ZUCIYA DA GWANINTA CHAPTER 5

ZUCIYA DA GWANINTA CHAPTER 5

 
Sai da suka gama sa key in, a tare suka zube kan gadon. Sai Kuma suka kalli juna su ka tuntsire da dariya. “Kai Ummah case ce wlh” Halima ta fada tana kara yin nishin gudun da suka Sha.
“Ina Sabon wayan naki? In gani” Sai da Haliman ta fadi hakan sannan Nabeelarh ta tuno tunda ta iso, ba ta bi takan wayan ba ma baki daya. Jakan ta, ta nuna ma Halima kawai. Don tsoron Kar ta fita Ummah ta titse ta, ruwan toilet ta bude famfo ta dirka tana cigaba da kwasan dariya.
“Keh wa ya Miki irin wannan missed call in wai?” Halima ta fada cike da mamaki. Dam! Taji gaban ta ya fadi. Sai lokacin Cooper Abubakar ya fado Mata, ba ta ko shakka shi inne yayi ta neman ta. Gashi ba ta jin ta fada mishi zata zo Bauchi ma.
“Mu gani” a tsorace ta amshi wayan tana bin shi da kallo. Barin ma da ta tabbatar dashi inne yayi ta neman ta. Ba ta tare da ta sani ba, nan take yanayin ta baki daya ya sauya. Har wani irin dimi take ji na ratsa ta, ga yanda ta kara kura ma wayan idanu kaman zata shige ciki.
“Ke lafiyan ki kuwa?” Jin muryan Haliman ne, ya sa ta juyo ta kalle ta. Kaman za tayi magana Sai Kuma ta rasa abin cewa. Ba su taba maganan saurayi da Haliman ba a rayuwan ta, bar su dai suyi tsokanan su, ayi gulman wance da wane. Shikenan kawance, Sai Kuma yayin da suke zuwa Islamiyya a tare, wannan Kam har malamin su, sun sa ma hawan jini kila.
“Wa ke Kiran ki?” Haliman ta kara tmby.
“Ehmm wan…” Kasa karasa zancen tayi saboda yanda Halima tayi tsalle tana fadin “Your Boyfriend right?” Hararan ta Nabila tayi, Sai dai duk yanda ta so boye abun. Fuskan ta ya riga da ya bayyana komai take kokarin boyewa. Why is she so obvious ne? Meyesa ba ta iya boye abinda ya dangance shi ne wai?
“Iyye ashe munyi saurayi, to ya sunan shi? Come on tell me about him mana” kasa magana tayi, Sai ma tsintan kanta da tayi da wani irin murmushi. Ganin irin kallon da Haliman take Mata Kuma sai tayi saurin boye fuskan ta cikin cinyoyin ta, tana faman dariya kasa kasa.
Duka Halima ta dada Mata a baya “Ke dai banza ce wlh, ni Kuma kike jin kunya? Wai tsaya ma, what so new about this?” Kallon ta Nabilan tayi sosai “Kya jiki, ke kina dashi ne?”
“Ina dasu dai” Nabilan tayi saurin fada. Ganin irin kallon da Nabila tayi Mata yasa ta cigaba da cewa “Kallon fa malama ban Kai bane ba? Kinfa san muna fara University Baba ke mana aure, so gwara inci duniya ta da tsinke kafin lokacin yayi”
“Ba dai kyau yaudara” tsaki Halima taja “Yaudaran me? Ina da dayan da yafi kwanta min ai, zai ma zo gobe, zamu je ki ganshi ai. Now tell me about yours”
So confuse, Nabilan tunanin ta Fara yi kenan is normal every girl her age ace tana da saurayi kenan? Ba ta gama tunani ba Sai ga Karan wayan ta ya kara shigowa. Jiki na rawa ta dauka, a hankali tayi Sallama.
Shi inma a Hankalin ya amsa. “Ignoring me?” Yanda ya fada hakan, Sai da ya sa Mata jin wani iri har ranta, he sounds disappointed sosai. Sam, tana jin ba ta kyauta ba. Gashi shi bai manta da ita ba, Yana ta faman Kiran ta. Amma ita Kam zuwa tayi kawai tana harkokin gaban ta.
“Are you not talking to me again?” Ya Kara fada cikin cool voice in da ke kara ratsawa har cikin jinin ta.
“Ehm Ehm am sorry please Sir na manta da wayan ne a cikin jaka tun dazu” cikin rawan murya ta amsa mishi, he can even sense it.
“Kin manta dani kenan?” Ya Kara fada cikin muryan da ya fara saukan mata da kasala. Gabadaya ma, ji take kaman ba ita ba. Too many feelings to accommodate for three days, straight.
“Aa fa, I travel ne. Munje bauchi da Abbah. Shine na shiga cikin gida na bar wayan muna gaisawa” dan jim yyi zuwa can yace “Kinje Ziyara kenan? Ya kika samu su Umman” An dan sabon da suka yi a school, ya san dayawa daga cikin Yan uwan ta.
Sun danyi magana, ya tmby ta yaushe zata koma Kaduna. Ta gaya mishi Sai Abbah ya sake dawowa kawai, so ba date kenan. Normal hira su kayi har Sai da ya zo wurin karshe sannan yace “To Nabila bara na bar ki, ki huta ko? Kin dauko hanya. I appreciate having your time and for the sweet voice, I will love to continue on hearing it every single day of my life” rasa abin cewa tayi, Amma tabbas zancen nashi ya samu wurin zama Mai kyau a kwakwalwar ta. She likes that, he compliment her voice. Ita kanta ba ta San muryan nata na canjawa in tana magana dashi ba Sai da taji Halima na tsokanan ta, da tana cikin wayan. Da ta natsuwa da kyau, sai ta lura, her voice is di!erent Sai dai ita kanta, ba zata ce ga yanda hakan ya faru ba.
“Baki ce komai ba” shirun ta kara yi, Sai ta bude baki za tayi magana Kuma sai ta kasa. Siririn dariya yayi ta yanda ta ke iya jiyo muryan shi “Nabeelarh kenan, to tell me do you enjoy hearing mine?” Murmushi tayi a fili, Sai dai ta kasa fadin komai. How can even she start describing how she feels a duk lokacin da sautin muryan shi ya sauka kunnen ta.
“Tell me mana, something sweet that will keep me to sleep”
“Ehm ehm” Sai Kuma tayi shiru, maimakon ya hakura kaman yanda take fata Sai taji ya sake cewa “ko rowa za kima Sadeeq in naki? Ehm?”
“Sir…” Ta fada cike da kunya, ji take kaman ta nutse a wurin ma duk kuwa da bai ganin ta.
“Eh mana, ko ni ba naki bane Angel?” Sai da ya jiyo sautin murmushin ta, duk da kankantan shi. Hakan ke kara tabbatar mishi yakin shi na kaiwa inda yake bukatan yaje in.
“Shknn tunda you can’t talk. Answer me in mssg, zan jira ki yanzu. Kuma soon zaki daina jin kunya ta, I promise.” Yana fadin haka ya kashe wayan.
Ta dade tana tunanin message in da ya kamata tayi composing. Sai zuwa can da kyar ta iya fara typing. Simply kawai ta rubuta “It always sound nice and lyrical. I like it” da kyar ta iya danna send. Don har gogewa tayi ta kara typing, Sai da ta gama contemplating sannan ta tura in. Halima na gefe Sai dariya ta ke Mata.
Sir: “You can’t voice this out? Lallai ke bakauyiya ce”
Dariya tayi bayan ta karanta, ba yau ya fara kiranta bakauyiya ba. Don haka tayi saurin typing back.
“A hakan dai a hakan dai” Sai da ta tura sannan tayi realizing mai words inta ke nufi. Sai dai she is already late, saboda zuwa lokacin har ya karanta ma.
Sir: “au haka kika ce? I wonder how i fall for you. Amma ya zanyi? You have squeeze your ways into the poor guy heart Beelarh. So zamu ajiye kunya and be romantic kawai” da kanta tayi giggling.
“Do you not like it choice, i mean your heart? Or do you wish am a better person than i am?”
Tsoro, karara ya bayyana daga cikin sakon da ta tura mishi. She is clearly worried she is not up to his standard, hakan na nufin ta damu da zabin shi kenan. Wow! Another progress for him.
Sir: “Budurwa ta is perfect for me, everything i need, I will guide her through. So ki kwantar da hankali, Kar kika sa bacci”
“Ni me zai hana ni bacci to?”
Sir: “Tunanin Sadeeq, ko bai Kai matsayin ba?”
“Ni bance ba” Dariya yayi ya Mata reply, daga haka kafin ta ankara sun Kai kusan 12 suna exchanging messages. Tun tana dariya ita kadai, har Halima ta gama wayan ta, tazo tana taya ta samo ideas in amsan da zata bashi. Da kyar ya kyale ta tayi bacci. Baccin ma tukunna, Sai da ta gama juye juyen ta kafin ta samu ta yi shi.
Washegari kuwa, ko da ta tashi ta iske Abbah ya riga da ya tafi. Don haka Kai tsaye kitchen suka nufa, sun samu baba ta ajiye musu abinci a kula. Don dai Ummah Kam sun san tun kusan bakwai da wani abu take karyawan ta. Sama sama suna jin tana mitan “Ayi yara zuciyar su ta mutu a kwanta ayi ta bacci har rana ta fito? In har mutum na neman cigaba kuwa a rayuwan shi, to dole ya ajiye bacci da safe. Kai rayuwa ma tafi albarka wlh. Mu dai iyayen mu ba haka su ka koya mana ba, Kuma mu ma ba haka muka koya ma naku iyayen ba. Su dai suka cuce ku, Kuma Allah zai tmby su” haka ta karaci mitan ta, ta wuce. Sai dai har zuciyan su, sun San cikin kalaman ta akwai gsky a ciki.
Ba laifi ba ta tsaya mita ba ta amsa gaisuwan su, don ta gama sallan walha kenan. Suna cin abincin tana gefe tayi banza dasu kaman ba zata tanka ba, Sai can tace “Amma dai Halimatu kinji kunya wlh, yanzu tsakanin ki da Allah abincin nawa kike ci? Sai kace kakancan naki bata daura murhu ba? To wai ma tsaya duk Matan da ubanki ya auro su miye amfanin su wai?” Kyabe Halima tayi ta cigaba da cin abincin ta. Don mitan Ummah ya riga da ya zame Mata jiki ita Kam. Duk cikin yaran gidan, ita ce suka fi sabawa. Haka za tazo side inta, ta zauna tana mitan tana korafi Amma da bata ganta ba, za ta sabi kafa har side Mama, dake tasan suna can. Tace ta zo bikon Halimatun ta. To ranar duk abinda take bukata yi mata ake, kafin a sake banbarewa. Don ko Inna, Halima ba tayi wannan sabon da ita ba.
Sai bayan sun yi Sallan Azahar suka nufi gidan Siyama, Wacce Halima ke bi duk da ba dakin su daya ba. Amma sun taso tare kaman kawaye, shekara biyu ta bata kawai. Duka duka auren ta bai wuce wata takwas ba. Tana aure Halima ta samu wurin zuwa, ko kawayen ta wani lokaci nan su ke samun ta. Duk sabon saurayin da tayi kuwa, a gidan suke haduwa. Tunda Siyama ba ta isa ta kwabe ta ba. Tasan gida har dukkan ta Ya Khalipha Sai yayi. Nan gidan Siyama kuwa karen ta, take ci babu babbaka. Ga Kuma mijin ta ba Mai zama bane, abinda ya Kara ma abun armashi kenan.
Suna isa, Siyama tasan akwai abinda ke tafe dasu. Ta dai ji dadin ganin Nabila, amma ba tayi zaton ita ma yanzu tana iya kula samari ba. Sai da ta ji Halima na tsokanar ta zancen Abakar. Girgiza Kai kawai tayi ta basu wuri. To dake ranar Wanda zai zo, cousin in mijin tane. Kuma ta wurin ta yake kamun kafa, don haka ita ma Sai ta taya su. Aka hada lafiyayyen abinci da abin Sha, komai yayi zam zam. Sannan Halima ta Sha kwalliyan ta, kaman Wanda mijin tane zai dawo.
Da yamma ya iso, tare da abokin shi. Har parlor kuwa aka sauke shi, aka musu iso Mai kyau. Gasu nan dai Ma Sha Allah, Sai dai kana ganin su kasan shirme ne kawai. Ko Kuma ganin mutane ne haka, oho.
“Ga Yar uwata Kuma kawata Nabila” Halima ta fada tana nuna ma saurayin nata Nabilan. Cikin wasa da dariya suka gaisa, har yana dan tsokanan ta. “To ke kuma yaushe zamu ga naki gwanin?”
“To ba gani nan ba” Abokin shi da ke gefe, yayi tsumbul ya fada. A tare suka juya suna kallon shi. Nabila Kam ba ta San Sanda ta aika mishi harara ba.
“Tab! Rufa ma kanka asiri, kafin Romeo ya ji wannan zancen.” Halima ta fada, tana Kara dariyan reaction in Nabilan, Wanda zuwa yanzu ranta in yayi dubu ya fara baci.
“Afuwan Yar uwata. Da alamun dai ana ji da koma waye wannan. Amma Kuma nima zan so a bani daman ai, in har ba matsala” da sauri ta juya ta kalli Halima, alamun ta dakatar dashi. Dariya Halima tayi, a kunnen ta, ta rada Mata wani abu. Kara tamke fuska tayi tana hararan ta, dai dai lokacin wayan ta Kuma ya hau ruri. Da murmushin ta, ta dauka suka fita daga falon.
Da hira ya dau hira ne, yake sanar da ita suna da Family meeting a Taraba, so zai tafi in 2 days. “Ko in tsaya a Bauchi in ganki ne?” Shiru tayi, duk da ranta na son hakan saboda ita ma tana muradin ganin nashi. Ba zai dai ta iya fadan bane kawai.
“Tun ban samu daman zuwa gaida Abbah ba, Sai inzo in gaida Ummah. Ita dai nasan ba wani matsala ko akwai?” A take ta girgiza Kai tace “Babu, Amma Kuma zata fada ma Abbah da su Baba Garba. Za ta sa suyi tunanin aure nake son yi”
“To wai ke miye in ance auren kike so Nabila, ai kin Kai kiyi auren ne.” Ya fada Kai tsaye yana mamakin sauran yarintar ta.
“In zo ko Kar inzo yanzu dai?” Dan jim tayi, Sai Kuma a hankali tace “Kazo in Amma ba gidan Ummah ba”
“Ya ilahi! Nabila to a ina zan ganki?” Kai tsaye tace “Gidan wata cousin sister ta, can in zai fi zama secret”
“I don’t want to be a secret” yayi saurin fada. “Umman dai zan zo in gaisar, tun yanzu ma ki fada Mata za ta yi bako Jibi in Allah ya kaimu. So sai ki shirya”
Da tunanin ta yanda zata fara ta wuni ranar, har samarin Halima suka tafi. Duk yanda abokin nan ya so ganin fuska ba alamun shi. Sun fita musu rakiya kenan, Sai ga motan Ya Khalipha. Kallon juna suka yi, lokacin da samarin su ka wuce, shikuma yayi parking. Da saurin su ka gudu cikin gidan, sanin yanzu Sai ya basu kunya. A tsaitsaiye ya shiga ciki, daman Mama ta aiko shi amsan sako wurin Siyaman. Yana amsa yace “Kira min marasa kunyan yaran nan, mu tafi gida” ita kanta Siyaman Sai da ta tausaya musu, Sai dai itan ma ba kyale ta yayi ba.
“Ke Kuma Zaki gaya min in kinyi aure ne domin gidan ki ya zame musu wurin tara samari”
“Wlh Yaya ba ruwana” hararan ta yayi “Ai suke Miki iko da gidan ko? Bara mijin naki ya dawo, da kaina zan tambaye shi ko shi ya bada izinin a dinga mishi haka a gida” bai tsaya jin magiyan ta ba, yasa su Nabila a gaba suka shiga mota.
“Kuma wato har kun girma kunsan tara samarin banza ba” Nabila Kam, don dai tasan rashin a bace yake. Kuma in ta maida mishi maganan da ta saba, ba abinda zai hana ya libge ta ya sa tayi gum. “To na rantse da Allah, na kara ganin wata yarinya da saurayi, Sai ta fiddo shi an musu aure. Kuma ku Kara ku gani” bayan hakan, Sai da ya Kara musu da rankwashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *