ZEHRA CHAPTER 12
ABU-YAZEED RESIDENCE Kwance take a kan doguwar kujerar falon sama yayinda take kallon wani cooking competition a tashar Food Network.+ Yasmeen ce take ta wasa da teddy bear dinta a nan tsakar falon yayinda take ta damunta da tambayoyi wanda kuwa akan dole take amsa ta idan ba haka ba kuwa ta addabe ta. Kamar daga sama ta ji Yasmeen tayi ihu inda tace “Abbu oyoyo” Zuciyar Zehra ce ta buga amma ta matse. A yau sati daya kenan rabon da su hadu, sati daya kenan tana wasan buya da shi, sati daya kenan da ya fadi mata cewar bai daina sonta ba wanda yake ta sauraron amsar ta amma ta qi yarda ma su hada ido balle suyi maganar. Kwata-kwata bata picking calls dinshi.. messages ma saidai ta karanta kawai amma babu reply… why??? Wannan dai qamshin nashi mai rikita ta kamar kullum shine yake ta tashi. Ji tayi yace “hello my cute Princess. How are you??” Yasmeen wadda ta ruga wurinshi yayinda ya dauke ta ne tace “Fine Abbu, ina ta neman ka” Yace “sorry my Princess, nima ina ta zuwa bana ganin ki, kina school. Me kike yi??” Ta juya tare da nuna mishi teddy bear dinta tace “Ina wasa ne, kai ma zaka yi??” Yace “zanyi amma sai na zo gobe” Ta bata rai kamar zata yi kuka yayinda yayi saurin hugging dinta yace “haba princess don’t cry mana, yanzu Abbu zai je wani wuri ne idan kuma bai je ba za’a zane shi da bulala.. Kina so a zane shi??” Zehra wadda take sauraron su sossai Mustapha yake bata mamaki yadda yake wasa haka. Ita ko a da she thought he will be the kind da zai zama strict da yara considering his nature. Yasmeen wadda ta ji yace bulala kuwa tuni ta rude. Da sauri tace “Abbu bana so a zane ka” Yace “yauwa my Princess, gobe idan na zo sai muyi wasa kin ji? Infact zamu je mu siyo babban Teddy” tace “yeeeeey” sannan tayi mishi kiss a kumatu tace “ina sonka Abbu” Yace “nima ina son ki my Princess” tace “kana son Ammi ma??” Yana kallon fuskar Zehra yace “Ina bala’in son Ammin ki kuma bazan taba daina son ta ba..” Zehra dai gaba daya ta rude da jin kalaman shi, zuciyarta ce take ta bugawa as usual. Yasmeen ta sauka daga kan cinyar shi ta ruga wurinta tace “Ammi kina son Abbu??”3 Zehra wadda hankalinta yake a tashe gani nayi ta danna mata harara tare da fadin “ke tafi ki bani wuri..” Da sauri Mustapha yace “Haba My Angel, why shout at the poor child? Ai sai ki firgita ta.. Ya dan yi murmushi yace “Zan zo gobe in fita da Yasmeen, hope an bamu permission?” Miqewa tayi zata wuce daki wanda yayi daidai da zamewar hular kanta yayinda gashin kanta ya bayyana. Mustapha dai yana kallon gashin nata ne yace “beautiful…” Harara ta danna mishi yayinda ya kashe mata ido daya ya miqe yace “koma ki zauna abinki, zan je Gym ne nace bari in zo in duba ku… I am going” STORY CONTINUES BELOW Ya kalli Yasmeen yace “Princess mu je ki raka ni” Aikuwa a guje ta bi shi yayinda suka bar ta a tsaye tana ta kallon su har suka bar falon. Gani nayi ta fada kan kujera yayinda take ta sauke numfashi. Ban ankara ba na ga hawaye suna bin fuskar ta. Ita dai gaba daya dawowar Mustapha ya birkita mata qwalwa, yau sati daya kenan da ta ji labarin halin da ya shiga a dalilinta tsawon shekaru, sati daya kenan da ya fadi mata he still loves her, why is she not happy?? hmmm… 🤔🤔 Gani nayi ta tashi da sauri ta nufi window tana hangen shi yayinda yake tsugunne a kusa da motar shi yana ta sauraron Yasmeen, da alama list take yi mishi na abubuwan da zai siyo mata. Hannu ya sa a aljihun shi ya zaro Chocolate ya miqa mata, bayan ta karba ne tayi mishi kiss a kumatu yayinda ya miqe tsaye. Daga mishi hannu tayi alamar bye bye wanda shima ya daga mata yana murmushi sannan ya bude mota ya shiga. Mustapha wanda ya shiga motar shi ya hangota ta window amma dayake motar shi tint ce bata kula da ya ganta ba. Murmushi yayi yace “I am not losing you for anything or anyone this time around My Angel” Ni kuwa nace da kyau Musty👍👍3 ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Washegari…. Anty ce zaune a falonta tare da Khadeeja suna ta hira. Basu ankara ba suka ga masu aiki suna ta shigowa da kayan wasan yara kala-kala da kuma kayan ciye-ciye, kai kace shago za’a zuba su. Anty sai salati take ta yi yayinda tace “yau an shiga uku, ya fara haukar tashi da ya saba kenan, toh yanzu ina za’a zuba wadannan kayan fisabilillahi??” Khadeeja kuwa sai kwasar dariya take yi. Mustapha ne ya shigo riqe da Yasmeen yayinda na hango wata doguwa, kyakyawa fara sol tamkar balarabiya tana biye da su. Sanye take cikin doguwar rigar jallabiya wadda ta dace da ita. Sossai tayi kyau. Ko da suka qarasa shigowa gani nayi yarinyar ta qarasa wurin Anty cikin fara’a ta duqa har qasa tace “Anty ina wuni” Anty wadda take murmushi tace “lafiya lau, ya gida?” tace “lafiya Anty” Anty ta kalli Mustapha cike da mamaki tace “saidai ban gane ta ba Mustapha” Yana murmushi yace “Sareenah sunan ta Anty, sister din Adda Ummie” Dayake Adda Ummie ta zo har gida sun gaisa da su Anty duk sun san ta. Tana murmushi tace “oohhh, Allah sarki. Ku dai ‘yan gidan ku duk kyawawa tabarkallah” Sareenah tayi murmushi. Khadeeja ce tace “Ina wuni” yayinda tace “lafiya lau” Gani suka yi tana dan waige-waige sannan ta kalli Mustapha tace “where is she??” Anty tace “Who?? Zehra?? Tana daki, duk yau ma sau daya na ganta a gidan” Khadeeja ce tace “bari in kira ta” Zaune take a kan gadon dakin ta yayinda take kallon wani abu a wayar ta. Khadeeja ce ta qwanqwaso ta shigo dakin ta qaraso wurinta ta zauna kan gadon. Gani nayi tayi shiru tana kallon ta, murmushi tayi sannan a ranta tace “aikuwa sai na tabbatar da wani abu yanzun nan” Ji tayi Zehra tana fadin “lafiya kika zo kika zauna mun babu Magana??” STORY CONTINUES BELOW Khadeeja tana murmushi tace “lafiya lau, Dama Ya Musty ne ya zo tare da budurwar shi shine….” Tun kafin ta qarasa maganar ta zuciyar Zehra ta buga wanda har sai da ta dafa qirjinta. Cike da masifa tace “toh me ya ruwana da su?? Deeja tashi ki fita daga dakin nan before I slap you” A rude Khadeeja tace “kiyi haquri, qila fa ba budurwar shi bace amma dai na ji kamar sunan ta Sareenah..” Bata rufe bakin ta ba ne Zehra ta sauka daga kan gadon ta shige bathroom, da alama kuka take yi. Khadeeja tayi murmushi tace “and she said she doesn’t love him anymore.. lallai ma Anty Zee” ta sauka daga kan gadon ta wuce ta fita. Ko da ta dawo ta tarar suna ta hira suna dariya. Kai tsaye tace “Bacci take yi” Mustapha ne yace “its okay Deeja” Sareenah tace “oooh, aikuwa na so ganin ta wallahi” yace “don’t worry zaku hadu kafin ki koma” hmmmm🤔 Sai wuraren qarfe shidda ne suka bar gidan. Bayan sun fita ne Khadeeja ta ba Anty labarin abinda tayi ma Zehra da yadda ta nuna kishi qarara. Anty dai dariya ta dinga yi tace “Ai na rasa gane kan Zehra wallahi, tayi aniya dai a janye shi. I am very sure wannan yarinyar son Mustapha take yi domin kuwa daga yadda take yi mishi magana kasan akwai soyayya” Khadeeja ce tace “amma dai kyakyawa ce gaskiya.. kamar balarabiya” Anty tana murmushi tace “tabbas Iyayen su sun haifi kyawawan yara” ************ Da daddare kamar kullum Zehra ta nufi dakin Yasmeen don kimtsa ta tayi bacci. Sossai tayi mamakin yawan sabbin kayan wasan da ta gani, wata Teddy din ma ta fi Yasmeen din girma. Yasmeen wadda take ta wasa ce tace “Ammi kin ga kayan da Abbu ya siyo mun?” Zehra ta qarasa wurinta ta zauna yayinda tace “na gani Yasmeen, sun yi kyau” Ta janyo ta jikinta ta rungume ta sannan tace “gaya mun ina da ina kuka je??” Yasmeen tace “mun je gidan su Anty Shayina sai muka je muka sha ice cream sai kuma muka hau lilo, Abbu ya tura mu..” Sossai ran Zehra ya baci yayinda duk ta bi ta shiga damuwa. Nan da nan yanayin ta ya canza gaba daya yayinda tayi regretting tambayar yarinyar da tayi wanda kuwa take ta zubo mata labarin abinda ya faru. Ji nayi tace “toh ya isa haka nan, mu je inyi miki wanka sai in karanta miki story dinki, dare yayi kuma akwai school gobe” Aikuwa har Yasmeen tayi bacci zuciyarta sai tafasa take. Bayan ta fito daga dakin Yasmeen zata nufi dakin ta ne na ji tace “I hate you”1 kuma dai??🤔🤔 ♤♤♤♤♤♤♤ Kusan sati daya kenan da Mustapha yayi tafiya zuwa Port Harcourt a dalilin wani meeting da za’a yi na sojoji. Asali ya je ne don ya wakilci wani Ogan su Brigadier General Yusuf Tanko wanda yayi tafiya zuwa America. Tsawon sati daya Zehra bata je ofis ba. Hidaya kuwa har gida ta zo don ganin abinda yake faruwa domin kuwa dukda ta fadi mata komai lafiya a waya bata amince ba… its so much unlike her. Physically kam she is okay amma kuma da alama mentally she is not. Tambayar duniya Hidaya tayi mata amma tace she is okay. STORY CONTINUES BELOW Su Anty dai fita batun ta suka yi domin kuwa sun tabbatar damuwar Zehra a yanzu bai wuce Mustapha ba. Sun sani sarai kamar yadda har yanzu yake sonta itama tana son shi, sun sani sarai qarya take yi da take fadin bata son shi. Toh amma tambaya anan abinda suke tunani haka ne?? Idan har haka ne then why is she pretending?? ♤♤♤♤♤♤♤ A yau babu kowa a gidan, Khadeeja ta tafi school yayinda Anty ta je gidan qawarta. Babu abinda kake ji a gidan banda motsin masu aiki. Zehra ce ta sauko hankali a tashe tana ta kuka. Sanye take cikin dinkin doguwar rigar atamfa, kanta ko dan kwali babu yayinda gashinta yayi buzu buzu. Gani nayi ta nufi hanyar fita gidan wanda kuwa a daidai porch suka yi karo da juna. Mustapha wanda ya ga tana qoqarin wuce shi ne yayi saurin riqo hannun ta yace “hey ina zaki je haka?? Why are you crying??” Zehra wadda har numfashin ta yana neman daukewa ne tace “Yasmeen…” Hankalin shi a tashe yace “me ya same ta??” “an kira ni daga school din su wai batada lafiya an kai ta clinic” Gani nayi ya janyo ta yana qoqarin komawa cikin gida da ita wanda hakan ya bata mamaki. Tana qoqarin qwacewa ne tace “baka ji abinda na ce maka ba ne?? ka qyale ni in je in dubo ta” Mustapha dai bai tsaya ba sai da suka shiga falon gidan sannan ya nuna ta yace “a haka zaki je?? Kin ga yadda kika fito kuwa?? No veil, no shoe…” Baraka ce da ta shigo falon ta duqa har qasa ta gaishe shi, bai amsa ba yace “dauko mata gyalen ta da takalmin ta” Da sauri Baraka ta haura sama yayinda ya juyo yana kallonta. Gaba daya ta birkice wanda har ta bashi tausayi. Ji nayi yace “calm down she will be fine Insha Allah, idan kinyi receiving news irin haka you shouldn’t panic, instead pray” Tana kuka tace “I was confused ne.. I don’t want to…” Yace “ssssshhh, I said she will be fine Insha Allah.. just relax” yayinda ya hada hannuwan ta biyu yana bubbugawa alamun yana lallashin ta. Bayan Baraka ta kawo mata takalman ne ta sanya yayinda ta karbi gyalen ta yafa. Gani nayi ya sa hannu ya janye gyalen sannan ya juya mata shi daidai ya yafa mata. Zehra dai saboda rudewa ashe inside-out ta yafa gyalen. Ko da suka fita ji nayi yana tambayar ta “ina Anty fa??” yayinda take ta yi mishi bayani… Ko da suka isa school din sun tarar an ba Yasmeen taimakon gaggawa, basuyi wata wata ba suka dauke ta suka wuce asibiti da ita. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ NATIONAL HOSPITAL ABUJA Yana riqe da Yasmeen wadda jikin ta yayi matuqar zafi yayinda take biye da su tana ta rusa kuka. Da sauri Nurses suka karbe ta aka shigar da ita yayinda jikin Zehra ya bi yayi sanyi, sai kuka take rusawa Kamar wadda aka ce ta mutu. Mustapha wanda yake ta lallashin ta ya fiddo wayar shi yana qoqarin kiran Zain ne ya ji tayi hugging dinshi yayinda take fadin “Baby I don’t want to lose her… please tell me she is going to be okay…” STORY CONTINUES BELOW Baby???🤔 Sossai wani shock ya ratsa jikin shi a dalilin wannan hug din da tayi mishi. Gaba daya jikin shi yayi sanyi. Ji yake yi kamar yayi wrapping hannuwan shi around her wanda kuwa bazai taba sakin ta ba har abada. Ya sani sarai Zehra ba cikin hayyacin ta take ba. Gani nayi ya saki ajiyar zuciya sannan ya banbare ta daga jikin shi ya riqe hannunta guda biyu yace “hey.. repeat after me..” Yana karanto addu’o’i yayinda take maimaitawa… da haka kuwa har tayi calming down. Kafadarta ya dafa sannan ya dan duqo saitin fuskar ta yace “she will be fine, just relax kin ji??” Ta daga mishi kai alamar “toh” Daga nan ya fiddo handkerchief daga aljihun shi ya fara goge mata hawayen fuskar ta. Dr. Malika wadda ta kasance Paediatrist din asibitin ce tace “Excuse me” Da sauri suka juyo wanda kuwa ganin Zehra ne tayi murmushi tace “No wonder, ni dai ina ta kallon yarinyar kamar na santa, ashe neice din Dr. Zain ce” Zehra wadda ta nufi wurin Dr Malika ce tace “how is she?? please can I see her?” Dr. Malika tace “she will be fine, it’s nothing serious. Zamu ajiye ta anan don akwai tests da zamu yi running akan ta, yanzu haka tana bacci but zaku iya ganin ta” A guje Zehra ta shige dakin Yasmeen yayinda Mustapha yace “thank you Doctor” sannan ya bi bayan ta. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Gaba dayan su suna dakin da aka kwantar da Yasmeen suna ta hira. Tun da rana Papa da Daddy suka zo suka duba ta briefly suka wuce. A wannan lokacin kuwa Yasmeen din tana kwance akan cinyar Zehra. Hannunta dauke da drip yayinda ake ta drama da ita akan ta ci abinci amma tace bazata ci ba. Qwanqwaso qofar aka yi yayinda ma’aikatan asibitin suka dinga shigowa da ledoji suna ajiyewa. Anty ce tace “toh bissimillah.. sarkin kashe kudi” Su Mummy kuwa sai dariya suke yi. Bayan sun ajiye sun fita ne Mustapha yayi sallama ya shigo. Ko qofar bai qarasa rufewa ba Yasmeen tace “Abbu oyoyo” yayinda ta fara yunqurin tashi. Da sauri ya qarasa wurinta ya zauna kan gadon yace “hey princess, how are you?” tace “fine” Yace “ina yake yi miki ciwo yanzu??” Ta nuna mishi drip din hannun ta tace “Abbu bana son wannan” ya dan yi murmushi yace “yi haquri Princess, idan aka cire bazaki warke ba muyi wasa… ko baki so muyi wasa??” Da sauri tace “ina so Abbu” Haka suka cigaba da hira yayinda Su Mummy suka dinga kallon su cike da sha’awa. Ita dai Zehra kallon su kawai take yi yayinda take mamakin strong bond din da yake tsakanin su wanda ko ita da ta haifo ta iyakar bond din kenan. Hatta abinci da ta qi ci ana ta drama da ita tun dazu, a yanzu da Mustapha ya bata sossai ta ci. Suna nan zaune ne Dr. Malika ta shigo tare da nurse. Bayan ta gaishe su ne tace “test result din ya fito” ta miqa ma Zehra takardun yayinda tace “its just fever” ta qarasa wurin Yasmeen tace “how are you feeling princess?” Tace “fine” Daga nan ta kalli Zehra tace “akwai allura da za’a yi mata…” Tun kafin ta rufe bakinta kuwa Mustapha yace “What?? wannan ‘yar qaramar yarinyar?? gaskiya baza’a yi mata allura ba. kawai ku bata magani ta sha ai duk daya ne..” STORY CONTINUES BELOW Su Anty ne suka fashe da dariya yayinda Dr. Malika tace “kayi haquri Sir, the thing is wannan allurar dole ce.. zai fi saurin putting effect a jikinta compared to maganin” Gani yayi Nurse din ta matso yayinda take qoqarin janyo ruwan allurar. Ita kuwa Zehra tana ta kallon shi yayinda ta ga ya qura ma hannun nurse din idanuwa cike da tsananin damuwa kamar shi za’a yi ma allurar. Labarin da Muhammad ya taba bata akan abinda yayi ma nurse ta tuno. Aikuwa bata San lokacin da yayi murmushi ba. Ko da Nurse din tace “Sir can you please hold her steady??” Ran shi a bace ya kalli Nurse din yace “what?? common you must be kidding” Zehra ce ta koma kusa da su tayi positioning Yasmeen yadda ya kamata. Basu ankara ba suka ga yayi saurin miqewa zai fita har Yasmeen tana fadin “Abbu please come” Yace “ina zuwa princess” Bai qarasa fita ba ma aka gama mata wanda kuwa ko kuka bata yi ba. Mummy wadda take dariya tace “toh ai sai ka dawo tunda an gama mata” Cike da mamaki ya juyo yace “an gama??” Gani yayi Yasmeen din tana kallon shi dukda ta bata rai amma dai bata yi kuka ba. Anty ce tace “su Abbu an ji kunya” Fadeela ce tace “wai Ya Musty meyasa baka son Allura?? akwai zafi ne?” Hararar ta yayi yayinda suka dinga yi mishi dariya. Haka ya dawo wurin Yasmeen cike da damuwa yace “Princess akwai zafi??” kwanciya tayi a jikin shi tace “No Abbu” Sossai yarinyar ta bashi mamaki sannan ta birge shi yayinda su Fadeela suka dinga yi mishi tsiya. Can wuraren qarfe goma na dare ne su Mummy suka tafi gida. Anty da Fadeela sun so su kwana amma Zehra tace su tafi kawai tunda khadeeja tana nan. Mustapha bai bar asibitin ba sai kusan qarfe sha biyu na dare. Duk zaman da yayi kuwa ko magana daya basuyi ba da Zehra, asali ma da Zain sukayi ta hira. Ita dai Khadeeja tana mamakin Zehra a yanzu, Har satan kallon Mustapha ta ga tana yi amma kuma idan ance tana son shi sai tace wai bata son shi. hmmmm… ♤♤♤♤♤♤♤ Washegari da yamma ne ya shigo asibitin. A lokacin kuwa su Mummy basu dade da komawa gida ba. Qwanqwasa qofar dakin yayi ya shigo. Zaune take a kan gadon Yasmeen wadda take ta bacci yayinda ya ga wani dattijo zaune a kan kujera suna ta hira har tana dariya.4 toh fa… Zehra dai tunda Mustapha ya shigo hankalin ta ya tashi amma kuma ta matse. Gani nayi ya tsaya ya qare mishi kallo tas sannan ya kalle ta. Ji suka yi yace “Sannu Baba, daga ina?” Zehra dai kadan ya rage ta fashe da dariya amma a kan dole ta matse. Alhaji Abdullahi Bungudu kuwa yana kallon Mustapha yace “na zo gaida Yasmeen ne…” Mustapha wanda ya murtuke fuska a yanzu yace “a matsayin ka na wa??” Cike da mamaki Alhaji Abdullahi ya kalli Zehra wadda ta zama confused yace “Zee baki fadi ma yayan naki about us bane??” Kut..🤔 Cike da tsananin mamaki Mustapha yace “what??? Yaya??” ya nuna su biyu sannan yace “about you??” Zuciyar shi ce take tafasa yayinda wani azababben kishi ya taso mishi. Runtse idanuwa yayi ya bude sannan yace “Baba, tashi ka bar nan” Zehra ce tace “meye haka?? Akan wane dalili zai tafi?? you should be the one to go not him…” Kafin ta rufe bakin ta kuwa ya nuna ta da yatsa yace “Just shut up..” Ya kalli Alhaji Abdullahi yace “da kake kira na yayan ta ka ga munyi kama ne?? zaka dai iya cewa mun dace da juna sabanin kai da ita” Ya qara murtuke fuska ya cigaba da fadin “..kawai ka tashi ka tafi kafin ran ka ya baci” Alhaji Abdullahi dai ganin Mustapha yana iya yi mishi rashin kunya ne ya tattara sauran girman shi ya miqe tare da kallon Zehra rai a bace yace “toh Zee ni na tafi, Allah ya bata lafiya” Mustapha yace “kar ka sake dawowa, She is TAKEN” Ko da Alhajin ya fita gani nayi Zehra ta tashi da sauri ranta a bace zata bi shi. Da zafin nama ya fizgo ta yayinda ya hada ta bango. Tuni idanuwan shi sunyi jajawur yayinda yake ta huci. Zehra kuwa ta tsorata a yanzu domin kuwa wani azababen kishi ta hango a idanuwan shi. Jikinta ne yake ta rawa. Ita kam ta sani sarai tun da can Mustapha yana da bala’in kishi akan ta don kuwa har masu aikin gida idan ya ga tana yi musu fara’a yana jin haushi sossai. Ji tayi yace “where the hell do you think you are going to?” Cikin masifa tace “leave me alone, zan je in bashi haquri ne, abinda kayi mishi ai cin fuska ne” Cike da mamaki Mustapha yace “yanzu tsakanin ni da shi wa yakamata ki ba haquri??” Kai tsaye tace “shi yakamata in ba ma haquri tunda shi kayi ma…” Bata qarasa ba na ji tace “oouch” a dalilin matse mata hannu da yayi. Tana neman yin kuka ne tace “you are hurting me…please stop” Fuskar shi a murtuke yayinda yake kallon ta cikin ido yace “Exactly what you are doing to me. You are hurting me… so just stop” Bai ankara ba ya ga hawaye na ta bin fuskar ta kamar an saki famfo. Da sauri ya saki hannun ta tare da shafa kan shi da hannuwan shi guda biyu yace “Look I am so sorry, me kike so inyi?? Wallahi I love you My Angel, I never for once stopped loving you. How do you expect me to see you with this old man and not react??” Tana kuka tace “ni ka qyale ni…” Muryar Yasmeen suka ji tace “Abbu, Ammi meyasa kuke fada??” Da sauri suka juyo suna kallonta yayinda Zehra tayi saurin share hawayen fuskarta sannan ta nufi wurinta. Shi kuwa Mustapha gaba daya zuciyar shi ce take tafasa. Gani nayi ya nufi qofa ya bude ya fita yayi tafiyar shi wanda yana ji Yasmeen tana kiran shi amma ya kasa waigowa balle ya amsa kiran nata. Gani nayi Zehra ta rungume Yasmeen yayinda hawaye suke ta qara gangarowa daga idanuwan ta. ♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Kwance yake a kan cinyar Mummy yayinda ranshi yake a bace. Idan ka kalli fuskar shi zaka rantse ya kwana uku ma bai yi bacci ba.+ Mummy da Fadeela kuwa basu dade da dawowa daga asibiti ba inda suka dubo jikin Yasmeen. Ji nayi Mummy tace “toh yanzu kai shikenan sai kayi fushi saboda kawai ka ga wani ya zo wurinta?? Haka ake yi??” Fadeela wadda take ta matse dariya a ranta tace “hmm, da ya san suna nan da yawa ashe haukacewa zai yi kenan” Ji suka yi yace “toh Mummy ni ya zanyi?? Kin ga wulaqancin da tayi mun ne??” Ya tashi zaune yana kallon Mummy yace “kuma fa wallahi bazan yi kaffara ba mutumin ya kusa shekarun Daddy da Papa, ko bai kai su ba kadan ne” Fadeela wadda take ta matsewa ce ta fashe da dariya wanda kuwa ya dago kai ya harare ta yace “duk laifin ki ne Dee, akan wanne dalili zaki barta tana ganin wannan tsohon mutumin??” Fadeela wadda take dariya tace “toh ni ya zanyi da ita?? Wallahi Zee ta canza yanzu, taurin kanta yayi yawa, ga masifa na bala’i” Mummy ce tace “toh yanzu dai haquri zaka yi ka lallaba ta tunda dai ka ga yanzu tana da right din zaben mijin aure sabanin wancan lokacin da iyayen ta suma suna da iko. This is not the time to get angry, ka ji??” Komawa yayi ya kwanta a kan cinyarta yayinda ya rufe idanuwan shi. Sossai zuciyar shi take tafasa. Ji yayi Mummy tace “aikuwa kayi qoqari ka je ka dubo Yasmeen don tana ta tambayar ka” Fadeela tace “eh wallahi, da qyar ta ci abinci ma fa… wai sai kai ne zaka zo ka bata. Hankalin Amminta kuwa duk ya bi ya tashi” Idanuwan shi a rufe yace “toh duk ba ita ta janyo tashin hankalin ba??… dagaske idan na qara ganin mutumin nan tare da ita sai na sa an kama shi” Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Mummy tace “akan wane dalili za’a kama shi Mustapha??” kai tsaye yace “Child Abuse Mummy” Qara fashewa suka yi da dariya yayinda Fadeela tace “toh fa, ashe akwai case babba a cikin garin Abuja, don Allah ka rufa mana asiri. Zehra is almost 26years old fa… just few months to go, she is not a child” Girgiza kai yayi yace “wallahi yarinya ce akan wannan mutumin, I am very sure last born din shi ta grime ta……” Haka dai ya dinga fada yayinda suka cigaba da lallashin shi amma fa sun sha dariya. Fadeela dai ta tabbatar akwai case domin kuwa ta san cewar masu neman Zehra yawa ne da su. ************ Dayake dai Mustapha yayi missing Yasmeen sossai akan dole ya je asibitin ya gan ta. Aikuwa tayi murna sossai, tunda ta maqale mishi ta qi sakin shi. surutu kuwa ya sha shi. Da alama kuma sauqi ya samu gareta don haka ne ma a ranar da daddare aka sallame ta. Da qyar Zehra ta amince ta bi shi ya kai su gida. A tunanin ta zai yi mata magana amma har suka isa gida bai ce mata komai ba. Da alama dai yayi fushi da ita. Asali ma hira suka dinga yi da Yasmeen. Washegari kuwa kayan ciye-ciye dayawa ya aiko ma Yasmeen wanda kuwa kamar koda yaushe Anty tana ta fada akan yawan kayan. STORY CONTINUES BELOW Sossai ran Mustapha ya baci da Zehra, maimakon ya cigaba da lallashin ta kamar yadda Su Mummy suka bashi shawara sai yayi watsi da ita dukda kuwa kullum yana zuwa gidan don ganin Yasmeen wanda a kullum yana kan siyo mata kaya kala-kala. Ita kam Yasmeen bala’in son Mustapha take yi. ♤♤♤♤♤♤♤♤ ABU-YAZEED RESIDENCE Wuraren qarfe tara saura na dare yayi horn a gidan yayinda gate man ya bude mishi. Cike da girmamwa ya duqa tare da daga mishi hannu alamun gaisuwa wanda kuwa yayi mishi horn kamar kullum. Mustapha wanda yayi parking motar shi kuwa gani nayi ya qura ma wata mota qirar Lexus Jeep baqa ido. Shi kam bai taba ganin wannan motar a gidan ba. Ko da ya fito ji nayi yace “Papa ya siyo sabuwar mota ne??” bai qarasa rufe bakin shi ba ya kula kamar akwai mutane a ciki. Gani nayi ya kira gate man din gidan yace “su waye a cikin motar can??” cikin ladabi yace “Hajiya qarama ce tayi baqo..” A razane ya kalli gateman din yace “baqo??” Kafin gateman din yayi Magana kuwa Mustapha ya nufi wurin motar. Qwanqwasa glass din motar yayi. Zehra wadda take zaune a cikin motar sossai ta razana yayinda hankalinta yayi matuqar tashi. Ita kam ta sani sarai ta shiga uku da zafin kishin Mustapha. Alhaji Idris Balarabe ne ya sauke glass din yayinda ya gan shi tsaye rai a bace. Miqa mishi hannu yayi yace “ashe yayan mu ne, ya gida??” Mustapha wanda zuciyar shi take tafasa ne yace “me kake yi da matar mutane a motarka?” Alhaji Idris ya kalli Zehra wadda ta zaro idanuwa yace “My Zee dama kinyi aure ne ban sani ba??”9 Ran Mustapha in yayi dubu ya baci a yanzu… A gaban shi wani qato yake kiranta ‘my Zee’???? Zehra ma kasa Magana tayi saboda rudewa. Mustapha ne yace “kai dattijo ka bar gidan nan yanzu kafin ran ka ya baci” Alhaji Idris yace “Yanzu kai don baka da kunya shine zaka kalli idanuwa na kayi mun irin wannan…” Mustapha wanda bai bari ya qarasa maganar shi ba yace “kai kana da kunya ka zo neman yarinya ‘yar cikin ka?? idan baka sani ba tana da miji don haka kar ka sake zuwa gidan nan.. Ja motarka kawai ka tafi” Gani suka yi ya zagaya ya bude qofar Zehra sannan yace “fita” Zehra wadda ta cika da bacin rai ta harare shi tare da fadin “bazan fita ba” Gani nayi ya duqo da alama daukar ta zai yi wanda kuwa nan da nan ta daga hannu tace “wait, zan fito”3 Aikuwa tana fita ta ture shi tare da fadin “I hate you” sannan ta ruga a guje ta shige gida yayinda take kuka. Mustapha wanda ran shi yake a bace ya juyo ya kalli Alhajin yace “idan ka qara zuwa gidan nan sai na sa an kama ka” Ya juya ya shige gidan yayinda ya bar Alhajin cike da tsananin mamaki. Ji nayi yace “ai dole in haqura da ke Zee” daga nan kuwa ya ja motar shi ya bar gidan. Anty wadda take zaune a falo kuwa ganin shi tayi ya shigo ran shi a bace yayinda yace “tana ina??” Anty dai ko da ganin yadda Zehra ta shigo ta san akwai matsala don haka ne tace “tana dakin ta” Daga nan bai ce komai ba ya bi ta dakin nata. STORY CONTINUES BELOW Kwance take ruf da ciki kan gadon ta tana ta kuka. Ko da ya shigo dakin yayi mamakin ganin yadda take ta kuka saboda abinda ya faru. A ranshi ne yace “does she like the old man so much da har take wannan kukan haka?? Does that mean bata sona kuma?? or is she doing this just to get back at me for what happened years ago??” Gani nayi ya shafa kan shi da hannuwan shi biyu yayinda ya saki ajiyar zuciya. Zehra dai tunda ya shigo ta san cewar ya shigo domin kuwa qamshin turaren shi duk ya cika dakin. Ji tayi yace “yanzu don na kori wancan tsohon mutumin shine kika dawo nan kina zubar da hawayenki??” Da sauri ta sauko daga ka gadon cike da masifa tace “toh akan wane dalili zaka kore shi?? me ya ruwan ka da shi??” Cikin sanyin murya yace “Haba Angel, fisabillilah me zakiyi da wadannan tsofafin?? Don Allah ki daina sauraron su??” Tace “Ni ka qyale ni, Ka daina sa mun ido ka tafi wurin taka budurwar mana…”2 Cike da mamaki yace “budurwa ta kuma??” ta danna mishi harara tace “Eh budurwar ka wadda kuke zuwa kuna shan Ice cream kana tura ta a lilo….” Shiru yayi yana tunani wanda kuwa bata ankara ba ta ji ya fashe da dariya. Wannan dariyar kuwa ta qara qona mata rai. Hannun ta ya kamo sannan yace “Haba Angel, Sareenah is just a friend. Kin ga ko ranan fa na kawo ta ku gaisa, she wanted to meet you but you were sleeping. Yanzu haka sun tafi Adamawa but idan ta dawo tace zata zo ku gaisa” Zehra dai qoqarin qwace hannun ta take yi amma ta kasa. Zuciyar ta kuwa sai zafi take yi a dalilin jin wai wata Sareenah zata zo su gaisa. Ji tayi ya cigaba da fadin “Hey, I am in love with one person a duk fadin duniyar nan… YOU my angel kuma na san kema kina so na har yanzu, please ki daina bamu wahala ki amince da..” Fizge hannun ta tayi tace “leave me alone” daga nan ta juya ta shige bathroom ta sa key. Runtse idanuwa yayi ya bude sannan ya nufi bakin qofar bathroom din yace “hey I am sorry, please come out. Ni na tafi… I love you. Good night” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ ZAIN ABU-YAZEED RESIDENCE A yau Saturday Zehra ta yini a gidan Fadeela wanda kuwa suka sha hira. Fadeela ce take ta bata labarin fadan da Mustapha ya dinga yi na Alhajin da ya gansu tare a asibiti. Zehra wadda bata damu ba ta bata labarin wanda ya tarar a gida. Aikuwa Fadeela ta sha dariya. Zehra ce tace “duk zai yi ya gama, ni kam bana son shi.. kawai ya haqura ya qyale ni” Fadeela wadda a kullum take daukar zancen Zehra da wasa tace “wai Zee ni ban fahimce ki ba, wai tsakanin ki da Allah da gaske kike yi ba kya son Ya Musty kuma?? Even after hearing what he has gone through a dalilin ki??” Zehra tace “precisely the reason why Dee, I don’t love him anymore kuma bazan taba auren shi ba” toh fa🤔 Jin haka kuwa Fadeela ta ja bakin ta tayi shiru domin kuwa kowa ya sani cewar qarya take yi. koma dai meye ta san cewar they will settle their differences.3 ************** Bayan Sallan Isha’I Zain da Mustapha suka shigo gidan. Zaune suke a dinning suna Dinner, tun kafin su qarasa shigowa ta ji qamshin turaren shi. Gaba daya sai ta ji dama tun da yamma tayi tafiyarta kamar yadda tayi niyya wanda Fadeela ce ta matsa mata akan lallai ta tsaya tayi dinner tunda one of her favourites za’a dafa. STORY CONTINUES BELOW Fadeela tana ganin shi tace “Na shiga uku Ya Musty ya baka fadi mun zaka zo ba? gashi worst food dinka aka yi” Zehra wadda take cin tuwon ta ko daga kai bata yi ba ta kalle shi balle ta gaishe shi. Shi kam tunda ya shigo hankalin shi gaba daya yana kan ta. Sanye take cikin wani pencil jeans da wata top mai zafin gaske sannan gashin kanta a bude yake wanda kuwa kitson Kalban da tayi ya sauka a kafadarta da bayan ta, Tayi masifar kyau. A wannan lokacin kuwa ji yake yi kamar ya qarasa wurinta yayi hugging dinta very tight yayi ta baza mata kisses domin kuwa she was looking so irresistible. Ajiyar zuciya ya saki sannan ya ja Kujerar da take gefenta ya zauna yayinda ya kafa mata idanuwa. Wannan abu kuwa bai yi mata dadi ba domin kuwa duk ya rufe ta da qamshin turaren shi wanda yake sa tana zama weak sannan babban matsalar ta a yanzu shigar da tayi.. Ita kam da ta san zai shigo gidan a wannan lokacin da ta sanya after dress dinta. Gaba daya ta rude domin kuwa kallonta yake tayi babu ko qyaftawa. Shi kuwa ya kula da cewar zaman shi very close to her is making her restless wanda ya kula hatta abincin ta kasa cigaba da ci. Murmushi yayi yace “My Angel how are you, kin yi kyau sossai” Ajiyar zuciya ta saki yayinda zuciyarta take ta bugawa. Ji tayi yace “Na ga kin daina cin abincin ki, ko in baki da kaina ne??” Zain da Fadeela ne suka fashe da dariya yayinda Fadeela tace “Ya Musty the Romeo” Hararar ta yayi yace “shut up..” Tace “sorry Sir, ni yanzu ya zamu yi da kai? Ko zaka yi haquri ka ci tuwon?” Ya kalli plate din Zehra ya girgiza kai yace “da dai Angel dina zata bani a baki da na haqura na ci…” Wannan karon kuwa Zain wanda yake dariya yace “toh ai kai Babyn ta ne, na tabbatar zata baka” Gani nayi Mustapha ya sa hannu ya matsar da gashinta wanda ya sauko ya rufe mata gefen fuska, yana mayar da shi bayan kunnen ta ne yace “wannan ai yana hana ni kallon fuskar Angel dina da kyau, dukda dai side view aka bani damar gani..” Cikin muryar tausayi yace “…but I am not complaining” Zain da Fadeela dai sai kwasar dariya suke yi yayinda suke mamakin abinda Mustapha yake yi. A da idan za’a ce maka zai iya flirting da mace haka zaka rantse qarya ne. Zehra dai suma ne kawai bata yi ba a wurin domin kuwa gaba daya zaman Mustapha a kusa da ita da yadda yake flirting da ita ya sakar mata muguwar kasala. Ko da ya matsar da gashin sai da ya dan shafa fuskar ta wanda kuwa da gangan yayi. Wayar ta ce tayi ringing wanda na ga yayi saurin kallon fuskar wayar. Gani nayi ran shi yayi masifar baci ganin sunan ‘Alhaji 5’ Zehra wadda ta dauki wayar kuwa amsawa tayi yayinda ta miqe tsaye zata bar dinning din wanda dama neman hanyar guduwa take yi. Ji suka yi tace “Alhaji ina wuni…” Aikuwa bata qarasa rufe bakinta ba ta ji an fizge wayar da qarfin gaske wanda kuwa ta juyo a gigice cike da tsananin mamaki. Ganin Mustapha tayi a tsaye riqe da wayar a hannun shi yana huci wanda kuwa basu ankara ba suka ga ya buga wayar a tiles yayinda ta fashe.3 Hakan kuwa ya razana Zehra matuqa, Zaro idanuwa tayi sannan ta bi wayar da kallo. Zain da Fadeela kuwa kallon su kawai suke cike da fargaban abinda yake faruwa. Zehra dai ganin yadda Mustapha ya fasa mata waya ran ta yayi masifar baci. Dago kai tayi ta kalle shi cikin ido wanda kuwa da sauri ta kawar da idanuwan ta domin abinda ta hango a idanuwan nashi bazata iya fassara shi ba. Cikin masifa tace “akan wane dalili zaka fasa mun waya?. What’s your problem??…” Kafin ta rufe bakinta ya nuna ta da yatsa yace “look na gaji da wannan Game din naki, why are you treating me like this?? Akan wane dalili zaki dinga bata mun rai??” Ya matsa daf da ita yace “wallahi idan baki rabu da wadannan dattijan ba duk sai na sa an kama su an kulle” Fashewa tayi da kuka, Kuka sossai ta shiga yi kamar wadda aka aiko ma saqon mutuwa. Nan da nan kuwa Mustapha ya rude yayinda hankalin shi yayi masifar tashi. Gani nayi ya shafa kanshi da hannuwan shi biyu yayinda ya saki ajiyar zuciya. Cikin sanyin murya yace “Hey please I am sorry, don Allah kiyi haquri ki daina kuka… for crying out loud my Angel I love you, I still love you very much, you are my life…. Wallahi ban taba daina son ki ba.. A da na cire rai akan zan qara samun ki. I even tried to forget you amma wallahi it wasn’t just possible.. My Angel soyayyarki yawo take yi a cikin jinina. Ko second daya baki taba fita daga tunani na da zuciya ta ba…. Rayuwa ta gaba daya na kasa yin ta yadda yakamata, kullum tunanina ke ce… Ke ce farin ciki na My Angel. Na sani cewar dukkan abinda ya faru a baya laifi na ne, and I am so sorry for everything. Please let’s leave the past in the past. I swear if I lose you this time I will die, don Allah ki daina bani wahala haka nan.. I beg you” Gani suka yi tana share hawayen fuskarta kamar wadda ta amince da bayanin shi, tana kallon shi tace “back off… bana yi” ta juya ta bar dinning din. Mustapha wanda idanuwan shi suka yi Ja ne na ga ya dafe kai yayinda hankalin shi yake a tashe. A yanzu dai ya tabbatar akwai babbar matsala, ya tabbatar samun Zehra zai yi wahala.. does that mean he has lost her again?? What is he supposed to do??..5 Gaba daya ma qwalwar shi ce ta kulle yayinda ya kasa yin tunani yadda yakamata. Bai ankara ba ya ji Zain ya dafa shi yayinda yace “hey I am sorry, gaskiya ban san cewar abin nata ya kai haka ba, gaba daya fa Zee ta canza..” Ya kalli Fadeela wadda itama a yanzu take tsaye a gefen su yace “but I thought she still loves him…” Fadeela tace “gaskiya nima I thought so but a yadda ta kafe I am sure akwai wani abu” Zain wanda yake kallon Mustapha ne yace “hey I have an idea..well, more like a plan” Da sauri Mustapha yace “is it going to be in my favour??” Yace “ofcourse yes my dear brother In-law.. zo mu je ka ji” Ko da suka kama hanyar falo ji nayi Zain yace ma Fadeela “Sweetheart dauko mun wayar ta” Fadeela tace “ta fashe ai Sweetheart” Yace “kar ki damu the sim card is still okay ai” Cike da mamaki Fadeela ta dauko wayar suka koma falo. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ “A father is neither an anchor to hold us back nor a sail to take us there but a guiding light whose love shows us the way.” ♤♤♤♤♤♤♤♤ BURJ-AL KHALEEFAH DUBAI Kwance take a suite din da suka sauka yayinda idanuwan ta suke a rufe tana tunani. Shekaru hudu da suka wuce ta tuno, lokacin da Mustapha yayi mata surprise visit a lokacin da suka zo hada kayan lefen Fadeela. Gani nayi ta bude idanuwan ta yayinda ta kalli yatsar ta wadda take sanye da zoben alqawarin su. Maganar shi a lokacin da suka je park ta tuno inda yake fadin: “Promise me bazaki taba cire wannan zoben daga hannun ki ba and the day you do, it will mean that babu ni a cikin zuciyar ki…” “but I don’t pray for that to happen anyway” Tun lokacin da ya sanya mata zoben ko sau daya bata taba cire shi ba. She claims she doesn’t love him anymore, why does she still have it on her??? Wasu hawaye ne suka gangaro daga idanuwan ta yayinda tayi saurin gogewa. Ji nayi tace “he promised me our honeymoon here, we planned everything but it all went down the drain” Fadeela wadda ta shigo riqe da robar Ice cream a hannun ta ce tace “Zee lafiya kike Magana ke daya??” Kai tsaye tace “Nothing Dee” Fadeela ta haye kan gadon tace “toh thank God” Ji nayi Zehra tace “Goben zamu fara shopping din kenan??” Tace “yes dear, we have just three days” Zehra wadda fuskar ta tayi displaying confusion tace “wai ni abinda ban gane ba, shi Abokin Ya Zain din meyasa bai ba amaryar kudin ba ta zo tayi siyayyan da kanta?? I mean if he has this much money ai..” Fadeela ta katse ta tare da fadin “ai matar ba wani son shi take yi ba, more like arranged marriage ne” Zehra tace “ayya, har ya bani tausayi, toh yanzu Dee ta ya zamu gane sizes dinta da taste dinta?? Haka kawai zamuyi ta siyayya without knowing her??” Fadeela wadda take dariya tace “kar ki damu.. Sweetheart yace ke ce sample din mu, da ke da ita babu banbanci.. ke hatta taste din ma duka naki za’a bi tunda dai na san kin fi ni iya zaben abubuwa” Ita dai Zehra sossai tayi mamakin wannan al’amarin. 🤔🤔🤔🤔 ♤♤♤♤♤♤♤♤ Washegari kuwa tun da safe suka shiga mall suna ta siyayya. Duk wani abinda Zehra ta nuna yayi kyau sai Fadeela ta amince yayi dagaske Wanda komin tsadar shi kuwa sai tace su siya. Takalma da handbags designers da Zehra ta dinga kwasa kuwa tun ina qirgawa har nayi losing count.. English wears kuwa haka suma ta dinga kwasar masu zafin gaske, duk wanda yayi mata kyau sai ta dauka. Turarukan da ta kwasa suma abin ba’a cewa komai. Wurin siyan nighties kuwa sossai Zehra ta kwashi gajerun rigunan bacci kamar irin wadanda take so. Wasu Sexy Lingeries da baby doll nighties da ta dinga kwasa kuwa Fadeela tana ta dariya wanda a ranta tana fadin “if only she knows” Ni kuwa nace if only she knows what??🤔3 A fili kuwa tace “Zee ki dan hada Mata da masu dama-dama mana, kin san fa ba son mijin take yi ba”3 STORY CONTINUES BELOW Zehra tace “gwara a kwasar mata wadannan din Dee, idan ya ganta a cikin su yayi ta romancing dinta har tayi laushi ta dawo hanya”2 Sossai Fadeela take dariya. A lokacin da suka shiga shagon sayar da sarqoqin Zinari kuma duk wanda Zehra tace yayi kyau sai Fadeela ta sa a dauko musu. Zehra wadda ta cika da mamaki tace “ke Dee, wai wadanne irin kudade mutumin nan ya bada ne haka da na ga sun qi qarewa??” Fadeela tana dariya tace “Ke kam Zee ba dai naki ki taya shi zabar ma amaryar shi kayan aure ba?? just fire on my dear” A cikin kwana biyu suka gama shopping din tas. Kaya ne masu yawan gaske suka siya. A dukkanin abubuwan da suka siya kuwa red colour sun fi yawa har Fadeela tana fadin amaryar dai ta shiga uku idan ba mai son Red colour ba ce. Har suka je Dubai suka dawo kuwa Mustapha bai kira Zehra a waya ba. Tana yawan ji Fadeela tana hira da shi a waya wanda suke dadewa sossai amma ko sau daya bai taba cewa a bata ba.. A tunanin ta yayi fushi ne ya qyale ta. Ni kuwa nace anya Mr. Romeo zaiyi fushi?? qila dai ya canza strategy ne😎 ♤♤♤♤♤♡♡♡♡♡ ABU-YAZEED RESIDENCE Papa na zaune a falo dadaddare tare da Anty suna hira. Zehra ce ta shigo falon cikin sallama yayinda Papa ya dago mata hannu alamar ta zo ta zauna kusa da shi. A yau dai kwanan su biyu da dawowa daga Dubai, A yau ne Papa ya kira Zehra akan wata muhimmiyar Magana da zai tattauna da ita wadda bata san ko meye ba. Kwance take a jikin Papa kamar wata qaramar yarinya yayinda take sauraron abinda zai ce. Ji nayi yace “My Baby da farko dai ina so ki sani a matsayina na mahaifin ki duk wani abinda zai cuce ki bazan taba hada ki da shi ba. Burina a koda yaushe shine in gan ki kina rayuwa mai kyau, hankalin ki a kwance. Ina so kiyi mun alqawari zakiyi abinda nake so” Da sauri tace “Papa you know I have always done everything you want, you have done alot for me in this world and I will forever be grateful. nayi maka alqawari Papa… just anything” Murmushi yayi yace “Maganar da nake so in yi miki ba wata Magana bace illa maganar aure…” Gaban ta ne yayi mummunar faduwa yayinda ta runtse idanuwan ta tana sauraron shi. Papa ne ya cigaba da fadin “shekaru uku kenan da Muhammad ya rasu.. kin ga bai dace ki cigaba da zama babu aure ba.. musamman idan aka yi la’akari you are not getting any younger” Zehra wadda ta tashi daga jikin Papa tana kuka tace “Papa why do I feel kamar kun gaji da ni a gidan shiyasa kuke so kuyi mun aure…” Wannan maganar kuwa ta kusa sa Anty dariya amma ta matse. Daddy yace “ko kadan my Baby, Ya za’a yi kiyi tunanin mun gaji da ke? On the contrary we love you very much” Ya shafa kanta sannan ya cigaba da fadin ” ..kawai dai kin san zaman ki a hakan babu aure bai dace ba kuma babu wani amfani. Gashi kuma na ga masu zuwa wurin ki sun yi yawa a yanzu… shin akwai wanda ya kwanta miki a cikin su??” Zehra wadda ta bi ta rude ji nayi tace “eh Papa akwai…”2 Whaat??🙄 Anty wadda ta cika da mamaki tace “akwai fa kika ce?? meye sunan shi?? ya akayi ban taba jin wannan maganar ba a bakin ki??” STORY CONTINUES BELOW A rude tace “Anty ban gama tsayar da tunani na akan wanda nake so din ba tukun… amma zan duba dai in gani..” Anty dai fashewa tayi da dariya tace “babu dai kenan Zee” Papa wanda yayi murmushi ne yace “My Baby a dalilin bani da right din zaba miki miji a wannan karon na baki sati biyu ki gabatar da wanda kika tsayar” Cike da tsananin tashin hankali tace “Papa sati biyu?? Don Allah kayi haquri ka bani wata daya, wallahi zan kawo muku shi” Papa ya girgiza kai yace “My Baby, Na tabbatar within two weeks zaki tsayar da tunanin ki akan wanda kike so din… Amma fa idan kika wuce sati biyu zan zaba miki da kaina…” Da sauri tace “papa dama akwai wanda zaka hada ni da shi ne??” Yana murmushi yace “No my Baby, a cikin maneman naki zan bincika in zaba miki kuma na tabbatar bazakiyi da-na-sanin amincewa da zabin nawa ba” Jikin Zehra kuwa yayi mugun sanyi a yanzu. Ji nayi tace “shikenan Papa, zan kawo muku wanda nake so cikin sati biyu. Idan har ban kawo ba na bar maka zabi” Hankalin ta a tashe ta bar musu falon. ********** Tunda ta shiga dakin ta take ta kai da komowa tana tunanin mafita yayinda take kuka. Akan wane dalili Papa zai bata sati biyu ta fiddo miji? Ji nayi tace “why all of a sudden??” Can kuma tace “toh waye zan fitar??” Gani nayi ta janyo wayarta ta zauna a kan gado tana duba sunayen maneman nata. Asali dai Zehra tayi saving sunayen su da Alhaji 1,2,3….. A yanzu haka ko yanka ta zaka yi bata san waye wanne ba. Sunayen su ma bata riqe ba. Gani nayi ta jefar da wayar yayinda ta koma kan gado ta cigaba da kuka. Fadeela ta tuno yayinda tayi saurin janyo wayar ta kirata. Hankalinta a tashe tana kuka ta ba Fadeela labarin halin da ake ciki. Fadeela kuwa danne dariyarta ta dinga yi yayinda tace “toh banda abinki Zee, Is it not better ki amince ma Ya Musty tunda dai na san ba son dattijan nan kike yi ba?” Zehra wadda ranta ya baci tsaki ta ja sannan tace “ai wallahi dukda bana son su gwara in fitar da wani a cikin su, ni kam na fadi miki bana son yayan ki.. wai meyasa bazaku gane ba??”5 Cike da tsokana Fadeela tace “Yi haquri Angel… na gane yanzu. Ni kam kiyi qoqari a cikin Alhazan naki ki dan duba mana mai qarancin shekaru don Allah, wanda zamu iya presenting dinshi a public…” Bata qarasa jin maganar Fadeela ba ta kashe wayar. Sossai ranta ya baci da maganganun Fadeela. A haka dai ta dinga saqe-saqen neman mafita har bacci ya kwashe ta. ♤♤♤♤♤♤♤ EM-ZEE KITCHEN AND CATERING SERVICE Zaune take a ofis dinta tana ta qoqarin kiran shi a waya. Alhaji Idris Balarabe wanda ya amsa wayar ne yace “Zee lafiya kike kira na?” Ajiyar zuciya ta saki yayinda tace “Haba Alhaji tun dazu nake ta kiran ka baka amsa ba…” Dakatar da ita yayi yace “ai ke din ce kika fi qarfi na Zee, ni kam bana son rigima a cikin garin nan don haka muyi haquri kawai ki je ki auri shi wannan saurayin naki” STORY CONTINUES BELOW Kafin Zehra tayi Magana kuwa ya kashe wayar. Gani nayi ta bi wayar da kallo cike da mamaki yayinda ta shiga tsananin damuwa. Tunda ta shigo ofis dinta take ta kiran maneman nata amma dukkanin su maganar daya ce. Tambaya a nan shine why is it that su duka suke nuni akan an yi warning dinsu??5 Hidaya ce ta shigo ofis din wadda kuwa tana ta yi mata Magana amma sam hankalin ta yayi nisa. Bata kula da ita ba har sai da ta taba ta. Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “hey yaushe kika shigo? Hidaya wadda ta zauna tace “just now.. me ya faru na ga kinyi nisa??” Zehra wadda hawaye suka fara gangarowa daga idanuwanta ta bata labarin abinda yake faruwa wanda kuwa sossai Hidaya tayi murna. Ji nayi tace “Babe are you sure ba gwara ki amince ma Ya Musty ba kawai mu sha biki??” Hararar ta Zehra tayi tace “what nonsense babes, nace muku bazan aure shi ba” Hidaya tace “toh yanzu ya zakiyi tunda dattijan naki duk sun ji tsoro sun gudu?” Gani nayi ta miqe tace “Zo mu je ki kai ni wani wuri” Hidaya wadda ta miqe tsaye tace “ina zamu je??” Zehra tace “idan bazaki kai ni ba just tell me in kira driver…” Da sauri Hidaya tace “yi haquri… mu je Angel” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ EM-SQUARE BODY FITNESS CENTRE Kwance yake a bench press machine yayinda yake working out. Muryar ta ya ji tana ta masifa yayinda Tony yake biye da ita yana fadin “ma’am please you are not supposed to be here” Mustapha wanda ya ji muryar ta yayi mamaki matuqa. Ji nayi yace “Its okay Tony, you can go” Zehra dai lumshe idanuwa tayi tare da jan numfashi a dalilin wani asirtaccen qamshi da yake tashi wanda ya gauraye da sanyin AC ya bada wani yanayi mai dadin gaske. Ga wani cool music wanda yake fita ahankali. Komai nashi classy… she thought Gani nayi tana ta zagaya wurin yayinda take neman shi. Tana gab da Bench press machine ne ta ga an daga wani qarfe yayinda ta gan shi ya tashi zaune. A razane na ga ta juya da sauri yayinda ta runtse idanuwan ta tana ta sauke numfashi kamar wadda tayi gudun kilometre hamsin, gaba daya ta rude a dalilin ganin shi da tayi babu riga sai wandon Capri pant da yake jikin shi. Murmushi yayi sannan yace “to what do I owe this special visit my Angel?” Muryar ta tana rawa tace “don Allah ka sa riga…” Kafin ta qarasa magana kuwa ta ji yace “okay” Aikuwa bata ankara ba ta ji ya riqo hannun ta ya janyo ta. Ita dai biye take da shi amma fa idanuwan ta a rufe yayinda qafafuwan ta duk suka yi sanyi. Zehra dai jin qarar qofa tayi wanda ya tabbatar mata da wani wuri na daban suka shiga. Sakin hannun ta yayi yayinda ya nufi wurin wani fridge ya bude ya dauko goran ruwa sannan ya dawo kusa da ita. Har yanzu idanuwan ta a rufe suke yayinda yake ta kallonta yana murmushi. Gani yayi ta bude idanuwan ta kamar wata marar gaskiya yayinda ta saci kallon shi, Ganin har yanzu bai sa rigar bane tayi saurin rufewa tare da fadin “yau na shiga uku, don Allah ka sa riga mana..” STORY CONTINUES BELOW Kai tsaye yace “toh ki zo ki sa mun My Angel” Jikin ta na rawa ya ga ta ruga a guje tana neman hanyar fita. Da sauri yace “hey wait, na sa… turn around and see” A hankali cikin fargaba ta juyo ta dan kalle shi ta ga dagaske ya sa wata Farar T-shirt. Ji tayi yace “zo ki zauna kusa da ni ki fadi mun abinda kike yi anan… Ko kinyi missing dina ne??” Zehra wadda take a rude har a wannan lokacin zama tayi a wata kujera nesa da shi wanda kuwa ya Harare ta yace “a haka zamuyi Magana??? I swear idan bazaki matso ba kawai ki tashi ki tafi” Shi kam ya sani sarai tunda har ta biyo shi lallai akwai abinda take nema don haka ne yake ta yi mata yadda ya ga dama. Babu Shiri Zehra ta koma kujerar da yake ta zauna daf da shi kamar yadda ya buqata. Juyowa yayi ya fuskance ta wanda kuwa hakan ya saukar mata da wata muguwar kasala. Gaba daya ma ji tayi dama bata zo ba. Yana kallon fuskar ta yace “I am listening my Angel” Muryar ta tana rawa yayinda take wasa da zoben hannunta ne tace “dama Papa ne ya bani sati biyu in fitar da mijin aure…” Cike da murna yace “Whoa… ni kika fitar kenan??” Gani tayi ya daga hannun shi sama yana fadin “Alhamdulillah… A dream come true for me…..” Bata bari ya qarasa maganar shi ba tace “Ni fa ba kai na fitar ba…” Kai tsaye yace “ban gane ba.. then why are you telling me this??” Dago kai tayi ta dan kalle shi sannan tace “ina so ne kamar yadda ka bi samari na kayi warning din su ka kira su daya bayan daya ka janye…” Ji tayi yace “wanne daga cikin su kike so in kira?? Alhaji 1 ko Alhaji 9 ko Alhaji….” Cike da mamaki take kallon shi yayinda yace “Kin dai san bazai yiwu ki aure su duka ba ko?? Toh gaya mun sunan wanda kika fi so a cikin su sai a kira miki shi…” Ko kafin tayi magana ta ga lokaci guda yanayin fuskar shi ta canza yayinda yace “are you mad?? a tunanin ki ina kallo zan bari ki auri daya daga cikin wadannan tsofafin ne?? idan kika aure su kiyi ya da su?? How can you even marry a man who is old enough to be your father??” Da sauri ta miqe tare da fadin “me ya ruwanka da irin zaman da zamuyi?? Ko sun girmi Papa ai ba wani abu bane tunda dai Allah ya halasta…” Ji tayi yace “just shut up and listen to me carefully, baki da mijin da ya wuce ni so better get use to the idea..” Cikin masifa tace “aikuwa da in aure ka gwara na auri zabin Papa” Gani nayi ya girgiza kai yayi murmushi sannan yace “All the best my Angel” Juyawa tayi zata tafi yayinda ta ji yace “bari in zo in raka ki…” Bata saurare shi ba tayi gaba abinta yayinda ya biyo ta a baya.1 *************** Hidaya wadda take zaune cikin mota sai ganin su tayi sun fito, Zehra tana tafe yayinda yake biye da ita. Fuskar ta a murtuke yayinda tashi take a sake. Ko da ta qaraso ta shige motar Hidaya tayi saurin sauke glass din gefen Zehran yayinda tace “ina wuni Ya Musty” yana murmushi yace “lafiya lau” Zehra wadda take zaune kuwa sai kubure kumbure take yi yayinda ta ji yace “qawar ki bata jin Magana, da alama ma she is confused.. ki dinga bata shawara” Ji tayi Hidaya tace “kayi haquri zamu gyara” Basu ankara ba suka ga wata dalleliyar Toyota Rav4 ta faka a gefen motar Hidaya Yayinda Sareenah ta fito daga motar. Gani suka yi Mustapha ya juya ya kalle ta yace “sai yanzu??” Sareenah wadda take murmushi tace “Yi Haquri wallahi Adda ce ta aike ni.. nima ina ta sauri in zo in kawo maka” Zehra wadda zuciyar ta take ta tafasa kuwa sai kallon Sareenah take yi yayinda wani mugun kishi ya rufe ta. Ko ba’a fadi mata ba ta sani cewar wannan itace Sareenah domin kuwa tana kama da Adda Ummie sossai har ma ta fi Adda Ummie kyau. Gani tayi sun bala’in dacewa da Mustapha ta kowanne fanni domin kuwa Sareenah kyakyawar yarinya ce, doguwa with beautiful body sannan ga ta fara sol. Hidaya wadda take ta kallon ikon Allah kuwa ji tayi Mustapha yace “finally yau dai ga ki ga kuma Angel dina..” Cike da murna Sareenah tace “haba??” ta duqo saitin windon Zehra tace “wooow, I am finally honoured to meet you our Angel…” Ganin fuskar Zehra a murtuke ne ta dago ta kalle shi yayinda tace “me kayi mata??” Yana murmushi yace “I swear banyi mata komai ba” Qara duqowa tayi tana kallon Zehra tace “kiyi haquri, dama fa baya jin Magana kuma kin sani but he is surely a great guy with a good heart” Zehra dai har yanzu fuskar ta a murtuke yayinda take ta qoqarin danne hawayen da suke neman zubowa daga idanuwan ta. Zuciyarta kuwa kamar zata faso qirjinta saboda tsananin bugawa da take yi. Sareenah dai ganin Zehra tana shirin yin kuka ne ta kalli Mustapha tace “da alama ka bata mata rai, ka ga fushin ma har ya shafe ni. I guess its not a good time…” Zehra dai Juyawa tayi ta kalli Hidaya muryar ta qasa-qasa tace “what the hell are we waiting for??” Hidaya tayi murmushi tace “nothing” sannan ta tada mota. Mustapha ne ya kalli Hidaya yace “drive safe and take care of her” Ya kalli Zehra yace “My Angel thanks for the visit, I love you… bye ” Ji tayi Sareenah tace “oh oh oh… I am jealous” yayinda yayi murmushi yace “where is it??” Ita dai zehra gani tayi Sareenah ta bude qofar motar ta yayinda ya shiga ya zauna yana duba wasu abubuwan da bata samu damar ganin ko meye ba. A haka suka bar wurin wanda kuwa Zehra ta rushe da kuka. Har suka isa ofis kuwa kuka take ta yi, Tun Hidaya tana lallashin ta har ta haqura ta qyale ta. ♤♤♤♤♤♤♤♤♤ Tabbas Mustapha yayi gaskiya… Zehra is confused!!1 I think she is Naive too🤔 Ga Papa ya sa ta a corner… shin wa zata fitar?? Ko zata haqura da zabin Papa ne?? will Papa’s trick work??? Is this actually part of Zain’s Plan???6