ZEHRA CHAPTER 10
LONDON, ENGLAND Kwance take a kan gadon shi tana ta rusa kuka yayinda yake zaune a gefen ta yana faman tunani.+ Conversation din shi da likitan ne yake yawo a qwalwar shi inda yace “Mr. Muhammad it doesn’t matter if it was a mistake, both of you made love and and this is the result” “Conception may take place as soon as three minutes after sexual intercourse, it may also take days. So yes Mr. Muhammad, fertilization can occur within minutes of sex” “Some women never get noticeable early pregnancy symptoms, it’s the case with your wife” Gani nayi ya dafe kai yayinda ya tuno kiran wayar da likitan yayi mishi a dalilin yayi insisting sai likitan yayi mata blood test. “Mr Muhammad it has been confirmed, she is 15weeks pregnant” Gani nayi ya qara matsawa kusa da ita yayinda ya kamo hannun ta yace “Babe please stop crying. I am very sorry about this. Look idan baki son pregnancy din lets take it out…” Shi kam ya fadi hakan ne ba wai don baya so ba sai don ya nuna mata cewar she has a choice kuma zai yi supporting dinta. Gani yayi ta taso da sauri tana kallon shi cike da mamaki yayinda tace “Yaaya?? Mu kashe rai?? Wallahi bazan aikata sabo ba. idan baka so ni ina son kayana…” Gani nayi ya saki ajiyar zuciya tare da gode ma Allah ya bashi mace mai hankali yace “Babe ya za’a yi in ce bana son gudan jini na?? kawai dai I feel you don’t want it ne shiyasa na baki option” Hawaye na zubowa daga idanuwan ta tace “ni ban ce bana so ba” Yace “toh meyasa kike kuka??” Qara fashewa tayi da wani sabon kuka yayinda ta kwanta a jikin shi tace “I don’t know, Yaaya yanzu shikenan rayuwata ta canza for good kenan??” Yana rungume da ita ne yace “I am sorry Babe” Haka dai ya cigaba da lallashinta. *********** Sossai Zehra ta tada hankalin ta da farko amma kuma a dole ta rungumi qaddara yayinda ta cigaba da rainon cikin nata. Kusan ma ace Muhammad din shine yake rainon cikin domin kuwa a yanzu komai da komai shine yake yi mata. Wanka ne kawai baya yi mata amma shima idan har ta shiga bathroom toh fa yana nan yana jiran ta har ta fito sannan ya dauke ta ya ajiye ta bisa Vanity stool. Har abinci shi yake bata a baki. Kullum tana nan kwance a jikin shi tana zabga mishi shagwaba son ranta. Dama dai da lafiya tana da son jiki balle kuma babu lafiya. Haka zata yi bacci ta dade a jikin shi har ta tashi. Kula yake da ita kamar sarauniya. Cikin Zehra ba mai laulayi bane amma a dalilin sangarta ta da Muhammad yayi duk sai ta bi ta langwabe mishi. Har wata qiba tayi amma fa dukda hakan Cikin bai fito ba. A yanzu ma wani ikon Allah ta rage yin maganar Mustapha. Shi kanshi Muhammad yana mamakin yadda har bata damuwa idan suka yi waya a gaban ta. Shin ta manta da shi ne???🤨6 STORY CONTINUES BELOW A lokacin da labarin cikin zehra ya kai kunnen su Mummy kuwa sunyi murna sossai. Fadeela kuwa abin ma har mamaki ya dinga bata. Zehra tana fadi mata cewar they are just friends amma kuma sai gata da ciki. Ko da ta matsa mata da tsokana sai ce mata tayi it was a mistake kuma babu yadda zasu yi. Sossai Fadeela take dariya a duk lokacin da take fadin Mistake ne. Sai da cikin Zehra ya kai wata Shidda sannan suka dawo Nigeria. A dalilin ta ji dadin zaman London din ne ta hana su dawo. Shi kuwa daman duk abinda take so shi yake yi. Zaman su a London meant incurring additional cost wanda kuwa ba matsala bane a wurin shi. For Zehra he can spend all of his money. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ 2 Months later… NATIONAL HOSPITAL ABUJA Gaba dayan su suna zaune a dakin da yake kusa da labour room yayinda suke ta jiyo ihun Fadeela wadda take ta naquda. Fadeela dai tun jiya da dare take ta fama da naquda wanda kuwa har safiyar yau ana ta sa ran haihuwa amma shiru. A jiyan da daddare ne aka kawo ta asibitin. Zehra wadda take zaune hankali a tashe tana ta kuka yayinda Mummy take rungume da ita tana ta lallashi. Anty ce tace “anya ba zan kira Muhammad ya zo ya kai ki gida ba kuwa?? Ai wannan ihu na Fadeela sai ta bata tsoro” Mummy tana dariya tace “ai Fadeela akwai raki, ko alama bata son wahala. Wallahi na dade ina tunanin rana irin wannan” Anty ma wadda take dariya tace “Allah dai ya raba lafiya” Fadeela dai bata haihu ba sai wuraren qarfe goma sha daya na safe wanda kuwa throughout labour din Zain yana nan tare da ita. Sossai ya sha duka da masifa. Dr Haleema wadda ta karbi haihuwar kuwa ta sha dariya ita da Nurses dinta. Zain kuwa har hawaye ya dinga yi. Fadeela dai ta samu danta namiji kyakyawa fari sol. Kwanan su biyu a asibitin sannan aka sallame su. Murna wurin families din biyu kuwa abin ba’a cewa komai musamman Zain. Tuni yayi ma jaririn huduba da sunan kakan shi wato Yazeed. Gidan Mummy aka wuce da ita saboda ta samu kulawa sossai. Tunda aka yi haihuwar kuwa kullum gidan cike yake da ‘yan barka. Qawayen Fadeela kuwa su Hauwa da Yusra sunyi mamakin jin labarin auren Zehra da Muhammad domin kuwa basu taba tunanin Zehra zata auri wani wanda ba Mustapha ba. Yusra ma har cewa tayi a hada ta da Musty din tunda dai dama ya kwanta mata a rai lokacin bikin Fadeela da ta gan shi. Dariya ma ta ba Fadeela domin kuwa ta sani sarai Yusra ba irin matan da Mustapha yake so bane. Zehra kuwa tuni ta tare a gidan Mummy. Roqon Muhammad tayi akan ya barta ta zauna a gidan har sai bayan suna wanda kuwa ya amince mata. Shi kam tun auren su duk abinda Zehra tace ko baya so haka nan yake amincewa. Bai taba hana ta yin abinda take so ba. ♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE A yau kwana biyar da haihuwar wuraren qarfe goma da rabi na dare Zehra tana kwance a dakin Fadeela yayinda take ta kallon Babyn wanda yake baccin shi cikin kwanciyar hankali. STORY CONTINUES BELOW A lokacin kuwa Fadeela tana bathroom tana wanka. Wayar Fadeela ce tayi ringing yayinda Zehra ta janyo. Gani nayi tayi freezing yayinda ta qura ma wayar idanuwa. Tuni jikinta ya fara rawa yayinda hawaye ya ciko a idanuwan ta. Har ta tsinke bata amsa ba sannan bata ajiye wayar ba. Muryar Fadeela ta ji daga cikin bathroom din tana fadin “Zee help me answer the phone abeg” A karo na biyu wayar ta sake ringing Wanda kuwa hannun ta yana rawa tayi answering. Gani nayi ta kai wayar kunnen ta yayinda Zuciyarta ta buga da jin muryar shi inda yake fadin “Hey Baby Dee how are you? How’s my charming prince…” Bai ankara ba ya ji sheshekar kuka wanda ya sa zuciyar shi ta buga. Shiru yayi yayinda ya kasa qarasa maganar shi. “Zehra ce…” abinda zuciyar shi ta fadi mishi kenan. Sossai kukan ta yake dukan qwalwar shi yayinda Zuciyar shi ta kasa samun natsuwa. Tsawon minti kusan biyar yana sauraron kukan ta yayinda ya kasa fadin komai. Da qyar yayi composing kanshi yace “Hey, I am sorry please” Daga nan ya kashe wayar. whoa… Aikuwa jefar da wayar tayi yayinda ta cigaba da kuka. Fadeela dai fitowa tayi ta tarar da ita tana ta kuka. Da sauri ta qarasa wurinta tace “Zee lafiya?? Wa ya kira ni a waya..” kafin ta gama Magana ta janyo wayar ta duba. Ganin sunan Mustapha ne ta runtse idanuwanta ta ajiye wayar sannan ta janyota ta rungumeta tace “Zee wai sai yaushe ne zaki manta da Ya Musty??” Cikin kuka tace “I swear Dee nayi qoqarin mantawa da Baby amma na kasa, soyayyar shi yawo take yi a cikin jini na. I swear I missed him alot.. Na shiga uku, Ya zanyi??” Fadeela wadda ta tausaya ma Qawarta tace “toh kiyi haquri, ki cigaba da addu’a Insha Allah zaki manta da shi” Tayi murmushi sannan ta cigaba da fadin “na tabbatar idan kika haifo mana prince or princess dinmu zaki manta da shi” Haka dai ta cigaba da lallashin ta yayinda take ta rusa mata kuka. ************* Wani ikon Allah tun daga wannan lokacin har aka gama suna Fadeela bata gane kan Zehra ba. Gaba daya ma Gidan an kasa gane kanta. Dayake dai an san masu ciki da mood swing shiyasa ba’a damu ba. Asali ma lallaba ta aka dinga yi. Muhammad kanshi ya kula tana cikin damuwa. Duk tambayar duniya yayi mata amma tace babu komai. Hakanan ya dinga bata haquri for no reason. A tunanin shi qila shine ya bata mata rai. Sam ta kasa samun sukuni tun ranar da ta ji muryar Mustapha a waya. haaaa…. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Days later… MUHAMMAD OMAR TAFIDA RESIDENCE Zaune take a kan stool din Vanity table din dakinta yayinda yake tsaye yana yi mata stretching. A yanzu kuwa tunda cikin Zehra yayi nauyi ya hana ta fita don haka ko da ta dinga yi mishi qorafin gashin ta yayi datti yace zai wanke mata yayi mata duk wani abinda yakamata. STORY CONTINUES BELOW Tunda ya fara yi mata stretching din kuwa take ta kallon shi ta mirror yayinda take wasu tunani wanda bata gane kan su ba. Zehra dai a ‘yan kwanakin nan sossai take ba Muhammad close marking wanda kuwa ta rasa dalilin hakan. duk inda ya shiga tana biye da shi. Wurin aiki ne kawai bata bin shi wanda kuwa ta dinga kiran shi a waya kenan har ya dawo. Haka take tsintar kanta tana kallon shi a kullum yayinda take samun wasu weird tunani akan shi. Shi kam ya kula da yawan close marking da yawan kallon nashi da take yi amma kuma bai taba yin Magana ba. A yau kuwa kallon ya fi na kullum domin kuwa har yayi mata Magana bata ma san yayi ba. Duqowa yayi ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “Babes why are you staring at me like that?? Ina ta noticing dinki for days.. me ke faruwa?? ko nayi miki laifi ne” Ayya… bawan Allah!! Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “Yi haquri Yaaya, nima bana sanin ina kallon ka wani lokacin” Murmushi yayi yace “toh a rage kallon kada idanuwa su fado..” Fashewa tayi da dariya yayinda yayi murmushi. Daga nan kuwa suka shiga hira. Yana gab da gama mata stretching din ne yace “Babes na manta ban fadi miki ba, zanyi tafiya jibi” Zuciyar ta ce ta buga. Tana kallon shi ta Mirror tace “don Allah kar ka je” Cike da mamaki yace “why??” Kai tsaye tace “I am going to miss you, kuma ka ga my EDD is near, I want you to be around when..” Murmushi yayi yace “hey its just 3 days fa kuma Kano zan je, the thing is akwai wasu estates da Government zata gina ma ma’aikatan ta and they gave me the contract. Ina da appointment da Governor so I have to be there” Ya dafa kafadarta yace “Insha Allah zamu yi welcoming princess dinmu tare, we will name her Aesha after your Mom Allah ya jiqan ta” Murmushi tayi tace “ameen, toh amma idan scan din da aka yi qarya ne sai na haifo namiji fa??” Murmushi yayi yace “I can feel it cewar Mace ce, mai kama da ke sak” Ya dawo gaban ta ya tsaya tare da fadin “baki san ance idan Mace ta fara haifo namiji it means she loves the husband more than he does ba??” Zaro idanuwa tayi yayinda ya cigaba da fadin “kin ga in our case ni ne nake bala’in sonki so its going to be a girl” Gani nayi ta duqar da kanta yayinda duk ya bi ya bata tausayi tace “I am sorry” Murmushi yayi yace “No I am sorry babes, things would have been different without me getting in the way..” Dago kai tayi ta kalle shi yayinda tace “I will try and..” Katse ta yayi yace “sssshhhhh, you don’t need to try anything, just let it be” Gaba daya duk jikin Zehra yayi sanyi yayinda ta rasa me ke damun ta. Haka kawai bata so yayi tafiyar..2 Why??? ♤♤♤♤♤♤♤ A yau ne Muhammad zaiyi tafiya zuwa Kano. Tun safe Zehra take zaune a dakin shi tana ta rusa kuka yayinda yake ta shiri. Shi kanshi a ‘yan kwanakin nan baya wani jin dadin rayuwar ma gaba daya. STORY CONTINUES BELOW Yanzu haka da take ta kuka gaba daya ta birkita mishi qwalwa. Tana zaune a kan gadon shi tana ta kuka har ya gama shirya kayan shi. Gani nayi ya nufi wurin ta ya tsugunna tare da riqe hannun ta yace “Babe please stop crying, kukan ki yana breaking heart dina..” Cikin kuka tace “toh kar ka tafi”1 Ya girgiza kai sannan ya miqe tare da janyo ta itama ta tashi Yayi hugging dinta sannan yace “kar ki damu, insha Allah I will be back in just 3 days” Yayi kneel down sannan ya kwantar da kan shi akan cikin ta yace “hey my princess, this is your Abbu.. please don’t stress your Ammi while I am away. Behave yourself and take care of her..Kin ji?? I love you soo much and I hope you will grow up to be just like your Ammi…” Zehra wadda ta dan bata rai ce tace “haba Yaaya, you are going away for just 3 days and..” Ji tayi yace “sssssshhhhh” Ya dago kai ya kalle ta sannan yace “she kicked, it means she heard me. da alama zata yi ladabi da biyayya kamar mahaifiyarta” Zehra wadda take sauraron shi gani nayi tayi murmushi yayinda tayi saurin sa hannun ta a kanshi tana ta wasa da gashin kanshi tace “please take care of yourself for us Yaaya, I swear I will miss you” Ya miqe tsaye yayinda yayi mata kiss a goshi yace “I will miss you too My beautiful Babe” Ya kalli agogo yace “let me get going” Suna riqe da hannun juna suka fito tsakar gidan. Musa Direba ne yayi saurin karbar trolley din hannun shi yayinda ya sa a boot. Zehra wadda take maqale a jikin shi tace “tare da Musa zaka je?” Yace “uhm yes, I really am not in the mood to drive” Tace “toh wai meyasa bazaka bi flight ba??” Yayi murmushi yace “just like that Babe, its been quite a while da nayi journey by road” Ya dafa kafadarta ya duqo saitin fuskar ta yace “hey relax, I will be fine insha Allah. I will call you. Yanzu dai smile for me please” Murmushi tayi yayinda yace “yauwa Babe, can I go??” Tace “yes, Allah ya kiyaye hanya” Yace “ameen” Har ya juya zai tafi sai kuma ta riqo hannun shi tace “hey come here” Ya dawo yayinda tayi mishi alama da ya duqo. Cike da mamaki kuwa ya duqo. Bai ankara ba ya ji tayi mishi kiss a kumatu tace “we will be waiting for you” Lumshe idanuwa yayi yace “Oh Allah I got my first kiss today dukda dai ba irin wanda na so bane” Fashewa tayi da dariya yayinda tace “I promise to give you irin wanda kake so idan ka dawo toh” Ya zaro idanuwa yace “dagaske???” Tace “yes” Sossai ya cika da murna. A ranshi ne yace “Allah yasa ta dan fara sona ne” A fili kuwa yace “can’t wait My babe” Ya qara hugging dinta wanda kuwa ta riqe shi gam yayinda ta qi sakin shi. Da qyar ya lallabata ta qyale shi ya tafi Wanda kuwa tana nan a tsaye har suka bar gidan. Ban Ankara ba kuwa na ga ta fashe da kuka. Ita kam ta rasa dalilin da yasa bata so wannan tafiyar da yayi ba. I really don’t like this feeling☹3 ♤♤♤♤♤♤♤♤ Sossai Zehra ta shiga tsananin damuwa akan tafiyar Muhammad. Bata taba sanin cewar he has become a part of her ba sai da yayi tafiya, gidan gaba daya yayi mata girma. Khadeeja ce ta zo ta zauna da ita har zuwa lokacin da zai dawo. Cikin kwanakin nan uku kuwa duk bayan dan qanqanin lokaci zaka ga sun yi waya. Haka dai har ya kammala abinda ya kai shi… Dayake da rana ya Kamala sai kawai suka kamo hanyan Abuja. Tunda suka kamo hanya kuwa yake ta waya da Zehra. Motsi kadan sai ta Kira shi don jin inda suke Shi kam ya sani sarai ko ya fadi mata inda suke bata ganewa tunda dai Zehra was born and brought up in Switzerland, ina ta sani a Nigeria banda Abuja?? Don haka ne yakan ce mata saura kadan. ************ A lokacin da suka kusa shigowa Abuja ne Zehra ta kira shi. Ko da ya amsa ji yayi tace “kuna ina yanzu??” Yace “very close to you Babe, mun kusa shigowa Abuja” Tace “Alhamdulillah Yaaya, can’t wait to have you back” Murmushi yayi yace “me too My Babe, I want you to take care of yourself and the baby for me…” Cike da mamaki tace “ban gane ba, you will help me do that ai Yaaya..” Yace “well yeah, I am sorry, uhm Kinyi sallah??” Tace “no, yanzu dai zan je inyi” Yace “toh hurry and please kiyi mun addu’a kin ji” Zehra wadda jikinta ya fara yin sanyi tace “I will but…” Yace “babes its okay, sai na dawo. I love you” Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “sai ka qaraso Yaaya” Yace “I expected to hear you say I love you too..” Cikin shagwaba tace “Yaaayaa” Yace “okay okay, sorry. Bye” Ko minti biyar basuyi ba da magana a waya ne wata trailer tayi losing control yayinda ta fado lane din da motar su Muhammad take..1 Kafin a Ankara kuwa trailer din ta ture motoci har uku wanda kuwa harda ta su Muhammad a ciki. Ni dai wani mugun qara na ji yayinda na ji Muhammad yana fadin “Inna lillahi wa’inna illaihir raji’un” Tuni motocin suka fada cikin daji harda trailer din. Babu abinda yake tashi sai qura da hayaqi. Ko kafin in qarasa wurin kuwa na hango daya daga cikin motocin ta kama da wuta. Tuni mutane suka kawo agaji yayinda suke ta salati.. Ina dafe da kai nima salatin nake ta yi… Abinda na kasa tantancewa…. Wace mota ce ta kama da wuta??? Ba dai motar su Muhammad ba😭😭😭3 ♤♤♤♤♤♤♤♤ NATIONAL HOSPITAL ABUJA Zaune suke a waiting room na Emergency yayinda hankulan su suke a matuqar tashe.+ Gaba dayan su Kuka suke yi yayinda Papa da Daddy suke ta lallashin su tare da yi musu nasiha masu sanyaya zuciya. Kusan awa biyar Muhammad yana cikin emergency room din yayinda likitoci suke ta aiki a kan shi. Likitoci ne har guda biyar suke ta yi aikin su cikin qwarewa. A lokacin da aka je rescuing dinsu kuwa babu wanda zai ga scene din yayi tunanin wani yayi surviving domin kuwa hatsarin yayi muni sossai. Muhammad shi kadai yayi surviving wannan hatsarin. Musa direba kuwa ko da aka dauko su kafin a qaraso asibitin ya rasu.3 Motar da ta kama da wuta kuwa mutum daya ne Wanda shima ya qone a ciki sai dayar motar suma gaba dayan su mutane ukun da suke ciki sun rasu. Direban trailer din kuwa da Co-driver din shi da qyar aka zaro su daga wani ramin da suka afka. suma tuni sun mutu. Basu ankara ba suka ga an bude qofar dakin da sauri yayinda aka turo gadon shi da zafin nama. Gaba dayan su suka miqe wanda kuwa saboda tsananin sanyi da jikin zehra yayi kasa ma tashi tayi. Zubewa tayi a qasa tana fadin “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un!! Yau na shiga uku, Don Allah Yaaya kar ka tafi ka bar ni… please stay with us. I need you now more than ever…” Su Daddy ne suke ta tambayar halin da ake ciki yayinda aka wuce da shi. Likitocin ne suka fito yayinda suke Tattaunawa. A cikin su kuwa harda Zain Wanda ya kasance daya daga cikin top Doctors na asibitin. Dr Albert ne yace “Uhm, he is still alive but in critical condition, we have managed to stabilize him for now and he will be kept in the ICU while we continue to monitor him” Ya kalli Zain yace “please Dr Zain calm them down” Bai tsaya sauraron su Daddy ba ya bi bayan colleaques dinshi yayinda Zain yake qoqarin yi musu bayani dalla-dalla. Basu ankara ba suka ga Zehra kwance a qasa… da alama suma tayi tun lokacin da aka fito da Muhammad. Anan kuma hankalin su ya dawo kanta wanda kuwa nan da nan Zain ya dauka ta aka shige emergency da ita. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Kwance take a kan gadon asibitin yayinda su Anty suke tsaye akanta. Tuni Dr. Haleema ta bata gado domin kuwa BP dinta ne yayi high. Gani suka yi ta tashi da sauri yayinda take qoqarin sauka. Da sauri Anty da Fadeela suka riqe ta yayinda take qoqarin qwacewa tana kuka tace “don Allah ku qyale ni, ina Yaaya yake?? Ku barni in je in gan shi I beg you” STORY CONTINUES BELOW Anty ce tace “relax Zee, please don’t harm your Baby. Muhammad yana nan, yana ICU right now, as soon as he is awake zamu samu ganin shi” Cikin kuka tace “Anty don Allah ku fadi mun gaskiya..” Fadeela tace “wallahi Zee its true.. Ya Moha is alive”…….. Haka dai suka cigaba da lallashin ta har ta koma ta natsu. Dayake an sa mata maganin bacci a cikin drip ba tare da bata lokaci ba kuwa bacci ya kwashe ta. Fadeela kuwa a kan dole ta koma gida saboda jaririn ta yayinda su Anty harda Khadeeja suka kwana a asibitin. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Washegari da rana Yana zaune dafe da kanshi yayinda yake ta jin labarin abinda ya faru a wurin Daddy. Gani nayi yana goge hawayen da ke fita daga idanuwan shi yayinda yake ta addu’a. Mustapha dai isowar shi kenan daga Italy wanda kuwa tunda aka sanar da shi abinda ya faru jiya da daddare hankalin shi yayi matuqar tashi. Gaba daya jikin shi yayi mugun sanyi. Zuciyar shi ce ta buga a dalilin jin muryar da take hana shi bacci a kowanne dare, Muryar da yake bala’in so a rayuwar shi, muryar macen da ya fi so a duniyar nan, macen da har ya koma ga mahaliccin shi bazai taba son wata kamar yadda yake son ta ba, muryar Matar Yayan shi… Muryar ANGEL dinshi ZEHRA. Cike da tsananin tashin hankali ta shigo waiting room din tare da Anty wadda take riqe da ita. Mustapha wanda ya daga kai ya kalli fuskar ta kuwa sai da tsikar jikin shi suka tashi. Gani yayi ta qara haske sossai, tayi ‘yar qiba sannan dukda tana cikin tashin hankali sossai tayi masifar kyau. Bai ankara ba ya ji tana fadin “….Ina Yaaya yake? don Allah ku ce musu su bar ni in gan shi….” Mummy ce ta miqe tare da rungume ta tace “kiyi haquri Zehra, har yanzu ba’a bamu izinin ganin shi ba amma insha Allah zai samu sauqi” Ta janyo ta suka zauna yayinda ta cigaba da fadin “ki kwantar da hankalin ki ko don albarkacin cikin da yake jikin ki…” Zuciyar Mustapha ce ta buga jin maganar Mummy. Shi kam har ga Allah bai kula cewar Zehra tana da ciki ba don bai gan shi ba. Anty ce tace “ah ah Mustapha yaushe ka iso??” Yace “just a while ago Anty..” Zuciyar Zehra ce ta buga a dalilin jin muryar Wanda yake riqe da zuciyar ta gaba daya, muryar wanda tunanin shi kadai yake sa ta jin sanyi a zuciyar ta, muryar wanda soyayyar shi take bin jini da jijiyoyin jikinta, muryar wanda har ta mutu bazata taba son wani kamar yadda take son shi ba, Muryan qanin mijinta… her BABY, MUSTAPHA. Ko da ta dago kai ta kalle shi gani tayi ya qara kyau da haske amma kuma bai yi qiba ba, sai ‘yar rama da yayi kamar wanda bai dade da tashi daga kwanciyar jinya ba. Sossai Zuciyar Zehra take ta zafi. Gani nayi tayi saurin komawa jikin Mummy yayinda ta sake fashewa da kuka. Zehra dai kuka biyu take yi a yanzu. Tana kuka a dalilin halin da mijin ta yake ciki sannan kuma tana kukan ganin masoyinta wanda duk duniya babu wanda take so irin shi. Gaba daya soyayyar Mustapha ce take yawo a jinin jikinta. Su Mummy ne suke ta lallashinta yayinda Hankalin Mustapha yake a matuqar tashe jin yadda take ta kuka kamar zata mutu. STORY CONTINUES BELOW Ganin ba zai iya jure sauraron sautin kukanta bane na ga ya miqe zai fita wanda yayi daidai da shigowar likitoci a guje suka shiga dakin Muhammad. Sossai hankulan su suka tashi yayinda Su Daddy suke ta tambayar abinda yake faruwa amma inaa babu wanda ya amsa su. Zain wanda ya shigo yana biye da su ne yace “Ya farfado but there is complication, I will just find out and come” Aikuwa sossai hankulan su suka tashi. Zehra kuwa komawa tayi wurin Papa ta maqale a jikin shi tana ta kuka. Mustapha kuwa sai shafa kai yake da hannuwan shi duka biyu yayinda yake ta kai da komowa. Addu’o’I kawai yake ta jerowa. A daidai wannan lokacin ne Fadeela ta shigo waiting room din. Ganin yadda hankulan kowa yake a tashe ne tace “me ke faruwa??” Mustapha wanda yake kusa da ita ne ya janyo ta ya rungume ta yayinda ta fashe da kuka. A cikin kukan ne tace “Ya Musty me ya samu Ya Moha??” “Sssshhh, relax. Insha Allah he will be fine” abinda ya iya ce mata kenan. Kusan minti talatin likitocin suna ciki suna ta neman ceto rayuwar Muhammad. Zain ne ya fito daga dakin hankali a tashe yayinda duk suka rufe shi da tambayoyi. Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “he needs blood right now..” Ko kafin ya rufe baki ne Mustapha yace “take mine please..” Hankalin Mummy a tashe ta kalli Daddy wanda shima a yanzu nashi hankalin ya tashi. Zain ne yace “okay, mu je..” Ko kafin su daga qafafuwan su ne Mummy tace “Jinin ka bazai yi ba Mustapha…” Cike da tsananin mamaki suka kalle ta yayinda Mustapha yace “ban gane bazai yi ba Mummy..” toh fa… Fadeela wadda take kuka ce ta kalli Zain tace “sweetheart mu je a debi nawa..” Ko kafin ta rufe bakinta Mummy ta qara fadin “naki ma bazai yi ba Fadeela” Kuma dai??? Daga nan kuwa ta fashe da kuka wanda ya sa suka shiga tsananin mamaki. Daddy wanda yake rungume da ita ne yace “Blood type din Muhammad is different from theirs.. nashi type B ne sannan nasu type A ne..” Zain ne yace “it means cikin kai ko Mummy kuna B ko AB kenan??” Daddy ya runtse idanuwa yace “unfortunately we are all A too and babu O a gidan, maybe da an qara haifo wani zai iya zuwa as Universal donor” Cike da tsananin mamaki Zain yace “whaaat??” Su Papa wadanda suke ta sauraron su duk sun zama confused yayinda Mummy ta qara rushewa da kuka. Anty ma kuwa a wannan lokacin kuka take ta yi. Daddy ne yace “lets find a solution right now..” Muryar Zehra suka ji tace “Ya Zain mu je a debi nawa, ba nawa B+ bane??” Zain ne yace “No Zee, you are pregnant and you cant afford to lose even a single drop of your blood right now… I will give to him tunda ni (Universal Donor) O+ ne”. Daga nan ya wuce ya koma cikin dakin yayinda su Daddy suke ta saka mishi albarka. Mustapha da Fadeela wandada kawunan su suke a daure ne suka yi saurin matsawa kusa da iyayen su yayinda Mustapha yace “Daddy, what is going on?? Ta ya za’a yi cikin mu babu wanda zai iya ba Moha Jini?” STORY CONTINUES BELOW Fadeela wadda ta riqe hannun Mummy cikin kuka tace “is there something you are not telling us??” Mummy wadda take kuka ce tace “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, ban taba tunanin rana irin ta yau zata zo ba. Ban taba tunanin cewar sirrin da ya dade a boye zai bayyana ba…” Papa wanda yake rungume da Zehra ne ya kalli Daddy yace “Abokina what is happening??” Daddy wanda hankalin shi yake a tashe ne yace “please calm down, kuyi haquri mu ji halin da Muhammad yake ciki daga baya zamu yi maganar” Ni kuwa nace wacce magana??? What is going on here??? I am confused already…1 ♤♤♤♤♤♤♤♤ 2 hours later… A yanzu kuwa likitoci sun tabbatar musu da cewar he is stable wanda kuwa idan har ya farfado zasu iya ganin shi. Zaune suke gaba dayan su a waiting room din yayinda suka sa ma su Daddy ido. Daddy ne ya riqo hannun Mummy sannan yace “I think its time we tell them the truth” Mummy ta fashe da kuka yayinda yace “sssshhh, kar ki damu everything will be okay” Daga nan kuwa yayi gyaran murya tare da kallon Mustapha sannan ya kalli Fadeela yace “Muhammad is not your brother, ma’ana ba mu muka haife shi ba” Oh my, Oh my, Oh Em Gee… what???🙄🙄 Gaba dayan su suka ce “whaaaaaat??” Mustapha yayi saurin miqewa tsaye hankali a matuqar tashe yace “Da…dd…y don Allah ka ce this is not true..” Fadeela da Zehra kuwa sabon kuka suka fashe da shi yayinda Anty tace “unfortunately dagaske ne Mustapha..” Yace “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” yayinda ya dafe kai ya koma ya zauna. Tuni hawaye suka fara gangarowa a fuskar shi. Papa wanda yake cike da tsananin mamaki ne yace “and you never told me abokina??” Daddy ya dan yi murmushi yace “its because we promised ourselves cewar baza mu taba disclosing maganar ba, Abinda yasa Fatima (Anty) ta sani saboda tana zaune tare da mu lokacin da komai ya faru ne” Ya saki ajiyar zuciya sannan ya fara basu labari kamar haka: “Sama da shekaru talatin da uku da suka wuce, Lokacin da muka dawo Nigeria mun yi tafiya zuwa Katsina a dalilin rashin lafiya da Alhaji yayi. A ranar da muke dawowa ne muka hadu da ita a wuraren Jere, wata qaramar hukuma a Kaduna. Tsaye take a gefen titi da tsohon ciki yayinda take cikin tsananin damuwa da tashin hankali. Duk motar da ta tsayar don neman taimako suka qi tsayawa a dalilin rashin yarda sannan kuma a wannan lokacin yamma ta riga tayi sossai, kusan ma magrib ne. A lokacin da muka ganta kuwa Mummyn ku ce ta dage mun akan lallai mu tsaya mu taimaka mata. Aikuwa ko da muka fito sai gani muka yi ta durqusa har qasa tana kuka yayinda take fadin don Allah ku taimaka mun kar su kashe ni.. Sossai ta bamu tausayi. Abinda ya bamu mamaki a lokacin kuwa shine, da alama ba ‘yar qasar mu Nigeria bace, na biyu daga ganin ta kasan tana da ilimi na boko da na zamani, sannan kuma yanayin shigar da tayi da ganin kasan daga babban gida ta fito. Sossai muka yi mamakin wane irin hali ta shiga da har ya sa muka gan ta a wannan wuri a wannan lokacin. Ba tare da bata lokaci ba muka taimaka mata. Har muka isa Abuja kuwa bamu tambaye ta komai ba, Illa iyaka tana ta kuka yayinda Muke ta lallashinta” Yana riqe da hannun Mummy yace “dayake kun san Mummyn ku da tausayi, tun tana lallashin ta kuwa har itama ta fashe da kuka wanda kuwa sai ni ne na koma lallashin su. Bayan mun isa gida Mun barta ta huta sossai sannan muka yi mata tambayar labarin ta da abinda ya faru da ita” STORY CONTINUES BELOW Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “Allah sarki Aisha, Labarin ta abin ban tausayi. Asalin Aisha ‘yar qasar Chad ce. Marainiyar Allah wadda ta taso a hannun kakar ta. Tayi karatun ta har jami’a a wannan lokacin. Ta hadu da Alhaji Muhammad Usman Dogara wanda ya je garin Chad a wannan lokacin a dalilin sana’ar shi. Alhaji Muhammad usman Dogara wani shahararren mai kudi ne a wannan lokacin domin kuwa duk Nigeria babu wanda bai san shi ba. A lokacin ya kasance mai sana’ar shiga da fitar da mai. Gaba daya duk Nigeria babu jihar da zaka je baka ga gidajen man shi ba. Soyayya ce ta shiga tsakanin su wanda kuwa kafin ya koma Nigeria ya nemi izinin auren ta wurin Kakar ta. Kakar ta a wannan lokacin bata so Aisha tayi nisa da ita ba amma a dalilin ganin ta nace shi din dai take so ne ta amince mata. A wannan lokacin kuwa basu da masaniya akan irin arzikin da Allah yayi mishi sai da aka kawo ta dakin ta cikin garin Kaduna. Bayan anyi auren nasu ba da dadewa bane kakarta ta rasu. Tunda aka yi auren kuwa dangin Alhajin suka kafa mata kafar tsana. A wannan lokacin ne Aisha ta fahimci cewar dangin basu so Alhajin yayi aure har ya haifi dan da zai gaje shi, burin su bai wuci idan ya kwanta ya mutu su gaji dukiyar shi ba. Wannan ne yasa suka kori matan shi har biyu wanda ya taba aure. Ana cikin wannan halin ne Aisha ta samu ciki wanda kuwa hakan yasa dangin Alhajin suka tada hankulan su. Sossai suka so su ga bayan Aisha a wannan lokacin amman hakan ya faskara. A lokacin da cikin Aisha ya kai wata takwas ne wani al’amari ya faru. A ranar da daddare ne ‘yan fashi suka shiga gidan Alhaji, ko kafin su isa dakin Alhajin tuni ya boye Aisha a basement sannan ya bata makullin wani emergency exit a gidan yace mata idan ta ji shi shiru ta fita ta exit din. wannan shi ya kasance ganin ta da shi na qarshe domin kuwa ko da ‘yan fashin suka gan shi basu yi wata wata ba suka harbe shi har lahira. Aisha wadda take cikin basement din bata san abinda yake faruwa ba, bata ankara ba ta ji muryoyin su a kusa da basement din inda daya daga cikin su yake waya yana fadin basu ga matar ba sannan sun kashe Alhajin amma suna kan neman ita matar. Jin haka ne tayi amfani da emergency exit na gidan ta fice hankali a matuqar tashe. Da qyar ta samu ta fita daga gidan wanda kuwa gaba daya ma’aikatan gidan an harbe su. Da wannan ne ta dinga yawo tana neman yadda zata yi har Allah ya hada mu da ita” Sossai hankulan su Mustapha suke a tashe jin wannan labarin daga bakin mahaifin su. Zehra, Fadeela, Anty da Mummy kuwa kuka kawai suke ta yi. Ji suka yi Daddy ya cigaba da fadin “A wannan lokacin kuwa babu shakka labarin rasuwar Alhaji Muhammad ya zagaye qasar mu baki daya domin kuwa sananne ne. Tunda kuwa muka dauki Aisha ciwon hawan jini ya kama ta, har kwantar da ita asibiti aka yi. A matsayina na lawyer na so in shigar da case dinta kotu don bi mata haqqinta da ita da jaririn da yake cikinta amma sam ta hana. A cewarta ko an bi musu haqqin su ba lallai bane su bar su da ransu domin kuwa a yadda suka salwantar da rayuwar mijin ta zasu iya salwantar da ita da dan nata don haka ta bar su da Allah. Haka dai muka cigaba da zama da ita cikin amana. A dalilin tsananin damuwa da ta sa a ranta lokacin lafiya ta qi samuwa gareta. Kullum muna hanyar asibiti da ita. Likitoci suka bada shawarar a ciro jaririn daga cikin ta domin kuwa a halin da take ciki idan aka bata lokaci za’a iya rasa su gaba daya. A ranar da aka ciro jaririn kuwa maganganun da tayi mana sune bazamu taba mantawa ba” Daddy ya dan yi shiru yayinda sautin kukan Mummy ya qaru a wannan lokacin. “Alhaji.. Hajiya… Fatima, Nagode muku da taimakon da kuka yi mun, kun ceci rayuwa ta da na jaririn da yake ciki na sannan nagode qwarai da kula da ni da kuka yi har zuwa yanzu. Ubangiji Allah ya saka muku da gidan aljanna. Ina rokon ku alfarma daya, don Allah ku tamake ni ku kular mun da abinda zan Haifa, kar ku sake ku mayar da shi zuwa dangin mahaifin shi domin kuwa kashe shi zasu yi. Ina so kuyi mun alfarmar sanya mishi sunan mahaifin shi Muhammad sannan idan da hali ya amsa sunan ka a matsayin uba…” Mummy wadda take kuka tace “wannan shine Magana ta qarshe da Aisha tayi mana wanda kuwa bayan an shiga da ita sai dai fito mana aka yi da Muhammad. Aisha kuwa tuni ta koma ga mahalicci… Allah” Daddy ne yace “tun daga wannan ranar muka dauki Muhammad a matsayin dan mu wanda muka Haifa, muka bashi kulawa ta musamman sannan muka bashi soyayya wadda har yaran cikin mu bamu basu irin ta ba. Mun ajiye wannan a matsayin sirri tsakanin mu wanda kuwa bamu taba sa ran sirrin zai bayyana ba sai yanzu da muke baku wannan labarin kuma ina rokon ku alfarma kar wanda ya sanar da Muhammad wannan maganar, mu ne iyayen shi kuma har mu koma ga Ubangijin mu zamu cigaba da zama iyayen shi sannan shi a matsayin dan mu na fari” Gaba dayan su tsit suka yi yayinda suke ta jinjina wannan labarin. Banda sautin kukan su Mummy babu abinda kake ji a waiting room din. Gani suka yi Mustapha ya miqe tsaye ya kama hanyar fita. Zain ne ya miqe da sauri ya riqo shi yace “hey ina zaka je??” Muryar shi qasa qasa yace “I need some fresh air ne, ina zuwa” Anty ce ta miqe ta bi bayan shi. ************** Zaune yake a garden din asibitin dafe da kanshi yana kuka. Tasowar su tun suna yara yake tunawa. Sossai Mustapha yake son dan uwan shi, bai taba ko sau daya sa ran cewar ba su Daddy suka haife shi ba. toh me zai sa shi wannan tunanin when all Moha has done is nothing but love them unconditionally. Ji nayi yace “no wonder we don’t look alike, no wonder we have different skin color and personality, no wonder he is so different from us…” Muryar Anty ya ji tace “Yes Musty.. No wonder he is different in a very good way… Yana daya daga cikin mutanen kirki a duniyar nan” Zama tayi gefen shi sannan ta riqe hannun shi tace “I have never seen a person with a heart of gold kamar Muhammad” Mustapha wanda ya qara matse hannun Anty a cikin nashi ne yace “I don’t want to lose him Anty, please tell me he will be fine” Anty ta dafa kafadar shi tace “Insha Allah he will be fine” Haka ta dinga lallashin shi tsawon lokaci yayinda suka dinga labarin rayuwar su tare da shi. Ji tayi yace “how is she holding up??” Anty dai ta gane Zehra yake nufi don haka ne tace “wallahi ban taba sanin she is as strong as this ba, I am very proud of her because she has taken everything in good faith tun lokacin da kuka rabu. My fear right now is her pregnancy, ga EDD dinta is next week” Cikin rashin fahimta yace “what’s that??” Murmushi tayi tace “it means Estimated Due Date na haihuwa..” Yace “oooh” ya dan zaro idanuwa yace “wait what??? next week kika ce??” Tace “yes, cikin nata ba mai girma bane, mutum bazai taba yarda ta kai 9 months ba” Gani nayi ya dafe kanshi sannan yace “Allah ya sauke ta lafiya, Allah kuma ya ba Moha lafiya” Tace “ameen” ♤♤♤♤♤♤♤♤ NATIONAL HOSPITAL ABUJA Washegari da rana ne Muhammad ya farfado. Bayan likitoci sun tabbatar da lafiyar shi ne suka basu izinin ganin shi.+ Idan ka gan shi zaka rantse ba survivor din wannan accident din bane domin kuwa daga karaya a hannun shi na dama, sai kan shi da aka nade da bandage sai kuma stitches din da aka yi mishi a minor injuries din da yayi sustaining a jikin shi da fuskar shi. Sossai suka yi murna yadda suka gan shi musamman Zehra wadda ko sakin hannun shi ta kasa yi. Mustapha dai ya kasa boye tsananin tausayin shi da yake ji domin kuwa da ka kalli yanayin fuskar shi kasan akwai damuwa. Ko da ya tambayi halin da Musa Driver yake ciki sunyi mishi qaryar yana nan yana karbar treatment. Sunyi hakan ne saboda kar ya shiga damuwa domin kuwa sun san halin shi da yadda yake kyautata ma ma’aikatan shi wadanda ya mayar da su tamkar ‘yan uwan shi. Gaba dayan su dayake a asibitin suka kwana duk sun gaji, ganin ya farfado ne suka tafi gida amma banda Mustapha wanda zai zauna da shi har su dawo. Da qyar aka lallaba Zehra ta amince su je gida don ta dan huta sannan ta dawo anjima. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Zaune yake a gefen shi yayinda yake riqe da hannun shi. Da ka ga fuskar shi zaka san yana cikin tsananin damuwa. Muhammad wanda yake ta kallon shi ne yace “hey kwantar da hankalin ka mana, I am okay dagaske” Mustapha yace “are you sure??” Ya dan girgiza kai yace “eh toh ina feeling pains kadan but I am holding up” Murmushi ya dan yi yayinda yace “I really missed you brother” Mustapha ya matse hannun shi yace “I missed you too Moha…” Ko kafin ya rufe bakin shi ya ji yace “she does too..” Ya gane sarai Zehra yake nufi don haka ne ya kawar da kanshi ba tare da yace komai ba. Yana kallon shi yace “The pregnancy.. it was a mistake” Da sauri Mustapha ya kalli Muhammad yayinda ya cigaba da fadin “Yes Musty, we are just friends… I tried to make her fall in love with me amma it wasn’t just possible to replace you a cikin zuciyar ta…” Ya dan yi murmushi yace “I am very sure kayi ma Zehra asiri Musty” Mustapha ne yace “hey bro please stop, you don’t have to tell me this” Yace “I am still telling you anyway” Ya dan gyara kwanciyar shi sannan yace “akwai alfarmar da nake so kayi mun Musty, Ko da rai na ko babu ina so ka kular mun da su..” Dakatar da shi Mustapha yayi yayinda ran shi yake a bace yace “hey, meye haka?? You are okay and Insha Allah zaka tashi daga gadon nan…” Muhammad ya girgiza kai sannan ya cigaba da fadin “Ina so in sa ma Babyna suna Aesha, sunan mahaifiyar ta…” Mustapha a ran shi yace “Allah sarki Moha, if only you know cewar sunan mahaifiyar ka Aisha…” Bai ankara ba ya ji hawaye suna gangarowa daga idanuwan shi wanda yayi saurin gogewa. Muhammad ya dan harare shi yace “haba Musty, meyasa kake saurin kuka ne yanzu?? where is the strong and tough Musty that I used to know a baya??” STORY CONTINUES BELOW Mustapha a ranshi yace “if only you know cewar kai ne ka gina wannan Musty din… if only you know cewar the real Musty is a fragile, emotional and weak one…” A fili kuwa yace “duk laifin ka ne Moha” Murmushi yayi yace “Toh na kusan daina sa ka kuka Insha Allah” 🤔🤔🤔 Mustapha wanda jikin shi yayi sanyi for no reason ne ya ji Muhammad din ya cigaba da fadin “I am really sorry for taking away the love of your life Musty, na sani cewar kana iyakar qoqarin ka wurin masking damuwar ka but I can see right through you. I know you are broken. Please ko bayan raina I want you to promise me cewar zaka auri Zehra, not out of pity but out of love.. the love you still feel for her” Kafin ya qarasa maganar shi kuwa Mustapha ya saki hannun shi sannan ya miqe yace “Moha don Allah ka daina irin wannan maganar, Alhamdulillah you are alive kuma insha Allah kana tare da mu, Zehra kuma taka ce har abada” Muhammad ya runtse idanuwa sannan ya bude yace “I’d take this as an acceptance from you Musty” Mustapha ma kasa magana yayi yayinda yake ta mamakin the kind of person Moha really is… Bai ankara ba ya ji yana fadin “help me up please, ina so inyi sallah” Mustapha ya matsa kusa da shi yace “hey, ka bari ka dan qara samun sauqi mana… ai lalura ce wannan kuma..” Muhammad yayi murmushi yace “please help me Musty” daga nan kuwa ya taimaka mishi. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Da yamma ne gaba dayan su suka dawo yayinda Mustapha shi kuma ya tafi gida. Sossai sun ji dadin ganin yanayin Muhammad domin kuwa har hira da dariya ana yi da shi. Har abinci ya ci wanda Zehra ce ta bashi da kanta. Haka suka dinga hira har wuraren qarfe goma na dare wanda kuwa a lokacin Mustapha ya dawo. Gaba dayan su suka tafi gida suka bar Mustapha wanda shine ya kwana da shi. Washegari jikin Muhammad ya qara warwarewa domin har tashi yake yi ya zauna da kan shi. Likitoci ma da suka duba shi sun ji dadin ganin yadda yake samun sauqi sossai. ♤♤♤♤♤♤♤♤ A yau kwana biyu kenan. Jikin nashi yayi sauqi babu laifi. Mutane suka dinga zuwa gaishe shi, abokanen shi da ma’aikatan shi duk sun zo sun duba shi. Zaune take a kan gadon shi kamar kullum yayinda take riqe da hannun shi. Mummy ce tace “Zehra tashi mu tafi gida, dare yana ta yi” Zehra wadda take riqe da hannun Muhammad gam ce tace “nima yau anan zan kwana Mummy” Ita dai tun safiyar yau take maqale da Muhammad, haka kawai bata son tayi nisa da shi ta rasa dalili. A yanzu haka qarfe goma sha daya na dare wanda kuwa tun tuni ake ta lallabarta ta tashi su tafi gida amma ta qi. Daddy ne yace “ku qyaleta ta zauna da shi tunda haka take so, Mustapha yana nan ai babu damuwa” Anty ce ta kalli Zain tace “Sai ka sa a shigo mata da extra gado don ta kwanta tunda dai na san bazai yiwu tayi ta zama throughout the night babu bacci ba” Zain yayi murmushi yace “I will do that Anty” Muhammad wanda yake kallon su ne yace “Mummy” tare da dago mata hannun shi. Mummy ta qarasa wurin shi sannan tace “menene Muhammad dina? Kana son wani abu ne?” yace “give me a hug please” Murmushi tayi sannan tayi hugging dinshi tare da yi mishi kisses a kumatu tace “I love you so much son”1 STORY CONTINUES BELOW Yana murmushi yace “I love you soo very much Mummy, please take care of yourself.. I will forever be grateful for having you as a Mum” Bakinta ta kai saitin kunnen shi tace “Allah yayi maka albarka Muhammad, can’t wait to have you back on your feet” Muryar Fadeela suka ji tace “Ya Moha ni fa???” Gaba dayan su suna dariya yayinda ya miqa mata hannu yace “Oya come…” Ko da tayi hugging dinshi ji tayi yace “Baby Dee I love you so much, take care of yourself and Ameer” tana murmushi tace “I will Ya Moha, wane abinci kake so in kawo maka gobe da safe???” Murmushi kawai yayi yace “I might not even need that Baby Dee..” Ta bata rai sannan tace “marar lafiya yana buqatar abinci so I will prepare your fav” Yana murmushi yace “alright then” Hannun shi ya miqa ma Daddy wanda shima ya matso yayi hugging dan nashi yace “hey son remember that Daddy will always and forever love you, Allah ya baka lafiya ka ji”3 Yana murmushi yace “Ameen Daddy, I love you very much. You are the best Daddy in the world, I can never wish for a better Daddy than you” Daddy yayi murmushi yace “thank you Son” Bayan sunyi breaking hug din ne yace “Anty you are next up” gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Anty ta qarasa wurin shi tayi hugging dinshi itama. Ji tayi yace “you will forever remain the best Aunt.. I love you, hope you know that?? tana murmushi tace “I love you more my cute Nephew, Allah ya baka lafiya” Yace “ameen” Daga nan kuwa ya kalli Khadeeja yace “come here” da sauri ta qarasa wurin shi itama tayi hugging dinshi yayinda yace mata “take care of your Mummy, she is a great woman so you should be very proud of her” Murmushi tayi tace “I will Uncle.. Allah ya baka lafiya” yace “Ameen Deeja” Papa wanda ya riqe hannun shi yace “Allah ya baka lafiya Muhammad, sai Allah ya kaimu gobe” Yace “ameen Papa, nagode” Zain wanda shima zai tafi gida tunda ba shift din dare yake ba a yau ne ya nufi wurin shi ya riqe hannun shi yace “Bro In-law sai da safe, Allah ya qara sauqi” Yace “ameen, thanks very much for everything” ************* A yau su duka sun tafi kowa da abinda yake saqawa a ranshi. Dukkanin su jiki a sanyaye suka koma gida. Why??? Wuraren qarfe goma sha biyu saura na dare tana nan zaune a kan gadon shi yayinda suke ta hira. Ji nayi tace “Yaaya EDD dina saura kwana hudu, it could be more or even less. I need you to get much better so we can welcome our Baby together..” Yana murmushi yace “I wish its going to be possible Babes, Ina so in ga what our Baby will look like, I would love to watch her grow up…. to become a beautiful woman just like her Ammi..” Bata rai tayi tace “meyasa kake magana haka Yaaya… you will Insha Allah..” A daidai lokacin ne Mustapha ya shigo dakin wanda kuwa Muhammad ya hango shi amma yayi kamar bai gan shi ba. Da sauri ya kalli Zehra yace “hey akwai abinda nake so in tambaye ki.. promise me cewar you will tell the truth” Tana riqe da hannun shi tace “I promise you Yaaya” Yace “Are you very much still in love with Musty?” Mustapha wanda yake tsaye tuni ya juya zai fita wanda kuwa amsarta ce ta sa shi tsayawa cak. STORY CONTINUES BELOW “Yaaya kayi haquri wallahi nayi qoqarin daina son shi amma na kasa but..” Yana murmushi yace “hey its okay, I am glad you still do, just hold on to that love..” Katse shi tayi tace “No Yaaya, Hakan ba daidai bane. I want to fall in love with you and that’s exactly what I will do. Baby is my past, yanzu kai ne Present dina..” Yace “wa yasan yadda future zai kasance..” Hararar shi tayi tace “kai ne future dina insha Allah Yaaya” Tana riqe da hannun shi har yanzu tace “ka tuna alqawarin da nayi maka kafin kayi tafiya??” Yace “The kiss?? Ofcourse babe amma na yafe. I don’t want to force you into doing…” Bai qarasa maganar shi ba ya ji ta rufe bakin shi da nata yayinda ta shiga kissing dinshi wholeheartedly sannan passionately. Ganin haka ne Mustapha yayi saurin ficewa daga dakin. Muhammad wanda tayi taking dinshi by surprise sai gani nayi yayi saurin pulling out of the kiss tare da fadin “hey… you really don’t have to….” Ranta a bace tace “thank you very much for telling me that I am a bad kisser…” Dariya yayi sannan yayi hugging dinta yace “not at all babes, you are the best kisser I swear…. I really love you” Murmushi tayi tace “thank you Yaaya” Daga nan ta gyara kwanciyar ta a jikin shi yayinda suka cigaba da hira wanda kuwa yawanci duk hirar Babyn su ne. Bacci ne ya fara fizgar shi yayinda yace “Babe ina jin bacci, kema ki kwanta kiyi bacci” Turo baki tayi tace “ni ban gaji da hirar ba Yaaya..” Murmushi yayi mata sannan yace “kiyi haquri, just continue to dwell on all what we have talked about. Yanzu dai dan taimaka mun ki kira Musty, I want to say good night to him” Zehra ta tashi tare da fadin “As you wish” Zaune yake a waiting room yayinda yake dafe da kan shi. Abubuwa dayawa yake tunani a halin yanzu, daga farkon soyayyar shi da ita zuwa halin da Muhammad ya shiga a dalilinta zuwa lokacin da yayi sacrificing mishi ita zuwa shocking revelation din da iyayen su sukayi cewar Moha ba dan uwan su bane zuwa yanzu da ya ji tana fadin cewar bata daina son shi ba… Toh shima din har yanzu bai daina sonta bane?? Muryar ta ce ta daki qwalwar shi inda ya ji tace “Yaaya yace in kira ka..” Ko da ya dago kai ganin ta yayi tsaye da dan qaramin cikinta yayinda ta kasa kallon shi directly. “She can’t even look at me directly” He thought… Shi kam Mustapha bai taba ganin macen da ciki yayi ma kyau ba kamar Zehra… hmmmm… Wani ikon Allah kuwa wannan ita ce magana ta farko da ta fara hada su tunda ya dawo. Ajiyar zuciya ya saki sannan ya miqe suka koma cikin dakin. Ganin sun shigo tare ne ya dan yi murmushi a ranshi yace “hoping they end up together someday” ayyah… Ko da Mustapha ya qaraso wurin shi zama yayi a gefen shi yace “Moha gani, kana son wani abu ne??” Yace “no Musty, I just want to say good night ne” Ya dago mishi hannu alamar ya matso. Mustapha ya matsa suka yi hugging juna yayinda Muhammad din ya kai bakin shi saitin kunnen shi yace “I am sorry about what you saw earlier, tana qoqarin cika wani alqawari da ta dauka ne but na tabbatar ka ji da kunnuwan ka, she still loves you so please kamar yadda nace maka..” STORY CONTINUES BELOW Da sauri Mustapha yayi breaking hug din yayinda yace “not again Moha, we are done talking about this please” Zehra wadda take zaune kan gadon da aka shigo mata da shi kuwa sai kallon su take yi tana mamakin wacce magana suke yi da har suke neman yin fada. Gani tayi Mustapha ya zauna gefen shi ya shafa kanshi sannan yace “Let’s talk about this tomorrow, just get some rest for now..” Yace “okay, but ka zauna a nan” Ya nuna mishi kujerar da take dakin yayinda Mustaphan yace “I will, good night” Ya miqe sannan yayi mishi kiss a goshi ya koma kan kujerar ya zauna. Zehra ta nufi wurin shi tayi mishi kiss a kumatu tace “Good night Yaaya” Kumatun ta ya ja sannan yace “Good night to you Babe” yayinda ya shafa cikinta cikin muryar yara yace “good night my princess, Abbu loves you very very much” Daga Zehra har Mustapha sai da suka yi murmushi na yadda yayi maganar yayinda Zehra tace “your princess loves you too Abbu” Ko da ta koma bisa gadonta ta kwanta tana ta kallon shi har bacci yayi gaba da shi. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Kusan awa biyu kenan da Muhammad yayi bacci. Har yanzu bata yi bacci ba, shi kam Mustapha ya saba da sleepless nights don haka yana nan a zaune yana ta tunani kala-kala. Wayar shi ce tayi vibrating yayinda ya duba incoming call din. Gani nayi ya dan runtse idanuwa sannan ya bude yayi answering. Ji nayi yace “I am fine dear, Gashi nan yana bacci. Jikin nashi akwai sauqi sossai… Alhamdulillah” Ya dan yi shiru yana sauraronta sannan yace “Yes kar ki damu, idan na dawo insha Allah” Murmushi yayi yace “thank you very much.. take care, bye” Ko da ya gama wayar gani yayi Zehra tana ta juyi, da alama ba bacci take yi ba kuma da alama she heard his telephone conversation. Bata ankara ba ta ji yace “Hey what’s wrong, are you okay?” Zuciyar ta kuwa sai da ta buga because bata yi tunanin zaiyi mata magana ba. Ta kula tunda ya zo its like he has been avoiding her. Muryar ta qasa qasa tace “so many things went wrong, nothing has being okay..” Daga nan ya ji ta fara sheshekar kuka wanda ya tada mishi da hankali. Ji tayi yace “I am sorry… I am very sorry please ki daina kuka. Everything will be okay” Tace “how do you expect me to believe you?? how do you know that everything will be okay??” Yace “I am just hoping ne… You need to rest so please try and get some sleep kin ji??” Girgiza kai tayi tace “bazan iya ba… I have tried to do that for the past hours amma na kasa” Sossai ta bashi tausayi. Ya sani sarai abubuwan da suke faruwa a rayuwar ta sun yi mata yawa.. he never thought she is capable of enduring so much pain. At this point in time ma gani yake yi kamar ta fi shi qarfin hali. Ajiyar zuciya ya saki sannan yace “ki dinga karanta Bismillaah, Bismillaah, Bismillaah ‘A’oothu billaahi wa qudratihi min sharri maa ‘ajidu wa ‘uhaathir, you will feel better” Aikuwa nan da nan ta dinga maimaito addu’ar wanda a haka har bacci ya kwashe ta. Jin alamar tayi bacci ne ya saki ajiyar zuciya yayinda ya cigaba da tunani kala kala. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Gab da asuba ne bacci ya dan dauke Mustapha. Kamar a mafarki suka ji kakarin tari babu kakautawa. A razane dukkan su suka farka yayinda suka hango shi a kan gadon shi riqe da wuyan shi yana ta faman tari. Ko da suka matsa kusa da shi ji suka yi yace “both of you please forgive me” daga nan ya juya musu baya yayinda ya fara fadin “La ila ha illallah…” Basu ankara ba suka ji qarar EKG running flat…3 just like that???🙄7 Zehra wadda ta fara kuka hawa kan gadon tayi yayinda take girgiza shi ce tace “Yaaya.. meyasa ka danne hannun ka mai ciwo??” Mustapha wanda ya kasa motsi babu abinda yake fadi sai “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..” Jin salatin yayi yawa ne tayi saurin juyawa ta kalle shi tace “Baby me ya same shi??” Likitoci ne suka shigo dakin da sauri a dalilin EKG machine din da yayi signalling musu matsala. Daya daga cikin likitocin ne yayi saurin janye Zehra yayinda yace ma Mustapha “hold her please” Mustapha wanda jikin shi yake a sanyaye ji yayi Zehra ta maqale a jikin shi tana kuka yayinda take tambayar shi “wai me yake faruwa ne?? why are you not saying anything?? Yaaya ya suma ne??” Bata ankara ba ta ga likitocin suna qoqarin reviving heart dinshi da Defibrillator wanda kuwa after the fifth try ne suka yi giving up. Abinda Zehra ta ji a bakin daya daga cikin likitocin ne ya firgita ta matuqa. “time of death is….” Numfashin ta ne ya dauke yayinda ta tafi zata fadi Wanda Mustapha yayi saurin riqe ta. Da sauri likitocin suka koma kanta yayinda aka yi emergency da ita. Shi kuwa Mustapha yana nan tsaye jiki a sanyaye kamar statue yayinda yake kallon Muhammad kwance babu rai…. Dr. Albert ne ya dafa kafadan shi sannan yace “I am sorry” ya bi bayan sauran doctors din. Muhammad ya rasu?? Yanzu shikenan??? Ganin Nurses din suna qoqarin rufe shi da sheet ne yayi saurin fadin “hey, stop it” Daga nan ya nufi wurin Muhammad da sauri ya tallabo fuskar shi wanda tuni jikin shi ya saki yace “Hey brother, ka tashi daga baccin nan I beg you. Ka ga mutanen nan sunyi declaring dinka dead but you can’t die on me, not now please, I need you in my life, she needs you now more than ever, we all need you Moha…” Rungume shi yayi yace “ka tuna abinda kake fadi mun tun muna yara?? you will always watch my back.. you told me cewar you will always be there for me. Kaine best friend dina duk fadin duniyar nan… My superhero. Ya kake so in cigaba da rayuwa babu kai?? Please brother don Allah ka tashi…” Gani nayi wasu daga cikin likitocin sun dawo yayinda na ji daya daga cikin su yace “please contact the family..” Da qyar suka banbare Mustapha daga jikin Muhammad suka janye shi sannan suka fitar da shi yayinda yake ta surutai kala-kala. Har wannan lokacin kuwa ban ga single drop of tear ya fado daga idanuwan shi ba. he is definately in shock… ♤♤♤♤♤♤♤ ……and every soul shall taste it- DEATH4 In