YAR NAJERIYA CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

BAKIN  KANON-DABO (MAGANA ZARAR BUNU….)

Kwanaki goman suka zo suka shude kamar kiftawar ido, a cikin kwanaki goman nan Hasna’u gata nan ne dai, ita ba mara lafiya ba ita ba mai lafiya ba. Uncle Saheeb bai kara neman ta ba yana can yana ayyukan sa amma komai yake yana tuna Hasna’u, yana Allah-Allah ranar hutu ta zo su tafi Kano tare. Yana so yayi amfani da wannan damar ya kara sanin Hasna’u ya kara jan ta a jiki ta saba da shi ta yadda zata iya gaya masa kowacce irin damuwa take ciki. Ya alkawartawa ransa zama bango abin jinginar ta wanda har nauyin karatun ta zuwa jami’a zai dauka in har Kawu Sama’ila zai bar ta.+

Aka ce yau da gobe kayan Allah, a kwana a tashi ba wuya yau Asabar ranar hutu ta zo. Tun asubah da Hasna’u ta dawo masallaci sallahr asubah bata koma barci ba, wanka ta yi ta sanya wankakkun uniform din ta wadanda ta ninke suka kwana kasan filon ta suka bada Karin guga. Sayayyar da Saheeb yayi mata tana nan cikin bagco ko rabi bata cinye ba. Cancanawa tayi ta ta yi don ta kaiwa Inna itama ta ci kayan dadin da ta ke da tabbacin ba ita ta aiko da su ba.

Kusan itace farkon fita daga hostel zuwa bakin get da bagcon kayan ta guda biyu, daya kayan sanyawar ta ne a ciki daya sayayyar Saheeb. Tun jiya Jumaah an basu hutu wanda in suka dawo zasu zana SSCE. Hasna’u zata gama Unity tana da shekaru goma sha bakwai cif. Watakila da ta san abinda zata je ta taras a gida da ba ta ci wannan wankan da wannan gugar ba, yau har kwalli ta saka wanda bata saba sakawa ba kuma ya taimaka wajen daidaita kalar kwayar idanun ta.

Daga nesa ta hango Uncle Saheeb na tahowa, kyakkyawan matashin basakkwace dogo siriri, fatar jikin sa luf-luf ta ‘ya’yan hutu wadanda suka dama suka kutsa cikin zuzzurfan ilmin boko mai tafiya da zamani, ya dau wanka ya dau kananan kaya masu daraja samfurin ARMANI CODE riga da wando designers kalar fari da ratsin baki, kai kace bakin fatar kasar Ethiopia ne, musamman da ya kawo siririn gilashi mai haske irin nasu na likitoci ya saya kwayar idanun sa.

Tun kan ya iso gaban ta kamshin turaren sa ya riga shi wanda har ta riga ta gane shikadai ke da wannan masculine kamshin a fadin makarantar wanda bazata ce ko na wane turare ne ba.

“Hasna’u are you ready?”

Ya tambaya muryar sa na ‘yar rawa, in ya tuna abinda zata je ta taras a gida. Da far’ar ta tace “ai tun tashin asubah ban koma barci ba Uncle, sabida yadda na matsu in ga Inna, ko barci ban samu ba jiya don bamu taba dadewa irin haka bamu ga juna ba”.

Saheeb sai ya juya ya kama tafiya, bayan ya sunkuya ya dauki bagcon nata guda biyu cikin kokarin hadiye kakkarfan hawayen da ke son balle masa.

“Biyo ni Hasna muje, we’re almost late”.

A parking lot na staff ta ga sun doshi wata kankanuwar mota mai kyau, dark blue, tunda Hasna take bata taba shiga motar gida ba sai yau, daga motar Rake sau Bus din kauyen su. Kofar gaba ya bude mata bayan yasa kayan ta a booth ya rufe.

“Hasna mu je ko?”

Ya fada yana rufe mata kofar motar, treating her just like a queen of the queens with care and caution. Koda ta zauna ya rufe mata kofar ya zagaya ya zauna a mazaunin sa, sai ya sunkuyo yana sanya mata belt. Hucin sassanyan numfashin sa ya sauka a wuyanta sannan wannan kakkarfan masculine scent din ya nashe ta har fiye da kowanne lokaci.

Ji tayi numfashin ta yayi sama, yana sassarfa tamkar zai dauke. Saheeb bai kula ba tsakanin sa da Allah belt ya sanya mata don ya san bata iya ba.

Saida ya karanta addu’a a fili ta neman tsari daga sharrin karfe sannan yayi reverse ya fita daga harabar Unity Kachako suka hau kan burjin da zai kai su titi. Sai ya kunna mata a|c ya kuma kunna sautin Shaikh Abdurrahman AS-Sudaith cikin Suratul Nisa’i. Shiru ya ratsa a motar baka jin komai sai sautin Sudaith-Abdurrahman da kuma karar a|c wadda ta soma takurawa Hasna’u. Tunda take bata taba jin sanyi mai ratsa jiki irin wannan ba. Sai ya lura tana takure jikin ta cikin hijabinta kamar mai jin sanyi.

STORY CONTINUES BELOW

Ya rage gudun motar yana tambaya “ko in kasha ne Hasna’u?” “da dai ya fi min” ta bashi amsa da sauri. Murmushi yayi ya kasha a|c din suka cigaba da tafiya.

Barci mai alaqa da yunwa suka soma fizgar Hasna’u, tayi hamma ya kai sau uku Saheeb na hankalce da ita, yadda yake hankalce da duk wani motsin ta cikin motar baya kula da tukin motar haka. “Yaya dai Hasna, barci?” “Umh” kawai tace, tana cigaba da hamma.

Sai ya mika hannu zuwa kujerar baya ya dauko wani dan madaidaicin foodflask ya mika mata. “ungo nan ki ci wannan kan mu isa Kano, eat fast, I cooked it for Hasna’u.

Tun jiya na fere dankalin nasa a firij ina idar da sallah na soya shi”.

Hasna’u sai taji dariya na son kwace mata don bata taba jin namiji da girki ba.

“Uncle baka da mata ne?”

Ya lura dariya take tana kunshe baki ta kuma karbi flask din da hannu biyu. Ya dubeta da kyakkyawar siga sannan ya maida kai ga tukin sa yana murmushi.

“Ana dai nema min har an kai kudi, amma ni gani nake ban isa aure ba”.

Dariyar Hasna’u ta fito fili yanzu, “me yasa kake ganin hakan? Katoto da kai haka? A garin mu kamar ka zaka samu yana da ‘ya’ya hudu”.

Ya rage gudun motar yana kallon ta keenly. “kice kema an kusa yi miki aure, tunda kin kusa gama makaranta”.

Nan da nan fuskar Hasna’u ta canza, wani yanayi mara dadi ya bayyana, duk abinda zai jawo mata gori da tozarci akan halittar ta tana gudun shi, ta san kuma aure shine a haqqu na janyo mata babban tozarci, don haka ta dade da haramtawa kan ta shi, kamar yadda Innar ta ma bata sa a ka ba.

“Kin yi min shuiru Hasna ko baki ji me nace ba?” tayi dan murmushi mai ciwo wanda ya fito daga kasan ruhin ta, a hankali ta yi Magana, wadda ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da bazai ji ta ba.

“Da dai a ce ba ZABIYA bace!!!”

Ta bashi amsa a gajarce.

Zuciyar Saheeb ta yi wani irin nauyi, wani ignition ya soki ran sa, sai da yayi nadamar sa ta yin maganar da ya ga hawaye sun tsatstsafo a idon ta. Sai ya tuna Hasna kwarin gwiwa take bukata daga kowa ba nuna raunin ta ba, ko nuna mata yes, ita din nakasahshiya ce.

Muryar sa da karsashi yace.

“Shi zabiyan ba mutum bane? Koko shi zabiya bashi da human feelings?”

Hasna’u ta yi shiru, don bata san ma’anar sentence din sa na biyu ba. Daga bisani ta ce “a wurin mafi yawan mutane hakane Uncle Saheeb, ba’a dauki zabiyan mutum komai ba, kamar wani aljani ake kallon sa. Just because of skin, eye and hair colour wanda ya barranta da nasu.

Duk da haka akwa mutane kalilan, very few, irin wannan da ke gefe na. (Ta dube shi da murmushi) kafin ta cigaba da cewa “Zuciyar ku daban take da ta sauran al’umma. Na gane hakan tun daga ranar da na hadu da kai, sai dai ka yarda irin ka din baku da yawa. You are extraordinary Uncle…..”.

Saura kadan ya karawa motar dake gaban sa, sabida yaddda kalaman Hasna’u suka girgiza shi, kallon wadda bata iya banbance komai yake mata ashe da hankalin ta da kyakkyawan tunanin ta.

“Hasna…!” Kawai ya iya ambato, sai ya rasa mai zai ce yayi shiru. Daidai lokacin da suka shigo Hotoro.

Hasna’u ta wara ido tana kallon birnin Kano, ta Dabo cigari ko da me ka zo an fi ka. Bata taba kiyastawa haka Kano take da girma da kyau ba. For the first time yau gata a Kano mai sunan Baban ta (Kanon-Dabo).

Kai tsaye Murtala Mohammed Specialist Hospital suka nufa. Dama tuni ya musu booking na ganin likita tun kafin su zo don ya san mutane a wurin, amma koda likitan ya duba Hasna’u cewa yayi is better yayi referring din su zuwa Aminu Kano Teaching Hospital su ga Dr. Turaki (duba littafin KULSUM). Koda suka je Aminu Kano sun dade akan layi kafin su samu ganin ophthalmologist din.

“Ocular Albinism shine albinism mai taba lafiyar ido, kuma shine na Hasna.’u. Ka san Albi ism din kala-kala ne. In this case, a person might need to wear special glasses or ‘contact lenses’ don ta huta da saka gilashi kullum. Saidai kulawa da shi da wahala. Yanzu in kun amince zan saka mata ‘Eccentric Contact Lenses’ mai kyau a cikin idon ta. Bayan mun auna ‘nearsightedness (myopia) farsightedness (hyperopia)  and astigmatism’ din ta yanzu. Ku kwantar da hankalin ku ‘Ocular Albinism’ baya kasha ido gabadaya.

As she grow older idon ta zai ke gyaruwa. Kuma contact lenses ba’a sanin da shi a cikin idon mutum, sabida a kan kwayar ido ake saka shi”. Inji Dr. Turaki Gaya.

Saheeb yace “it will be difficult for Hasna’u ta iya kulawa da ‘contact-lenses’ sabida a kauye take kuma babu wanda zai taya ta kula dashi, disposable din kuma zai yi mata wahalar samu akai-akai, don haka ayi mata glasses kawai”.

STORY CONTINUES BELOW

Dr. turaki ya yarda da shawarar sa don haka ya tura Hasna dakin awon ido, bayan an rubuta prescription aka bata zabin gilashi karami mai kyau ta zabi wani shade dan siriri, Saheeb ya biya komai aka bashi sanda zai dawo ya karba.

A cikin AKTH ya kaita restaurant ta ci abinci mai rai da motsi, tana ci tana kallon sa ganin shi ko ruwa bai sha ba. Sai ta aje cokalin ta ta tura mishi plate din gaban sa.

“Na koshi Uncle”.

Ya dago daga kan wayar hannun sa cikin damuwa ya dube ta ya ce “babu dadi ne?”

Tayi rau-rau da ido tace “gani nayi kaima baka ci komai ba tun safe” sai yayi murmushi yace “kada ki damu da ni ni namiji ne, kuma sau biyu nake cin abinci a rana, amma yanzu to mu cinye tare”.

Ya debo abincin a spoon ya kai bakin ta, ta rufe ido cikin jin kunya amma sai ta kasa tankwabe wannan nagartacciyar kulawa ta Uncle Saheeb, ta bude bakin ya saka mata.

Sannan shima ya diba ya ci. With one spoon, one plate haka suka cinye abincin. Tun Hasna’u na jin nauyi har ta ware suka ci suka koshi, daidaikun mutanen dake cikin restaurant din sai kallon su suke. 1

Da suka gama tsaf ya bata tissue ta goge bakin ta yace. “Yanzu zamu je gidan mu kiyi sallah nima in yi, sai mu kama hanyar Kachako”.

Da sauri ta dago ta dubeshi da blue eyes din ta, sannan ta girgiza kai tace “a’ah Uncle, ka nema min masallacin mata inyi a nan”.

Seriously Dr. Saheeb ya ci magani “sabida me bazaki gidan mu ba Hasna’u?”

Ba komai Hasna’u ta tuna a wannan lokacin ba sai Maman sa, wadda ta ce “Allah ya raba ta da mummunar haihuwar zabiya”, kuma ta kwashi kafa ta je har gidan ta? Ta gan su again tare da Saheeb? Kamar ya san tunanin da take yi sai y ace “ta shi mu je, in dai Mama ce bata nan ta tafi seminar Abuja. Nusaiba ce kadai a gidan”.

In ta juyawa maganar Uncle Saheeb baya ai ya zama rashin adalci da rashin kunya, ta gama gane Saheeb ko me zai yi zai yi ne for her own benefit bai da wata riba a ciki. Sannan ba zai taba cutar da ita ba.

A hankali yake zura hancin motar zuwa cikin get din gidan wanda ke a sahun farko na unguwar Giginyu. Hasna’u ta daga ido tana kallon gidan su Uncle Saheeb, ko cikin mafarki bata taba ganin kyakkyawan farin gida kamar sa ba, hawan bene ne mai tsayi wanda ya kunshi sassa uku. A lokacin da maigidan ke raye daya nasa ne, daya na Sahib wanda ya kasance da namiji kwaya daya da Allah ya basu sai sassan Haj. Muneera wadda ‘ya’yan ta ke kira Mama, daura da dakin ta dakin auta Nusaiba ne.

Alhaji Bello Wamakko tsohon ma’aikacin SHELL ne. Wanda ya rike manyan mukamai a SHELL Company a lokacin rayuwar sa. Ya auri Muneerah a Kano wadda sabida ita ya bar Wamakko ya dawo Kano don tace bazata iya zaman kauye ba haka bazata iya zama a Sokoto ba. Ko a lokacin da yake raye kowa ya san mama itace mijin shine matar. Mama akwai son nuna isa da son ‘ya’ya kamar agwagwa. Haj. Muneera ‘yar siyasa ce ta gani kashe ni domin har mukamin senator ta yi, a yanzu kuma tana cikin shuwagababnnin jam’iyyar su.

Bayan rasuwar Alhaji Wamakko Mama bata kara yin aure ba sai rainon ‘ya’yan ta biyu, dai dai gwargwado mahaifin su ya bar musu dukiyar data ishe su rayuwa har suka tsaya da kafafun su. Saheeb (Abubakar Wamakko) kamar yadda abokan sa ke kiran sa yayi karatun sa a jami’ar Ahmadu Bello inda ya karanci MBBS (Medicine), a yanzu yana hidimar kasa a matsayin karamin likita karkashin hukumar hidimtawa kasa (NYSC). Shekarunsa 27 cif. Yayinda kanwar sa Nusaiba da suke kira Nusy take da shekaru 18. Zata kammala Unity a bana. Set din su daya da Hasna’u sai dai aji kowa da nasa, kuma babu wata mu’amala data taba hada su bayan ta ranar da suka wulakantata. Amma ta san ta, don jefi-jefi tana ganin ta.

Yayi parking a inda suke adana motocin su cikin wata rumfa mai ban sha’awa sannan ya juya ya dubi Hasna’u wadda ta saki ido da hanci tana kallon komai kamar cikin mafarki. Yanzu wannan muhalli ne da ‘yan adam ke zaune? Shi kansa Saheeb ta jinjina masa yadda ya iya barin wannan gidan ya tafi kauye ya zauna don hidimtawa kasar sa.

“welcome home Hasna, yanzu muje wajen Nusaiba ki sallah, if possible kiyi wanka don kiji karfin jikin ki, sai mu kama hanya, amma lallai ne kan mu isa Kachako sai magriba”.

Hasna’u  ba tace komai ba ta fito ya rufe motar, ta wani corridor suka bi sai gasu a wani yalwataccen falo komai dake cikin shi ruwan goro ne da ratsin lemon green. Nusaiba ce a zauna a daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon tana sanye da doguwar riga ta atamfa kanta babu kallabi, gashin kanta mai yawa sosai, tana kallon tashar Bollywood tana shan cornflakes a cikin wani bowl. Sahib ne yayi sallama amma Hasna’u a cikin cikin ta tayi tata sallamar. Zuciyar ta na dar-dar don bata san irin tarbar da zata samu daga Nusaiba ba.

Da sauri ta juyo tana kalonsu suna shigowa. Dogo da doguwa, black and white, cikin uniform din makaranta. A hankali idanun Nusy suka hau kara girma. Wannan zabiyar again? Bata san cewa a fili ta fada ba.

Saheeb yayi kamar bai ji ta ba, ya ce “Nusy ga bakuwa ta ki kaita tayi sallah pls yanzu zamu kama hanyar Kachako, in tayi sallah sai tayi wanka”.

Nusaiba ta zaro ido tana kallon sa da idanu a zazzare. “Yaya Saheeb? A toilet din wa? Kuma da soso da sabulun wa? Zabiya ce fa!”.

Saheeb ya kifa kai a jikin kofa ya rufe idon sa yayin da Hasna’u ta sunkuyar da kan ta. Sai da tace bazata zo ba ya takurawa baiwar Allah. Ya manta Nusy ba hankali. Gata da kyankyami. Shi ba’a bun ya dake ta ba ya firgita Hasna’u ko ya zageta Hasna’u ta ji mummunar kalma ta fito daga bakin sa.1

Kawai sai ya kama hannun Hasna’u ya jata zuwa ciki. Dakin Nusaiba ya kaita, ya bude mata toilet yace “shiga kiyi alwallah in kin fito ga darduma. In kika yi sallah sai kiyi wankan mu tafi” idon ta fal hawaye tace “kayi hakuri Uncle bazan yi wanka anan ba innaje gida zan yi” baya so ya tsaya ya ga gangarowar hawayen idon ta dson haka ya fita.

Rasa yadda zata yi tayi amfani da komai dake cikin toilet din tayi, she has never been in a place like this, gashi komai kal-kal tana tsoron kada ta bata wani abun. Da kyar ta yi alwala a tsaye cikin sink ta fito. Ta tada sallah kenan taji muryar Saheeb yana ta yiwa Nusaiba fada. Maganar da ya fada a karshe ita ta kusa sa ta sakin fitsarin da ta makale mata a mara bata yi ba don gudun kada ta batawa Nusaiba toilet.

“Gara ma tun wuri ki sayo majanyi da zanin goyo ki soma shirin goya ZABIYU, domin wannan zabiyar ce uwar ‘ya’ya na insha Allahu!!!

Fitsarin ya kwace ba shiri daga marar Hasna’u ya jika wandon makarantar ta tun daga sama har kasa……….

TAKORI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *