ZUCIYA CHAPTER 13
Nafi ta shiryasu tsaf sun zauna a falo sunata hirar su, labarin makaranta kawai suke bata itakam kai kawai take d’agawa amma sam hankalinta ba’a gunsu yake ba, abubuwan da suka faru a d’akine suke dawo mata.+ Ta zarfafa cikin tunani sam bataji shigowar Little ba, sai jitai an dafa ta, ta d’an xabura kad’an sannan tace ” Amrah me kika ce?” Little ta zagayo ta gabanta tare da harararta tace ” Feenah wato baki mayi tunani na ba ko?” Nafi ta kalleta sannan tai murmushi tace ” My Little tuba nake wlh sam hankalina yayi wani gun ne.” Little ta zauna kusa da ita tare da cewa ” Alamin yau ai karamar hauka yaso min.” Nafi ta d’an tabe baki tace ” Name kuma?” Little ta girgiza kai cikin takaici tace ” wai shi a dole ke da Ya Ashraf akwai wani abu a tsakaninku.” Nafi ta zaro ido tace ” kamar ya kenan?” Little ta d’aga kafad’a tace ” ohon masa, shi wai yanda kukeyi keda yaya sam bayaso, hankalinsa bai kwanta da yanayin yanda kuke ma juna ba.” Nafi tasa dariya sannan tace ” lalai da alama baisan Ya Ashraf ba shiyasa, me zaiyi dani?” Little ta d’an harareta tace ” kijiki ke kuma, wai ashe yaje gunsa kafin ki fita yana gaidashi amma yaya wai da kyar ya amsa mai.” Nafi tad’an turo baki kad’an tace ” wannan kuma ai yanayinsa ne ba wani abu ba.” Little tace ” Na fad’amai amma kamar zigashi nake, sam ya hanani zama agun kamun nan shidai wai sai na fad’amai ko kina sansa.” Tsaki Nafi taja tace ” daga had’uwa sai soyayya sai kace wata taxi?” Little ta kwashe da dariya tace ” Love at first sight yake so ku zama.” Nafi ta had’e fuska tace ” lalai wayaga.” Dariya sukai a tare. Bayan sallar sukaji kararrawar tarawa, Little cikin mamaki tace ” Meeting kuma?” Nafi tace ” Ai nikam kafin ki dawo nayi bacci.” Mikewa Little tai tace ” Bazaki ba?” Nafi ta jawo pillow ta kishingid’a sannan tace ” Family Meeting.” Little ta harareta sannan ta mike tai waje. Nafi ta gyara kwanciyarta tare da kalan wayar da Alamin ya bata, kai ta girgiza alamar a’a dan zuciyarta na raya mata ta kunna wayar. A can falo kuwa kowa ya hallara, Ashraf ne ya shigo daga karshe, ya ja kujera ya zauna. Kawu ne ya fara sallama nan ya tambayi dalilin taron? Asim ne ya mik’e sannan yace ” Abba in anci abinci zan sanar da kowa.” Anci ansha kafin Asim ya mike yace ” A gaskiya Abba bazan juri ganin abinda Ashraf yakema kanwata ba, yau cin mutuncin har yakai ya fifita wata kucakar ‘yar kauye akan matarsa.” Wani murmushi Ashraf ya saki, Mumy kam kallan Ashraf tai cikin damuwa, ganin abinda yai yasa ta fara tsoron karfa ya b’allo wata maganar dan tasanshi sarai. Kawu ne ya katseta da cewa ” Ban fahimceka ba, Fad’an tsakanin Ashraf ne da Matarsa?” Asim yace ” Eh.” Kawu ya kalli Ashraf yace ” Ashraf ya akai?” Kallan Asim yai ba tare da ya d’auke idansa ba yace ” Asim za’a tambaya ai kawu ni me na sani banda sani da akai nazo nan.” Kalaman sun ba kowa haushi sai dai ya zasuyi? Kawu ya kalli Anisa yace ” ke me ya faru?” Little kam fatanta Allah yasa ba Nafi ake nufi ba. Anisa ce cikin sanyin murya tace ” yarinyar nan ‘yar kauye ce ta nemi kawomin raini dan na sata aiki shine na mata fad’a akan ni ba sa’arta bace shikuma shine ya shigar mata ya wulakantani a gabanta.” Mumy ta kalli Ashraf, Kawu ne yace ” Ashraf me yasa ka wulakanta matarka akan tana nunama yarinya karama ‘yar kauye laifinta?” Ashraf ya kalli Anisa sannan ya kalli Kawu yace ” wannan kuma itace takeda amsar tambayar, me yasa nabi bayan yarinyar? ” Mumy ta kalleshi tace ” Ashraf me yasa kai haka?” Bai amsamata ba sai juya kai dayai, ya sani sarai dama yarda zatai da duk abinda akace mata yayi. Anisa ta kalleshi cikin sakalcin magana tace ” Yaya kaine fa kamin fad’a akanta.” Ashraf ya mike tsaye cikin takaici yace ” fad’a? Ai banaji wanda na miki yau sunanshi fad’a, sannan Umma ki maida ‘yarki kusa dake dan banaji tasan me ake nufi da aure, da kuma darajarsa.” Yana kainan yai waje abinsa. Cikin zafin rai Asim ya mike ya sha gabansa yace ” ce maka akai mun gama magana?” Ashraf ya kalleshi yace ” Me ya rage?takardar kanwarka? Ko ‘yan daban daka turo d’azu?”3 Asim ya kalli Ashraf cikin wani irin yanayi, Ashraf ya bubugamai kafad’a sannan yai gaba. Bakin ciki ne ya cikama Asim ciki a zuciye yai wani irin ihu. An gama taro kowa zuciyarsa ba dadi, Little ta shigo d’aki. A kwance ta hango Nafi rike da Qur’ani a hannunta. Ta shiga ta zauna kusa da kafarta. Nafi takai aya sannan ta kalleta tace ” kun gama? Little tace ” A kanki ma akai taron.” A tsorace Nafi tace ” ni kuma? Me nai? Nashina.” Little tai d’an yake nan ta zayyane mata abinda ya faru……Nafi ta mike a zabure tace ” Haka suka ce? Wow! Lalai na jinjina ma matar Yaya.” ta fad’a tare da tafa hannunta.+ Little tai dan dariya tace ” hmm dan ma Ya Ashraf suka samu? ” Nafi ta koma ta zauna tare da jan tsaki tace ” Ni fa gani nake Yaya nada zafi amma baya iya wani abun kuzo mu gani. ” Little tai murmushi tace ” Nafi bakisan halin Yaya bane, yanada masifar zuciya da taurin kai abu d’aya ne yake hanashi yin komai a gidan nan. ” Da mamaki Nafi ta kalli Little tace ” me kenan? ” “Mumy. ” Little ta fad’a fuskarta d’auke da damuwa, sannan tacigaba “Nafi yau zan fad’a miki tarihin gidan nan. ” Da jin haka Nafi ta gyara zama cikin zukud’in san taji meke faruwa. *TUNA BAYA.* ” Kakan Ashraf wato Sale ya kasance mutumin wani kauye ne dake garin Kila a karkashin jahar Jigawa, ya taso cikin wahala kasancewar mahaifinsa bashida hali sannan shi kad’ai ne namiji kuma babba agun mahaifinsa. Wahala kam na rayuwa ya shata, dan mahaifinsa ba cikaken lafiya gareshi ba, duk wani arzikin gona iin ya samu akan kannensa da iyayensa yake tafiya, hatta kayan da yake sawa sun jeme saboda tsabar wahala. Sam bai taba tunanin aure ba ganin nauyin dake gabansa sun mai yawa, har Allah ya kawo kanwar mahaifiyarsa ita da ‘yarta sukazo hutu gidan. Tunda Sale ya ganta yaji ya kamu da santa sai dai ganin ita daga birni take yasa ya kunshe abinda ke ransa. Fanna wanda take ‘yar kanwa ce ga mahaifiyar Sale a garin maiduguri suke, yarinya ce wacce ba ruwanta , tunda tazo gidan ta lura Sale kaya d’aya yake maimaitawa sannan sam ta kula baya zaka kullum aiki yakeyi. Ranar yazo fita ta d’au mayafinta tace ” zata rakashi. ” Ba musu suka fita tare, wannan fitar itace mafarin soyayya mai karfi data kullu a tsakaninsu, iyayenta sunyi takaici sun kuma so hanata wannan auren ganin ba komai Sale ke da shi ba. Fanna ta dage wanda hakan ya kaisu ga aure. Nan aka gyara mata b’angare anan cikin gida aka mata jere. Shekararsu d’aya da aure Allah ya azurtata da d’a namiji sai dai tana haifarsa Allah ya karb’i ranta. Aka sama yaron Abbas, Sale yayi kuka sam rayuwarsa ta canza kullum yana tare da d’ansa ko gona zaiji haka yake d’aukansa sutafi. Gulmar da ake a kauyen ne yasa mahaifin sa ya d’aura mai aure da Ruma ‘yar gidan babban wansu. Ruma na san Sale sosai sai dai shi d’ansa ne kawai a ransa, wanda hakan ne yasa Ruma ta d’au soyayya itama tasama Abbas. Ganin yanda takesan d’ansa ne yasa shima ya fara kulata har Allah ya bata ciki ta haifi namiji itama shine aka samai Mansir. Sun taso cikin kulawar iyaye sai dai kowa yasan sanda Sale yakema Abbas wanda sam baya iya b’oye hakan koda kuwa a gaban waye. Abbas na shekara 8, shikuma Mansir na shekara 5 Allah yama Sale rasuwa. Wannan mutuwa ta girgiza kowa, iyayen Fanna sukazo akan a basu Abbas ya zauna a gunsu. Sai dai Abbas ya tubure akan baza’a rabashi da kaninsa ba, hakanan dole suka had’a da Mansir suka taho maiduguru. A can kuwa kowa yafi nuna kulawa da damuwarsa akan Abbas, dan yana isa garin aka sashi a makaranta, Abbas na kokarin ganin duk abinda aka mai an ma Mansir sai dai duk yanda yaso abu ya faskara. Makarantar kud’i aka sashi aka sa Mansir ta government, sannan kafin asai ma mansir kaya d’aya to Abbas ya tara 5 dan ‘yan uwa ma na aikomai, wani sa’in haka zai dau saban kayansa yaba kaninsa. Haka suka taso cikin wannan rayuwa, Mansir yana tsananin kishin kauna da Abbas yake samu ta ko ina, a haka har Abbas ya gams karatunsa ya tafi Buk a kano. Mansir kuma yana aji biyar. Mansir tun yana Js1 ya fara san wata yarinya wacce akama mahaifinta transfer daga kano zuwa maiduguri. Yana tsananin santa sai dai ganin yarinyar bata Shiga harkar kowa yasa ya kasa sanar mata, har shima ya gama secondary ya fara poly dake nan garin Maiduguri. A kullum ya taso daga makaranta sai ya biya ta islamiyar su yarinyar wato Ruma, haka zai tabin bayanta har sai sunje gida ba tare da saninta ba. Kwatsam wani hutu Abbas yazo gida lokacin yana level 4 yaga Ruma, ba tare da gazawa ba yaje gidansu ya sanar da ita soyayarsa, cikin sa’a ta amsa masa, bai sanar da kowa ba saboda Ruma tace bataso a sani saboda mahaifinta yace karatu kawai yakeso. Soyayya mai zafin gaske ce ta shiga tsakanin masoyan biyu, a lokacin da Abbas ya sanar da Mansir akwai wacce yake so shima Mansir din yacemai akwai wacce yakeso sai dai shi kunyar sanar da ita yake. Abbas yai dariya sannan yace ” Kanina ai yanzu da zafi zafi ake bugan kirji karka kuskura ka jinkirta soyayyarks kar a maka shigo shigo…. ” Wannan kalamai na yayansa sun karfafamai gwiwa bayan Abbas yabar gida Mansir ya bugi kirji yaje gidan su Ruma. Sun gaisa kafin cikin fara’a zai fara koro mata abinda ke ransa ta katseshi da cewa ” Mansir ko? Kanin Abbas. ” Mansir ya washa baki yace ” Eh nine. Ruma ta d’anyi kasa dakai sannan tace “Ai koka yai? ” Cikin mamaki Mansir yace “a’a. ” Ta d’ago sannan tace ” ba wani nan, yace bazai fad’ama kowa muna soyayya ba amma wai bazai min alkawarin kin fadama ba. ” Gaba Mansir ne ya fad’i yace ” Kinsan yaya ai. ” Tai murmushi tace ” Yana sanka dayawa komai sai ya ambaceka. ” Mansir kam jiyai kafafuwansa suna neman Kasa d’aukansa hakan yasa yace mata kansa na ciwo ya tafi. Mansir ya rame, sam karatun ma ya kasayi, a lokacin ne Abbas ya gama nashi karatun, yama Mansir fada sosai ganin takardunsa ba abin arziki, duk yanda yai akan ya sanar dashi matsalarsa ya ki. Hakan yasa ya zauna da kansa yake koyamai karatu. Sai dai abin mamaki ya kula yanzu sam Mansir baya yarda suyi wata magana mai tsawo. Hankalin Abbas ya tashi, yana tsakiyar wannan kangi mahaifin Ruma aka maidashi kano, sannan mahaifinta yace ta fito da miji. Ruma kam kai tsaye ta gabatar da Abbas, nan aka kai kud’i tare da sa rana.” Little tai ajiyar zuciya tare da kallan Nafi wacce tai shiru tana sauraranta, tace ” Kinsan su waye mutanen nan uku? Nafi tace ” Abbas mahaifin Yaya, Mansir kuma Abban ki ko? ” Little ta d’aga kai sannan tace ” Ruma fa? ” Idanu Nafi ta zaro cikin shakkun abinda yazo ranta tace ” Don’t tell me???” Kai Little ta d’aga tace ” Yes! Mumy ce. ” Nafi ta zaro ido sosai cikin mamaki, Little tai yake sannan tace ” wannan shine mafarin komai dake faruwa. ” Nafi kam baki ta saki tana mamaki wannan sarkakiyar….. Little ta nisa sannan ta cigaba………….. Ayusher Mohd+ ” Mansir ya shiga wani yanayi ganin anata shirye shiryen auren yayansa da budurwar da yake masifar so, sam ya daina zama a gida wanda hakan ya tada hankalin yayansa. Abbas duk abin duniya ya dameshi ganin kaninsa a wannan hali, ana saura wata d’aya biki Mahaifin Ruma ya nemarma Abbas aiki a wani company na AL-Food.ltd, dan takardun Abbas sunyi kyau sosai. Company ne babba wanda ake ji dashi bama garin kad’ai ba har kasa baki d’aya. Kowa yayi murna sosai da wannan al’amari sai dai wanda ake dominsa sam baya farin ciki, an tsaida bayan aure da sati uku zai fara zuwa aiki a nan garin kano. Saura sati biyu biki Mansir ya shirya bada sanin kowa ba ya tafi kano,address din Ruma daya amsa agun wata kawarta yabi yaje gidan. Ruma kam alokacin ta dawo kenan daga amso dinkunanta na biki ta ganshi tsaye a bakin gate. Fara’arta ce ta karo ta karaso inda yake tace” Mansir yau kaine a garin namu?” Idanu ya kura mata gani yai ta kara wani kyau jiyai santa na kara ratsashi, ita ta katseshi da cewa “Mu shiga ciki mana.” Kai ya girgiza alamar a’a, tad’an had’e rai tace “na d’auka mun zama d’aya?” Sun shiga ya fara kallan tangamemen gidansu, lalai yaya ya cuceshi ya kwacemai Ruma sannan an bashi aiki ga iyayenta masu kud’i sosai?auren da yake fata kenan. Falon baki ta kaishi sannan ta shiga gida ta had’omai abinci da drinks. Fita tai ta barshi yaci abinci kafin nan ta koma,suka sake gaisawa sannan tace” D’an lelen Abbas ya akai?” Mansir yasadda kai kasa tare da d’agowa a marairaice yace “Ruma!” Yanda ya kira sunanta yasa jikinta yai sanyi cikin tsoro tace ” Badai wani abun ne ya samu Abbas ba?” Kai Mansir ya jijiga alamar a’a tai ajiyar zuciya sannan tace” Kaine ka tsorata ni Mansir.” Ya d’anyi yake sannan yace” Wata magana……” Katseshi ta sakeyi da cewa” kasan Mansir ni in na tashi da kai zanyi kishi?” Cikin rashin fahimta yace name fa? Ta d’an rangwab’a kai tace “yanda yayanka ke sanka mana, shifa babban burinshi shine yaga ya samu aiki ya fara kula da karatunka da kansa sannan yaga duk wani abu da kakeso a duniya ya maka shi.” Mansir jikinsa ya d’anyi sanyi,Ruma kam zuciya d’aya ta cigaba da sanar dashi tsarindaya shirya na ganin ci gaban ka,sam baya tunanina da kansa.” Mansir yai shiru, Ruma tace ” ya akai bai fad’amin zaka zo ba??” Kallanta yai da sauri yace ” shima baisan nazo nan ba” “Why?”ta fad’a cikin mamaki. Ya kara gyara murya yace “garin na shigo shine naga bari nazo mu gaisa, dan banaji zamu had’u da bikinku.” Bata gamsu ba sai dai da alama bayasanya fad’i gaskiyar abinda ya kawoshi. Murmushi tai sannan ta mai alama da ta tauke bakinta tace ” nima bazan fad’amai ba” Yai murmushi jiki a sanyaye ya mike zai tafi, ya kalleta yace “Me kikeso game da Yaya? Tai dariya sannan tace ” Mutum ne mai mutunta na gaba dashi, yanada ilimi,ga addini, gashi bashida kyashi.” Shiru yai, a zahiri gaskiya ta fad’a, yasan kuma yaya yafishi da komai,ya saki yake yace “Allah ya baku zaman lafiya.” Da sauri tace “Amin.” Ya fito jiki a sanyaye. yayan Ruma shine ya nemomusu gidan haya anan kano dan sam Abbas yaki yadda akan ya zauna a d’aya daga cikin gidan Mahaifinta ko na yayan nata. Ranar d’aurin aure da sassafe Mansir yabar garin maiduguri ya shiga motar Jigawa. Tunda Abbas ya tashi yaga ba d’an uwansa ya shiga wani yanayi nan ya bazana naimansa sai dai sam ba Labari, ga duk wayoyinsa a kashe. Har lokacin d’aurin aure Abbas bai dawo ba nan shima aka shiga naimansa a tasha aka ganshi duk ya rikice da naiman kaninsa,da kyar aka samu aka mai dashi aka shiryashi aka wuce dashi gun d’aurin aure. An d’aura aure sai dai ko jira baiyi ayi gaishe gaishe ba ya fita,wannan abu yaba iyayen Ruma haushi, a maiduguri aka d’aura auren gidan yayan babanta, dan dama mahaifinta ne kawai a kano da iyalansa. Mansir kam ya isa kila sai dai yayi dana sai,babu inda zai zauna kakaninsu sun rasu, mahaifiyarsa kuma tana aure a wani gidan tare da yaranta. Haka aka wuce da Abbas kano yana cikin tsananin tashin hankali, a ranar aka kai Ruma sai dai ganin halin da yake ciki yasa itama hankalinta ya tashi,Abbas ya sanar da ita akan gobe dole zaije Kila neman kaninsa, ba tantama ta amince. Abbas ya isa kila yaje gidan mahaifiyar Mansir nan aka kirashi, da kyar Abbas ya shawo kansa ya yarda suka taho, wannan ma sai da Mahaifiyarsa tasa baki,ganin in ya zauna a garin ma a ina zai zauna yasa ya amince suka koma,Abbas ya dage yanata tambayarsa akan menene matsalarsa sai dai Mansir yaki fad’amai, kano suka wuce,Abbas ya roki mahaifin Ruma akan subar Mansir ya zauna a b’angaren baki dake gidan,Abbas ya naimomai Buk. Haka rayuwa ta cigaba, sam Mansir baya sh ga harkar yayansa, har ya gama karatu shima yai aure, a lokacin Abbas ya kara samun matsayi saboda kwazonsa. Ruma har Mansir yai aure ko b’atan wata batai ba wannan abu na tsananin damunta, har matar Mansir ta haihu ta haifi namiji aka samai Asim, shekarar Asim 3 Allah ya ba Ruma ciki, farin ciki kamar suyi ka ka,a kuma wannan lokacin ne Abbas ya Fahimci ashe Mansir matarsa yakeso tun yana Js1, hakan ya faro ne sanda yaji Mansir suna hira da abokinshi wanda suke a maiduguri sai dai yana gama aji uku aka kaishi makarantar kwana, tundaga nan suka rabu sai yau suka had’u shine yake tsokanarsa ina Ruma kuwa? Dafatan ya aureta. Hankalin Abbas ya tashi ya tausayama kaninsa wanda yake gani kamar shine sanadiyar durkushewar farin cikin kanin nasa. Daga sanda Ruma ta haihu alheruruka sukai ta faruwa da Abbas, ansama d’anta suna Muhammad Ashraf. Dukiyar Abbas tayi yawa a lokacin da Ashraf yakai shekara 8 yanzu company ne nasa na kansa, sanda ya gina tafkekn gidan wanda zai ishesu rayuwa duk yawan ‘yayan da zasu tara shi da kaninsa. Ashraf ya taso mai tsananin san mahaifinsa, sun shaku sosai, alokacin ne kuma Abbas yake yawan zancen had’in aure tsakanin Ashrafda Anisa wacce take shekara biyu.” ” Abbas ya sanar da Ruma akan lalai ko bayan ransa karta kuskura tabar gidan nan sanda ta taimakeshi ya cika alkawari na ganin gidan nan ya zauna lafiya.” Mansir kam yana kishin yayansa ta harkar komai ganin duk abinda yakeso aduniya daga arziki, ilimi,mata da sauransu Allah yabad’aj uwansa ba shi ba.” Little tai ajiyar zuciya tare da share kwallarta tace “a lokacin Yaya na shekara 9 ne Mahaifinsa ya rasu,hatsarin mota yai, sannan Mumy na gama Takaba aka d’aura mata aure da Mansir wanda kowa bai san dalilin amincewarta ba. Har Baban Yaya ya rasu bayan an kaishi asibiti zancenshi d’aya ne akan Mansir ya yafemai. Nafi ta share kwallarta cikin tausayi, chakwakiya kenan, ta fad’a a ranta……….