki ba”.

“Ban gane bai shafeni ba Alhaji?”.

“Kamar yanda kika ji na fad’a miki ba!”.

Abba na gama fad’in haka ya nufi hanyar bedroom d’insa ya bar ta nan tsaye, girgiza kai Ammah tayi tare da furta,

“Ai idan kasan wata baka san wata ba”.

Daga haka ta juya ta fice daga d’akin tana danna wayarta, har ta lalubo number Kuzeem, bata kirata ba saida ta isa bedroom d’inta tare da zama bakin gado, sannan ta danna mata kira.

Kuzeem na k’ok’arin kabbarta sallar Azahar kiran Ammah ya shigo wayarta, saidai ko kad’an batayi tinanin kiran daga Ammah ne ba, hakan yasa ta fara gabatar da sallarta cike da nutsuwa. Saimah da ta fito daga bathroom na shirin k’arasawa domin d’aukar kiran sai taga ya katse, hakan yasa batama k’arasa wurin wayar ba itama tayi aniyar fara gabatar da sallar a gefen Kuzeem.

 Ammah na ganin har kiran ya katse Kuzeem bata d’aga ba, ya bata tabbacin hala kam bata kusa da wayar ne, saisa bata d’aga kiran ba, don ta san duk abunda Kuzeem keyi komai muhimmancinsa, indai aka zo b’angaren iyayenta zata ajesa a gefe don sun fiye mata muhimmanci akan komai da kowa. Jiyo hayaniya daga palor ya sanya Ammah mik’ewa ta fice d’akin, inda ta tarar da Raudah rungume da wata kyakkyawar matashiyar mace mai yanayin Ammah da Kuzeem saidai batayi hasken su ba.

Fuskar Ammah d’auke da fara’a take fad’i,

“Tou ashe Zulaihatu ce tazo”.

Dariya sukayi, kana Zulaihat d’in tace;

“Ina yini, ya jikinki?”.

“Alhamdulillah, ina kika baro yaran?”.

“Suna School Ammah”.

Zulaihat ta fad’a tana murmushi, itama Ammah murmushin tayi tace;

“Tou madallah,  Allah ya dawo dasu lafiya”.

Dukansu suka amsa da ameen, nan Ammah ta koma d’akinta domin gudanar da sallah, yayinda Raudah taja Zulaihat d’akinsu don suna matuk’ar shiri da junansu.

                 **********

“Binta mik’omin wayata, gata can akan stool”.

Kuzeem ta fad’ama Binta da ta fito daga bathroom, tana mata alama da stool d’in. Da sauri Binta ta d’auko mata wayar ta kawo mata. Cike da mamaki Kuzeem ke kallon kiran Ammah, ba b’ata lokaci ta kirata saidai har kiran ya katse ba’a d’aga ba, saboda lokacin Ammah tana bathroom wurin alwala. Ganin Ammah bata d’aga ba ya sanyata kiran number Raudah saidai itama ba’a d’aga ba, hakan yasa hankalinta ya d’an fara tashi, ta fara tinanin ko ciwon Ammah ne ya tashi, gabanta na fad’uwa ta dannama Abba kira.

Abba na dawowa daga masallaci, kiran Kuzeem ya shigo wayarsa, baisan sanda ya saki wani murmushin farin ciki ba, saboda tun d’azun yake son kiranta don tambayarta wani abu, saidai ya kasa don ya san halin Kuzeem sarai zata iya tuhumarsa har sai ta gano manufarsa, yanzu ma saboda tsaro bai d’aga kiran ba sai yana gaf da tsinkewa.

“Abba”.

Kuzeem ta fad’a calmly, sannan ta cigaba da fad’in,

“Ina yini ya aiki?”.

“Alhamdulillah ‘yar lelenah, fatan kina lafiya?, ya yanayin garin na RADDAL?, kinajin dad’insa kuwa?”.

Jin yanda Abba ke maganar hankali kwance ya sanyata sauke wata b’oyayyar ajiyar zuciya, don ta gama tabbatar da babu abinda ke faruwa, sai a lokacin ne ma tayi tunanin hala kam sallah suke yi lokacin da ta kira.

“Lafiya lau Abba”.

“Masha Allah!, ina fatan wurin da kike akwai tsaro?, kinsan fa bana son wani abu ya sameki ‘yar lelenah”.

Yanda Abba yayi maganar ya sanyata d’an murmusawa, kana tace;

“Ka kwantar da hankalinka Abba, babu abinda zai sameni da yardar ubangiji”.

“Tou  Allah yasa haka, yanzu kina ina ne?, ma’ana ina kike zama?,  Allah dai yasa babu marasa d’a’a a wurin da kike don nasan maganinsu zakiyi”.

Abba yayi tambayar cike da taka tsantsan yana sakin dariya, don kawar da muhallin zargin wani abu a zuciyarta. Itama dariyar tayi hardai da ta tuno su Mom Eshmal.

“Ina nan Nagarta Estate Abba, kamar kuwa kasan d’azun nayi maganin wasu k’ananan k’wari”.

Kuzeem ta fad’ama Abba tana tsagaita dariyar da take.  Abba kam wata dariyar farin ciki ya kece da ita, ganin yanda tarkonsa yayi tasiri akanta, sannan yace;

“‘Yar lelena ho!, ai daman ni nasan za’a rina, yanzu dai ina wani abu ne anjima zan sake kiranki don ki bani labarin yanda lamarin ya kasance”.

“Tou shikenan Abba”.

Kuzeem ta fad’a kana ta katse kiran tana murmushi, daidai lokacin kuma kiran Ammah ya shigo wayarta saurin d’agawa tayi tace;

“Ammah!”.

“Na’am”.

Ammah ta amsata, a hankali Kuzeem tace;

“Ammah tah! ina yini, ya jikinki?, ina fatan kina shan maganinki?”

“Jiki Alhamdulillah Kuzeem, ya aikin?, ba dai wata matsala kou?”.

Murmushi Kuzeem tayi, cike da k’aunar mahaifiyartata, kana tace;

“Ba matsalar komai Ammah, d’azun kin kirani ina sallah ne, da na kammala na gwada  kiranki sai baki d’auka ba, hankalina ya tashi nayi zaton bakida lafiya sai na kira Raudah itama bata d’agaba daga nan na kira Abba”.

Duk cikin maganganun Kuzeem babu kalmar da Ammah ta tsinta sai *na kira Abba*, cikin sauri tace;

“Kin kira Abbanki kika ce?”.

Cikin mamakin jin yanayin muryar Ammah yasa tace;

“Ammah lafiya kuwa?”.

Ajiyar zuciya Ammah ta sauke kana tace;

“Eh lafiya, dama na kiraki ne don muyi wata magana ne game da Abban naki, ina fatan baki sanar dashi inda kike ba kou?”.

“Ya tambaya na fad’a masa, amma meyasa kike wannan tambayar?”.

Ba b’ata lokaci Ammah ta sanar da Kuzeem wayar da tarar Abba nayi, sannan ta cigaba da fad’in,

“A yanda na fahimci manufarsa, yasa a bibiye ki ne, don a rik’a bashi bayanai a kanki, da kuma mutanen da kike mu’amala dasu don gudun kar wani ya d’auke miki hankali ki sab’a alk’awalin da kika d’aukar masa na auren Mu’az Salame”.

’Yar dariya Kuzeem tayi tace;

“Au ashe Abba ne yasa ake bibiyata tun jiya, ai tun a airport na gano ana bibiyata saidai duk iya hasashena na kasa gano wanda ya sanyasu, ki kwantar da hankalinki Ammah, na san yanda zan b’ullowa lamarin”.

Murmushi Ammah tayi tace;

“Tou shikenan Kuzeem Allah ya taimaka”.

“Ameen ya rabbi,  Yanzu ma zanje gidan Dady in gaisar dasu, ga ‘yarki nan duk ta takura ni”.

Ta k’arashe maganar tana hararar Saimah dake mata kallo mai cike da tarin tambayoyi, fisge wayar Saimah tayi ta fara  gaisawa da Ammah, yayinda Kuzeem ta mik’e ta nufi palor tana nazarin kalaman Ammah, tabbas maganarta babu tantama a ciki.

Abba kam tun bayan gama wayarshi da Kuzeem ya kira su Rabson ya shaida musu Kuzeem tana nan dai a Nagarta Estate don haka su sa ido sosai, kar a koma samun matsala.

*Few minutes later*

Kallon Binta Kuzeem tayi cike da tausayin yarinyar, kana tace;

“Binta tashi in mayar dake wurin Auntynki”.

Ko kad’an yanayin yarinyar bai nuna farin ciki ba, cike da damuwa tace;

“Banason inyi nisa dake Aunty”.

Saimah ce ta rik’ota tare da mik’ar da ita sannan tayi mata murmushi tace;

“Ki daina damuwa, Kuzeem na tare dake a koda yaushe kinji kou”.

“Tou  Aunty”.

Bintar ta fad’a a hankali, Kuzeem kuwa bata sake cewa komai ba tayi gaba, yayinda suka rufa mata baya. Saida Saimah tasa basket a back seat kana suka nufi gidan Mom Eshmal.  Koda suka shigo palorn gidan basu tarar da ita ba sai kayan kallo daketa faman aiki, d’an kallon palorn Kuzeem tayi sannan ta maida dubonta kan Binta tace;

“Ina ne d’akinta?”.

Binta ta nuna mata d’akin, daga haka Kuzeem ta bata umurnin taje ta kirata. Baje Binta ta samu Mom Eshmal kan gado daga ita sai k’ananan kaya idanuwanta a lumshe, yayinda Eshmal ke kwance gefenta tana bacci. Cikin d’ar-d’ar tayi sallama. Kamar a mafarki Mom Eshmal taji saukar muryar Binta a dodon kunnenta, cikin sauri ta bud’e idanuwanta sai kuwa taga ita d’in ce. Dak’yar ta yunk’ura ta mik’e zaune don duk jikinta ciwo yake, ko kad’an bata jin dad’in jikin.

“Aunty tace kizo”.

Inji Binta tana sadda kanta k’asa, a hankali Mom Eshmal tace;

“Tana ina?”.

“Palor!”.

“Okay kice ina zuwa”.

Mom Eshmal ta fad’ama Binta, kai kawai ta gyad’a mata sannan ta fice daga d’akin, yayinda Mom Eshmal ta mik’e ta nufi closet d’inta dake shak’e taf da kaya, wani iron maroon hijab ta ciro tare da zurawa a jikinta sannan ta fice daga d’akin. Kallo d’aya Kuzeem tayima Mom Eshmal ta maida hankalinta akan wayarta tana cigaba da karanta sak’on Bilal dake fad’a mata, ya kama hanya ta tayashi da addu’ar nasara, nan itama ta tura mishi da addu’ar sauka lafiya.

“Sannunku”.

Maganar Mom Eshmal ta ziyarci dodon kunnen Kuzeem, a hankali ta d’ago ta kalleta sai taga itama kallonta take. Saimah ce ta iya amsa Mom Eshmal tare da fad’in,

“Yawwa”.

Kuzeem kuwa wani guntun murmushi tayi ganin yanda Mom Eshmal tayi wani ladabu, ta takure wuri d’aya kan kujera.  Ajiye wayar hannunta tayi a gefe kana tace;

“Gamanar da kikace zaki rik’e nan a karo na biyu”.

Ba k’aramin dad’i ne ya ziyarci Mom Eshmal ba, don ko kad’an batayi tsammanin Kuzeem zata amince ba. Kuzeem kuwa cigaba tayi da fad’in,

“Ki tabbatar kin cika alk’awalin da kika d’auka, don gujewa abinda zai biyo baya, karkiyi tinanin na amince da ta cigaba da zama a wurinki ne saboda jin tausayinki, sam abun ba haka bane kin gane kou?”.

Saurin gyad’a kai Mom Eshmal tayi alamar eh, daga haka Kuzeem ta mik’e tare da kallon Saimah tace;

“Malama tashi muje”.

Tana gama fad’in haka ta nufi hanyar ficewa daga palorn, Saimah kuwa kallon Mom Eshmal tayi tace;

“Dan Allah ki rik’e amana, ko ba komai zaki samu lada mai tarin yawa a wurin ubangiji”.

“Insha Allahu, nagode sosai”.

Kallon Binta da tayi wani iri tayi, tare da sakar mata murmushi tace;

“Sis sai anjima kou?”.

Kai kawai ta gyad’a mata bata ce komai ba, daga haka Saimah ta mik’e itama ta fice daga d’akin. Mom Eshmal na murmushi tace;

“Ki kwantar da hankalinki Binta, ki kuma saki jikinki dani bazan sake cutar dake ba”.

A hankali ta gyad’a kanta alamar to, bud’e mata  hannuwa Mom Eshmal tayi alamar tazo, saidai ko motsawa batayi ba, ganin haka yasa ta iso wurinta tare da janyota ta rungumeta a jikinta tace;

“Kema ‘yata ce kamar Eshmal”.

Sai a lokacin hankalin Binta ya kwanta sosai, hannunta taja tace;

“Muje kici abinci”.☺️

Daga haka suka nufi dinning, ita da kanta tayi serving Binta.

Kuzeem kuwa tuni suka fice daga Estate d’in a motar Saimah, a hanyarsu ne take ma Saimah bayani akan aikin jaridar da ta samu, tare da yimata k’aryar ta ajiye aikin DSS saboda wani babban dalili, daga nan suka cigaba da fira jefi-jefi har suka iso unguwar su Saimah, inda Saimah ta tsaya gaban wani makeken gida tare da danna horn, cikin sauri get man ya zuge musu get kana ta shige cikin farfajiyar gidan mai kyan fasali.

Around 3:00pm wani k’aramin jirgi mai saukar ungulu ya sauka a cikin wani babban daji. Cikin azama Bilal dake zaune cikin jirgin ya mik’e ya sauya kayan jikinshi, daga na k’warai zuwa wasu k’ananan kaya da suka ji jiki, don har sun fara b’arkuwa. 

Wata bak’ar leda dake d’auke da toka  da aka had’eta da bak’in gawayi ya kwance, tare da d’ibar mai yawa ya shafamawa fuskarshi har zuwa wuyanshi, sannan ya cud’e sauran a saman bak’ar rigar jikinshi, nan take ya sauya kamannu ya dawo tamkar wani mahaukaci. 

Tsayawa yayi yana kallon jikinshi sai kawai yayi murmushi, daga haka ya bud’e k’atuwar backpack d’inshi dake ajiye gefensa ya ciro wani k’aramin kwali, bud’e kwalin yayi tare da fiddo k’aramar SPY Camera dake ciki, wacce ta kasance ‘yar mitsitsiya, don idan ta fad’i a k’asa sai kasha wahalar nemanta. Da sauri ya mak’alata cikin wata ‘yar k’aramar huduwa dake gaban tsohuwar P-cap dake kansa, wacce take fara amma tsabar jin jiki har ta koma ash.  Sungumar backpack d’in yayi ya goye a bayanshi, kana ya taka zuwa mazaunin direban jirgin yana fad’in,

“David what’s the time now?”.

“Sir it’s 3:10pm o’clock”.

D’an inyamurin ya fad’awa Bilal. Kai ya gyad’a alamar gamsuwa, sannan yace;

“Alright, I have to go”.

“Okay Sir!”.

Inji direban yana murmushi, shima Bilal murmushin yayi mishi kana ya bashi hannu suka sake gaisawa, daga haka k’ofar jirgin ta zuge, inda Bilal yasa kai ya fice da sauri, yana gama sauka ko minti biyu ba’ayi ba jirgin ya d’aga, tare da barin wurin.  Bilal kuwa kallon gabas, yamma, kudu da arewa yayi, yaga babu alamar wani mahaluk’i a cikin dajin, sai kukan tsintsaye. Daga haka yasa kai zuwa yamma.

Tafiyar 20 minutes yayi ya fara hango d’an k’aramin garin/k’auye mai suna *HAYIN TALLE* saboda dama gaf da gaf jirgin ya ajiyesa. Dakatawa yayi da tafiyar da yake tare da rik’e waist d’inshi yana sauke wahalalliyar ajiyar zuciya, saboda nauyin backpack d’in bayanshi wacce take tamkar dutse, saboda abubuwan da ke cikinta. 

Kallon tsaf ya shiga k’arema wurin yaga babu ko dabbobi balle mutane, hakan yasa ya isa bayan wata babbar bishiya dake gefen hanyar tare da duk’awa ya sauko da backpack d’inshi, kana ya bud’e ya ciro wani d’an k’aramin magini, abunda ake hak’a rami, cikin sauri ya shiga hak’a ramin yanayi yana masa fad’i, da d’an zurfi ya hak’a ramin yanda zai samu backpack d’inshi ta shige ciki, maginin ya mayar cikin backpack d’in tare da rufewa, yana sakata a cikin ramin kuwa ta shige tsaf, murmushi yayi sannan ya fara maida k’asar cikin ramin, har ya kammala rufesa kaf, sannan ya mik’e tare da sa k’afafunsa yana daddane wurin yanda zai daddale kar wani ya gano abinda akayi.

Yana gamawa ya tank’washe hannuwan rigar jikinshi, sannan ya tank’washe k’afafun wando, daga haka ya zura a guje zuwa hanyar shiga garin, yana  gudu yana tsayawa har ya samu ya kai daf da shiga garin. Hango wasu mutum biyu dake tafe kan jakunansu alamar daji zasuje, ya sanyashi tsayawa ya fara taka rawa ba wasa.😂  A yanda yanayin shigarsa take da kuma yanda yake kwasar rawar sai ka rantse da Allah mahaukacine na gaske, wanda hauka ta kama tuburan.

Kallon ikon Allah matasan suka tsaya yi, ganin yanda Bilal ke cashewa kamar mazari. Da yaga kallonshi kawai suke sunk’i k’arasowa inda yake kawai sai ya zura a guje zuwa wurinsu yana washe hak’oransa. Haba malam! ai suna fahimtar wurinsu yayo fa suka aniya dirowa daga saman jakunansu, tare da komawa cikin garin, yayinda Bilal yaji dad’in hakan, baiyi sanyaba ya rufa musu baya.

Ganin yanda matasan suka shigo cikin k’auyen afujajan dan tuni suka yada takalminsu, yasa tsirarun mutanen dake wurin suka shiga arcewa suma don a tunaninsu gayu ne suka kawo musu farmaki(B’arayi). Babu wanda ya tsaya tambayarsu abinda ke faruwa, saidai kowa yayi ta kansa, su kuwa basu tsaya ko’ina ba sai fadar Hakimin garin.  Cikin mamaki mutanen dake wurin suka shiga binsu da kallo ganin yanda suke hak’i. Hakimin na k’ok’arin magana Bilal ya iso wurin a sittin, cikin muryarshi mai amon sauti yake rewa wak’a yana fad’in, 

“Ku kamosu!, ku yanka!, ku soyasu!, ku cinye!, ku tauna k’ashi rumus-rumus!, kai! rumus-rumus!!”.

Bala’i! ai kan kace me Matasan da Hakimin tare da ‘yan tanyon zamanshi kowa ya ba babbar rigarshi iska, don neman hanyar b’uya. Sai wani dattijo da yak’i tashi, ya kafe Bilal da idanuwa, wanda ke dariya yana cigaba da rera wak’arsa yana rawa. Lokaci k’alilan ya fahimci abubuwa da dama game da Bilal, shikuwa Bilal ganin yanda yake kallonsa yasa ya fara mishi gwalo, irin yanda mahaukata suke yi.

                    *******

“Hisham nifa gaskiya na gaji, kasan kuma akwai motar da zan gyara anjima banso Baba ya dawo ban gama ba, kawai in mutumin nan baida lokacin mu sai mu kama gaban mu “.

Miswar ya fad’a yana k’arema had’ad’d’en wurin da suke zaune kallo, wanda za’a iya kiransa da aljannar duniya. 

“Matsalata da kai kenan mugun gajen hak’uri, idan baida lokacin mu zai ce mu samesa a nan ne?”.

“Tou shikenan don yace mu samesa a nan?, sai ya wani shanyamu?, ai wannan rainin wayau ne”.

Cikin sauri Hisham ya zungureshi da k’afa hango mutumin da tun d’azun suke zaman jira yana nufo inda suke, amma hakan bai hana Miswar cigaba da fad’in,

“Na tsani wulak’anci da rainin wayau wallahi, don kawai sunada kud’i sai su rik’a wulak’anta mutane…”.

Hisham bai tsaya sauraren k’arshen zancen Miswar ba, ya mik’e da sauri ya isa wurin mutumin da ke gaf da isowa inda suke zaune. Fuska d’auke da murmushi Hisham yace;

“Barka da fitowa Ranka shi dad’e”.

Hannu Mutumin ya mik’a ma Hisham sukayi musabaha kana yace;

“Kuyi hak’uri na barku kunata jira tun d’azun, mun shiga meeting ne sai yanzu muka fito”.

Cike da girmamawa Hisham ya d’an rissina tare da saurin fad’in,

“Ah! wallahi Ranka shi dad’e babu komai, ai muna muku uzuri abubuwan ba kad’an ba”.

“Mu k’arasa daga ciki”.

Mutumin ya fad’ama Hisham fuska d’auke da fara’a. Jin haka yasa Hisham yayi saurin juyawa ya kalli Miswar dake zaunensa yana danna wayarsa, ko alamar tasowa baida. Hisham ji yayi tamkar ya samesa a wurin yayi ta jibga tsabar takaici. Cikin d’an d’aga murya yace;

“Miswar!, taso manah”.

Sai a lokacin Mutumin ma ya lura da Miswar. Shikuwa basaraken mik’ewa yayi ya nufosu, fuskarnan tashi a tamke, don ba k’aramin haushi jiran da sukayi ya bashi ba. Yana isowa wurin da suke Mutumin ya mik’a masa hannu, kamar wanda akayiwa dole shima ya mik’a hannun sannan yace;

“Barka da warhaka Oga”.

Murmushi kawai mutumin yayi baice komai ba, kana yayi gaba suka rufa mishi baya, har suka iso cikin wani k’aton room mai azababben kyau da tsaruwa, duk inda ka d’ora idanuwanka maza ne manyan mutane zazzaune akan k’ayatattun dining table na alfarma suna cin abinci, ga wasu manyan bottles d’in drinks masu shegen tsada da aka ajema ko wannensu a gabanshi.  Sai firarsu suke suna dararraku cike da annashuwa. 

Kusan daburcewa Miswar da Hisham sukayi ganin yanda mutanen suka yo musu caa da idanuwa, tamkar sunga wasu ‘yan mata. Hankalin Hisham da Miswar bai gama tashi ba saida sukaji wasu dake gefensu suna fad’in,

“Wow!, wad’annan da zafi-zafin su”.😱🔥

A take jikin Miswar ya mutu don ya gama tabbatar da wannan wuri ba wurine na alkhairi ba. Jiki sanyaye suke bin bayan mutumin har ya kaisu wani k’ayataccen masauki sannan yace su zauna, kamar wad’anda k’wai ya fashewa a cikin ciki haka suka zauna, kowannensu gabanshi na dukan uku-uku. Daga haka mutumin ya ba wasu mutum biyu umurnin su kawo ma su Miswar abun motsa baki. Shikuma ya bar wurin.

Wasu manyan mutane uku ne suka iso wurin su Miswar, suna murmushi kana d’aya daga cikinsu yace;

“Muna maraba da ku a wannan duniya ta jin dad’i da more rayuwa, duniyar ‘yanci mai cike da gata. Ina mai yimuku albishir da babu wani abu da zaku nema ku rasa a cikin duniyar nan, indai kuna cikin wannan k’ungiya tamu mai zaman kanta, zakuyi mahaukatan kud’i, zakuyi suna kai abubuwa dai da dama duk sai kun mallakesu”.

😂Hankali tashe Miswar ya kalli Hisham, lokaci d’aya jikinshi ya fara rawa kamar mazari. Duk da kasancewarshi namiji mai jarumar zuciya, amma a wannan lokacin jarumtar nemanta yayi ya rasa, don kuwa ba karamin firgici da tashin hankali ya shiga ba.

                  *******

Kwance Kuzeem take a kan tamfatsetsen gadon Saimah, gashin kanta duk ya zubo a ta gefen k’asan gadon, saboda yanayin yanda tayi kwanciyar.  Saimah kuma na gefe tana aiki a system d’inta. Daidai lokacin wayar Kuzeem ta fara ruri alamar shigowar kira.  A hankali ta mik’e zaune tana gyara himilin sumar kanta, sannan ta d’auki wayar, ganin mai kiran ya sanyata d’an satar kallon saitin Saimah, sai taga headphone mak’ale a kunnenta, sannan ga baki d’ayan hankalinta na akan system d’inta, da alamar tana wani muhimmin abu ne. Dauk’e kai Kuzeem tayi kana  a hankali ta furta.

“Ina yini Sir!”.

(Nasan wasu zasuce Kuzeem bata sallama in zatayi waya, kunsan halin mutuniyar taku tsaitsaye take kamar nonon maza🤭😂)

Daga chan b’an garen L.G Aliyu Iko murmushi yayi kana yace;

“Lafiya lau Kuzeem, ya gajiya?”.

“Babu gajiya Sir”.

Kuzeem ta fad’a tana tank’washe k’afafuwanta. Yayinda L.G Aliyu ya cigaba da fad’in.✍️

*ALHAMDULILLAH!*

*ALHAMDULILLAH!!*

*ALHAMDULILLAH!!!*

_DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MAD’AUKAKIN SARKI DA YA NUFENI DA KAMMALA WANNAN LITTAFI NA *’YAR LEK’EN ASIRI KASHI NA D’AYA(PART 1)*. INA ROK’ON ALLAH YA YAFEMIN KUSKUREN DA NAYI A CIKI, DAMA WANDA ZANYI NAN GABA CIKIN RASHIN SANI.🙏😔 LADAR DAKE CIKI KUMA ALLAH YA HAD’EMUNA NI DA KU BAKI D’AYA._

*KUMA INA NEMAN ALFARMAR DUK WANDA NA B’ATAWA RAI KODA DA KALMA D’AYA NE A CIKIN WANNAN BOOK TO YA YAFEMIN DAN ALLAH*🙏

_Anya KUZEEM da BILAL zasuyi nasara akan wannan aiki da suka sanya a gaba? wad’anne irin k’alubale zasu fuskanta?_

_Meye manufar amincewar KUZEEM akan auren MR SALAME?_

_Waye MISWAR?_

_Wanne wuri ne MISWAR da HISHAM suka tsinci kansu?_

_Shin KUZEEM da MISWAR zasu had’u kuwa har ya fad’a mata sirrin zuciyarsa?_

_Wanne irin babban al’amari ne MISWAR yake ji game da KUZEEM?_

_Ko BILAL zai sanar da KUZEEM yana k’aunarta?_

_Me kuke tsammani idan MAJOR KHALIL ya gano abunda ake b’oye musu?_

_Ya zata kaya tsakanin jarumarku KUZEEM da ABREEN AL-MASHKOOL?_

_*NASAN ZUWA YANZU DUK KUN MATSU DA SON JIN AMSAR WAD’ANNAN TARIN TAMBAYOYIN. KU KASANCE DANI A CIKIN LITTAFIN ‘YAR LEKEN ASIRI PART TWO. TA HANYAR BIYAN NAIRA 200 KACHAL.  A NAN NE ZAKU SAMU DUKA AMSHOSHIN WAD’ANNAN TAMBAYOYIN DA SUKA TSAYA MUKU A RAI. DON LITTAFIN ‘YAR LEKEN ASIRI PART 1 SOMIN TAB’I NE KAWAI.  BILLAHI!  YANZU WASAR ZATA SOMA  A PART 2_🥳

#Anup💋

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *