YAR NAJERIYA CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
SADAUKARWA
Sadaukarwa ne ga dukkan ALBINISM din Najeriya….
You are special a yadda Allah ke son ganin ku.
+
“YAR NAJERIYA
Na taso cike da dokin ranar zuwan ziyarar ‘yan makaranta, ba don komai ba sai don in ga Inna ta, na san kuma Inna zata kawo min kanzo, kuli da kwaki, wadanda su ne kadai abinda nake samu a kowanne visiting, sabanin sauran dalibai masu uba a raye, idan aljihun Inna da dan nauyi (in ta samu surfe mai yawa) kafin zuwan ranar ziyarar mu to tana hadomin da mankuli, manja, da dunkule wani lokacin har da busashishiyar yakuwa (rama) wadda zan dade ina jikawa ina kwadantawa.
Makarantar mu makaranta ce ta hadakar ‘yan Najeriya (UNITY COLLEGE) wadda nayi nasarar samu sabida hazakata ba don ina da gatan zuwan ta ba. Duk fadin kauyen mu na fi kowa kwazo a karatun boko da na muhammadiyya har wani suna ake kira na da shi (Huda-Huda ‘yar Inna) wasu su ce (Mungu Park ‘yar Inna) sabida tsabar son karatu na da son Inna ta.
Bayan son karatu Allah yayi ni da son tsafta, wadda aka ce itace cikon addini, duk da irin halittar da yayi min wadda ta banbanta data sauran al’umma, kai bazaka ce girman kauye bace kuma tashin kauye, sabida yadda nake kula da tsaftar jiki na. Tsaftar da Inna kan ce aljanu ke sani yin ta, domin ta wuce misali. Na taso ban san kowa ba sai Inna ta ban kuma shaqu da kowa ba sai ita, mahaifi na tun ina ciki ya rasu, kuma nice kadai diya ga iyaye na. Sannan ba kowa ke son mu’amala da ni ba (da mutum mai irin halitta ta) sai wadanda muka zamewa dole.
Mahaifi na Mal. Dabo dan asalin karamar hukumar Kabo ne ta jihar Kano, wanda sana’ar sa ta iyaye da kakanni itace ‘jimar fatu’. Da wannan sana’a yayi aure ya kuma rike Inna ta da mahaifiyar sa Kaka A’I. kakata A’I bata tare da mu yanzu haka, tana can garin Kabo.
Mahaifiya ta ‘yar asalin garin Kachako ce inda ci-rani ya kai mahaifi na ya auro ta, bayan auren su ya taho da ita garin su wato Kabo suka zauna gida daya da mahaifiyar sa A’I. duka-duka auren bai rufa shekara biyu ba ciwon ajali ya kama mahaifi na Malam Dabo, kuma bai dade yana jinya ba ya amsa kiran mahaliccin sa.
Mahaifiya ta Inna Zulai ta cigaba da rainon ciki na a gidan mahaifi na har ta haife ni. Na zo da halittar data barranta data kowa a gidan mu, ga dai kyau har kyau amma zabiya ce, don haka ni ban gado kalar fatar jiki na a wajen iyaye na ba kamar sauran zabiyu, kudurar Ubangiji kadai ta sa aka haife ni haka.
A lokacin ne manema suka fara kawo mata caffa, don haka A’I tace ta yaye ni ta bata ni ta samu ta yi aure, amma Inna ta kafe kan cewa ita ba auren da zata yi raino na kawai zata yi har karshen rayuwar ta, sabida irin halittar da Allah yai min, da ba kowa ke son raba ta ba, sannan bata son tayi wani aure da zai sa a kira ni AGOLA. Ko in rasa mai kulawa da ni sabida rauni na.
Zaman mahaifiya ta da kakata A’I sai ya canza salo bayan rasuwar mahaifi na, sabida A’I ta dage sai ta yi aure shine mutuncin ta kuma ta gaji da dawainiya da mu, ta kan ce “da wannan zabiyar ‘yar taki wadda ba miji zata samu ba”. A karshe ba tare da shawara da ita ba ta amsawa wani malamin makarantar sakandire Malam Saminu da ya nace yana son auren Inna ta.
Rannan A’I ta fita makota sai dawowa tayi ta tarar babu mu babu alamun mu a gidan, Inna ta goye ni mun bar Kabo, cikin bacin rai, don har ta fara gayyatar daurin auren Inna ta, muka koma garin Kachako gidan su mahaifiya ta, iyayen ta duka sun kwanta dama gidan na gadon su ne ita da Yayan ta Sama’ila.
Yaya Sama’ila na zaune a gidan da matar sa Hajjo, sai mahaifiya ta ta share daya bangaren na iyayen su muka yi zaman mu. Nan Inna ta fara tunanin sana’ar da ya kamata mu fara don mu dinga samun na cin abinci kasancewar Yaya Sama’ila shima fama yake da kan sa ga nauyin iyali duk da haka yana da matukar zumunci akan Inna ta duk abinda ya samu daidai karfin sa yana bata, sana’ar sa itace noman Rake.
Garin Kachako na nan a karamar hukumar Albasu ta jihar Kano. Gari ne ni’imtacce da al’ummar garin duka masu zuciyar nema ne, kusan babu wanda bai da kwakkwarar sana’ar da yake cin abinci da ita, tashin farko muka soma sana’ar danwake da wake da shinkafa a tashar Kachako. Kuma babu laifi muna samun rufin asiri, ni nake wanke kwanuka tare da mikawa masu bukata in an saya. Da muka dan yi karfi muka buga rumfar kwano anan cikin tasha muka saka dogayen bencina guda biyu suna kallon juna.
STORY CONTINUES BELOW

A wani marece Yaya Sama’ila ya shigo yana ta fada kamar zai ari baki wai akan Dagaci yace ya kai su Hassan makaranta su daina sayar da Rake, cikin fushi yace “in sun daina sana’ar Rake shi Dagacin ne zai ciyar damu? Karatun nan da aka ce yana maida ‘ya’ya kafurai su kuma fi karfin iyayen su zan dauki Hassan da Hussaini in kaisu? Mu da bamu yi karatun ba me ya same mu? Hajjo na kara zuga shi da cewa “ah to dai, ka biyewa Dagaci ya lalata maka ‘ya’ya su zama ‘yan daba in bazasu saida rake ba”.
Innata na jin su haka kawai sai taji tana min sha’awar ni in yi karatun, ni da banida future, ‘ya’ya iri na dole su nemi madogara a rayuwa ko su kare da bara bisa titi, madadin bin ta tasha dana ke yi muna sayar da danwake sai ta zaba min zuwa makaranta. Sanin halin YaYa Samaila yasa bata yi shawara da shi ba ta wanke hannu tayi lullubi ta kama hannu na muka tafi gidan Dagacin garin Kachako.
“Allah ya taimaki Dagaci ga ‘ya ta HASNA’U marainiya ce, ina so a sata makaranta, daga nan har zuwa lokacin da zata isa aure, duk da bana jin zata iya samun mijin aure”.
Dagaci ya sanyawa Inna albarka yafi cikin Kwando tare da cewa “‘yar ki mutum ce lafiyayya kamar dan kowa, ki daina maida ita koma baya sabida Allah yayi mata halittar zabiya, ya ce inama sauran jama’ar gari zasu yi koyi da Innata, su kawo nasu ‘ya’yan ya hada da nasa suyi karatun zamani, da mun fita daga duhun jahilci mun shiga sahun ilmin zamani da ke kara karfi a kauyuka a wancan lokacin.
Daga wannan lokacin na fara karatun firamare tare da ‘ya’yan Dagaci da wasu tsirarun ‘ya’ya da ga al’ummar kauyen mu duk da karatun ba wani mai inganci bane amma mun koyi Huruful Hija’iyyah da rubutu da karatun haruffan boko dana Hausa.
Sanda na gama karatun firamare ba da jimawa ba gwamnatin Tarayya ta kafa UNITY COLLEGE KACHAKO, a matsayin mu na wadanda suka samu alfarmar yin firamare mune dalibai na sahun farko (pioneers) a Kachako wadda ta hada dalibai daga kowanne yanki na Najeriya ciki har da ‘yan kudu da yammacin Najeriya.
Na fara Unity Kachako da kafar dama domin babu jimawa kwakwalwata ta dinga budewa karatu yana shiga, sai a lokacin nasan a firamare ba karatu muke ba, ga islamiyya muna yi da yamma a renakun mako, ga abinci wadatacce gwamnati na bamu a wancan lokacin makarantu sun fi samun gatan gwamnati sabida neman masu yin karatun ake yi ruwa a jallo.
Ubangijin da ya halicce ni sai ya halicce ni ba kala daya da sauran mutane ba, bansan cewa halitta ta abin kyama bace kuma abin gudu sai da na fara sakandire, inda ya kasance makarantar kwana, na gane ba kowa ke son mu’amala da ni ba haka ba kowa ke cin abinci dani ba, ke ko kayana babu mai tabawa sabida Allah ya halicce ni ZABIYA.
“Albinism” halittar Allah ce ga daidaikun bayin sa, yadda yake halittar kowa haka yake halittar zabiya, yawanci gado ne amma ni ba gado bane, farin mu ya wuce misali sannan bama jure zafin rana, gashin kanmu ba baki bane kamar na kowa, sannan masu halittar “albino” na fama da raunin gani (short-sightedness).
Duka ban gane haka ba sai da na fara shiga shekarun balaga, a baya na dauka fari na is normal sabida babu mai goranta min ko kira na ‘zabiya’. Sai zuwana Kachako da naji ana kira na ‘Hasna-Zabiya’. Sai na gane ni ba fara bace mara lafiya ce, abin kyama ga wasu daidaikun al’umma.
Amma hakan bai sagar min da gwiwa ga neman ilmi ba, na saka a raina bazan taba aure ba, zan yi ilmi har sai naga karshen sa. Wanda zai sa in samu abin yi da zan kula da kai na da Innata.
Yau ta kasance ranar ziyarar dalibai, tun safe mun sha wanka mun zuba wankakken uniform muna jiran iyaye da ‘yan uwan mu. Ta fanni na nasan babu wanda zai zo min sai Inna, don haka ina daga layin farko na masu rarraba ido don jiran nasu amma har kusan azahar babu Inna ta.
Sai na koma gindin wata bishiyar darbejiya na zauna abin duniya ya ishe ni, na hada kai gwiwa amma ba kuka nake ba, tunanin halin da Inna take ciki shi ke damu na, don bata taba tsallake rana bata zo min visiting ba. Ga yunwa da ta fara galabaitar da ni. Sai nasa kai na a tsakanin gwiwoyi na, ni kadai nasan irin damuwar dake cunkushe a kasan rai na. Bazan manta ba shekaru na goma sha shidda a lokacin.
Kamshin masculine turare na ji a hanci na mai karfi na maza, sannan naji ana Magana kasa-kasa a kai na.
“Are you alright?”
Da farko ban zaci da ni ake ba sai da aka kara maimaitawa tare da sunana
“Hasna’u are you okey?”,
Da sauri na dago ido na dubi mai Magana; he’s tall and slim, shi ba fari ba shi ba baki ba, gashi nan dai wankan tarwada mai kyawun siga kuma ma’abocin tsaftar jiki wanda kallo daya zaka yi masa ka fahimci ilmi ya wadata a tare da shi. Sannan bai nemi komai ya rasa a rayuwa ba.
Kusan zan iya cewa na taba ganin sa sau daya ko biyu, a rashin sani na shine wanda zai juya duniya ta daga yadda take zuwa ga inda ban taba mafarki ba, zuwa ga inda bana fatan kai kai na, shine wanda zai juya kaddarori na daga yadda nake fatan su. Sannan shine tsanin da zan taka ya ruguzo da ni daga kan kyakkyawar turbar dana ke kai.
Da bai shigo rayuwata ba da watakila komai ya cigaba da tafiya min normal a yadda Allah ya halicce ni na kuma mallaki ‘mental well-being’ dina dai-dai. Kada ki ce ko kyawun sa da tsaftar sa ne ya rude ni a’a, wata irin ‘kamala’ ke gare shi da kwarjini mai daukar hankali da ba duk ‘yan adam suka mallaka ba.
A cikin muryar sa akwai ‘maturity’ da ‘intonation’ mai nuna sanin ciwon kai, a nitse yake magana tamkar ba daga bakin sa take fita ba, yana daga cikin masu kula da asibitin makaranta, ko likita ne ko ma’aikacin jinya shine abinda ban sani ba, sau biyu na je clinic da bani da lafiya kuma shine ya bani magani ya kuma sa nurse ta yi min allura.
“I’m alright Sir”,
Na bashi amsa a lokacin da na dago idanuna masu rauni da suka kada suka yi jawur na dube shi, haduwar idanun da ya janyo rushewar duk wani tubali da na aza harsashin rayuwa ta a kai. Na cewa har abada bazan yi aure ba….tunda ni ZABIYA ce…..