ZANEN DUTSE CHAPTER 5 BY AISHA-SHAFIEE

ZANEN DUTSE CHAPTER 5 BY AISHA-SHAFIEE

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

ASALIN LABARIN.+

Kowanne labarin duniya yana da tushe. Kowanne yana da mafari. Me kenan? Wani abu da ya faru har ya zama sanadin wanzuwar jirkitattun al’amura.

Zahra Tabi’u. (Farin Wata)2

YOLA, Jimeta.

Shekarar 1987.

Motar ƙirar Peugeot ce 305, mai kalar ruwan ƙasa sabuwa dal sai ƙyalli take cikin hasken safiyar da rana bata gama buɗewa sosai ba, fitilar danjojinta a kunne suke yayin da ƙarar horn ke fita daga cikinta alamun matukin na jiran a bude masa tangamemen gate din ginin dake gabansa wanda a samansa aka zana harafan sunan ‘Sectariate’ (Sakateriyar ƙaramar hukumar ta Jimeta)

Minti daya, biyu, sai gate din ya bude cikin sauri motar ta kutsa ta karasa ciki.

“Allah ya huci ranka yallabai, Allah ya ƙara girma, ayi mana afuwa wallahi muna can ciki ne ana tattauna wani al’amarin da ya faru.”

Dattijon da ya bude kofar ta fada cikin durkusawa yayin da hannunsa ke dunkule a iska yana kallon matuƙin cikin motar wanda yaja ya tsaya bayan shigarsa ciki.

Alhaji Ahmad Uba Kamsusi wanda ke riƙe da muƙamin ‘H.O.D Community Development’ anan cikin sakateriyar ya juyo ya kalli maigadin da mamakin daya maye gurbin ɓacin ransa kafin yace.

“Wane al’amari ne ya faru?”

Lawan maigadi ya sake sunkuyawa.

“Wallahi yallabai yaro su Haruna suka tsinta a can ta baya wajen da ake kiwon shanun nan ɗazu da asuba, to shine ake ta jajanta zancen.”

“Yaro? Wane irin yaro Lawan?”

“Alhaji wallahi yaro dai, dan mutum, zai kai kusan shekaru huɗu a ƙiyasi, kuma anyi maganar duniyar nan yaƙi cewa komai balle a san dagaina yake, tunda tun da duhu a gari shi Harunan ya ganshi tsakanin shanu biyu yana bacci.”

Maganar ta ɗan tsaya a ran Alhaji Ahmad kafin ya girgiza kansa yace.

“Allah ya sawwake.”

Sannan yaja motarsa zuwa ciki, ƙaton waje ne mai dauke da ƴan gine-gine tsilli-tsilli na mabanbantan ma’aikatu kamar dai kowacce sakateriya take, ga bishiyu fal na darbejiya da wasu dangin na ƴaƴan itatuwa, daga gaba ne ma kaɗai wajen yake da katanga da kuma gate, amma zuwa can ƙarshe baya ya haɗe ne da dajin da zai fidda kai har wani bangare na cikin garin yola.

Alhaji Ahmad ya ƙarasa gaban ginin ofishinsa ya ajiye motarsa sannan ya fito, sai dai saɓanin yadda a kullum yadda zai zo ya tarda da ofishin nasa a bude masinjansa ya share ya jera abubuwa, sai arba yayi da katon kwaɗon da bai taba ganinsa ba, ya sani cewa akwai muƙullin kwaɗon a cikin na wajensa, amma maimakon ya buɗe sai ya zagaya ta baya don neman wanda zai tambaya yaji lafiyar masinjan nasa, tunda a jiya sun rabu lafiya ƙalau kuma bai taba ganin ya makara irin haka ba.

Ai kuwa yana zagayawa ta baya, sai ga Musa, wani matashi dake aikin kula da shuke-shuken wajen yana jan ruwa, bayan Musan ya gaishe shi be sai ya tuntuɓe shi da tambayar inda Iliya masinjan nasa yake.

“Ai yallabai can na baro shi ɗazu wajen yaron nan da aka tsinta, da yake yana wajen sanda su Haruna suka kawo shi, kuma naji dai suna maganar tafiya wajen mai unguwa, to bayan na taho dai ban sani ba ko sun tafin.

Alhaji Ahmad ya tsaya da mamakin wane irin yaro ne haka da za’a tsinta kuma gabadaya hankalin ma’aikatan yayi kansa? Kamar ya juya ya koma ofishinsa sai kuma ya sake kallon Musa yace.

“Kaini in da suke naga yaron.”

Musa ya ajiye gugan hannunsa sannan yayi gaba tinkis-tinkis suka dinga bi ta kan barandun gine-ginen wajen har zuwa wajen harabar ginin masallaci, inda bishiyu suka yi wajen ƙawanya, iskar safiya na ratsa ganyayyakinsu tana fitar da wani ƙamshi mai daɗi.

STORY CONTINUES BELOW

Daga bayan masallacin ya tadda dandazon mutane wanda mafiyawancinsu masu aikin wajen ne sai kuma tsilli-tsillin ma’aikata irinsa wanda suma da alama zuwansu kenan suka tsinci zancen.

“A’a yallaɓai, da kanka? Ashe ka samu labari kenan? Wallahi yanzu isowata kenan nima Lawan maigadi ke sanar dani nace bari nazo na gani.”

Cewar Alhaji Isah, wani ma’aikaci shima a cikin sakateriyar, mai yawan son burga da nuna iko yana magana muƙullin motarsa ƙirar marsandi a hannu sai kaɗa shi yake yi. Alhaji Ahmad ya gyaɗa kansa sannan yace.

“Allah ya sawwaka, ni ai har na karasa ofis sai na ganshi a ƙulle Iliya bai buɗe ba, na tambaya kuma akace yana nan shine nace to bari inzo in gani me akeyi ne haka.”

“Wallahi fa ranka ya daɗe…”  Alhaji Isan ya faɗa, yana kiransa da inkiyar da kowa a ma’aikatar ke laƙaba masa ta ‘yallaɓai’ ko kuma ‘ranka ya daɗen’ sanin cewa shine ɗa na farko a wajen mai martaba sarkin Kiyari.

“Yaro ne ƙarami na ganshi, kuma ba hausa ba fulatanci, anyi masa yare kala-kala ma ya kasa mayarwa, kuma an rasa wanda ya sanshi, to shine wai suka yi masa wanka zasu kaishi wajen mai unguwa ayi cigaba da cigiya.”

Alhaji Isah ya rufe bakinsa daidai lokacin da wasu ma’aikatan da suka iso a lokacin ke ƙarasowa wajensu don suma su ji ba’asin me ke faruwa. Alhaji Ahmad yasa aka kira nemo masa Iliya a cikin mutanen wanda ya ƙaraso da sauri yana mai neman afuwa.

“Je kace su ƙaraso mana yaron mana nan su ganshi.” Alhaji Isah ya faɗa cikin nuna son iko irin nasa tun kafin Iliyan ya gama durkusawa.

Iliya ya juya da sauri ya nufi can gefen masallaci, ƴan mintuna kaɗan sai gashi tare da wasu mutane biyu sun nufo inda suke, kums tun kafin su ƙaraso idanun Alhaji Ahmad suka gano masa yaron dake riƙe a hannunsa, ƙarami ne kamar yadda suka siffanta don ba zai fi shekaru hudun ba, sai dai bai san me yasa ba idonsa ya kasa ɗaukewa daga kansa ba har sanda suka karaso gabansu, yaji muryoyinsu na gaishe shi amma har a lokacin yaron yake kallo.

Daga ganinsa zaka kiyasta cewa yana da jikin da yafi nasa girma, amma wataƙila saboda wahala ko yunwa, ya rame ƙwarai har wuyansa na nunawa, idanunsa madaidata ne, masu aheƙi kamar ya tara kwalla a ciki yayin da suke jujjuyawa kan dukkan mutanen dake tsaye a wajen.

“Wallahi yallaɓai a tsakanin shanu biyu muka dauko shi, da fari da kyar ma muka yarda mutum ne sai da duhun asuba ya yaye tukunna sannan muka ganshi sarai! Yanzu ma Lado ne ya kawo kayan ɗansa aka canja masa da yake na jikin nasa sunyi datti kwarai.”

Cewar ɗaya daga cikin mutanen kenan, yayin da yake bayanin suna duban yaron.

“Yanzu gidan Mai unguwan zaku kaishi kenan?” Alhaji Isah ya tambaya.

“Eh yallabai, don anyi masa tambayar duniyar nan baya iya mayarwa, to can zamu kaishi in Allah yasa anyi sa’a, sai a samu iyayensa.”

Mafi yawan mutanen dake wajen suka hada baki da fadin ‘Allah ya kyauta’ kafin kowa ya juya ya nemi hanyar ofishinsa.

Sai dai har sanda Alhaji Ahmad ya isa cikin nasa ofishin, fuskar yaron nan bata bar wulgawa a ransa ba, mamaki yake mai haɗe da tunanin yadda iyayen ɗan ƙaramin yaro kamar haka zasu yi sake dashi har ya baro gida a cikin duhun asuba haka, a halin da ake ciki shekararsa uku kenan da aure babu haihuwa, kuma a yadda suke ƙulafucinta shi da matarsa, baya hango cewar ko sun haifi guda goma zasu iya wannan gangancin.

Haka yayi ayyukansa a daddafe a wannan ranar ya koma gida, fuskar ɗan talikin yaron nan bata bar ransa ba, kuma duk tarin ayyukan da yaci karo dasu a kwanakin da suka biyo baya basu kore waɗannan kyawawan idanun yaron ba.

Ƴan kwanaki kaɗan bayan hakan sai ga Iliya masinjansa ya shigo da tsakar rana.

“Iliya ya akayi? An karbo min sako na daga layin Jodan?”

STORY CONTINUES BELOW

Iliya ya kai har kasa a gefen teburinsa kafin ya amsa.

“Eh ranka ya dade shirin tafiyar naje dama, to sai Haruna kuma yazo da wani zance.” Ya faɗi haka yana ɗan sosa bayan kunnensa.

Ba tare da ya ɗago ba ya tambaya.

“Zancen mene ne?”

Iliya ya sake ƙasa da muryarsa.

“Wallahi Alhaji akan yaron da aka tsinta ne kwanakin baya, to bayan an kai shi can gidan mai unguwar anyi neman duniya ba’a sami ko da wanda ya sanshi ba, shi kuma yaron yaƙi yayi magana har yanzu, to shine mai unguwar yasa aka dawo dashi yace wai wallahi ya daina riƙe yara irinsa saboda wai ana samun matsala daga baya, kuma a yanzu haka ma gaskiya da yara da yawa a wajensa, ba zai iya ɗaukanr nauyinsa ba.

To shine yanzu Harunan yake neman kudin mota wai zamu je mu kai shi gidan marayu na can kan hayi, sai nace bari in tambaye ka yallaɓai ko zamu samu ƴan canji aje a kai yaron…”

Tunda ya fara magana Alhaji Ahmad ya ajiye biron da yake rubutu ya ɗago ya kalle shi.

“Yanzu ina yaron?”

“Suna can bakin gate ranka ya daɗe don basu ma shigo dashi ba.”

“Je ka ce su kawo shi.” Kai tsaye ya faɗa ba tare da wani tunani ba. Kuma shima Iliyan bai yi wani tunani ba ya mike da saurinsa ya juya.

Alhaji Ahmad yabi kofar da kallo abubuwa da yawa na wassafawa a tunaninsa, tausayin yaron dake kwance a ƙasan ransa ya sake tasowa, wannan wace irin masifa ce? Ace har kwana nawa iyayen yaron nan basu neme shi ba, ashe shi yasa ya kasa mantawa dashi?

Mintuna kaɗan sai ga Iliya sun shigo dashi da Haruna da kuma yaron, kallo daya Alhaji Ahmad yayi masa ya tabbatar da cewa inda aka kaishi ɗin babu wani canji daga wahalar da ya fito, wataƙila ma sai ƙarin rashin kwanciyar hankali da fargaba don waɗannan idanun nasa da ya kasa mantawa dasu sun ƙara ɗashewa cikin maiƙonsu

Wani ɓari na zuciyarsa ya matse tare da tunkudowar wani abu da bai gama tantance shi ba a lokacin, abinda ya sani kawai shine, gidan marayu ba maslaha bace game da yaron, rayuwarsa zata cigaba da tafiya ne babu wani bigire mai inganci. Sai yaji cewa kamar Allah ya nuna masa wata alama ne da zai iya kare hakan daga faruwa ta hanyarsa, don da ace ba wajen sa suka zo neman kuɗin motar nan ba da wataƙila a yanzu haka ma suna titi.

“Yaka zo.”

Kai tsaye  muryarsa ta kira yaron dake rakuɓe a hannun Iliya yana kallon sa cikin rauni.

A lokacin guda tsananin mamaki da da kaduwa ta sanya su Haruna da.l Iliya buɗe bakinsu, don tun daga lokacin da suka tsinto shi, yaron baya taɓa gane dukkan maganar da ake masa, amma sai gashi a yanzu ya saki hannun Harunan ya nufi wajen Alhaji Ahmad, wani abu daya dasa mafarin rubutacciyar ƙaddarar dake ajiye a gurin Allah, domin a take a wajen  zuciyar Alhaji Ahmad bata nemi shawarar kowa ba ta yanke hukuncin karɓar yaron, su kansu su Iliya sunyi mamakin jin hakan don har aka gama fafutukar cike-cike a ofishin gidan marayun inda suka hadu suka tafi gabaɗaya  basu bar tunanin cewa Alhaji Ahmad zai iya fasawa ya canja ra’ayi ba.

Sai da ya buɗe gidan gaba na motarsa ya bude ya sanya yaron a ciki ya ja motar zuwa hanyar gidansa, sannan zuciyarsu ta tabbatar da zahiri.

Su suka tsaya suka bada shaida mai kyau akansa bayan an debi duk wasu bayanai da manya da ƙanana nasa, sannan dasu aka tabbatar cewa zai riƙe yaron tsakaninsa da Allah kamar yadda yayi alƙawari kuma wataƙila hakan ne ya faranta ransa har yayi musu kyauta mai tsoka bayan fitowar tasu.

***

Hafsat Muhammad Gani.

Matashiyar budurwa ce dake tsananin ji da kanta a bangaren kyau da kuma dukiya ta mahaifinta wanda ya kasance hamshaƙin ɗan kasuwa. Tayi tashe mai tsawo a zuciyoyin ƴan siyasa da kuma Alhazawan da suke ganin sun isa su mallake ta, sai dai Allah baiyi ita ɗin rabon kowa bace sai Alhaji Ahmad Uba Kamsusi, ɗa na farko a wajen Sarkin garinsu da kowa ke mutuƙar darajawa.

STORY CONTINUES BELOW

Sun haɗu ne a watarana da ta raka mahaifiyarta fada don halattar tafsirin ƙarshe na azumin watan ramadana, anyi sallar magriba har ma an raba ɗimbin kayan cima kala-kala a matsayin kayan shan ruwa, ana dab da fara tafsirin ne ta biyo hanyar soro na uku don komawa sashen da suka sauka na matar Galadima ta dauko jakarta.

Ta shiga soron a daidai sanda ma’aikatar wutar nepa suka zabi lokacin don su dauke wuta, sai kawai ji tayi taci karo da mutum yana tahowa, tayi baya zata fadi amma sai taji hannu ya tare ta.

“Idan waje babu haske, ki dinga tsayawa har sai hasken ya dawo ko kuma ki juya.”

Mai maganar ya faɗa cikin wani irin sauti mai kwarjini. Sai tayi saurin yin baya ta fita daga hannun nasa sannan tace.

“Kaima ya kamata kayi amfani da hakan don ka daina buge ƴaƴan mutane a cikin duhu.”

“Wanda ya san hanyarsa bashi da matsala musamman a gidansu, ƴaƴan mutanen da basu san koina ba su ya kamata su dinga kiyayewa.”

Ya faɗi hakan a daidai lokacin da hasken wutar ya dawo, don daman ɗaukewar tata bata wuce wasu ƴan sakanni, Hafsatu ta ɗago ido ta kalli wanda ke tsaye a gabanta, wata fuska da ko yaro mai rarrafe a Kiyari ya santa, fuskar da ko a jiya da safe data je kaiwa mahaifinta shayi, akwai ta a jikin jaridar da yake karantawa.

Shi kadai kwallin kwal! Amma ya cika rabin soron a idanunta, sanye yake da rantsatstsun kayan da samari mara sa aikin yi zasu iya musu har da zage-zage akan tantamar farashinsu, sai tayi saurin sadda kanta kasa sannan tace.

“Ayi hakuri ranka ya daɗe.”

Mafarin kenan! Domin ba’ayi sati ba sai da yasa aka nemo ta har cikin gidan mahaifinta da wani bayani mai girma, wani bayani daya haddasa farin ciki a zuciyar iyayenta dama duk wanda ya raɓe su, wani bayani da yasa ta tattara duk wasu samarinta sababbi da tsoffi ta zuba a kwandon shara, don Ahmad shi kaɗai yana da duk wani qualities da guda ashirin ɗinsu suka tara, to me take nema dama? Kuɗi, ɗaukaka, mulki, wayewa dama duk wasu ƙananan abubuwa da mace zata iya hasashensu a mijin da take fata.

Tana tuna wannan lokacin kamar jiya, bidiri da bikin da aka sha sai da labari ya mamaye garuruwa cewa ita din tayi aure na girma! Wani aure da har a yanzu da ake lissafin shekaru bata ga makamancinsa a kurkusa ba.

Ta gama yanka tufa ta ƙarshe ta rufe farantin, a yanzu ƙarfe shida ne na yamma, aikin Ahmad na ƙananan hukumomi ne, don haka a kodayaushe cikin canje-canjen wajen zama suke, ɗadinta shine tun bayan da suka baro gidansu inda aka yi mata jere, kayan sawarta kawai take dauka a duk sanda aka canja masa wurin aikin, suna tadda komai a gidan da zasu tare. Don haka tun bayan dawowarsu Jimetan ƙarfe huɗu da ƴan mintuna kullum yake dawowa gida, amma a yau sai gashi har ƙarfe shida bashi ba alamarsa, ta tabbata dai duk abinda ya tsare shi to lallai a yanzu yana kan hanyarsa.

Bata kai ƙarshen tunaninta ba kuwa taji ƙarar motarsa na durfafowa, kasancewar wajen quaters ne shi yasa shiru ke fallasa komai. Sai ta ajiye farantin kan ɗan ƙaramin teburin tsakiya na falon inda ta jera masa kulolin abincinsa kafin tayi hanyar fita. A yau tayi ado ne da wani rantsatstsen leshinta da tun daren amarcinsu rabon data sanya shi, don haka take son ya fara yin tozali da hakan tun kafin ya shigo don ta sanya farin ciki a zuciyarsa.

Tana son Ahmad kuma a zamansu bata da wata matsala, kuɗi ne gasu nan falala da zarar ta tambaya sannan ga tsananin kulawa da take samu daga gare shi, idan akace sunje Kiyari kuwa cikin masarauta, to ko mahaifiyarsa bata fita iko ba. Matsalar ɗaya ce, Haihuwa! Ta sami magaji don ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ta faranta ran Ahmad na samun ƴaƴa, ta kuma samarwa kanta magajin dukiyarsa, kuma hakan mai yiwuwa ne kwanan nan don mahaifiyarta ta haɗa ta da wani sabon malami a yanzu kuma bata da shakka a kansa.

STORY CONTINUES BELOW

Ta fito ta barandar gidan lokacin da motarsa ke tsayawa, fuskarta dauke da murmushi tana kallonsa ta cikin motar, kuma ko kaɗan idanunta basu hango ɗan kan yaron dake zaune a kujerar gefe ba. Ya kashe motar ya fito sannan ya zagayo, sai dai maimakon ya iso ya rungumeta kamar yadda tayi hasashe sai taga yaja hannun ƙofar gefe ya buɗe, kuma har ya gama kwance seatbelt ɗin jikin kujerar bata yi tunanin ɗan mutum zai fiddo ba, a hasashenta ya wuce ledar lesuka da atamfofi sababbin yayi daya gani ya siyo mata?

Ɗan yaro ne ɗan ƙarami, sai dai duk ƙankantarsa akwai wani abu mai girma kamar kwarjini tare dashi, zuciyarta ta buga sanda kyawawan idanunsa masu sheƙi suka kalle ta, wani kallo kamar na ɗan da yaga uwarsa bayan tsawon kwanaki.

“Ranka ya dade, kai da waye haka?”

Babu dalili, muryarta ta fito kusan a shaƙe.

“Ibrahim, sunansa Ibrahim.”

Cewar Alhaji Ahmad, don sunan da ya laƙaba masa kenan a tun lokacin da akayi cike-ciken takardu a gidan marayun.

“Daga ina yake? Na dauka sanda zamu taso kace baka san kowa a Jimeta ba.”

Maimakon ya bata amsa, sai ya iso har gabanta ya kamo hannunta daya kawai suka nufi cikin gidan, na dama riƙe da yaron, na hagu kuma rike da ita. Wani tubali da ya zamo mafari kenan wajen haddasa wutar tsanar yaron da bata ko gama sanin kammaninsa ba a zuciyarta.

“Ban gane ka yanke shawarar riƙe shi ba Ahmad, wane yare ne wannan?”

Fuskarta a haɗe murtuk ta tambaya a lokacin da ta kasa ko zama tana jiran fitowar mijin nata daga wanka, bayan ya fito ɗin ne kuma ta kasa ta tsare cewar sai yayi mata bayanin ɗan da suka bari a falo yana cin abincin da ko ita bata kai bakinta ba.

Ya juyo ya kalle ta jin sautin ta ya canja akan yadda ya sanshi, yayin da yake goge ruwan fuskarsa.

“Hausar ce yau ke haɗe miki Hafsat? To in baki gane ba sai ince yaren Jimeta ne wannan. Tun daga farko ai kin fahimce ni, to me yasa ba zaki gane karshen ba?”

“Ta yaya kuwa zan gane manufarka Ahmad, cewa fa kayi a riƙe shi kafin mu sami namu, kana nufin har na gaza kenan? Shekara uku kawai amma ka kasa hakuri sai ka kawo ɗan da bamu tabbatar da halaccinsa ba kace in riƙe? Ni na hana kaina haihuwar da na kasa samar maka ƴaƴa ko kuwa…”

“Kinga ya isa…!” Kakkaurar muryarsa ta katse ta cikin iko irin nasa na ƴaƴan sarauta.

“Nace miki ina zarginki da rashin haihuwa ne? Ko kuwa nace miki ƙulafucin ƴaƴa ne yasa na ɗauko wannan yaron? Ina imaninki ya tafi ne Hafsat? Ke baki tsinci tausayi a labarin dana baki ba? Ta yaya zan bari rayuwar yaro kamar wannan ta salwanta alhali ina da hanyar da zan iya karewa?”

Yana rufe baki ta cafe.

“Tausayi? Ina tausayi yake da mazauni anan? Su ƴaƴan da ka baro a gidan marayun baka jin tausayinsu kenan? Ko kuwa ka manta tulin yara marayun dake taruwa duk juma’a a Fada ne wajen sadaka? Naga kafin tahowarmu ma sai da muka je sansanin da yaƙi yaci garin Farɓe, ka manta waɗannan kananan yaran da aka rabawa sutura da kayan abinci ne? Yaran da harda na goye babu uwa balle uba? Me yasa duk su baka dauko ɗaya ko ka tattaro min su kace in riƙe kafin in sami nawa ba? Sai wannan da ban san asalinsa ba?

Haba Ahmad! Mace kamar ni? Zan riƙe yaron da aka tsinto a kwararo? In ya girma ince me? Nawa ne ko na wata da baza ta wuce karuwa ba?”

Maganganunta sunyi zafi kwarai! Amma duk da haka sai ya tattaro dauriya da matsayinsa na miji yayi mata uziri, mace ce ita, mai zuciya a ƙirji, ta taɓa yi masa hakan ne tsawon zamansu? Idan bata nuna kishinta ba ai ko shi ya dasa ayar tambaya akanta, saboda haka ya kamo hannunta duka biyu sannan yayi ƙasa da tasa muryar.

STORY CONTINUES BELOW

“Dan Allah ki fahimci ni Hafsatu, na sani cewa dama zaki ji zafin wannan al’amarin, tabbas na hasaso cewa zaki ji haushinsa har ma ki faɗa mun waɗannan maganganun, sai dai a duk bayan haka kuma na hango cewar zaki fahimce ni, zaki dubi yaron nan da idon rahama, zaki kwatanta irin abinda nake ji a zuciyata game dashi ko don ki cika alkawarin da muka ɗaukarwa juna cewa komai tsanani da halin rayuwa ba zamu bari wani abu ya shiga tsakaninmu ba.

Ki ɗauki kanki a matsayin mahaifiyar yaron nan mana, wata mata da giftwar ƙaddara ta raba ta da abinda ta kawo duniya, yaya zaki ji idan har…”

Hafsatu ta kara tunzura, ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, idanunta suka rufe ruf! da baƙin hayaƙi, bata iya ji da ganin komai sai abinda zuciyarta ta wassafa mata a lokacin, abinda zuciyarta ke biya mata har take koƙarin fara haddacewa saboda haka har Alhaji Ahmad ya kai ƙarshen zancen sa bata fahimci komai ba, sai da taji muryarsa ta daina amsa amo a cikin kanta sannan ta dube shi da idanunta jawur!

“Ka san Allah Ahmad? Ka san ubangijin da ya halicce mu ya halicce duniyar nan? To na rantse da buwayarsa idan na riƙe yaron nan ban haifu a cikin uwata ba! Tun wuri gwara ka san inda zaka kaishi don ba zai raɓe ni ba wallahi balle har abinda zanzo in haifa a gaba.”

Kalaman sunyi mutuƙar shayar da Alhaji Ahmad mamaki, don bai taɓa ganin wannan ɓangaren na matarsa ba, zamansu mai daɗi ne cike da biyayyar da ko me yace tayi, a tunaninsa in ma tayi ƙorafi to zata yin, amma har wannan ɗan ƙaramin abin da a wajensa bai kai ya kawo ba zai sanya ta gaya masa waɗannan maganganun? A tunaninsa komai ra’ayinta zata so duk wani abu daya buɗe baki yace yau yana sonsa ganin irin tsananin biyayyar da take masa.

Saboda haka sai ya saki hannayenta sannan ya miƙe tsaye, ya ɗauki rigarsa dake gefe sannan ya tabbatar mata da cewar ya san Allahn.

“…kuma na san ƙarfin buwayarsa Hafsat, don haka ba zan sa ki shega ta kanki ba, yaro ne baza ki riƙe ba to na fahimta, amma ni a yanzu mutuwa ce kaɗai zata iya yanke min wannan alƙawarin dana ɗauka, don haka kisha zamanki ke da abinda zaki zo ki haifa ɗin. Ni zan riƙe yaron kamar yadda nayi alƙawari don haka kar ki sake ki ƙalubalanci duk wani abu da zanyi akansa daga wannan daren har ƙarshen rayuwarki, in kika yi hakan_- ina tabbatar miki baza ki sake samun matsala daga ni ba insha Allahu.”

Kalaman daya faɗa kenan yana mai ƙoƙarin saka rigarsa a gaban mudubi, wasu kalamai da Hafsatu taji su kamar ɗoruwar ƙarfen da yayi ja a wuta cikin zuciyarta, don sun bar wani tabo da ta yarda cewa har ta koma ga mahallicinta ba zai goge ba.

Kuma wannan daren shi ya zama na farko da suka fara raba makwanci ita da Ahmad, ta kwana ne ita kaɗai a ɗakinta yayin da ya kwanta a nasa ɗakin tare da yaron!

Kuma washegari da sassafe yayi wani abu da duk ƙarfin zuciyarta sai da ta tsorata, sai da tuna cewa da gaske namiji ta aura, namijin da ko a cikin maza ya amsa sunansa, wanda duk ƙarfin ikon mace a zuciyarsa bata isa taja da al’amarinsa ba.

Wata Dattijuwar mata ya shigo da ita gidan mai sunan Atine, kuma ba tare da yayi mata bayanin komai ba yasa aka buɗe musu ɗaki a can boys-quaters ɗin dake bayansu, a ranan aka cika ɗakin nan da duk wani kayan buƙata na amfanin uwa da yaro ƙarami, sannan ya dauki yaron da bai ko barshi a gidan ba tun safe ya danƙawa Atinen da cewar ta zauna ta kular masa dashi, tana kallon komai ta taga kuma har ya shigo gidan daga baya ‘ta tafasa, sauke’ akan al’amarin baice da ita ba.

Don haka a wannan ranar ne shaiɗan ya taka mummunar rawa wajen halittar wata irin ƙiyayya da za’a shafe tsawon zamani guda kafin a samu mai makamanciyarta a ƙirjinsa, kuma mafarin kenan!

Mafarin Komai!

*

Ibrahim Ahmad Madaki.

STORY CONTINUES BELOW

Tsawon watanni hudu da fara wata sabuwar rayuwa, waɗannan kalaman guda biyu sune kaɗai a cikin kwakwalwar ɗan talikin yaron nan, bayan haka babu abinda yake ganewa daga cikin yaren mutanen da suka ɗauke shi sai dai kawai yayi amfani da alamar inkiya kawai ya kintaci maganar da ake masa. Bashi da wani wayo kuma bai san tarin abubuwa ba, bai san ya akayi ya tsinci kansa a wajen nan da aka tsinto shi ba, abinda yake tunawa kawai shine fuskar wani mutumi a lokacin da yake gaya masa wani abu da ba zai iya tunawa ba, a lokacin da ƙafafunsa suka kumbura sannan a lokacin da yake wani irin tari wanda yake fitowa tare da fallatsowar jini…!

Ya san cewa ya san fuskoki da yawa ta mutane a can inda ya taho, amma bai zai iya zayyano sunayensa ba ko matsayinsu a rayuwarsa.

Matar da ake kira Baba Atine ita ke kula da komai nasa, tana kula dashi kamar kaka da jikanta, kuma a hankali yake fahimtar duk harafan da take masa magana dasu sai dai har zuwa wani lokaci bai damu da yayi magana ba don bai san me zaice ba, har asibiti aka kaishi wai don ayi bincike ko da akwai wata matsala a makogwaronsa, amma da aka gano ba komai sai Alhajin ya rabu dashi da fatan cewar zaiyi maganar wata rana.

Tun bai san ma’anar kalmar Kirki ba, ya fahimci  cewa Alhaji Alhmad mallakinta ne don yayi wayo ne kamar yadda kowanne ɗa yake tasowa yaga mahaifinsa, ya kula da dukkan wata ɗawainiyarsa ta duniya, ya bashi dukkan wata kulawa da Uba ke bawa ɗansa, ya kyautata rayuwarsa, ya daraja shi ta kowanne fannin daya bashi cikakken suna na ‘Mutum’ sannan bai juya masa baya ba ko a lokacin da ya samu nasa ƴaƴan.

Ya tashi yana ganin girmansa fiye da kowanne mutum a duniya, ya tashi yana kare daraja da martabarsa da dukkan wata iyawarsa, baya yi masa musu, bai taɓa bijirewa umarninsa ba balle har ya saɓa masa. A kullum yana kallonsa ne kamar mudubi, yana fatan watarana ya tashi ya zama tamkar shi, yana kwaikwayon duk abinda yaga yana yi, hatta tafiya wannan, Ibrahim sai wadda yaga Alhaji Ahmad nayi sannan zaiyi tasa, bai taɓa kallonsa da matsayin komai ba sai na Uba kuma mahaifi.

Amma komai yasha banban a ɓangaren matarsa, wata halitta da tun daga zamanin da baya iya fahimtar komai sai motsin fatar bakinta ya san cewa shine abinda tafi tsana a rayuwarta, yasha azaba da tsinuwarta tun baya fahimtar hakan har yazo ya gane, don kasancewarsa a wajen Baba Atine baiyi mata katanga da komai ba, tana samin damarta da zarar Alhaji Ahmad ya fita zuwa aiki, shi kuma yana samun ƴancinsa ne da zarar lokacin dawowarsa yayi.

Wani abu da sai da aka shafe shekara da shekaru anayi kafin Alhaji Ahmad din ya farga, don a gabansa babu ruwanta da sha’anin yaron balle har yayi tunanin wani abu, tana nuna masa cewar ta dauki maganganunsa na cewar ba zata sami matsala dashi ba in har zata tsame kanta a sha’anin yaron, don haka koda Allah yayi wa Baba Atine rasuwa, sai bai sake neman wata mai kula dashi ba ganin shi kansa Ibrahim ɗin ya fara tasawa kuma a lokacin sun haifi ɗansu na farko ‘Saifudden’, sai yayi zaton ko Hafsatu bata janye ƙudirinta akan Ibrahim ba, ba zata cutar dashi ba tunda a yanzu ta san ciwo darajar haihuwa.

Kuma haka rayuwar ta tafi tsawon shekaru har zuwa haihuwar ɗansu na uku Umarul Faruk, Ibrahim bai tab’a bashi shakkun da zai canja tunaninsa akanta ba.Yana jure dukkan dubunnan wahala da tsinuwarta ba don komai ba sai don darajar miji irin wanda ta samu, miji wanda yake wa kallon Uban da bashi da tamkarsa a duniya. Don haka ne ma duk irin abinda take masa bai hana shi son ƴaƴan ta ba, bai hana shi jansu a jiki yana nuna musu soyayya irin wacce kowanne d’anuwa ke yiwa ƴanuwansa, irin son da ubangiji ke halittawa a tsakanin jini da jini, kafin hakan ya shuɗe daga lokacin da ya fahimci cewa su babu hakan a tasu zuciyar.

Musamman bayan da saki ya shiga tsakanin Alhaji Ahmad da mahaifiyar tasu akansa, wata rana da ya dawo ya tadda shi yana dirzar manya-mayan carpets ɗin gidan a maimakon kasancewarsa a makaranta. A wannan ranar duk wani bayani da kwana-kwanar Hafsatu bai shiga kunnensa ba, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci har ya furta cewar ya sake tan! Wani saki da ko bayan yayi shi baiyi dana sanin ba, don sai da aka kai ruwa rana da ban bakin manya da komai sannan ya yarda ta dawo, tare da nata ban hakurin itama na cewar tayi nadama kuma zata riƙe shi tamkar ‘ɗanta’, asalin sunan kenan! Asalin dalilin da yasa har zuwa yau, mai martaba baya kiransa da kowanne suna a wajenta sai ‘Ɗanki’.

Sai dai daga lokacin da ya kammala secondary ya fito da wani irin sakamako mai kyau sannan komai ya dawo sabo, a lokacin da Alhaji Ahmad ɗin ya ware wasu makudan kuɗi ya tura shi ƙasar waje don yin karatun degree a fannin kasuwanci kamar yadda yake buri.

Alheri ba zai tab’a isar maka ba, kasa a ranka wannan itace nasara ta k’arshe da zaka samu a rayuwarka, wannan rantsuwa ta ce…

Kalamanta a wannan lokacin suna ɗaya daga cikin abubuwan da ba zai taɓa mantawa, wanda kafin dawowarsa ne kuma rayuwa ta sauya a bangare da yawa, don Alhaji Ahmad ya ajiye aikinsa ya karbi sarautar mahaifinsa wanda ya rasu, wani tsohon da bai taba ƙin Ibrahim ɗin ba amma dai ya hana shi amfani da jigon sunan zuri’ar masarautar wato ‘Kamsusi’ don haka ne ma sunansa yake a Ibrahim Ahmad kaɗai, sai bayan rasuwar tsohon nan Madaki ne sannan ya samu laƙabi na uku a sunansa, wani laƙabi daya manne a bakin mutane ya mantar dasu sunansa na Ibrahim ɗin.

Bayan kammala karatun jami’ar tasa har zuwa bigiren Masters ne kuma wani babban al’amarin ya sake faruwa, Mai martaba ya ɗauki dukiyar da yayi shekara da shekaru yana tarawa ya danƙa ta a hannunsa baki ɗaya, da cewar shi ya juya dukiyar, Saifudeen kuma da yake ɗansa na jini ya gaji sarautar gidansu. Wani hukunci da ya sake taso da tsohon tsumin tsanarsa a zuciyar Fulani, don me yasa baza’a hadawa ƴaƴanta duka biyun ba? Me yasa za’a raba abinda yake halalinsu da wani bare?

Idan har kana ganin wannan wata dama ce ta sake bud’e maka to kayi kuskure, Allah ya sani na tsaneka Madaki, ka riga ka san hakan kuma a yanzu ina ganin lokaci ya wuce da kalamaina ma zasu dinga b’oye manufata, kasa a ranka cewa ko zanyi yawo tsirara sai na kwatowa ‘ya’yana hakk’i da matsayinsu daka danne, ratsuwa ta ce Ibrahim!

Rantsuwarta. Rantsuwar da ta sake tada ta tsaye wajen koƙarin ganin bayansa ta hanyoyi mababanta har kuwa zuwa matakin da ake ciki a yanzu.

Madaki mutum ne mai saukin kai, mai daraja mutane, mai son jama’a, mai kyauta, mai alkunya da kara, mai sanin halacci da kuma ya kamata. Zuciyarsa mai tsafta ce, bashi da mugunta balle cuta, yana da alƙawari da kuma tsayawa akan gaskiya, ya rasa wata rahama da mafi yawan mutane a duniya ke da ita ta sanin iyaye da kulawarsu, musamman ma Uwa! Wadda ke zama ginshiƙin farin ciki na kowanne ɗan adam, amma bai taba bari hakan ya shafi ɗabi’unsa ba.

Wannan shi ya kawo mu har ga matakin da ake ciki a yanzu!1

***~~~~

Komai ya faru ne a lokacin da ya saki hannun bindigar, a lokacin da harsashin ciki ya fito cikin tsananin gudu zuwa inda aka aike shi…. A lokacin da wannan matashin ya shigo cikin hoton da yake hangowa ta cikin ramin bindigar alamun yazo ne ya buɗe ƙofar motar da yarinyar ta kasa buɗewa…!+

*

“Kin kasa buɗewa ne?” Madaki ya tambaya a lokacin da ya bude ƙofar tasa motar ya zira ƙafa ɗaya ciki.

Jidda ta sake jan ƙofar ba tare da ta amsa ba da hannunta ɗaya, ɗayan kuma riƙe da robar yughurt dinta, sai kawai ya mayar da tasa ya rufe shima sannan ya zagayo wajenta, ya tsaya a daidai bayanta sannan muryarsa ta fito a hankali daidai saitin kunnenta.

“Matsa, let me.”

Al’amarin ya faru ne cikin abinda bai fi wucewar sakan ɗaya ba, daidai lokacin da Jidda ta zare hannunta daga handle ɗin ƙofar tana shirin matsawa, daidai sanda take ƙoƙarin motsa ƙafafunta su bar wajen… sai kawai ji tayi Madakin dake tsaye a bayanta ya taho da wani irin ƙarfi ya bugu da jikinta, ta haɗe gabaɗaya da murfin ƙofar yayin da kanta ya bugu matsanancin sauri da gilashin ƙofar cikin wani irin ƙarfin da yasa har sai da motar ta girgiza, kuma hatta robar Yogurt ɗin hannunta data fadi sai da murfinta ya fice saboda yadda ta daki ƙasa da ƙarfi, ragowar na ciki ya fallatse a iska da kuma rabi na jikinsu.

A mutuƙar tsorace ta juyo da fuskarta ta kalle shi hannayenta dafe da motar yayin da shima yake ƙoƙarin tsayawa akan kafafunsa, taga sanda ya dafe saman kafaɗarsa ta hagu da sanda yake ƙoƙarin juyawa bayansu yana kallon can saman asibitin… Sai dai tazarar dake tsakanin yunƙurinta na buɗe baki tayi magana da sanda ya sake dawowa da baya ya bugu da jikin motar bai fi ƙiftawar ido da budewarsa ba.2

Kuma kafin ta gai ga furta wata maganar idonta ya hango mata tashin hankalin da ya juya ƙwaƙwalwarta ya kasa fahimtar da ita gaskiya da zahirin abinda ta gani ɗin… Jini! Wani irin jini mai kauri na tsatstsafowa daga tsakanin yatsunsa inda ya dafe kafaɗar tasa ta baya…3

Innalillahi wa’inna ilahir raji’un…. Me ya faru?

“Wani ne ya jefe ka? Da dutse ko da me?… A baya ne? Ta yaya? Banji ƙara ba…”

Muryarta ta fito yayin da take kokarin mantawa da nata buguwar tana ƙoƙarin kai hannunta wajen, sai dai da saurinsa Madaki yasa ɗaya hannunsa da bai danne wajen ba ya hana ta.

“Kar ki taɓa, ina tunanin harbi ne.” Muryarsa ta fito da wani irin amo mai tsitstsinkewa da bata taɓa ji ba.

“Harbi? Harbi ta ina? Wane irin harbi? Da danƙo?”1

Tsakani da Allah tayi tambayar muryarta a rikice don nauyin ƙwaƙwalwarta ko kaɗan bai kai yayi tunanin wani harbin bindiga ba, to ina ma ta santa banda a suna? Ko a can gida ba kallon fim ɗin turawa take ba balle har tunanin bindigar ya zauna a ƙwaƙwalwarta…

**

“You missed the target?”

(Baka same ta ba?)

Cewar gabjejen ƙaton mutumin nan cikin tsananin mamaki da fushi daga can saman ginin asibitin, yayin da idanunsa ke kare da binoculars (madubin hange) yana kallo can ƙasa.

“I’ve already set the fire when he just came into the view… Tell me how was I supposed to control that?”

(Na riga na gama sakin harsashin kawai sai ganinsa nayi ya shigo wajen, ka gaya min ta yadda zan tsaida komai?

Muryar mai bindigar ta fito cikin nata karaji itama yana kallon ɗayan. Na tsayen ya dafe kansa cike da takaici yana hasaso muryar ogansu a lokacin da yake jaddada masa cewar kar su sake wani abu ya sami matashin, yarinyar kaɗai itace target ɗinsu, ya sake kara binoculars ɗinsa yana hango su daga can ƙasan.

STORY CONTINUES BELOW

Yarinyar ta rikice sai ƙoƙarin tara hannunta take a kafadar matashin inda jini ke zuba, yana ganin yadda yake ƙoƙarin hanata amma tana fizge hannunta tana taya shi dafe wajen har daga baya…

“You know what? Shoot again, shoot the girl…”

(Ka san me? Sake wani harbin, Harbi yarinyar itama..)

Ya faɗa ba tare da ya sauke binoculars ɗin daga idanunsa ba.

“What? Is that on the list? ‘Cus you pay for only one bullet?”

(Hakan na cikin tsarin? Don kuɗin harsashi ɗaya kawai aka biya ni?)

Na tsayen ya ɗauke madubin hangen daga fuskarsa, sannan ya juyo ya kalle shi sosai sannan yayi maganar dalla-dalla.

“I. say. shoot. the. girl!”

(Nace ka harbe ta!)

Mai bindigar ya gyada kansa kawai sannan ya koma ya ɗora idonsa cikin kwarmin bindigar.

Yarinyar ta kasa tsayawa waje daya, juye-juye kawai take alamun tana neman taimako tunda sun baro harabar asibitin wajen mutane, parking space ne kawai inda sai mutum zai dauki motarsa zai ƙaraso… Duk da haka yayi ƙoƙarin gama saita ɗan hasken bindigar tasa ta bayanta kafin mummunar rashin sa’ar ta faru, kamar matashin nan yaga hakan, sai kawai gani yayi yaja hannunta sunyi ƙasa, kuma wata ɗindimemiyar Rav4 ta kange shi daga ganinsu…!

*

“Kar ki tashi, kar ki sake tashi suna nan basu tafi ba…”

Muryar Madaki ta fito a tsakiyar numfashi lokacin da ya damƙe hannayen Jidda dake ƙoƙarin sake tashi.

“Su waye? Wani zanje in nemo, ba zan iya ɗaukan ka ba, ka manta a asibiti muke? Jini ne fa yake zuba daga jikinka… Innalillahi wa’inna ilahir raji’un..”

“Nace ki… ki… ɗauke ni ne?” Ya tambaya yana furzar da numfashi daga bakinsa.

“Nace kar ki tashi!” Ya sake faɗa cikin tsawar da muryarsa zata iya dauka ganin da gaske ƙoƙarin fizge hannun nata take zata tashi. A lokacin jikinsa gabaɗaya ya fara rawa don jinin da yake zubarwa ya fara yawa, ta baya ne amma har ta gaba tsatstsafowa yake don kusan rabin gaban rigar tasa ya jiƙe da jinin yayin da yake sake tunkuɗowa ta tsakanin yatsunsa dake dafe da wajen.

Jidda ta rikice iya rikicewar da bata taba yi ba a rayuwarta, jikinta yafi nasa rawa sannan in banda karar bugun zuciyarta ba abinda take ji yana dokawa a ƙirjinta, so take kawai ta ga wani yazo, an kawo agaji, mutane sun taru an ɗauke shi zuwa cikin asibitin, amma yace kar ta ta tashi… Kar ta tashi… Ga jininsa ya na ƙoƙarin ƙarewa a gabanta… Shi yake jingine da motar amma duk da haka kansa ya lanƙwashe ta gefe alamun babu wani ƙarfi a jikinsa sai wanda yasa ya damƙe hannayenta…

Bata san lokacin da wani irin ƙarfin yazo mata ba, ta fizge hannayen nata a lokaci guda sannan ta shiga ƙoƙarin zaro bakin ɗankwalin data daure kanta dashi wanda shima mayafin wata rigar ne, ta ɗaura daya, ta yafa ɗaya…

“Me zaki yi?”

Muryarsa ta sake tambaya babu amo alamun rauninsa na kara tasiri, kuka take sosai tun daga ƙasan zuciyarta tana kallonsa, idanunsa sun fara ja kamar suma jinin na ƙoƙarin cika su ne.

“Babu inda zaki je…” Ya sake faɗa da muryar dake nuna cewa ko da zata tashin ma, a yanzu ba zai iya riƙe ta ba.

“Babu inda zani…” Ta faɗa itama tana kukan.

” … Zan ɗaure maka wajen ne kar jininka ya ƙare…”

Ta fada tana ƙoƙarin janye hannunsa daga yadda ya fafe shi kuma da yake ƙarfinsa ya riga ya tafi dama, tana taɓa hannun ya faɗi ya koma gefe yayin da hakan yasa karuwar tunkudowar jinin ta karu, fitowa yake kamar ana turo shi har da wani guda-guda alamun ko meye ya fasa wajen ba ƙarami bane…

STORY CONTINUES BELOW

“Ibrahim..! Ka kalle ni… Ka kalle ni Ibrahim..”

A lokaci guda muryarta ta fito kusan da ƙarfi ganin idanunsa sun fara lumshewa… Sai ta saki ƙullin da take yi ta hau tattaba fuskarsa da hannayenta dake  ɓace duk da jinin suna karkarwa, so take ta buɗe idanun nasa…

“Ibrahim, Madaki… Ka kalle ni kar ka rufe idonka, yanzu wani zai zo… Yanzu zanje in kira wani…”

“Kar ki tashi…”

Kwata-kwata sautin muryarsa bai fito ba, motsin fatar bakinsa kawai ta kalla ta gane me yace, sai ta hau gyaɗa kanta kamar ƙaramar yarinya…

“Ba zan tashi ba, babu inda zanje… Ka bude idonka ka kalle ni, yanzu wani zai zo yanzun nan… Zamu koma ciki asibitin… Dan Allah ka buɗe idonka kar ka rufe su, kar ka mutu, kana jina… Ibrahim….”

A tsugunne a gefensa take amma kusan gabaɗaya tana kansa ne yayin da fuskarta tayi dab da tasa, ta rike ta cikin hannayenta sai faman jujjuyata take tana ƙoƙarin bude idanunsa da yatsunta… Idonta ya sake kaiwa kan kafadar tasa inda bata gama ƙullewa ba jini ke cigaba da fita yana jiƙa su gabaɗaya… Sai ta saki fuskarsa da sauri ta koma ɗaurewar da hannayenta dake karkarwa suma babu wani ƙarfi a jikinsu…

Ta sake juyowa kan fuskarsa, kansa lilo kawai yake yayin da idanun nasa ke cigaba da rufewa..

“… Ibrahim, Ibrahim ka kalle ni, ina kusa da kai, Ba abinda zai same ka… Ka buɗe idonka, ga mutane nan suna tahowa, ka ji su? Kaji motsin su? Gasu nan… Yanzu zamu shiga ciki, zaka ji sauƙi kaji? Kana ji na? Ka buɗe idonka, ciwon zai daina.. ka buɗe idanunka don Allah…”

A yanzu kusan marin fuskarsa kawai take yi kotawanne bagare tana ƙoƙarin bude idanunsa da suka rufe ruf! Yayin da kukanta ya karu.

“… Ba zan tashi ba, su zasu zo… Gasu nan suna tahowa, ka buɗe idonka zasu fi gane ka Ibrahim, dan Allah, ka kalle ni, ba zan bari wani abu ya same ka ba, Ina kusa da kai, kana gani na? Ibrahim… Ibrahim… Ibrahim… Ibrahim…”

A daidai wannan lokacin wasu magidanta biyu suka karyo kan kwanar parking space ɗin inda su Jiddan suke, jin muryar mace na ta ambaton suna cikin tashin hankali yasa dukkaninsu suka taho wajen.

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un… Me ya faru?”

“Me ya same shi?”

Muryoyinsu suka sa Jidda ta ɗago da kanta ta kalle su, domin har suka karaso girgiza fuskar Madaki kawai take tana kiran sunansa. A lokaci guda hawaye ta  ya sake tunƙuɗowa cikin wani irin kuka…

“Harbinsa akayi, yace harbinsa akayi dan Allah ku taimaka mana.”

“Harbi??”

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un.”

Ɗaya daga cikinsu yayi salatin kafin dukanninsu su zube a gabansa yayin da ita ta miƙe, sai dai ganin baya ko motsi yasa basu ɓata wani lokaci ba suka shiga kiciniyar ɗaukarsa, wanda ya ɗan fi ƙwari a cikinsu shi kusan ya cicciɓe shi yayin da ɗayan ya riƙe ƙafafunsa suka juya zuwa hanyar asibitin nan cikin sauri.

Kamar wata sabuwar mahaukaciya haka Jidda ke jin kanta, gaban rigarta gabaɗaya ya ɓaci da jini yayin da kanta ba ɗankwali sai mayafin kawai dake zamewa, da sauri ta tsugunna ta ɗebi takalmansa da suka zube da kuma muƙullin motarsa da ya faɗi a ƙasa sannan ta ruga da gudu itama tabi bayansu, bata ko lura da cewar ta bar nata takalmin a wajen ba balle matar ɗaya mutumin dake tsaye tana kallon komai cikin tashin hankali.

Tun a hanya mutane ke ta binsu da kallo ana matsawa ganin yadda har a lokacin jini ke zuba daga jikinsa yana bin ƙasa, a cikin asibitin kuwa tun kafin su karaso wasu Nurses biyu dake magana a gefe suka hango su, ai kuwa da sauri suka taho kansu suna nuna musu hanyar A&E, yayin da taga ɗaya daga cikin mutanen nan yanuna musu ID Card ɗinsa, Jidda na binsu a baya har a lokacin tana kuka, nata ƙafafun da babu ko takalmi na taka duk inda jininsa ya ɗiga akan farin tiles din dake wajen, da ita aka shiga har cikin A&E ɗin aka kwantar dashi a wani gado, sannan daya Nurse ɗin ta juya da sauri don zuwa kiran likita, yayin da sauran Nurses ɗin dake cikin ɗakin suka juyo gabaɗaya suka yo kansa.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma kafin Jidda ta gama fatan cewa su maza don taga fuskarsa, Nurse din nan ta dawo tare da wani likita don haka aka tattaro ta ita da mutanen da suka kawo shi akace su fito waje. Suna fitowa wanda ya nuna ID Card ɗin nan nasa ya zaro wayarsa ya shiga kira yana wani bayani da ba jinsa Jidda ke yi ba.

“Kiyi hakuri kinji baiwar Allah, zai sami sauƙi insha Allahu.”

Cewar ɗaya mutumin da kusan shi ya dauko shi.

“Ai kowanne irin ciwo ne bai taɓa zuciyarsa ba, a kafaɗa ya tsaya insha Allahu komai zai zo da sauƙi.” Ycigaba da faɗa sai kuma ya kara da…

“Ki kira gida, ƴanuwanki ko nasa ki faɗa musu halin da ake ciki.”

Ɗayan ya ƙaraso a daidai wannan lokacin.

“Kar ki damu kinji Madam, komai zai zo da sauƙi, harbin a kafaɗarsa kawai ya tsaya don haka zasu yi handling situation ɗin, suma waɗanda suka yi abin ina fatan za’a kama su don na kira patrol na ƴan sanda, indai suna wajen nan baza su fita ba.”

Daga yanayin yadda hausar sa ke fita zaka san cewa ba bahaushe bane balle musulmi, sai dai da alama yana da dan muƙami mai girma a harkar tsaron duk da ba kayan aiki ne a jikinsa ba.

Jidda kuka kawai take tana ɗaga kanta alamun ta fahimci zancen da bata fahimta ba ɗin, kuma ganin yadda ta rikice sai basu tafi ba suka tsaya suna ƙara bata hakuri da tabbatar mata cewar zai warke, ɗayan ma yayi-yayi ta faɗo namba a kira wani da zai zo ganin babu wayar a hannunta amma banda kuka ba abinda take yi, a lokacin matar ɗaya mutumin da yake ƙabila ta ƙaraso itama, babba ce sosai kamar mijin nata, saboda haka ta zaunar da ita a wasu kujeru dake gefe tana bata baki cikin tata hausar da bata fita itama.

Sai kusan bayan isha sannan Nurse ɗaya ta fito riƙe da tarkacen wasu kaya a cikin wani silver faranti irin na aiki, a lokacin ɗan sandan nan ya fita waje don bada bayani ga mutanensa, sai matarsa kawai da ɗaya mutumin a wajen, Jidda na ganin Nurse ɗin ta miƙe tsaye da sauri koina a jikinta na faman rawa kuma har a lokacin hannunta riƙe fa takalminsa da kuma muƙullin motarsa. Nurse ɗin ta ƙaraso ta miƙawa mutumin kayan hannunta sannan tace.

“Ga kayan dake jikinsa, an shiga dashi operation ne za’a cire bullet ɗin, zaku biya kuɗi a can wajen lab na farko, aikin yana bukatar sauri ne shi yasa har aka fara ba’a tuntuɓe ku ba.”

“Babu komai, babu komai Allah yasa a dace.”

Cewar mutumin yana mai haɗe kayan cikin hannunsa.

Ya juyo wajen Jidda sannan ya miƙo mata su duka, wayoyi ne guda biyu sai wallet dake dauke da kudi fal, da kuma wasu ƴan I.D cards da basu shiga cikin wallet din ba.

“Ki buɗe wayar tasa a kira wani yazo don su san halin da ake ciki.”

Har a lokacin hawaye bai bar sukalowa akan fuskarta ba ta gyaɗa kanta kawai alamun ta gane, duka wayoyin suma sun ɓaci da jini, ɗaya ma ta mutu alamun jinin ya shiga jikinta sosai Iphone ɗin ce kawai a kunne, yatsunta na rawa tasa hannun ta bude ta, cikin wata sa’a sai babu password a jiki, hannayenta suka cigaba da karkarwa akan wayar ba tare da ta san nambar wa zata nema ba. Babu wanda ta taɓa sani nasa sai Mai martaba, to nambarsa za’a kira yanzu a gaya masa cewa an harbe shi? Sai tayi saurin gigiza kanta, ganin hakan ba mai yiwuwa bane ta hau laluben wata hanyar.

A lokaci guda kuwa sai ta tuno da wani abu da bata taɓa tunanin ta riƙe ba, ta tuno da wata magana da ya fada a ranar da yake waya a mota bayan ya dauko ta daga Kiyari…

Kar ka damu Mubarak, babu abinda zai gagare ni insha Allah.

Idan har zai iya kiran wani Mubarak ya gaya masa halin da yake ciki a wannan lokacin to tabbas yanzu ma kuwa ba zai damu ba don an gaya masa abinda ya faru yanzu, saboda haka ba shiri yatsanta ya danna ɓangaren call log, ilai kuwa sai ga nambar Mubarak ɗin a sama ɓaro-baro alamun shine mutum na karshe da yayi waya dashi a wannan wayar, don haka kai tsaye ta danna nambar kiran ya shiga, sai kuma ta miƙawa mutumin alamar cewa shi yayi masa magana don har ga Allah ita bata san me zata ce ba.

STORY CONTINUES BELOW

Yazo an harbi abokinsa ko kuma yazo mijinta zai mutu?

***

“Daddy idan na girma zan iya girki kamar mommy?”

Hanan ta tambaya a lokacin da suka baje akan carpet suna cin abincin dare. Mubarak ya kai lomar abincin bakinsa kafin ya amsa mata.

“Idan kika girma Hanan, sai kin fi Mommy ma iya girki…”

Ya faɗa daidai lokacin da Khadijan ta ƙaraso da wani bowl na sauce a hannunta, ta zubawa Aliyu dake gefe yana kallon cartoon din ‘How To Train Your Dragon 3’ a Tv, sannan ta matso kan Hanan lokacin da take kallon Daddyn nata da tsantsar farin ciki tana tambayar…

“Da gaske kake daddy? Da gaske da gaske?”

Mubarak ya sake gyaɗa kansa yana tauna.

“Ba girkin mommy kaɗai ba, idan kika girma sai kinfi kowa iya komai Babyna, sai kin zama kamar princess dinki ta ‘Silver Castle’ da mutane ke sonta.”

Bakin Hanan ya washe lokacin da Khadija ke zuba wa Mubarak tasa sauce ɗin akan abincinsa, dariya kawai take tana kallonsu cike da farin ciki irin wanda zuciyar kowacce mace ke yi in taga iyalinta a farin ciki, har zata wuce ta koma kitchen sai Mubarak yayi saurin kamo hannunta ɗaya.

“Ina Salwa?”

“Tana ɗaki tunda kuka dawo.”

“Lafiya?”

“Tace dai kanta ciwo yake shi yasa na kyaleta.”

Sai ya gyaɗa kansa a hankali sannan ya saki hannun nata, sai dai kafin tunaninsa ya janye zuwa wani abin, wayarsa dake gefe tayi ƙara, yana dubawa yaga sunan ‘Mdee’ ɓaro-ɓaro akai sai kawai yayi murmushi sannan ya haɗiye sauran abinda ke bakinsa.

“Ka san me Man? Muyi ciniki kawai in buɗe maka class na yadda abubuwa zasu dinga tafiya..”

Ya faɗa tun kafin ma yaji muryar na cikin wayar.

“Uhm, yi hakuri ba shine akan layin ba…”

Muryar mutumin data fito ta sanya Mubarak sakin kwanon abincinsa a take ya miƙe tsaye, don ya sani cewa ba ƙaramin abu ne a duniyar nan zai raba Madaki da wannan layin nasa ba.

Khadija dake shirin komawa kitchen din taja ta tsaya idanunta na kallonsa da ruɗanin neman ƙarin bayani, don ta sani cewa ba ƙaramin abu ne zai sa ya zubar mata da abinci ba. Aliyu ma ya rage volume ɗin kallonsa ya juyo.

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un…. Innalillahi wa’inna ilahir raji’un.”

Abinda Mubarak ke fada kenan kawai a lokacin da ya shiga laluben muƙullin motarsa a kujerar dake bayansa.

“Wane asibitin ne?” Muryarsa ta tambaya cikin tsananin ruɗani.

“Daddy me ya faru? Waye ba lafiya?” Khadija ta tambaya a lokaci guda.

Ya juyo ya kalle su, su duka ukun sun zuba masa ido sunyi tsuru-tsuru, idan yace ba zai gaya musu ba ma zai ƙara sanya taraddadi ne a zuciyarsa, don haka a sai kawai ya girgiza kansa sannan a hankali yace.

“Madaki ne bashi da lafiya, amma da sauƙi, zanje in duba shi yanzu zan dawo.”

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un… To Daddy muje tare mana muma mu duba shin.”

Ya sake girgiza kansa.

“Ku zauna, zan fara zuwa, yanzu zan dawo.”

Yana faɗin haka yayi waje da sauri ya faɗa motarsa. Ya kunna ta a lokacin da maigadin gidansa ya fito da sauri cike da mamaki kafin ya shiga ƙoƙarin buɗe masa gate ɗin, da wani irin sauri Mubarak ya fitar da motar ya hau kan titi yayin da yake ƙoƙarin tattaro dukkan nutsuwa a ransa, bakinsa kuma nata maimaita kalmar Innalillahi wainna ilaihir raji’un har a lokacin…

STORY CONTINUES BELOW

Waye zai harbi Madaki a wannan daren? Laifin me yayi? Ta yaya ma aka san inda yake? Waɗannan tambayoyin su ke yawo akansa lokacin da yake ƙoƙarin lalubar titunan da ba zai haɗu da traffic ba… A lokaci guda kuma sai wani tunanin ya ɗarsu a ransa, kar dai ta sanadiyyar yarinyar nan haka ta faru? Don itace a tare dashi kuma babu wanda ya san taƙaimaimai location ɗinsa sai ita, kar dai zargin da Madaki yake akanta tun farko gaskiya ne…? In ba haka ba me yasa duk tsawon rayuwarsa ba a taba samun abu makamancin haka ya same shi ba sai yanzu data shigo ciki??

Hasashen hakan ya cigaba da yawo a kansa yana haskawa ta cikin idanunsa da wani irin tsantsar ɓacin rai mai cike da ruɗani, a lokacin ne kuma ya karyo kwanar asibitin ta cikin wani layi, fitilolin ginin asibitin dake ci tamkar rana suka haska tar! a idanunsa.

***

KIYARI.

A cikin falon Fulani, a tsakiyar kasaitattun kujerunta, Jakadiyar soro ce tsugunne tana lissafo wani bayani dake rubuce a takarda, yayin da Fulanin ke kame kan daya daga cikin kujerun mai zaman mutum uku, kwata-kwata idonta baya kan Jakadiyar balle har ta fahimci dukkan abinda take cewa.

“… Su waɗanda zasu yi abincin an basu odar yin komai na faranti ɗari, sannan katan ɗin lemo da ruwa suma guda ɗari akace za’a kawo…”

A lokacin kalmar ɗari ta shiga kunnen Fulani da idonta ke manne da rantsatstsun labulayen falon, sai ta juyo ta kalle ta.

“Ɗari?” Ta tambaya.

“Tun farko ban shaida muku cewa ba taro zanyi ba, to don me za’ayi odar komai ɗari? Wa zan bawa?”

Jakadiyar tayi diri-diri da idanunta sannan ta shiga ƙoƙarin canja rubutun tana faɗin

“Afuwa ranki ya dade, na sha’afa ne, Afuwa dai garkuwar al’umma.”

“Nawa zaki mayar da kike koƙarin canjawa? Kinji nace wani abu ne?”

Muryar Fulanin ta sake fitowa cikin faɗa tana kallon hannun jakadiyar dake ƙoƙarin rubutu, jin haka yasa tayi saurin tsayawa sannan ta ƙara sunkuyar da kanta tana jiran umarni.

Ran Fulani ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, zuciyarta ta sake matsewa, har yaushe rabonta da fuskantar irin wannan shirmen, da ace komai bai faru tsakaninta da Jakadiya Babba ba wa zata ɗora kan wannan harkar in ba ita ba? Shirye-shiryen bikin nadin Saifudeen a matsayin Ciroma suke, amma ita gani take kamar shirin wani al’amarin daban ake, don zuciyarta kwata-kwata ta kasa kwanciya da komai, ta kasa samun nutsuwa a ranta shi yasa ma ta yanke shawarar cewa ba wani taro zata yi ba.

Sannan kuma daɗin tashin hankalinta shine rashin dawowar Jakadiyar Babbar har yanzu da gari ya rufe, ta san cewa dare zai iya yi musu a hanya in sun fito gari su sami wajen su kwana zuwa gobe amma zuciyarta ta kasa nutsuwa da hakan ma, gani take aƙalla in hakan ne kamata yayi ɗaya daga cikinsu ita da Sanin ya kira ya gaya mata abinda ake ciki amma babu wani bayani har yanzu, ta kira wayoyinsu yafi sau shurin masaki kowanne baya shiga, to ta yaya kuwa hankalinta zai kwanta?

Ta cigaba da kallon Jakadiyar dake tsugunne tana jiran umarni kafin ta ja tsaki a hankali sannan tace.

“Ki maida adadin hamsin, kuma kar a kara min komai daga hakan.”

“An gama ranki ya daɗe, an gama.”  Cewar Jakadiyan soron tana mai rufe littafinta sanin cewa an sallame ta.

Bayan fitar ta ne Fulani ta miƙe tayi hanyar Turakarta da niyyar kiran Hajiya Bilki, don bata san me ya dace tayi ba bayan hakan, dole ta ajiye duk wani girman kai a yanzu ta lallaɓa ta sami gsashshen bayani game da asirin nan, tana tsoron ƙurewar lokaci kuma tana tsoron bacin rana.

A Falo na uku ta tadda Safina sun fito ita da ƙawarta Juwaira zasu fita, Juwairan ta durkusa har kasa ta gaishe ta yayin da Safinan ke amsa waya, dukkaninsu sunci uwar kwalliya sai tashin ƙamshi suke.

“Ina zuwa haka?” Muryarta ta tambaya a shake tana ƙara kallonsu.

Safina ta kashe wayar da take yi.

“Mama bikin Sarah da na gaya miki last week, yau ne dinner.”

Fulani ta jinjina kanta.

“Waye ya muku wannan uwar kwalliyar kuma?”

“Mai kwalliya ce, ɗazun nan ta fita, nasa an maida ita.”

A daidai lokacin wayar Juwairan tayi kara itama, don haka tayi gaba tana faɗin.

“Mama mun tafi sai anjima.”

“Ke Safina koma ciki, ba inda zaki.” Cewar Fulanin.

Safina ta haɗe ranta a lokaci guda cikin alamun rashin fahimta.

“Kamar yaya? Mama ban gane ba, bikin ne ba zani ba?”

“Eh..” Fulani ta tabbatar mata.

“… Saboda banga lokacin da aka tafi wata dinner a yanzu har aka dawo ba.”

“Mama ni fa ban gane ba? Kin taɓa hana ni zuwa biki ne? Ta yaya za’ace duk shirin da nayi ba zani ba?”

“Ni ba uwarki bace, har akwai abinda zance miki ne ki kalubalance ni?”

Har Safina ta buɗe baki zata yi magana wayarta ta sake ƙara alamun kira, ganin haka yasa Fulani ya shige hanyar ɗakinta ta barta nan a tsaye wayar na motsi a hannunta yayin da fuskarta ke a haɗe, don a sanin da ta yiwa mahaifiyar tata, duk sanda take cikin hali irin wannan to kar ka sake ka kalubalance ta zai fi komai sauƙi, amma me yasa ran nata bai tashi ɓaci ba sai a yau data shirya fita ta musamman zuwa wani party da Ahmad ya gaiyace su? Me yasa sai a yau data gama tanadin komai sannan zata zo ta rushe mata? Sai da kiran yaje can ƙarshe yana dab da tsinkewa sannan ta tsaida zuciyarta waje ɗaya.

“Hayatim muna hanya.”

Abinda ta faɗa a ciki kenan kawai sannan ta kashe, ta riga ta tsaida zuciyarta kuma baza ta fasa ƙudirinta ba, don wani abu can ya ɓata mata rai ita baza ta ɗauki alhakin hakan ba, ba zata fasa niyyarta ba, ta juya tayi hanyar fita.

Fulani ta isa cikin turakarta daidai lokacin da kiran da take dannawa a wayarta ya shiga.

“Salamu Alaikum..” muryar Hajiya Bilkin ta ratso cikin speaker wayar tar da ita.

Tun bayan ranar da suka yi waya ta ƙarshe har ta kashe mata wayar, babu wanda ya sake neman ɗanuwansa.

“Ki gaya min an sami aikin nan Hafsatu, kice kin gano inda yake komai ya dawo hannunki.”

Hajiya Bilkin dake nuna cewar ta manta da saɓaninsu ta bata ƙarfin gwiwar iya yin magana.

“Wallahi komai yana nan a yadda kika sanshi Bilki, daga ni har Jakadiyar munyi iya ƙoƙarin mu wajen neman jakar nan ba tare da an  fahimci komai ba amma mun rasa ta, a yanzu dai halin da ake ciki na tura Jakadiyar wajen wani tsohon malami na don ya duba mana mu sami sauƙin gano ta.”

Hajiya Bilki tayi shiru kamar mai nazari kafin ta gyaɗa kanta.

“To kinyi kyan kai, amma fatana shine Allah yasa dai a ganta kafin komai ya lalace, don wallahi ina tsoron sharrin malamin nan, don hatsabibin gaske ne baya taba aikin da bai ci ba, kuma kin san dai yanayin yadda harkar nan take, in har sunyi aikin nan da cewar dole sai yaci wani ba zai tafi a banza ba to kuwa in har aka sami matsala kanki komai zai dawo tunda da sunanki aka tsuma aikin.”

Gaban Fulani ya fadi, zuciyarta ta dungura ta sake dungurawa sannan ta tafi gaɓar wani rami mai zurfi. Da kyar ta iya tattaro karfinta ta hadiye yawu a cikin busashshen maƙogwaronta sannan tace.

“Abinda na kira ki tabbatar min kenan dama, amma kar ki damu Bilki, zan yi iya ƙoƙarina gani komai bai lalace ba, babu abinda zai faru ina tabbatar miki, Hafsat bata karaya.”

“Ina miki fatan hakan, don ni kaina har cikin zuciyata ba zan so wani abu ya same ki ba.”

Da haka suka yi sallama, sai dai abinda daga Fulani har Hajiya Bilkin basu sani ba shine komai zai fara ne daga lokacin da agogon ɗakinta ya kaɗa ƙarar cikar ƙarfe tara na dare.

A yanzu haka, tara saura minti bakwai!Tara saura minti biyu!+

Fulani ta jefar da wayar hannunta kan gadon da take zaune cikin takaici, ƴan mintuna tsakaninta da gama waya da Hajiya Bilki amma ta kira wayar Jakadiya kusan sau goma kenan har yanzu labarin dai bai sauya ba, kiran baya shiga, kamar yadda kai baya shiga ramin tulu.

Da haƙoranta na sama ta tamke lebbenta na kasa tana cigaba da gyaɗa kai cikin ƙwafa, biyawa kawai take a ranta cewa ko bayan wannan hargitsin ya ƙare Jakadiya Babba sai ta biya bashin wannan zulumi da ɓacin ran da ta saka ta, ita ce fa! Hafsatu. Wannan Hafsatun dake take jama’a da ikonta tamkar yadda takalmi ke murƙushe kwayar gyaɗa a dandaryar ƙasa.1

kamar ta kwanta ta ɗan runtsa tunda yau ba itace da turakar Mai martaba ba, sai kuma ta yanke shawarar fara yin wanka tukunna, wataƙila hucin da take ji a ranta ma ya tafi da saukar ruwan sanyin da take marari, saboda haka ta miƙe ta isa ga ƙofar makeken bandakinta na alfarma dake manne da da ɗakin.

A cikin banɗakin taji bata son sakin shower akanta balle shiga kwarmin wankan na bathtub, saboda haka ta jawo wani ƙaton bokiti dake gefe ta shiga tara ruwan zafi dana sanyi daga famfo yayin da ta koma ta buɗe wata drawer a gefe ta ɗauko wani ƙaton towel tana shirin naɗe jikinta dashi.

A daidai wannan lokacin ne daga can cikin ɗakinta, agogo ya karaɗe da sautin kiɗan algaita, kiɗan dake shaida cikar ƙarfe tara daidai na dare! Kuma a daidai lokacin ne ba tare Fulani ta sani ba wasu abubuwa suka juya a cikin ƙwaƙwalwarta, suka canja mazauninsu daga daidai zuwa akasinsa. Ta dai ji kanta ya sara kaɗan sai dai kafin ta fahimci komai ta tsinkayi ƙarar bugun kofar ɗakin daga can waje, wani bugu da yazama sila kuma masomin faruwar wata ƙaddara da ƙoƙari da taimakawarta ya samar da ita, don tabbas ne wasu ƙaɗororin, bawa nr ke zana su da hannunsa cikin allon rayuwarsa!1

Bugun ƙofar da ɗan ƙarfi yake don har sai da bugun zuciyarta ya daya a lokaci guda tare da mamakin wanda zai ƙaraso mata har ciki haka kuma ya tsaya buga ƙofar tunda ta san da Safina ce ba lallai ne ta buga ɗin ba, sai kawai ta fasa cire kayan sannan ta juya ta kashe ruwan da tara ta fita.

Kanta babu ko ɗankwali sai manya-manyan kalbar da ta kitse gashinta dashi saboda rashin lokaci ta ƙarasa ta bude ƙofar, kuma a take zuciyarta ta sake ɗaukewa da wani guntun taraddadi.

Wata fuska mai cike da haiba da kamala ta baƙunci idanunta, ta ninka taraddadin ta ya tashi daga wani abu guntu sannan haka kurum kuma jikinta yayi sanyi. Mai martaba a turakarta? Da wannan daren? Me ya kawo shi?? Yaushe rabon da ya tako ƙafarsa zuwa cikin sashenta?… Tun a ranar da yazo ya sanar da ita zancen maneman auren Aisha, zuciyata ta bata amsa kai tsaye shima kuma yazo ne ba da daddare ba, ta juya ta kalli agogon dake bayanta… karfe tara daidai, ai bai daɗe da shigowa cikin gida ba ma, to me zai sa ya nemeta a wannan dare kuma a lokacin da ba gurbinta ba? tabbas dai ta san ba ƙaramin abu ne zai kawo shin ba, sai dai ta kasa aunowa? Zancen bikin naɗin ne ko wani abu daban?

“Ranka ya daɗe…” A lokaci guda bakin ta ya ambata cikin ƴar ƙaramar gigicewa.

“Tare da naki sarautar mata…” Muryarsa ta fito a hankali yana ƙoƙarin yin murmushi.

“… Yau ikon naki ne ai tunda kece riƙe da kofa.” Ya sake faɗa da wata ƴar guntuwar raha a cikin sautin nasa.”

Sai a sannan ta lura tana tsaye ne riƙe da hannun ƙofar har yanzu, bata bashi damar shigowa ba, saboda haka tayi saurin yin baya kafin tace.

STORY CONTINUES BELOW

“Mamaki ne ya riƙe ni ai kuma na kasa tsinto komai a cikinsa.”

Ya shigo tare da mai da kofar sannan ya girgiza kansa.

“Ya kamata kuwa ace kin tsinto wani abun a cikinsa Hafsatu, bai kamata ki manta baya ba.”

Sai ta tuno wani zamani a lokaci guda, wani zamani daya shuɗe, wani zamani da mutanen yanzu zasu hasaso shi cikin kalar baƙi da fari, a lokacin da suke gaɓar cin amarcinsu, a sanda yake matsayin Ahmad ɗinta ba wani mai sarauta ba, a lokacin da zata ɗaura zani da ƴar blouse shi kuma yasa wando da shirt babu mai hana su, babu mai tare su… A wannan lokacin ya kan zo ya ƙwanƙwasa ƙofarta yazo ban haƙuri a fakaice duk sanda suka sami ɗan saɓani. Sai ta girgiza kanta.

“Tuna baya ai shine roƙo ranka ya daɗe, ta yaya zan manta kuwa? Kawai dai naga zamani ya shuɗe ne, abubuwa sun canja, a cikinsu kuma har da cewar yau bani ce da lokacinka ba.”

Duk yadda Mai martaba yaso ga daurewa, sai da yaji wani ɓari na zuciyarsa na ƙoƙarin karyewa da maganarta don yafi kowanne mahaluki saninta a duniya. Ya san Hafsatunsa tun asali, ya san irin ƙaunar da take masa, kuma har a yanzu da yake kallon ƙwayar idanunta gani yake kamar komai ɗin bai canja ba, gani yake kamar yau ne ya haɗu da ita a soro cikin daren azumin nan har ya kasa sukuni sai da ya sami bayanin inda take, yana ganin kamar yau ne aka kawo masa ita dauke da tarin ƙaunarsa fal a idanunta da kuma burin ganin cewa shi ɗin nata ne shi kaɗai…

Amma kamar yadda ta faɗa ne abubuwa sun canja ɗin. Zamanika sun shude kuma a yanzu ya riga ya horar da zuciyarta da tarin abubuwan da bata yi tunanin akwai mai saka ta ba sai don shi ɗin shine! Yasa ta yarda ta ture dukkan wasu burika da mafarkanta ta canja tsarinta saboda shi ɗin dai! Ya riga ya san da hakan tun daga daren da ta nuna masa bata son rikon Madaki har zuwa kan gangarowar fara aure-aurensa. Wata mace ce ita kamar kowa mai zuciyar dake son cigaban mijinta dana ƴaƴanta…  Matsalar ɗaya ce, rashin iya daurewa zuciyar tata har shaidan yaci galaba akanta ta wurare da dama.

Sai kawai ya ƙaraso daidai gabanta sannan ya riƙo hannyenta da yake ganin kamar sun fara rawa.

“Zuwa nayi in baki wani labari Hafsatu, wani labari da baya canjawa a rayuwar kowanne ɗan adam. Don haka ki kwantar da zuciyarki dan Allah ki fahimce ni.”

Kalaman tsofaffi ne waɗanda Fulani bata saba jinsu a wannan zamanin ba, saboda haka yadda take kallonsa, gani take kamar za’a saka wani abu ne mai zagwanye shekaru a maido mata da matsayinsa na Ahmadunta ba wani mai muƙami ga kowa ba.

“Zuciyata ta kasa tsayawa, ka gaya min me ya faru kawai.”

Ta tambaya bakinta na shirin fara rawa, duk kuwa da yadda take ƙoƙarin danne taraddadin nata.

Mai martaba yaja hannunta zuwa bakin makeken gadonta suka zauna sannan shima ya tattaro dauriyar da ya hado kafin ya iya shigowa wajen nata, dauriyar gayawa UWA mutuwar ƊANTA!

“Hafsat, zaki iya tuna shekararmu nawa da aure kafin mu fara samun haihuwa ko?”

“Ta yaya zan manta? Shekarar mu uku har da watanni biyar kafin na sami cikin Saifudeen.”

Kai tsaye muryarta ta furta, tana fatan a tsallake komai a kai gaɓar da zata kai su ga bayanin da take son ji.”

“Zaki iya tuna abinda nake gaya miki a duk lokacin da kika damu kanki da tunani a wancan lokacin?”

Ta sake ɗaga kanta.

“Ƴaƴa da dukiya wata rahama da kyauta ce ta ubangiji duk sanda yaso sai ya baka ko ya karɓe.”

Mai martaba ya haɗiye yawu a maƙogwaronsa kafin yace.

“Na san kin yarda da hakan ko Hafsat? Tunda gashi ubangijin ya bamu ƴaƴan a lokacin da yaso kuma har mu raine su tsawon lokacin nan mun ma aurar da wasu. Haka ne?”

STORY CONTINUES BELOW

Wannan karon Fulani bata amsa ba, kallonsa kawai take yi, tana son tabbatar da abinda zuciyarta ke wassafawa.

“Ina so ki ƙarfafa zuciyarki Hafsatu, kiyi tawwakali kamar yadda kika yi tsawon shekarun da kika zauna a gidana ke kaɗai kina fatan haihuwa, ki sani cewa…”

“Ahmad!”

Sunansa da ta kira kai tsaye yasa dukkan wata magana dake bakinsa ta guntule, don ko a baya sai ranta ya baci sannan take tufe ido ta kira sunan nasa, daga lokacin da ƴaƴansu suka fara wayo ma sai ta yakice sunan a bakinta gabaɗaya ta dinga binsa da ‘ranka ya dade ko Daddy’ saboda haka zai iya cewa shekaru da yawa sun wuce rabon da ta kira shi hakan sai dai ko cikin wasa.

“Waye ya rasu? Ka gaya min wa na rasa? Saifudeen? Nadiya? Aisha? Umar? Ko kuwa Safinan data fita yanzu?”

Cikin wani irin amo mai karyewa ta lissafo sunayen duka ƴaƴan nata, yayin da duk yadda yake hango dauriya a idanunta sai da wata guntuwar ƙwalla ta baiyana. Kallonsa take kamar tana son ya zaɓa a ciki ya faɗa mata kamar kuma tana son ya girgiza kansa yace ba haka zancen yake ba.

“Umarul-Faruk.”2

Ya furta sunan kai tsaye cikin wata dakakkiyar murya da a yanzu ke shaida cewa shi ɗin Sarki ne.

Fulani bata ko ƙifta ba, sai kawai ta cigaba da kallonsa kamar bata ji me yace ba tana jiran ya maimaita ne.

“Ba’a sanarwa da kowa ba, da yamman nan aka kira Saifudeen daga can Embassy aka faɗa masa rasuwar, sun ce cancer ce ta kama shi kuma shi kansa bai sani ba, yana ta karatunsa ne kawai yana shan ƴan ƙananan magunguna, sai da ciwon ya ɗanyi karfi sannan abokansa suka kaishi asibiti. Kuma abin yazo da ajali ne kawai Hafsatu, ki yarda da hakan ki sawa zuciyarki hakan don na san ki san cewa akwai waɗanda ciwonsu yafi nasa ƙarfi ma amma sun tashi. Ki yarda cewa Faruk ya tafi ne dama ba don ya dawo ba, a can ajalinsa yake ko da wannan cutar ko babu.”

Kalaman tafiya suke a hankali, Fulani na jin shatin da suke bari akan fatarta har zuwa cikin kanta inda suke yiwa kansu masauki a bayan kan, don ta kasa gane ta yadda zata karɓe su ma balle har suyi ma’ana a cikin ƙwaƙwalwarta, Umar din nata ne ya mutu? Ɗan da ta shekara huɗu bata ganshi ba sai dai taji muryarsa a waya? Ɗan da taci burin ya kammala karatunsa ya dawo ya karɓi dukiyar mahaifinsa ya cigaba da juyawa? Me shi kansa Ahmad ɗin ke gaya mata ne a duk lokacin da tayi masa maganar kasuwanci wa Saifudeen?

…ki d’ora wannan burin naki akan Umarul-Faruk, fa’idar samun ‘ya’ya da yawa kenan…

To sai da ta gama yarda da hakan ta tsara komai cewar kafin Umar ɗin ya kai ga kammala karatunsa ta cimma manufarta ta kassara Madaki, ta karɓo dukkan dukiyar dake hannunsa ta kawo masa don shi ya juya, sannan kuma zai ɗauko ƙafa yazo yace mata wai ya mutu? Tsaya! Wace irin mutuwa ma wai?

“Nifa ban gane ba, ka gaya min komai yadda zan fahimta, wane Umar ɗin ne ya mutu? Sannan don me?”1

“A’uzubillah! Kar kiyi saɓo Hafsat, an taɓa tambayar ubangiji don me zai ɗauke bawansa? Naki ne? Halittarki ce? Ba kulawarsa ya bamu na ɗan wani wucin gadi ba? A yanzu don yaga damar karɓe abinsa sai muce bamu yarda ba? Ko kuwa…”

“Kaga tsaya, ya isa! Nace ya ishe ni Ahmad!”

Ta faɗa tana mai zare hannuwanta daga cikin nasa, a wannan lokacin me kuma waɗannan abubuwan da suka canja mazauninsu a cikin kanta suka shiga aiki.1

“Wallahi karya kuke! Daga kai har wanda ya kira wayar ya gaya muku wai Umar ɗin ya mutu! Ai ba’a halicci duniyata don inzo a tutar babu in koma ba wallahi, shikenan ribar me naci kenan? Na aure ka na haifi ƴaƴa? Ban tara abinda har tsawon shekaru sunana da na zuri’ata ba zai bar zukatan al’umma ba? In haka ne meye fa’idar halittar tawa tun farko?2

STORY CONTINUES BELOW

In don Cancer ce ke damun Farouk ai ba matsala, kasa Saifudeen da wasu su hau jirgi su ɗauko min abina zuwa gobe, ba dai ni na kawo shi duniyar ba to ina nai tabbatar maka cewa na san yadda zanyi in tashe shi da ƙafafunsa! Kai kanka shaida ne ai, tsawo zamana da kai akwai wani abu da na taɓa sawa a gaba kaga ban ci nasara ba? Ko zancen Madaki da duniya ke ganin na gaza ɗan taƙin kaɗan ne a yanzu, dawowar Jakadiya Babba kawai nake jira balle kuma akan abinda ni na haifa da kaina? Don haka kar ma a fara wata sanarwa, ka aika a ɗauko min ɗana Ahmad ni na san yadda zanyi dashi!”

Tun da ta fara maganar, wani abu ya sarƙafe Mai martaba a zaune, wani abu da bai san menene ba balle har ya fassara shi da suna… Ƙwaƙwalwarsa na ɗaukan duk kalamanta tana sake biya su ne a ɓangaren ƙwaƙwalwarsa mai tacewa da fahimtar kowanne bayanai.

Abinda ya sani kawai shine ya fahimci abubuwa guda biyu kwarara… Dukkan maganganun da take faɗa maganganu ne dake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta cike da wani yaƙini da babu shaci faɗi a cikinsa, sannan kuma ƙarara komai yake cewa ba’a haiyacinta take faɗarsu ba, watakila ma ba’a hankalinta ba!

Kallonta kawai yake kamar yadda tayi shiru itama tana kallonsa, dukkan jikinta na rawa, gaɓobinta na girgizawa da wata irin karkarwa yayin da zuciyarta ke dokawa a ƙirjinta har yana jin ƙarar bugunta daga inda yake zaune, tana bugawa tamkar zata daka tsalle ne ta faso ta ƙirjin nata.

A daidai wannan lokacin ne kuma motar Hamza tare da motar ƴan sanda guda ɗaya dake binsa a baya ta shigo cikin ginin masarautar, hannunsa na hagu riƙe da sitiyarin motar yayin da hannunsa na dama ke riƙe da I.D Card na shaidar aikin direban matar sarki, wanda ke ɗauke da sunan Sani direba da kuma wasu ƴan bayanansa!

 

***

LAGOS.

Voilá Private Hosital, No 1388 Gyari Park.

Ƙarfe bakwai ne na safiya don haka komai daidai yake da irin yanayin da yake buƙata a ɗakin, iskar mai daɗi da gamsarwa yayin da hasken ɗakin yake madaidaici mai rangwamen tasiri. Ibrahim Ahmad Madaki ya buɗe idanunsa a hankali bayan yunƙirin da yayi kusan sau uku.

Kuma a lokaci guda nauyin dake gefen ƙirjinsa ya tuna masa da halin da yake ciki, abinda ya faru jiya, komai yana kansa. Yadda zafin harbin nan ya ratsa kowacce jijiya ta jikinsa, yadda ya dinga jin zafin na tafiya zuwa sauran ɓangare na jikinsa, da yadda kowacce gaba ta jikin nasa tayi nauyi zafin na harbawa zuwa duk inda ya san saƙonsa zai isa.

Ya tuna sanda ya sake hango ƙyallin wannan ƴar jar fitilar a jikin baƙin mayafin Jidda, alamun waɗanda suka yi harbin basu gama ida manufarsu ba, sai ya maida idanun nasa ya sake rufewa sannan ya buɗe su, duk yadda ya kai ga tuna zafin da yake ji a wancan lokacin, muryarta da yake tunawa taso ta daine hakan, yana iya tuno yadda sautin nata ke karyewa cikin wani irin kuka kamar wancan lokacin da take roƙonsa cewa kar ya mutu, kamar shine abu mafi muhimmanci a rayuwarta, kamar zata shiga wani hali ne in har babu shi ɗin…

A lokacin ne kuma tunaninsa ankarar dashi wani abu na biyu a jikinsa bayan nauyin da yake ji a ƙirjinsa, wani abu tamkar ɗumi a tsakanin ɗaya hannunsa wanda babu ciwon, sai ya murza yatsunsa, yaji sun hadu da wasu daban ƴan ƙanana masu madaidaicin laushi, saboda haka ya yunƙura ya kai idonsa wajen, a take kuwa idanun nasa suka yi kyakkyawan gani.

Jiddan ce zaune kan wata kujera dake jikin gadon da yake kwance, ta kwantar da kanta a gefen gadon itama inda jikinsa bai cinye ba. Sai dai ba wannan ne abinda yafi ɗaukar hankalinsa ba illa hannunta dake cikin nasa, yatsunta da suka ratsa a tsakanin nasa ɗauke da ɗigo-ɗigo na wani abu tamkar jinin da bai gama fita ba, yadda yatsunta suka shiga nasa sak irin yadda ya riƙo ta ne ranar da ya rabo ta da ƴan uwanta a Kiyari, ranar da ubangiji ya ƙaddaro ta cikin rayuwarsa.

STORY CONTINUES BELOW

Baya iya ganin duka fuskarta don ta cusa ta cikin bargon da aka rufe jikinsa dashi, sai saman kanta kawai inda mayafinta ya zame babu ɗankwali, gaban gashinta da yake rabi kitso rabi a tsefe ya fito da yawa, yaji kamar ya miƙa ɗaya hannunsa ya rufe mata shi amma ya kasa, wani irin tausayinta ya ratsa zuciyarsa, kayan jiya ne a jikinta wanda har yanzu suna bace da jini alamun bata koma gida ba. Ya sani cewa a yanzu zan iya dafa Alqur’ani cewar zuciyar yarinyar nan mai kyau ce, tana tausayi ga kowanne ɗaya adam a duniya tunda har zata shiga irin wannan tashin hankali ga shi ɗin da bai taɓa tsinana mata komai, shi ɗin da ƙarara ya nuna mata cewar zarginta yake akan wani abu da a yanzu yake fahimtar bata san dashi ba.

Don tun sanda ya fara bincikensa a kanta bai taba samun wani abu da ya aibata masa halinta ba, komai yana siffanta ta ne da dukkan halin da ya same ta dasu, bata taɓa bashi wata kofa da zai ɗorar da zarginsa guda ɗaya akanta ba, ana cikin hakan ne kuma yazo ya rungume, yasa zuciyarsa ta kara damalmalewa da al’amarinta, ya fara jin wani abu game da ita da bai taɓa danganta kowacce mace dashi ba, kuma wannan abin shine tunanin cewa zai iya samun wani farin cikin rayuwa ta hanyarta bayan aiki da ibadar da yake ganin su kaɗai ne hanyar annashuwarsa.

A hankali idonsa yakai kan drawer dake gefen gadon inda wasu ƴan tarkace suke, takalminsa ne da muƙullin motarsa sai wayoyinsa da wallet, bayan haka babu ko robar ruwa akai, alamun tun a jiyan nan bata sa komai a cikinta ba kenan tana gadinsa dashi da kayansa.

Kulawa irin wannan, wani rami ne mai zurfi da bai taba samun wani yayi koƙarin cike shi ba a rayuwarsa, bai san ma yaya take ba balle har ya taɓa hasashenta, watakila ita a wajenta abinda take yi ba komai bane illa taimakawa, amma a wajensa wani abu ne da a baya yasha hasashen cewa zai iya bada dukkann abinda ya mallaka don ace yau bayan mutane biyu a rayuwarsa wato Mahaifinsa da Mubarak, an wayi gari akwai wata zuciya da zata rikice wajen alhinin lafiyarsa irin yadda tayi, ace tsakani da Allah ba don wani abu nasa ba wata zuciya tayi taraddadin rasa shi, yaji cewa atleast he matters to one more person out there…!

Sai kawai ya sake haɗe yatsunsa da nata a hankali yayin da tunaninsa ke tariyo maganganun Mubarak.

…ina gaya maka ka saki ranka game da yarinyar nan ka juye sharrinta zuwa alkhairi, ka fahimtar da ita cewa ba ƙaramar sa’a tayi ba data same ka.’

Sai ya maida idanunsa a hankali ya rufe saboda allurar baccin bata kai ga gama sakinsa ba, zuciyarsa ta ayyana cewa wataƙila lokaci yayi da zai maida sharrin Fulani ya koma alkhairi gare shi!

**

11:30 Am.

“Anyi sa’a sosai, da yake a gefen kafada ne, bullet din bai lalata masa wasu organs da tissues masu yawa ba, sannan duk zuciyarsa ta buga  bata yi bugun da zai haifar masa da wani ciwon ba, muna da visiting doctors na ciwon zuciya sosai, zaku iya magana da can asibitin nasa, a kawo file dinsa nan sai su duba da da zarar sun zo… Akalla dai bana jin zai wuce kwana bakwai zuwa takwas kafin mu sallame shi.”

Duk wannan bayanin yana fitowa ne daga bakin wani farin likita dake tsaye yana rubutu a gefen gadon Madaki, yayin da Mubarak da wata Nurse ke tsaye a kowanne ɓangarensa.

A sannan ya buɗe idanunsa a karo na biyu, hasken ɗakin mai yawa a yanzu ya shiga idanunsa, da kyar ya iya saita ganinsa akan mutanen dake tsaye a gefen nasa.

Ganin ya farka yasa likitan ya saki rubutunsa ya fara wasu ƴan aune-aune a jikinsa Nurse din na taimaka masa. Idanun Madaki suka tsaya akan Mubarak bayan ya tabbatar da cewar iya su kenan a ɗakin. Kallonsa yake shima da idanunsa daje shaida irin kaɗuwar daya shiga da kuma tashin hankalin al’amarin, sai dai duk da haka wani abu ya canja game dashi ɗin, a yadda ya sanshi ko da wannan tashin hankali, zaiyi ƙoƙarin yi masa wani ɗan barkwanci ko raha, amma a yanzu kallonsa kawai yake cikin tausayawa.

STORY CONTINUES BELOW

“Bugun zuciyarka na kan track daidai, ka sami abinci mai laushi da ruwa haka wanda zai ƙosar da kai kaci a yanzu, zaka ƙara jin sauki insha Allah.”

Cewar likitan yana Kallon Madaki bayan ya tamaka masa ya dan jingina da gadon, Mubarak yaso yayi wa wannan bayanin, amma wani irin kwarjini da firmness da ya tsinta a idanunsa yasa shi fahimtar cewa ko bashi da lafiya shi ɗin dai shugaban kansa ne.

Madaki ya gyaɗa kansa.

“Nagode Doctor, sai dai ina ganin za’a rage min kwananakin da naji kana faɗa, don akwai ayyuka da yawa a gabana.”

Likitan yayi wani guntun murmushi sannan ya juya ya karanto su ansa a jikin file din.

“Komai yawan aikin dake gabanka Ibrahim ai sai da lafiya zai yiwu ko? Ta yaya zaka yi signing takardu da hannunka a ɗaure. Muyi fatan sauƙi kawai.”

Da haka ya tattara ƴan tarkacensa ya fita Nurse din na bin bayansa.

Ya kalli Mubarak dake tsaye kyam har yanzu yana kallonsa sannan yace.

“Kaima nagode haka zaka iya tafiya, ba sai ka nuna min cewa yau asabar na katse maka baccinka ba.”

“This is not a joke Mdee, ka gaya min waye zai harbe ka a garin nan? Laifin me kayi? Ta yaya aka san inda kake ma?”

“Ban sani ba Mubarak, harbin ya taho ne daga can sama, ta yaya zan gane su waye a can?…”

Sai kuma ya ɗan tsaya kafin ya cigaba.

“… You mean ba’ayi involving ƴan sanda ba ma? Ta yaya asibitin suka yarda suka karbe ni?”

“Ɗaya daga cikin mutanen da suka dauko ka security personnel ne, ya kira mutanensa sun duba koina tun a jiyan amma ba’a sami kowa ba, so now case din ya dawo kanmu,  kuma I don’t care how long you sit on that bed in dai zaka tashi, the only thing I’m after is dole ne mu samo mutanen nan Mdee, wallahi zuciyata ba zata iya ɗaukan wannan al’amarin ba, na dauki abubuwa da yawa akan rayuwarka a baya, na maida komai ba komai ba, na kalli abubuwa da yawa ta fuskar alkhairi amma banda yanzu. Zuciyata ta kai ƙarshe Mdee kuma wallahi ba zan dauka ba.”

Madaki yayi shiru kawai yana nazarin maganganunsa ba tare da yace komai ba, a tsawon rayuwarsa ya san Mubarak kuma ya san dukkan abubuwan daya faɗa gaskiyane, a kullum shi mai bashi fata ne akan abubuwan da yake ganin aibunsu, shi ke ƙarfafa masa gwiwa ya tunkari dukkan abinda yake shakka komai tsaurinsa kuwa , don haka in har a yanzu yace an kaishi karshe, to tabbas an kai shi ɗin don ko masu azancin magana kan ce mai haƙuri bai iya fushi ba.

“Then who are you suspecting?” (Wa kake zargi kenan?)

Mubarak ya gyada kansa bai tabbatar da abinda yake zargi ba har yanzu don haka ba zai fallasa komai ba, don duk yadda zuciyarsa ta kai ga turniƙewa yana tsoron yin abinda zai iya dana saninsa a gaba.

“Bincike zamu fara, amma kasa a ranka cewa ba zamu kyale ko waye ba wallahi.”

Madaki ya gyaɗa kansa, kamar ya fada masa cewa bashi suka zo da niyyar harbi ba sai kuma ya tuna da Jiddan, saboda haka yayi tambayar da yake son yi tun bayan farkawarsa.

“Ina take? Ɗazu na farka na ganta a nan.”

Mubarak ya fahimci wa yake nufi Saboda haka ya ɗan cije leɓɓensa.

“Nasa an maida ita gida a motarka, tana bukatar canja kayan jikinta.”

Ya fadi hakan yana tuno yadda Jiddan ta dinga kallonsa a lokacin da ya dage sai ta tafin, idanunta na shaida kamar itama bata yarda dashi bane, kamar zai sace Madakin ne bayan tafiyarta.

“Nayi waya, su Khadija zasu ƙaraso maka da abinci yanzu.”

Cewar Mubarak ɗin, sai dai yana rufe bakinsa lokacin yayi daidai da sanda kofar dakin ta bude daga bayansu, dukkaninsu suka juya a lokaci guda kuma a lokaci gudan idanunsu suka sauka akan Jidda, tayi wanka ta canja kaya cikin wata doguwar riga baƙa data ƙara fito da hasken da fatarta ta fara a ƴan kwanakin, sannan hannunta riƙe yake da wani ƙaton kwali duk samansa ya yayyage, ta tallafo abinta da duka hannayenta.

STORY CONTINUES BELOW

“Cewa Baba Saminun nayi ya jira nayi wanka mu dawo tare don ban san wa zai dawo dani ba idan ya tafi.”

Muryarta ta fito bayan tayi sallama tana kallon Mubarak ɗin dake mata kallo kamar na tuhuma, a tunaninta ganin Baba Saminun daya aika ya kaita ya dade ne yasa yake binta da wannan kallon irin na dazu, a cikin kanta gani take kawai duk irinsu daya da Madaki, kowa ba mutunci ne ya ishe shi ba shi yasa har suka zama abokai, amma tunda ta iya da Madakin to shima mai sauƙi be, sai da ta karaso kamar zata wuce shi sannan tace.

“Ina kwana? Ya mai jikin?”

A lokaci guda Madaki dake can zaune yaji wani abu kamar daɗi ya ratsa zuciyarsa, ko ba komai ta girmama Mubarak ɗin dabyake abokinsa duk kuwa da cewa fuskarta babu wata fara’a.

“Lafiya ƙalau.” amsar ta fito a gutsire daga bakin Mubarak.

Abinda ya ɗan bawa Madaki mamaki kenan har ya maida idonsa kansa, a yadda ya sanshi da zumudin ganinta ya ɗauka ai gaisuwar tasu zata fi haka, ko dai wani abu ya faru ne? Shi bai ga komai ba, don haka sai kawai ya alaƙanta hakan da yanayin da Mubarak ɗin ke ciki a lokacin. Idonsa ya koma kan Jidda da ta karaso ta ajiye katon kwalinta akan ƴar drawer dake gefen gadon, ƙamshin turarensa ya ziyarci hancinsa a take, sai dai kafin ya gama nazarin kwalin sai jin hannunta ɗaya kawai yayi a ƙasan wuyansa, kamar a jiya sanda take ƙoƙarin riƙe kansa kafin ya suman da yayi ya dauke shi, mamakin hakan ya sarke shi yayin da a lokaci guda sanyin hannayen nata ya ratsa fatarsa har cikin ɓargo.

“Yaya jikin naka? Da sauƙi? Me suka ce?”

Kafin ya amsa waɗannan tambyoyin yaji ƙarar rufewar ƙofa alamun Mubarak ya fita, basu gama zancen da suke ba amm sai kawai ya juyo da idanun nasa ya kalle Jiddan, a lokacin ne ta janye hannunta da sauri sannan tace.

“Kayi haƙuri, wata Nurse ce yanzu a hanya tace in taɓa jikinka, idan da ɗumi to kar kasha abu mai zafi a yanzu.”

Jidda ta fadi hakan a lokaci da wani ɓari na gefen zuciyarta ke ƙwafa, ta san ta jawowa kanta kenan don ta sani cewa ba yarda da maganganunta yake ba kuma babu ta yadda zai fara a yanzu. Kallon fuskarsa kawai take tana tunanin waye zai kalle shi yace shi aka harba jiya? Gabaɗaya jinin nan daya ɓata jikinsa da fuskarsa an goge shi tas sannan an canja kayansa da wasu na asibitin masu hannu guda, don haka hannunsa daya dake daure da bandeji ya fito waje yayin da idanunsa da kamar sun ɗashe suka kara wani kyau da haskawa. Yana da dauriya tabbas, don watakila da ita aka harbin nan ya samu, da yanzu zaman jana’iza ake.

Bata yi aune ba a cikin tunaninta sai kawai ji tayi ya miƙo hannunsa ɗaya da babu ciwon kuma babu allurar drip ɗin ya kamo nata duka biyu, ya janyo ta zuwa kan gadon sannan ya zaunar da ita a gabansa, fuskarsa dab da tata, tana jin ma kamar numfashinsa na busawa ne a saman hancinta, sai duk da mamakin dake cinta sai ta kasa dagowa ta kalle shi kamar yadda ta kasa janye hannun nata, don da zarar rike ta ba abinda take iya tunawa a cikin kanta.

“Meye a cikin kwalin?”

Ya ilahy! Yadda muryarsa ta fito a hankali da wani zaki kamar an zuba mata sukari ya sata jin wani iri, amma duk da haka maimakon ta kalle shi, sai ta maida idonta kan tsohon kwalin itama sannan tace.1

“Abinci na kawo a ciki, kuma ba zan iya ɗauko duka kayan a hannu ba shi yasa nasa su a kwalin. a cikin store na samo shi, kamar na T.v ne ko wani abun, idan zan koma zan mayar maka da abinka ai.”1

Maganar taso tasa Madaki murmushi, a tunaninta tuhumarta yake game da kwallin? kwallin da bai san dashi ba ma, bata san shi ta abinda ke cikin kwalin yake ba don ya manta rabonsa da cin wani ƙwakwaƙwaran abinci a ƴan kwanakin nan. A lokacin ne kuma yaji kamar sannan ya kamata ya gode mata, ya nuna mata ɗimbin godiyarsa game da karamcinta da kuma taimakonta amma ya rasa ta ina zai fara, bai ma san me zai ce ɗin ba saboda haka ya yanke shawarar tafiya kai tsaye ga abinda yafi fahimta a lokacin.

“Me kika dafa?”

Saura kadan Jidda ta dago ta kalle shi saboda mamakin tambayar tasa, ta zata ai a yanzu ma zai ce baya cin abinci mai nauyi ne ta koma da kayanta, don sanda take girkin, har ƴar mita take a cikin kanta cewar ba ƙaramin aikinsa bane ya juyo da ita da kayanta don taga alama shi anfi yin abu arziki dashi in har baya cikin haiyacinsa, sai gashi ya bata mamaki. Amma data lura luma sai taga ba abin mamakin don yunwa ba kanwar uwar kowa bace, inda zai dore a haka ma komai zai fi sauƙi don ita ba bakuwar zafi bace har hira sai su dinga yi kafin sanda zata koma garinsu. Saboda haka ta haɗiye yawu a hankali sannan tace.

“In ka saki hannuna zan zuba maka sai ka gani.”

Ta fada tana kallon hannayen nata daya riƙe, kamar yayi murmushi kar kuma bata tabbatar da hakan taji ba, sai ya zare hannun nasa a hankali sannan yace.

“Muna kwarya.”

Karo na farko tun bayan saninta dashi Jidda tayi murmushi mai kama da dariya har haƙoranta suka baiyana, ashe in ya sauke fadin ran nan da yake yi tsaf zai koma mutum?1

A lokacin da tayi murmushin kuma ta miƙe Madaki yaji zuciyarsa ta matse da wani tunani mai nisa… Ranar da ya dara ganinta ranar da ta juyo daga gaban saurayin nan ɗauke da wannan murmushin da ba nasa ba, a yau sai gashi shima yayi nasarar samun nasa a wajenta, watakila ma har ya fi na saurayin, sai dai tsaya! Wai wanene wannan saurayin ne? Ya samu kansa da yin tambayar da bata taba ɗarsuwa a ransa ba.1

“Baddo tace alaiyahu yana da mutukar amfani a wajen wanda bashi da lafiya, wai yana sa cikin mutum ya buɗe ya dinga cin abinci sosai, shi yasa na saka a ciki.”

Muryarta ta dawo dashi daga ɗan tunaninsa a lokacin da ta buɗe flask take zuba abincin. Baddo. Kakarta kenan, har ta fara bashi labarin danginta? Sai ya juyo ya kalle ta.

Ƙamshin abin da take zubawa a plate ɗin ya cika hancinsa dama iskar ɗakin, Potate ɗin dankali ne da alaiyahun da kuma nama fal! Bakinsa yayi magiya kamar bai san cewa shi za’a kawowa ba.1

“Beleive me, idan cikina ya buɗe ba zaki ya ciyar dani ba.”1

Ya faɗa yana girgiza kansa tare da kallonta, sai ta sake wani murmushin ɗan karami ba tare da ta juyo ba, dama ba wuya ne wai sata dariya?

“Tab! Ai baka sanni bane shi yasa, akwai fa sanda har tukunya guda ta tuwo muka tuƙa ni da Sadiya sanda ana wani biki a ɓangaren mu, kaga kuwa zan iya.”1

Sadiya. Ya sake rubuta suna na biyu wanda ya riga ya sanshi a zuciyarsa sanda ta ƙaraso gabansa, sai dai bata zauna akan gadon ba sai ta jawo wata kujera a gefe kamar ɗazu ta zauna sannan ta ajiye plate ɗin a akan gadon. Ya kalli plate din a hankali yana shirin ya gaya mata cewa ba zai iya ci da hannun hagu ba sai kawai gani yayi ta ɗebo a cokalin ta miƙo masa… Ya dago ya kalle ta, itama shi ɗin take kallo da alamar yaci mana.

“Babu zafi.” Muryarta ta furta a hankali tana ɗan girgiza kanta.

A cikin zuciyar Madaki, a wannan lokacin fata kawai yake a cikin zuciyarsa cewa ubangiji yasa bai cuci yarinyar nan ta kowanne bangare a dan zamansu ba, don bai san ta yaya zai wanke kansa ba. A yanzu ya fahimci cewa bayan saukin kanta, in zata yi abu kawai zata yi shi ne babu ruwanta da wani iyayi irin na mata wanda ke kaisu ya baro a mafi yawan lokuta.

Sai kawai ya lumshe idanunsa a hankali, ya ajiye komai a gefe sannan ya raba fatar leɓɓen bakinsa slightly yana shirin hango abinda bai taba hasashe a rayuwarsa ba, Jidda tayi murmushi a hankali itama sannan ta saka cokalin a bakinsa daidai lokacin da ƙofar ɗakin ta buɗe… Khadija ta shigo riƙe da Hanan yayin da Aliyu ke bin bayansu, a nasa bayan kuma, Salwa ce ɗauke da wani haɗaɗɗen basket mai ɗauke da foodflask kala-kala na abinci iri-iri!.17

A cikin wayar Madakin kuma dake gefe, text ya shigo na labarin rasuwar Umarul- Faruk!1

***Hoto ƙarya ne!

Abinda Salwa ta ambata kenan a lokacin da tayi arba da fuskar Madaki kuma numfashi ya tsaya a maƙogwaronta, don yana da wani irin kwarjini da kamala wanda ya fito karara fiye da yadda take ganinsa a idanunta. A lokacin da yayi murmushi wa Aliyu dake nufar wajensa kuwa, sai da zuciyarta ta buga cikin ƙirjinta sannan a take wani gefe na ƙwaƙwalwarta ya tuna mata da nata kammanin, kamannin fuskarta… Musamman wasu ƙananun ƙuraje da suka fito akan kuncinta duka biyu.1

Sai kawai ta juyar da kanta gefe sanda muryar Khadija kewa Aliyu daya ruga magana cewa kar taje ta hau kansa, a lokacin ne kuma idonta ya sauka a gefem, gefen gadon… Inda duk da ɗimbin abinda take ji take zuciyar ta gaya mata cewa yarinyar da take kallo itace wannan halittar dake cikin jerin abubuwan da take son kawar wa a duniya, amma yarinya kamar wannan? Ta yaya hakan zai yiwu? Ta yaya za’ace da wannan abar take gasa wajen mallakar sunan Matar Madaki? Ta yi zaton zata ga irin wayayyun matan nan ne da suka goge da duniya ta hanyar kudi da kuma dukkan wata wayewa ta zamani, amma wannan? A lokaci guda sai taji wani dunƙulen abu ya zarce cikin busashshen maƙogwaronta.1

Akan wannan yarinyar da bata da ko kyau balle daukar hankali ta rikita nutsuwarta? Akanta ta ɓata dubunnan kuɗaɗenta da har aka tafka wannan akasin? Akan wannan yarinyar da baifi cikin kwana ɗaya Namama ya tarwatsa ta da dukkan ahalinta ba? Allah ya sani ba irin nadama da takaicin da bata yi ba a lokacin da ta samu labari abinda ya faru, wanda ta danganta komai da rashin ƙwarewar mutanen kawai ba don wata ƙaddara ba.

Saboda tun a Abuja sau nawa tana ganin ana gudanar da ayyuka irin wannan kuma ba’a taba samun wani akasi ba sai akan nata? Zuciyarta taso ta kumburan tun a jiyan da Khadija ke gaya mata abinda ya faru bayan fitar Mubarak, amma da ya dawo ya shaida musu halin da ya baro shi a ciki cewar al’amarin da sauƙi sai itama ta sami nata sauƙin a zuciyarta.

Tana ganin watakila hakan ma ya zame mata wata hanyar da zata fara aiwatar da kudirinta akansa, watakila tunda bai raunana da yawa ba, hakan somin hanyar nasararta ne, musamman a yanzu da tayi ido biyu da yarinyar sai ta sake raina komai, take ganin cewa ba sai ta tashi hankalinta ta sake wahalar da kanta a karo na biyu ba… Babu abinda yarinyar ta sani kuma babu abinda zata iya tare mata, don in ba aikin ƙaddara ba kamar yadda Mubarak ya siffanta ta yaya ma za’a haɗata da Madakin? Ai ko makaho idan ya shafa zai san cewa banbancin a baiyane yake! Mata irinta masu wayewa da sanin rayuwa su suka dace da maza irinsa ba wannan ƴar abar da wani sai ya duba sau biyu tukunna zai ganta ba.1

Baki da wata matsala! Gefen zuciyar tata ya ayyana hakan a ranta, yana gaya mata cewa an sami wannan akasin ne don ta daina wahalar da kanta, tabi komai a sannu… Ibrahim ba zai taɓa son wannan yarinyar ba kamar yadda itama ba zata san darajar abinda ke hannunta har ta iya karkato da hankalinsa kanta ba…

Khadija na ta ƙoƙarin gaisawa da yarinyar data miƙe rike da plate ɗin abinci a hannunta yayin da har a lokacin Madaki ke murmushi wa yaran, ya miƙowa Aliyun hannu suka yi musabaha kamar wanda ke gaisawa da sa’ansa… Wani ƙullutun abu ya taru ya sake cika maƙogwaronta fam, tayi ƙoƙarin haɗiye yawu amma wannan karon ya kasa tafiya, tana jin kamar zuciyarta ce ke ƙoƙarin tahowa ta fito… Ina Naja’atu take ne? Tazo ta gaya mata tunda suke yawace-yawacensu akwai namiji irinsa da suka taɓa gani, sai dai maza wanda za’ace sun fi shi a kyawun fuska amma ba kamala da kwarjini ba, to ta yaya kuwa ba zata yi dukkan ƙoƙarin ta akan ta mallake shi ba?

Tana tsaye a kofar har a lokacin babu wanda ya lura da ita, kamar ta daurewa komai ta karasa ciki sai kuma taji cewa bata shirya ba, sun taho ne da dan guntun firgicinsu na halin da zasu zo su tarar dashi a ciki, amma tun da har ya warke haka yana iya gane mutane da wannan murmushin… To sai ta shirya tukunna, sai ta shirya a yanayin da kowannensu zai ga darajarta, kowannesu zai ga ƙimarta, Salwa ce ita! Wadda ke shirin hawa matsayin matar Madaki, don haka Madakin ba zai ganta a haka ba sai a yanayin da ko daga mafarki ya tashi zai ga banbancinta da wannan baƙar yarinyar da bata ko hango ta a cikin idanunta!

STORY CONTINUES BELOW

Saboda haka sai kawai ta sunkuya ta ajiye basket ɗin hannunta tare da katan ɗin lemon Rani dake hannunta sannan ta juya.

*

Kwarai Jidda taji dadin zuwan baƙin da daga baya ta fahimci cewa matar Mubarak ce da kuma ƴaƴansa biyu, Khadija ta girme mata sosai don ko a ido zata iya cewa tafi sa’ar Jamila ma, amma yadda ta dinga janta a jiki da hira sai taji kamar ta ga wata ƴaruwarta ne daga gida, kamar taga wanda ta sani bayan daɗewar wani lokaci, kuma da yake itama Khadijan tana da ƴar magana har sai suka saba kafin tafiyarsu, ta dinga mamakin yadda take da tsananin kirki sosai ba kamar mijinta ba wanda zuciyarta ta saka shi a wani layin can daban.

Sun dade har yamma bayan tayi ta kiran nambar wata a waya wai ita Salwa, tace tare suka zo amma ita dai bata ganta ba sai kayan da aka ajiye a bakin kofa tace a hannunta suke, daga baya ne ta same ta a wayar take shaida mata cewa wai bata jin daɗi ne taje taga likita anan cikin asibitin sai kuma ta koma gida. Ta lura sai a lokacin Khadijan ta dan ji dadi don tana ta faɗin dama bata san abinda zata gayawa Mubarak din ba tunda ƙanwarsa ce.

Yarinyarta mai suna Hanan itama tayi ta bibiyarta har tana faɗin cewa ta mata kitso irin nata mai iya rabi kawai, Jidda tace ai karta damu tunda sabon style ne da ita ta fito dashi to kuwa ta sami kitson yi. Kuma duk tsawon wannan lokacin in banda waya ba abinda Madaki yake yi, kala-kala wadda bata fahimtar komai a ciki saboda yadda sautin muryar tasa ke fita a hankali kamar wanda ke cikin wata damuwa, ta dai fahimci kamar ba wayar aiki bace tunda aƙalla yau asabar ma, sai dai bata san me ya faru ba.

Da kyar ma ya cinye abincin data fara bashi bayan wata Nurse ta shigo da azahar ta cire masa drip ɗin, a kayan su Khadija kuwa fruits kawai yasha, hannunsa daya riƙe dana Aliyu wanda ya manne masa alamun shima mai son manyance ne irinsa.

Abinda Jidda ta kasa ganewa shine wane irin ƙarfin hali ne da Madaki, don duk da damuwar da taga kamar yana ciki, da la’asar bayan an cire masa drip ɗin ita yasa ta miƙo masa gogaggun kayan jikinsa da aka cire yace wai masallaci zai je, sai Allah yasa lokacin yayi daidai da shigowar wani likitan yamma, shi ya dage yafi karfin hujjar da Madakin ya kafa cewar zai iya fita ɗin yace dole ba zai bar ɗakin nan ba.

Ana dab da sallar magriba su Khadija suka tafi, a lokacin Mubarak ya dawo sun fi kusan awa guda suna tattauna abubuwan da su kadai ke fahimta, don yadda suke magana ƙasa-kasa kuma Madakin na cigaba da amsa waya daya bayan ɗayan bai sa ta fahimci komai ba.

Har can waje taje ta raka su Khadijan riƙe da hannun Hanan, sai dai bata karasa wajen parking space din ba don har yanzu bata jin zuciyarta tayi kwarin da zata iya tunkarar wajen nan.

A hanyarta ta dawowa ta dinga kallon kyan tsarin asibitin da ko a ranar da suka zo bata lura dashi ga, zuciyarta ta ayyana mata cewa dole ne a cafki mugwayen kudi a wajen nan don tabbas ba zasu yi wannan haɗaɗɗen ginin a banza ba, sai ta hango asibitin garinsu na gefen masarauta, wajen da warin izal dana kwata kadai ya isa wani ya kamu da wata cutar, banda ƴan banzan ciye-ciyen da mata ke yi a wajen zaman likita, suyi ta siyan abubuwa suna jefawa a baki ba tare da sanin yadda aka yi su ba.

Hanya ta kawo ta wajen wannan lab din da aka mata test ɗin nan, taji kamar ta leƙa ta gaya musu an kwantar da baban nan nata a asibitin ko zasu zo dubiya tunda ta san bayan iyalin Mabarak ɗin nan basu da kowa a garin, amma sai taga babu kowa a ciki don haka ta karkato hanya ta dawo ɗakin.1

Ƙarar ruwa a famfo ya tabbatar mata cewa Madaki yana ciki yana alwalar da bata san ya yake yinta ba tunda hannu ɗaya a ɗaure yake, saboda haka sai kawai ta juya ta sake fita. A ɗan bayan ward ɗin kaɗan akwai wani waje da akayi shuke-shuke da fanfo a tsakiya wanda aka saka masa mesa don bawa fulawowin ruwa, bata ko damu ƴan karafunan da aka zagayen wajen dasu ba ta tsallaka ciki ta zare mesar jikin fanfon ta kunna sannan tayi alwalarta, tana yi tana bin duk wanda suka haɗa ido dashi kallo itama tana mamakin abinda yasa suke kallon nata, ilai kuwa sai ga wani security nan yazo da bayanin cewa ba’a shiga nan ta fito.

STORY CONTINUES BELOW

Slippers ɗinta duk ruwa ta koma ɗakin a lokacin yana sallah akan wani ɗan center carpet dake gefen ɗakin, yana zaune cikin tahiyya ya juya mata bayansa ɗakin shiru baka jin komai illa ƙarar fitar A.c, sai dai yana miƙewa tsaye cikin raka’a ta uku da muryarsa ta fara rero surar fatiha a hankali cikin sautinsa sai da taji tasirin amon muryar tasa har a jikinta.

Ta matsa zuwa kan carpet ɗin da niyyar binsa jam’in, a karo na farko bin wani namiji jam’i bayan limaman islamiyarsu, har zata tayar sai kuma taga kamar bata yarda da carpet din ba tunda ta kula yawanci ma’aikatan asibitin arna ne, musamman masu shara, likitan ma ɗaya kawai ta gani kamar musulmi sai kuma waɗannan matan na lab wanda da alama su hausawa ne ma.

Saboda haka sai ta kwanto ɗankwalinta ta shimfiɗa a saman carpet din sannan ta gyara mayafin kanta kafin ta tayar.

Ko kaɗan Madaki bai san shi take bi sallah ba sai bayan da yayi sallama ya juyo sannan yaga ta miƙe tsaye, a lokaci guda sai yaji kamar wani abu ya ratsa zuciyarsa dake da tauri a lokacin, ya kasa sabawa da al’amarinta har yanzu, ya kasa sabawa cewa akwai wataa karƙashinsa dake cikin ikonsa, shekaru fiye da talatin yana rayuwa shi kaɗai, bai taɓa samun wani makusanci irin haka ba saɓanin Mubarak da suka hadu tun a makaranta, shi yasa dole a dauki lokacin kafin ya gama fahimtar hakan.

Carpet ɗin bashi da wani girma, saboda haka a yanzu da ya juyo sai yayi kusa da ita sosai, don da tayi sujjada ma kanta da kaɗan ne bai ƙaraso ƙafarsa ba. Idonsa ya sauka akan sauran jikinta, shape din jikinta… A cikin kansa tunani yake in har da gaske ya yarda zai gyara alakar tasu to ta ina ya kamata ya fara ne? Bata hakuri? Yarda da ita ko kuma shawarar da Mubarak ya taɓa bashi tun a farko? Wayarsa a ƙasan carpet ɗin tayi ƙara, ya jawo ta ya ɗauka.

“Assalamu alaikum, barka da yamma.”

Yayi gaisuwar a lokacin da ciwon kafaɗarsa ya shiga zugi, alamun lokacinsa yayi.

“Alhamdlillah, mun yini lafiya Hajja?”

Ya sake wata gaisuwar a lokacin Jidda ke yin sallama.

“Banso kika ji labari ba, ba wani ciwo ne mai yawa ba Hajja, ko ciwon wannan ƙafar taki ma yafi shi zafi.”

Akayi magana cikin wayar wanda yasa shi wani ɗan guntun murmushi, Jidda ta kalle shi sai kuma tayi niyyar tashi ganin yadda yake zaune kusa da ita sosai. Ta damƙo mayafinta a lokacin da ya riƙo nata hannun, ta juyo ta kalle shisai ya mata alama da ido cewar ta dawo ta zauna kafin ya faɗi wani abu kuma a cikin wayar da ya sanya zuciyarta bugawa.

“Gobe za’a kawo gawar tasa ne?”

Sai ta dawo ta zauna ɗin tana jin kamar hannunta na rawa a cikin nasa, ba wai don ya riƙe ta ba don a yanzu tana jin kamar ta saba ne da hakan. Tunanin waye ya rasu kawai take don daga yanayin yadda yake wayar kamar yana magana ne da wata ƴaruwarsa.

“Kar ki damu Hajja, insha Allah I’ll be there, zan zo, dani za’ayi komai.”

Ya sake yin shiru sai kuma yace.

“Tare zamu zo, zaki ganta insha Allah.”

Ya gyaɗa kansa sannan ya ƙara da..

“Allah ya ƙara haƙuri.”

“Waye ya rasu?”

Yana sauke wayar Jidda ta tambaya. Ya juyo ya kalle ta sosai, ba tare da ya saki hanunta ba yace.

“Wa kika sani a cikin ƴaƴan Mai martaba?”

“Ban san kowa ba, Sadiya dai tana gaya min sunayensu ko kuma ta nuna min su idan ana wani taro.”

“Ta taba ce miki akwai wani Umar.” Muryarsa a hankali take fita yana kallonta.

A lokaci guda Jidda ta tuna wannan ranar da suka taɓa leƙawa b’angaren wani ɗan mai martaban da tace sunansa Umarul-Faruk, wanda tace mata yana ƙasar waje yana karatu ranar an buɗe wajen ne kawai ana share-share.

STORY CONTINUES BELOW

“Na san sunanshi… Ban taba ganin shi ba dai.”

Ya hadiye yawu a hankali har hakan ya motsa Adam’s apple dinsa sannan yace.

“Shine ya rasu, jiya, a can kasar da yake karatu.”

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un…. Allah ya jikansa, Allah ya gafarta masa.”

“Ameen.”

“Rashin lafiya yayi?”

“Sun ce Cancer ce ta kama shi.”

A hankali ta sake gyada kanta ta kara cewa Allah ya jikansa shima ya amsa da Amin. Sai kuma suka yi shiru ba wanda ya sake magana yana rike da ita har a lokacin, sai a sannan kuma Jidda ta fahimci dalilin da damuwarsa ta ɗazu da kuma wayar da yayi ta amsawa tun safe. Abinda har yanzu bata gane ba shine, shi qmeye matsayinsa ne a masarautar nan? Ta san kowa na masa kallon ɗan Mai martaba ne amma ita bata taba ganin wata alama a wajensa ta hakan ba, a yanzu ma me yace ne? ‘Ta san ƴaƴan Mai martaba?’

“Me kika dafa bayan dankali?”

Muryarsa ta sake sawa ta kalle shi, kafin ta sunkuya a hankali.

“Shi kadai na dafa, sai kayan tea a flask, amma ga abinci nan kala-kala su Aunty Khadija sun kawo.”

Yayi shiru kamar mai nazari sai kuma yace.

“Ki haɗa min tean.”

Sai ta zare hannunta sannan ta mike tsaye, a cikin kanta tana tunanin dalilin da yasa ne a yanzu yake kula ta haka, watakila don yana ganin tana tausayinsa ne.

“Idan zan tafi, in tafi da kayan abincin kenan?” Ta tambaya sanda ta sake dawowa ta miƙo masa kofin kakkauran tean data haɗa. Ya karɓi kofin.

“Ina zaki je?”

“Idan zan tafi gida.”

“Yaushe zaki tafi?”

“Idan Baba Saminun ya dawo.”

“Yace zai dawo ne?”

Sai ta ɗan tsaya tana nazari.

“Zaki iya kwana ke kadai ne a gidan?”

Tambaya ce mai ma’ana, wadda bata ma yi tunanin ta balle nazarinta, ba laifi ta san gidan na dan dan girmansa don haka dole zata ji tsoron kwana a cikinsa ita kaɗai, ranar da bashi da lafiyan nan ganinsa ne kawai bata yi ba amma ko bacci ta kasa, amma idan har bata koma ba anan zata kwana kenan?

Sai dai kafin ta sami amsarta ƙofar ɗakin ta buɗe, wasu Nurses biyu suka shigo da likita ɗaya, kowannensu da kayan aiki a hannunsa, sai tayi saurin matsawa kaɗan duk da wannan karon ba a kusa dashi take sosai ba.

“Jiki ya fara kyau kenan? Har ka sauko?” Cewar Namijin.

“Gashi kuma zamu ɗan ƙwace mata shi ba, don lokacin dressing ne yanzu.”

Cewar daya daga cikin Nurses ɗin.

Madaki yayi murmushi yana miƙawa Jidda kofin hannunsa kafin ya miƙe a hankali.

“Kar ka damu, nima ba zanyi musu ba ai ‘cus I need it.”

Suka yi murmushi bakiɗayansu.

“Sannu, ashe baban naki ne tsautsayi ya faru akansa.”

Cewar ɗaya Nurse din ta ƙarshe bayan sunyi gaba. Jidda ta ɗago ta kalle ta, a lokaci guda ta gane ta, tana ɗaya daga cikin waɗannan Nurses din nan na lab, saboda haka ta gyada kanta sannan tace.

“Eh wallahi, kuma Maman tawa bata nan ne shi yasa nake kula dashi. Mun gode.”5

Nurse ɗin ta juya kawai bayan ta fitar da wani ɗan siririn tsaki. Jidda ta bi ta da kallo sannan kuma idonta ya sauka a can kan gadon da Madaki ya koma ya kwanta, rigar asibitin mai maɓallai ce a gaba don haka namijin ya cire su gabaɗaya an buɗe ƙirjinsa suna ƙoƙarin fara aikinsu, sai tayi saurin dauke kanta saboda hakan wani abu ne da bata taɓa gani ba tsawon rayuwarta. Amma tsaya, don me ita zata juya bayan ga Nurses ɗin nan tsaye suna kalle shi? Su da basu haɗa ma komai ma dashi ba, saboda haka sai kawai tayi ƙarfin halin juyowa kofin tean nan riƙe a hannunta. Ai kuwa shima ita yake kallo, straightly ta tsakanin jikin Nurses din.1

STORY CONTINUES BELOW

Kallonta Madaki yake, cikin idanunta sosai kamar mai son binciko wani abun, kamar mai neman wani abu da yake tunanin cewa yana nan ciki, a sannan ne kuma namijin nan ya ɗage auduga da plaster dake rufe ciwon nasa baki ɗaya, sai yabi idanunta da kallo sanda ta kalli ciwon da kuma sanda ta sake dawowa ta kalli fuskarsa, sai ya girgiza mata kai a hankali alamun kar ta janye idanun nata, kamar roƙonta yake, kamar kallon nata shi zai sa ba zai ji zafin ciwon ba.2

Kuma haka kurum sai Jidda bata daina kallon nasa ba.

*

“Saura guda ɗaya…”

Muryarta ta faɗa bayan wani lokaci, bayan an gama dressing din, don har sai da idar da sallar isha’i ma sannan suka kammala, suka ajiye wasu magunguna da zummar cewa idan yaci abincin dare sai yasha su.

Wannan karon a zaune yayi sallar ishar saboda raɗaɗin da yace ciwon na masa sosai ba zai iya sunkuyawar sujjada da ruku’u ba, kuma teansa kawai ya karba ya shanye bai ce mata zai ci wani abincin ba don haka ta debo magungunan ta shiga bashi. Kuma daga yanayin yadda yake sha, sai taji dama ta bashi a lokacin da yake shan tean don watakila ruwa ya masa yawa ne.

“Ko za’a ajiye wannan sai anjima?”

Ta tambaya riƙe da maganin na ƙarshe. Sai ya girgiza kansa.

“Akwai maganin bacci a ciki, so ba lallai in kai anjiman idona biyu ba.”

Muryarsa ta fito baya kallonta, tana ganin yadda yake yamutsa fuska kaɗan alamun dannewa raɗaɗin ciwon da aka tabo kafin ya karbi ƙwayar maganin a hannunta, sai dai wannan karon maimaikon ta mika masa robar ruwan, sai kawai ta kaita daidai saitin bakinsa ta ɗago masa da ita, shima sai ya dora hannunsa na hagu akan yatsunta yana taya ta tallafewa.

A yanzu Jidda ta riga ta saba da hakan, don duk sanda ya rike tan, tana jin yatsun nasa kamar wani ciko ne da ya kamata dama ace akwai a hannun nata, kamar dama wajen bai taɓa zama complete ba sai da ya fara riƙe tan.

Bayan ya gama shan maganin, ta taimaka masa ya gyara kwanciyarsa sosai sannan ta isa wajen ƙofa ta rage hasken fitila daya a dakin, babu zancen komawarta gida ta sani don da gaske ne bai kamata ta tafi ta barshi shi kadai ba, sai a yanzu ma take ganin wautarta da ta tambayi tafiyar, ai baza ta taba samun kwanciyar hankalin bacci ita kaɗai a gidan nan ba ma.

Ta dawo ta ɗan saɓa murafan flask din abincin da su Khadija suka kawo don gudun lalacewa sannan ta ɗauko wani sabon katon bargo da wata matron ta kawo tun da yamma akan fridge sannan ta zagaya zuwa gefen gadon daidai saitin fuskarsa.

“Kana bukatar rufa?”

Muryarta ta tambaya a hankali tana kallon idanun nasa dake ƙoƙarin lumshewa, Jidda bata lissafa fa ba balle har ta hango sanda hannun nasa ya dago ya kamo nata, ta dai ji yatsunsa a cikin nata ne kawai kafin ya jata gabaɗaya ta tafi zuwa kan gadon, kanta ya sauka a gefen filonsa yayin da rabin jikinta ke cikin nasa ɓangaren da babu ciwon, gadon da take gani karami mai cin mutum daya sai gashi har da space a bayanta.

“Yes, ki rufe mu…”3

Muryarsa ta fito dab da kunnenta, dumin ta ya busa akan fatar ta, ya haddasa ƙarin rawar da zuciyarta ke yi, a hankali ta ciji saman lebbenta wajen ƙoƙarin saita kanta sannan ta ware bargon dake hannun nata ta shimfiɗa a jikinsu.

“Thank you.”

Madaki ya sake faɗa daga can kasan maƙogwaronsa, a wannan lokacin kwata-kwata bai damu da komai ba, so yake kawai ya fara aiwatar nufinsa na gyara alakar tasu don shi mutum ne mai tsari, kuma idan ya tsayar da zuciyarsa kan abu to babu wani abu dake sa shi ya canja, hakan wani sirri ne na nasarar kasuwancinsa dama dukkan rayuwarsa bakidaya, don haka bai damu da dukkan tunanin da Jidda zata yi a lokacin ba, so yake yama yi nasarar goge duk wani hasashen nata ya saka mata wani sabon tunani na yadda yake son rayuwarsu ta tafi tare daga yanzu.

STORY CONTINUES BELOW

Yana jin yadda take motsi a gefen nasa kamar mai son gyara kwanciyar tata, kamar kuma ta rasa yadda zata kwanta ɗin, a ƙasan bargon yasa hannunsa ɗaya ya riƙo nata, wani abu da yasa tayi saurin ɗago da idanunta ta kalle shi, shima ita yake kallo, don haka yaga sanda maƙogwaronta ya motsa kamar ta haɗiye wani abu kafin ta sake sadda idonta ƙasa.

Bai san me take tunanin ba amma dai ko meye ɗin, ya hango cewa bata da niyyar bijire masa a cikin idanunta, bata da niyyar challenging ɗinsa. Shiru ya wuce tsawon wani lokaci babu wanda yace wani abu amma zuciyoyin kowannensu da abinda take tunanin. Zuwa can kawai sai yaji muryarta tayi magana.

“Zan iya tambayarka wani abu?”

Sauyin ya fito a hankali kamar tana tsoron in tayi maganar da karfi zata fama masa ciwon ne, sai yayi motsi da yatsunsa a cikin nata kafin muryarsa ta fito very low shima.

“Ina jinki…”

“Umar ƙanin ka ne?”

Tambayar ta shammace shi don bai taba tunaninta a yanzu ba, amma sai hakan ya haska masa wani bangare na tunanin da zuciyarta ke yi akansa, tana son ta san wanene shi ne, tana son aƙalla ta san wani abu nasa don daga yadda tayi tambayar har cikin zuciyarta ne ya san bata sani ɗin ba, zuciyarsa ta ƙara yarda cewa ita ba yarinyar Fulani bace, bata san komai akansa ba.

Kuma idan ta tambaya din a yanzu ba laifi tayi ba, shi ya riga ya san duk wani bayani karami da babba akanta, ita kuwa da alama bata san WAYE SHI ba, kawai ta daurewa zuciyarta ne tana rayuwa da shi din da akace mijinta ne kawai. A hankali ya cigaba da wasa da hannunsa a cikin nata sannan muryarsa ta fito.

“Farouq dan Mai martaba da Fulani ne, amma bana jin zan iya kiransa da kanina.”

“Saboda me?”

“Saboda ni ba ɗan Mai martaba bane…”

Kafin tayi wani yunƙuri ya cigaba.

“Sarki ya tsince ni ne a lokacin da ban fi shekaru huɗu ba, a can state ɗin Yola wajen aikinsa, tun daga lokacin ya rike ni kamar dansa har zuwa yanzu, shi yasa mutane da yawa ke tunanin nine babban ɗansa ba Saifudeen ba.”

Yana iya hango tsananin mamaki da kuma wani abu daban a lokacin da ta dago da idonta ta kalle shi cikin hasken ɗakin mai rangwame.

“Su waye iyayenka to? Baka koma wajensu ba?”

Wani abu kamar murmushi yayi playing akan leɓɓensa.

“Ta yaya zan koma wajensu? Ban taba saninsu ba, ban taba samun wani abu da zai danganta ni dasu ba, a lokacin da Sarki ya tsince ni ko hausa bana ji kuma ban san sunan yare na ba, ban san ma wa na gani na karshe kafin ɓata na ba.”

Kallonta yake yayin da idanunta ke haskawa da dimbin abubuwan da zai so ta fassara masa su kafin ta mai da idanun nata ƙasa a hankali.

Dubunnan tunani ne ke faruwa akan Jidda wannan lokacin, ta san dama shi ba dan Fulani bane tun farko shi yasa take ƙoƙarin cutar dashi ta hanyoyi kala-kala, amma bata taba sanin cewa shi ba dan Mai martaba bane sai yanzu, ashe shi yasa ƙiyayyar tasa tayi yawa a zuciyarta? Ganin cewa Sarkin baya banbanta shi da ƴaƴan ta? Shi yasa har take binne asiri kala-kala a cikin kansa? Zata so kwarai ace zai san da hakan don duk rashin hankalinta ta san dai bai dace a wannan yanayin ta bude baki tace masa ta taba tone asiri akansa ba, dama yaya lafiyar kura balle..? Yaushe ya daina nuna alamun zargin ta yake akan abinda bata sanshi ba.

Tunaninta ya ganganra kan abinda ya gaya mata, bai taba sani  iyayensa ba, kenan haka yayi rayuwarsa tun daga lokacin yarinta har yanzu babu wanda zai taba kalla ya kira danginsa? Haka ya taso babu mai uwa mai gaya masa daidai da akasinsa? Babu mai sanin kukansa idan abubuwa sun cakuɗe a rayuwarsa? ta tabbata akwai ɗimbin labari akan rayuwarsa ta yadda ya kawo har zuwa yanzu amma sai ta kasa kara tambayarsa komai saboda wani irin abu yake zanawa a hankali cikin hannunta, wani irin abu mai wargaza dukkan tunanin data fara…

STORY CONTINUES BELOW

“Me kike sawa hannunki?” Muryarsa a hankali ta sake fitowa cikin tambayar da bata taba tsammaninta ba, sai ta dago da idanunta ta kalle shi da ɗan sauri.

“Babu komai… Me yayi?”

“Ba kya aiki da yawa a gida?” Shima yayi mata tambayar maimakon amsa. Sai ta girgiza kanta, hancinta ya gogu da saman kafaɗarsa.

“Ina aiki sosai mana.”

“Kamar me?”

“Ɗebo ruwa, shara, wanke-wanke, wanki, girki da daka, sau da yawa har geron kunu ma ina sirfawa Baddo a turmi.”

“Ke ɗin?”

Ta daga kanta alamun tabbatarwa, sannan muryarta ta fito free, alamun ta fara sakewa da yanayin nasu.

“Sosai ma, ka zata bani da ƙarfi? To har bokitin ruwa nata taba kaiwa saman bene kuma akaina.”

Madaki yayi murmushi mai dan fadi, yana mamakin irin innocense ɗinta, kafin a hankali yace.

“May be zan gwada ƙarfin naki kenan watarana.”6

Bata fahimci komai a maganar tasa ba saboda haka ta gyaɗa kanta tace.

“Allah ya kaimu, ka fada min me hannun nawa yayi?”

Ya kifta idanunsa yana kallon idanunta, wannan waɗannan idanun da suka bashi dukkan wahalar da suka ga dama a kwanakin baya wajen mannewa a tunaninsa.

“Yana da laushi sosai, so soft!”

Sai tayi wani guntun murmushi sannan tayi saurin sadda ganinta ƙasa ba tare da tace komai ba. A lokacin ne kuma Madaki yayi ƙoƙarin daurewa raɗaɗin ciwon dake harbawa a gefen kafaɗarsa, ya ture komai a cikin kansa ya sunkuyo daidai kanta ya lalubi saman kunnenta. Jidda taji saukar ɗumin numfashinsa a fuskarta yayin da tunaninta yayi cilli can wata duniya daban! Ruɗani da kasala suka ƙara mamaye jikinta sannan wani abu kamar kunya ya lullubeta tun daga ƙasa har sama… Sautin bugun zuciyarta na fita da wani irin ƙarfi data tabbata ko na tsaye a gefen gadon zai ji shi balle shi kuma…

A hankali ya raɗa a cikin kunnen nata tambayar data kara girgiza duniyarta fiye da halin da take ciki.

“Kin shirya zuwa Kiyari jibi?”

***

Kiyari, Expressway.

09:05Pm.

Motar gudu take cikin wani irin saurin da kyakkyawar macen dake zaune a baya take ganin kamar ta buɗe baki tace da direban yafi haka ma, ko kuma tasa hannu ta kara tunkuɗa su don su isa ga cikin garin da wuri har zuwa cikin masarauta.

Wayar dake yashe akan cinyarta tayi kara cikin mode ɗin vibration wanda ya shiga gurzawa akan stones din hadaɗɗen lace ɗin dake jikinta, ta dago ta ta kara a kunnenta ba tare da ta damu da maida hankali kan sunan mai kiran ba don ta riga ta san waye.

“Mama mun yini lafiya?”

“Lafiya kalau.” Daga cikin wayar muryar wata dattijuwar mace ta amsa.

“Kina ina ne Nadiya?” Matar ta sake tambaya.

“Ina hanya, mun sauka daga jirgi a kano dazu, yanzu haka mun kusa ƙarasawa cikin gari.”

Kai tsaye itama Nadiyan muryarta ta fito tana kallon kyakkyawar ƴarta fara tas! Dake bacci akan cinyarta, Ta riga ta san abinda zai biyo baya kenan dama, tun a safiyar yau data wayi gari da labarin rasuwar ɗanuwanta, Umar, da kuma rashin lafiyar da akace mahaifiyarta na ciki.

Kai tsaye ta shaidawa mijin nata Abdallah bayanin kiran wayar da ƴaruwarta Safina tayi mata, amma budar bakinsa bayan yace Allah ya jikansa, cewa yayi ta jira zuwa jibi idan anyi luncheon din sabon branch na kamfanin sai da motocinsa anan cikin Abujan da suke sai su taho tare. Kuma hakan ba wai abin mamaki bane dama a yanayin zamansu, don tun daga zamanin amarcinta take shan takaici kala-kala na halin Abdallah, tun a wancan lokacin kuma take dana sanin auren nasa, dana sanin burin data dorawa kanta na cewar sai kyakkyawan saurayi mai aji da kudi sannan zata aura, kyakkyawan da fuskarsa zata dace da tata, wanda in sunyi kwalliya sun dauki hoto zai zaga dukkan social media musamman ace kuma da ƴaƴansu a gefe..

STORY CONTINUES BELOW

Kuma sai gashi ta sami abinda take so ɗin don Abdallah dan wani shahararren minister ne da mahaifiyarsa ta kasance Shuwa-Arab, daga lokacin da yaga hotonta a social media yasa aka nemo masa contact dinta, sai ta tattara dukkan wadanda take kulawa tasa a shara, kuma da asiri da kissa da komai ita da mahaifiyarta Fulani suka samu suka ribace shi har akayi auren, wanda ko shekara guda ba’ayi ba ta fahimci cewa ta tafka babban kuskure.

Don Abdallah irin ƴaƴan masu kudin nan ne da aure bai taba hana su dukkan wani shashanci da watsewar da suka tashi dashi a rayuwarsu ba, ga babban kalubalen da take fuskanta na mahaifiyarsa, irin Shuwa-Arab din nan ne masu ci da asiri suma, don kamar yadda ta mallake mahaifinsa sai abinda tace to haka ƴaƴan ta ma da matayensu babu mai tsallaka umarninta, haka take yi tun akan matan yayyen Abdallah har zuwa ita ɗin da ta shigo, duk abinda ake ciki a gidan wani sai ta sani, hatta sirrin auratayya wannan a wajensu ba komai bane su kwashe su gaya mata, ga sauran ƙannensa mata basu da tarbiyya balle mutunci. Haka ita da kowacce a cikin matan nan ke fama dasu tunda sun rufe idonsu sunce sun ji sun gani kudi da kyau suke muradi.

A fuska dai da zahiri zaka gansu tsaf cikin kogin daula, musamman ace sun dauki hoto sun saka a yanar gizo, yanzu zaka ga tarin masu sharhi da fatan samun irin rayuwarsu, amma a cikin zuciya dubunnan talakawa da masu rufin asiri da yawa sun fi su samun nutsuwa da kuma kwaciyar hankali.

To a yanzu ma abinda ke faruwa kenan, ta tabbata Abdallan ne yaje ya gaya mata cewar ta taho ba tare da ta saurare shi ba.

“Kin san cewa ƴan jaridu da masu mujallu, zasu wajen buɗe kamfanin nan kuma za’a so ganin hotonku ke da Hidaya amma shine kika tsallake kafa kika tafi bayan yace miki ki zauna zaku je tare?”

Mahaifiyar tasa ta fada cikin banbamin faɗa.

Nadiya ta hade siraran girarta waje guda.

“Mama danuwana ne fa ya mutu? Har sai in zauna jiran sai an bude wani kamfani?”

“To don ya mutu an kawo gawar tasa ƙasar ne? Ba sai ki jira sai an kawo gawar tasa ba kafin nan kuma kun gama abinda zaku yi?”

Baƙin ciki ya cike har wuyanta, ta ma rasa me zata ce akan hakan sai kawai ta canja zancen da cewar.

“Mahaifiyata ma bata da lafiya ai.”

“Ko a gadon asibiti take yi wannan zancen mijinki ne muke yi Nadiya, bai baki izini ki fita ba kin sa kafa ki fice, alhali in kin jira shi sai jibin babu abinda zai faru?”

“Akan wani kamfani Mama zan zauna uwata bata da lafiya banje na ganta ba? Idan itama ta mutu kuma fa? Shikenan sai in…”

“Eh ai kinyi kauri dole ki zaɓa kuma ki aibata masa sana’a Nadiya…” Ta katse ta.

“… kinci kin koshi kina ganin kin fara ajiye magada ko? To bari kiji in gaya miki kar nake kallon kowa wallahi, ba’a min wata muna-muna wallahi, kuma dama na dade fahimtar mugun manufarki ke da uwar taki, kyale ku kawai nake yi amma duk shirinku a banza ne, ba zan bari ina ji ina gani ki halaka min ɗa ba, don haka in kinje kar ki dawo, kije ki zauna da mahaifiyar taki zan saka ya aiko miki da takardarki kowa ya huta.”

Dib! Kiran ya katse, wata ƙatuwa ƙwalla mai dumi ta gangaro kan fuskar Nadiya, ta gangaro ta ziraro har ta sauka akan yala-yalan gashi ƴarta, bata san kuma kwallar ta mecece ba don ta san in da zata kira Abdallan da ta tabbata yana kusa da ita a yanzu ta bashi hakuri, tsaf zaiyi kokarin shawo kan mahaifiyar tasa ko don Hidaya ƴarsu don yana mutukar son yarinyar sosai, amma ba zata yin ba, zata barsu su aiko da tarkardar sakin, watakila lokaci yayi da ya kamata ta saukewa kanta wannan ƙaddararren auren itama ta huta kamar yadda ta faɗa.

Basu isa cikin masarauta ba sai wajen ƙarfe tara sosai, a lokacin motocin masarautar sakkwato sun cika fal a harabar ajiyar motocin gidan alamun kanwarta Aisha da tayi aure a can ta iso kenan, a lokaci taji wani abu kamar kunya da takiaici sun ratsa zuciyarta, haka ita zata shiga ziƙau! Daga ita sai ƴar ta, don ko a baya ma babu wani daga dangin Abdallah da ya taba tako ƙafarsa mahaifarta balle a yanzu.

STORY CONTINUES BELOW

Kafin ta isa bangaren Fulanin dogarawa sun rufe bayanta ana tayi mata bangajiya da kuma gaisuwar mutuwar, wani abu da ya ɗan wanke duhun zuciyarta ta dan ji ta sakayau, aka tuna mata cewa itama mutum ce mai daraja ba a wani waje da ko mota tafi ta daraja ba.

Ta isa cikin ɓangaren inda ya fara cika da mutane daban-daban wanda yawanci duk dangin mahaifiyar tata ne, a falo na uku dangin mijin Aisha ne ƴan sawkwato, a can falo na ƙarshe ne kuma ta tadda makusantan Fulani sosai irin ƙannenta da yayyenta, dukkansu ta gaishe sannan suka yiwa juna gaisuwa da kuma addu’ar nemawa Fulanin sauki, wani ciwo da har yanzu ita Nadiyan bata sanshi ba. Daga nan ta miƙe tayi hanyar ɗakin ƙanwarta Safina, inda akace Aisha ma na can don tayi sallah ta huta, tunda ance ita Fulanin tasha allurorin bacci har yanzu bata farka ba.

Tana bude ƙofar ɗakin, fuskokin ƴanuwanta biyu suka yi mata maraba, sai da ba’a halin farin ciki ba, dukkaninsu sunyi zuru-zuru, Safina ma idanunta a kumbure alamun tasha kuka. Sai kuma ta taso da sauri ta karɓi Hidayan da ta sake komawa bacci a kafaɗunta.

“Sannu da zuwa Adda, ya hanya?” Kusan a tare suka gaishe ta.

Da kyar ta iya amsawa saboda yadda take jin muryarta kamar ta shake sannan suka yiwa junansu ta’aziyya da kuma jajen abinda ya faru.

Kafin ta fito daga wanka a toilet din Safinan an kawo mata katon akwatin kayanta, sannan kuma an wadata su da abincin tarba kala-kala, sai da ta idar daga sallah bayan ta canja kaya ne sannan idonta ya iya kallon Aisha sosai, a lokacin Safinan ta fita don raka wasu kawayenta da suka zo yi mata ta’aziyya.

“Ishsh me ya same ki ne wai? Abinda ya faru ne yasa kika yi wannan ramar ko kuwa? Idanunki sun fada sosai.”

Aisha ta dago ta kalle ta daga kwancen da take sai kuma ta girgiza kanta.

“Babu komai Adda, ba muna waya ba? Na taba gaya miki wani abu ne? I’m fine.”

“I don’t buy that..” cewar Nadiyan.

“Idan a waya ne na yarda, amma banda yanzu da idona suke ganinki, da haka kike? Ko ba kya kallon fuskar ki ne a mudubi? Har baki fa kinyi.”

Sai ta taso ta zauna a gefen gadon ta take kwance ta kamo hannunta tace.

“Ishsh, ni fa ƴaruwarki ce, yayarki guda daya a duniya, akwai wanda ya kamata ki gayawa damuwarki ne bayan ni? Bayan yanzu kina ganin Mama ma a kwance take.”

A lokacin sai duk wata dauriya da Aishan ke yi ta kwance, tulin abubuwan da ta dade tana dannewa a kirjinta suka wargaje, sai kawai ta fashe da kuka, wani irin kuka dake tasowa tun daga kasan zuciyarta.

“Adda dlwallahi bana jin daɗin auren nan, har dukana yake…”

“Subhanallah, shi Muhammad din?”

Cikin kuka Aisha ta sake daga kanta.

“Wallahi Adda tunda aka kai ni ban taba jin wani dadi ba, duk abinda nayi sai ya hantare ni yace wai siyar masa dani akayi saboda iyayena na son kudi, har su Daddy zaginsu yake, daga baya kuma sai ya fara dukana, Adda wallahi har fin ƙarfi yake min.”

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un…” Cewar Nadiyan.

Me ke faruwa a rayuwarsu ne? Me suka jawowa kansu ne? Wannan wane irin bala’i ne? Ace ita bata yi sa’ar aure ba sannan ga Aisha ma? Ba gwara ma nata an ɗauki shekaru ba? Amma Aisha duka-duka watanta nawa?

“Ƴanuwansa suna da kirki, danginsa gabadaya suna mutunta ni, shine kawai daban Adda, kuma wallahi babu wanda zan tunkara a masarautar nan in gaya masa ya yarda. Munyi maganar da Mama kwanaki sai tace min wai zamu je wajen wani malami komai zai wuce, ni kuma bana son harkar bin wasu malamai shi yasa na daina gaya mata. Na daina gayawa kowa.”

Kafin Nadiya tayi magana, Hidaya ta tashi cikin ɗan kuka tana mutstsika idonta, don haka Aishan tayi saurin miƙewa ta ɗauke ta. Tana buɗe ido kuwa tace fitsari zata yi don haka tayi bandaki da ita, Nadiya tabi bayansu da kallo wani abu na ƙullewa a cikin ƙirjinta. A lokacin ne kofar ɗakin ta bude, Safina ta dawo. Ta shigo ta zauna a gefen gadon tana fadin.

“Adda baki ci abincin ba, kun sha hanya fa.”

Ta girgiza mata kai.

“Bar abincin nan kawai Safina, gaya min taƙamaimai me ya sami Mama wai?”

Safina ta dan yi ajiyar zuciya kafin tace.

“Tun jiya da daddare ne da aka kawo gawar Jakadiya Babba cewar sunyi hatsari wa ita da Sani direba a mota, ance dai Sanin bai mutu ba amma wallahi Adda ita baki ganta ba, gawar duk ta daddatse haka, ni ban ma iya kallonta sosai ba bayan na dawo, saboda na fita ne, to shigowata ne su Jakadiyan soro suke gaya min wai Mama tana ta wasu surutai bayan taga gawar, tana rantsewa wai ba Jakadiyan bace ita ta san Jakadiya bata mutu ba.

Da na shiga na same ta an riƙe ta tana ta rantse-rantsen cewa wai wallahi Yaya Farouq ma bai mutu ba haka ma jakadiyan, wai ita ta san tana nasara a komai kuma malamanta basu taɓa nuna mata wannan ranar ba. Adda maganganun da take fada wallahi ba zaki ce a hankalinta take ba, ina ta rokonta tayi shiru amma bata daina ba. Daga baya sai ta sarƙe a maganarta shikenan ta fara tari, sai kuma jini ya shiga fitowa, da yawa tana ta zubar dashi akan carpet.

Yaya Saif ne ya kira likita yazo wajen ɗayan dare ya mata allurar bacci don yace shi bai san me ya same ta ba. Dazu da safe aka binne gawar Jakadiyan, sannan wasu likitocin kuma suka ƙara zuwa suja duba Maman, ni dai ban tabbatar ba amma naji kamar ɗayan yace wai kwaƙwarta ce ta dan taɓu, shi yasa hankalina ya kara tashi, don ban san ya za’ayi jibi ba in aka kawo gawar Yaya Farouk.”

“Mama haukacewa tayi fa.”3

Kai tsaye muryar Aisha ta fito daga bayansu a lokacin da Safina ta rufe bakinta.

***

Lagos.

Gidan Mubarak.

10:15Pm.

“Ya Allah! Na manta.”

Cewar Khadija a lokacin da take ƙoƙarin hawowa kan gadon baccinsu bayan ta canja cikin kayan bacci.

“Me ya faru, Mubarak ya tambaya daga kwance yana danna Tab a hannunsa.

“Ban buɗe windon ɗakin su Hanan ba wallahi, tun da safe da zamu je asibiti dana rufe.”

Ta fada tana ƙoƙarin miƙewa, sai yayi saurin kamo hannunta.

“Dawo ki zauna, kin gaji, bari inje.”

Tayi murmushi mai fadi.

“Awwn nagode sosai King, A dawo lafiya.”

Ta faɗa tana komawa da baya ta fada cikin laushin gadon. Mubarak ya ajiye tab ɗinsa yana dariya sannan yayi hanyar kofa, ya fito daga ɗakin ya biyo hanyar korido zuwa wani koridon da zai kaishi ga hanyar ɗakin yaran, har ya wuce ƙofar wani toilet a farko sai kuma yaga ƙofarsa slightly a buɗe, saboda ya dawo da niyyar jawo ta ya rufe a lokacin da maganganun dake fitowa daga cikin suka shiga kunnensa.

“Kar ki damu Naja, ai ni na raina komai yanzu, da ace ma naga yarinyar tun farko me zai sa mu hayo ƴan bindingar nan har a sami wannan akasin?”3

Muryar ta kyalkyale da dariya cikin wayar da take yi sannan tayi magana ta gaba.

“Wallahi Naja, abinda nake shirin yi ko wani ƙaramin shaidan sai ya faɗa tarkona balle kuma wani Madaki, ai ki bari kawai ni naga abinda na gani, don haka dole ne in mallaki gayen nan ko me za’ayi wallahi, wallahi!”3

Muryar Salwa tar! Ta rantse ta kuma rantsewa a cikin kunnen Mubarak!13

***Mubarak yasa hannunsa ya tura ƙofar banɗakin a hankali, katakon ƙofar ya bada wata ƙara ta katako irin ƙiiiii ɗin nan, ƙarar da ta shiga kunnen Salwa tasa ta juyo da wani irin sauri mai haɗe da fargabar data haska tar a cikin idonta.1

A lokaci guda kuwa wayar hannunta ta sulale ta daki dandaryar tiles ɗin banɗakin, ta rikice kuma diririce tana kallon Mubarak ɗin da nasa idon da ke haskawa da wani irin ɓacin ran daya haddasa kalarsu canjawa.1

Tasa hannu ta dafe gefen sink ɗin tana jin kamar zata fadi sai kuma ta sake shi ta shiga takawa baya a hankali tana cigaba da kallonsa haɗe da girgiza kai cikin amsar da ba’a tambayeta ba. Mubarak ya haɗe hannayensa biyu yayin da yake kallonta da idanunsa da a yanzu suka rikiɗe suka kaɗa jazur!

“Wane Madakin kike cewa zaki mallaka?”

“Yaya… Ba wai ni bace, kawai… Kawai tunani nayi…”

“Cewa nayi dan ub*nki wane Madaki kike cewa zaki mallaka?”

Sai da ta zabura saboda yadda ƙarar tsawar daya daka ta karaɗe bangwayen toilet ɗin. Ta cigaba da girgiza kanta hannayenta na rawa, saboda Allah ya sani tunda take a rayuwarta baza ta taba cewa ta taba sanin wannan kalar ta Mubarak ba, a kullum shi wanta ne mai fahimta da kuma yi mata uzuri a lokacin da kowa kr ƙalubalantarta, amma a yanzu fuskarsa tamkar na wani zaki ne dake shirin yunƙurowa ya keta ta…

“Ke kika sa aka harbe shi?”

Wannan karon muryarsa na karkarwa alamun tsananin ɓacin ran da yake son daurewa. Salwa ta cigaba da girgiza kanta tana ƙara yin baya har sai da ta dangana da bangon karshe.

“Wallahi tallahi Yaya ƙawata ce tace…” Sai kuma ƙaryar ma ta ruguje ta rasa me zata kamo ta fada.1

A lokacin ne Khadija ta ƙaraso cikin wani irin sauri hannunta damƙe da da tsakiyar top ɗin data ɗora akan siririyar rigar baccinta, ƙarar tsawar da Mubarak ya daka ce ta fito da ita ba shiri a firgice.

“Me ya faru Daddy? Me nene?…”

Ta tambaya a ruɗe tana kallon yanayin Mubarak ɗin da ita kanta bata taba gani ba tsawon zamansu. Sai kuma ta juya cikin banɗakin ta kalli Salwa da jikinta ke faman faman karkarwa cike da tsananin tsoron dake haskawa a idanunta.

“Wallahi Yaya, wallahi tallahi… Na rantse ka saurare ni, ka tsaya, ka tsaya, ka tsaya kaji…”

Cewar Salwan cikin ihu a lokacin da Mubarak yayo cikin toilet din, wayarta data fadi a kasa ya tsugunna ya ɗauka sannan hannayensa biyu ya ɓalla ta gida biyu da wani irin ƙarfi ta tsakiya.

Har a lokacin Salwan ihu take tana roƙonsa cewa ya tsaya zata masa bayanin komai.

“Mubarak me nene wai? Me tayi? Dan Allah ka saurara tunda tace ka tsaya…”

Mubarak bai saurari Salwan ba balle Khadija, ya ƙarasa ya damƙo hannayenta duka biyu a lokacin da ta ƙara rikicewa ta shiga ƙoƙarin tirjewa tana ƙara roƙonsa amma karfinta da nasa ba daya bane, ya jawo ta yana mai ture Khadija dake tsaye a kofa tana ƙoƙarin riƙe shi gefe sannan ya cigaba da jan ta suka fita daga toilet ɗin.

“Yaya dan girman Allah kayi hakuri, ka tsaya kaji, wallahi ban san shi zasu harba ba…”4

Roƙonsa take yi tana magiya yayin da take juyawa tana kallon Khadija dake bin bayansu kamar mai neman taimako, suka isa har falo kuma anan din ma bai tsaya ba, gadan-gadan ya nufi hanyar ƙofa da ita bayan ya suri wasu tarin muƙullai da suka haɗa har da na motarsa akan dan center table ɗin dake falon.

“Mubarak ina zaka kaita? Fita zaka yi? Ƙarfe goma fa ta wuce… Ina zaka je a daren nan…?”

Khadija.

STORY CONTINUES BELOW

“Dan girman Allah Yaya… don darajar Allah ka tsaya, ka saurare ni… Wallahi tallahi ba shi nace su harba ba… Yaya…”

Salwa.

Mubarak ya buɗe ƙofar gidan yana mai cigaba da jan Salwa wadda ke sanye da doguwar riga ta atamfa da kuma ɗaurin baƙin mayafi akanta, yana jin yadda take cigaba da ƙoƙarin tirjewa tana ƙoƙarin zubewa a ƙasa amma yasa dukkan ƙarfinsa ya hana ta, zuciyarsa ta riga ta kai bango kuma idanunsa sun rufe in banda wani baƙin hayaki da baƙin tiriri ba abinda yake gani a idanunsa kuma yake ji a cikin ƙirjinsa.1

Daga shi har ita babu mai takalmi a cikinsu ya buɗe motarsa bayan ya zube sauran muƙullan a ƙasa, Khadija ta biyo su har jikin motar tana ƙara roƙonsa da bashi hakuri akan taƙamaimai abinda bata sani ba, amma bayan ya buɗe gidan gaba ya tura Salwan da ta shiga da ƙyar kallonta kawai itama yayi tasha jinin jikinta musamman da ta tuna kayan dake jikinta, ta koma can kan porch ɗin falon da sauri tana cigaba da kallonsu a rikice, Mubarak ya zagayo ya buɗe motar ya shige yayin da a lokacin Aliyu daya farka ya fito shima, cike da nasa mamakin shima ya tsaya kusa da mahaifiyarsa yana kallon yadda motar ta tashi da wani irin sauri ta nufi gate inda maigadi ke ƙoƙarin buɗewa.

A cikin motar ba abinda ya canja, Salwa magiya take yi tana cigaba da roƙar Mubarak ɗin da baya ko jinta, idanunsa jazur na manne akan titi yayin da huci ke faman fita daga hancinsa, tun tana zaune a kujerar har sai da ta tsugunna a ƙasa tana cewa.

“Yaya don darajar ma’aikin Allah ka saurare ni, wallahi ba shi nace a harba ba, mistake suka yi, nima ba zan taɓa so in yi wani abu da zai taba shi ba, kuma abinda kaji ina cewa ba akansa zanyi ba…”

Ina! Mubarak baya ko jinta, tituna kawai yake ratsawa yana bi ta tsakanin motocin da fitilar danjarsu ke ƙara ƙawata nasa jan idon. Kuma duk tarin magiyar da Salwa ke yi, babu ko ɗigon kwalla a idanunta, tunaninta ne kawai ya rikice amma karfin ruɗanin nata bai kai ga fitar hawaye ba sai a lokacin da ta ji tayoyin motar sun ja birki alamun an iso inda ƙaddarar da take shirin fuskanta take, a lokacin da idanun ta suka juya da wani irin sauri yayin da ta dafo saman dashboard ɗin gabanta ta ɗago daga tsugunnen da take, a lokacin da duk da ƙarancin haske a harabar wajen idanun nata suka gane mata kalar fentin ginin dake gabansu.

Yellow.

Blue.

Green.

Police station!5

***

09:00 AM

Voilá Private Hosital, No 1388 Gyari Park.

Jidda ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin a hankali da niyyar shiga, a hannunta wannan basket ɗin ne mai kyau da su Khadija suka kawo da kwanuka a ciki. Jiya duk da ta saɓa murafan sai da wasu daga cikin abincin suka ɗan canja ƙamshi saboda haka yanzu ta tattara su ta kaiwa masu gadi a can bakin gate, suna ta godiya kuwa suka karba, itama har sai da yawunta ya tsinke a lokacin da suke juye wani farfesun nama cikin kwanukansu, amma ya zata yi ne, Madaki ya riga yace shi ba zai ci ba don haka kawai itama sai taji ɗan shakkar ci tunda dama tun farko ba ita aka kawowa ba.2

A lokacin da ta fita kuma baya ɗakin, don tun ƙarfe takwas da ƴan mintuna da aka gama masa dressing ɗin safe, yabi Nurses din da cewar zai je wajen likitan da file ɗin da ke hannunsa don su tattauna wani abun, wani abun da take ganin kamar akan zancen tafiya Kiyari ne kamar yadda ya faɗa mata jiya, ya faɗa a kunnenta…

Wani abu da har yanzu ta kasa ganewa kenan, ta kasa gane yana nufin zai maida ita ne gaba ɗaya in sun je a can zai rabu da ita shi ya dawo ko kuwa? Don da alama ya gama a yanzu ya kammala zargin da yake akanta, kuma duk da ta san dai saboda rasuwar yayi zancen tafiyar amma bata sani ba ko zaiyi amfani da damar ne ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.

STORY CONTINUES BELOW

Taso tayi masa wannan tambayar Tun jiya amma ƙiri-ƙiri ta kasa, bata taɓa sanin cewa a duniya akwai wani abu da zai sa bakinta ya mutu ba sai jiyan, wannan lokacin da babu abinda take iya ji a hancinta sai ƙamshinsa, wani ƙamshin turare mai sanyi daya haɗu dana fatarsa ya cika kanta, sannan ɗumin jikinsa kuma kusan gabaɗaya ya zagaye nata saboda yadda ya sunkuyo da fuskarsa daidai kunnenta, tata fuskar ta shige cikin wuyansa.3

Bata taɓa jin wani abu irin haka ba, zuciyarta ta rabu gida biyu a lokacin, tana jin kamar ta kara matsawa ta shige jikin nasa tana kuma jin kamar ta janye ta bar gadon ma bakiɗaya, data rasa me zata yi sai kawai ta haɗe nata jikin waje ɗaya, ta dunƙule hannunta akan ƙirjinta, na ƙafa kuma ta dunƙule su a cikin tafin ƙafar ta. Kuma babu wanda ya sake magana a cikinsu har sanda ya janye fuskarsa ba tare da ya sake tambayar amsarta ba, kuma a haka daren ya wanzu zuwa sanda bacci ya ɗauke su, hannunsa riƙe da nata cikin bargon nan har aka ƙwalla kiran sallar asuba…

“Zuwa nan da 12 insha Allah komai zai zama ready, bari in tafi da waɗannan.”

Muryar wannan Nurse ɗin Namiji ta shiga kunnen Jidda a lokacin da ta tura ƙofar ɗakin ta shiga ciki. Yana tsaye a gefen gadon rike da wasu takardu da kuma dan tray ɗin dake ɗauke da magunguna yayin da Madakin ke zaune daga gefe ya zuro ƙafafunsa ƙasa da alamun magana suke yi har yanzu, don Nurse ɗin shi ya raka shi gurin likitan da yace za shi ɗazu.

“Bari inje, zuwa 12 ɗin idan ya shigo I’ll contact you as soon as possible insha Allah.”

Cewar Nurse ɗin yana mai tahowa wajen ƙofar inda Jiddan ke tsaye, sai da yazo dab da ita sannan tace ‘Sannu da aiki’ ya amsa da ‘Yawwa’ har da ɗan guntun murmushi sannan ya fita.

Tana juyowa idanunta suka haɗe dana Madaki dake kallonta daga inda yake zaune, Ya ilahy! Idanun nasa a lumshe suke har yanzu kamar maganin baccin nan bai gama sakinsa ba, babu shiri wani abu ya zarce maƙogwaronta a lokacin da ya ɗago hannunsa ya miƙo saitinta alamun tazo.

Babu yadda zata yi, in tace ba zata ba ma zuciyarta ba zata barta ba, saboda haka ta ƙarasa a hankali basket ɗin nan riƙe a hannunta, ai kuwa kamar lokutan baya tana zuwa daidai tsawon hannun nasa ya naɗe yatsunsu waje daya sannan ya jawo ta dab dashi sosai.

“Kin tashi lafiya?”

Sun gaisa fa, ɗazu kafin ya fita, sakewa zasu yi? Ta ayyana hakan a zuciyarta kuma maimakon ta amsa sai itama tace.

“Yaya jikin naka?”

“Alhmdlilah, da sauƙi sosai.”

A can ƙasar maƙoshinsa zancen ya fito, Adam’s apple ɗin sa na motsawa sama da ƙasa a hankali, sai ya kalli basket ɗin hannunta sannan yace.

“Har wanke plates ɗin suka miki?”

Ta girgiza kanta, haka yasa yaji ratsawar numfashinta akan fuskarsa.

“A’a ni na wanke da kaina, a wani fanfo anan baya.”

Fanfon dai da aka hana ta alwala jiya, kuma tana sane yau ma ta koma, da zummar duk wanda ya mata magana tace ai kuɗi suka biya ba kyauta suke zaune a asibitin ba kuma ruwa ma ai dukiyar Manzon Allah ce don haka fanfon bana kowa bane. Sai gashi har ta gama ta fito Allah bai kawo mai tanka mata ba.2

Madaki ya gyada kansa yana motsa yatsunsa cikin nata kamar mai son ɗauko wani abun kafin ya sake magana.

“Me zamu ci kenan mu?”

Tamabayar ta rungume zuciyarta amma sai tayi ƙoƙarin ture ta, ta sake haɗiye yawu a bakinta sannan ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba tace.

“Idan ka kira Baba Saminun ya kaini gida sai in dafo maka duk abinda kake so qarfin.”

STORY CONTINUES BELOW

Sai ya girgiza kansa shima.

“Ba inda zaki koma ki dawo, tare zamu tafi, sunce zuwa 12 likitan da zai sallamenin zai ƙaraso.”

Sai a lokacin ta ɗago ta kalle shi.

“Da gaske? Baka warke ba fa, Kwana biyu kawai?”

“Na warke mana, idan ban warke ba ta yaya zamu tafi Kiyari gobe?”

Jidda ta cigaba da daurewa kallonsa mamaki na sauka akan fuskarta, dama abinda yaje yi wajen likitan kenan? Takura musu yayi su sallame shi don suyi tafiyar gobe? Ita fa har ga Allah bata gama tsaida zuciyarta akan tafiyar nan ba, tana masifar son ganin su Baddo amma kuma ta san tafiyarta baya nufin dawowarta, shi yasa take so sai ta gama tsaida zuciyarta waje ɗaya tukunna, sai ta gama sallama da duk abubuwan data san ta fara sabawa dasu.1

“Saboda zuwa Kiyari zamu tafi baka gama warkewa ba?”

“Na gaya miki na warke.”

Jidda ta sake girgiza kanta.

“Baka warke ba, aiki fa aka maka a wajen, kuma kwana biyu kenan kawai.”

“Kin iya naushi?”3

“Me?”

Tambayar tazo mata babu zato, don ba amsar da tayi tsammani bace.

“Ki gwada, ki naushi ciwon yanzu, zan tabbatar miki na warke.”

Madaki ya faɗi hakan ne kawai don tayi tunanin cewa ya fara warkewa ba wai don shi kansa ya yarda da ƙarin jikinsa ba, sai dai da gaske bai san halin Jidda ba, don kallonsa tayi na wasu ƴan sakanni kafin ta sunkuya ta ajiye basket ɗin hannunta, kuma ɗagowar da zata yi kawai yaga hannunta na dama a dunƙule alamun da gaske naushi nasa zata yi, don haka a lokaci guda ya saki ɗaya hannun nata ya kamo shi sannan ya jawo ta jikinsa gabaɗaya.6

“I’m just joking, ya ilahi ke baki san wasa ba?”5

Ya faɗa a daidai fuskarta yayin da ya zaunar da ita akan cinyarsa, Jidda bata ce komai ba don da gaske tayi niyyar dukan nasa, ko bada karfi ba idan dai ta fama ciwon watakila ba lallai a sallame shi yau ɗin ba.2

“Ko ciwon nan zai dawo sabo, we’re leaving this place yau, saboda haka ni da ke kawai zaki ƙara bari da jinya.”

Ya faɗa a hankali daidai gefen fuskar tata, ƙamshin toothpaste ɗin bakinsa na busawa akan fatarta, a lokaci guda jikinta ya ɗauki dumi kamar an ƙyasta ashana daga tafin ƙafarta, kuma kafin tayi wani yunƙuri Madaki ya manna leɓɓensa akan kumatunta na gefensa sannan muryarsa ta fito akan fatarta…3

“Kin iya dressing ai ko…?”

A lokaci guda wani abu tamkar wuta ya sake tafiya zuwa ƙarshen kowacce jijiya ta jikin Jidda, yana ƙara rura ɗumin da jikinta ke ɗauka, ita bata san wannan abin ba, bashi ma da suna a ƙwaƙwalwarta balle har ta iya fassara ma’anarsa.

“… Sun ce ko na tafi dole sai ana yiwa wajen dressing..”

Ya ƙara faɗa leɓɓensa na sliding akan fatarta, a wannan lokacin duk yadda Jidda ta kai ga dunƙule yatsun ƙafarta sai da duk wata nutsuwarta ta wargaje, ta kasa cigaba da daurewa komai saboda haka bata san sanda ta juya da wani irin sauri ta cusa kanta a gefen wuyansa ba cikin neman sauƙi, hannyenta duka biyu na dunƙule akan ƙirjinsa…2

A lokacin ne kuma ƙofar ɗakin ta buɗe, waɗannan Nurses ɗin na lab suka shigo har su biyu, ɗauke da kayan test ɗin da zasu yiwa Madakin don a fitar da result na ƙarshe kafin zuwan likitan da zai sallame shi.3

Kalaman ‘Booked for Honeymoon’ suka tabbata a zuciyar ɗaya daga cikinsu.1

***

“Why are you not picking my calls? Tun safe nake kiranka.”

STORY CONTINUES BELOW

Madaki ya faɗa a cikin wayar da yake yi tsaye daga wata baranda a harabar asibitin, yayin da yake hango motarsa a can gaba, inda Jidda ke ta ƙoƙarin harhaɗa kayan flask ɗin nan daga baya yayin da Baba Saminun da zai yi driving ɗin su ke tsaye a waje daga bakin ƙofar zaman direba. An riga an sallame shi tun dazu bayan likitocin sun kafa masa wasu ƴan sharuɗa da shi bai gansu a matsayin ƙalubale ba kamar yadda suka nuna a farko sanda ya nemi a sallame shin.

A yanzu shi suke jira kawai su tafi amma haka kurum sai yaji kamar baya son fita daga asibitin ba tare da ya samu Mubarak ba, don tun safe yake kiransa a waya amma bata ko shiga balle har yasa ran za’a ɗauka. Don haka dole ya tashi Habibu a tsaye wanda yake office yayi roaming file ɗin Mubarak ɗin na aiki a computer office ɗin sannan aka samo nambar matarsa Khadija.

Wadda itama bayan ta ɗauka, da kyar ta iya haɗa shi da Mubarak ɗin bayan ta gama inda-indar da bai fahimta ba.

“I’m sorry wayar tana kashe ne, yaya jikin naka?” Muryar Mubarak ɗin ta amsa daga cikin wayar.

Madaki ya ɗan haɗe girarsa alamun nazari kaɗan saboda jinsa da yayi kamar mara lafiya.

“An sallame ni, kai kuma me ya same ka?”

“Kuma ka tabbata zaka iya tafiyar nan a haka?” Mubarak ɗin ya tambaya shima, don ya riga ya san dalilin da yasa aka sallame shin.

“Zan ƙokarta insha Allah don dole ne inje, and why are you not here? Yau Lahadi fa? For God’s sake we should fight this together in kaga da yadda suka yi discharging ɗina.”

(… Me yasa baka shigo ba? Yau lahadi fa? Tare ya kamata ace munyi fafutukar nan, in kaga da yadda suka sallame ni.)2

Daga tsallaken Mubarak ya cije leɓɓensa na ƙasa da ƙarfi, ya cusa yatsunsa cikin gashinta har zuwa ƙeya sannan ya sunkuya ba tare da ya cire hannun ba, Allah ya sani da kyar ya karɓi wayar a yanzu da Khadija ta kawo masa, sai da ta nuna masa fuskar screen ɗin tare da lokacin kiran dake tafiya akai sannan a fili tace ‘Madaki ne ke son magana da kai..’ don haka bashi da zaɓi dole ya karɓa ɗin.

Amma har ga Allah bai so fuskantarsa a yau ba, musamman wannan lokacin da ko rana bata gama buɗewa ba, awanni basu shuɗe ba daga sanda ya riga yaji wani abu daya gigiza zuciyarsa fiye da duk wani hali daya taɓa shiga a rayuwarsa, don ko a lokacin da iyayensa suka rasu bai wani gama mallakar hankalinsa sosai ba balle ace yaji zafin da yafi haka.

Madaki abokinsa ne da ya dade da juyewa ya zama ɗan uwa, ya taimake shi fiye da duk wani taimako daya da wani ɗan adam ya taɓa yi masa a duniyar nan, ubangiji ya ƙaddara samun duk wata darajarsa a duniya ne ta silar Madaki, babu wani abu koda makamancin allura ne da zai iya warewa a cikin dukiya da nasararsa yace wai babu sunan Madaki a silar samunsa, komai da ya samu ta hanyarsa ne, komai da ya zama ta dalilinsa ne, wani mutum ne shi da yake ganin inda ana iya ɗora wani a gurbin iyaye tsaf zai iya cike wannan gurbin nasa da Ibrahim Madaki.

Amma ace wai an wayi gari saboda wani shashancin banza da shirmen mahaukaciyar kwakwalwar Salwa ta sanya an harbe shi, harbi da bindiga wanda da yayi kuskuren wucewa gefen kafaɗarsa da shikenan yanzu ta kashe shi saboda wani mahaukacin hasashenta na ganin cewa zata mallake shi, A tunaninta yau ko ita tafi kowacce mace hankali a duniyar nan zai taɓa bari Madaki ya aureta ne? Wato ya ƙare rayuwarsa a ƙarƙashin su bai amfani wasu da komai ba kenan saboda su kaɗai ne mutane…3

Ya riga ya rantse ya kuma rantsewa da Allah sai ya hukunta ta daidai gwargwadon yadda ba zata sake kwatanta irin wannan tunanin akan wani ba nan gaba, haka ya faɗa a lokacin daya shigar da ita cikin police station din nan tana magiya tana bashi hakuri amma bai ko saurare ta ba yace da ƴan sandan so yake a tuhume ta saboda tayi ƙoƙarin kashe wani, so yake ta faɗa musu gaskiya akan duk abubuwan da ta daɗe tana shiryawa in yaso ko karyata suka yi daga baya ya biya a kaita asibiti.

STORY CONTINUES BELOW

Ya dade yana mata uziri, ya daɗe yana goyon bayanta akan abubuwa da dama, kallonta yake a kodayaushe da wannan tausayin na cewar bata taɓa sanin ɗumin mahaifiya ba don a sanadiyar haihuwarta ta rasu, yana tausayin wannan kewar rashin uwar data taso dashi shi yasa bai taba barin zuciyarta taga aibunta ba, amma a yanzu komai ya buɗe akan idanunsa, wancan tunanin nasa akanta ya ruguje, kuma a karo na farko ya yarda da abinda yayarsu ke yawan gaya masa cewar ‘Salwa bata da hankali Mubarak, Ina kokwanton idan da imani ma a kasan zuciyarta..’

A yanzu zuciyarsa ta yarda da hakan, don kuwa babu wani mai imanin da zai hallaka wani don cikar burinsa kaɗai, shi yasa ya rantse ya kuma rantsewa cewar sai ya hukunta ta da wani hukunci da duk yadda zuciyarta ta kai ga ƙeƙashewa sai tayi laushin da zata fahimci kuskurenta ƙiri-ƙiri.

Don haka a yanzu fama kawai yake da kansa na irin kunyar Madakin da zai ɗauka duk ranar da ya fahimci abinda ke faruwa, da kuma kunyar ƴar talikai yarinyar da bata ji ba bata gani ba. Ya san tun a ranar Madaki zai iya fahimtar cewa yana zargin yarinyar nan don ko daga yadda ya amsa gaisuwarta ba kamar yadda ya dace bane a yadda yake son ganin nata a baya, amma da yake shi yafi adalci da daurewa zuciya sai bai ce komai ba, kuma bai nuna ba har a yanzun da ya kira yake cigiyarsa.

Ba tare da ya ɗago daga sunkuyawar da yayi ba, Muryarsa ta fito a hankali tana shiga cikin wayar.

“Wallahi bana jin daɗi ne, kuma ma dai wani abu ne ya taso min unexpected.”

Madaki ya kaɗa kansa.

“To Allah ya warware mana, but gaskiya we have to meet kafin goben don jirgin ƙarfe takwas nayi booking, Ina son in sami jana’izar ne tunda Saifudeen yace min wajen 11 ake saka ran kai shi, and also there’s something we need to talk about. (… akwai abinda zamu tattauna.)”

Mubarak ya ɗago da kansa a lokacin yana kallon Khadija data shigo da wani tray na kayan breakfast ɗin da da bai bata damar kawowa ba tun ɗazu.

“Insha Allah Mdee, zan shigo wajen yamma.”

“Ka nemi Nasiru ku taho tare, akwai takardun da zan bashi don watakila zuwa wednesday Jack na HRS zai iya shigowa ya karɓa, tunda kaga kaima may be zuwa wednesday ɗin zaka shigo.”

“Insha Allah.”

Mubarak ɗin ya amsa yana karɓar plate ɗin soyayyen ƙwai da chips wanda Khadija ke miƙo masa.

A ɓangaren Madaki kuwa yana sauke wayar, idonsa ya sake kaiwa kan Jidda wadda ta fito daga motar a yanzu ta tafi kan wata baranda dake gefe, inda wata mata ke ta fama da wasu ƙananan yaranta, akwai babba da bai fi shekaru uku ba sai kuma ƴan biyu mace da namiji dake ta faman kuka yayin da take ƙoƙarin haɗa musu abincinsu, babban kansa bashi da wayo don ƙannen nasa na kuka amma yana kara jan mayafin Maman alamun shima da abinda yake so. Macen ce riƙe a hannun Jidda sai jijjiga ta take yi tana busa iska kaɗan a kunnenta yayin da Maman ke jijjiga ɗayan tana kuma cigaba da haɗa musu abincin.

A lokaci guda yaji kamar bugun zuciyarsa ya ɗan ɗauke kaɗan sannan kamar iska ta ɗauke a ƙirjinsa, bai taba ganin mace kamar ta da bata dauki kanta komai ba irin Jidda, don daga yadda take jijjiga yarinyar tana kuma kokarin yiwa babban magana na nesa zai rantse cewar ita kanwar matar ce tare suka zo ba wai taimaka mata kaɗai ta tsaya yi ba.

Ba zancen aiki kaɗai yake son yiwa Mubarak a yau ba, har da zancenta, yana so ya gaya masa cewar ya fahimci kyawawan halin yarin yar nan kuma zuciyarsa ta ture dukkan wani zargin da yake akanta, A yanzu gani yake kowacce irin ƙaddara ce ta haɗa shi da ita mai kyau ce don baya tunanin inda ba’ayi hakan ba a duk sanda ya tashi yin aure a rayuwarsa zai iya haduwa da mace mai saukin kai da tsaftatacciyar zuciya irinta, komai da take yi a rayuwarta hakika ne daga zuciyarta, bata da riƙo ko kaɗan balle kuma mugunta.

STORY CONTINUES BELOW

A ɗan zaman da yayi da ita wannan halin nata shi ya canja kaso mafi yawa na tunanin da yake dashi akanta ba wai bincikensa ba, kuma hakan ne a yanzu ya haddasa wani abu kamar ƙaunarta a zuciyarsa, tunda dama zuciyar fanko ce bata taɓa sanin wani abu makamancin haka ba, a kullum yana danne dukan wani emotion da feelings ɗinsa ne a ƙasan ciwonsa, yana gayawa zuciyarsa dake da rauni cewar ba zai iya raba ta da kowa ba, tasa ce shi kaɗai daga shi sai ciwon nasa.

Amma a yanzu gani yake kamar ma bashi da control da zuciyar sai iya inda ya rage Jidda bata mamaye da kyawawan halayenta ba wanda dashi yake son cimma burinsa na son canja duniyarta itama ya koya mata wata sabuwar rayuwa da tafi wadda su duka biyun suka taso a ciki, so yake ya inganta zamansu, ya samar da wani farin ciki a zuciyoyinsu ta yadda ko da ciwonsa bai bashi isashiyar dama ba aƙalla zai san cewa bayan ibada, bai ƙare rayuwarsa aiki kawai ba.

Kallonta yake tana ta jijjiga Babyn wadda a yanzu tayi shiru alamun ta haƙora, daga zaune a kujerun gefe kuma Maman na bawa ɗaya namijin abinci, a ɗazu ba don shigowar Nurses ɗin nan ba, yaso aiwatar da wani abun da zai fara fahimtar da ita manufarsa akanta, zai sa ta fahimci cewa a yanzu tana daya daga cikin abubuwa mafi muhimmanci a rayuwarsa kuma zai kare ta da dukkan iyawarsa, amma akace wai sannu sannu bata hana zuwa…

A lokacin ne kuma ta juyo ta kalle shi, wani kallo da ya ƙara nauyin iska a ƙirjinsa yayin da murmushin leɓɓenta kuma ya yanke shigar iskar ma baki ɗaya, ba mummuna bace kuma bata da wani shahararren kyau ya sani, sai dai a idanunsa tafi kowacce mace a daraja da ƙima a rayuwarsa.

“Ka gama?” Motsin fatar bakinta da kuma alamar da tayi da hannunta yasa ya fahimci me take nufi tun daga can.

Sai ya ɗaga mata kai idanunsa na nazarin yadda hasken ranar na ƙarfe ɗaya ke dallare fuskarta yana ƙara ƙawata masa kammaninta da kuma tsarin halitta, wannan karon bata yi magana ba, da hannu tayi masa alamar komai cikin wani ɗan dogon sentence.

“Dan Allah. Ka jira. Minti ɗaya. In bata. Babyn.”

A hankali wani ɗan guntun murmushi yayi playing akan leɓɓensa ba yayin da wayar hannunsa ta shiga ƙara alamun shigowar kira. Sai dai bai ɗaga ba balle ya daina kallonta, itama shi ɗin take kallo kamar tana jiran amsarsa, yayin da a tasa zuciyar tunani yake daki-daki na yadda zai fara fahimtar da ita manufarsa akanta, me Mubarak yace ne?

… Ka san hanyoyin ka fa…

***

Kiyari.

Fadar Mai Martaba.

04:30 Am.

Lafiya maigidan bawa da baiwa

Lafiya dubu jiran mutum ɗaya

Lafiya Adalin sarki

Lafiya gagara gasa

Hifzullahi na Allah

Kanzullahi basasa

Amin Alfanda

Amin mai nasara

Amin zullillahi…

Wannan kirarin shi ke tashi daga bakin fadawa a lokacin da Sarki ya dawo daga masallacin sallar la’asar ya dawo cikin faɗarsu domin cigaba da karɓar gaisuwa daga tarin al’ummar dake ta tururuwa a masarautar, duk da cewar har a yau ba’a kawo gawar ba, Saifudeen tare da wasu daga cikin ƴaƴan ƙannensa sun tafi tun a jiya kuma a ɗari da akayi waya dasu safe since an gama duk wasu cike-cike da komai har ma an basu gawar kuma zasu taho da safe, wanda a agogon Nigeria ya kama karfe uku kenan na dare. Don haka aka sanar da jana’izar da misalin ƙarfe goma yadda duk daɗewa zuwa sha ɗaya an kammala komai an kaishi.

Sarki Ahmad Uba Kamsusi ya san cewa shi shugaba ne, mai dauke da nauyin dubunnan al’umma a kafaɗunsa, wanda ba yau ya saba ɗaukan hakan ba, yana riƙe da wannan nauyin tsawon shekaru amma duk tsawon wannan lokacin bai taba jin nauyin hakan a tattare dashi ba sai a cikin kwanakin nan, sai a yanzu da hankalinsa yake a mutukar tashe yake ganin cewa rayuwa ta juyo dashi da kuma iyalansa zuwa wani ɓarin nata mai tsananin duhu, don ko a jiya da su Nadiya suka zo yi masa ta’aziyya sai da ya fitar da ƙwalla a idanunsa bayan fitarsu duk yadda yaso ga daurewa.

A baiyane yake cewa dukkaninsu suna cikin tashin hankali da zuciyoyinsu ne kadai zasu iya fassarawa, don babu wani abu a duniya da yafi rashin ɗan uwa da kuma mahaifi, Farouk ya tafi, Fulani bata mutu ba amma gangar jikinta ce kadai a raye, babu wannan Hafsatun da take uwa kuma mata a wajensa, ya fahimci hakan tun daga lokacin da ta fara sambatu a gabansa kafin ma a kawo gawar Jakadiyarta abubuwa su ƙara rincaɓewa.

Halin da ta shiga kamashonta ne, laifinta ne, kuma ta riga ta gama tonawa kanta asiri a gaban kowa, ta fallasa asiri da ya daɗe a ɓoye, abinda aka daɗe ana tsegunta masa yana turewa, yana ganin haddasa ce kawai daga makiyanta, yana ganin Hafsatun da ya sani ba zata aikata haka ba. Sai gashi a yau komai ya kwance, kuma bahaushe yayi gaskiya da yace rana dubu ta ɓarawo, daya tak! ta mai kaya, a yanzu anzo gaɓar da Fulani zata karbi sakamakon duk wani abu da ta daɗe tana shukawa, kuma a yanzu duk wanda ke karkashin alhakin ta lokacin sakayyarsa ya fara kenan don har yanzu ma ba’a san takamaiman abinda ya same ta ba.

Saboda bayan ta farka daga baccin da ta dade tana yi a kasan allurai ne sai kuma aka zo masa da bayanin cewa bata iya tashi kwata-kwata ko magana, don haka a yanzu aka kira likitoci suka shiga ƙara duba ta, wanda bayanin hakan ne a yanzu Galadima ya shigo dashi kamar yadda likitocin suka shaida masa.

Sarki ya gaishe ka, kogin gabas maci yammawa,

Sarki ya amsa mai ado da kurar doki,

Lafiya dai Galadima jakadan Sarki…

Fadawa suka rufe da kirari a lokacin da Galadiman ya shigo ya durƙusa a gaban mai martaba, bayan yayi gaisuwar ne kuma sai ya ɗago ya kalle shi da zummar ya sallami dogarawan kafin ya shaida masa bayanin da yake tafe dashi, amma ga mamakinsa Sarkin kallonsa yayi shima sannan ya buɗe baki yace.

“Ina sauraren ka Galadima.”

Saboda haka sai ya taso ya matso a hankali daidai saitin kujerarsa sannan ya ajiye wani file mai ɗauke da bayanin dukkan wasu gwaje-gwaje da likitocin suka gabatar. Kansa a sunkuya yace.

“Kamar yadda suka shaida min ranka ya dade bayan sun kammala dukkan binciken su sun gano cewar Fulani tana dauke da matsalar ƙwaƙwalwa ne wanda since za’a iya magance shi cikin ƙananan lokaci in har ba’a bari ya cigaba da tasiri ba.”

Sarki ya gyada kansa, Galadima ya sake gyaran murya sannan ya sauke muryarsa ya fadi magana ta biyun, magana ta karshe kuma magana mafi girma kwatankwacin labarin rasuwar Umarul- Faruk.

“A bincike na biyu kuma ranka ya dade, sun ce ta kamu da cutar ɓarin jiki koma fiye da rabi ranka ya daɗe don idanunta ne kawai ke iya motsi a duk jikin nata!”5

***

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *