ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

 ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 


                Www.bankinhausanovels.com.ng 

 Cikin kuka ya rungume dan uwansa ya ce. “Yaya Jafar ba mutuwa tayi ba, amma a yanzu zan so ace: Aziza ta rasu domin ta samu nutsuwa akan wadannan masifu da suke ta_ faruwa da ita, daga wannan sai wannan. Wai_ likita ne yanzu yake fada min wai tana dauke da juna biyu na tsawon wata uku”,. Mutuwar tsaye Alh. Jafar ya yi, nan da nan ya shiga cewa.”Ya Hayyu ya Kayyumu!”. _
Abinda ya yi ta maimaitawa kenan a bakin sa.
Haamwed da yake gefe dora hannu biyu yayi akai yana salati hade da kuka, haka itama Haj. Asiya. – .
Ya koma gefe yana ta buga hannunsa a jikin garu, Mukhtar ya yi sauri ya riKe shi ya ce. .
“Hameed baka da hankali? So kake ka ji: ma kanka rauni ne?”
“Uncle.ka barni, bani da wani amfani a rayuwata tunda har…”. . Hameed ba zaka yi shiru da bakinka ba sai kana mana surutan banza!”
Alh. Jafar ya katse shi cikin hanzari, da sauri ya zo ya riKe masa hannu ya ce.
“Hameed, idan ba zaka tsaya ka kwnatar da hankalin ka ba zan hana ka zuwa nan gurin, baka ganin mu ma kullum hakuri muke yi? Yadda kake jin abin nan mu ma haka muke ji”.

Abba ya Karaso gurin shima ya ce, “Hameed mu dauki Kaddara, haka Allah Ya rubutawa ‘yar uwarka tun fil’azal, babu wanda ya isa ya goge ko ya hana faruwar hakan”, Kuka sosai Hamced ya saka ya sulale Kada yana kukan ba don komai ba sai don tausayin Abba, yadda ya gama yarda da shi amma ace shi’ ne, yayi sanadin jefa rayuwar ‘yarsa cikin wannan halin. Tabbas yasan ba zai taba gafarta masa ba har zuwa Karashen rayuwar

Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan sun dan nutsa sai Uncle Mukhtar yace.
“Yaya Mustapha to me yasa tun farkon zuwan mu nan basu yi mata wankin ciki ba? Ai
da tuni an zubar da shi. To yanzu meye abin yi don ba zamu barta da cikin wani ba wanda bamu san asalinsa va
Alh. Jafar da Asiya hade da dansu suka hada idanun su guri guda cikin rudani. Cikin alhini Mustapha ya ce, “Mukhtar nima nayi musu wannan tambayar, sun ce min _ duk abin da nake tunani sai da suka yi a farko, suka ce idan an kawo yara da hakan ta faru da su shi ne abin da suke farayi. Mu aynzu babu abinda za muce sai yadda Allah Ya yi da ita”. “Yaya mu fitar da cikin nan daga jikin ta, shi ne kwanciyar hankalin mu”.
“”Mukhtar meye ribar mu na yin haka? Idan mun kashe rai me za muje mu ce da Allah tunda Shi ne Ya aiko hakan ta faru to da sanin Sa, sai mu tsaya mu ga yadda Zai canza mana. Amma ni dai da hankalina ba zan ce a cire cikin nan ba, idan kuma an samu akasi an rasa ranta da abin da yake cikin ta ka ga mun yi laifi biyu, __ dole haka zamu hakura mu karbi Kaddara.
Idan kana jin tsoron surutun jama’a to kowa yasan ba rashin tarbiyya bane ya kaita taje tayi cikin, cikin Karfi aka hakke mata. Haka idan kana tunanin cikin ZURI’A kake tunanin ayi mana gori, to duk ZURI’A DAYA muke, duk wanda yake cikinta. abin nan ya shafe shi. Don haka mu dai mu yi fatan Allah Ya raba ta da shi lafiya, su kuma wanda suka aikata ko ya aikata gashi nan ga duniyar, Allah Yana gani, Ya fimu sanin me Ya tanadar masa, ko iya hakKin mu ma ya ishe shi kafin aje gare ta”, Www.bankinhausanovels.com.ng
Gabe daya duk wanda yake gurin babu wanda jikinsa bai yi sanyi ba, domin kalaman sa sun taba zuciyar kowa a gurin. Gumi ne ya keto a jikin Alh. Jafar, domin bashi da wata kalma da zai iya fada sai cewa yake. “Allah Ya kyauta”. Haj. Asiya kuwa ban da kuka babu abin da take yi, haka tayi sallama da mu ta ce ba zata iya sayawa a gurin nan ba, da tasan haka zata zo taji wannan bakin labarin da bata zo ba. . —
Babu wanda ya iya cewa da ita komai, haka ta fice tana kuka, kowa da abin da yake ji cikin ransa. .
Hameed ne ya mike daga inda yake ya
nufo kan gadon da take kwance hawaye na zuba
a fuskar sa, ya zo kanta ya tsaya ya sa hannu ya
Dafa kanta, baccinta take abinta; nan ya shiga
kuka mai tsuma rai domin ya kasa ya furta komai
banda kuka. Na Karaso gurin na dafa kafadar sa, na ce. “Abdul babu abin da zamu yiwa Aziza sai addu’ar Allah Ya raba ta lafiya da abin da yake yikinta, tawakkali shi ne abin yi a gare mu ba
kuka ba tun da abin haka yake tun ran gini tun ran zane”. Daga kai ya yi bai iya cewa komai ba banda tsabar malala da hawaye suke a fuskar sa.
Aisha na gefe tayi jigum bata iya wani kwakKwaran motsi tsabar kaduwa da jin abin da ya faru da diyar ta, sam ta kasa yin kukan sai na zuci da take yi .
Hameed na mikewa zai fita sai Aziza ta farka daga baccin da take yi, tana farkawa sunan Abba ta fara kira. Da sauri ya Karasa gurinta yana tambayar ta me take so? ko me yake mata ciwo? Jin muryar Aziza yasa Hameed ya Kame a tsaye, wato ya yi mutuwar tsaye. Nan take zuciyar sa ta shiga bugawa akai-akai, domin tsoro ne ya gama kama shi. .
“Abba kai na, kaina zai cire, zafi yake min, wayyo ciwo abba, don Allah nike min kaina zai fashe”. Abin da take fadi kenan. Da sauri Abban ya-rikce mata kan kamar yadda ta nema, ya shiga tofa mata addu’a, nan da nan ta soma lumshe ido alamun ta fara jin yana lafa mata. Daga masa hannu tayi alamun ya fara saki, ya ce, “Ya daina miki ciwon ko?” . “Eh”.Ta fada. -da Haka ta dinga bin kowa da kallo daya Www.bankinhausanovels.com.ng bayan daya, ta ga duk kansu cikin tashin hankali, ta so tayi magana sai ta fasa. . Can ta hangi Hameed ya ba da baya ya tsaya Kyam, sai hankalinta ya yi wajen sa, ta ce. “Abba wancan wanene ya tsaya haka?” Nan da nan ya KirKiro murmushi ya ce, “Yayanki ne, yana ta zuwa baya ganin ki kina ta bacci lokacin. Hameed, zo ga Kanwar ka tana _ tambayar ka, yau da rabon za ku gaisa”.Ji yayi kamar an dauki. guduma an doka masa a tsakiyar kansa, nan take yaji Kafar sa tana KoKarin kasa daukar ganganr jikinsa, ya ji juyawar ma tana gagarar sa. “Hameed!”Ta fada hade da runtse idanunta na dan wasu lokaci. Damm! Yaji hantar sa tayi rawa, ya yi kamar ya furtsa da gudu. Sunan ta ci gaba da maimaitawa, ko yana jinta. Jin yawan ambaton sunansa ya Kara tsinkewa, gabansa ya ci gaba da dakan uku-uku, haka ma Alh. Jafar shima rudewa yayi dole kasa. komai yayi yana jiran ya ga me ya yi saura? Sai dai cikin ransa yana ta kiran sunan Allah.
Runtse idanu Hameed ya yi kawai ya saddakar, ya juyo ya nufo gurin lokacin ita kuma hankalinta ya fisga zuwa wani guri. –
Yana zuwa kusa da gadon ta juyo, tana ganinsa ta ji Wani irin mugun firgita ta sosai,.nan da nan ta shiga saukar numfashi akai-akai, ta saki baki hade da tsananin tsoro da ya mamaye fuskar ta. Wata muguwar Kara da kururuwa ta sa, nan da nan ta rungume Abbanta tana KanKame shi jikinta na rawa, nan take hankalin kowa ya tashi.
Nan take Alh. Jafar ya dakawa Hameed tsawa akan ya zo ya fice daga dakin tun da bata son ganin shi.
Mustapha ya ce, “Haba Yaya, meye na daukar zafi haka? Ammi na ba wani bane fa’ _ yayanki Hameed ne, bude idanunki ki ganshi”,
Girgiza kai tayi ta Kara rungume shi tana kuka, jikin kowa yayi sanyi, nan kowa ya shiga zancen zuciya yana mamakin wannan al’amarin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hameed ne ya yi Karfin hali ya zo da sauri ya kama hannunta ya dago ta yana kuka yana cewa.
“Aziza na kalle ni sosai ki gani, ni ne yaya Hameed dinki ba wani bane, ki cire idonki kikalle ni sosai don ki shaida ni”. Yanayin kukan da yake da irin nacin da
yake akan Aziza ta dago ta kalle.shi ta Ki, hakan sai yasa kowa yajitausayin sa.  Da Kyar ya samu:‘ta dago ta kalle shi, amma cikin rudani, tana kallon sa tana ajje numfashi da sauri irin narazana. Da sauri ta fisge hannunta daga nashi ta koma jikin babanta tanacewa. -Abba bana son shi, bana son shi, Abba
(please) ya.tashi bana son shi”, Tana fada idanunta a rufe. Nan ta shiga kurma ihu dole Alh. Jafar yasa sai da ya fice sannan aka samu tayi shiru.
Ana cikin haka sai ga (Nurses) guda biyu sun shigo dakin cikin sauri don suga me yake
‘faruwa, nan daya ta tsaya tayi ta koma taje ta
kira likita. . Nan da nan sai gasu su biyu, nan suka zo suka ganta a dimauce, suka nemi a basu guri su duba ta, haka suka fito jiki a sanyaye muna ta jimamin me hakan yake nufi?
Sun dan dauki lokaci zuwa can suka fito, Mustapha kawai suka nema akan yaje suna son ganinsa, har Alh. Jafar zai bisu suka ce ya yi haKuni shi kadai suke buKatar gani. Bai yi musu
ba ya barsu suka tafi tare abin su, haka suka shiga (offuce) abinsu. Hankalin Alh. Jafar ya yi mugun tashi, domin bai san me za su fada masa ba, amma ~ haka ya yi KoKarin danne tashin hankalin sa don kada a gane yana cikin rudani a zargi wani abin.  Guri suka bawa Mustapha ya zauna, nan daya daga cikin su ya ce. “Alh. Mustapha don Allah muna son yi maka wasu tambayoyi duk da kuwa ba aikin mu bane yin bincike”.
Ina jinka Doctor, wani abu ku ke son sani gare ni?” .
akan malsalar yarinyar gurinka ne, domin yadda binciken da gwajin da muka yi ya nuna mana tunanin ta yana son dawowa a kowane irin lokaci, domin a yanzu wani abu ta gani da ya razana ta yake son tuno mata abin da ya faru da ita”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskar sa, ya ce”Kai Allah na gode Maka”.
“A cikin ku wani bakon fuskar da ta gani ya ta da mata da hankali wanda ganinsa ne yasa wurin ma’adanar tunaninta ya dan soma motsawa, sannan meye dangantakar sa da ita?”  Shiru Mustapha ya yi yana musu wani irin kallo na rashin fahimta, can ya ce. Wai me kuke magana akai ne?” “Alh. Mustapha ka kwantar da hankalin
‘ka, muna son gano wani abu ne, amma don Allah kayi hakuri”.. – “Yayanta ta gani ta razana”.Bakwa yin zargin cewa ko shi ne ya yi mata wannan aika-aikar? Domin ba Karamin razana tayi ba da ta ganshi wanda hakan yasa (memory) dinta ya kusa dawowa yadda yake”. Cikin zafin nama ya daki tebirin gaban Dr. Sa’id yana mai huci, yace Kaga Doctor ka tsaya iya aikin ka, wannan ai cin fuska kake son yi min, kasan yadda muke da uban yaron nan kuwa? Ubanmu daya da shi, ZURI’A DAYA muke, me zai kai
Shi ya yi mana wannan illar? Sam kada na Kara. jin wannan furucin a bakin ka gudun kada ka zo ka jefa zumuncin mu cikin matsala”;
“(Relax) Ranka ya dade, duk abin bai kai, ga daga hankali haka ba”. Dr. Umar ya ce.
“Haba Doctor, maganar tashi ce bata yi – min dadi ba, me yasa zai sa zargi akan dan dan’uwana? Allah Ya kiyaye hakan ma ya faru a cikin mu”.”Ameen” Dr. Sa’id ya fada, kana ya ci gaba da cewa,
“Mu ma bama_-fatan hakan a gare ku, abin da aikin mu ya nuna mana shi ne yasa har muka yi maka wannan tambayar, amma don Allah kayi hakuri zamu yi abin da ya dace kaji, za muyi wani gwaji don mu sake dubawa ko dai Kwakwalwar ta ne ya dan motsa yasa hakan ya faru, Amma don Allah kayi haKuri don naga ka fusata sosai, ni kuma na fadi haka ne ba don wani abu ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Shi kenan Doctor naji, ya wuce, Allah Ya taimaka, da fatan zan iya tafiya ko?”
“Za ka iya tafiya, amma yanzu ba ma son kowa ya shiga gurinta domin muna son gwada wani abu a tare da ita na zahiri, don mu gane me hakan yake nufi? Don haka ku jira mu”.Babu laifi”.
Ya fada a lokacin da yake KoKarin tashi
‘ daga inda yake zaune, shi ya fara fita sannan suka tsaya suna dan tattaunawa.
Haka ya zo ya same mu tsaye bakin dakin yanayin sa duk ya sauya, Alh. Jafar ne ya yi saurin tare shi yana tambayar sa me suka ce :. shi?
Sakin fuska ya yi ya ce, “Cewa suka y suna son duba Kwakwalwar ta su gani, domin ihun da tayi ya yi yawa, don su gano ko wani abu ya faru daita”.
Sakin ajiyar zuciya yayi, yace “Mun gode
Allah, Allah dai Ya bata lafiya don girman ‘ Manzon mu”.Duk gurin aka ce, “Ameen”,
Muna tsaye a gurin sai ga likitocn nan sun ° dawo, wannan karon har da wasu samari su uku, babu wanda suka yiwa magana, suna zuwa suka tsaya sai suka tura wani daga cikin matasan nan guda uku cikin dakin da Aziza take. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana shiga bai fi minti uku ba sai muka – jiyo Aziza na ihu kamar yadda tayi lokacin da ta ga Hameed, jin haka sai suka sake tura mutum biyun nan, nan ma dai wani ihun ta shiga saki babu KakKautawa. ‘tana cewa.’ Ban son ganin ku, bana son ganin shi, Abba! Abba!!”. Cikin gaggawa likitocin suka bude Kofar sai ga matasannan sun fito, su kuma sai suka shiga ciki, wannan karon har damu domin cewa suka yi muma mu shiga. Sai da muka shiga Aziza na ganin mu ta fito daga inda take buya da sauri ta zo ta. rungume Abbanta tana ccwa. — “Abba me yasa ka bari suka shigo? Tsoron su nake ji, Abba don Allah kada ka tafi ka barni su Kara shigowa”,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *