ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
Rausayar da kai yayi, a cikin kallona, ya lumshe idanunsa ya bude.
“Yaya akayi kika sauya haka? ‘What a sudden and awkward change! I need an explanation if you want to go out”.
Idanuna suka wani irin lumshe da kansu, na debo karfin zuciya na bude su tangararau akanshi.
“Allah Ya hana bincike, kaga Allah Yaya Fa’iz yunwa nake ji… ka bude min kofa”.
“Allah Ya hana bincike, amma ke kika yi?”
Na fiddo ido na ce, “Binciken me nayi maka?”
Murmushi yayi (again), “Za ki rantse da Allah baki shiga dakina ba?”
“Na shiga mana, amma ban bincika komai ba wallahi, gyarawa kawai nayi”.
Ya miko min hannun shi na dama na alamar karbar abu.
“Bani DIARY dina!’.
Na kai tafukana na rufe fuskata cikin matsananciyar kunya.
“Koda na gani, ba lallai ne ya zamo na karanta ba. Kuma ma ai duk rabi Larabci ne ba iyawa nayi ba”.
Ya girgiza kai, “Fa’eezah! Kin dauka ban san cewa tun kina ‘yar ficikar ki kike yara Larabci ba? Kin zaci ban san cewa (B.A Arabic) kike karantawa a BUK ba???”
Baki na saki galala! Ina kallonsa.
“Rufe bakin kada kuda ya fada”.
Dariya nayi na juya masa keya.
“Duk wani motsi na rayuwarki nasan dashi, haka duk wani abu da kike aiwatarwa a kan wadannan fitinannun idanun ne, ko ba haka kuke cewa ba keda ‘yan uwanki Ummi da Zaneerah?”
“To mai yasa kake sa min idon? Ko kasan sa min idon da kake yana daga cikin abubuwan da suka sa na ki jininka a lokacin? Ina ganin kana sa min ido ne domin ka kuntaci rayuwata”.
“Kina so ki ji dalili?”
“Eh”.
“To amsa min tambayata, ta shin kin karanta min DIARY bada izinina ba ko?”
“Eh, na karanta, shi kenan? Amma wallahi ba bincike nayi don na samo shi ba, tuntube nayi dashi a dokin kofa”.
Murmushi yayi, “…Fa’izah matar Fa’iz! Insha Allahu jirgi ba zai zamo ajalina ba sai SON FA’IZAH!”.
Na dago cikin (slow) na dube shi, kwayan idanunmu suka hadu, suka sarke da juna. Babu komai cikin kwayar idanunshi sai ‘gesture’ wato motsi mai nuna zahirin abinda ke zuciya.
Tsigar jikina ya tashi yarrr! Jikina yayi bala’in sanyi, ban san yaushe kalaman ke fitowa a hankali daga baki na ba.
“Balle ma in Allah Ya yarda tare zamu mutu, tare za’a binnemu, kuma ba ta hadarin jirgi ba. Tukin-jirgi, hanyar abincin mu kenan ba hanyar ajalinmu ba, yanzu muka fara tukashi muna saukewa daga kuruciya har tsufa, ranar da ba zamu iya ba ‘ya’yanmu su karba, haka har jikoki”.
Ni kadai nasan abinda naji… da na tsammaci mutuwarka! Da ka mutu a wannan lokacin Yaya Fa’iz I’ll no longer be in existence. Na tabbata in ‘so’ bai kasheni ba kewa da ‘kauna’ za su kasheni…’
Wata irin runguma Fa’eez yayi min da saida kasusuwana suka amsa. Hawayen dake makale tun dazu suka balle mini suka shiga shan sharafinsu a kundukukina zuwa gadon bayan sa.
Ya kai hannu ya shafo hawayen, “Daina zubar dasu haka nan Fa’izah. Na tabbata ba ni ne baki so ba HALINA NE. Wanda a zahiri ba halina bane KISHI NE. Ba ke nake sanyawa ido ba, SOYAYYAR DA KIKE YIWA YAYA ALIYU NE!
Ina kishin Aliyu Fa’izah, yadda bakya zato, har gobe ba zan daina ba. Domin wani mutum ne shi da kika so da zuciya daya saboda HALINSA! Na yarda na amince halin mutum jarinsa ne daga yau nima na zama dan kirki, dama ke kadai nakewa rashin kirkin, kema kuma don kina son ALI NA’IBI ne! Tunda kin maido son gareni na miki alkawarin zama mai kirki fiye da Yayanki ALIYU HAIDAR NA’IB A.B GIWA!”
Na dago kaina ido sharkaf da hawaye.
“Ko baka canza ba INA SON KA HAKA!
I go along with the people I love da halinsu…”.
Dariya yayi, “Da can dinma bakya ki na, bacin ranki kike expressing’ na bakanta miki da nayi. Da kina ki na da kinbi shawarar dana baki a RIVER NIGER”.
Na dunkule hannu na bugi kirjinshi da shi.
“Kai ne baka iya kishin ba ai, kishi na mugunta?”
Na sake bugunshi, “Ba’a nuna KISHI da KIYAYYAH… Ga wanda aka yimawa KIYAYYAH NE. Ka daina kishi da Yaya Aliyu don Allah, dan uwanka ne, kuma surukinka.
Na so yaya Aliyu, kasancewar shi wani mutum da ya wahalta mini, da gangar jikinsa, da zuciyarsa, da aljihunsa da lokacin shi a kaina. Ya shiga kunci a lokacin da ya rasa ni. Kai da ka samu bai yi kishinka ba ya bada kyakkyawar gudunmawa wurin ganin na hakura na rungumi aurenka Yaya Fa’iz.
Aliyu ne ya sani yin zuciyar da na tsaya nayi karatu na shiga sahun dalibai nagartattu a lokacin da nake cikin shagaltattu. Don me ba zan so shi ba a wancan lokacin tunda an halicci zuciya ne da soyayyar mai kyautata mata? Ina son shi ne a lokacin, amma wani irin so irin wanda nake yiwa BABA NA ban taba kimsawa zuciyata sha’awar tarayya a tare dashi ba sai so na ‘KAUNA’ da mutuntawa hadi da ganin kimar juna.
Amma wannan son da nake ji a yanzu akan Hafizin Hajjah? Wani iri ne da harshe ba zai iya bayyanawa ba, kwakwalwa ba zata iya fassarawa ba, da ya gagari fahimtar mutum sai dai zuciya ta jishi amma ba zata iya bayyanawa ba.
Haka nan zuciya da kwakwalwa basa iya daukar shi ba tare da sun nuna gazawa ba saboda GIRMANSA! Daban yake dana YAYA ALIYU kazalika NAZIR SANI GALADANCI. A kansu duka, banji irin wannan lullubabben son da nake yiwa FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA BA!!!”.
“Barni haka… kada ki kasheni da raina”.
“Ya fadi ne a galabaice, cikin tsananta rungumar da yayi min.
“Allah Ya bani tsawon ran da zan ninka farantawar da Aliyu yayi miki, Allah Ya bani tsawon ran da zan nuna miki bakiyi asarar Yaya Aliyu ba! Nayi alkawari Fa’izah zan nuna miki so da kulawa fiye dana Yaya Aliyu. Ko da can din ban samu dama bane, babu kuma hanyar da zan samu damar. Sai dai kisa a ranki, na rantse ALIYU BAI FINI SONKI BA… DAMA YA FINI SAMU!”
Ni kadai nasan halin rudun da na shiga a lokacin da kike neman hallaka kanki don kiyayyata, sai ko abokina Maajid. Kada ki kara sawa a ranki wai bana son ki. Kisa a ranki Fa’eez naki ne KE KADAI”.
Shudewar mintuna masu tsayi cikin wasu al’amura masu tsayawa a rai, da zuciyar wanda ake mawa. Na nemi ji na da ganina na wucin gadi na rasa.
Fa’eez ya daukeni ya kai wata duniya ta daban irin ta Adamu da Hauwa’u da ma’aurata kadai ke zuwa kwatankwacinta. Ya manta da yunwar cikinsa na manta da tawa, da kyar muka rarrafa zuwa cikin gidanmu muka dangana ga dakin baccinmu.
A can komai ya kwance, al’amuran suka sauya taku, baga Fa’iz ba, ba ga Fa’izar ba, kowanne so yake ya nunawa dan uwansa ya fishi so da kaunar kansa. Ina rokon Allah Ya tsawaita rayuwarmu, Ya kara soyayyar junanmu cikin zukatanmu, ya bamu ‘ya’ya masu albarka da biyayya ga iyaye.
Bana burin in haifi da mai irin halina na kafiya, riko da taurin zuciya. Addu’a nake, Allah Ya bani Da ko ‘YA mai hali irin na Ubansa/ubanta, mai yakanah irin ta Ubana da Baban Kaduna, mai son zumunci da kyautatashi irin HAJJAH. Mai tsaftattar zuciya irin ta MOMI na ma’abociyar rungumar kaddarorin UBANGIJI.
(Ku ce Ameen, makarantan TAKORI).
* * *
Kwanaki bakwai da suka biyo baya, babu abinda ke wanzuwa a gidan sai amarci zallah, na a buga a jarida. Babu inda Fa’iz ke zuwa daga gida sai masallacin wani gida makwabtanmu, sai gidansu a Jabi Road shima duk dadewarsa baya wuce rabin awa.
Ranar da ya cika kwana goma sha hudu ya ce in shirya zamu je zaga dangi daga nan mu wuce Giwa wajen Hajjah, sun dawo daga Jeddah ita da Baba Na’ibi da Aunty Zainab inda aka kaita asibiti tsayin sati biyu.
‘Yan uwa dake kewayen Kaduna muka fara zagewa, su Aunty Hauwa Maman Ummi, sai Jabi Road. Mama dai hadiyeni ne kawai bata yi kullum sai zuba mana albarka, haka Baban Kaduna albarka suke saka mana babu kakkautawa a duk lokacin da kafafun mu suka taka gidajensu. Da kara jan hankalinmu kan riko da ZUMUNCI. Su kan ce. “Ko babu aure mu ‘yan uwan juna ne, don haka hakuri da junanmu ya zama dole don cigaba da (maintaining) burin Abubakar Bamalli, ya cigaba da ganin abinsa can inda yake, suna rokonmu ko bayan ransu…kada mu warware wadannan igiyoyi da suke kukkullawa a tsakaninmu kan kannenmu da ‘ya’yayenmu, jikoki da tattaba-kunne.
Mun dauko hanyar Zaria bayan mun baro Kaduna, bayan motarmu shake da tsarabar su Walida (trolly) guda da Fa’iz yayo musu. Amma cikin rashin sa’a bamu same su a gidan ba. Walida tana makarantar WTC Soba tana shirin zana jarrabawar fita (SSCE) yayin da Abdallah ke makarantar horas da sojoji a Jaji (National Defence Academy). Kausar na S.S I a Sarauniya Amina, inda Walid autan Momi ya shiga shekararsa ta farko a karamar sakandire.
Babana Prof. Ahmadu A.B da Momina Maimunatu A.B, sun rasa ina suka-saka-ina-suka aje damu don farin ciki. A fili Baba ya daga hannu yana yiwa Allah godiya a cewarsa da Ya nuna masa wannan rana, wadda Hajjah har kullum ke ce da su tana zuwa! Yayi addu’a Allah Ya karawa Hajjah lafiya da tsawon kwana., Ya jikan ABUBAKAR BAMALLI. Gaba daya muka shafa da amsawa da
“Ameen”.
Fa’eez ya tafi cikin city ya barni, ya ce zai je yaga Surajo ya dawo.
Bayan fitarsa ne Baba ya dubeni yana murmushi yake fadin.
“Yo ko ke fa Fa’izata?”
Na dago kai na dube shi nina murmushin nake yi. Rabon da inga yana walwala irin haka tun muna kanana sanda yake kaimu (Nursery) ‘staff school’. Yana tuki yana mana tatsuniya har muje makaranta.
Idan ya debo mu akan hanya zai tsaya ne ya sai mana dafaffen kwai da gishiri ni da Walida da Abdallah. Kullum ne ranar Allah sai ya sai mana dafaffen kwai da zuma wai suna kara kwanyar karatu.
Idona ya ciko da kwallah da na tuno wahalar da na bashi ‘in return’
“Na ce ko kefa? Dubi yadda kika yi kyau, kika ciko, da kika kwantar da hankalin ki. Amma watannin baya baki ga irin takaicin da kike sanya ni ba. Kullum idan na daga ido na dubeki a gidan nan wai na kasa lankwasa ki, wani abu ne ke tokareni a kahon zuci. Kullum tunanina wai ‘yar da na haifa tafi karfina, tafi karfin UWATA da yayye na, a duk sanda nayi tunanin haka, na duba na hanga naga cewa babu wanda keda irin wannan dan cikin A.B … sai inyi dakacen dama ba ni na haife ki ba!!!’.
Da rarrafe na isa ga Babana, kuka sosai nake har da majina.
“Ka yafe min Babana, ka dubi Allah kayi min afuwa, kuskure ne da aikin shaidan ina rokon Allah Ya kara nisantani da shi.
Duk abinda nayi nayi ne a bisa kuskure da rashin fahimta. Na roki afuwar yaya Fa’iz tuni ya yafe mini… Ina rokon ku kuma ku dubi Allah da nadamata ku yafe mini ko na cigaba da ganin haske a rayuwata… Ku taya ni rokon Hajjaty ta yafe mini…”.
Baba yasa hannu ya dago ni, “Tuni na yafe miki Fa’izah, ina gaya miki halin da na shiga a baya ne ba don ban yafe miki ba. Allah Yayi muku albarka, Ya kyautata gabanku da bayanku, Ya baku zuri’a masu albarka!!!”.
Ya sanya hannu ya janyo ‘brief-case’ dinshi ya fiddo wasu takardu, ya duba sannan ya miko mini.
“(Share) ne na banki na saya muku dukkanin ku, ke kuma na hada da bude miki ‘account’ da bankin JA’IZ don saukakawa mijinki wasu daga cikin lalurorinki. Na kuma bude shi ne da niyyar duk wata idan na dau albashi zan sanya miki wani abu a ciki, haka kason ku na wata-wata da ake baiwa duk wani da na A.B shi kuma na bude mishi ‘account’ daban da Bankin ‘Fidelity’ ga (details) dinnan ki adana a wurinki ko ki bawa mijinki ya adana miki”.
Hannu biyu nasa na karba ina godiya. Na kare da cewa.
“Baba Allah Ya bar min kai!”.
Murmushi yayi, “Nima Allah Ya bar min ke”.
Momin tayi dariya tana jinmu bata ce komai ba, dana juya gareta sai naga ta sunkuyar da kai hawaye na diga daga idanunta.
Wato wannan din wata irin soyayya ce ta da da mahaifi da ita bata samu ba!
Kaico da iyayen dake haifar ‘ya’yan su zubda su ko masu sacewa su raba su da iyayensu, saboda cimma wata manufa ta duniya. Ya Allah ka barmu da iyayenmu har karshen rayuwarmu, Ka kara musu lafiya da tsawon kwana, Ka basu ikon kula da hakkokinmu, muma Ka bamu iko da zuciyar yi musu BIYAYYAH don gamawa da duniya lafiya (Ameenm summa Ameen).
Dai-dai lokacin da Fa’eez yayi sallama shi da Surajo, Surajo ya gaida Baba da Momi ya koma tsokanata.
“Yau sati biyu kacal cikin takaba amma aka rangada kwalliya?”
Na galla masa harara Baba kuwa dariya yayi suka shiga hira na abinda ya shafi aikin Surajon (Banking), tashin zabuwar ‘Doller’ da ‘sterling pounds’ abin babu dadin ji. Sun dade suna hirar, tare da yiwa kasar mu addu’a. Muka yi sallama dasu muka dauko hanyar Giwa, shi kuma Surajo suka yi hannu ya shige motarsa ya koma cikin city inda gidan iyayensa yake. Har zuwa yanzun bai yi auren fari ba, na dai ji jiya Fa’iz na fadin ya kai kudin aure.
Muna tafe akan hanyar Giwa, sanyin na’urar sanyaya mota na ratsa kasusuwa zuwa bargon mu, sautin Abdurrahman Sudaith na tashi cikin Suratul Tagabun, Nake gayawa Fa’iz.
“Ko kasan rabon da kalami mai dadi ya hadani da Momi da Baba irin na yau, tun ranar da tsinkayi labarin daurin aurenmu? Na rasa wane irin so kafatanin A.B ke maka, kana da wata ilhama ta musamman da duk cikin zuri’armu babu mai ita. ‘I salute!”
Na kai hannu na gefen goshi na daga. Gaisuwar girmamawa irinta bature.
Dariya na bashi sosai yayi harda bugun sitiyari.
“The salute best suits you! Yarinyar da ta gasawa kafatanin A.B gyada a hannu. Ta nuna musu JIYA BA YAU BA… GABA DA GABANTA WAI ALJANI YA TAKA WUTA… I salute too!!!”.
Ya daga hannu a goshi, ya kankantar da ido cikin kallona.
Murmushi nayi cikin jin kaina yayi girma kamar fanteka. Na mika hannu na rike nasa, ya ce.
“Kinga matsa, kar kisa in watsar damu tun ban ajiye mai ce min BABA ba”.
Dariya ta kamani sosai saboda yadda yayi maganar cikin zare ido da barazana launin idonsa na canzawa.
“To Baba Abubakar, direban zuciyata, the pilot that drives me crazy…”.
Kuuu!!! Ya ja wani irin birki a tsakiyar titi, saura kadan ya yiwa wani mai babur diban albarka, motar tayi gaba tayi baya kamar zata hantsila. Kafin ayi haka kankame nake dashi ina shahada, idan mutuwarce ta zo ta daukemu tare ko yanzu ne na shirya mata.
A hankali ya gangara muka sauka a gefen titi.
Rikon da yayi min mai tsauri ne da saida kasusuwana suka amsa. Idan al’amuranshi suka birkita bana iya doje su a ko’ina ne. Ko nayi kokarin hakan bana cin nasara. Al’amuran soyayyarsa unimaginable, unabandonable’ ne a gareni, and also, irresistible.
“Yaa Allah ka barni da Fa’iz, ka makantar da duk ‘yan matan duniya daga kan mijina Fa’izu Abubakar, ka munanta shi a idanunsu ya zamo ni kadai nake ganin kyansa.
“You are my life Yaya Fa’iz… I’ll always keep on loving you…”
“To say I love you Fa’izah, is not a way to express the feelings. …..!!!”.
Muryarshi har bata fita, kuma kalaman, yana fadinsu ne tun daga karkashin zuciyarsa.
Bamu isa Giwa ba, sai karfe shidda na yamma.
***
MURFI
Hajjah na kwance tsakiyar falonta, ‘yan kananan jikokinta zagaye da ita lokacin da muka shiga tana ta faman bari-barinta data saba daga kwance. Hannuna cikin na Fa’iz muka yi mata sallama a falon.
Allah Sarki Hajjah! Mikewa tayi zaune daga kishingiden da take akan tuntu tana kyafta ‘yan makyabtanta amma bata iya ta gane ko su waye ba.
Hakika tsufa ya zo, amma mai tafe tare da nutsuwa wadda riko da addini ke haifarwa a shekarun tsufa, hakoranta duka rabi sun zube, gilashin take lalube don ya kara ma ganinta karfi ta gane mu. Kasancewar bayan sallama da mukayi kasa-kasa, daga ni har Fa’izun babu wanda ya sake magana balle ta shaida muryarmu.
A tare muka isa ni da Fa’iz zuwa ga akwatin gilashin nata wanda yayi gefe guda, hannuna ne ya riga na Fa’iz sauka akan akwatun gilashin. Don haka ni na dauka na sanya mata.
Kallon-kallo ake tsakanin Hajjah Hadiza Giwa, da jikokinta Fa’izah da Fa’izu. A nasu fatar bakin, murmushi ne. A nata kuma cewa tayi cikin raunin murya.
“Abin tamkar a mafarki, ranar dana dade ina jira. Ranar da Fa’izu zai zo min tare da Fa’izah a matsayin matarsa, suna masu farin ciki da juna… suna annuri a fuska da zuci…”.
Na zame hannuna daga na Fa’iz na runtuma na rungume Hajjaty….
“Yau ga ranar Hajjah… Ki yafe min Hajjah kuskure ne, ajizanci ne irin na dan Adam!”
Ta rungume ni sosai a jikinta tana dariya ina kuka.
“Daina kuka Fa’izan Hajjah, ni ai nasan wannan ranar na nan zuwa, ni ai nasan dama shirmenki kike da tarin kuruciya ke haifarwa.
Fa’izu nawa! Mijina na kaina, Abubakar Saddiku… akwai gaular data isa tace bata son sa? Ai sai dai ta fada don kawai taji dadin bakinta”.
Murmushi Fa’iz yayi, ya zauna a gefen ta yana kada ‘yan mukullayen shi.
“Hajjah tawa! Hajjaty!”.
Duk sai suka bani dariya, su basu yadda ba mata da mijin ne.
Ina dariya mai cakude da hawaye na ce, “Tsinkayenki dai dai ne. Hasashenki bai zama a banza ba. Ki yafe min Hajjah kuskure ne wanda babu dan Adam din da ya isa ya kauce masa. Na yarda na amince ko iyayenda suka haifeni basu fiki so na ba, sai dai su ce su suka haifeni. Ina kira ga ‘yan mmatan zamani su nutsu, su dawo cikin hayyacin su daga tasirin ilmin zamani, wajen akida da al’ada. Su daina kallon zurfin iliminsu da wayewarsu wani mataki na fin karfin iyayensu, sanin ciwon kansu ko abinda yake dai-dai ga rayuwarsu. Muna jarabtuwa da son abu alhalin shi din ba alkhairi bane a garemu, haka mu kan ki abu karshen ki a yayinda shi ne alherinmu. Mafi a’ala shi ne mu baiwa Allah ZABI a dukkan lamuranmu musamman ‘AURE’ mu daina bin soye-soyen zuciya da baiwa soyayya muhimmanci idan aka zo magana ta aure. Mu yiwa iyayenmu biyayya shine mafita.
Soyayya ta kwarai a hankali ake samunta ba farat daya take samuwa ba. Ba ina nufin babu ‘Love at first sight’ ba, ‘a’ah, ‘it is normally not a geniune one’. Kuma bata da karko.
Na gaba har gobe na gaba ne, haka iyaye har gobe iyaye ne koda a kungurmin daji suke zaune karewar rashin wayewar kai.
Ina rokon Allah Ya barni da ku Hajjaty! Ya kara muku lafiya da tsawon rai. Ya bani ikon yi muku biyayyah koda ta wuta kuka hura ganga-ganga kuka ce in shiga anan gaba. Hajjah Allah Ya bar mana ke!!!”.
Murmushi tayi, wanda ya fadada zuwa dariya, ya fiddo wawulon da ya kara fadi a bakinta a dalilin faduwar hakora uku a bayan rabuwa ta da ita. Amma bata ce komai ba.