YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 2 BY ANUP JANYAU (_SPY_🎥)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 2 BY ANUP JANYAU

(_SPY_🎥)

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

“What!!!?”.

Wani farin mutum wanda kallo d’aya zaka yimishi ka gano yana cikin lokaci, ya fad’a tare da saurin mik’ewa daga meeting d’in da suke yi. Da kallon mamaki mutanen dake zazzaune suka bishi. Shi kuwa bai tsaya kula kallon da suke yimasa ba ya bar wurin hankalinsa a d’an tashe, wurin da babu mutane ya isa, murya k’asa-k’asa yake fad’in,

“Hello Kana jina?”.

“Ina jinka Mai gida”.

“Ina so ka sanya ido sosai a kansu, ka tura amintattun mutanenka a sirrin ce su dubo mai suke yi a can bayan garin, wallahi hankalina a tashe yake don kuwa jikina yana bani akwai wata a k’asa, anya bazan sa a kashe su kawai mu huta ba?”.

“A’ah Mai gida, kashe su shine babban kuskuren da zamu aikata domin kuwa bamu san ko su d’in su waye ba, kuma bamu san da wane irin shiri suke ba, bari dai in tura a dubo su d’in kamar yanda ka buk’ata”.

“Okay!, yanzu muna meeting ne zan tab’oka daga baya”.

Yana gama fad’in haka ya katse kiran, sannan ya saita hankalinsa wuri d’aya ya koma wurin da suke meeting d’in.

Tana isowa wurin da ta barsu tace;

“Ku shirya zamu tafi”.

Saimah ce tace;

“Maganar gaskiya wannan karon bazan iya cin sola ba saidai ki goyani”.

Shareta Kuzeem tayi tare da yin gaba tana kara wata ‘yar k’aramar waya a kunnenta. mik’ewa sukayi suka bi bayanta inda suka bi hanyar da suka biyo sai fadar Hakimin, akayi daidai yana dawowa fadar tashi sukuma suna isowa wurin. kallo d’aya Kuzeem tayi mishi ta gano yanayin rashin nutsuwar da yake ciki. Maida dubonta tayi wurin Rau’an dake fad’ama mutanen garin wucewa zasuyi yanzu, amma zasu sake dawowa nan bada jimawa ba. Godiya suka shiga yimusu kamar ba gobe. Har bakin garin wasu daga cikin mutanen suka rako su tare da yimusu addu’o’in sauka lafiya, akayi rabuwar arziki sannan su Kuzeem suka mik’i hanyar komawa.

Suna tafe suna fira don wannan karon hankalinsu a kwance yake, yayinda lokaci-lokaci su Saimah kan tsaya suyi hotuna don sai a wannan lokacin suka  d’an yaba tsaruwar dajin, tare da tsayawa tantance wasu abubuwa a cikin dajin. basuyi wata tafiya mai nisa ba suka ji kukan jirgi kuma da alama yana gaf da k’arisowa inda suke ne, lokaci d’aya tsoro ya bayyana a fuskokinsu suka shiga bin dajin da kallo. Ganin haka ya sanya Kuzeem kwashewa da wata irin dariya harda rik’e ciki, da kallon mamaki suka bita ganin yanda take dariyar sosai don abune mai wahala kaga Kuzeem na dariya, saida tayi dariyarta mai isarta sannan tace;

“Na kasa tantance ku d’in ko wane jinsi ne a cikin duniyar matsorata, jirginmu fa ne yazo d’aukar mu”.

Kusan a tare suka sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, Saimah na dariya tace;

“Wallahi bakiji yanda hanjin cikina suka hautsine ba, kinsan fa wannan shine karon farko da na fito yawon bud’e ido a cikin irin wannan babban daji, kuma bi’iznillahi shine na k’arshe anyi d’an ba k’ari”.

Ga baki d’ayansu k’yalk’yalewa sukayi da dariyar Saimah, daidai lokacin jirgin  nasu ya fara saukowa wurin, fuskokinsu bayyane da zallar farin ciki suka k’arasa wurin jirgin suka shiga, ba b’ata lokaci ya d’aga suka bar cikin dajin.  K’arfe biyu suka sauka cikin garin *RADDAL*

Around 8:00pm 

Kuzeem ce zaune kan chair ga baki d’aya hankalinta na kan laptop d’in dake gabanta, sanye take da wata maroon polo neck wacce ta kama jikinta sosai.  A hankali ta kai santala-santalan fararen yatsunta ta fara sarrafa laptop d’in cike da k’warewa, lokaci d’aya hoton wata kyakkyawar budurwa ya bayyana a jikin laptop d’in. 

“Abreen Al-mashkool”.

Ta fad’a a hankali tana cigaba da k’arema hoton kallo, daga haka ta cigaba da sarrafa laptop d’in tana duba wasu muhimman abubuwa. wayarta ce ta fara k’ara hakan yasa ta dakata daga abinda take, tare da d’an kallon inda wayar ke ajiye, ganin mai kiran nata ya sanyata d’an sakin murmushi kana ta mik’a hannunta ta d’auko wayar a hankali tace;

“Saimah”.

Daga chan b’angaren Saimah tace;

“Agogo sarkin aiki, nasan yanzu haka kina nan kin duk’ufa maimakon kije ki huce wannan uban gajiyar da muka kwaso”.

“Ke kinfa sanyamin aiki a gaba, wayace miki ni raguwa ce irin ki?, sam sam baki chanchanci zama likita ba”.

Kuzeem ta fad’a tana had’e rai kamar Saimar na gabanta.

“Ni wallahi tausayin mijin da zai aureki nake yi, domin kuwa inada tabbacin bazai samu wata kulawa ba, tunda kin dad’e da d’aurawa kanki aure da wannan aiki naki”.

K’yalk’yalewa da dariya Kuzeem tayi tace;

“Saimah bana son inskanci fa”.

Itama Saimah dariyar tayi, saida suka tab’a ‘yar fira kad’an kana sukayi sallama. 

_Washe gari_

7:30am ta kammala shirinta cikin wata white abaya da tayi masifar yimata kyau tare da rolling veil d’in abayar a kanta, daga haka ta fito main palor nan taci karo da maid d’inta, bayan sun gaisa ne ta wuce dining area domin yin break, a gurguje tayi break d’in sannan ta mik’e ta nufi harabar get d’in gidan.

Wata Lexus Rx350 golden ta dannawa key, sannan ta bud’e motar ta shiga, horn ta dannawa mai gadi yayi saurin wangale mata get, a tsiyace ta cillah motar kan titi, ta nufi wurin aikinta.

_United Kingdom_

Abreen ce kwance kan wani tamfatsetsen gado mai masifar kyau da tsada tamkar ba za’a mutu ba, kallo d’aya zakayi mata ka tabbatar da hutu tare da kwanciyar hankali suna lullub’e da kyakkyawar fatar jikinta.  A hankali ta fara bud’e lumsassun idanuwanta jin yanda k’arar wayarta ya dameta, janyo wayar tayi tare da jan guntun tsaki kana ta d’aga kiran, cikin wata shagwab’ab’b’iyar murya tace;

“Dad!”.

Banji mai aka ce mata ba naga ta turo baki tana fad’in,

“Nifa lafiya nake Dad, kuma gobe zan dawo na gaji da k’asar nan”.

Shiru tayi tana sauraren Dad d’in nata dake magana, sake turo baki tayi sannan tace;

“Okay, bye”.

Tana fad’in haka ta katse kiran tare da maida idanuwanta ta lumshe.

      *** *** *** ***** ******

“Sannu da zuwa ranki shi dad’e”.

Hulaim ta fad’a tana sakarma Kuzeem murmushi, itama murmushin ta sakar mata sannan tace;

“Nagode Hulaim”.

Daga haka tabar wurin, wata kofa ta tura ta shigo cikin wani babban office mai d’auke da na’urori kala-kala. Cike da nutsuwa tayi sallama, cikin fara’a wani babban mutum ya amsa sallamar yana mai nuna mata kujera alamar ta zauna, ba musu ta zauna sannan tace;

“Barka da warhaka ‘Yallab’ai”.

“Yawwa barka dai Kuzeem”.

Takardar hannunta ta ajiye masa akan table tace;

“Takardar neman izini ce ‘Yallab’ai, ina buk’atar sa hannunka ne, jikin Mahaifiyata ne ya tashi, zanje in dubota idan Allah ya kaimu gobe”.

“Subhanallah,  Allah ya bata lafiya”.

Ya fad’a cike da alhini sannan yaja takardar a gabansa, a hankali tace;

“Ameen nagode”.

Lokacin ya mik’o mata takardar, nan ta karb’a tare da yimasa godiya kana ta fice ta nufi office d’inta shima yanada girma sosai, ga kuma na’urori ta ko’ina, hakan zai baka tabbacin ita babbace a ma’aikatar.

Tana zama wayarta na fara k’ara murmushi tayi ganin sunan Bilal dama tun jiya take expecting kiransa. bata d’aga kiran ba har ya katse, office d’in tabi da kallo taga duk na’urorin suna aikine, mik’ewa tayi ta isa jikin wata k’aramar computer tayi ‘yan danne-danne lokaci d’aya duka na’urorin suka dena aiki.

Daga haka ta dawo ta zauna daidai lokacin kiran nashi ya sake shigowa, da sauri ta d’aga tare da fad’in,

“Kana magana da Kuzeem Yusuf!, Ma’aikaciyar Jaridar MCTv”.✍️

   Murmushi mai sauti Bilal yayi don yasan tana wurin aikine saisa tace masa haka, daga haka ya fara magana. Shiru tayi tana sauraren shi, saida ya d’au kusan 5 minutes yana mata bayanin wasu muhimman abubuwa sannan ya dakata domin jin abinda zata fad’a.

“Duk na fahimceka Bilal, Idan na koma gida zamuyi magana ta Skype”.

Tana jin ya katse kiran ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, sannan ta mik’e ta kunna na’urorin da ta tsayar. Agogon wayarta ta duba taga 8:30am hakan na nufin lokacin da zata gabatar da shirin *INA MAFITA?* ya gabato, da sauri ta fice daga office d’in.

Cikin wani babban d’aki ta isa wanda ke d’auke da Computers ta ko’ina, ko wace da kalar abinda take nunawa, hakan ze baka tabbacin a wurin suke gabatarda shirye-shiryensu. 

Ra’is da wani  mutum ne kawai zaune a gaban wata k’aramar laptop suna aiki, wurinsu ta k’araso tana fad’in,

“Sannunku da aiki”.

A tare suka amsata da fad’in,

“Yawwa Ranki shi dad’e, barka da fitowa”.

Idanuwanta na kan abinda suke tace;

“Ra’is yau ina so shirin nan ya kasance Live, sannan kuma a haska shi har RTA Channel503”.

Cike da girmamawa ya mik’e yana fad’in,

“Angama Ranki shi dad’e”.

Murmushi tayi wanda yayi sanadiyar lotsawar duka dimples d’inta biyu. Daga haka ta wuce inda zata fara gabatar da shirin yayinda Ra’is yayi saurin bin bayanta. daidai lokacin Hulaim da wasu maza biyar suka shigo wurin, suma k’arasawa sukayi wurin su Kuzeem d’in, nan suka shiga shirye-shiryen yanda shirin zai kasance.  A k’a’idar shirin baza’a nuno fuskar mai gabatar da shirin ba kai tsaye, saidai a rik’a jin muryarshi kawai kamar dai kana sauraren radio. Saida suka tabbatar da komai yayi daidai sannan suka koma gefe suna kallon Kuzeem da ta fara gabatar da shirin cikin nutsuwa da kamala kamar yanda ta saba.

“BARKANMU DA SAKE SADUWA DAKU A CIKIN WANNAN SHIRI NA INA MAFITA?, WANDA NI KUZEEM YUSUF ZAN GABATAR MUKU TARE DA TAIMAKON ABOKANAN AIKINA.  ZANYI MAGANANE AKAN ILIMIN MATASA, KO SHAKKA BABU BA WANI MUTUM DA ZAIYI TABABA AKAN CEWA ‘JAHILCI RIGAR K’AYA NE’ ‘ILIMI KUMA SHINE GISHIRIN ZAMAN DUNIYA’. IDAN HAKANE KUWA TABBAS NEMAN ILIMI YA ZAMA WAJIBI AKAN KOWANE MATASHI DAKE FAD’IN K’ASAR NAN KAI HARMA DA DUNIYA BAKI D’AYA, DOMIN SAMUN CIGABAN RAYUWARMU DA KUMA K’ASARMU,  A SAMU ZAMAN LAFIYA TA HANYAR MAGANCE MATSALAR RASHIN TSARO DA MUKE FAMA DASHI A CIKIN WANNAN K’ASAR TAMU”.

Fuskokin su Hulaim d’auke da murmushi suke jinjina mata, Daga haka Kuzeem ta cigaba da gabatar da shirin kai tsaye, inda ta dinga zak’ulo muhimman abubuwa tana fayyacesu.

Girgiza kai wani Babban mutum dake zaune cikin aljannar duniyar office d’inshi yayi yana cigaba da kallon k’atuwa Tv plasmar dake manne jikin bangon office d’in. wayarshi ya d’auka tare da lalubo wata number ya kira, yana jin an d’aga kiran yace;

“Honorable kana ganin wani shiri da ake haskawa a RTA Channel503 kuwa?”.

Daga chan b’angaren wanda ya kira da Honorable d’in yayi ‘yar dariya yana fad’in,

“Ina gani Alhaji Lati, yau aka fara haska shirin a Channel d’in, saidai na kasa fahimtar inda kalaman wannan yarinyar suka dosa”.

Wani murmushi Alhaji Lati yayi yace;

“A yanda na fahimta maganganu ne takeyi masu halshen damo, saidai bata fito fili ta bayyana manufarta ba”.

“Babu wata manufa a cikin maganganunta Alhaji Lati, kawai shirmene da rawar kai na yara, ai kai ko daga jin yanda take wasu maganganun kasan k’urciya na damunta”.

A tare sukayi dariya kana suka katse kiran tare da barin abun a shirme, suka cigaba da sabgogin gabansu.

“IDAN HAR MUKAYI K’OK’ARIN KORAR JAHILCI A CIKIN RAYUWARMU DA YARDAR ALLAH ZAMU GANO MATSALOLIN DA SUKA DABAIBAYE WANNAN K’ASA TAMU, TARE DA MAGANCE SU CIKIN HANYA MAI SAUK’I. TO MASU SAURARE DA HAKA NA KAWO K’ARSHEN WANNAN SHIRIN MAI TAKEN INA MAFITA?, SAI KUMA IDAN ALLAH YA KAIMU SATI MAI ZUWA”.

Tana gama fad’in haka ta fito daga wurin, nan su Hulaim suka shiga tab’a mata kowanensu na fad’in albarka cin bakinshi akan shirin. Kai tsaye office d’inta suka wuce ita da Hulaim, cikin sauri Hulaim ta isa wurin frigde dake office d’in ta ciro mata robar ruwa ta kawo mata, bayan ta gama shan ruwan ne ta d’an jingina bayanta ga kujerar da take zaune tare da lumshe idanuwanta tana nazarin wasu abubuwa a ranta.  A hankali Hulaim ta zauna gefenta tace;

“Rankin shi dad’e!”.

Ba tare da ta bud’e idanuwanta ba tace;

“Ina na samu bindiga ko?”.

Cikin mamaki Hulaim ke kallonta, taya ta gano abinda take son tambaya kenan?, d’an murmushi Kuzeem tayi har lokacin idanuwanta na lumshe sannan tace;

“A idanuwanku ne kuka ganta a matsayin bindigar gaske, amma ta roba ce, Ina bin k’a’idar aikina a koda yaushe don haka ki dena zargin wani abu a ranki, kawai nayi amfani da ita ne domin tsoratar da wad’annan mutanen”.

Murmushi Hulaim tayi tace;

“Afuwan Ranki shi dad’e, wallahi ko kad’an ban zargeki akan komai ba”.

Sai a lokacin ta bud’e kyawawan idanuwanta ta saukesu akan Hulaim sannan tace;

“Bakiyi laifi ba don kin tambaya, hakan na daga cikin martaba aikin da kike yi”.

“Nagode Ranki shi dad’e”.

“Zanyi tafiya gobe idan Allah ya kaimu”.

Fuska d’auke da damuwa Hulaim tace;

“Ranki shi dad’e tafiya kuma?”.

Kai Kuzeem ta gyad’a mata alamar eh, daga haka ta sanar da ita zataje duba Mahaifiyarta ne. 

Sai k’arfe 5:30pm Kuzeem ta dawo gida, wanka tayi ta sanya wasu jumpsuit red, sannan ta d’auko macbook ta shiga skype cikin sa’a ta tarar da Bilal d’in online da alama ita yake jira, nan suka fara magana, sun d’au tsawon mituna goma suna tattaunawa kana sukayi sallama. 

Kiran sallar magrib da aka fara ne ya sanyata mik’ewa ta koma d’akinta domin gabatar da sallah, bayan ta kammalane ta koma wurin Macbook d’in don tana buk’atar ganin farin cikinta wato ahalinta. 

Wani k’ayataccen murmushi Kuzeem tayi lokacin da wata kyakkyawar budurwa wacce bata kai shekarunta ba ta bayyana a jikin macbook d’in, a hankali tace;

“Raudah!”.

Itama budurwar murmushi tayi, cikin wani yanayi na farin ciki take kallonta sannan tayi saurin kai hannunta a forehead d’inta alamar sarawa tace;

“Na gaida jarumar jarumai!, yakike ya aiki?”.

Kai Kuzeem ta girgiza tana cigaba da murmushi kana tace;

“Alhamdulillah Raudah, Fatan kuna lafiya?, Ina Ammah da Deedee?”.

“Lafiya lau muke Adda Fatima, gasu can a dining area suna cin abinci”.

Daga haka ta d’an juya bayanta tana fad’in,

“Deedee kizo ga Adda Fatima”.

Da sauri wata ‘yar matashiyar budurwa ta iso wurin fuskarta d’auke da zallar farin ciki tace;

“Adda Fatima nayi kewarki, Yaushe zaki zo?”.

D’an hararar wasa Kuzeem ta sakar mata tace;

“Ban sani ba, wato bama zaki tambayeni lafiyata ba sai neman sanin yaushe zanzo”.

Turo baki tayi tace;

“Sorry Addanah!, fatan kina lafiya?”.

Kuzeem na murmushi tace;

“Lafiya lau Autah jaja manya, nidai kafin ku cikani da surutunku da baya k’arewa, ku had’ani da Ammah tah”.

A tare sukayi dariya, sannan suka isa wurin kyakkyawar matar dake zaune a dining, wacce kallo d’aya zakayi mata ka hango tsananin kamarsu da Kuzeem. Cike da k’auna take gaisawa da ahalin nata, tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a cikinsu, sunsha fira sosai sannan sukayi sallama bayan Ammah ta cikata da addu’o’in da ta saba yimata a koda yaushe.

Around 7:00am flight d’in da Kuzeem ta shiga ya d’aga zuwa UK.🇬🇧✍️Ā¹ā¶ Ā²ā°

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *