YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 8 BY ANUP JANYAU (_SPY_🎥)

YAR LEKEN ASIRI CHAPTER 8 BY ANUP JANYAU

(_SPY_🎥)

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani irin dirowa Saimah tayi daga kan kujerar da take zaune, saboda ba k’aramin tsorata da ganin Binta tayi ba, don tunda ta shigo bata lura da ita ba sai yanzu. Saurin kallonta Kuzeem tayi sannan ta maida dubonta wurin Binta. D’an guntun tsaki taja tare da b’alla ma Saimah wata uwar harara tace;

“Tou shugabar matsorata, mutum ce ba aljana ba, tunda kika shigo fa take d’akin nan amma mitar da kike bata baki damar ganinta ba”.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Saimah ta sauke tare da k’yalk’yalewa da dariya sannan ta koma ta zauna tace;

“Yoo ai tsoro halas ne, ya za’ayi inga mutum bansan daga ina ya fito ba in rasa tsorata”.

Murmushi kawai Kuzeem tayi bata ce mata komai ba, sai mamakin tsoro irin na Saimah take. 

“Aunty fitsari nake ji”.

Binta ta fad’a tana isowa wurin Kuzeem, jin hakan yasa Kuzeem ta mik’e tare da rik’a hannunta suka nufi d’akin da ta shiga d’azun, saida ta duba bathroom d’in taga akwai ruwa a ciki sannan ta barota ta dawo palor, tana zama Saimah tace;

“Kuzeem wannan yarinyar fa?”.

D’an lumshe idanuwa Kuzeem tayi kamar ba zatayi magana ba sai kuma can tace;

“Ki ajiye maganar wannan yarinyar a gefe, zamuyi ta daga baya”.

Gyad’a kai Saimah tayi alamar gamsuwa kana tace;

“Tou amma me kika zo yi a RADDAL haka?, harda su kama gida sai kace wacce batada kowa a cikin garin”.

Guntun murmushi Kuzeem tayi ba tare da ta bud’e idanuwanta ba tace;

“Na samu aiki ne”.

Cike da tsantar mamakin jin furucinta Saimah ta gyara zama tana fuskantarta da kyau sannan tace;

“Hajiyata ban gane kin samu aiki ba?, fahimtar da ni”.

A hankali Kuzeem ta bud’e lumsassun idanuwanta kana tace;

“Shima zan miki bayani daga baya”.

Saimah da haushin halin Kuzeem ya cikata bata sake cemata komai ba ta maida hankalinta kan wayarta, daidai lokacin Binta ta dawo palorn, kallonta Kuzeem tayi tare da fad’in,

“Kinyi breakfast?”.

Saurin girgiza kai Binta tayi tace;

“A’ah”.

Kuzeem bata ce mata komai ba ta maida dubonta kan Saimah tare da fad’in,

“Dr please ki kai yarinyar nan eatery taci abinci”.

D’agowa Saimah tayi ta kalleta tace;

“Tou ke kinyi breakfast d’in ne?”.

“Karki damu bana jin yinwa”.

Kuzeem ta bata amsa, tare da maida dubonta kan wayarta da kira ya shigo,  da hanzari ta d’aga kiran tare da karawa a kunnenta.

“Barka da warhaka”.

Kuzeem ta fad’a tare da yin shiru tana sauraren abinda ake fad’a mata, bayan kamar 5 minutes tace;

“Okay”.

Tana gama fad’in haka ta ciro wayar daga kunnenta ta katse kiran. Car key d’inta ta d’auka ta mik’ama Saimah tace;

“Ki fita da motar da kika gani waje, nima zan fita da taki akwai inda zanje, ina so ki wuce da yarinyar nan wurin aikinki, idan na dawo zan biya in d’aukota”.

Kai kawai Saimah ta gyad’a mata, tana mamakin Kuzeem a ranta, don ta kasa gano komai tattare da ita, karb’ar key d’in da Kuzeem ta mik’o mata tayi kana ta mik’a mata nata Car key d’in motarta tare da mik’ewa ta kalli Binta tace;

“Tashi muje”.

Ba musu ta mik’e tare da bin bayan Saimah da ta nufi hanyar fita kana suka fice daga palorn. Kuzeem kuwa kallon agogon hannunta tayi taga har 11:20am tayi, mik’ewa tayi ta nufi wurin trolleyn ta dake ajiye a palorn, tare da bud’e zip d’in sama ta ciro wani file mai d’auke da tarin takardu ta ajiye gefe, sannan ta bud’e ainahin babban zip d’in trolleyn ta ciro wata maroon satin silk gown, da wani glass golden wanda cikinsa yake orange, daga haka ta rufe trolleyn.  

Wasu maza biyu dake tsaye a d’an nesa da Estate d’in na ganin fitowar su Saimah, sukayi saurin fad’awa cikin motarsu tare da bin bayan su cikin dubara yanda wani ba zai fahimci su suke biya ba.

D’an kallon jikinta tayi,  Allah ya sani tana buk’atar tayi wanka saidai babu lokacin da zatayi wankan da zai gamsar da ita a halin yanzu, a gurguje ta tub’e abayar dake jikinta sannan ta zura rigar da ta d’auko, ba k’aramin kyau tayi mata ba, veil d’in rigar tayi rolling kanta da shi tare da kafa tsadadden glass d’in a idanuwanta wanda yayi azabar yimata kyau, ya k’ara fiddo da karan dogon hancinta sosai, duk da bata fesa turare ba amma hakan bai hana ma jikinta fitar da sanyayyen k’amshin turarenta ba mai shegen dad’i.  

D’aukar file d’in tayi tare da nufar wurin da wayarta da Car key ke ajiye ta d’auka, sannan ta fice daga d’akin, kai tsaye wurin da Saimah tayi perking motarta ta nufa tare da bud’e k’ofar motar ta shiga sannan ta tada, a hankali ta fara yin baya kana ta juya motar cike da k’warewa, tare da nufar hanyar get, daidai lokacin wata arniyar mota ta kunno kai cikin get d’in, hakan yasa Kuzeem dakatawa har saida motar ta shigo sannan taja motar ta fice daga gidan. 

A harabar wani tsadadden eatery Saimah tayi perking sannan ta bud’e k’ofar motar ta fita tare da zagayawa ta bud’ema Binta ta fito, kana ta rik’a hannunta suka nufin cikin wurin. Fuska d’auke da mamaki mutanen da ke biye da su suka kalli juna sannan d’ayan yace;

“Mun samu matsala ba yarinyar ba ce a cikin motar”.

D’an shiru d’ayan yayi sai can yace;

“Tabbas ba ita ba ce, amma kuma ai a airport munga lokacin da ta shiga cikin motar kuma tunda suka baro airport d’in ba’a tsaya da ita ko ina ba sai cikin Nagarta Estate balle muyi zaton ko ta fita daga cikin motar ne”.

“Gaskiya da sake bari mu kira Alhaji mu shaida masa, domin mu samu mafita don wallahi da zaran munyi sake wannan aikin ya wuce mu tabbas mun tabka babbar asara”.

“Kaji shirme, kai a tunaninka in mun kirashi zamu samu wata mafitar ne?, tou bari kaji wallahi bamu gayawa Alhaji, tsayawa zamuyi a nan har sai wannan yarinyar ta fito mu bita muga inda zata koma”.

Tafiyar kusan 40 minutes Kuzeem tayi sannan ta iso cikin wata area da shirunta yayi yawa, saboda jefi-jefi mutane ke gilmawa, kuma babu gine-ginen gidaje a wurin saidai manyan gini masu kama da Company’s.  Gaban wani tafkeken gini Kuzeem ta tsayar da motarta tare da d’an sauke glass d’in gefenta tana k’arema wani symbol dake gefen wurin kallo, wanda aka rubutama *MCTV RADDAL*

Mayar da glass d’in tayi sannan ta fara danna horn, cikin sauri get d’in wurin yayi wani irin zugewa gefe tamkar an turashi saidai babu kowa a wurin, ba bata lokaci Kuzeem ta cillah kan motar cikin farfajiyar had’ad’d’en gidan talabijin d’in, wanda yayi mugun k’ayatuwa duk inda ka kalla saika sake kallo, komai a tsare yake gwanin birgewa, babu kowa a wurin saidai tun kallon farkon wurin zaka sha jinin jikinka saboda na’urorin dake wurin ba ma gaskiya ba ne.  

Kai tsaye perking lot ta nufa tare da tsayar da motar, sannan ta d’an jingina bayanta ga kujerar da take zaune tare da fara danne-danne a wayarta, cikin Email d’inta ta shiga tare da d’aukar wata Special number da aka turo mata, sannan ta kira number,  tana jin an d’aga kiran tace;

“Hey I’m Kuzeem Yusuf Garba, gani na k’araso a cikin wurin”.

“Okay mun ganki, yanzu za’a zo a shigo da ke”.

Abinda aka fad’a mata kenan, d’an murmushi Kuzeem tayi tace;

“Alright!”.

Daga haka ta katse kiran sannan ta d’au file d’in gefenta ta bud’e motar ta fita tare da d’an jingina da jikin motar tana k’arema tsarin wurin kallo don ba k’aramin birgeta yayi ba, tsawon 3 minutes sannan ta hango wani babban mutum ya fito ta cikin wata k’ofa, kallo d’aya tayi mashi ta d’auke kanta ta mayar kan na’urar da mutumin ya bayyana a cikinta. Fuska d’auke da murmushi ya iso wurinta tare da fad’in,

“You’re welcome Kuzeem Yusuf Garba”.

D’an murmushi Kuzeem tayi masa bata ce komai ba, daga haka yace ta biyosa, hakan yasa Kuzeem ta bi bayansa suka nufi k’ofar da ya fito.

Tun Mom Eshmal na zuba idanuwan ganin dawowar Binta harta cire ranta, sai mamakin take meyasa tak’i dawowa, tunda ta san ba yau ta saba cin ubanta ba kuma bai hana ta dawo. Shigowar mijinta ya sanyata saurin mik’ewa tana kallonshi, da mamaki tace;

“Honey lafiya ka dawo?”.

Kan kujera ya zauna tare da d’an shafa kan Eshmal dake bacci kan kujerar kana yace;

“Tafiya ce ta kamani shiyasa na dawo in sake d’an watsa ruwa”.

“Ina kuma zaka je?,  duka yaushe ka dawo RISAM zaka wani ce tafiya ta kama ka”.

Wani kallo yayi mata sannan yace;

“Tou zan miki k’arya ne?”.

Saurin gayyato murmushi tayi akan fuskarta, tace;

“Ba haka nake nufi ba”.

“Okay, ina Binta?”.

Wani irin bugawa k’irjinta yayi, tayi shiru tana kallonsa ba tare da ta bashi amsa ba.

“Wai bakiji ina tambayarki Binta ba?”.

Ya fad’a a d’an fusace ganin Mom Eshmal tayi shiru, gefenshi ta zauna tare da d’an had’e rai ta cinno baki gaba sannan tace;

“Honey sai faman tambayar yarinyar nan kake, sai kace dafata nayi na cinye”.

Wani kallo ya watsa mata kana ya maida dubonsa saitin d’akin da Bintar ke zama, cikin d’an d’aga murya yake fad’in,

“Binta!, Binta!!”.

Dak’yar Mom Eshmal tayi k’ok’arin daidaita nutsuwarta, tare da yakice tsoron da ya mamaye zuciyarta, tace;

“Honey bata nan fa”.

“Tana ina?”.

Murmushi tayi mishi tace;

“Wallahi ta raka Mom Arif unguwa ne, ka san Binta mutuniyarta ce”.

“Okay!, dama naso kira mata Nafisa ne su d’an gaisa, tunda kwana biyu bataje wurinta ba, jiya ma muke magana da ita akan batun School d’in da nace miki zan sanyata”.

“Allah ya taimaka Honey, gaskiya samun irinka zaiyi wuya a wannan lokaci”.

Inji Mom Eshmal har lokacin fuskarta na d’auke da murmushi. 

“Ameen Ameen ai yiwa kaine, ko kin manta kirkin Nafisa ne?”.

“A’ah ina kuwa zan manta?, tunda ga ‘yarta nan ta bamu sukutum”.

“Tou kin gani, ai saidai kawai fatan mu rik’e amanar da ta bamu, ko don maraicin yarinyar”.

D’an kawar da kai gefe tayi tare da tab’e baki sannan tace;

“Hakane kam”.

“Yawwa, tashi ki had’amin ruwan wankan, in kama jiki”.

“Angama mai martaba”.

Mom Eshmal ta fad’a kana ta mik’e ta bar wurin tana sauke ajiyar zuciya.

                     ******

Kuzeem na biye da mutumin har suka iso cikin wani babban office mai kyan fasali da tsaruwa, wanda mutane hud’u ke zaune a gaban wani dogon table, kowanensu na danna laptop d’in gabanshi, shigowar su Kuzeem ya sanyasu dakatawa daga abinda suke. Gefen macen cikinsu mutumin ya nuna ma Kuzeem alamar ta zauna, babu b’ata lokaci ta isa wurin tare da jan kujera ta zauna fuskarta a sake.  Yayinda mutumin ya iso wurinta ya d’auki file d’in da ta ajiye akan table d’in, sannan ya nufi gefen d’aya daga cikin mutanen wanda da alama shine babbansu, ya ajiye masa file d’in a gabansa kana ya koma ya zauna.  

                   ********

“Kin k’oshi da abincin ne?”.

Saimah ta tambayi Binta, ganin ta daina cin abincin ta rafka uban tagumi.

“Eh”.

Binta ta fad’a a hankali, Saimah na k’ok’arin sake magana wayarta ta fara ruri hakan yasa ta d’aga kiran tare da fad’in,

“Hello Sis Hanan”.

“Wai ina kika tafi ne tun d’azun?, gashi za’a shiga meeting baki nan”.

Daga can b’angaren wata mace ta fad’ama Saimah, cikin sauri Saimah tace;

“Oh ganinan kan hanya Sis Hanan, thanks”.

Tana gama fad’in haka ta katse kiran tare da d’aukar Car key ta mik’e tana kallon Binta, tun kafin tace da ita wani abu itama ta mik’e sannan suka fice daga wurin.

“Yawwa gata nan ta fito”.

Inji d’aya daga cikin mutanen dake biye da su, da kallo suka bi su Saimah har suka shige cikin mota, nan suma suka shiga tasu motar tare da rufa musu baya, sunyi tunanin Estate d’in Saimah zata koma sai sukaga ta sanja wata hanyar,  suna biye da ita har ta iso Hospital d’in da take aiki, hakan yasa suka dakata daga biyarta don sunsan bazasu samu damar bin ta har ciki ba saidai suyi zaman jiran fitowarta.

                  ********

“Well done Kuzeem Yusuf Garba”.

Suka fad’a mata fuskokinsu d’auke da murmushi, itama murmushin tayi musu tace;

“Thank you”.

Wata doguwar takarda macen dake kusa da ita ta mik’o mata, tace;

“Ki duba dakyau duk abinda baki fahimta ba zaki iya tambaya”.

Kai Kuzeem ta gyad’a mata alamar gamsuwa tare da karb’ar takardar ta maida hankalinta akanta, ta d’au tsawon wasu mintuna tana duba takardar kana ta d’ago tace musu duk ta fahimta, ba k’aramin dad’i sukaji da hakan ba, saida suka k’ara tattaunawa kana suka ba Kuzeem damar tafiya sai kuma Monday wato ranar da zata fara zuwa aiki.

Driving take cike da k’warewa, b’angare d’aya tana k’arema yanayin garin na RADDAL kallo, saboda yana d’aya daga cikin garuruwan da take jin dad’in kasancewa a cikinsu, musamman ma da ya kasance nan ne mahaifarta,  daga baya kuma ta tattara hankalinta wuri d’aya ta shiga nazartar wasu muhimman abubuwa. Saida ta tsaya wani tsadadden restaurant tayi take away abinci, sannan ta nufi asibitin su Saimah, tana isowa bakin get d’in asibitin tayi wani murmushi mai tarin ma’anoni ko mai ta gani?, oho, har tayi perking a harabar asibitin bata daina murmushin ba, tana fitowa ta wuce office d’in Saimah, saidai Binta kawai ta tarar don su Saimah sun shiga meeting, da wannan damar Kuzeem tayi amfani da ita wurin yima Binta tambayoyi, inda ta bata had’in kai d’ari bisa d’ari ta amsa mata duk tambayoyin da tayi mata, d’an shiru Kuzeem tayi tana nazarin abubuwa da dama a ranta, sannan ta d’ago ta kalli Binta tare da fad’in,

“Amma meyasa baki tab’a fad’ama Mijinta ba ko Mamanki?”.

Wani irin zaro idanuwa waje tayi tace;

“Haka tace idan na sake na fad’ama wani saita yanka ni, kuma dagaske take”.

Kuzeem bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba ganin yanda Binta ta zaro manyan idanuwanta, sai kawai Saimah ta fad’o mata a rai.

“Kina son na mayar dake gida?”.

“Eh Aunty, dan Allah ki maidani wurin Mamana”.

“Tou zan mayar dake gobe”.

Cikin tsananin murna Binta tayi tsalle ta rungume Kuzeem tace;

“Nagode Aunty, zan fad’ama Mamana ke mutuniyar kirki ce”.

Ba k’aramin tausayi yarinyar ta ba Kuzeem ba, hakan yasa taci alwashin saita koyama Mom Eshmal hankali. Suna nan zaune Saimah ta dawo, gefen Kuzeem ta zauna tana mata sannu da zuwa sannan suka fara d’an tab’a fira, wanda yawanci duk Saimah ce k’arfin firar don Kuzeem ba wani amsata take ba saboda hankalinta na kan wayarta tana duba wani abu. Sai misalin 2:30pm ta mik’e tace ma Saimah zasu wuce, nan kowacensu ta karb’i Car key d’inta, har harabar asibitin Saimah ta rakasu, sallama sukayi sannan suka shige motar, yayinda Kuzeem taja motar suka nufi get d’in asibitin na baya wanda ba kowa ya san akwai shi ba. 

“Miswar kaga motar d’azu”.

Hisham ya fad’a yana nunama Miswar motar Kuzeem da ta kunno kai cikin layin,  fuska a d’an tamke Miswar ya d’ago ya d’an kalli motar yana k’ok’arin d’auke kansa yaga motar ta tsaya a d’an nesa da inda suke.  

Kuzeem kuwa hango wani d’an tsoho zaune a gefen titi ya sanyata tsayar da motar domin ta bashi sadaka, a hankali ta bud’e k’ofar motar sannan ta fito.  Wani irin bugawa zuciyar Miswar tayi har saida ya lumshe idanuwansa, yanajin yanda bugun zuciyarsa ke k’ara tsananta, wanda tunda yake bai tab’a tsintar kansa cikin irin wannan yanayi ba sai a yau, sakamakon arba da yayi da Kuzeem, wacce baima gama tantance ya yanayinta yake ba, saboda akwai ‘yar tazara a tsakaninsu.

“Subhanallah!”.

Inji Hisham yana cigaba da kallon Kuzeem da ta nufi wurin d’an tsohon, sai kuma ya d’an kalli Miswar yaga idanuwansa a lumshe.

“Abokina kar in gani ni d’aya, bud’e idanuwanka kaga wata kyakkyawar halitta”.

Saurin girgiza kai Miswar yayi tare da fad’in,

“Ba buk’atar hakan”.

“Mtssww kai ka sani”.

Hisham ya fad’a yana maida hankalinsa kan Kuzeem da har ta mik’ama tsohon sadaka ta dawo wurin motarta, shiga tayi tare da jan motar ta bar wurin, Miswar kam ya kasa bud’e idanuwansa har lokacin don shi kad’ai yasan me yake ji.

“Wai Miswar lafiya kuwa?, meyake damunka ka wani lumshe idanuwa?”.

Cewar Hisham yana kallon Miswar d’in cike da mamaki, ba tare da Miswar ya bud’e idanuwansa ba yace;

“Babu komai Abokina”.

Kuzeem na shigowa cikin Estate d’in wayarta ta hau ruri, ganin Bilal ne ke kiran nata ya sanyata d’agawa, a hankali tace;

“Bilal ya ake ciki”.

Daga can b’angaren Bilal yace;

“Daidai Kuzeem, ya yanayin gidan da kike?”.

Bata bashi amsaba saida tayi perking motarta kana ta sauke wata ajiyar zuciya tace;

“Babu dad’i sam, naso in bar gidan a gobe saboda wani dalili, saidai akwai abinda nake son aiwatarwa tukuna”.

Murmushi mai sauti Bilal yayi kana yace;

“Da fatan dai bai shafi mutanen cikin gidan ba?”.

“Inhar abinda hasashenka ya baka kenan, to tabbas yayi gaskiya”.

Inji Kuzeem tana bud’e k’ofar motar ta fita, ‘yar dariya Bilal yayi yana mai k’ara jin zazzafar k’aunar Kuzeem a ransa, ina ma ace zuciyarsa nada k’arfin halin tunkarar zuciyar Kuzeem ta sanar mata sirrin da ke tattare da ita.

“Sai anjima”.

Sassanyar muryar Kuzeem ta tsamoshi daga duniyar bege da shauk’inta da ya fad’a, saidai bai koyi yunk’urin magana ba, har Kuzeem ta katse kiran, bud’e back seat tayi tare da ciro ledodin take away da tayo.

Cikin sauri Mom Eshaml da tun dazun dake tsaye bakin windown palorn ta tana zaman jiran dawowar Kuzeem ta fito daga palorn, tana isowa wurin su Kuzeem tasha gabanta tace;

“Ke k’aramar ‘yar iska ce, amma zan nuna miki nawa iskancin yaci uwar naki gaba da baya”.

Tana gama fad’in haka ta cafko hannun Binta da nufin janta su wuce, saurin sakin hannun tayi jin azababben cizon da Bintar ta gatsa mata a d’ayan hannunta, yayinda Bintar ta koma wurin Kuzeem da gudu.

“Kam ubanchan, ke Binta ni zaki ciza?, lallai..”.

Maganarta ta sark’ene ganin sun shige cikin gidan sun barta tsaye a wurin, cizon yatsanta tayi sannan tabi bayansu saidai jin k’ofar a kulle yasa jikinta yayi sanyi, bubbuga k’ofar ta shigayi tana surfama Kuzeem zagi kamar wata hauka sabon kamu, da dai taga alamar Kuzeem bazata bud’e mata k’ofar fa ta bar wurin.  

Kuzeem kuwa saida ta watsa ruwa ta sanja kaya sannan ta zauna cin abincin don ba k’arya yinwa ta tasota a gaba, ko don jiganiyar da tayi, tunda ta saba da rashin cin abinci da wuri, barinma yau ko breakfast bata yi ba, shiyasa abun yayi mata yawa.

Kusan mayar Mom Eshmal biyar tana bubbuga musu k’ofa akan Kuzeem ta bari Binta tazo, amma sukayi uwar shegu da ita tamkar basu san tanayi ba, dole ta hak’ura don kanta.

                    ******

“Rabson wallahi na gaji, haba sai kace wasu ‘yan iska tun d’azun muna kime wuri guda kamar wasu kayan wanki, kawai mu fad’a masa bamu ganta ba”.

“Matsalata da kai kenan Bash mugun d’an ujila ne kai wallahi, dama ba sai an wahala ake samu ba?, naga dai halas d’in mu ne muke nema tunda dai uban yarinyar nan ne da kansa ya sanyamu mu rik’a bimasa diddiginta, ai ko kaga ya yarda damu d’ari bisa d’ari to meyasa mu bazamu basa had’in kai ba?, kaga inkai baka iyawa kawai ka kama gabanka”.

Yana gama fad’in haka ya tada motar, ‘yar dariya Bash d’in yayi yace;

“Na fahimce ka abokina, ya kuma naga ka tada motar?”.

“Zamu tafi sai kuma gobe, tunda safe zamuje wurin Estate d’in mu tsaya, daga bisani mu dawo nan”.

“Tou shikenan hakan ma yayi”.

Inji Bash d’in, daga haka suka bar wurin.

*The following day*…….✍️

 

#Anup💋⁷⁶ ⁞⁰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *