ZANEN DUTSE CHAPTER 1 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 1 BY AISHA-SHAFIEE

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Duk da girma irin na gidan sarautar KIYARI, babu lungu da sak’on da zaka kurd’a sautin wak’ar da ake gudanarwa daga can wajen kamun bikin bai shiga kunnenka ba, sannan ga mutane nan birjik! Tun daga bayi na cikin masarautar har zuwa tarin jama’ar gari da suke d’id’ikowa don gane wa idonsu shahararren bikin da aka fara gudanarwa a yau.+

Biki na gimbiya kuma ‘ya mace ta biyu a gurin mai martaba ‘Ahmad Uba Kamsusi’, Haka nan kuma biki na farko da aka fara gudanarwa a gidan sarautar tun bayan zamanin da mai martaba ya gaji mahaifinsa.

Duk inda zaka duba ko ka kalla ado ne na k’awa anyi shi birjik cikin nau’i kala-kala don burge al’umma da kuma dangin ango wanda suma suka kasance jinin sarauta daga garin Sakkwato. Ba wai barin mutane ake su k’arasa can inda ake gudanar da

Kamun ba, amma duk da haka saboda wadata abubuwa kai ba zaka ce ba ko’ina ake bikin ba, don kalolin abinci yawo kawai suke tsakanin mutane kowa na zab’ar ra’ayinsa yaci ya cika cikinsa harda guzurin na gida ma, sannan kuma kid’an daya karad’e ilahirin masarautar ma ya k’ara zirga-zirga da kuma hada-hadar mutane.

A cikin wannan hayaniyar Maijidda na can tsaye ita da Suraj daga bayan hanyar da zata kai ka shamaki inda babu wulgawar mutane sosai. Hannunta rik’e yake da wani kwando mai cike da wasu k’anana abubuwa masu kyalli sai juya shi take cikin yatsunta.

“Dan Allah ki gaya min mana, me Baddon tace da kika gaya mata?”

Muryarsa ta tambayeta a hankali amma cike da zumud’i. Ta d’an cije lebb’enta kad’an tana kallonsa sannan tace.

“Me kake tunanin zata ce?”

“Wallahi ban sani ba tunda kinga ai ba saninta nayi ai sosai ba, kawai ki yanke dogon zancen ki fad’a min ko zuciyata ta nutsu…”

Girarta biyu ta had’e alamun rashin fahimtarsa.

“To meye duk ka wani tashi hankalinka ka san dai ai ba zaginka zata yi ba ko?”

Maganar tasa shi dariyar da bai shirya ba a lokaci guda.

“Zagi kuma Jidda? Wa yake zancensa anan? Kawai fatana Allah yasa ta amince dani ne.”

Jin haka yasa ta juya ga barin kallonsa sannan ta d’anyi murmushi kad’an tace.

“Ai kaima ka san da tace wani abu da ba zan tsaya anan ina sake maka magana ba.”

“Allah da gaske kike? Bata ce miki komai akaina ba?”

Wannan rashin fahimtar ya sake dawowa kan fuskarta, ta juyo ta kalle shi.

“Me kake tunani zata ce? ni fa kawai tace min ne ta san Babanka ya tab’a aiki a b’angaren Fulani kafin ya koma wajen mai martaba, bayan haka bata ce komai ba.”

“Haka ne…” Ya fad’a yana gyada kai.

“… zata sanshi, Baddo ai ta dad’e a masarautar nan, ina jin tun farkon zamanin Sarki Uba take ko?”

Ta d’aga kanta a hankali.

“Na san dai tun mai martaba na yanzu bai yi aure ba suka zo ita da mamanta.”

Ya sake gyad’a kansa sannan yayi shiru kuma, zuciyar Jidda ta d’an matse kad’an, ta zata a lokacin ko zaiyi mata zancen turo iyayensa ko kuma wata maganar auren da zata kaisu ga mataki na gaba kamar yadda ta dad’e tana sak’awa a zuciyarta amma kuma baice komai ba.

STORY CONTINUES BELOW

Yatsun hannunta na dama na kanannad’e cikin hannun kwandon ta d’an b’ata rai, Allah ya sani zuciyarta tana bashi wata irin yarda tun daga lokacin da ta fara saninsa kafin ma yace yana sonta, amma kwanan nan yanayin mu’amalarsu yana yawan zana mata ayar tambaya a tunaninta… Bata jin kuma zata jure hakan gwara ta fito kiri-kiri ta tambaye shi me yake nufi game da ita, amma zata bashi lokaci dai tukunna.

“Jidda.”

Muryarsa a hankali ta katse tunaninta, ta d’ago da sauri ta kalle shi sannan a lokaci guda tunaninta ya wargaje saboda irin kallon da yake mata, ta san Suraj yana da kyau kuma saboda haka ma take sonsa ko don ace saurayinta na da kyau… Don irin kyan nan ne da baya cikin k’abilar Hausa-Fulani illa irin jinsinsa na Shuwa-arab, amma me yasa kullum take k’ara ganin kyan nasa ne?1

“Kin san me na taho miki dashi?”

Ya tambaya shima yana kallonta, sai ta sake k’ank’ame kwandon hannunta tana murmushi alamun dad’i kafin tace.

“Kace min fura.”

Ya girgiza kansa.

“Tanderi?”

Ya sake girgiza kansa.

“Awara? Dan Allah ya zama Awara?”

Ta fad’a tana langab’ar da kai had’e da k’ank’ance ido, hakan yasa shi dariya mai zurfi yana girgiza kai kafin ya mik’o mata ledar hannunsa.

“Allah ya amsa miki, Awara ce mai zafi ina zuwa gida na tarar Mama tayi.”

Ta karb’a da hannun dama ta bud’e, idanunta suka haska da kyallin murna da godiya sannan ta d’ago ta kalle shi.

“Jidda!”

Muryar Jamila data karyo kwana ta katse abinda shi da ita ke shirin fad’a.

“Yanzu tun dazu kina nan? Hankalin Baddo ya tashi an kusa gama wankan amarya, Jakadiya Babba sai fad’a take ba’a kawo kyallin ba.”

“Kinga kije kawai ba matsala, Gobe zan shigo ai insha Allah.”

Cewar Suraj sanda Jamilan ta k’araso inda suke tsaye.

“To shikenan, Nagode, Nagoode!”

Ta fad’a da k’aton murmushi tana sake damk’e ledarta.

Shima ya mata murmushin, sannan ya gaida Jamila da ka, kafin ya juya ya tafi.

“Allah zaki ci fad’an Baddo, da kika san wajensa zaki tsaya ba sai ki kawo mata aiken ba tukunna.”

Jin haka yasa ta d’an b’ata rai tace.

“Ni ai bata ce min yanzu za’ayi amfani dashi ba shi yasa da na ganshi na tsaya…”

Sai kuma tayi murmushi, ta nuno mata ledar hannunta game da d’aga gira.

“Kin san me? Awara ya kawo min.”

Jamila ta ja tsakin ta bata shirya masa ba kafin ta fizge kwandon hannunta tayi gaba.

“Wallahi abinda kike baya kyautuwa Jidda, nasha gaya miki da ace a wajen wata kike ba Baddo ba da tuni kinsa an dad’e da korar mu daga gidan nan, yanzu in banda sh*g*n kwad’ayi duk abinci da yake yawo a gidan nan me zaki yi da wata awara…”

Tana magana Jiddan na biye da ita, jinta kawai take yi don daga fad’anta har na Baddon ba wanda zai dameta, suna gamawa zata sami waje taci awararta, bata san kuma me ta manta ba bayan hakan.

“… Na rasa waye ya shiga kwakwalwarki ya goge miki sanin cewa a duniyar nan ba kowa ake yarda dashi ba, don wallahi bani ba na san ko ita Baddon ba son wannan Suraj d’in take ba.”

“Wai yaushe za’a daina zancen nan ne?  tunda nace ni ina sonshi ba shikenan ba.”

Ta fad’a cikin kunkuni sanda dogarawan dake tsaye suka basu damar shiga babban soron da zai sada ka da kwaryar gidan sarautar inda ake gudanar da bikin. Jamila ta harare ta da gefen ido sannan ta girgiza kanta kawai.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan tarin adon dake wajen idonka zai gano maka taron mutane birjik! Wand’anda ke zazzaune akan wasu tausasan dardumai kashi-kashi da aka tsara maimakon tebura, kowa cikin kwalliya sannan mafi yawansu rik’e da waya suna d’aukar wankan amaryar da ake gudanarwa daga tsakiyarsu, kan wani d’an dandamali da aka fitar masa da rariya musamman saboda bikin.

Amaryar, Gimbiya Aisha Ahmad Kamsusi, na zaune kan wani sabon turmi cikin shigar wata farar doguwar riga da lullubin farin mayafi yayin da tsofaffi dangin iyayenta ke ta kwara mata ruwan farar Humra suna zubo tarin addu’o’insu wanda ya had’e da yanayin wak’ar wajen ta yaren al’adarsu da aka kunna.

Jidda na iya hango fuskar Amaryar ta tsakanin matan dake kanta, ta sunkuyar da kai sai sheshek’ar kuka take, wani zaice ba itace mai d’agawar kan nan da zuba tarin rashin mutunci ga bayin masarautar ba kamar mahaifiyarta, Fulani Hafsatu, hamshakiyar uwargidan Sarki mai cika da izza.!

Allah ya sani tun zuwanta masarautar ranta baya son matar nan, saboda bak’in halinta da kuma bautar da kakarta keyi a k’ark’ashinta, bautar da tun kafin rasuwar mahaifiyarta ba irin k’ok’arin da ba’a yi akan ta bar gidan sarautar ba amma fafur Baddon tak’i, a cewarta yadda mahaifiyarta ta mutu k’ark’ashin kulawar masarautar haka itama zata koma ga Allah anan.

“Jidda tun d’azu muke nemanki, ina kika shiga?”

Muryar Sadiya ta fad’a sanda ta dafo ta daga baya.

“Wallahi Baddo ce ta aike ni can wajen Magajiya na karbo mata sak’o.” Ta bata amsa sanda Sadiyan ta tsaya kusa da ita.

“Taho muje ki zauna tare damu mana, ga inda muke zaune can ana ta hoto a wayoyin su Amina.”

Jidda ta juya ta kalli can inda ta nuno mata, darduma ce guda ta ‘yanmata irinsu ‘ya’ya ko jikokin bayin masarautar har da wadanda bata fiye ganinsu ba, dukkaninsu sun sha ado babu mai babanta su da sauran ‘yan bikin, don haka ne ma duk irin abincin da aka ajiye a kowacce darduma suma akwai a tasu, sai hayaniya suke yi suna d’aukan hotunan kamar yadda Sadiyan ta fad’a. Zuciyarta ta d’an had’e kad’an, taji zata so ace itama tana cikinsu ana hirar, amma sanin abinda zai biyo baya yasa ta girgiza kanta.

“Kin san bana son rashin mutuncin k’awayen nan naki Sadiya, don haka kije kawai.”

“Haba Jidda, wai ta yaya ba zaki manta komai bane ba, wallahi yanzu babu me miki ko kallon banza tunda kun riga kun fitar da raini.”

Ta sake girgiza kanta.

“Allah kije kawai, tare da Jamila ma fa nake, ta tafi kaiwa Baddo sak’on yanzu zaki ga ta dawo.”

Daga yanayin Sadiyan bata so haka ba, amma sanin Jiddan ba canja ra’ayi zata yi ba yasa ta gyad’a kai tace.

“Toh shikenan sai mun had’u a cikin gida.”

Bayan ta juya, Jidda ta sake hangar wajen ‘yanmatan a karo na biyu kafin kuma ta

shiga neman Jamila ta cikin tarin hayaniya da kid’an dake tashi a wajen, sai dai duk irin hangen da take yi ba Jamila ba alamarta balle kuma uwa-uba Baddon da sune masu gudanar da tafiyar bikin.

Saboda haka ta juya don neman waje taci awararta, ganin kusan ko’ina da wulgawar mutane yasa ta nufi hanyar fita ta k’ofar yamma inda zata kaika ‘Cikin Gida’ ma’ana b’angaren iyalan Sarki da kuma Turaka da fadarsa ta zaman hutawa, sai dai kafin ta kai ga fita wani daga cikin masu rabon abincin yazo wucewa da katan-katan d’in ruwa don haka ta tsaya rok’arsa ya bata d’aya.

Kafin ya farka katan d’in idonta ya hangi sanda ake zubawa Amaryar wannan kyallin da ta karbo yayin da wani tartsasin wuta daga cikin wasu abubuwa da wasu inyamurai suka zo suka kafa tun safe ya shiga baibaye ilahirin wajen. Gud’a da tarin hayaniya ta sake rud’ewa, wajen yayi kyau sosai taji ya burge ta kuma ta san zata iya ganin Baddon yanzu don a matsayinta na Babbar Jakadiya dole tana wajen amma sai ta yanke shawara fara cin awararta tukunna don haka ta karb’i ruwan ta fita.

STORY CONTINUES BELOW

A bayan wani gini cikin tamfatsesen tsakar gidan ta samu waje ta zauna, anan d’in ma mutane ne ke ta zirga-zirga daga wajen bikin zuwa cikin b’angaren Fulani (mahaifiyar Amaryar) amma inda ta zauna saman tudun wani tanki ya shiga daga d’an lungu saboda haka ba kowa ne zai ganta ba sai hankali yaje wajen.

Ta bud’e awarar ta fara ci hankalinta a kwance, hannunta d’aya na wasa da ‘Fullo’ dake rataye a wuyanta kamar sark’a. A hankali kamar koyaushe idan ta kad’aita ita kad’ai kalaman mahaifiyarta na k’arshe suka shiga yawo a kwakwalwarta.

‘Bana son ki koma wajen dangin mahaifinki Jidda, nafi son kije ki zauna tare da Baddo, ba wai don ina son zaman inda take ba sai don ko ba komai in kina gabanta na san zaki tashi da irin tarbiyar data bani, watak’il ma wannan halin naki ya gyaru saboda wata k’addarar…’

Ta rufe idonta a hankali tana tauna wadda ke bakinta, amon muryar rad’au yake amsawa a kunnenta kamar yanzu aka yi ta, don tana d’aya daga cikin doguwar magana ta k’arshe da mahaifiyar tata tayi mata kafin ciwo yaci k’arfinta ya zamo harshenta ya nad’e har ta daina iya magana kwata-kwata.

A wannan ranar ne kuma ta bata ‘Fullo’ d’an zagayayyen dunk’ulen zinaren data mallaka daga wajen mahaifinta, tace mata mahaifina ya bata shi ne a ranar da aka saka ranar aurensu, don haka ta sanya masa sunan ‘Fullo’ wanda ma’anarsa shine ‘Baiko’ da fulatanci.

Bata san wace irin k’addara mahaifiyarta take nufi ba, amma Allah ya sani ita kanta ta matsu k’addarar ta k’araso ta canja akalar rayuwarta don ko kad’an ba jin dad’in zaman masarautar take ba, daga Baddo har Jamila hankalinsu yafi karkata ga aikinsu fiye da ita, shi yasa babu wayewar garin Allahn da bata kewar mahaifiyarta da kuma rayuwarta ta baya…

“Kin tabbata nan kuwa tace?”

Muryar wata mata data fito daga d’an nesa da bayan tankin yasa tayi saurin bud’e ido, tunaninta ya katse.

“Wallahi nan gurin tace Ladi, bakina da nata fa tayi min bayani, tace daidai bayan ginin nan malamin daya bada aikin yayi kwatance kuma in ya wuce gobe ba’a binne ba aikin ya lalace, to kema ai kin san kuwa ba zan kuskure ba, duba dai kiga ba kowa ko?”

Ba tare da ta san dalili ba, Jidda ta nad’e k’afafunta zuwa kan tudun sanda k’arar takun matar ya shiga kunnenta, taji alamun tayi ‘yan dube-dube kafin tace.

“Babu kowa, kinga dan Allah muyi sauri mu hak’a mu bar wajen nan, bana son wani ya gan mu.”

“Ki kwantar da hankalinki Ladi, nace miki babu abinda zai faru ba mai ganinmu, kudinki kuma cas! Zaki kwana dasu a hannu don Jakadiya bata da sab’a alk’awari.”

K’arar hak’a ta shiga kunnen Jidda kafin wadda aka kira da Ladin ta sake magana.

“Hankalina ne bai kwanta ba jin yawan kud’in nan da za’a bamu, tunani nake in babu hatsari a cikin aikin nan Fulani ba zata fitar da kudi haka ba.”

D’aya muryar ta ja tsaki.

“Ke fa matsalarki gidadanci, to wallahi Jakadiya ta tabbatar mun in muka bada had’in kai fin haka ma zamu iya samu, don Fulani babu abinda take so illa ganin k’arshen MADAKI, kuma ni kaina shaidace zata iya komai akan hakan don wannan had’in da kike gani tace tun daga can k’asar Gabon aka karb’o mata shi.”

Jidda ta had’iye yawu, jin cewa asiri suke binnewa a wannan lokacin kuma cikin umarnin Fulani da Jakadiya, tukunna ma wacce daga cikin Jakadiyar? Ba dai Baddonta ba? Ta sake had’iye wani yawun tare da ragowar awararta sanda muryarsu ta cigaba da magana k’asa-kasa.

“Kin san jikina na bani Fulani zata sami abinda take so wannan karon, saboda kinga na san tasa anyi masa na kiranye mai k’arfi, don Jakadiya tace dole ne zai dawo gida wannan karon sai dai ba’a san yaushe ba. Sannan wannan kuma tace daya sako k’afarsa cikin gidan nan ba zai sake mararin komawa ba, wanda za’a binne wani satin kuma a cikin lambun bayan turakar mai martaba shi kuma na k’ulle bakinsa ne, tace in har aka same shi, to bai fa isa ya sake mararin komai ba bayan umarnin Fulanin.”

“Cabd’ijam!” Cewar Ladin.

“Wai yanzu duk taurin kai irin na Madaki shine zai sauko har ya dinga biyewa Fulani? Anya kuwa Hadiza? Abinda ba’a same shi tun da ba kina ganin zai yiwu yanzu?”

Hadizan ta sake jan tsaki.

“Me ko zai hana shi yiwuwa? Aikin baya da aka kwantar dashi jinya har ta sami wad’annan kud’ad’en ke kika hana shi yiwuwa? Balle yanzu da aka sami wannan garantin malamin… Ance shekararsa saba’in kenan yana wannan aikin kuma ko sau d’aya bai tab’a bada maganin da bai ci ba.”

Jin Hadizan na neman hasala an tab’a uwargijiyarta yasa Ladin tace.

“To ni dai ta kud’in da za’a bani nake, don haka in kina yiwa Allah muyi mu rufe mu bar wajen nan kan wani ya hange mu.”

Har suka gama tone-tonensu kusan minti goma suka rufe suka bar gurin, Jidda bata motsa daga inda take ba, kuma cikin sa’a babu wadda ta lek’o bayan tankin a cikinsu balle su ganta, suka bi ta d’aya hanyar da suka shigo suka tafi cike da jin dad’in kammala aikinsu.

Ba shiri kuwa ta ture ledar awarar gefe sannan ta sauko ta zagaya ta bayan tankin, da ace bata ji sanda suke kokawar maida wani dutsen interlock ba, babu ta yadda zata iya ganin wajen da suka gama hak’awar don sun mayar da komai tsaf sun rufe sai d’an burbud’in k’asa kawai akansa.

Ta juya kowanne gefenta taga ba mai ganinta, sai kawai zuciyarta ta d’arsa mata da ta tone taga me suka binne, tunda ba abinda zata yi kuma ma ai bata tab’a ganin yaya asiri yake ba, saboda haka ba tare da ta bari zuciyarta ta yanke tunani na biyu ba ta nufi wajen.

Ta tsugunna tasa k’arfi ta d’age dutsen,  sannan da saman robar ruwan dake hannunta ta sake hak’o k’asar da bata gama dank’arewa ba, sai da tayi d’an rami mai zurfi sannan idanunta suka ci karo da dank’areriyar layar dake kwance a ciki.

Sai a lokacin kuma gabanta ya d’an fad’i, zuciyarta ta buga, taji kamar wannan lokacin ne da take shekara biyar in tazo d’aukar takalmin sallarta a b’oye don nunawa k’awayenta.

Kar ki jawa kanki bala’i Jidda, Babu ruwanki…

Wata zuciyar ta shiga kokarin yi mata gargad’i amma d’aya b’arin zuciyar tata yaja tsaki ya kore hakan, saboda haka ta had’iye yawu kad’an sannan tayi bismillah a fili tasa hannu ta ciro ta.

A take wani irin sassanyan k’amshi kuwa ya sulale zuwa hancinta, tsadadden k’amshi mai dad’i irin wanda ba sai an tsaya tone-tone ba ta san bata tab’a jin irinsa a rayuwarta ba.

“Anya kuwa wannan asiri ne?…” Ta tambayi kanta fili.

“… Na zata ai asiri wari yake.”

Layar ja ce jawur! An nad’e ta da wasu zarurruka kala-kala kusan guda goma, ta sake kallon hanyar da matan suka bi da kuma bayanta kafin hannunta ya shiga warwarewa babu tunanin abinda zai iya samunta.

A ciki farar takarda ce k’al anyi mata rubutu da abinda babu shakka jini ne daga irin bushewarsa, sai dai bata iya karanta komai a cikin dogon rubutun ba, don in ma yare ne to ta tabbata yaren aljanu ne don a duniya bata ga mahaukatan da zasu zauna su kirkiri irin wannan rubutun a matsayin yarensu ba.

Sai dai me? Daga can k’asan rubutun, idonta ya sauka akan sunan da zata iya karantawa, wanda aka yi shi b’aro-b’aro da harafan boko cikin manyan bak’ake.Ranar da Maijdda ta fara sako k’afarta cikin masarautar KIYARI bayan rasuwar mahaifiyarta da sunan zama ba ziyara irin ta baya ba, kakarta Baddo wadda ta kasance babbar Jakadiya ta sake biya mata bayanin tsarin masarautar wanda a baya bata fiye maida hankali akansa sosai ba don bai shafe ta ba.

Tayi mata bayani dalla-dalla na yanayin gidan sarautar da kuma iyalan dake cikinsa… Wanda har a lokacin bata ga amfaninsa a wajenta ba sai a yanzu da take son sanin waye mutumin data hak’o wani b’ari na k’addararsa jiya.

Mai martaba Ahmad Uba Kamsusi shine d’a na farko a wajen mahaifinsa cikin ‘ya’ya tara wanda cikinsu uku ne kawai maza, ma’ana k’anne biyu ne kawai dashi maza duka sauran mata ne. Bayan rasuwar mahaifinsu sanadiyar wata ‘yar mashashshara, sai ya gaji mulkin a matsayinsa na Babban d’a kamar yadda yake a al’ada da kuma addinance.

K’annensa mata duka sunyi aure kuma bayan su mazan ma duka suna da ‘ya’ya wanda suke sa’anin na mai martaban. Iyalan Sarki guda uku ne, amma banda Fulani wadda ta kasance uwargida, za’a iya cewa sauran guda biyun a suna suke kawai matan sarki amma basu da cikakken iko game da abubuwa da yawa.

Fulani Hafsatu, mace ce wadda kallo d’aya zaka yi mata ka sanya ta cikin jerin manyan mata masu iko, izza, dukiya da kuma ji da kansu. Fara ce k’al mai d’auke da ‘yan k’ananan billen da akewa lak’abi da ‘tsugunna kaci doya’ idanunta na d’auke da wani irin kwarjinin dake sadda gwiwar duk wani na k’asanta, fuskarta kawai ta ishi mutum cikakken bayanin kalmar nan ta ‘isa’.

‘Ya’yanta biyar sune a jere cikin lissafin manya a gidan, Saifudden ne Babba wanda yake rik’e da sarautar ‘Turaki’ don haka ake kiransa da hakan, sai Nadiya mai bi masa, Umarul-Faruk ya biyo baya kafin Aisha (Amaryar da ake biki) da kuma autarta Safina.

Haj. Maimuna, matar Sarki ta biyu tazo ne sanadiyar giftawar rasuwar mijinta wanda yake aboki ga shi Sarkin kafin lokacin da ya karb’i mulki, kwarai Fulani ta tada hankalinta lokacin auren kuma babu irin fafutukar da bata yi ba don canja k’addara amma k’arfin ikon wanzuwar ‘ya’ya uku ya danne duk wata dabararta. Na’ima itace Babba a ‘yayan Haj. Maimuna sai k’annenta Amira da Amina. ‘Ya’yan Haj. Maimuna uku tare da mijinta na farko, maza biyu mace d’aya wanda suke can wajen dangin mahaifinsu, amma a masarautar Allah bai bata namiji ba.

Nene Hadiza, mace ta uku a turakar mai martaba tazo ne a matsayin kyauta ga Sarki daga wani aminin mahaifinsa Hakimin katsina a lokacin da ya hau Sarauta, don haka ita d’a d’aya gareta wanda bai kai shekara goma ba mai sunan Sarkin da kansa Ahmad.1

Dukkanin wad’annan matan suna rayuwa ne a cikin gidan masarautar amma babu ruwan kowacce da kowacce, gwara ma tsakanin Maimuna da Nene Hadiza anyi shiri kad’an a baya wanda ya ruguje daga ranar da Nenen ta haifi d’a namiji. Amma Fulani, bata bi ta kan shirgin kowacce balle kuma ‘ya’yansu, ta tattare komai daga ita sai nata kawai, sannan ita ke da iko akan kusan komai da ya shafi cikin gidan sarautar kuma duk yadda kowacce a cikinsu ke ji da kanta haka suke hak’ura subi tsarinta, don in ba Mai martaba da kowa ke shakkarsa ba, Fulani bata saurarawa kowa.

Hakan yasa zamantakewar gidan ta tab’arb’are saboda idan ba lokuta irin wanda mai martaban kan tara su gabad’aya a rumfarsa ba, za’a iya cewa wani zai shekara ma bai ga d’anuwansa ba saboda hadaniyar komai da shige da fice tana b’angaren Fulani ne inda su ba zuwa suke ba.

Tun kafin zuwan Jidda har kuwa bayan fara rayuwarta a gidan, wannan itace irin rayuwar gidan sarautar KIYARI kamar yadda kowa ya sani.

Abinda a yanzu bata sani ba shine waye IBRAHIM AHMAD MADAKI? Meye alak’arsa da Fulani da har take b’ata lokacinta wajen binne asiri akansa? Kuma har a irin wannan lokacin da take cikin hayaniyar aurar da ‘ya? Me yasa ma ya samu sunan mai martaba a sunansa amma kuma babu jigon sunan zuri’arsu na ‘Kamsusi’?

STORY CONTINUES BELOW

“Kinci wannan?”

Muryar Sadiya ta dawo da Jidda daga tunaninta sanda ta d’auko wani abu mai kama da dunk’ulallen nama.

“Sun saka masa tafarnuwa da yawa wallahi ba dad’i.” Ta karasa tana fitar da ragowarsa daga bakinta.

Suna zaune ne kan wani d’an tudu daga can k’arshen tamfatsetsen filin dake cikin gida, ma’ana k’aton filin daya had’a fuskokin ginin kowanne b’angare na matan sarkin da kuma nasa b’angaren hutawar daga tsakiya, b’angaren Fulani shi yafi kowanne girma sai na Maimuna da Nene wanda yake iri d’aya, dogwayen gine-ginen da suka sha k’awa irin na zamani masu d’aukar hankali don ga fitilu nan ko’ina a cikinsu.

Duk girman filin cike yake da hayaniyar d’imbin jama’ar dake ta kai da kawowa a b’angaren Fulanin, don yau rana ta biyu gagarumar walimar dare ce aka had’a a can wani waje ba masarautar ba, don haka daga mata har maza, manyansu da yara na b’angaren ita Fulanin da kuma dangin mai martaba dana k’annensa kowa yayi shigar kece raini sai fitowa ake don wasu har sun fara tafiya can waje inda ake faka motoci.

K’anwar mahaifiyar Sadiya tana da babbar hanya a b’angaren Fulanin, don haka ta hanyarta Sadiya ta samo musu abincin da akayi musamman don bak’in Fulanin, saboda ita tun wayewar garin Allah bata sa Baddonta a ido ba ma balle har ta san me taci, Jamila kuwa ba ta ita take yi ba tana can cikin k’awayenta itama.

Wajen da suke zaune na fuskantar k’ofar b’angaren Fulanin inda hayaniyar mutane take, don haka sai shilla k’afa suke cikin iskar dake kad’awa saboda ba ga su kad’ai ba lokacin yayi mutuk’ar kyau da dad’i ga duk wanda ke wajen… Ba koyaushe ne ubangiji ke azurta duniya da yanayi irinsa ba.

“Allah naso muma zamu iya zuwa wajen nan, da ba haka ba.” Cewar Sadiya.

“Me zaki je ki musu? Keda ba danginki ba?” Jidda ta tambaya tana k’ok’arin b’are wani alalan ganye.

“Kallo zanyi mana, kema kin san wallahi ba tantama wajen ba k’aramar had’uwa zaiyi ba, kuma za’aci abinci iyakar dad’i.”

Jidda taja d’an guntun tsaki.

“Allah ya sawwak’e miki, wannan da kike ci k’asa ne? Ko yanzu ma fa a k’oshe kike.”

Ta kai alalan bakinta sannan tace.

“Ni kwalliyar Amaryar kawai nake so in gani.”

“Tab! Waya gaya miki tana gidan nan?  Ai tun shekaranjiya suka koma wani hotel ita da k’awayenta wai ba zata iya zaman cikin mutanen nan ba.”

Jiddan ta juyo ta kalle ta.

“Da gaske? Amma tayi asara wallahi to meye dad’in bikin? Kawai tazo taga mutane ta koma wani wajen kamar ‘yar gaiya?”

Sadiya ta kai cinyar kaza bakinta.

“Rabu da masu kudin banza ke dai… Kalli waccan yarinyar kiga, ta tsaye a kusa da Namijin nan…”

“Na ganta… Ba mai green kayan can ba?”

“Ita, wallahi tun shekaranjiya ranar k’unshin nan shigarta ke burge ni, ‘yar k’anwar Mai martaba ce a Abuja suke.”

“Ke wai kin san duka zuri’ar gidan nan ne?”

“Kin manta su Hajiya (kakarta) a falon Fulanin suke aiki, shi yasa idan naje nake yawan ganin mutane. Wai me yasa duk ‘ya’yan masu kud’in nan zaki gansu farare ne”

“Saboda iyayensu maza sai mata farare masu kyau suke aura, ba irin mu normal mutanen gari ba.”1

Sadiya ta girgiza kanta.

“Ina ga gaskiya da hutu ma kuma…  Kalli ga yayar Amaryar can ma ta fito, Nadiya.”

Ta fad’a tana nuna wata farar mata ‘yar gayu, sanye cikin wani rantsatsatsen lace da kwalliyar da ba shakka ta canja kammaninta, tana rik’e da hannun wata ‘yar kyakkyawar yarinyar da ta kasance ‘yarta kuma jika ta farko a gurin Fulani da Mai martaba, waya take tana ratsawa ta cikin mutanen da mafi yawancinsu ke gaisheta yayin da wasu maza ke binta rik’e da manyan ledoji nik’-nik’i na kaya.

STORY CONTINUES BELOW

Jidda ta bisu da kallo har zuwa hanyar da zasu fita harabar motocin, sannan ta sake jan tsaki kad’an, bata jin a duniya zuciyarta zata so wani daga jinin Fulani.

“Ni wallahi haushin bikin nan nake ji, an rik’e su Baddo da aiki tunda aka fara bata zama balle ta huta sosai, kin san jiya har na gaji nayi bacci bata dawo ba, sai Jamila ce kawai ta lek’o wajen sha biyu saura ta sake komawa, sannan ana yin asuba kuma Baddo ko laziminta bata yi ba ta fita.” Ta k’arashe da wani tsakin.

“To ai kinga sune masu bada umarnin abinda za’ayi, shi yasa nace miki kizo muje cikinmu kinga jiya sai wajen sha d’aya fa muka bar wajen nan, damu aka tashi in gaya miki kuma har kusa da amaryar muka je.”

Jidda tayi shiru kawai, don Allah ya sani har cikin zuciyarta tana son komawa cikin sahun ‘yanmatan musamman jiya ma data gama bilinbituwarta ita kad’ai, amma hakan ba zai yiwu bane.

Tun farkon zuwanta masarautar ne Baddo ta had’ata da Sadiya, jikar aminiyarta da suka shafe shekara da shekaru suna aiki a masarautar tare, jininta ya had’u dana Sadiyan sosai suka saba a d’an kankanin lokaci, matsalar shine Sadiya tana da tarin kawayen da suka taso tun yarintarsu tare a cikin masarautar, wanda k’ungiya guda ne sun kai su goma sha takwas.

A cikinsu kuma akwai wasu mutum hud’u da suke ganin sunfi kowa ido da kwalli, su suke juya kowa don sai abinda suka ce ake yi saboda suna da baki, ita kuma Jidda babu wanda yake mata ta kyale balle har yasa tayi abinda bata yi niyya ba, hakan ya janyo banbantar ra’ayinsu, tun daga musun baki kad’an-kad’an har aka fara fad’ar maganganu.

A lokacin bata fi ‘yan watanni da zuwanta ba, daga k’arshe ma ita Jiddan ta haddasa fad’an gaske wanda ta yiwa biyu daga cikinsu dukan tsiya har saida manya suka shigo ciki. To ta yaya kuwa zata iya yarda ta sake komawa cikinsu?

A hankali hannunta ya kai kan ‘Fullo’ dake rataye a wuyanta, bata san adadin yadda take son abin nan ba, don bayan cewar mahaifiyarta ce ta bata shi, shi kad’ai ne kuma abinda baya tab’a barinta a kowanne hali na duniyar nan, koyaushe yana tare da ita kamar mutum da inuwarsa.

A daidai sannan, tunanin data yini tana son ta tambayi Sadiyan ya gifta cikin ranta, ta juyo da sauri ta kalle ta sai faman taune k’ashin hannunta take tace.

“In tambaye ki wani abu?… Idan mutum ya tono asirin da aka binne, wani abu yana samunsa?”1

Sadiya ta zare ido.

“Ke kuwa me yazo kanki? Asiri zaki tone?”

Ai na riga ma na tone!

Taji kamar ta fad’a mata hakan amma sanin halinta na mugun tsoro yasa tace.

“Haba dai kawai so nake in sani ne, kwanaki a makarantar dare ba kince min a ajinku anyi muku bayanin tsubbace-tsubbace ba.”

“Eh, to amma ni wallahi a shari’ance ban san wannan ba, a hankalina dai na san ba lallai a rasa abinda zai sami mutum ba, tunda su kansu masu yin asirin zaki ji ance in suka kuskure wajen sakawa wani abin zai iya samunsu.”

Ta d’anyi shiru tana cigaba da kallonta kafin kuma ta juyar da kanta zuwa inda mutanen gabansu ke raguwa saboda tafiya da ake tayi.

“Ki daina irin wannan tunanin Allah Jidda, wani in yaji sai ya kalle ki da wani abun.” Cewar Sadiyan.

Bata ce mata komai ba don hankalinta ya yarda da abinda tace, tunda har ta tone layar jiya ta k’ona ta akan gas d’in kitchen d’insu babu abinda ya same ta, to ta tsallake koma meye kenan sai dai ma taimakon wanda aka yiwa da tayi, don haka hankalinta ya koma kan maganganun matan nan na jiya… Sunce anyi masa asirin Kiranye a baya, wannan ta san ba lallai ta san inda yake ba don k’ila ma ba a cikin masarautar nan suka binne ba, amma kuma kamar sunce akwai wani…

_’…wanda za’a binne wani satin kuma a cikin lambun bayan turakar mai martaba, shi kuma na k’ulle bakinsa ne, tace in har aka same shi, to bai fa isa ya sake mararin komai ba bayan umarnin Fulanin.’_

Rad’au tunaninta ya dawo mata da wannan zancen, kuma a take ta yanke shawarar sake tone wadda zasu saka d’in tunda dai babu abinda zai same ta, watak’ila ma Allah yasa taje wajen ne jiya don ta zama silar canja k’addarar ko waye IBRAHIM AHMAD MADAKI.

Matsalar yanzu itace tun farkon zuwanta masarautar nan, ranar da Baddo ta gabatar da ita wajen Fulani bata k’ara taka kafarta wajajen b’angaren ba balle har ta san inda wani lambu yake, sannan ma bata san kowa ba balle ta iya gano su waye wad’annan matan har ta san ranar da zasu binne asirin.

“Na manta ban samo mana ruwa ba, kinji cikina kuwa…”

Muryar Sadiya tasa ta juyo ta kalle ta, a lokaci guda tunaninta ya haska mata wani abu… Ta hanyar Sadiya zata iya gano

inda matan nan suke, sannan ita kanta kuma hanya ce tiryan-tiryan da zata kai ta ko’ina a b’angaren masarautar! Ko’ina na nufin har inda zasu bi suje wajen lambun ba tare da an gansu ba!LAGOS.

139A Emina Crescent, Ikeja.

“This is bullshit! Wannan ai shirme ne.”

Muryarsa ta fita a hankali yayin da yake rik’e da takardun da yake karantawa, d’aya hannun nasa na dunk’ule akan hannun kujerar da yake zaune.

“Wallahi abin nan rainin hankalin ne Mdee, nafi tunanin k’arya mutanen nan suke in ba haka ba ai they have to raise the disagreement within a week, ba zai yiwu sai bayan mun basu komai har sunyi signing kuma suzo suce mana ga matsala ba.”

Cewar Mubarak, suna zaune ne a kujerun dake fuskantar junansu, cikin d’an karamin falon dake tsakiyar office d’in.

Wanda aka kira da Mdee ya sake k’ank’ance idonsa yana nazarin takardar, dunk’ulallen hannunsa ya koma kan bakinsa alamun tsantsar mamaki kafin yace.

“Quality issues, Mock ups, wheather reports… Duk da basu san da wannan ba sai yanzu?”

“They are talking millions fa, gani suke yadda a lokaci guda muka d’auki rabin kud’insu muka basu yanzu ma wannan ba zai yi wuya ba, sunyi tunanin su caje mu ne kawai tunda sun san ba sake samun wani aikin damu zasu yi ba.”

“Ka san me Mubarak, bani number Contractor d’in kawai zanji komai.”

Ya ajiye papers d’in sannan ya nufi can kan table d’insa inda sai ka taka wasu ‘yan steps kafin ka isa, akan teburin tarin takardu ne fal cikin folders da basket na k’arfe bayan k’aton screen d’in wata ‘yar siririyar destop da kuma tarin wayoyi kala-kala.

Hannunsa na kaiwa kan d’aya daga cikin wayoyin k’ofar ofishin ta bud’e, k’aramar sakatariyarsa Toyin, wadda ke kula da harkar shige da fice a office d’in ta shigo.

“Yallab’ai, kayi baki daga IHBC.”

Ta fad’i hakan cikin harshen turanci, ya juyo ya kalle ta sannan ya k’ara k’ank’ance idonsa kad’an alamun nazari kafin yace.

“Dama muna da appointment dasu yau ne?”

Jin haka yasa ta girgiza kai game da sosa k’asan kuncinta.

“A’a yallab’ai, sun ce dai suna da zance mai muhimmanci ne kuma cikin gaggawa shi yasa nace bari na duba ko baka da aiki da yawa.”

Daga jin haka ya san kwanan zancen, sun bata kud’i ne don ta shigo dasu su ganshi, saboda haka ya girgiza kansa.

“I’m not available, kije ki san yadda zaki yi dasu.”

Toyin ta d’an tsaya lebb’enta na motsi tana son tace wani abin, amma shi bai sake ko kallonta ba ya wuce wajen Mubarak wanda ke danna tasa wayar alamun yana kokarin tura masa lambar da yake nema, sanin cewa ba saurarenta zai sake yi ba yasa gwiwa a sake ta juya ta fita.

“Me yasa zaka mata haka? A ganina IHBC ba kamfanin yadawa bane.”

“Kyale ta kawai, zan iya ganinsu ko anjima ne, so nake inda hali su karb’e kudin da suka bata kafin ni kuma na kore ta…”

“Idan har ka kore ta ka cire sunana a masu sake nemo maka wata sakatariyar don na gaji wallahi.”

Kafin ya bashi amsa k’arar shigowar message ya harba a wayar da ya d’auko.

“Yanzu zasu fad’a min meye matsayin progress reports d’in da suka bamu wancan satin.”

Ya fad’a sanda ya wuce can k’arshen office d’in inda fuskarsa ta fita ta waje d’auke da manya-manyan gilasan da suka haska kuma suka d’auki yanayin kalar sararin samaniya na lokacin. Lokaci na yamma wanda ido zai nuna maka cewa ba’afi ‘yan mintuna da d’aukewar ruwan sama ba kamar yadda yake koyaushe na yanayin garin.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sanyin danshin ruwan dake jikin gilasan akwai kuma sassanyan sanyin na’ura wanda ya gauraye ilahirin cikin ofishin da kusan komai na cikinsa kalar ruwan toka ne, hakan yasa yake da wani kyau mai sanyi a idanun mai kallo.

Mubarak ya bishi da kallo har zuwa inda ya tsaya ya kara wayar a kunnensa, wannan tsaiwar tasa mai cike da k’asaita da tak’amar da ko wad’anda suka gaji sarauta cikin jini da asalinsu basu samu ba, don ba kowa ne Allah ke mallakawa kwarjini da cikar zati irin tasa ba… A hankali yake magana cikin wayar amma kuma idanunsa na lumshewa tare da d’imbin b’acin ran da yake ciki.

Bayan wannan b’acin ran kuma, a matsayinsa na Amininsa wanda zai iya bugar k’irji game da sanin kowanne sirrinsa, yana iya hango wannan ciwon dake manne da rayuwarsa a kowanne b’angare, wannan ciwon da yasha dannewa tare da hana masa tarin ‘yancin da yake dasu a b’angarori da yawa, amma kamar koyaushe yana kokarin yak’arsa ne da makami d’aya da yake dashi a duniya.. wato b’oye damuwa a fuskarsa ta hanyar da baza ta tab’a karantuwa ba.

Ya gyara kafarsa dake d’ore kan d’aya sannan ya koma ya jingina da kujerar da yake kai… Dole ne ma baza su sake aiki da wannan kamfanin ba, don a baiyane yake cewa basu san waye IBARAHIM AHMAD MADAKI ba, basu kuma san irin abinda zai iya ba.

***

“Abubuwa nawa ka sani mara sa dad’i a rayuwa?”

Mubarak ya tambayi Madaki lokacin da suke zaune kan d’aya daga cikin teburan wani katafaren gidan cin abinci mintuna kad’an bayan barinsu office.

Madaki ya d’aga kafad’unsa yana kokarin gutsirar nama da fork da kuma wuk’ar hannunsa kafin yace.

“Kai ma ka san suna da yawa, ya danganta da yanayin kowanne mutum ne kawai.”

“Haka ne..” Cewar Mubarak sanda ya kai nasa cokalin baki.

“Akwai su da yawa, kamar rashin lafiya, faduwa jarabawa, yunwa, hatsari, yaudara, tuntub’e…”

“Da kuma damun mutane ma.”2

Madaki ya katse shi yana masa alama da mutanen sauran teburin dake d’an kallonsu da gefen ido alamun maganarsa da k’arfi na d’aukar hankalinsu.

“…Mdee ka san duk bayan wad’annan ma akwai cewar mutum na jiran abu kuma a k’i gaya masa?”

Ya k’arashe zancensa ba tare da ya kula shi ko mutanen ba.

Madaki ya d’aga kafad’unsa kad’an.

“Kaima ka san ba abinda nake ganewa idan ina jin yunwa.”

Mubarak ya ajiye cokalin hannunsa sannan ya nad’e hannaye biyu yana kallonsa.

“Right yanzu kaci abinci, fad’a min yaya kuka yi dasu.”

Ya sake kai fork d’in bakinsa ya shiga tauna naman jiki, sai dai bai koyi rabi ba ya had’iye shi gabad’aya, don Allah ya sani ko a cikin tunaninsa abinda yake shirin fad’a nauyi yake masa.

“Dole ne zanje KIYARI.”

“Me?” Fuskar Mubarak ta nuna tsantsar mamaki had’e da rud’anin da maganar tasa shi.

“Mutanen nan da gaske suke Mubarak, shi Contractor d’in ya tabbatar min duk abinda suka fad’a haka yake har da ma k’arin wata matsalar ta transportation don kasan komai kaiwa suke yi can, kuma wai ma yana gaya min suna da evidence d’in komai ba k’arya suke ba, ni kuma gaskiya ba zan iya salwantar da wasu miloyoyin akan abinda ban tabbatar ba, so zanje ko zuwa sati d’aya ne ayi site meeting har da duka Consultant team d’in don in tabbatar kuma in ga komai kafin ma inyi wani tunani.”

Mubarak bai saki hannayensa ba ya cigaba da kallonsa kafin yace.

“Kamar koyaushe kai da zuciyarka ka yanke wannan shawarar ko?”

STORY CONTINUES BELOW

“Haka ne, amma ka san zan jira ai ka fad’a min taka shawarar kafin dai in d’auki tawan.”

“Mdee bana jin tafiyarka Kiyari shine daidai kaima kuma ka sani, akwai tarin hanyoyin da zamu iya tackling matsalar nan ba sai kaje ba, ko kuwa wani ya fad’a maka cewa kai kad’ai ka iya komai ne?”

Ya d’ago ya kalle shi, fork d’in rike dai a hannunsa.

“Ka gaya min wa ya dace ya sami mutanen nan in ba ni ba Mubarak, ka san dai baka cikin project managers d’in don haka ba mai saurarenka, to in ba kai ba su Habibu da kasa nayi replacing d’inka dasu zan tura a sake had’a baki dasu ace wani abin ko kuma wa? A tunani na ma kana da babban kamashon laifi cikin wannan harkar, tun farko kai kasa na cire sunanka da cewar aiki ya maka yawa na saka na mutanen da ba’a komai za’a yarda dasu ba.”

“Wannan ya wuce kuma idan babu sunana, ai akwai na Turaki..”

Girarsa biyu ta d’an had’e waje d’aya.

“Waye Turaki?”

Mubarak yaja karamin tsaki.

“Saifuddeen nake nufi shi ba yana can gida ba? For God’s sake rana nawa ne zai bar aikinsa yaje ya duba wannan matsalar? Baka ganin cewa a yanzu ya dace ya fara sanin wannan harkar?”

Maganar ta d’an daki tunaninsa ta wata hanya da in ba Mubarak d’in ba babu mahalukin daya isa ya fahimta, saboda haka sai shima yayi saurin gyara zancensa da cewar.

“Ka gane ina nufin tunda kamfaninsu ne ba namu ba su zasu amfana da wannan harkar, saboda me ba zaiyi komai ba?”

“Saboda shima ban yarda dashi ba.”

Kai tsaye amsar ta fito daga bakin Madaki, yayin da idanunsa ke kan kofin tambulan na lemon gabansa.

Mubarak ya gyara zamansa sannan ya dunk’ule hannu akan bakinsa.

“Na san hakan, amma gaya min wani abu… kana ganin cewa in har ka cigaba da rik’e wannan akidar zaka zo kuma ka iya bashi kulawar wani b’angare na wannan kasuwancin?”

Sai ya ajiye fork d’in hannunsa sannan ya d’ago da idanun da kullum ke danne damuwarsa ya kalle shi yace.

“Idan har an kammala komai, na ciro wani kaso na wanan dukiyar na dank’a musu, to kowa ya san cewa wannan kason ya fita daga hannuna kenan, kuma komai salwanta ko habb’akar da zaiyi duniya ma baza ta danganta hakan dani ba, amma yanzu komai a k’ark’ashina yake Mubarak, kuma kaima ka san ba zan d’ebi tarin miloyoyi in bawa wasu mutane a banza ba don haka dole ne inje in tabbatar musu hakan.”

“Haka ne Mdee, bayan haka kuma na san cewa had’uwarka da FULANI ma ba abune mai kyau ba..”

Karo na farko tun bayan wani lokaci murmushi ya sub’uce a fuskar Madaki, ya damk’e tissue d’in tsakiyar teburin daya yago sannan bakinsa ya maimata sunan.

“Fulani…!”

A take yaji kamar wani waje daga can k’asan zuciyarsa ya yanke ne da ambaton sunan, Harafai shida kacal dake siffanta matar data zama kamar wani k’alubale na biyu a rayuwarsa, matar da ko yaushe sunanta ya ratsa cikin kunnensa, tunaninsa na dawo masa da kausasan kalaman data fad’a masa ranar nad’in sarautar Mai martaba, kalaman dake k’one cikin tunaninsa. Idan har kana ganin wannan wata dama ce ta sake bud’e maka to kayi kuskure, Allah ya sani na tsaneka Madaki, ka riga ka san hakan kuma a yanzu ina ganin lokaci ya wuce da kalamaina ma zasu dinga b’oye manufata, kasa a ranka cewa ko zanyi yawo tsirara sai na kwatowa ‘ya’yana hakk’i da matsayinsu daka danne!

Ba wanda ke tara sani da ubangiji balle abinda ke b’oye, watakila da ta san irin sirrin da yake yawo dashi a k’irjinsa… da ta san cewa shi d’in mai wasu k’aiyadaddun kwanaki ne kawai a duniya, data hutar da kanta da kowacce fafutuka ta maida hankali wajen d’inka tarin suturun da zasu ishe ta cin zamani mai tsawo ita da ‘ya’yan nata bayan baya duniyar.

“Kaga…”

Mubarak ya yanke shirun dake shirun yin tsawo kamar koyaushe sunan na Fulani ya ratso cikin zancensu.

“Kayi maganar da Mai martaba ne?”

Wannan tambayar kad’ai tasa ya gane cewa ya fahimci abinda yake nufi kenan, ya fahimci cewa babu wata mafita dole sai ya taka k’afarsa cikin garin da ba zai tab’a iya kira da ‘Gida’ ba, saboda haka ya girgiza kansa.

“Kamar koyaushe kaine na farko da ka fara sani.”

Har Mubarak d’in zai sake magana dariyar wasu mata daga gefen daman teburinsu ta katse shi, sannan wata murya mai zak’in gaske ta biyo cikin fad’in ‘Hey!’

Dukkansu su biyun suka juya, wasu kyawawan mata ne su uku cikin shiga ta k’ananan kaya da kuma dogon gashi irin na kanti, biyu daga ciki suka d’ago musu hannu had’e da murmushin da ya k’ara fito da kyan fuskarsu. Madaki ya juya, Mubarak kuma ya maida musu martanin d’ago hannun da cokalin daya d’auka a hannunsa.

“Ina ganin ni na gama da nan, mu had’u a office kawai.” Cewar Madakin sanda ya d’auki wata tissue d’in ya goge bakinsa sannan ya zame daga kujerar ya mik’e tsaye. Mubarak ya bishi da kallo.

“Me kake nufi? Ka manta tare muke ne ban zo da mota ba?”

Kamar bai ji ba, ya k’ara fad’in.

“Zan tsaya in biya su kud’in abincin, sai na ganka.”

Daga haka ya nufi hanyar fita daga wajen, yana jin kowanne taku na tafiyarsa na bugawa tare da sautin kid’an zuciyar dake zuba tsere a k’irjinsa.

Sai dai ba office d’in ya sake komawa ba kamar yadda yace, d’an madaidaicin flat gidan daya mallaka cikin unguwar ” ya nufa, don baya jin kwakwalwarsa zata sake iya karb’ar wani lissafin a yau bayan wanda ke tarawa da d’ebewa a cikin kansa.

Da ya isa kuma zai kira Mai martaba ya shaida masa zancen zuwan nasa tun da wuri, don a yadda yake lissafa komai baya son ya tafiyar ta wuce cikin satin nan, dole ne kuma yayi compling duka ayyukan daya fara don Mubarak ya samu saukin fara sababbi na watan da zai kama a gaba…. Tunaninsa ya tirje tare da tsayuwar tayar motar sanda fitilar danja ta tsaida motocin b’angarensa.

Me ya same shi ne? Me yasa yake lissafin wani watan alhalin abinda zai kaishi kwata-kwata bai fi sati guda ba? Ba shiri ya dunk’ule hannunsa sannan ya daki tsakiyar sitiyarin motar, hakan ya fitar da k’arar horn mai k’arfi, mutanen dake motocin gefensa suka shiga juyowa suna kallonsa.

Sai kawai ya koma da baya ya kwantar da kansa saman kujerar motar, ya rufe fuskarsa da duka tafukan hannayensa sannan ya fitar da iska ta bakinsa.Yanzu Allah Jidda baza kiyi sauri ki gama tsifar nan ba? Tsifa kawai amma kin kusa awa biyu kamar baza ki gama ba?”+

Baddo ta fad’a daga kan shimfid’arta inda take kwance.

Jamila ta lek’o daga d’an k’aramin kicin d’in da yake manne cikin d’akin tace.

“Wai ace ma kitso yafi sati biyu akan mutum amma sai an saka shi a gaba zai tsefe?”

Jidda dake zaune a can bakin k’ofar d’akin ta d’ago da buzu-buzun gashinta ta kalli k’ofar kicin d’in tace.

“To ina ruwanki? Ai in za’a lissafa ma wallahi bai fi sati biyun ba.”

“Kinga… Kinga in ba ki rufe min baki ba na taso zan make ki, ba gaba take dake bane wai?”

Baddo ta fad’a tana nuno ta da yatsa, sai ta zumb’uro baki kafin ta sunkuya ta cigaba da tsifar, ita kanta ta k’agara ta gama don ta san Sadiya na can na jiranta, amma duk laifin Jamilan ne ai da tayi mata kitson ‘yan k’anana a cewarta wai itama tayi kwalliyar biki. Bikin da har akayi aka gama aka tafi da Amaryar can Sakkwato babu wanda ma ya lura da ita.

Ta tsakanin gashinta ta kalli Baddon dake kwance, ta tabbata ba don ta fad’i jiya ta gurd’e kafarta ba da a yau d’in ma tana can b’angaren Fulanin, don har yanzu wajen a cike yake da mutane wai ana ta gyara da share-share.

Jamila ‘yar wan mahaifiyarta ce, ‘ya’ya biyu da Baddon ta haifa a duniya, amma shi ya riga mahaifiyarta rasuwa don tun kafin a haifi Jamilan ya rasu, bayan ta kai shekara uku kuma mahaifiyarta ta rasu itama, don haka Baddon ta karb’eta ta girma a hannunta, yanzu kusan shekarunta ashirin da biyar kenan tare da Baddon, kuma itama har ta zama ma’aikaciya a masarautar don an dad’e da sanya ta cikin masu karb’ar albashi. Tana da wa guda d’aya Muhammad, amma shi yana can Ringim inda iyayensu suka zauna yana sana’arsa.

Ta riga ta saba da Jamila tun kafin rasuwar mahaifiyarta, don haka alak’arsu kamar ta yaya da k’anwa ne suyi fad’a su shirya, amma duk da haka tana jin haushin yadda take mata shishigi a al’amuranta wani lokacin… Tunaninta ya katse sanda muryar Jamilan ta sake fitowa.

“Sannan Baddo wallahi ki hana ta ganin wannan yaron, wasa kawai yake da hankalinta amma ita ta d’auki son duniya ta d’ora masa.”

Ranta ya b’aci a lokaci d’aya, bata san meye matsalar Jamila da Suraj ba, shi yana girmama ta amma ita bata gani, ta cije lebb’enta na k’asa tana gyad’a kai, koma me zata fad’a akansa sai dai ta yi tayi, tunda ta san Baddo baza ta hana ta ganinsa ba kuma ita tana son shi har cikin zuciyarta, tana mahaukacin sonsa ma.

“Yo Jamila al’amarin nan fa na Allah ne, ni dai ban san wani aibun yaron ba balle iyayensa, to kinga kuwa don me zance ta rabu dashi? Ba don dangin mahaifinta ma sunce zasu sake biya mata kud’in jarabawarta da bata yi kyau ba ai da sai ace masa ma ya fito kawai a had’a da naki tunda ba wani abu take yi yanzun ba.”

Jamilan ta sake cewa.

“Da wani mutumin arzik’in ne dai, amma Allah Baddo wannan yaron…”

Jidda na jinsu bata ce komai ba sai faman kwafa kawai take yi a cikin ranta tana laluben abinda ta san zata b’atawa Jamilan rai itama, sallamar Sadiya ta katse tunaninta, ta d’ago da sauri sanda ta bud’e k’ofar net d’in d’akin ta shigo, ta mata kallon ‘dama kina nan?’ Kafin ta matsa ciki.

“Baddo ina wuni? Ya k’afar taki?’

“Mun gode Allah, amma kin ganni dai tun safe na kasa tashi, su Hajiya Laraban sun dawo daga cikin gida ne?”

“A’a suna can nima na shiga ba’a gama aikin bane… Aunty Jamila ina wuni?”

Jidda tayi saurin tufke gashinta cikin ‘yar  jela guda d’aya har da wanda bata gama tsefewa ba sannan ta kamo hannun Sadiya sanda Jamila ke amsa gaisuwarta daga can kicin.

STORY CONTINUES BELOW

“Dalla rabu da ita zo muje, Baddo muna zuwa, yanzu zan dawo Allah.”

Kafin Baddon tace wani abu kuma taja ta suka bar d’akin, bata sake ta ba sai da suka tsaya daga can k’arshen dogon tsakar gidan wanda ya had’a fuskokin d’akunan manyan Jakadai na gidan sarautar.

“Ya akayi? kin gansu?” Ta tambaya tana kallonta cike da zumudi.

Sadiya ta d’an b’ata rai kadan.

“Na gansu, amma Allah Jidda wannan abin fa akwai hatsari, ni banga dalilin da zai sa mu kai kanmu cikin wannan bala’in ba, don wallahi kin san aka kama mu bamu kad’ai ba har su Baddo sai abin ya shafe su.”

Jidda taja k’aramin tsaki.

“Wai sau nawa zan gaya miki ne cewa babu wanda zai gan mu? Wallahi matan fa kwata-kwata ba wani wayo ne dasu ba, suna barin wajen kawai zamu je mu tone, sannan in ma tsoro kike kar wani abu ya same ki ai na nuna miki tokar wadda na k’ona, kuma ba gashi ba abinda ya same ni ba.. Yanzu gaya min kinji sunyi zancen?”

Kafin ta bata amsa wata d’iyar Jakadiya Nafi da take bazawara ta fito daga d’akinsu ta kalle su tace.

“Me kuke yi anan da tsakar ranar nan? Ke Jidda ina d’ankwalinki?”

Bata kalle ta ba tace.

“Tsifa nake yi yanzu zan koma.”

Sai ta sake jan Sadiyan suka koma can kan wata ‘yar kwana.

“Bana son munafuncin mutane wallahi, ina jinki me kika ji sun ce?”

Sadiya ta had’e hannayenta a k’irji.

“A wajen famfo na gansu, sun tsaya daga gefe suna magana shine na d’auko bokiti naje wajen kamar ruwa zan d’iba, ban dai ji me suka ce gabadaya ba amma na ji ita Ladin tana gayawa Hadiza wai Jakadiya Babba tace dubu goma-goma za’a basu wannan karon sannan kuma wai jibi zasu binne a cikin lambun k’asan wata bishiya, ko bishiyar lemon tsami ce akace musu? Na dai manta.”

Jidda ta gyada kai.

“Da yaushe suka ce zasu je kuma?”

“Bayan la’asar.”

“Allah ya kaimu, mu sai muje bayan magariba, fitila kawai zamu d’auka sai wukar da zamu hak’a, kin dai ce zamu iya shiga ba tare da an ganmu ba ko?”

Sadiya ta d’an yi shiru.

“Jidda ko dai kema biyanki akayi ne?”

“Me? Waye zai biya ni? Wama ya san dani a gidan nan?”

“To ai abin ne mamaki yake bani, ko ni fa ba sanin mutumin nan nayi ba, don na gaya miki ba’a nan yake ba kuma babu wanda ya san alak’arsa da mai martaba, sannan ke baki san ma waye mai gaskiya tsakaninsa da Fulanin ba, haka kurum kina shirin saka mu cikin bala’i.”

Jidda tayi shiru kawai tana saurarenta gira a had’e, sai da ta gama sannan tace.

“Kinga nifa na riga na saka raina a abin nan, kuma na san kema tsoro kawai kike ji amma ba dole, in ba zaki je ba sai ki min kwatancen hanyar tsaf zan gane, kuma ba mutuwa zanyi ba in naje ni kad’ai.”

Sadiya ta sake yin shiru fuskarta na nuna irin d’aurin da maganar tayi mata, sai kuma tayi ajiyar zuciya sannan cikin murya irin ta wanda aka fi k’arfi tace.

“Shikenan, Allah ya kaimu jibin.”

A lokaci guda Jidda ta fad’ad’a murmushin ‘ko ke fa’ a fuskarta sannan ta rungumeta.

Kamar yadda kowanne d’an adam bai san lokacin zuwan k’addararsa ba, haka itama a wannan lokacin bata san cewa abinda suke shirin yi shine mataki na farko wajen canja akalar rayuwarta zuwa k’addarar da ubangiji ya tanadar mata ba… K’addarar da lokaci ya riga ya rantse akanta sannan k’addarar da take tamkar ZANEN DUTSE wanda ba zai tab’a goguwa ba!1

STORY CONTINUES BELOW

***

D’akin babba ne wanda zai iya amsa sunan ‘tamfatsetse’ ma, yana da manya-manyan tagogin da aka rufe su ruf! da dogwayen labulaye na alfarma wanda kalarsu ta ruwan makuba ta dace da tattausan carpet d’in da yake mamaye a ko’ina na d’akin da kuma sauran wasu k’ananan carpet d’in dake samansa.

Akwai wasu irin maka-makan kujeru na alfarma da suke kalar ruwan labulayen da kuma ratsin ruwan gwal, a jikin bangon dake gabansu kuma akwai tarin kayan wuta na kallo wanda suka had’a da wata had’addiyar Talabijin da tsawonta ya kusa kaiwa na wani d’an adam d’in.

Sannan idan ba idonka ya kai d’aya gefe na d’akin ba inda wani makeken gado na alfarma yake, babu ta yadda tunaninka zai danganta cewa d’akin bacci ne kawai, don kayan k’awa da na adon cikinsa kawai ya isa ya tashi kud’in mallakar wani gida gudan.

K’ofar jikin d’akin ta bud’e sannan wata farar dattijuwar mace k’al cikin shiga ta alfarma ta shigo hannunta d’auke da wani faranti mai cike da kayan cima, ta nufi inda wani dattijon mutum mai cike da kwarjini ke zaune k’asan maka-makan kujerun nan.

Sai dai har ta yiwa kanta mazauni a kusa dashi bai d’ago daga rubutun da yake ba bayan amsa sallamarta da yayi, saboda haka tayi murmushin da ya fallasa irin tata izzar itama sannan tace.

“Ahmadu magajin Sidi,

A kiyayi malami idan yayi Sarki,

Da tsinin alk’alami ya kan fasa dutse.”

Jin haka yasa shi guntun murmushi, ya ajiye biron hannunsa sannan ya juyo ya kalle ta yace.

“FULANI kenan, ran gida, mai maida shi Sarkin bafade.”

Sai ta sake wani murmushin mai cike da kissa.

“Mun yini lafiya ranka ya dad’e?”

“Lafiya mun gode Allah, ya kuka ji da hayaniyar cikin gida?”

“Muna kokartawa, ayi hakurin jinkirina, Jakadiya ce bata ji shigowar Zabiya da wuri ba.”

(Zabiya itace matar dake shigo da Sarki gida bayan an kammala zaman fada.)

Sai ya koma ya jingina da kujerar bayansa.

“Babu matsala, ya wajen d’iyar ki?”

Ta janyo farantin data ajiye, ta shiga kokarin had’a masa ruwan shayi sannan tace.

“Amarya? Tana lafiya mun yi waya da safiyar yau.”

Ta cigaba da cewa.

“Har tana yi min shakiyanci wai yau data zaga sai taga masarautarsu tafi tamu kyau.”

Ya karb’i kofin data mik’o masa sannan yace.

“Au, Sakkwato birnin shehu? Wa zai had’a ta da Kiyari dama? Amma ba komai, muma mun godewa Allah da tamu.”

Suka sake murmushi a tare sannan ya shiga kurb’ar shayin, idanun Fulani na nazartarsa, sannan cikin salo irin nata ta kintaci daidai lokacin da take son isar da sak’onta tace.

“Ranka ya dad’e, tuni zanyi akan zancen Turaki, ko kunyi magana da Gwamnan?”

“Akan me kenan?” Ya tambaya yana neman inda zai ajiye kofin.

Sarai ta san ya fahimci zancen amma sanin hali yasa kamar koyaushe ta ture duk wata tak’amarta da bata tasiri gabansa tace.

“Akan filayen nan na bayan gidan Gwamnan da yake son ya fitar da Estates don kasuwanci, kwanaki da ya nemi siya basu bada dama ba shine har na tambaya ko mai martaba zai sanya baki.”

Ya juyo ya kalleta.

“Kadarorin Turaki sun fara yawa a cikin gari, me yasa kike son ya matsa daga gareni ne?”

“Ba haka bane ranka ya dad’e..”

“To a bar zancen.” Ya katse ta.

“Har kullum ina gaya miki Turaki a Fada ya dace ba cikin siyasa da kasuwanci ba, don haka ki d’ora wannan burin naki akan Umarul-Faruk, fa’idar samun ‘ya’ya da yawa kenan.”

A lokaci guda wani duhu ya baiyana a cikin idanunta, kammaninta suka shiga kokarin juyewa zuwa ainihin Fulanin da take a halitta, mai k’ek’asashiyar zuciyar dake da kaushi akan duk wanda zai shigo hanyarta, saboda haka sai ta sadda kanta k’asa.

Shima bai k’ara cewa komai ba ya janyo takardunsa yana k’ok’arin cigaba da rubutu, sai kuma ya juyo ya kalle ta yace.

“Hakan ya tuna min zamu yi bak’o… D’anki zai iso jibi insha Allah.”

Kamar yadda walk’iya ke haskawa kafin zuwan rugugin tsawa, haka wani haske ya haska a idanunta sannan k’arar rugugin tata zuciyar ya biyo baya, mutum d’aya Mai martaba ke kira da ‘D’anta’ duk duniya… MADAKI!

Ta d’ago ta kalle shi, kyallin mamakin bai gama barin idanunta ba.

Sai kuma zuciyarta ta doka wani tsallen murnan a take, kar dai ta samu tabbataccen Malami wannan karon? Saboda bata tab’a tunanin cewa asirin kiranyen da aka binne zaiyi tasiri da wuri ba, a tunaninta da wuya ne a iya fasa rik’akk’yar ak’ida irin ta Madaki cikin k’ank’anin lokaci, amma wai me? Har zai zo? Mutumin da rabon da ya tako k’afarsa cikin masarautar shekaru biyar kenan!

Kenan layar Farra’un da aka binne ranar kamun Aisha itama zata yi aiki akansa? Ko kuma hantar farin zakaran da za’a binne jibi na K’ulle bakinsa shima zai yi tasiri kenan? Zuciyarta ta sake bugawa da taraddadin dad’i… Bata san yaya farin ciki zaiyi da ita ba muddin buk’atarta ta tabbata wannan karon, watak’ila malamin nan na k’asar Gabon, yayi aikin da zai zama silar arzikinsa a duniya.

Mai martaba ya juya kan rubutunsa sannan yace.

“Yace zai zo ne akan zancen Kamfanin takalman da nace a bud’ewa su Umarun anan.”

Sai zuciyarta ta matse a take, don zancen wannan Kamfanin yana d’aya daga cikin abubuwan data tsana a jerin lissafinta, har me ‘ya’yanta zasu yi da wani Kamfanin takalma alhali abinda take hari ya ninka d’aruruwansa?

Amma kuma sai tunanin samun nasarar aikinta ya danne wannan d’an b’acin ran… In har zata sami bukatarta wannan Kamfanin ba komai bane illa k’arin d’igar ruwa a cikin bokiti kawai, saboda haka tayi murmushin da bata shirya masa ba sannan sassanyar muryarta ta furta.

“Maraba da Madaki.”LAGOS.+

ASABAR, 09:00AM.

K’arar rurin wayar dake yashe akan durowar gefen gado ya shiga kad’awa cikin sautin k’ira’ar addu’a daga Sheikh Abdurrahman Sudais, sannan vibration d’in jikin kid’an kuma ya dinga gurzawa akan katakon durowar, hakan ya tashi d’aya daga cikin mutanen dake kwance akan gadon d’akin.

Mubarak ya mik’o hannunsa cikin magagin barci ya d’auki wayar sannan ya kara a kunnensa.

“Wai an gaya maka cewa kowa ne tuzuru irinka?” Muryarsa ta fito da alamun bacci.

Daga can gidansa, Madaki ya d’auke kofin shayinsa daga kan island d’in kitchen sannan ya biyo hanyar da zata dawo dashi falo.

“Idan na tashi Madam tayi hakuri, amma kai in ba lalaci ba baccin me kake yi har yanzu k’arfe tara na safe?”

Mubarak ya murza idanunsa.

“Tsakani da Allah yau asabar fa? Ni itace ne da ba zan huta ba?”

Madaki ya nemi kan d’aya daga cikin lausasan kujerun falonsa ya zauna sannan ya kai kofin shayin bakinsa.

“Ya akayi?” Mubarak d’in ya sake tambaya.

“Jirgin da zan hau k’arfe goma zai tashi, kuma Habibu ya kira ni d’azu yace min FreTRUST zasu shigo yau akan zancen profit d’in nan, so dole ne zaka shiga anjima ka gansu.”

Jin haka yasa ya mik’e ya zauna akan gadon sosai sannan suka shiga tattaunawa game da aikin, zuwa can kuma yace.

“Insha Allah zamu yi making, bari dai su kawo reports d’in tukunna.”

“Allah yasa hakan..” Cewar Madaki. “Sai naji ka kenan.”

Ya k’arasa yana kokarin katse kiran, sai dai cikin hanzari Mubarak d’in ya katse shi.

“Me ya faru a appointment d’inka da doctor jiya?”

Madaki ya runtse idanunsa sannan ya shafo sumar kansa, tun jiya bayan dawowarsa daga asibiti yak’i bawa zuciyarsa damar da shi da ita zasu tattauna zancen, don kamar yadda bai san me zai gayawa kansa ba haka bai san ta yadda a yanzu zai gayawa Mubarak cewa kwanakin da likitocin ke saka masa rai dasu a duniya suna k’ara raguwa ne sakamakon dad’uwar ciwonsa ba.

“Zancen aortic stenosis ne dai, yace aortic valve d’in ne yake k’ara tsukewa…”

“Mdee ka min yaren da zan gane mana.”

Sai ya d’auki kofin shayinsa ya sake kurb’a sannan yace.

“Wannan jijiyar dake d’aukan jini daga zuciya zuwa sauran b’angaren jiki ce take k’ara tsukewa, yace shi yasa nake fama da yawan ciwon k’irjin da kuma jiri.”

“Allah ya sawwak’e.” Cewar Mubarak bayan yayi ajiyar zuciya.

“Kar ka manta dai ka tafi da defibrillator d’inka, Allah ya kiyaye hanya.”

“Insha Allah, Nagode.” Da haka suka yi sallama.

Ya ajiye wayar sannan ya kalli d’an madaidaicin akwatin dake d’auke da kayansa a saman kujera, tunani da yawa ke yawo a cikin kansa amma mafi rinjaye shine, ya kasa gane dalilin da yasa a yau zuciyarsa tafi hargitsewa fiye da ko wad’anne lokutan na tafiyarsa a baya, ya kasa gano dalilin da yasa taraddadinsa yafi na koyaushe, zuciyarsa ta kasa nutsuwa tun daga ranar daya yanke shawarar tafiyar har a yanzu da awa guda kawai ya rage kafin tashinsa.

Ya sake kallon akwatin sai kuma ya d’auke kai ya shiga ambaton istigfari cikin ransa, ya kunna wayar hannunsa sannan ya shiga laluben number mutumin da zai kawo masa mota bayan Jirgi ya sauke shi a garin Kano.

STORY CONTINUES BELOW

Abinda bai sani ba a wannan lokacin shine, wannan karon tafiyar tasa itace mataki na farko da zai canja akalar rayuwarsa zuwa wata k’addarar da ubangiji ya tanadar masa… K’addarar da lokaci ya riga ya rantse akanta sannan k’addarar da take tamkar ZANEN DUTSE wanda ba zai tab’a goguwa ba!

***

KIYARI

ASABAR 10:00 AM.

Jikan Sidi hankalinka gare ka,

Saifu tsinin takobi kowa yak’i gaskiya ya ganki,

Yawan magana kan sa k’arya,

Ai ko kurum magana ce,

Jigon sarakuna jikan Muhammadu Sidi,

Takawarka lafiya yariman zamani,

Sai kayi sai ka barwa jikokinka yardar ubangiji,

Goshi mabud’in alkhairi na Fulani mai danda…

Wannan kirarin shi ke amsawa daga bakin fadawa tun daga k’ofar k’ayataccen falon farko na b’angaren Fulanin wanda alamu ne dake nuna isowar Turaki wajen mahaifiyar tasa. Nan da nan kuwa matan dake zazzaune a k’asan d’akin suka shiga k’ok’arin mik’ewa tsaye yayin da Jakadiya Babba ta rugo har da gudu ta tare shi tun daga bakin k’ofar shigowa, hannunta na dama a dunk’ule ta shiga fad’in.

Barka da isowa ranka ya dad’e,

Barka da sauka balaraben yarima jikan Sidi,

Barka dai d’an mai masallacin juma’a jikan mai masallacin juma’a…

Turaki wanda yake cikin shiga ta alkyabba marar nauyi da k’aramin nad’i mai kama da hula ya d’aga mata hannu kawai sannan ba tare da ya cire takalmansa ba ya mik’e ciki zuwa k’ofar da zata sada shi da falo na biyu. Fadawansa suka tsaya daga nan yayin da jakadiya ta taka masa zuwa bakin k’ofar, bai ko saurari sauran matan dake k’ok’arin gaishe shi ba ya shige ciki.

“Haka ne, na fahimta…”

Cewar Fulani cikin wayar da take yi, tana zaune ita kad’ai kan d’aya daga cikin kasaitattun kujerun dake zagaye cikin falon, shigowar Turakin yasa ta d’ago da kanta ta kalle shi, yanayin fuskarsa kad’ai ya tabbatar mata da cewar ba zai jira ta gama ba saboda haka ba tare da tunanin komai ba ta katse wayar.

“Kin san cewa Madaki zai zo garin nan?”

Muryarsa ta fito a hankali ba tare da ya ko zauna ba, Fulani tayi murmushi sannan ta ajiye wayar akan wani d’an k’aramin tebur mai kyau dake gefen kujerar.

“Na sani, samu waje ka zauna zamu yi magana dama.”

Ya d’anyi shiru yana kallonta da fararen idanunsa dake shaida halinsa na miskilanci da kuma tak’ama irin ta jinin sarauta sannan yace.

“In kina yiwa Allah Mami, kar kiyi wani abu da zai shafe shi wannan karon, don girman Allah ki barshi yayi abinda zai kawo shi ya tafi cikin lumana.”

A lokaci guda hasken fuskarta ya yaye, ta k’ank’ance idanunta tana kallonsa tace.

“Bana son mu dauwama muna maimaita abu guda d’aya Saif, idan kai baka san ciwon kanka ba ni na sani, kuma babu wani abu da zaka yi da zai sa na fasa k’udirina, idan yaso idan nayi nasara ka fito ka fad’awa duniya cewa uw*rka tayi laifin kwato muku dukiyarku a hannun wani bare.”

Sakan d’aya, biyu yana kallonta ba tare da yace komai ba, sai kuma ya juya kawai ya nufi k’ofar fita.

“Saifuddeen…”

Muryarta ta kira shi cikin kaushi amma bai ko juyo ba ya bud’e k’ofar ya fita, itama ta san ba zai dawo d’in ba, don a duniya kaf tafi kowa sanin halinsa, tafi kowa sanin cewa ya dad’e da daina yi mata biyayya akan duk al’amarin da ya shafi Madaki, kuma daga kansa ta koyi hankalin daina had’a al’amuranta da ‘ya’yanta.

STORY CONTINUES BELOW

Makusantan bayinta a kullum sune abokan shawararta amma ba ‘ya’ya ba, don bata tunanin zata iya jure bijirewar wani daga cikinsu bayan ta Turakin, alabarshi duk ranar data ci nasara sa ci moriyar fafutukarta.

Saifudeen ya cije lebb’ensa lokacin da fadawansa suka rufa masa baya bayan fitarsa, Allah ya sani yana son mahaifiyarsa kuma yana ganin kokarinta wajen kyautata rayuwarsu amma ko kad’an a yanzu baya k’aunar irin hanyoyin da take bi wajen cimma hakan, shi yasa baya tunanin zai iya cigaba da daurewa ganinta tana da aiwatar da ire-iren surkullenta…

Ya lumshe idonsa a hankali lokacin da zuciyarsa ke yanke shawarar cewa dole ne idan Madaki ya k’araso yaje ya gargad’e shi akanta, sai kuma ya runtse idanun nasa gabad’aya sanin cewa aikin banza zaiyi, don an dad’e da wuce zamanin da Madakin ke yarda dashi… Fulani ta riga ta shafa masa bak’in fentin da har abada ba zai tab’a goguwa a idanunsa ba.

A baya Madaki yaso shi, irin son da kowanne d’anuwa ke yiwa d’anuwansa, irin son da ubangiji ke halittawa a tsakanin jini da jini… Amma tun daga lokacin da yayi kuskuren ture hakan ya biyewa ra’ayin mahaifiyarsa, wannan son ya shud’e cikin tarihi.

Ya had’iye yawu a hankali cikin mak’ogwaronsa lokacin da duhun fatar idanunsa ya hasko masa wannan daren da ya shiga d’akin Madakin rike da layar da Fulani ta bashi, a cewarta daya d’ora ta kan goshinsa yana bacci ba zai k’ara farkawa ba kenan har abada…

Da kuma sanda Madakin ya bud’e ido ya damk’e hannunsa!

***

07:00 PM.

“Dan Allah Jidda muyi sauri mu dawo, na gaya miki Ibrahim yace min zai zo bayan anyi sallar isha, kinga ba dad’i yazo kuma ya tarar bana nan.”

Sadiya ta fad’a tana kallon Jidda wadda ke k’ok’arin sanya hijabi iri d’aya dana jikinta don shine uniform d’in makarantar daren da suke zuwa anan gefen Cikin gida.

“Wai nace miki kar ki damu babu abinda zai tsaida mu, da mun gama zamu taho k’ila ma har mu koma makarantar basu tashi ba amma kina zancen wai bayan isha.”

Sadiya ta d’auki jakarta dake gefe sannan tace.

“Tunani nake kafin mu iya gano wajen zai d’auki lokaci don…”

Jidda ta juyo da sauri ta rufe bakinta da yatsunta sannan da ido tayi mata nuni da inda Baddo ke kwance tana gyangyad’i.

“Sai kin tona mana asiri ne wai? Ki bari in mun fita sai muyi zancen mana.”

Ta fad’a a k’asan numfashinta kafin juya ta nufi saman wata ‘yar kanta a kusa da k’ofar kicin inda suke ajiye tarkacensu ta d’auko tata jakar, saboda k’arin tabbaci sai ta bud’e taga ‘yar karamar fitilar data saka a ciki tana nan da kuma wata wuk’a da suka daina amfani da ita sannan ta rufe.

“Baddo mun tafi makarantar dare.”

Baddo tayi saurin bud’e idonta tare da gajeren salati sannan tace.

“To Allah i kiyaye, Kinga d’ankwalin wata atamfata da Hajiya Laraba tace zata yanko min hijabinsa, in kun tashi ki biya ki kai mata dan Allah.”

Ta dawo baya ta karb’i d’ankwalin ta jefa a jakarta sannan tace.

“Sai mun dawo.”

Bayan sun fito sun rufo kofar net d’in d’akin ne Sadiya ta kalle ta tace.

“Wai Jidda ina Suraj d’inki kuwa?”

“Yana nan..” Ta fad’a tana kokarin gyara hijabinta.

“… Jamila ce take k’ok’arin ganin bayansa amma na san ta inda zan b’ullo mata nima.”

“Saboda me? Wani abu ne dashi?”

“Ina fa? Wai ala dole sai na rabu dashi tunda ita uw*ta ce ta gano wai wasa da hankalina kawai yake…”

STORY CONTINUES BELOW

Daga nan ta shiga bata labarin duk irin abinda Jamilan ke fad’a akansa, yayin da suke kurd’awa ta cikin manyan soraye da kuma tsakar gida na cikin masarautar har zuwa hanyar da zata sada su da Cikin gida maimakon hanyar islamiyar.

“Sadiya ina zaki?” Muryar wata Amina ta katse su a daidai bakin kofar shiga soron Sallama, suka juyo su duka biyun suka kalle ta, tana sanye da irin hijabinsu ta fito daga gidan Sallaman don iyayenta a gidan suke aiki.

Jidda ta gallara mata harara don tana d’aya daga cikin ‘yan group d’in da suka yi fad’a tare, Sadiya ta d’anyi inda-inda sannan tace.

“Baddon Jidda ce ta aike mu wajen Magajiya mu karb’o mata magani, kin san ta fad’i ranar kai amarya ta gurd’e k’afarta.”

Ta tab’e bakinta sannan ta juya tana fad’in,

“In kin makara zaki had’u da Malam Aminu ne.”

Sadiya ta d’an had’iye yawu sannan ta juyo ta kalli Jidda wadda ke bin bayan Aminan da harara.

“Kin san Allah har yanzu gabana fad’uwa yake yi, gani nake kamar fa za’a kama mu.”

“Idan ma an kama mu zance ke baki san komai cewa nayi ki rakani, don haka ki taho.” Cewar Jiddan tana yin gaba.

Mintina biyar daga nan ta kaisu zuwa cikin lambun inda suka samu suka shiga ta baya ba tare da ‘yan tsirarun mutane dake kai kawo a wajen sun gansu ba.

Tun Sadiya tana baya-baya har dai ta saki jiki ta ajiye jakarta suka tone sabuwar hak’ar da suka gano a k’asan wata bishiyar lemon tsami.

Basu da tabbacin inda suke hak’awa nan matan suka binne sai da idanunsu suka ci karo da abinda ke can k’asan ramin, wanda a maimakon laya, wannan karon wani abu ne mai d’auke da jini a jikinsa kamar hantar wata dabbar, Jidda tasa tsinin wukar da suka yi hak’an ta d’ago shi tare da ‘Bismillah’ yayin da jinin jikinsa ke d’iga, ai kuwa kamar wancan karon wani sassanyan k’amshi ya ziyarci hancinsu su duka biyun a lokaci guda.

“Anya kuwa wannan asiri ne? Na zata asiri wari yake.” Cewar Sadiya.

“Nima haka nace wancan karon…” Jidda ta fad’a tana k’arewa abin kallo.

“… Allah kad’ai ya san wane irin munafunci aka kulla a jikinsa da yake wannan k’anshin.”

Sai kuma ta d’ago ta kalli Sadiyan tace.

“Kina ganin mu k’ona shi anan?”

Ta rufe bakinta daidai lokacin da wata murya a bayansu itama tayi tata tambayar.

“Me kuke yi anan?”

“Jamila!”

Jidda ta fad’a da k’arfi lokacin da su duka biyun suka juyo suka kalleta idanu a zare, Sadiya ta dafe k’irjinta sannan tayi ajiyar zuciya a fili.

“Me yasa zaki biyo mu?” Jiddan ta sake tambaya.

“Me yasa kuwa ba zan biyo ku ba? Na fito daga gidan su Na’ima na ga kun kamo hanyar cikin gida maimakon ta islamiya.”

Ta fad’a tana kallonsu, sai kuma ta kalli hannun Jiddan sannan tace.

“Me ye wannan a hannunki?”

Da sauri Jidda ta bud’e jakarta ta jefa abin ciki sannan tace.

“Ba komai.”

“Ni zaki rainawa hankali ga abu na gani kice ba komai?”

“To ina ruwanki? Shuka muka zo mu yi… Ko Sadiya?”

Sai dai kafin Sadiya ta samu damar amsawa suka ji motsin tafiya na tunkaro su, sannan hasken fitila ya shiga haskawa akan bishiyun gefe kafin k’atuwar muryar wani namiji ta shiga fad’in.

STORY CONTINUES BELOW

“Waye anan? Nace su waye anan?”

Jamila ta juyo ta sake kallonsu.

“Waye shi kuma?”

“Bamu sani ba, watakila maigadi ne.” Cewar Sadiya bakinta na rawa.

“Kuna nufin bashi ya baku izinin shigowa ba?”

“Ke ya san kin shigo?” Jidda ta tambayeta.

“Banga kowa a k’ofar ba sanda na shigo… Wai Jidda me kuka zo yi nan ne?”

Jidda ta kalli hasken fitilar dake k’ara tunkaro su sannan tace.

“Guduwa zamu yi yanzu, in baza ki taho ba ki tsaya anan ya kama ki.”

Tana fad’in haka Sadiya ta damk’o jakarta dake gefe sannan suka ruga da gudu ta tsakanin jerin bishiyun dake wajen, Jamila ta juya ta kalli inda maigadin ke tahowa, zuciyarta ta gaya mata cewa babu abinda zata gaya masa idan yazo ya same ta anan sai kawai itama tabi bayansu.

Maigadin lambun mai suna Babangida ya k’araso wajen da saurinsa yana sake tambayar su waye sakamakon motsin da yaji, sai dai bakinsa bai k’arasa tambayar ba yaci karo da abinda ya sanya zuciyarsa hautsilawa tare da tsananin bugu mai k’arfi.

Aikin da wasu mata suka zo suka yi d’azu, aikin da Jakadiya Babba ta aiko ayi… aikin da yake sirrin Fulani, aikin da shi kansa ya sama masa dubu biyar a d’azu-d’azu bayan an gargad’e shi da kar ya baiyanawa kowa… Shi aka tone yashe a gabansa, jikinsa ya shiga rawa, fitilar hannunsa ta shiga k’ok’arin sub’ucewa amma yayi k’arfin halin rik’e ta ya k’arasa ya haska cikin ramin.

Anan wani bugun zuciyar ya k’ara kamashi, babu komai a ciki… Duk da bai san me aka saka ba amma yana da tabbacin matan nan har uku baza su zo su hak’a rami a banza kawai su tafi ba.

Tunaninsa ya rikice, sai kawai ya yar da fitilar sannan yayi hanyar waje da gudunsa ko Allah zai sa yaga wanda ya fita a lokacin.

***

A daidai wannan lokacin, daga can wani b’angare na masarautar, Madaki yayi parking motarsa k’irar kamfanin “Elantra’ a makeken filin da ake ajiye motoci. Motar sabuwa ce fil don kamar kowanne zuwansa haka yake karb’ar sabuwar mota a wajen mutumin daya saba cinikin hakan dashi, idan ya tashi tafiya kuma sai ya sake siyar masa da ita sannan ya bi jirgi ya koma.

Ya daidaita ta tsakanin tarin motocin dake zube a harabar wajen sannan ya zare muk’ullin daidai lokacin da sassanyar wak’ar ‘I Beleive in you’ dake tashi daga rediyon motar itama ta mutu, sai ya tattaro wayoyinsa guda biyu dake d’aya seat d’in ya had’a da muk’ullin sannan ya fito.

Zuciyarsa ta matse a lokaci guda sanda wata sassanyar iska mai d’auke da k’amshin ganyayyakin bishiyun wajen ta shiga hancinsa, wani kamshi daya had’u ya cakude dana bangwayen gidan… Gidan da ta sanadin sa rayuwarsa ta kyautata har ya zama abu mai daraja a idon duniya.

Ba tare da b’ata lokaci ba k’afafunsa suka nufi hanyar b’angare guda d’aya tal da duk fad’in masarautar zai iya shiga kansa tsaye, wajen da anan kad’ai zuciyarsa ke iya sakewa har yaji irin nutsuwar da kowanne d’an adam ke ji a lokacin da yake gida.

B’angaren Hajja wadda take tsohuwar matar Mai Martaba mai rasuwa, a yanzu haka ita kad’ai ta rage a cikin matan nasa don itace k’arama, kuma ita kad’ai ma tayi masa takaba. Sai dai ita Allah bai taba b’ata haihuwa ba don duk sauran ‘ya’yan gidan sun fito ne daga d’akin kishiyoyinta, shi yasa ba’a fiye bata wata daraja a masarautar ba.

Amma tsakaninta da Madaki akwai fahimtar juna sosai, don yana d’aya daga cikin ‘yan kad’an d’in jikokin gidan dake ganinta a matsayin ‘Kaka’.

Madaki ya shiga b’angaren daidai lokacin da yake amsa wayar ‘Sunusi’ mutumin da ya nemi ya nema masa iso wajen Mai martaba tun lokacin da ya shigo cikin gari.

STORY CONTINUES BELOW

“Yi hakuri ranka ya dad’e, wallahi ance Mai martaban wanka ya shiga ne bayan zaman fadan, amma na samu fad’awa Kilishin, yanzu zai aikawa Jakadiya ta isar da sak’on insha Allah.”

“Shikenan.”

Ya fad’a kawai sannan ya katse kiran, Allah ya sani yayi kewar wannan lokacin da k’ofa kawai zai bud’e ya gana da mahaifin nasa.

Cikin b’angaren babu bayi sosai kamar yadda yake a koyaushe, sai tsilla-tsilla kawai dake ‘yan k’ananan ayyuka, don haka a gajarce ya amsa gaisuwarsu sannan ya shiga cikin makeken falon na Hajja wanda a ciki k’ofofin d’akunan kwananta biyu suke, k’amshin sabon fenti da kuma na turaren wuta suka ziyarci hancinsa a take, ya riga ya sani cewa mahaifinsa yana d’aya daga ciki d’aid’aikun ‘ya’yan dake kulawa da ita da kuma muhallinta.

“Yo ai ni da naga dare ya raba, cewa nake labarin k’anzon kurege aka kawo min da akace zaka zo.”

Muryarta ta fad’a a daidai lokacin da yayi sallama ya sanyo k’afarsa cikin d’akin, sai ya d’ago idonsa daga kan wayar hannunsa ya kalle ta zaune daga cikin kyawawan kujerun falon, sannan a gefe kuma ga shimfid’ar bargonta nan a k’asa, shimfid’ar da kullum ya santa akai.

Ya d’an tsaya daga tsakiyar falon kafin yace.

“Wai shekaru aka rage miki ko me? Har kike iya hawa kujera?”

“Ai labari baya shiga Ikko, shi yasa baka san cewa na koma budurwa shar ba, amma tunda Allah ya kawo ka yanzu, kaga sai a sake aure kawai..”1

Suka yi dariya gabad’ayansu har da wata ke tsugunne wadda da alama ita ta kawo mata labarin shigowarsa. Sai ya k’araso ya zauna kan shimfidar tata dake k’asa yayin da jakadiyar tayi sallama ta fita.

“Wallahi na d’auka k’arya yaran nan suke min da suka ce wai a cikin gida ana ta rad’e-rad’en zuwanka, ashe da gaske suke… Wa yaga wata sabon gani. “

Madaki ya zube wayoyin hannunsa a k’asa sannan ya koma ya kishingid’a da bayan kujerar.

“Ki bari kawai Hajja, aiki ne ya kawo ni kuma nasha wahalar tuk’i daga Kano wallahi, sannan nazo nayi ta gararamba a cikin gari wajen neman abinci, kwata-kwata na manta kina raye.”

Hajja ta d’anyi dariya sannan tace.

“Yanzu ma ai bata sauya zani ba, in dai abinci ne sai ka ture Madaki, ice dai ko kayi Sallah ko?”

Ya lumshe idonsa kafin yace.

“Har da wadda bakya yi, nafila ba.”

Sai ta sake yin dariya tana fad’in..

“In kai ke karb’a ai sai ka ture idan nayi..”

Sannan ta juya ta danna wata k’ararrawa a gefe ta kiran masu aikinta kafin ta sake juyowa ta kalle shi, mamaki ya kamata a lokaci guda ganin ya rufe idonsa ruf kamar wanda bacci ya d’auka, don haka sai ta fasa maganar da take shirin yi ta mik’e da kyar don bashi waje ya runtsa. Allah ya sani zuciyarta na tsananin tausayin Madaki, akwai tausayawa sosai a rayuwar namijin da ya rasa kulawar uwa da kuma duk wani mahaluki a duniya da zai iya kallo ya kira da nasa na ‘Jini’.

Ko kad’an Madaki ba bacci yake a lokacin ba, ya rufe idonsa ne kawai saboda wani irin ciwon dake harbawa a tsakiyar kansa ga kuma tarin abubuwan da suka cakud’e a tunaninsa.

Bayan tsare-tsaren yadda zai gudanar da aikin da ya kawo shi, akwai tunanin ayyukan daya baro da kuma tunanin yadda Mubarak zai iya dasu, sannan bugu da k’ari har yanzu zuciyarsa a hargitse take, yayi zaton zai samu nutsuwa idan har ya riga ya iso cikin garin ‘Kiyarin’ amma tunda yazo d’in har a yanzu bai ji ya dawo daidai ba, fatan sa d’aya kawai ubangiji yasa ba ciwonsa ne ke shirin tashi ba.

Bayan wani lokaci ya bud’e idanunsa ya kalli agogon dake kafe a jikin bango, k’arfe takwas har da ‘yan mintuna, ya ja tsaki kad’an don kusan minti talatin kenan a amma har yanzu Sunusin bai sake kira ba.

STORY CONTINUES BELOW

Yana da abubuwa fa da yawa a gabansa, don bayan ya gama ganawa da Mai martaba, dole ne yazo ya tafi masaukinsa kuma, don kamar kowanne zuwa akwai guest inn da yake zuwa ya kwana a cikin gari.

Ya lumshe idanunsa ya sake bud’e su sannan ganinsa ya sauka akan makeken hoton da aka d’auka ranar nad’in mai martaba, yana kafe kusan bango guda tun daga sama har k’asa don yafi tsawon k’ofar d’akin ma, d’auke da siffar kownne jini da ya shafi gidan sarautar har da shi kuwa.

A cikin tarin fuskokin nan idanunsa suka sauka kan fuskar matar data tarwatsa rayuwarsa kuma ta zamo silar mafi yawa na bak’in cikinsa.

Zai so kwarai ace bata san da zuwansa ba amma hakan ba mai yiwuwa bane, saboda ya san dole ne ma daga bakin Mai martaba zata ji, saboda ya riga ya yarda da ita kamar irin wannan yardar da uwa ke bawa d’anta, kuma shima duk irin abinda ke tsakaninsu bai tab’a bashi shakkun da zai canja tunaninsa akanta ba.

Wa ya sani ma ko ta riga ta shirya masa wani tanadin nata?

**

“Ibrahim..”

Bayan wucewar rabin awa, cikakkiyar muryar Mai martaban ta kira sunansa sanda ya samu ya isa cikin turakarsa.

A lokaci guda wani sanyi da yafi k’arfin na Acn dake hurawa a d’akin yabi cikin jijiyoyinsa, sai ya durk’ushe gwiwoyinsa gaban mutumin daya kyautata rayuwarsa, ya daraja shi ta kowanne fannin daya bashi cikakken suna na ‘Mutum’ sannan ya dank’a masa amanar da ko ‘ya’yan cikinsa bai bawa ba.

“Barka da yamma ranka ya dad’e.”

Muryarsa ta fito cikin sadda da kai da darajawa bayan irin zaman girmamawar da yayi.

“Barkan mu dai, tun safe nake ta zuba ido a hanya nayi tunanin ai sammako zaka yi.”

Kulawar dake cikin muryar ta faranta ransa a take, don ita d’in wani babban gib’i ne a rayuwarsa, ‘Kulawa’ kalma ce kawai da yake jin ta a baki.

Sai ya k’ara sunkuyar da kansa sannan ya amsa.

“Na d’an tsaya a garin Kano ne bayan saukata ranka ya dad’e, sannan bayan na iso cikin garin nan kuma na biya ta wani wajen shi yasa ban iso da wuri ba.”

Sarki ya gyad’a kansa tare da fad’in.

“Haka ne, fatan dai kana lafiya ko? Yaya jikin naka yake yanzu?”

Sai ya had’iye yawu kad’an jin nauyin da tambayar tayi masa, don tun farkon rashin lafiyarsa ne watarana ya nemi shi a waya, Mubarak ya d’auka kuma har yayi kuskuren shaida masa cewar yana kwance ne baya jin dad’i, shikenan tun daga wannan ranar bai tab’a daina tambayar lafiyarsa ba, wanda a yanzu kusan shekara biyu kenan da faruwar hakan.

Zuciyarsa ta matse da tunanin yaya zai ji idan har ya san abinda yake b’oye masa tun daga wancan lokacin, yaya zai ji idan har ya san cewa wannan rashin lafiyar itace mafarin ciwon da ya hargitsa rayuwarsa?

A hankali ya lalubo muryarsa sannan ya amsa kalmar ‘Da sauki’

“Wannan karon ban yarda da kwananka a ko’ina ba Ibrahim, Na sanya an tanadar maka masauki a cikin gidan nan kaje ka huta, duk sauran wata magana zamu yi ta a tsanake, don nima ina da magana mai muhimmancin da nake son mu tattauna.”

Sai ya hadi’ye yawun da bai san da zamansa ba don cikin maganganun guda biyu bai san wacce tafi d’aukar tunaninsa ba, jin cewa a yau Sarkin ne da kansa yasa aka tanadar masa masauki ko kuma taraddadin mecece maganar daya kira da ‘mai muhimmanci’… don zai iya tunawa lokacin na karshe da ya furta masa kalmar muhimmanci shine wannan ranar daya d’auki dukiyarsa gabad’aya ya dank’a a hannunsa.

***

Washegari, 9:05 am.

Bayanta ya fara gani lokacin da ya d’ago daga danna wayar da yake yi, don suna tsaye ne daga jikin wata katanga ta wani dogon gini da bai san na meye ba, tana sanye cikin wata doguwar riga kalar ruwan makuba da mayafi mai kyalli, shigarta tayi kama sosai da mai shirin zuwa wani taro na musamman, sai dai hannunta na dama na rik’e ne da wani k’aton bokitin k’arfe duk yayi tsatsa.

STORY CONTINUES BELOW

Watak’ila k’arar takunsa suka ji, don a lokaci guda Saurayin ya d’ago ya kalle shi sannan itama ta juyo gabad’ayanta zuwa saitinsa…

Yarinya ce ba kamar yadda yayi tunani da farko ba sannan fuskarta na d’auke da murmushin da ba nasa ba, don suna had’a ido tayi saurin tsuke bakinta kafin kuma idanunta su haska cikin nasa da kallon rashin sani kamar yadda matashin ke kallonsa shima.

Sai kawai ya juya ya koma ta hanyar da ya fito, domin daman yana bin hanyar da babu mutane ne don ya samu ya isa ga b’angaren Saifuddeen ba tare da idon sani ya lura dashi ba. A yau k’arfe sha d’aya zai fara ganawa da masu kwangilar ginin kamfanin kuma ya riga ya yanke shawarar cewa tare da Saifudden zasu halarci wajen… Saboda gaskiya maganar Mubarak ke nufi, lokaci yayi da ya kamata ya fara sako shi cikin al’amuransa.

Jidda ta juyo ta kalli Suraj dake tsaye a gabanta tace.

“Waye shi?”

“Watakila wani d’an masu kud’in ne ya biyo ki.”

Ya fad’a tare da d’aga kafad’unsa, sai ta gallara masa ‘yar harara da gefen idonta tana murmushi tace.

“Ko kuma zuwa yayi ya kama ka ba.”

‘Ni?..” Ya tambaya yana nuna kansa.

“Me nayi da za’a kama ni?”

“Kace min zaka zo tun ranar nan, amma sai yau na ganka.”

Ya shafo lallausar sumar kansa data sha gyara sannan yace.

“I’m sorry dear, na gaya miki karatu ne yake rik’e ni, sannan kuma tunda muka bar nan bana iya shigowa masarautar nan sosai.”

Sai tayi murmushin daya tala d’an lebb’enta.

“Shikenan yanzu dai ya wuce, meye a k’asa?”

Shima yayi murmushin da bai shirya masa ba yana kallonta.

“In kina magana wani lokacin sai ace ke ‘yar kasuwa ce.”

“Au baka san muna kasuwanci ba? Jamila fa tana siyar da ‘yan kunnaye.”

“Jamila, wannan yayar taki da bata sona.”

Ta sunkuyar da kanta sannan ta girgiza shi tana kallon hannun data rik’e bokitin.

“Ba haka bane kawai dai ina jin bata fahimceka bane.”

Ya sake wani guntun murmushin yace.

“Ai ni ba karatu bane da zata fahimce ni Jidda, anyway zan wuce makaranta ne nace bari nazo in tambaye ki yaushe zan zo ki raka ni wata unguwa?”

Sai ta d’ago ta kalle shi da fararen idanunta sannan ta girgiza kai.

“Kaima ka san ba zai yiwu ba ai.”

“Saboda me?”

“Saboda Baddo baza ta tab’a barina ba, yanzu ma fa nace mata zan je d’ebo ruwa ne amma da sai ta tambaye ni ‘da safen nan ina zaki..”

Ya kalli bokitin hannunta da yasha tsatsar sa ta k’asa sannan ya girgiza kai, ya dad’e da fahimtar cewa ita in zata yi abu kawai zata yishi babu ruwanta da wani iyayi.

“Ai ba sai kince mata ni da ke zamu je unguwa ba Jidda, zaki iya ce mata kawai zaki je wani wajen ne.”

“Ta riga fa ta san ban san ko’ina ba a wajen masarautar nan, ina zan raka ka ne ma?”

Ya d’an gyara tsayuwarsa yana kara hard’e hannuwansa a k’irji.

“Gidan wani abokina ne da matarsa, ina yawan basu labarinki kuma sun matsu su ganki, shine nayi musu alk’awarin zan kawo musu ke.”

Tayi shiru na wasu ‘yan sakanni kafin ta gyad’a kanta.

“To shikenan zan gwada, sai muje tare da Sadiya ince mata zan raka Sadiyan wani waje ne.”

“Sadiya kuma?” Ya tambaya yana girgiza kansa.

“Ni ke kad’ai na gaiyata banda ita.”

Ta d’an bud’e baki saboda mamaki.

“Menene in taje?”

“Yaya za’ayi in d’auke ku biyu? Infact ni bana son irin gulmar k’awayen nan ma.”

Ranta ya soma b’aci.

“Ai kuwa wallahi Sadiya ba ruwanta da wata gulma, sannan ma ta yaya wai zan bika wani waje ni kad’ai?”

Sai ya had’e ransa shima.

“Oh kina nufin baki yarda dani ba kenan? Wai Jidda for how long ne muke tare?”

Idanunta suka nuna nazari kafin tace.

“Shekara biyu.”

“Kuma a duk a cikin lokacin nan ban samu yardarki ba? Kenan aikin banza nake tayi.”

“Aikin banza? Zama tare dani d’in ne aikin banza?”

“Idan ba aikin banza ba me kenan? Ace yarinyar da nake so tana min kallon cewa zan iya cutarta?”

Ran Jidda ya k’ara b’aci, taso ta gaya masa magana itama amma kalmar ‘Yarinyar da nake so’ ta danne b’acin ran nata saboda haka tace.1

“Ba haka nake nufi ba Suraj, kaima ka san ko a musulunce bai dace bane in bika wani waje.”

“Ai ba haka kika ce da farko ba, Just… Kin gane… ina ga zan makara bari in tafi kawai.”

Sai yanayin fuskarta ya canja zuwa damuwa kafin muryarta ta fito a hankali.

“Fushi kayi?”

Ya girgiza kansa ba tare da ya kalle ta ba.

“Ko kad’an, kin fad’a min ra’ayinki game dani ne kawai kuma na fahimta.”

Ta shiga mutsikka yatsunta cikin juna kanta a k’asa sannan a hankali ta sake magana.

“Kayi hakuri…”

“Ki manta kawai, Sai anjima.”

Da haka ya juya ya barta a wajen, a lokaci guda ranta ya taru ya k’ara dugunzuma, ta san tana son Suraj amma wannan abinda yayi mata rainin hankali ne, hak’uri fa ta bashi amma ya wuce ya barta a tsaye? har ya isa yayi fushi ma bayan itace da gaskiya? A tunaninsa zata kama hanya ne kai tsaye ta bishi wani waje? Me ya maida ita?

Sai kawai ta cije lebb’enta na k’asa sannan ta gyad’a kai cikin kwafa, bata tab’a nuna masa wacece Maijidda bane.4

***

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *