SAINA AURI MARUBUCI CHAPTER 4 BY Xayyeesherthul-humaerath
Dubawan da zai yi kuwa ya tarar group din cike yake ba damar Kara wani in ba wai wani ko wata sun fita ba.
Komawa Private ya yi tare da fadin, “Ba waje fa, group din acike yake sai dai ki bata hakuri ta jira ko wasu zasu fita.”
Har cikin ran Farida bataji ba dadi ba Sam kawai sai ta ce, “To ni dai in an samu hali asata Dan tana da bukatar kasancewa agidan matukar gaske.”
Wa she gari
Shiru shiru Nafeesa ta ga ba asata A group ba hakan ya sata Kiran Nusaiba,Nusaiba na ganin kiran Nafeesa ta kau da kai tare da yin tsaki, aranta take mita, “Kai wallahi Aunty bata kyautamin ba zata ja min raini.” Ficewa tai fuu sai bangaren Anty Farida, tana shiga ta fara, “Haba Aunty Dan Allah, kina so yarinya ta rainani ne wai? Tun jiya kisa asata a group kin ki.
Farida ta ce, “Oh ni kam dai, na bada number ta daman na Fada miki group din acike yake,dole sai wani ko wata ya fita kan asata Amman har na bada numberta.”
Nusaiba ta ce, “Ok shi ke nan Amman wallahi ko ta kira ma ba zan kara daukaba sai dai kawai ta gannta a group ta Kara ganin girmana ma,ba na son raini.”
Dariya Farida ta yi, “Allah dai ya shirya mana kai.”
Da Ameen Nafeesa ta amsa kan ta fice fuu kamar yadda ta shigo.
********Kwanaki nata tafiya har sati Amman ba asa Nafeesa a group ba, hakan ya Sa ta tsintar kan ta da fara rubuta wani littafi Wanda ta mai lakabi da SHI NAKE SO, kamar wasa ta Sa A group din su nan take taga an fara rububi tare da fadin cewa tayi ma su cigaba Dan Allah, har da ma su binta private suna hadata da Allah kan cewa labarin ya yi dadi ta cigaba.
Mamaki Nafeesa take har cikin ranta shin itace take rubutu kamar yadda Nafseen ke yi? Shin itace ake ta rububi kan karanta labarinta,ji take tamkar amafarki domin salo da tsarin rubutun sak irin ba shi ta bi,tamkar shi ke tsara mata labarin, ba mai tunanin cewa sabuwar marubuciyace.
Misalin karfe biyar na Ranar ba yan ta gama tura littafin rububin sharhi ya ragu tana kokarin kashe data da mamakinta kawai sai ganinta tayi tsimdin acikin wani group mai taken MARUBUTA.
Nafeesa ba ta San lokacin da ta tashi tana murna da ihu ba tare da washe baki,kara kallon wayar tai tare da rungumarta, “Alhamdulillah, Allah na gode maka.”
Gyara zama tayi tare da wata nutsuwa ta mussaman ta shiga cikin group din, hira ake ba ji ba gani raha da wasa, wannan ya tsokani wannan wancen ya tsokani wancen abun gwanin sha’awa bin hirar ta fara yi ba tare da tace uffan agidan ba, sai dai ga Mamaki har yanzu bata ga alamar gilmawar Nafseen ba,Wanda ko wani suna ta gani sai ta kura ido Amman har yanzu bataci karo da shi ba.
Ganin cewa da alamar duk yan gidan na da saukin kai ya bata damar yin sallama.
Nafeesa “Assalam alaikum”
Wani ba da ba a tantance mace ne ko na miji ba kasancewar ba suna ya ko ta ne amsa da “Wa’alaiki sallam Yan mata.”
Nafeesa ta yo reply da , “Ina Hini Yaya zan ce ko Aunty.”
Da alamar murmushi aka maido mata da amsa, “duk Wanda kika zaba kina ganin ya yi miki to ba tantama.”
Tsintar kan ta murmushin da ya bayyana har a zahiri tayi tare da fadin, “To ina ganin dai Yayane.”
“To, aiko kin canka na Yarda ke din fasihiyar marubuciyace.” Ya maido mata da reply.
Kan Nafeesa tai Reply
Karaf……
Wani ya yi sallama agidan.
Alamar murmushi “Umm.” Kawai Nafeesa ta tura sannan ta amsa sallamar da Mai suna Dan gidan Imam ya yi.
Wancen ko ga duk alamu ya sauko domin bai kara fadin komai ba.
Sauran Mutanen Gidan Mata da Maza duk sun fito sai hira ake, Nafeesa da surutu kamar wasa arana guda har ta fara sabawa da Mutanen cikin Group din Marubuta Amman gabadaya hankalinta na waje gudu damuwarta ta ga gilmawar Masoyin nata Amman shiru har ta fara fidda rai.
Rufe data kawai tai domin lokacin sallar La’asar ya yi kamar yadda ta ga duk sauran yan group din na fadin lokacin sallah ya yi atashi ayi,har cikin ranta tsari da yanayin group din ya burgeta yau daya.
Alwala ta dauro sannan tai sallah ta jima tana addu’o’i tana idarwa ta gyara zaman glass din ta afuska, sannan ta duba wajen littafanta gani tai kaf ta karance su duk da ta saba maimaici daman Amman taji aranta cewa tana da bukatar Sabi,hakan ya sa ta duba jakar makarantarta Kudin da Mammah ke bata na kashewa bata kashe take Tarawa daukowa tai taga dubu daya ne da ita a yanzu, tsaki ta yi, “Ni kam ma ko za su isheni in siyo oho.”
Janyo hijabinta tai tasa Wanda ya rufe mata jiki har kasan kafafunta,ta fito falo ba Mammah hakan ya bata damar nufan kichin domin ta San in bata falo to tana kichin.
Jin alamun taku ya sa Mammah ta daga batare da Nafeesa ta isa gareta ba, Murmushi ta yi, “Ah Ammien Abhi ina zuwa da yamma haka? Ina shirin Sa Sabeer ya tasoki ki karba girkin ina son yin wani bincike.”
Nafeesa ta shagwabe fuska, “Ayyah Mammah agidan su Maryam zani in karbo littafina an bamu assignment kuma ma ba zan Iya ni daya ba tare zamu yi.”
Mammah ta ce, “To Allah ya kiyaye hanya,ki kula bana son shashanci kin sani ko? Ki kama kanki kamar yadda shigarki ta nuna kuma karki kai dare.”
Murmushi Nafeesa ta yi, “To Mammah in sha Allah zan kiyaye sai na dawo,Sabeer byebye.”
“Bye bye Anti ki siyomin chocolate.” Cewar Sabeer ya na wasa
Nafeesa na fita ta nufa gidansu Maryam da sallama da shiga,Aunty ce zaune afalo tana kallo, ta amsa mata da fara’arta, “Ah Yau Nafeesa ce agidan namu? Lallai munyi babbar bakuwa.”
Nafeesa na Murmushi ta durkusa, “Ina hini Anty?.”
“Lafiya lau Nafeesa fatan kina lafiya,ya su Mammah kuma?”cewar Aunty
Nafeesa ta Amsa da, ” Duk lafiya lau, Aunty Maryam fa.”
Kan Aunty ta bada amsa Maryam ta fito da Sauri, “Oyoyo Habeebbty muryarki naji kamar amafarki Ashe da gaske ke din ce.”
Aunty ta tashi tana, ” kamar an shekara ba aga juna ba,ina jin dai miji daya zamu Baku.”
Dariya kawai Maryam da Nafeesa sukai.
Nafeesa na ganin Aunty ta Shiga daki ta ce, “Habibbty littafi zaki rakani siyowa karya nawa Mammah nace assignment zan zo muyi, kin San in taji littafi zan siya zata hanani wai idona yanzu ma karatun aboye nake wallahi kuma ni ba zan Iya dainawa ba.”
Maryam ta ce, “Allah Habibbty da gaskiyar Mammah so ki ke ki rasa idanun naki gabadayane? Haba Dan Allah yakamata ki rage karatunnan fa.”
Rike hannun Maryam ta yi, “Dan Allah Habibbty kar Ku toshemin hanyar farincikina,karatun littafinnan kadai ke bani walwala da nishadi,Ina son karatun littafin Marubuci Nafseen kuma inda rai da rabo watarana sai na ganshi kuma na auresa muddin ina numfashi.”
Magana take hawaye na gangarowa daga cikin idaniyanta.
Maryam ce tasa hannu tana goge mata ya yinda itama ta fara kwallan, “Ki daina Kuka Habibbty zaki gansa kuma zaki auresa in sha Allah,yanzu bara na fadama Aunty ta ba dreba motarta ya kai mu kasuwan ko?”
Nafeesa ta ce, “Eh jeki dawo akwai labari Nima na zama marubuciya fa.”
Maryam ta fito tana dariya, “ai ke kam zaki Iya zama labarin ma da kansa ba mai rubutawan ba.”
Da key din motar Aunty Maryam ta dawo ahannunta yawwa, “Habibbty muje.”
Suna fita Maryam ta baiwa dreba key ita da Nafeesa suka shige baya tare da fadin ya kai su sabuwar kasuwa.
Dai,dai gun masu saida littafi inda Nafeesa ta saba siya Maryam ta ce dreba ya tsaya.
Aiko Nafeesa ta yi nasara zuwa domin sababbin littafan marubucinta har biyu sun fitofito,SO SHAMATAR ZUCI Da kuma YAN MAZA.
Nafeesa ta kasa Boye farincikinta hakan yasata sai was he Baki take awajen.
Sun gama siya ke nan Nafeesa ta hango shagon da ake saida Films, ta ce, “Habibbty zan siya film.”
Maryam ta kalleta cike da Mamaki, “Habibbty ke da bakya kallo me za ki yi da film kuma?”
Harararta Nafeesa ta yi, “To na fara kallon daga yau,ni muje shagon cen mu siya.”
Binta kawai Maryam ta yi domin bata da tacewa.
Da sallamarsu suka shiga shagon cikin fara’a kuwa mai shagon ya amsa.
Nafeesa ta ce, “Films muke so Amman Wanda marubuci Nafseen ya rubuta.”
Murmushi mai shagon ya yi, “Ah madam an gama daman ko duk wa’inda ya rubutane Sabin fitowa Dan dazu da safe ma na karbo biyun nan,SIRRIN DA KE RAINA, NIDA KE MUN DACE, Da sauri Nafeesa ta karba tana mai yi masa godiya tare da mika masa kudin.
Suna komawa Mota Maryam ta ce, ” Yawwa Habibbty kin ce min kin zama marubuciya tayaya?”
Dariya Nafeesa tai, “Ta inda kowa ke zama mana duk abin da zai hadani da Nafseen dina kusa gareni koma miye zan Iya ina tabbatar miki da hakan,na fara rubutu na zama marubuciya domin kasancewata da shi kawai.”
Maryam ta gyara zama , “Kice min kun hadu ma.”
“Umm haba dai ba ajima da sani ba,kuma kaf na duba cikin group din ba mai irin sunansa Abu daya na rike akullum jikina na bani cewa yana group din,ko da wannan aka barni ina jin dadi araina.”
Murmushi kawai Maryam ta yi domin bata da tacewa, sai da su kai Nafeesa har gida sannan suka koma na su gidan.
***Tun da Nafeesa ta koma bayan ta yi sallah kallo kawai ta Sa tanayi.
Mammah ta ce, “ai da karatun littafancen gwanda miki kallonma wallahi.”
Nafeesa ba ta ce komai ba sai murmushi.
Sai da Nafeesa ta gama kalle films din tsaf wajen 10 kan ta tafi daki ta kwanta, sha biyun Dare dai,dai ta fara mafarkin Nafseen na Online kamar da wasa ta farka,ji ta yi barcin ya bace a idonta gabadaya,wayarta ta dauko ta kunna,abun mamaki tare suka hau online awannan lokacin.
Sallama ya yi agroup din marubuta kasancewar komin dare ba a rasa yan surutu aciki.
Nafeesa…….¹¹