YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 3 BY ANUP JANYAU
(_SPY_🎥)
Www.bankinhausanovels.com.ng
UK 🇬🇧
Flight d’insu na sauka airport ta tari cab tare da fad’a mishi sunan Hotel d’in da zai kaita, don UK ba bak’uwarta ba ce. Suna isowa Hotel d’in ta sallameshi sannan ta wuce reception ta karb’i key ta nufi room d’in da zata sauka.
Wanka tayi domin jin dad’in jikinta, sannan ta gabatar da sallar azahar. daga nan bacci ya kwasheta, bata falka ba sai wuraren 3:30pm. Sai a lokacin tayi order abinci ta samu ta ci. Ga baki d’ayan yinin ranar babu aikin da tayi sai hutu kawai don tana tattare da gajiya.
*Washe gari*
Around 12:35pm ta gama shirinta, pink t-shirt ce jikinta da black jeans sai wani black veil data d’aura a kanta amma hakan bai hana saukowar bak’ar sumarta akan shoulder d’inta ba, sosai tayi kyau kamar wata baturiya. Cikin sauri ta d’auki wayarta ta fice daga room d’in.
Cab ta tara tare da sanar da shi inda zai sauketa wato address d’in Abreen. daga d’an nesa tace ya sauketa, kana ta fito tana k’arema had’ad’d’en ginin Bungalow d’in kallo, wanda Security’s suka zagaye, kasancewar babu get a gidan hasalima a filin Allah yake ba’a zagaye shi ba.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ta wace hanya zata bi ta shiga cikin gidan?,duk da tasan abune mai wahala. Tana cikin wannan tunanin Abreen ta fito daga cikin gidan. Sanye da wasu Blue Jumpsuit da sukayi masifar amsar farar fatar jikinta, ga dukkan alama fita zatayi.
Wurin wata arniyar mota da zata kai a k’alla kusan 50.6million ta nufa. Da sauri wasu daga cikin security’s d’in suka iso wurinta tare da bud’e mata k’ofar motar, tsaye tayi ba tare da ta shiga motar ba cikin halshen turanci tace;
“Yau bana buk’atar kowa a tare da ni”.
Wani daga cikinsu ne yace;
“Kiyi hak’uri Ma’am, Dad d’inki ya gargad’emu sosai akan kar muyi kuskuren barinki fita ke kad’ai ba tare da mun rakaki ba”.
Cikin tsiwa tace;
“Bana so nace!, baze yiwu ba ace duk inda zanje kuna biye dani kamar wasu jeluna, da anyi magana kuce wani tsaron lafiyata kuke, an fad’a muku ni jinjira ce?, duk wanda yayi kuskuren biyoni daga cikin ku wallahi a bakin aikinsa”.
Tana gama fad’in haka ta shige cikin motar ta bar wurin a tsiyace. Wani murmushin jin dad’i Kuzeem tayi sannan tayi saurin tsaida Cab tabi bayan Abreen. Cikin wani tsadadden gidan cin abinci Abreen tayi perking motarta, sannan ta fito ta nufi cikin wurin, inda ta tarar babu mutane a wurin, don dama ba kowa ke zuwa cin abinci wurin ba sai manya.
Kuzeem kuwa tsaye tayi a harabar wurin, saida ta tabbatar Abreen tayi 5 minutes da shiga kana shige cikin wurin itama. Zaune ta sami Abreen tana dannar wayarta. K’arasawa tayi wurin wani table dake fuskantar inda Abreen d’in take, sannan ta zauna tana d’an satar kallonta. Daidai lokacin waitress ta iso wurin tana mik’a mata menu akan ta zab’i abinda take so, nan tace Pizza kawai take buk’ata. Sannan waitress d’in ta wuce, ba’a dad’e ba sai gata ta kawo mata Pizza d’in.
Abreen wayarta kawai take dannawa fuskarta d’auke da kyakkyawan murmushi da alama akwai abinda take dake sanyata nishad’i. Yayinda Kuzeem ke ankare da duk wani motsi nata, sai sak’a abubuwa da dama take a ranta. a hankali ta d’ora kanta akan table tare da lumshe idanuwanta. D’an d’agowa Abreen tayi don tunda Kuzeem ta shigo wurin k’amshin tularenta ya daki hancinta amma game d’in da take bai bata damar d’agowa ta kalli ko waye ba sai a yanzu. cikin mamaki take kallon Kuzeem da ta d’ora kanta a table d’in, a zuciyarta tace anya wannan lafiya take kuwa?, daga haka ta mik’e ta nufi wurin Kuzeem d’in, cikin halshen turanci ta fara magana don ita a tsammaninta baturiya ce.
“Hey!, wani abu yana damunki?”.
Banza Kuzeem tayi da ita tamkar bata san akwai mutum a wurin ba. d’an d’age gira Abreen tayi ta sake fad’in,
“Hey gurl!, Kina nufin bacci kike ne?”.
A hankali Kuzeem ta d’ago ta zuba mata kyawawan idanuwanta, lokaci d’aya ta tsuke fuska, a d’an fusace tace;
“Miye zaki wani zo ki dameni da tsiwa?”.
Zaro ido Abreen tayi tace;
“Hakama zaki ce?, don kinga na damu da sanin meke damunki, yi hak’uri to”.
Kuzeem na yimata wani kallo tace;
“Ki rik’e hak’urinki”.
Cike da mamaki Abreen ke kallon Kuzeem lokaci d’aya kuma ta kwashe da dariya don sosai Kuzeem d’in ta bata dariya, chair dake kallon Kuzeem taja ta zauna fuskarta d’auke da murmushi tace;
“Ga dukkan alamu na fahimci kina cikin damuwa sosai, ki fad’amin abinda ke damunki nayi maki alk’awalin zan baki shawara”.
Ajiyar zuciya Kuzeem ta sauke tana jin wani dad’i a ranta, don zuwa yanzu ta gama fahimtar halayen Abreen, ita d’in mai sauk’in kai ce, ga kuma surutu, a hankali tace;
“Dama a wannan duniyar har akwai wani wanda zai damu da son sanin damuwar wani?”.
Zaro ido Abreen ta sake yi jin Kuzeem tayi maganar kai tsaye cikin halshen Hausa. cike da mamaki tace;
“Dama ke ‘yar k’asar *SARBIK* ce?”.
Kai kawai Kuzeem ta gyad’a mata bata ce komai ba. Fuskar Abreen d’auke da tsantsar farin cikin da ya kasa b’oyuwa tace;
“Gaskiya naji dad’in had’uwa dake, kina wane gari ne a *SARBIK*?”.
“RADDAL STATE”.
“Wow! nima a can nake fa”.
Cike da taku Kuzeem ta basar bata nuna komai ba, daga haka ta kai dubonta ga agogon wayarta kana tace;
“Yayi kyau, ni zan wuce sai mun sake had’uwa”.
B’ata fuska Abreen tayi tace;
“Zaki wuce kuma?, Dan Allah ki bari mu k’arasa firarmu manah, tunda nazo k’asar nan ban tsinci kaina cikin yanayin farin ciki kamar yau ba”.
D’an kawar da kai Kuzeem tayi gefe tare da sakin wani shu’umin murmushi a ranta tace;
“Yarinya kin kawo kanki, dama d’an kuka shike jama uwarsa jifa”.
“Gashi mun had’u ko sunan juna bamu sani ba, Kuma baki sanar da ni damuwarki ba”.
Maganar Abreen ta sake ziyartarta, kallonta tayi tace;
“Kaina ke ciwo a yanzu, saisa zan wuce”.
“Ayya, to amma please ki bani address d’inki zan zo dubaki anjima ko gobe”.
Saurin gayyato murmushi tayi a fuskarta cike da jin dad’in yanda tarkonta ya kama Abreen cikin sauri. Nan Kuzeem ta bata address d’in Hotel d’in da ta sauka, tare da karanta mata digit d’inta. daga haka suka rabu.
Cike da farin ciki Kuzeem ta dawo, nan ta kira number Bilal ta sanar dashi nasarar da suka samu akan Abreen d’in, sosai yaji dad’in hakan don yasan nasara ce ke tunkaro su.✍️
_Note; Sunan k’asa da garuruwa duka k’irk’irarrune_
*GARGAD’I!!!*
_TUN FARKON FARA WANNAN LABARI NA MANTA SHAF INYI GARGAD’I. DON HAKA BAN AMINTA BA, KUMA BAN LAMUNTA BA WANI/WATA SU JUYA/SANJAMIN LABARI TA KOWACE IRIN SIGA BA TARE DA IZINI NA BA. IDAN KUWA HAKAN YA FARU BAN YAFE BA!!!_
________The following day, around 1:30pm wayar Kuzeem ta hau ruri alamar shigowar kira, ganin bak’uwar number ya tabbatar mata da Abreen ce, dama tun safe take ta expecting kiran nata, bata d’aga kiran ba sai yana gab da tsinkewa. Bayan sun gama gaisawa ne Abreen ke sanar mata gata a reception, da sauri Kuzeem ta mik’e taje ta tarota suka dawo cikin room d’in. zuciyarta cike da farin ciki ta tsiyaya mata drink a glass cup ta mik’a mata. Abreen na murmushi ta karb’a tayi sipping k’ad’an sannan ta ajiye cup d’in a kan wani cristal table dake gabansu, tare da fad’in,
“Thank you!”.
“The pleasure is mine”.
Inji Kuzeem tana k’irk’iro murmushi a fuskarta. Cike da zumud’i Abreen ta sake fad’in,
“I’m Abreen Al-Mashkool”.
Kuzeem ta gyad’a mata calmly alamar gamsuwa. Daga haka Abreen ta cigaba da zuba tamkar wacce aka tambaya.
“Kamar yanda kika ji na fad’a miki sunana Abreen, ni d’aya iyayena suka mallaka a fad’in duniyar nan. Nayi karatuna a k’asar Spain inda na karanci Business administration domin in biyo Dad a harkar kasuwanci”.
D’an lumshe idanuwa Kuzeem tayi tare da bud’e su a hankali. Allah ya sani ko kad’an bata son yawan surutu, saidai ya ta iya?, tunda yanayin aikinta ya had’ata mu’amala da kalolin mutane. Abreen na k’ok’arin cigaba da magana, wayarta dake ajiye kan table ta fara ringing, d’an zaro idanuwa waje tayi ganin Dad d’inta ne ke kiranta, ba tare da ta d’auki wayar daga inda take ba tayi receiving call d’in tare da sanyata a handsfree.
“Abreen! kina ina ne?, meyasa zaki na fita ba tare da Security’s ba?”.
Daga chan b’angaren Dad d’inta ya fad’a muryanshi cike da damuwa.
“Uhnm Dad zan iya kula da kaina a duk inda nake, so ka daina damun kanka, nd kuma bana buk’atar Security’s suna biyoni duk inda zani kamar wata maras gaskiya”.
Abreen ta fad’ama Dad d’inta cike da shagwab’ar da ta zame mata jiki. A mugun fusace yace;
“K’aniyanki Abreen!, nace k’aniyanki!. ki sanar dani a ina kike?, bana son shashanci”.
“Ina wurin friend d’ita ne, please Dad ni kam ka barni na gaji da zaman kad’aici a gidan”.
“Har yaushe kikayi friend a UK?, Abreen meyasa bakya jin maganata ne?, sau nawa nayi miki kashedin ki daina sakin jiki da mutane?, ehh?”.
Ganin ran Dad d’in nata ya d’an b’aci, ya sanyata yin sanyi da muryarta tace;
“I’m so sorry Dad!. Gani nan yanzu zan koma gida tou”.
Dad d’in nata bai sake cewa komai ba ya katse kiran. Abreen kuwa kallon Kuzeem tayi wacce hankalinta ke kan wayarta kamar batajin wayar da suke yi.
“Kina jin Dad ko?, ni shikenan kullum banida daman shak’atawa?, sai an had’ani da security’s”.
Inji Abreen cikin shagwab’ab’b’iyan muryanta mai cike da zallar k’urciya. Ba tare da Kuzeem ta d’ago ta kalleta ba tace;
“Tou ai yanada gaskiya, dama haka ake so iyaye su rik’a kula da ‘ya’yansu tamkar yanda zasu na kula da rayukansu”.
Turo baki gaba Abreen tayi tace;
“Naji!, nidai ki fad’amun ya sunanki?, kafin in wuce, don na gan kaman rowa kike mun”.
“I’m Kuzeem!”.
Ta fad’a mata a tak’aice, tana cigaba da danna wayarta.
“Wow! what a beautiful name? *Kuzeem!*”.
Inji Abreen tana sake maimaita sunan, kana tace;
“Nice to meet you”.
“Me too”.
Kuzeem ta dad’a mata kuma har lokacin bata d’ago ta kalleta ba sai danna wayanta takeyi ba. Hakan bai wani damu Abreen ba saima murmushi ta saki tace;
“Tunda na tashi banada friends Coz Dad baya barina mu’amala da mutane sai yaran Aminanshi kawai. Can we be friends?”.
Fuska a sake Kuzeem ta d’ago ta kalleta sannan ta gyad’a mata kai tace;
“Yes of course!”.
Cike da farin ciki Abreen tace;
“I’m glad. when zaki koma SARBIK?”.
“Next week”.
“Alright, ni gobe zan wuce, da ace kin tashi komawa sai mu tafi tare ta P-J(Private Jet) d’ina. Ina fatan zaki kawomin ziyara idan kika dawo?, nima na miki alk’awarin zan na kawo miki ziyara har sai kin gaji da ni”.
“Keda Dad d’inki baya son kina mu’amala da mutane taya kike tsammanin zan ke kawo miki ziyara?”.
Kuzeem ta fad’a mata cike da taku tana waro kyawawan idanuwanta waje. K’yalk’yalewa da dariya Abreen tayi tace;
“C mon babe! Karki wani damu da wannan, zan mishi k’arya”.
D’an murmushi kawai Kuzeem tayi bata ce komai ba, don ta lura ba k’aramar k’urciya ke damun Abreen d’in ba, ga kuma sangarci da gata da ke d’awainiya da ita. Nan Abreen tace Kuzeem ta bata number da take amfani da ita ta k’asar SARBIK, ba musu ta karanto mata tayi saving da *Fav*, sannan ta mik’e tace zata wuce, hakan yasa Kuzeem tayi mata rakiya saida ta bar Hotel d’in kana ta dawo tare da fara shirin barin k’asar UK a yau. Tana gama shirinta kai tsaye ta wuce airport, ba’a wani jima ba jirgin da ta shiga ya d’aga zuwa k’asar SARBIK.
_Safe Journey Kuzeem_👋🌝😘
*FLASHBACK*
_F.C.T FUNADE_
*KARAMCI ROAD*
House no. 16
A hankali wata rantsattsar MASERATI 2020 ash color ta tsaya gaban katafaren gidan tare da tsala uban horn!, *fii fiiii fiitttt!* nan take wasu security’s biyu suka zuge rafkeken get d’in gidan. Ba b’ata lokaci motar ta shige cikin farfajiyar gidan tare da nufar Perking lot ta perka. Tsawon wasu seconds sannan aka bud’o murfin motar, cikin natsuwa wata kyakkyawar matashiyar budurwa fara da zata kai 24 years a duniya, ta fito daga cikin motar, jikinta sanye da wasu Black Suit riga da wando da sukayi masifar yimata kyau, tayi rolling wani k’aramin white veil a kanta. Doguwa ce amma ba sosai ba, haka ma tana d’an da kaurin jiki kad’an, don ba za’a kirata siririya ba, Kallo d’aya zakayi mata ka hango tarin gajiya a cikin k’wayar idanuwanta saidai yanayinta bai nuna tana tattare da gajiyar ba, laptop bag d’inta ta ciro daga cikin motar sannan ta rufe motar, daga haka ta bar wurin. Yanda take taka k’asa kawai ya isa ya baka tabbacin ita d’in ba ragguwar mace ba ce, saboda tafiya take kanta tsaye cike da jarumta duk da kuwa cikin nutsuwa take tafiyar amma hakan bai b’oye jarumtarta ba.
Da sallama ta shigo cikin wani had’ad’d’en palor mai d’auke da wasu luntsuma-luntsuman kujeru na alfarma. Wata kyakkyawar mace da ke zaune cikin palorn wasu ‘yan mata biyu da sukayi kama da masu aiki na danna mata k’afafuwanta, ta amsa sallamar fuskarta bayyane da murmushi, wacce a k’alla zata kai 55 years a duniya, suna tsananin kama da wannan budurwar hakan ya bani tabbacin ita ce mahaifiyarta.
“Ina yini Ammah!”.
Inji budurwar tana zama gefen kyakkyawar matar. Cike da kulawa Ammah tace;
“Lafiya lau KUZEEM! Ya aikin?”.
“Alhamdulillah”.
Kuzeem ta fad’a mata tana murmushi, kana ta amsa gaisuwar da ‘yan aikin ke mata, tare da mik’ewa tace;
“Barin watsa ruwa Ammah”.
Tana gama fad’in haka ta nufi hanyar zuwa d’akinta, a hankali ta murd’a handle d’in k’ofar d’akin nata ta shiga. D’aki ne mai d’auke da tsabta ta musamman, komai na d’akin fari ne k’al!, kama daga fentin d’akin har zuwa had’ad’d’un furnitures d’in Chinese dake cikin tafkeken d’akin, sai k’yalli sukeyi saboda kulawar da suke samu, ga wani irin sihirtaccen k’amshi dake fitowa ta kowace kusurwa dake cikin d’akin.
A natse ta fara cire Suit d’in jikinta tare da yin hanging d’insu a hanger. sannan ta d’aura wani k’aramin white towel a jikinta ta shige bathroom domin watsa ruwa. Bata wani jima ba ta fito daga bathroom d’in, a gurguje ta gama shafama kyakkyawar farar fatar jikinta wani tsadadden cream, sannan ta nufi closet d’inta ta ciro wata red gown mai shegen kyau ta zura a jikinta, tare da d’ora hula red a kanta. Fatabarakallahu ahsanal khalik’ina, na fad’a a raina ganin yanda tayi masifar kyau kamar wacce zata je gasar sarauniyar kyau ta duniya.
Gently ta nufi tamfatsetsen mirrow’n d’ake d’akin, tare da feshe jikinta da turarukkan dake jere a wurin masu k’amshin dad’i. daga haka ta dawo kan makeken bed d’in d’akin tayi kwanciyarta, don ba k’aramar gajiya take tattare da ita ba, bata wani jima da kwanciyar ba, wani nannauyan bacci ya kwasheta. Sai wuraren 6:30pm ta farka daga baccin. Kai tsaye bathroom ta wuce ta d’auro alwala ta fito, don lokacin har an fara kiraye-kirayen sallar magrib. Tana kammala sallar tayi azkar sannan ta fice daga d’akin, a palor ta tarar da Sisters d’inta Raudah da Deedee. Kusan a tare suka had’a baki wurin fad’in,
“Ina yini Adda Fatima!”.
Fuskarta a sake tace;
“Lafiya lau ‘yan matan Ammah”.
Murmushi suka yi mata a tare. Kai tsaye dining area ta nufa saboda yinwar dake addabarta don rabonta da abinci tun safe. Deedee ce tabi bayanta tayi serving d’inta. Pineapple fried rice ce da taji kayan had’i sai k’amshi ke tashi. Lumshe idanuwa Kuzeem tayi tace;
“Ya rabbi!, girkin Ammah na daban ne”.
Dariya Deedee dake tsiyaya mata kunun madara a glass cup tayi, tace;
“Kai Adda Fatima, tun yanzu kina santi, to ina ga kin fara cin abincin?”.
Murmushi kawai Kuzeem tayi bata ce komai ba ta fara cin Abincinta a natse. Yayinda Deedee ta zauna tana mata fira saidai ba wani amsata take sosai ba, hakan bai damu Deedee ba bai kuma sa ta daina mata firar ba don ta riga ta san halin Addan tata.
_Washe gari_
8:53am Kuzeem ta iso cikin wani wuri mai girman gaske da tsayi, don kuwa duk inda ka d’ora idanuwanka iya ganinka, yayinda security’s keta kai kawo ta ko’ina a cikin wurin, kai kace gidan wani president ne ko governor, saidai yanayin tsarin buildings d’in wurin kawai zai baka tabbacin ba gida ba ne, daga tsakiyar wurin wani tamfatsetsen upstairs ne mai masifar kyau da tsaruwa wanda dukkanshi glass ne. Sai kuma wasu manyan buildings da ba upstairs ba amma sunyi mugun tsaruwa.
Tana gama perking a wurin da aka tanada domin ajiye motoci, ta fito daga motar tana kai dubonta ga tsadadden Iwatch d’in dake d’aure a hannunta na dama, don lokacin meeting d’in da zasuyi ya gabato gashi ta makara yau. Cikin sauri security’s d’in da ke ta wurin suka shiga k’amewa tare da sara mata alamar girmamawa, hannu kawai ta d’aga musu sannan tayi hanzarin barin wurin ta isa bakin had’ad’d’en upstairs d’in tare da d’ora yatsanta manuni a kan wani d’an abu dake jikin glass door d’in shiga wurin, nan take k’ofar ta bud’u daga haka ta shige sannan k’ofar ta rufe kana ta bud’u ta ciki, fita tayi ta shiga elevator da zai kaita meeting hall d’in saboda tayi saurin isa, yana tsayawa ta fito ta shige cikin hall d’in, nan ta tarar da abokanan aikinta duk sun halarto a wurin, suna zazzaune kan wasu bak’ak’en kujeru na alfarma dake zagaye da wani k’aton glass table wanda ke tsakiyar had’ad’d’en hall d’in mai fad’i da tsayi. zasu kai su 20 duk maza ne, both muslims nd christians, suma duk sanye suke da black suit irin na jikin Kuzeem, ko wannensu a gabanshi akwai abun sautin magana, wasu ma har da laptop.
A natse Kuzeem ta zauna d’aya daga cikin kujerun, daidai lokacin wani Dattijo mai cike da kamala ya shigo cikin wurin, saidar shi Ash suit ne jikinshi, kai tsaye ya nufi masaukinshi na musamman, hakan yasa dukkansu sukayi saurin mik’ewa tare da k’amewa suka yimishi salute cike da girmamawa, saida ya zauna kana suma suka zazzauna. 9:00am na bugawa, Dattijon ya mik’e tsaye, cike da kamala ya fara magana cikin harshen turanci yace;✍️
*Saidai ni da hausa zanyi*🥴😉😹
✨Thanks for reading my story✨
#Anup💋
*Short chappy i know😩🥺, please manage*🙏😉
😘Ā²ā¶ Ā³ā°