DAN ADAM CHAPTER 3
Wani sanyi da daddadan kamshin (roomfreshner) ne ya soma yi musu marhabin kafin dariya da hirar jama’ar falon ta doki kunnawansu. Suka shiga da sallama, Ummi gabanta banda bugu babu abinda yakeyi. Ga wadanda kunnensu ya ji suka amsa musu sallamar, wadanda basu ji ba kuwa, sai hira suke. Babban falo ne wanda ba’a cikashi da kayan ado sosai ba, saidai iyakar wadanda aka dan kawatashi da su masu kyau da tsada ne. Kujeru masu jikin leda farare tas ne zagaye a tsakiyar falon, iyayen na zaune saman kujera harda dattijon kwarai, wato maigidan Alhaji Atiku Modibbo, tare da uwargida ran gidansa, mahaifiya ga Hajiya Fatima, Hajiya Madina da karamarsu gaba daya wato Hajiya Sadiya(Hajiya Mama). Sune a zaune saman kujera, su kuwa jikokin suna a kasan tattausan kafet din dake shimfid’e a tsakar falon. Kallo d’aya Ummi tayiwa 6angaren da suke tayi gaba ta bi bayan Amina zuwa inda ta nufa. Tsakiyarsu ne Amina ta shimfid’a katuwar leda ta cin abinci, suka ajiye komai anan. Anan ne ta ji Amina ta shiga gaishesu, itama ba shiri ta gaishesu. Ba zata iya tantance wadanda suka amsa ba da kuma wadanda basu amsa ba don kuwa sauri takeyi su bar wajen, haka kawai ta kara jin ta raina kanta, ji take kamar wari takeyi ma tsabar kamshin wajen. Cikin yaren fulatanci ta ji wata cikin yanmatan tayi magana da bata fahimci ko menene ba. Gaba daya matasan suka dara, tana ganin sadda wani a samarin ya jefamata filo. “Baki da kirki.” Daga haka bata da masaniyar abinda ya karu don kuwa tuni sun bar wajen sun sauka da niyyar dauko sauran kayan. Larai ta taimaka musu itama. Haka sukayita zirga-zirga, bayan sun kammala kawowa, suna shirin tafiya, Hajiya Mama tayi musu magana. “Yauwa Amina sauranku lemu da ruwa ko?” “Toh.” Amina ta amsa. “Muje.” Cewar Amina tana duban Ummi wacce ke tsaye. Suka nufi falon kasa, suna jin sadda Hajiya Fatima ke tambayar Inna ko Ummi sabuwar yar aikinta ce. Inna ta amsa da aa, Hajiya Mama ta sanarmata a wajen Mami take. Nan fa Alhaji ya hau fadan yawan chanje-chanjen masu aiki da takeyi. Daga haka basu kara jin tattaunawar ba suka yo k’asa suna dariya don abin ma dariya ya basu. Amina ta dubeta. “Kinsan wani abu kuwa? Duk fa abin su Mami, suna gudun abinda zai 6ata ran iyayensu, duk abinda suka ce suyi basa musawa shikenan ta zauna. Wallahi suna burgeni yanda suke kaunar iyayensu.” Ta karashe lokacin da take kokarin bude firij. Ummi tana murmushi tace “Toh Anti ai sune abin alfaharin, idan baka da mai maka fad’a ina wani jin dadi a rayuwa?” Amina ta jinjina kai sadda ta soma ciro lemuka tana dorawa a saman firjin. “Gaskiyane kam, mik’o tire a kicin mu dora.” Larai ta tambaya ta mikamata, ta goge sannan ta koma suka dora akai, wannan karon Ummi ce a gaba tana biye da ita, saida suka zo daidai dan korido wanda daga shi sai kofar shiga, ta ja baya ta marairaice. “Don Allah Anti shiga gaba.” Abin sai ma ya bawa Amina dariya, babu musu ta shiga gaba da sallama sannan itama Ummin ta bi bayanta. Ido hud’u tayi da wannan matashin na dazu, ya tamke fuska ya kauda kai, hakan da ta gani yasa itama dauke nata idanun da sauri ta cigaba da tafiya a tsanake, tuni sun soma zubawa, har Hajiya Fatima na yiwa wani cikin matasan fada akan bayason cin abinci alokacin da kowa yake ci, wanda akeyi domin shi murmushi kawai yakeyi. “Shiyasa fa bana sonshi, wannan idan mukayi aure mai yiwuwa nima haka zai dunga hora ni da yunwa, barni dai na lalla6a da Gadanga.” Cewar Inna kenan, aka sanya dariya gaba d’aya. “Kai tsohuwa, dad’ina dake kenan. Ai Faruk banda harkar neman kudi bana jin akwai abinda yasa a gaba, yanzu sai ya juya miki biyar zuwa dubu.” Cewar wani wanda ga dukkan alamu shine babbansu, don fuskarsa kadai ya nuna akwai shekaru. “Yauwa Usmanu, ashe ka fahimta.” Ummi da Amina tuni suka bar wajen, Amina na rike da Samir d’a awajen Rahila babbar d’iya ga Hajiya Madina. Haka sukayita zolayarsa ko kusa bai mayar da martani ba, asalima banda murmushi babu abinda yakeyi, idan kuma abin ya wuce murmushi, sai ya dara. Acan k’asa suma abinci suka ci sukayi nak, bayan sun kammala kuma sukayi zaman hira har zuwa sadda akayi kiran sallar La’asar. Sai lokacin samarin suka sauko, Ummi ta bisu da kallo kamar yanda Amina ta umarceta. Ta kara jaddada mata cikin rad’a-rad’a. “Kinga na farkon nan mai dan jiki shine babban d’an Hajiya Babba ta Abuja, Yaya Usman yana da matarsa d’aya da yaransu uku, na biyun shine Yaya Faruk, shine autansu baiyi aure ba, na ukun mai farar shadda shine Yaya Ridwan, shima yana da matarsa daya ‘yar Ghana ce, yaransu biyu. Na karshen shine Yaya Haidar, shi ake shirye-shiryen bikinsa yanzu tare da Yaya Intisar babbar d’iya ga Hajiya Mama, bikin baifi ragowar sati uku ba.”