ZUCIYA DA GWANINTA CHAPTER 4

ZUCIYA DA GWANINTA CHAPTER 4

 
 
 
Duk wani hiran su da Amina sun gama shi, shirin bacci su kayi don har sun kashe wuta. Amina kam har ta tofa addu’a sai ga Mami ta shigo ta kunna musu wutan.
“Har kun kwanta ne?” Ta tmby su, a tare su ka amsa mata. Tace “okay it brief, Nabeelarh Abban Ku zai je Bauchi gobe, Umma ba ta dan ji dadi zai je dubo ta. Yace in tmby ki zaki bishi ne ko kuma sai nan gaba?”
“Mami me ke damun Umman?”
“Kawai ba ta jin dadi ne kwana biyu kinsan an fara tsufa. Za kije in?”
Shiru tayi tana tunani, to kadunan ma ba wani dadi ya ke mata ba ko bakomai a can Umma za ta na sata nishadi “zanje mami” da sauri Amina tace “mami nima ina son zuwa” hararan ta mami tayi ta kashe wutan dakin “ke da ke zuwa school, lafiyan ki kuwa?” Dif Aminan tayi.
Tunda Asuba ta tashi, ta san tafiyan Abbah da Safe yake yi ko da kuwa Zaria za shi balle bauchi. Su Aiman da Siyama kaman su yi kuka da zasu wuce School, lallaban su dai tayi su ka wuce. Aiman da Siyama su Hampos su ke, Amina ce dai ke Universal sai Sadeeq da ke Darul Iman, makarantan da Nabeelarh ta gama.
Wuraren takwas da yan mintuna Abbah ya fito su ka kama hanya. Ita dai har wani irin ta keji ba ta ji dadin barin yan kannen ta da mami ba, yaushe rabon da ta zauna gida ta dade sai daiyanzu kuma da dama ya samu za ta kwashi kafa tayi bauchi? Anya ba za ta biyo Abbah su dawo ba kuwa? Ita kadai abinda ta ke ta kullawa tana kuncewa. “Daughter lafiya na jiki shiru kuwa?” Abbah ya tmby ganin yanda jikin ta yayi sanyi.
Murmushi ta kakalo ta ce “Lah bakomai Abbah”
“Applied Chemistry kika yi applying ko?” Da eh ta amsa mishi yace “Daughter za ki iya KASU kuwa? Ko dai in kaiki private University, ga baze, Nile a Abuja ga Alqalam katsina ko Alhikmah Ilorin” dan jim ta yi tana tunanin ina ne mafita. Can kuma sai tace “Abbah ko ina ka kaini zan iya karatu In sha Allah” murmushi yayi sanin halin yar tashi akwai kawaici ko da ko akan abinda ta ke so ne “ba za ayi haka ba Daughter, ki dai yi tunanin duk inda kika ga ya miki sai ki fada min, in ma Kasu in ne duk ai ba matsala”
Karfe biyun rana su ka isa garin bauchi. Old GRA a nan gidan Umman. Da fara’an ta, ta karasa ciki tana Kiran “Ina kike fito na iso” daga daki taji Umman tayi gyaran murya.
“Hajiya Umma Sallau kenan” ta fada da dan dariyan ta, sannan ita ma tayi saurin shiga bayi. Abbah Kam suna shigowa ya nufi Masallaci, dake shima ya tarar ana Sallan. Har ta idar da Sallan ta, ta gama azkar Umma ba ta gama Nafilfilun da take yi ba. Dan tabe baki tayi, a hanyan kitchen ta hadu da baba saude, Mai aikin Umman. “Baba Sannu da aiki, Allah ni dai Yunwa nake ji”
Dariya baban tayi tana fadin “Maraba da Uwar dakina, Hajiya Nabee ashe har dake ake tafe” turo baki Nabila tayi tana hade rai.
“Ni fa nace miki ban son sunan, babah mana”
“Afuwan Uwar dakina, je ki abinki yanzu zan kawo abincin” da dan gudun ta Nabeelarh ta fita zuwa falon gidan. Girgiza Kai babahn tayi, tana mamakin har yanzun akwai sauran yarinta gun Uwar dakin nata, duba da yanda ta ke kwasan gudu hankalin ta kwance, ba tare da wani damuwa ba.
Sai lokacin Umma ta idar da Sallah ta fito falon “ke Kuma me ya kawo ki? Nace ki zo ne?” Nabeelarh ba ta amsa ta ba ma Sai ma saurin rungume ta da tayi.
“Ni dai nayi kewan ki Ummah, shiyasa nazo” dariya Umman tayi tana fadin “in dai kika karya ni, to wlh Uban naki da ya kawo ki ban neme ki ba shi zai biya ni Kashi na. Kuma ba asibitin da aka isa a kaini”
Share zancen Nabeela tayi, don ba yau Umman ta saba fadin haka ba. “Ni dai zo ki bani abinci a baki, don wlh yunwa nake ji. Ni gidanmu ban saba da zama da yunwa ba gsky” dakuwa Umman tayi Mata.
“Kinsan ni kuwa ban gaji Yunwa ba. Kuma ni banda halin Uwar taku, da sai ta Kai karfe Tara na safe fa sannan wai zata tashi ta daura ma mutum abinda zai ci. Shiyasa ai na daina zuwa wannan gidan naku, banda ganawa mutum azaba ba abinda ake” Nabeelarh dai bata ce komai ba, tasan tana fadin wani abu Mami zata ja ma zagi. Ta rasa dalili, Sam Umma ba ta shiri da Mami. Duk kuwa abinda Mami zata Mata to bai birge ta. In kuwa aka ce yau Umma na hanyan zuwa Kaduna, to fa ranar tashin hankalin Mamin ya zo kenan. Duk dai cikin jikokin ta ba Wanda ta ke hantara, dan tsaf take zama ayi ta wasan jika da kaka da ita to Amma Uwar fa Sam ba ta daukan mata ba. Abun naci ma Nabeelarh tuwo a kwarya sosai, don ta dau alwashin watarana Sai ta tasa Umma ta gaya Mata mai mahaifiyar su ta mata haka da zafi.
Suna cikin cin Abinci suna hira ga Kuma Tv dake ta faman aiki shi kadai dan dai a cikin su ba Wanda yake kallo. A haka Abbah ya shigo ya same su. Hade rai tam Ummah tayi kaman bata taba dariya ba tana ganin shi. Shi kuwa zama yayi a kasa yana fadin “Ummah mun same ku lfy?”
“Da ba Lfy ba ai kana shigowa zaka gane. Yanzu Kai tsakanin ka da Allah in Kira ka musamman in gaya maka ban jin dadi kazo ka duba ni, shine don Ma’u ta fiye maka ni shine zaka fara zuwa duba iyayen ta kafin ka shigo min nan” Murmushi kawai yayi, daman yasan za ayi hakan.
“Aa Ummah ba inda na shiga, kawai dai mun hadu da su Ba!ah Waziri dasu Yaya Garba ne a masallaci shine na tsaya muka gaisa Sai Kuma Muka dan tattauna” tabe baki tayi kaman ba ta gamsu ba, can Kuma tace “To ba laifi, ai shi zumuncin irin haka Yana da kyau. Shiyasa ban so komawan ka kadunan nan ba ni. Kai yanzu da ban Kira ka ba nace ban jin dadi ashe baka San kazo dubani da jiki na ba ko. To Maryama ma dai da bani na tsugunna na haife ta ba, ba haka take min ba. Haka ma dan uwan ka Idriss ba Wanda ke min haka a cikin su” Rusunawa yayi kawai ya bata Hakuri, ba wai don laifin yayi ba Sai dai ba yanda ya iya.
Abinda ma yake bashi dariyan shine, bai wata daya bai tako bauchi ba. Mamma da take magana kuwa tana Abuja, Sai tayi 3 to 4 months ba ta samu zuwa Bauchi ba to balle Kuma Idriss da ke aiki da LNG a can bonny island dake Port Harcourt. Yaushe ma ya samu hutun balle ya tako zuwa Bauchin. Kawai dai yasan bai dade da komawa bane ya sa ta fadin hakan.
Ummah kenan, yawancin hiran a mita ya Kare. Shi dai Abbah bin ta yake sau da kafa, Nabeelarh Kam ko a jikin ta. Tana gama cin abincin ta ma ta debi jiki ko sallama bata ma Umman ba ta nufi can cikin gida. Tunda Family house ne, dukkan Yan uwan mahaifin nasu da ma na Mami na cikin gidan. Abinda ke kara daure Mata kai kenan, domin dai Mami da Abbah yan uwa ne. First cousins ne, duk a cikin gidan suka girma tunda ya’yan Wa da Kani ne. Sai da labarin da suka samu, Umma da Inna (Mahaifiyar Mami) kishiyoyin balbali ne, tun daman ba wani jituwa suke a tsakanin su ba. Duk da dai ba sa Fada ko cacan baki.
Amma tsakanin Ummah da Ba!ah Waziri, Baban Mami kenan. Mutunci ne zalla da girmama juna.
Wurin Inna ta Fara zuwa domin gaishe ta, Kaman kullum Innan ba wani sake Mata fuska tayi ba, a yamutse take amsa mata gaisuwan nata. Daya daga cikin abinda ke damun ta kenan Kuma, ta rasa dalili duk sauran jikokin nata faran faran take dasu Amma banda ita. Saboda haka ma wani lokaci ba ta ganin laifin Ummah in tana mata wani abun. Ta taba tmbyn Mami dalilin da yasa Innah ta ke mata haka, Amma Kuma sai mamin ta kwabe ta da Kar ta kara Mata irin tmbyn nan. Ba ta da hankali ne, da za tace mahaifiyar ta ba tason ta. Ta dai yi shiru ne Amma ta san dagaske Innah ba ta son ta. Kaman yanzu, ko tmby su Mami ba tayi ba balle Kuma jin ya tazo ko yaushe tazo in. Illa iyaka ce mata da tayi “Kije ki zuba abinci a kitchen”
“Naci a wurin Ummah”
“Toh Madallah” Innah ta fada daganan ba ta sake cewa komai ba. Don takaici ko Sallama Nabeelarh ba ta tsaya mata ba, ta taso tayi ficewar ta. A hanya ta hadu da Ba!ah , Wanda suke cewa Ba!an Mami. Shikan da fara’an shi yake cewa “Au ashe da matar tawa aka zo” Dan daure fuska tayi, ta turo baki. “Gsky ni ka daina fada, kullum fa Kara tsufa kake kaja min wancan tsohuwan matar taka tana kishi dani” da gangan ta fadi hakan, saboda tasan tsaf in Ba!ah yaji abinda Innah ta Mata Sai ya wanke ta tas. Yanzun ma kuwa yanayin fuskan nashi ya canja amma Kuma Sai ya fuske yace “Share ta tayi ta kishin ta, ko zata yi ya Amaryata Sai ta shigo gidan nan. Ya kika baro mutanen gidan?”
Nan su ka gaisa, a kasan ranta tana jin dadi tasan Ba!ah dole zai ma Innah fada. “An gama Sakandiri in ashe?”
“Eh Ba!ah ko kazo graduation in Amaryar taka Kuma” Sai da ya dan dara yace “Rufa min asiri, a ganni tsofe tsofe dani ai Sai in korar miki samarin. In rasa Kuma wa zan makala ma” dariya tayi “kaji Ba!ah Sai dai kace wata kaya” yanzun ma da dan gudun ta, ta fita daga sashen nasu.
Sashen su Baba Garba ta nufa, Wanda yake da na farko a wurin Innah. Ya girmi Abbah ma don Ba!an su Mami ne Babba akan nasu Abbah. So Sai da yayi aure kafin a auro Ummah. Matan shi Uku, kuma duka Allah ya wadata su da arzikin yara dayawa.
Halima, Yar Ammi. Second wife in Baba Garba ita ce sa’a Kuma kawar Nabeelarh. Yanzu haka tare suka yi Candy in. Ita ma Halima makaranta kwana tayi, can alkaleri ta gama. Tana da yayyi manya dayawa, musamman daga dakin Mama, Uwar gidan Baba kenan. Yawanci Kuma Mata ne, shiyasa duk sunyi aure. Sai Khalipha Wanda yanzu haka yana bautan kasan shine.
A dakin Ammi kuwa Haliman ce babba, Sai kannen ta Mata da maza. Wasu na makaranta kwana wasu Kuma day. Anty ce dai Amaryan Baban, ita yaranta uku. Babban ma yana primary five ne.
Tun daga soron sashen take cin karo da yara na fitowa daga ciki. Da ke gidan na cike da wasu Yan uwan da ba zata ce ga ta yanda suka hada ba ma. Domin dai tun Zamanin Mal, kakansu Abban ma. Shi ya gina gidan, ya Kuma cika gidan da Yan uwan shi da Kuma ma makota, wasun ma Almajirai ne, da zama yayi dadi suka dawo yan gida. Suma su kayi aure suka ajiye iyalan su a nan gidan.
Gida ne Babba, Wanda ba a iya tsayawa kimanta yanayin girman shi ba. Sashen Innah da Ummah ne kawai daman yake daban Kuma a wuri daya. Sai kuma sashen Baba Garba, da aka ware shi musamman aka yi ginin zamani. Gidan Yana da girman da ba Sai wani yaro daga ciki ya fita neman fili ba. Ko su Nabeelan da, a cikin gidan su ke. Transfer in da aka ma Abbahn ne yasa suka bari. Amma duk da hakan, sashen nasu na nan in sun zo hutu.
“Ke Kuma daga ina?” Daga bayan ta, taji an fada. Tana juyawa ta ci karo da Ya Khalipha yana ta murmushi. Ita ma da saurin ta karasa inda yake “Kai Yaya baka San na fara tashi ba hala?” Hararan ta yayi, daman yasa ba a binta bashin zance kam.
“Kaniyan ki Nabeelarh, da Abbah kuka zo ashe. Irin kema an yi Candy an zo hutu kenan ko?”
Dariya tayi kawai, tana mamakin yanda ya San ta iya maida magana dai dai da yanda aka Mata. Amma Kuma hakan bai hana ya tsokane ta cikin wasa ba. Kallon dan yaron dake gaban ta tayi. Usman Mai sunan Abbah “Yaya to wannan ma ya fara tafiya…” Tana fadin haka ta kwasa da gudu don ta san yanzu ba karamin aikin shi bane yace zai rankwashe ta, gashi daman ta San shi da mugun ta ga Kuma zafin hannu.
Side in Mama ta shiga, ta same ta tana fama lissafin balance in da aka kawo Mata na businesses in da take yi. Mama kenan, sarkin sana’a. Mace da ta San mahimmancin neman na Kai sosai. Tana ganin Nabeelarh, fara’an ta ya dadu tana fadin “Maraban da mutanen garin gwamna, ashe hutun candyn mu za a zo ma. Itan ma da fara’an ta, ta karasa. Tana son Mama, saboda yanda take ji da ita. Tun dama in su kayi rashin jinta ita da Halima, Mama ke Kare su duk fadin gidan.
Da gudu Halima ta fito daga cikin dakin har tana cin tuntube “Muryan wa nake ji kaman na Beelah” ita kadai ke ce Mata Beela a gidan. Tana ganin ta kuwa, su ka rungume juna suna ihun murna. Mama Kam tsayawa tayi kawai tana kallon su, a ran ta Kuma tana tunanin yaushe yaran nata za su girma. A nan side in Maman su kayi zaman su, suna ta hira abun su. Ko Ammi da Anty Sai daga baya suka je suka gaishe su. Ammi daman ba gwanar magana bace hakan yasa yawanci yaran tarewa a bangaren Mama. Anty kuwa har yanzun Nabeelarh ba wai ta gama sabawa da ita bane.
Ba ita ta koma wurin Ummah ba Sai bayan Isha’i. Hakan ma da Halima suka tafi akan a can zasu kwana. Suna shiga ta gansu tayi saurin mikewa, nuna musu hanyan kofa tayi “Ku fita maza ku koma inda kuka fito. Ni Kam ba Zan iya da shedanci ku ba Wlh. Ku baro iyayen ku, ku zo nan ku hanani bacci, iyayen ku na can na juyi ko? To bazan dauka ba” Nuna Nabeelarh tayi da dan yatsa “Ke tsabagen kin raina ni, tsallake ni kika yi a nan ba ko Sallama kika tafiyan ki gantali Uwa duniya” koma wa gun Halima tayi, ya cigaba da cewa “Ke kuma nasan Abinci na kika zo ci, Sai kace uwayen naki ba Wanda ke daura murhu. Inma ba su yi ba ki tafi wurin Kakan ki mana” Duk basu tanka ta ba, Sai ma kallon juna da suka yi a tare kaman suna Shirin hada plan. Ai kuwa daga ma juna gira su kayi, da gudun su suka afka cikin daki tana “Kai! Kai! Ina wasa daku ne wai?” Ba ta samu amsa ba, Sai Karan key kawai da taji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *