ZEHRA CHAPTER 2

ZEHRA CHAPTER 2

OMAR TAFIDA RESIDENCE Kwance yake a kan makeken gadon shi wuraren qarfe Goma na safe yana ta bacci. Tunda ya dawo sallan Asuba ya koma bacci domin kuwa har lokacin a gajiye yake.+ Qarar Alarm dinshi ne ya tada shi. gani nayi ya bude idanuwan shi ahankali yayinda ya janyo alarm clock din wanda yake kan bedside drawer ya kashe. Burying kan shi yayi a pillow yayinda ya cigaba da shaqan qamshin mai dadi. Bayan kusan minti biyar ne ya tashi zaune tare da yin addu’ar tashi daga bacci. Sauka yayi ya shige dressing room dinshi don shirin yin wanka. Kamar jiya ma haka ya dade a cikin bathroom din. Yana zaune cikin jaccuzi yana enjoying qamshin turarukan wankan ne ya janyo daya daga cikin turarukan yana duba sunan. Zaro idanuwa yayi tare da fadin “what the hell, for her??” Runtse idanuwa yayi yace “I will deal with you Dee” ************ Bayan ya shirya cikin three quarter wandon Sweatpant da farar T-shirt ya nufi gaban Vanity table dinshi yana qoqarin brushing gashin kanshi ne ya hango note din da Zehra ta rubuta a gefe. Gani nayi ya sa hannu ya dauka sannan ya karanta saqo kamar haka: “I may not be your perfect Sister, but to me, you are the perfect brother of this world. Welcome home Brother. Hoping we’d get to spend quality and memorable moments together” Murmushi ya dan yi sannan yace “emotional blackmail right??” jefar da note din yayi ya cigaba da brushing kan shi. Turarrukan da Zehra ta ajiye mishi a kan Vanity Table din ne ya kalla. Ganin ba irin taste dinshi bane ya girgiza kai ya kwashe su duka ya zuba a drawer ba tare da ya ji qamshin su ba. Ji nayi yace “For the great things you’ve done, I will spare your life this time Dee” Wayar shi ce tayi ringing ya nufi gadon shi ya dauka. Ganin sunan Mummy ne yasa shi yin Murmushi ya amsa cikin sallama. Bayan ta amsa ne yace “good morning Mummy” Mummy tace “how are you? Ashe ka dawo jiyan, yanzu Iro yake sanar da ni” Mustapha ya dan sosa kai sannan yace “yes Mummy na dawo very late ne shiyasa ban shigo ba, gani nan shigowa yanzu” *************** Tsaye take a kicin din gidan tana qoqarin zuba popcorn a cikin cup. A yadda take zubawa zaka san cewar she is rushing to meet up with something domin kuwa kusan rabi ya zube. Zehra dai sauri take yi ta je kallon Chopped a tashar Foodnetwork wanda ma an riga an fara. Da sauri ta qarasa zubawa ta rugo a guje riqe da cup din popcorn din zata wuce falo. STORY CONTINUES BELOW Wani ikon Allah kuwa tunda ta fito daga kicin din ta ji zuciyar ta tana ta bugawa wanda har sai da ta dafa qirjinta. Zehra dai bata ankara ba ta ji tayi karo da abu wanda kuwa gaba daya popcorn din hannun ta ya watse yayinda ta fadi a qasa. Da sauri ta dago kanta don ganin abinda ta buga amma kuwa kafin ta ga fuskar shi har ya wuce ta ba tare da yayi reacting to what happened ba. Cikin fushi da masifa Zehra ta miqe ta bi shi a baya tana fadin “hey, what the hell did you just do to me?? You threw me on the floor and you just walked past me without an apology. Who the…..” Kafin ta rufe bakinta kuwa ta ji saukar wani mugun marin da sai da tayi ihu tare da zubewa qasa dafe da kumatun ta.2 A daidai wannan lokacin ne Mummy ta sauko yayinda hankalin ta yake a tashe tace “lafiya?? Me ke faruwa ne haka??” Da sauri ta qarasa wurin Zehra ta dago ta tare da duba kumatun nata wanda yayi Jajawur. Hawaye ne ke ta gangarowa a kumatun ta yayinda take ta sheshekan kuka. Mummy ta kalle shi tace “what have you done Mustapha? Ka fara ko??” Cike da mamaki ne na ga Zehra ta dago kai ta kalli kyakyawar fuskar shi wadda babu expression. A ranta ne tace “Ya Musty???” gani nayi ta sa mishi idanuwa yayinda zuciyar ta take ta bugawa. Zehra ta sha’afa a kallon shi ne ta ji Mummy tana fadin “Yanzu daga shigowar ka me yarinyar nan tayi maka da har zaka yi mata irin wannan marin?” Mustapha kuwa ko kallon fuskar Zehra bai yi ba yace “uhm dama na shigo in gaishe ki ne Mummy” Cikin masifa Mummy tace “da ka sani kayi zamanka ma..” cikin girmamawa yace “yi haquri Mummy” sannan ya juya zai tafi. Muryar Mummy ya ji tace “bazaka yi breakfast bane zaka tafi ka bar ni da shi?? abincin da aka tanadar maka jiya ma haka dole sai dai aka saka a fridge…” ba tare da ya juyo ba yace “na qoshi” Mummy ta sani sarai qarya yake yi, a dalilin bata mishi rai da Zehra tayi ne yasa yayi fushi. Sanin halin shi ne yasa ta qyale shi. Bai ankara ba ya ji muryar Zehra tana fadin “I am sorry Ya Musty, I didn’t mean to disrespect you…” Bata qarasa ba ta ga ya fiddo wayar shi daga aljihu yana amsa call har ya fice daga falon. Hankalin Zehra a tashe ta juyo ta rungume Mummy tare da fashewa da kuka. Mummy ce take shafa bayan ta tare da fadin “yi shiru ki daina kuka” Fadeela ce ta sauko yayinda ta ga qawar ta tana kuka. Cike da tashin hankali tace “what is going on here?? Zee meya faru?” Mummy ce ta bata labarin abinda ya faru yayinda Fadeela ta girgiza kai cike da takaici tace “wallahi Ya Musty mugu ne, Allah sai ya saka miki wannan wulaqancin” ta janyo Zehra tayi hugging dinta yayinda suka tafi daki. Mummy kuwa sai masifa take ta yi. Zaune suke a kan gado yayinda Fadeela take ta lallashinta. Fadeela tace “I told you babes, the guy is bad. Gashinan kin fara gani” STORY CONTINUES BELOW Zehra tana share hawayen fuskar ta tace “its all my fault Dee, I disrespected him kuma Insha Allah zan bashi haquri” cike da mamaki Fadeela tace “what??? Ki bashi haquri?? In baki shawara Zee, forget about the guy and stay away” Zehra tace “hell no babes, I want to make things right and God help me I will” Shi kuwa Mustapha yana fita daga gidan ya nufi sashen shi ya dauki jakar shi da makullin mota ya fito ya wuce Gym. ♤♤♤♤♤♤ Washegari da yamma bayan Fadeela ta dawo daga aiki. Suna zaune a Garden din gidan suna hira. Zehra ce tace “Dee wai shi Ya Musty baya shigowa cikin gida ne? tunda ya mare ni jiya fa ban qara ganin shi ba, yau ma kwata kwata ban gan shi ba” Fadeela ta bata rai tare da fadin “ai haka ne dama, we don’t even feel his presence. He is around amma kuma kamar baya nan. Ni sai yau da safe ma da zan tafi aiki na hadu da shi tunda ya dawo. Sannu da zuwan da nayi mishi ma da qyar ya amsa, mutum sai tsabar fadin rai..” Zehra ta dan yi murmushi tace “ni kuwa I like his life style, babu ruwan shi da rikici. He only needs to associate a bit and he will be very much good to go” Fadeela ta Harare ta tace “mu ‘yan rikici ne hala?” Tana dariya tace “I didn’t say….does he even have friends at all?? because I know people like him hardly make friends” Fadeela ta fashe da dariya tace “friends??? tab… ai kuwa bana ji yana da su. sai dai qila colleagues dinshi wurin aiki.. the only person fa da Ya Musty yake relating da shi shine Ya Moha. With him kuwa he is an entirely different person” Zehra ta girgiza kai tace “Allah sarki, I would love to become his friend Dee, I really wanna study people like him” tana murmushi ta cigaba da fadin “who knows ma qila inyi nasarar canza muku shi” Fadeela tana murmushi tace “Allah ya baki sa’a. I’d be glad if you change him gaskiya” Cikin tsokana ta cigaba da fadin “daga nan ma ku fara soyayya kawai a daura muku aure…” Zehra ta zaro idanuwa tace “what?? please Dee….” Kafin ta qarasa maganar ta ne ta hango tattabarun gidan sun taru a tsakar gidan. Da sauri ta miqe cike da murna tace “Yeey… Dee bari in je in dan yi wasa da Friends dina..” Kafin Fadeela tayi Magana kuwa har ta ruga a guje. Girgiza kai tayi tace “oh my friend, you and birds” Ban fadi muku cewar Zehra tana bala’in son wasa da tsuntsaye ba ko?? Yeah she loves Birds a lot. Idan tana hira da su zaka rantse suna jin abinda take fadi. *********** Tsugunne take a tsakiyar Tattabarun yayinda take ta basu abincin su wanda daya daga cikin masu aikin gidan ya kawo mata. Sossai take cikin nishadi yayinda suke ta cin abincin. Security din gidan ne ya bude gate da sauri yayinda Farar Mercedes din shi ta shigo gidan. A lokacin da ya shigo gidan yana magana da wani colleague dinshi a waya don haka bai kula da Zehra wadda take tsugunne a tsakar gidan ba. Hankalinta yayi nisa da bata ji qarar motar ba dukda kuwa dai dama irin motocin nan ne marassa qara. A lokacin da Mustapha ya kawo daf da ita ne ya ankara yayinda ya taka wani irin emergency brake wanda kuwa hakan yasa gaba daya tattabarun suka tashi yayinda Zehra ta miqe a razane tare da fadin “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” Mustapha wanda yake kallonta ji nayi ya saki ajiyar zuciya tare da fadin “this garl must be very stupid” Zehra wadda take tsaye a rude yayinda zuciyarta take ta bugawa tayi zaton zai fito daga motar don duba lafiyarta amma abin mamaki sai gani tayi ya dan yi reverse tare da matsawa ya zagaye ta ya wuce abinshi. Fadeela wadda ta hango al’amarin tuni ta qaraso wurin Zehra tana fadin “hope dai bai bige ki ba??” Zehra wadda ta bi motar Mustapha da ido har yayi parking a parking lot kuwa sakin baki tayi yayinda ta cika da tsananin mamaki. Gani suka yi ya fito daga motar riqe da waya a kunnen shi yayinda ya wuce ya nufi sashen shi ba tare da ya waiwaye su ba.4 Gani nayi Zehra ta dafe qirjinta wanda yake ta bugawa tare da runtse idanuwan ta tace “I can’t believe this” ♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Wuraren qarfe daya na dare tana kwance kan gado yayinda ta kasa bacci.+ Babu abinda take tunowa illa encounter dinta da shi wanda a karon farko ta kwashi mari sannan a na biyu kuma ya kusan hawa kanta da mota. Abinda ya fi bata mamaki shine on the second occasion he didn’t even react, he simply ignored her as if nothing happened. Gani nayi ta juyo ta fuskanci Fadeela wadda tayi nisa a bacci. Ajiyar zuciya ta saki yayinda ta zame duvet din da suka rufa ta sauka daga kan gadon. Komawa tayi kan resting chair ta kwanta tare da rufe idanuwan ta. Ahankali tace “I am sure he is not a bad guy, he might just be an Introvert with a good heart” Gani nayi ta bude idanuwan ta tace “I need to get him out of his head, its not going to be easy but I am going to do it Insha Allah” wata zuciya ce tace “why are you doing this Zehra? Why do you care??” Murmushi tayi sannan ta miqe tare da fadi a fili “because it’s my hobby” ☆☆☆☆☆☆ A yau da safe suna zaune a dinning suna breakfast ne Zehra ta kalli Mummy tace “wai Mummy meyasa Ya Musty baya shigowa yin breakfast with the rest of us??” Fadeela wadda ta miqe don tafiya ofis ce ta fashe da dariya tace “a ta ina zai fara shigowa nan yin breakfast?? Dama dai Ya Moha yana nan da ya shigo, shi ma sai bayan mun gama mun tashi” Ta kalli Mummy tace “ni kam na tafi I am late sai na dawo” Zehra tace “take care Dee” tace “thanks love, you take care too” Mummy tace “kar ki manta ki karbo mun saqo na wurin Hajiya Umaima idan kina dawowa” tace “Insha Allah Mummy” Bayan ta fita ne Zehra ta kalli Mummy tace “amma Mummy halin Ya Musty baya damun ki?? As in don’t you feel bad about how he lives his life?” Mummy ta girgiza kai tare da yin murmushi tace “toh ya zan yi Zehra, he has always been like this tun yana yaro. Da farko mun damu da hakan, har asibiti an kai shi a duba qwalwar shi idan akwai matsala amma the response was that he is perfectly fine, I guess halitta ce haka Allah yayi shi” Zehra ta dan yi murmushi tace “Mummy if you will help me I want to try something on him” cike da mamaki Mummy tace “really?? What is it??” Zehra tace “I want to change him a bit” Mummy tana dariya tace “ki fita batun wannan miskilin yaron Zehra, babu abinda hakan zai janyo miki banda bacin rai. Kin dai ga abinda yayi miki daga haduwar ku ta farko” Zehra tana murmushi tace “that was my fault mummy, I still owe him an apology, please just help me lets see if we can change him even if it’s a bit” Mummy tace “I will be more than glad to see him change my dear, Anything you need” ☆☆☆☆☆☆ Tsaye yake a gaban madubin dakin shi yayinda yake shirin fita. Yanayin kayan da suke jikin shi ne suka tabbatar mun da lallai Gym zai je. Mustapha dai a kullum yana zuwa Gym domin motsa jiki. kun san sojoji da son motsa jiki. STORY CONTINUES BELOW Wayar shi ce tayi ringing. Ko da ya duba gani nayi ya dan yi murmushi sannan ya amsa. A dayan bangaren kuwa Mummy ce tace “kana ina ne?” yace “ina gida Mummy, I am just about going to the Gym” tace “yauwa, idan ka shirya ka zo kafin ka tafi” Bayan ya gama shirin shi tsab ne ya dauki jakar shi ya fito. Boot din motar ya bude ya ajiye jakar sannan ya rufe ya nufi main section din gidan don jin dalilin kiran shi da Mummy tayi. Zehra wadda take zaune a main palour din gidan ce na ga tayi saurin dafa qirjin ta yayinda ta runtse idanuwan ta duk kuwa a dalilin Sallamar shi da ta ji. Mummy ce ta amsa yayinda tace “har ka fito??” yace “yes Mummy” Tace “dama Zehra ce zata je cooking school shine nace ka sauke ta…” Mustapaha Wanda yake tsaye a bayan kujerar da Zehra take zaune ne yace “what?? Driver fa??” Zehra wadda take sauraron muryar shi a bayan ta kuwa sai bugawa qirjinta yake yi yayinda ta ji Mummy tace “zan aiki Iro yanzun nan kuma ita bata iya driving ba..” A ranshi ne yace “what foolish girl her age doesn’t know how to drive??” A fili yace “amma Mummy I am running late fa..” Mummy ta katse shi tare da fadin “bazaka ajiye ta ba kenan??” Ya runtse idanuwan shi tare da fadin “I am sorry Mummy” daga nan kuwa ya juya yayinda Mummy ta kalli Zehra tace “go with him, all the best” Jiki a sanyaye Zehra ta miqe ta fita yayinda Mummy tayi murmushi tace “how I wish…” Ni kuwa nace how she wish what???10 ********** Sanye take cikin doguwar riga ta atamfar Super Wax Red colour yayinda ta yafa dan qaramin gyale ja a kanta. Flat shoe ne na Vincci a qafar ta yayinda ta riqe Jakar Louis Vuitton ‘yar qarama Red color. Sossai Zehra tayi kyau domin kuwa Red abu yana yi mata kyau, banda qamshi babu abinda take zabgawa. A lokacin da ta qaraso yana nan zaune cikin motar fuskar shi with no expression as usual. Kafin ta shiga kuwa sai da ta dafe qirjinta wanda yake bugawa yayinda tace “All the best Zee” Tana bude qofar zata shiga ne tace “Assalamu Alaikum” For the fisrt time Mustapha ya ji impact na muryar mace. Sossai muryar ta tayi mishi dadi a yau amma ya basar. Ba tare da ya kalle ta ba yace “Ameen wa’alaikis salam” Bayan Zehra ta rufe qofar motar ne tace “Good morning Ya Musty” kai tsaye yace “morning” daga nan ya ja mota yayinda Zehra tayi murmushi a ranta tace “Whoa.. I didn’t even expect him to respond…” Ko da suka bar gidan gani tayi ya dauki hanya ba tare da ya tambaye ta wurin da zata je ba. Itama kuwa bata yi mishi Magana ba because he is on track. Bai ankara ba ya ji muryar ta tana fadin “Uhm, Ya Musty I really want to apologise for what I did to you the other day. Wallahi I didn’t mean to disrespect you. I am not a bad girl I promise” Ji tayi yace “its okay” Gani nayi ta zaro idanuwa tace “dagaske ka yafe mun?? ya wuce??” Murmushi tayi tace “but you are not smiling, I know for a fact cewar ka amsa ne saboda baka son zancen” Cike da mamaki Mustapha a ranshi yace “what the hell, how comes she read my mind??” ji yayi tana fadin “na sani cewar baka riqe ni a rai ba dukda na bata maka rai, well atleast it’s a good thing” STORY CONTINUES BELOW Shi dai Mustapha sauraron ta kawai yake yi ba tare da yace komai ba. Tace “sorry I forgot to introduce myself, ni sunana Zehra Abu-Yazeed. Iyayen mu sun kasance aminan juna tun suna yara but unfortunately mu bamu san juna ba sossai. My Papa is married to your Anty…” A ran shi ne yace “ooh, she is Papa’s daughter…” Ji yayi tace “I really want to know you better Ya Musty, will you give me a chance??” Bata ankara ba ta ga ya faka a gaban wani qaton Gym wanda ta ga an rubuta Em-square Body fitness Centre. Ba tare da ya kalle ta ba yace “this is my destination” Zehra dai ta gane abinda yake nufi don haka ne ta bude qofa ta fito. Abin mamaki Gym din is very close to cooking school din nata don haka ne tayi murmushi tace “nima ai My school is just behind this street, I will proceed on my own” Bai saurare ta ba ya bude boot yayinda wani ma’aikacin wurin ya zo cike da girmamawa ya gaishe shi tare da daukar jakar. Zehra dai tsayawa tayi tana kallon ikon Allah. Gani nayi ta daga kai sama ta qara kallon sunan wurin sannan ta qaraso wurin shi da sauri tace “is this place yours??” can kuma tace “yes I guess, its beautiful, would love to come check it out someday. Bari in tafi, I am running late” Juyawa yayi ya shige Gym din.28 ********* Kusan minti goma kenan da Mustapha ya tafi ya bar Zehra tana qoqarin tsallaka titi. Irin titin nan ne mai lane uku kafin ka kai tsakiya. Ga ta kuma da tsoron mota. Ji nayi tana fadin “yau na shiga uku, how do I cross this road?? My mission is definitely a failed one tunda gani nan na maqale”1 Ban ankara ba na ga Zehra ta kwasa a guje wanda kuwa tana kai tsakiyar titin ne wata mota ta doso ta. Gani nayi ta tsaya cak tare da zabga ihu yayinda ta runtse idanuwan ta. Motar kuwa tsayawa cak tayi a dalilin emergency brake da mamallakin motar ya taka. Zehra kuwa tuni ta zube qasa tana kuka. Mutane ne suka qaraso wurin suka zagaye ta yayinda mai motar ya fito don ganin abinda yayi. Yana qoqarin shiga power rack machine ne daya daga cikin ma’aikatan wurin ya rugo yace “Sir, wannan wadda kuka zo tare dinnan ce aka bige da mota” A firgice Mustapha ya juyo tare da fadin “subhanalillah” Cikin hanzari kuwa ya fita don ganin abinda yake faruwa. Tana nan a zaune tana ta kuka ne Mustapha ya qaraso wurin. Mutumin da ya kusa bige ta ne yake ta faman bata haquri yana fadin “did you get hurt??” Zehra wadda take kuka ta dago hannun ta wanda ya dan gurje kadan tace “nan ne na ji ciwo” Mutumin kuwa duk ya damu yace “mu je in kai ki asibiti” da sauri Mustapha yace “don’t worry I got this, zaka iya tafiya” Bayan mutumin yayi godiya ya tafi ne Mustapha yace “tashi mu je..” Zehra ta miqe tsaye. Daya daga cikin mutanen da suke wurin ne ya dauki jakar ta wadda bata ma san ta bari ba yace “kin bar jakar ki” Mustapha ya karbi jakar sannan suka nufi Gym din. Tafe yake yayinda take biye da shi. Zehra dai gaba daya ta manta da ciwon da yake hannun ta yayinda ta sha’afa a kallon Gym din. Wurin yayi masifar tsaruwa. Bata qarasa rikicewa ba sai da suka haura wani lounge mai masifar kyau. Ganin cewar komai white ne a ciki yasa ta yin murmushi tace “this place is definitely yours, how beautiful” Mustapha dai bai kalle ta ba balle yayi mata Magana. Gani tayi ya dauki wayar intercom ya kira sannan yace “please come fast, its an emergency” Cikin mintuna biyu ta ga wata mata ta shigo sanye da lab coat da kuma first aid kit. Gani tayi matar ta dan russuna tace “morning Sir” yace “Morning Cynthia, please check her wound, I will be going for my training. just let me know when you are done” tace “okay Sir” Zehra dai tunda ya fara Magana take kallon shi. gani nayi ta girgiza kai a ranta tace “is it that Dee doesn’t understand her brother ne or what?? The guy is cool fa, it seems there is nothing to change about him afterall” Bata ankara ba ta ji Cynthia tana fadin “let me see the wound Ma’am” Zehra ta dago hannunta ta nuna mata. Ji tayi Cynthia tace “I am finally honoured to meet you Ma’am, I must say that he has a great taste” Zehra ta zaro idanuwa tare da fashewa da dariya tace “you are mistaken dear, Its just cordial.. I mean the family friends kind of relationship. You understand me right??” ♤♤♤♤♤♤ hmmmm… OMAR TAFIDA RESIDENCE+ Zaune suke a falon sama yayinda Fadeela take ta mamakin labarin da Zehra take bata a game da abinda ya faru tsakanin ta da Mustapha a yau. Fadeela dai girgiza kai tayi tace “lallai ma Zee, kina nufin Ya Musty ne yayi miki haka?? He even took you to your cooking school afterwards?? Ki ce kun zama 5 & 6 kenan, aikuwa na ji dadi don albarkacin ki zan samu sauqin sharewar da yake yi mun” Zehra ta fashe da dariya tace “I doubt Dee, kin san kuwa duk haduwar mu bai taba kallo na ba ma?? Ni fa I doubt in zai gane ni idan ya gan ni a kan hanya. Kawai dai I am certain cewar he is not as bad as you say” Fadeela ta dan yi murmushi tace “Well its possible, Sometimes dai I feel saboda ni ba namiji ba ce shiyasa baya relating da ni because wallahi idan kika ga bond din da yake tsakanin shi da Ya Moha zaki yi mamaki sossai. Their bond is so much strong that they can sacrifice their lives for eachother. Ko Mummy da Daddy baya relating da su the way he does with Ya Moha” Zehra ta girgiza kai tace “Allah sarki, dama fa Introverts are like that at times. I still like his personality gaskiya” ************** Washegari da daddare suna zaune a dinning suna dinner yayinda suke ta yaba ma girkin Zehra kamar kullum. A yau ne Papa da Anty tare da Khadeeja suka ziyarci Aminin nashi don yin zancen Zain da Fadeela. Zain bai samu zuwa ba a dalilin yana da aiki a asibiti. Gaba dayan su sun hallara a dinning din amma fa banda Mustapha. Papa ne yace “wai ni kam ba ance Mustapha ya dawo bane?? Yana ina ban gan shi ba?” Daddy yana murmushi yace “ka san halin shi ai, ni kaina tunda na dawo ina ganin sau biyu na gan shi” Papa yana dariya yace “Soja kenan, rabona da shi har na manta” Mummy ce tace “aikuwa bari a kira shi ku gaisa” Zehra da Fadeela suka kalli juna suna murmushi. Mummy ta dauki wayarta ta kira shi. ji nayi tace “kana ina ne??” daga nan kuma tace “Ka zo ku gaisa da Papa” bayan ta kashe ne tace “gashinan zuwa” Zuciyar ta ce ta fara bugawa yayinda ta dafe qirjinta. Bata ankara ba ta ji sallamar shi cikin muryar shi mai sanyi. Da sauri ta dago kai tana kallon shi. Sanye yake cikin wani farin yadi mai kyan gaske. da ganin yadin kuwa ka san ya ja kudi. Kan shi babu hula yayinda gashin kan nashi yake a kwance gwanin ban sha’awa. Ga sajen shi da ya sha gyara. Sai zabga qamshi yake yi. Gani nayi Zehra ta lumshe idanuwa a ranta tace “now this is the definition of cuteness”9 Kusa da Papa ya je ya tsugunna har qasa yace “sannu da zuwa Papa, ina wuni” Papa kuwa cike da jin dadi ya shafa kan shi tare da fadin “lafiya lau soja, ya aiki?” yace “Alhamdulillah Papa” Yace “madallah” Dago kai yayi ya kalli Anty yace “Anty ina wuni” tana murmushi tace “lafiya lau Mustapha, rabo na da kai har na manta” STORY CONTINUES BELOW Murmushi kawai yayi yayinda Daddy yace “ai kin san halin, sannan kuma ga wannan aikin nashi da baya barin shi zama” Khadeeja ce tace “Ina wuni Uncle” ba tare da ya kalli inda take ba yace “lafiya” Miqewa yayi yace “uhm bari in koma Papa” da sauri Mummy tace “abincin fa??” yace “ki sa a kawo mun Mummy” Zehra ce tace “haba Ya Musty kawai ka zauna ka ci anan mana”5 Fadeela wadda ta zaro idanuwa ce a ranta tace “ka ji Zee da rigima”2 Kafin yayi Magana kuwa Papa yace “yes dear, zo ka zauna nan kusa da ni mu ci abinci” Ba tare da ya musa ba kuwa ya ja kujerar gefen Papa ya zauna. As usual fuskar shi babu expression. Zehra kuwa a ranta tace “yes Zee, good job” Tana kallon shi ta ga ya ja plate ya zuba pepper soup na cat fish dan kadan yayinda ya fara ci cikin natsuwa. Sossai girkin yayi mishi dadi har yana tunanin me ma ya hana shi zuba dayawa.. Daddy ne yayi gyaran murya yace “Papa ka ga idan muka sa bikin nan da five months na san lokacin Muhammad ya dawo and na sani cewar duk wani shiri za’a kammala” Mustapha wanda yake sauraron su ne a ran shi yace “waye zai yi aure??” Ji yayi Papa yace “its okay ai hakan” su Mummy ne suke ta sa albarka yayinda Mustapha ya shiga confusion. Ji sukayi yace “who is getting married??” Mummy tana dariya tace “your sister Fadeela..” Aikuwa Fadeela cike da kunya ta tashi ta bar wurin yayinda Suka dinga yi mata dariya. Mummy ta cigaba da fadin “zata auri Zain, yayan Zehra” Yace “Allah ya sanya alkhairi” suka amsa da “ameen” Zehra dai tunda ya zauna babu abinda take yi banda studying dinshi. Tuni ta riga ta gama analysing din halin shi wanda kuwa she found him to be just perfect.2 Anty ce tace “aikuwa yakamata ku san juna don ina kyautata zaton baku taba haduwa ba” Papa ya kalli Mustapha yace “you will have to visit me frequently kafin ka tafi” Mustapha yayi murmushi yace “insha Allah Papa I will” ********** Wuraren qarfe goma na dare suna zaune a dakin Fadeela. Zehra ce zaune a kan resting chair tana kallon wani cooking competition a tab yayinda Fadeela take kwance kan gado tana chatting da Zain as usual. Ji suka yi an qwanqwasa qofar dakin yayinda Fadeela tace “come in” budewar qofar yayi daidai da qaruwar bugun zuciyar ta. gani nayi ta dafe qirjinta da sauri yayinda ta kai idanuwan ta kan qofar. Mustapha wanda yake sanye cikin wandon track suit Baqi da farar T-shirt ne ya shigo. Cike da mamaki Fadeela tace “Ya Musty what brings you?? Why didn’t you call me??…” Yana jingine da Vanity table dinsu ne yace “I came to congratulate you Dee. I am so happy for you. Allah ya sanya alkhairi” Cike da murna tace “ameen, thank you so much bro. this means a lot to me” Murmushi ya dan yi yace “if it does why aren’t you standing here giving me a hug then??” Zaro idanuwa tayi tace “whoa…” aikuwa a guje ta sauka daga kan gadon ta qarasa wurin shi tayi hugging din shi tare da fadin “thanks a lot Ya Musty” a kunne ya rada mata “anything for you Baby Dee” STORY CONTINUES BELOW Zehra wadda take zaune kuwa sai kallon su take yi cike da sha’awar moment din tsakanin siblings din. Gyaran murya yayi ahankali yace “hey, kinyi hugging dina so tight that I can’t even breathe properly, wannan irin qarfi haka ai aikin soja ya kamace ki” Zehra dai ji tayi sun fashe da dariya yayinda Fadeela tayi saurin sakin shi tace “sorry Bro” Girgiza kai yayi yace “let me get going, Good night” Tace “good night and thank you once again” Zehra dai ganin kamar bai ma ganta bane tayi saurin fadin “good night Ya Musty” ba tare da ya kalle ta ba yace “good night” ya fita. Bayan ya fita kuwa Fadeela ta zaro idanuwa tace “I still can’t believe he came to congratulate me, wallahi I am so happy”3 Ta koma kusa da Zehra ta zauna tace “honestly Ya Musty ya fara canzawa” Zehra wadda take murmushi tace “dama can haka yake, ku ne dai baku gane shi ba” Fadeela tace “toh ke kin gane shi ne??” can kuma tace “oops, na manta cewar that’s your specialty” Gyara zama tayi tace “see na manta ban tambaye shi wannan sketch din da muka gani a dakin shi ba, I swear Zee kamar fa idanuwan ki. Kin tabbata baki san Ya Musty ba before now??” Zehra ta fashe da dariya tace “I swear I don’t babes and please don’t talk to him about it, I don’t want him thinking mun yi mishi bincike a daki” Fadeela tace “well yeah it’s true, I won’t then” Bata ankara ba ta ji wayar ta tana ringing. Da sauri ta miqe ta koma wurin gado ta dauka. Gani nayi tayi tsalle tare da fadin “Laaa…Ya Moha” Bayan ta amsa ne tace “Ya Moha….” A dayan bangaren kuwa ji nayi yace “Baby Dee how are you?” Cike da murna tace “Fine Ya Moha” yace “Mummy just told me the good news, a big congrats to you. Allah ya sanya alkahiri” tana dariya tace “thanks a lot big brother, how are you doing?? Yaushe zaka dawo??” Yace “uhm, I think in less than 5 months, I am almost through here, cant wait to see you all” tace “me too Ya Moha, I missed you a lot” Gani nayi ta zauna kan gadon tace “hmmmm… Ya Moha you won’t believe what just happened, Yanzu Ya Musty ya zo dakin na yayi congratulating dina.. harda joke fa yayi cracking” cike da mamaki yace “you don’t say..” tace “dagaske, I was so happy” Yana dariya yace “I am glad he did, he is not as bad as you say Dee, trust me nature dinshi ne” Fadeela tana dariya tace “haka Zee tace..” kafin ta qarasa sai ta miqe tace “Ya Moha yau dai bari in ba Zee ku gaisa, duk lokacin da kake kirana we are not together” Kafin yayi Magana kuwa tuni ta miqa ma Zehra wayar wadda ta karba ta kai kunnen ta tace “hello, Ya Moha Ina wuni” A dayan bangaren kuwa shiru Muhammad yayi yayinda Muryar Zehra ta daki kunnuwan shi… gaba daya a rayuwar shi bai taba jin murya mai dadin wadda ya ji ba a yanzu. Bai ankara ba ya ji tace “ya Moha are you there??” Gyaran murya yayi yace “I am here Zee, how are you?” tace “fine” yace “that’s good, Dee tana bani labarin ki sossai. The inseparables right??” tayi dariya tare da fadin “yes” Yace “great, you guys should remain like that” tace “insha Allah” Yace “alright Zee, looking forward to seeing you when I return” dariya kawai tayi yayinda yace “good night then” tace “good night” ********** ✈✈✈✈✈✈ LONDON Muhammad wanda yake zaune a kan resting chair dinshi a gidan shi na birnin London ne na ga ya riqe wayar shi yayinda idanuwan shi suke a rufe. Gaba daya muryar Zehra ta rikita qwalwar shi.. banda amsa kowa babu abinda muryar nata yake yi mishi a kunnuwan shi. Ji nayi yace “what a sweet voice, she must be a great girl from labaran ta da nake ji a wurin Dee. Can’t wait to get back home” ♤♤♤♤♤♤♤♤ Oh oh oh… Can’t wait to get back home and do what?? hmmm🙃

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *