YAR MAKIYAYA CHAPTER 13

YAR MAKIYAYA




CHAPTER 13




Uncle Ahmad yayi abunda ya dace, tambayar anan shine shin Dad zai hak’ura ya kyale Suraj sannan ya amince da Laila a matsayin suruka?
Ameer kuma fa? Wasan shi ya k’are ko kuma da saura? Saeed ma ba’a bar shi baya ba domin duk duniya babu macen da yake targeting irin Laila! +

Anya kuwa tsugunno ta k’are???

1:30pm

Sanssayar iska ce ke shigowa ta window wanda yayi sanadiyyar fire wa da labulen d’akin yake yi ,hasken full moon ya hasko cikin d’akin daga windon hakan yasa d’akin ya bada wani launin haske mai ban sha’awa da burgewa.

A tsanake ya bud’e idanuwan sa yana k’are ma d’akin kallo kafin ya yi yunk’urin tashi zaune ,rad’ad’in da yaji ne yasa yayi saurin rik’e cikin sa ya d’an saki k’ara gami da rufe ido.

Da sauri ta d’ago kai tana murza idanuwa wanda daga ganin su kasan barci bai isheta ba daidai lokacin ya juyo yana kallon ta cike da mamaki.
Zaune take a k’asa ta kwantar da kanta a gadon hannun ta cikin nashi.

“Laila?” Ya k’ira sunan ta ,ta d’ago kai suka had’a ido.

“Me haka kika yi? Ya zaki zab’i ki kwana a haka bayan ga gàdo ?”

“Kawai bana so in takura maka ne kuma ina kula ne kar ka fama ciwon ka”.
Murmushi yayi ya ce “Laila wannan ba hujja bane? Haka zamu yi Daren farkon? Amarya ta kwana a k’asa? No way! Taso ki dawo gado”
Zata yi magana ya katse ta

“Umarni na baki dan haka ki zo gareni” ba musu ta mik’e ta zagaya, duk takun ta d’aya ,duk motsin ta babu wanda Suraj yayi missing, ya kasa runtsa idanuwan sa sedai Murmushi da ya fad’ad’a a fuskar shi.

Zama tayi gefen shi ta jingina da gado kanta a k’asa. Kallon ta kawai yake yi kafin ya sauk’e idon shi a kan agogo yaga biyu saura. Hannun ta ya rik’e yace
“Kin kuwa san yanzu k’arfe nawa? Daga gani kina jin bacci ya kamata ki kwanta”

Bata kula shi ba sam, dan haka ya fisgo hannun ta bata ankara ba taji ta fad’o jikin shi, duk iya k’ok’arin ta ta kasa kwace kanta dan haka ta hak’ura tayi lamo a k’irjin sa , duk wani tafiyar bugun zuciyar sa tana ji , lumshe ido tayi ,duk lokacin da tayi tsammanin yayi bacci se tayi k’ok’arin zame jikin ta amma se ya k’ara matse ta a jikin sa yayi Murmushi, haka ta hak’ura barci b’arawo ya sace ta.

SURAJ’S POV.

*tun farkon had’uwar mu da ke, nasan k’aunar ki nake, Allah ya amsa addua na, kwatsam kika aminta da ni kika bani zuciyar ki ,and taught me to trust , a karo na farko a rayuwa ta! Yes, for the first time ever!*”

Kukan tsuntsaye ,iska mai sanyaya rai , ga kuma window mai ban mamaki wanda daga bakin sa zaka iya ganin wanda yake wajen Masarautar, tsaye yake yana k’urban cappuccino hankali kwance ko riga babu a jikin shi sai nad’in bandage da yayi masa d’amara. Sannan se towel fari da ke d’aure a kunkumin shi yana Murmushi kafin ya juyo ya k’ura mata ido yayinda take sharar baccin ta tayi d’add’aya duk gashin kan ta ya baje rabi ya rufe fuskar ta. Ajiye mug d’in yayi ya k’arasa kan gadon ya kwanta gefen ta ya k’ura mata ido babu ko kyafta wa kafin ya sa hannu ya yaye gashin duk tana baccin ta harda gyara kwanciya

“Sweetie” ya furta kamar mai yin rad’a yayi sa’a kuwa ta bud’e ido , rau rau tayi da ido ganin shi yayi mata rumfa, k’irjin ta yana dukan uku uku tana neman hanyar zame masa kamar zata yi kuka da kyar ta samu hanya ta zille masa tana dariya shi kuwa da gangan ya saki k’ara
“Ahhh Wayyo!!”
Ba shiri ta dawo ta kama hannun shi tana tambayar menene matsalar , janyo ta yayi ta fad’a jikin shi yace

“An gaya miki ke kad’ai ce mai wayo? Sweetie bazan tab’a bari ki zille min ba ko da wasa” haka tayi ta k’ok’arin kwace wa amma ta kasa saida yayi niyya don ransa ya hak’ura ya sake ta yana dariya.

 Da gudu ta bar wajen gadon ta nufi bathroom
Shafa kansa yayi sannan ya sauk’a diga gadon ya nufi closet   yana neman kayan da zai sa, in the mean time ya shirya tsaf cikin bak’in jeans ya d’auki ocean blue shirt ya saka sannan ya nufi bakin madubi yana saka mab’allan rigar.

K’ofa bathroom ta bud’e ta fito Sanye da bathrobe gashin duk a jik’e se d’igan ruwa yake ,hakan ba k’aramin burge Suraj yayi ba, hannun ta ya janyo ya zaunar da ita kan stool gaban mirror ita de nata ido, towel yasa ya tsane gashin sannan ya k’ona hair dryer ya fara bud’ar mata da gashin.

   Kwankwasa k’ofa tayi a tsanake ,hakan yasa. Suraj ya juyo ya kalli kof’an kafin yace 
“Shigo”.
Ba b’ata lokaci ta shigo d’auke da lafiyayyen breakfast ta ajiye sannan ta tsaya a nutse tace

“Barka da Safiya Yallabai, ko akwai abunda ya kamata nayi?” Kai ya girgiza yace

“Fati Ki dawo nan da twenty minutes and tidy up the room for now zaki iya tafiya”. Cikin ladabi ta fice kai a sunkuye. Ya juya yaci gaba da abunda yake yi .
Its not over Suraj!   Bazan tab’a bari kayi nasara , ban saba fad’uwa ba am not a loser! Yanzu asalin wasan zai fara! +

Uncle Ahmadu ne ya shigo yana kallon Ameer da ke ta faman b’ab’atu idanuwan sa har sun chanja yace
“This is what I call my own son!

Albasa bata yi halin ruwa ba, daman tun da naji matsala ta taso nasan cewa dole kana da hannu a ciki , Ameer kabi duniyar nan a hankali, babu ribar da zaka samu in ka shiga tsakanin d’a da mahaifi kuma d’an ma jinin ka ! Bazan ce komai ba yanzu amma nan gaba kad’an zaka fahimci illar abunda kake aikata wa, ni ubanka ne , akwai rana tana nan zuwa zaka tuna this very day! Cewa na tab’a maka gargadi. Kana da zab’i biyu walau ka gyara walau ka yi watsi da abunda na fad’a amma zan yi abunda ya dace a matsayi na na uba, zan cigaba da maka adduar shirya don wannan cuta ce wallahi”. 
  Uncle yana kai nan ya fice ya ja k’ofa Ameer ya bi k’ofar da kallo yana Murmushi.

     “Ki shirya ina zuwa, bar na je na sallami abokai na ,nasan jiya komai bai tafi daidai ba zan dawo yanzun nan” kai kawai ta girgiza tana kallon yadda ya gyara mata gashi tsaf ya daure tayi Murmushi sannan ta mik’e ta nufi closet tana neman kayan da zata saka….

    Da tangad’i ya shigo ya tsaya yana k’are wa falon kallo kafin ya nufi saman bene yana Murmushi daga gani kasan cikin maye yake duk ya addabi hadiman dake kai kawo daga downstairs zuwa upstairs kowacce sai ya yi k’ok’arin shafa jikin ta su kuma sai rakub’e wa suke wasu na sakin k’ara duk suka yi b’arin abinda suka d’auko dedai lokacin Suraj ke sauk’o wa diga upstairs a tsanake yake bin staircase d’in har ya kawo inda suke

“Saeed! What the hell is this? Miye hakan kake yi ka bar su su wuce mana! Wannan fa cin zarafin mata ne ko ka sha giya ne?”

Jin muryar Suraj yasa Saeed ya mance batun Y’anmatan ya matso kusa da Suraj daf da shi kamar zasu shige jikin juna kafin ya bud’e baki zai yi magana

Da sauri Suraj ya kawar da kai gefe yana toshe hanci yace
“Ewww! Yanzu Saeed da girman ka rana tsaka zaka sha giya kayan maye ka shigo kana molesting mata haka? Wannan ya sab’a wa doka da kuma koyarwan wannan gidan.

“Hahahhaha! Look who’s talking! Angon ka sha k’amshi, nima Nazo ne in fad’a maka abunda ka aikata ya sab’a wa dokar Saeed!  Y’ar Makiyaya tawa ce ni kad’ai! Abun mamaki kuma se gashi ka Aure ta, Nazo in d’auki kaya na Nazo in d’auki kaya na!!”

Wani tafarfasa zuciyar Suraj ya fara yayi k’ok’arin ya bawa Saeed lafiyayyen naushi se kuma ya sauk’e hannun sa ya Hankad’a Saeed gefe guda ya fice yana gyara tsayuwar rigar sa ya sauk’a daga staircase saida ya isa tsakiyar falo yace “Guards”.

Da sauri wasu katti hud’u suka shigo kamar daga sama suka zube suna jiran umarni daga Suraj

“Ku fitar min da wancan abun sannan in kuka kuskura ya sake shigo min sashen sena yi muku abunda Baku tab’a tsammani ba!

Jiki na rawa suka fara kokawa da Saeed suka yi waje da shi se barazana yake yi musu.

“Kai! Ku kyale ni nace kun san ko ni waye kuwa? Am the second in line to the throne you can’t treat me this way!!”
  Tsaki Suraj yayi yace “second in line to the throne? A wannan rashi dabi’u masu kyau d’in wa zai iya baka mulki stupid!” Yana kai nan ya girgiza kai ya fice ,jiki a sanyaye matan suka cigaba da ayyukan gaban su.

     Da kyar ta iya zab’in abunda zata saka shima da taimakon Fati, bayan ta gama da lingerie ta d’auki tsadadden dogon rigar ta na atamfa me launin turquoise ta zira tana k’ok’arin rufe zip ta kasa ga Fati ta fita…..

  K’ofar sashen ya biyo ,wannan karon ta baya ya shigo se rangaji yake yana gauraye hanya yana tafe yana bud’e duk wata k’ofa da yagani, Fati ya hango ta fito daga wata k’ofa Hanan ya tabbatar masa cewa a nan Laila take dan haka ya lab’e seda Fati ta wuce sannan ya k’arisa gami da tura k’ofar d’akin ya bud’e yana dariya duk idanuwan sa sun kad’a
Hannuwan sa biyu yasa ya tokare k’ofar yana kallon yadda take kokawa da zip ta kasa rufe wa

    Jin motsi yasa ta jiya ,tabbas ko daga bacci ta tashi wannan fuskar bata manta shi ba,nan da nan jikin ta ya d’au b’ari yana  rawa ta fara ja da baya ,ganin ya iso daf da ita gashi abun tsoro hakan yasa ta kwalla ihu  har Sau biyu yayinda Saeed yayi sanadiyyar chafke ta se tirka tirka suke tana k’ok’arin kwatar kanta ga bata daina ihu ba

    Tare da Habeeb da Sapna suka shigo sashen nasa suna hira basu ankara ba suka jiyo ihu ,cikin firgici Suraj ya ruga a guje yace “Laila”? Haka Sapna da Habeeb ma suka bi shi.Duniya budurwar wawa #fact. +

    Saeed yana k’ok’arin rungume Laila ta zame k’asa ta sulale ,ganin ta samu ta kwace kanta bata tsaya b’ata lokaci ba ta ruga waje har tana fad’uwa inda suka ci karo da Suraj ya rik’e ta gam amma duk da haka k’ok’arin kwace wa take don bata lura cewa Suraj d’in ne ba, d’akin da ke opposite ya bud’e ya tura Laila ciki sannan ya ja k’ofar ya rufe duk da haka bata daina k’ok’arin kufce wa ba. daga gani yasan ta gama fita hayyacin ta dan haka ya sumbace ta a baki, suka tsaya a haka har saida yaji numfashin ta ya daidaita jikinta yayi sanyi sannan ya d’an janye jikin sa ya d’ago fuskar ta yace

“Ya isa nine Suraj, zauna pls.”  Tana zauna wa bisa kujera sarkin zuciyar ya juya ya bar d’akin gami da janyo k’ofar ,direct d’akin da Saeed ya iske Laila ya shiga ya kuma yi sa’a Saeed yana nan kwance se surutai yake .marasa kan gado 
  A zuciyance Suraj ya fisgo shi ya dinga surfa masa mari yana jibgan shi har jikin sa rawa yake gashi duk k’ok’arin Habeeb na yaga ya fisge Suraj daga jikin Saeed ya kasa da abun yaci k’arfin sa kawai ya k’ira Dad a waya, Habeeb yasan bai kamata ya k’ira Dad ba amma yasan zuwan Dad zai sa Suraj ya bar fad’an don in har mom ya k’ira sasu zatayi a gaba tayi ta kukan ta.

     Cikin k’ank’anin lokaci bandage d’in da akayi wa Suraj dressing ciwon sa duk ya tashi daga launin fari ya koma jajir don ciwon ya fame.

“Suraj!!!!!” Dad ya k’ira shi gami da fisgo shi da k’arfin tsiya ya kafa masa mari , shi kuma Saeed ya fad’a chan gefe guda yana rawar jiki dan ya narku da duka ba kad’an ba Suraj ya had’a masa jini da mijina.

“Kayi hauka ne? Suraj are you exactly in your senses? Yanzu Ashe har zaka iya fitar wa d’an uwan ka jini? Me kake tunani? In ka kashe shi fa?”

Wani Murmushi ne na tsantsar takaici ya bayyana a fuskar Suraj ya dubi Habeeb daidai lokacin su Mom suka shigo su ma ya dube su kafin ya maida duban sa ga Dad yace

“Of course Dad ! Am in total control of my senses, ai Wannan karatu ne wanda na koya a makarantar ka Dad! Jiya jiya ka d’aura min Wannan karatun kuma yau na bada hadda, jiya ka tabbatar min da cewa fitar wa wani naka jini ba aibu bane ,

  As a son! Ka fitar min da jini saboda na auri y’ar talaka kuma *y’ar MAKIYAYA* wanda ban tab’a jin wata ruwaya ba da ta hana mai arzik’i auren talaka ba but remember Saeed as an elder brother ya shigo nan ne yana k’ok’arin keta wa mata ta na sunnah haddi kaga kuwa se yadda k’arfi na ya k’are , wannan ma kad’an na masa duk ranar da ya k’ara kamanta abu makamancin haka Toh Lallai sai na nuna mishi nima ba tayar baya bane yadda ko sunan Laila yaji se ya chanja hanya!”

  Mari Dad ya k’ara wanka wa Suraj yace “ni kake fad’a wa haka? Because of Wannan kaskantacciyar?”

Kai Suraj ya girgiza kafin ya kalli Dad cike da mamaki yace ” bazan yi mamaki ba, tun ina k’arami ban tab’a yin abu da ya kasance dedai ba,a gun ka komai ba daidai bane, some times se in dinga tambayar kai na ko shin kai mahaifi na ne? Coz ……….

Marin da Mom ta bawa Suraj yasa yayi Shiru yana hawaye kai a sunkuye ta fisgo Suraj ta yanda saida ya zube a kan gwiwar sa ,ga azabar ciwon da yake ji a cikin sa ga jiri da ya k’i barin shi har idanuwan shi rufe wa suke tace

“How dare you speak to your father like this? Wannan ba koyarwan da nayi maka bane,ba karantar war addini bane Suraj dan haka ka nemi gafarar mahaifin ka”   Suraj babu yadda ya iya haka ya bawa Dad hak’uri sannan mom tace a basu waje kowa ya fice ciki har da Suraj wanda duk iya k’ok’arin da Ummi tayi dan shawo kansa ya bari likita ya duba shi amma fir ya k’i , hankalin ta a matuk’ar tashe yake ,daga k’arshe ma k’ofar d’akin da Laila ke ciki ya bud’e ya shiga sannan ya dannawa k’ofar lock.

   Jin motsin shi yasa ta ruga ta rungume shi Amma yanda taji jikin shi a wani sake se ta d’an zame jiki tana kallon sa cike da fargaba. Da kyar ta yi supporting d’in shi suka shiga d’aki ta kwantar shi kan gado sannan ta juya domin k’iran Ummi ko Mom.

  Hannun ta ya rik’e da kyar yace “bana buk’atar taimakon kowa! Kawai zan nuna miki abunda zakiyi ”  first aid kit ya nuna mata ta d’auko haka ya dinga gwada mata yadda zata yi tayi treating ciwon kuma tayi ,cikin k’ank’anin lokaci Suraj yayi bacc finally away from damuwar su Dad and co.

Amma ni Jiddah ina da tambaya! Anya za’a bar Suraj da Laila su ci amarci cikin kwanciyar hankali??

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *