YARIMA MUS’AB CHAPTER 4
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai la’asar suka tashi daga nan sukayi wanka da sallah suna kan wanke² su Yarima suka shigo niki² da kaya a hanunsu Hafsa ce tayi saurin dauraye hanunta taje ta amshi kayan dake hanun Yaya Sadiq tana cewa “sannun ku da zuwa Yaya”
Ya dago ido suka kalli juna tuni yaji wani abu na motsi cikin zuciarsa ita kuma da sauri tayi kasa da kanta ta shige falo da kayan ta koma wajen da suke aiki Mami kam tuni ta dauraye nata hanun tabi bayansu tana raba ido
Sadiq da ya gama fahimtar inda ta dosa yaki ko kallon ta Ammi itama da ta fahimce ta tace “Wuce kije ki tayata ku karisa tun dazu ita ke ta aiki banda shirme ba abinda kk iya”
“Kwadayayya” cewar Sadiq
Tana dan turo baki ta fita har Hafsa ta gama tana share wajen suka dawo dakin suka zauna Yarima ne ya jawo ledar ya mika mata “ke lallai Blacky akwai kwadayi in ba baki akayi ba babu zaman lfy”
Da sauri ta karba “eh dai naji” ta ciro roba daya ta mika ma Hafsa “Besty Ungo naki”
Ta amsa amman ta kasa sha don duk dago idanu sai taga Sadiq yana kallon ta nan ta kasa sakewa a wajen Ammi da ta lura sai ta shiga daki ta kira Sadiq ya zauna kusa da ita
“Ammi na ba dai laifi nayi ba koh?”
Tace “a’a naga dai ka tsare ‘yar mutane da ido ne ta kasa sakewa”
Ya dan sosa Kai cikin jin kunya “to Ammi ni yaushe na ke kallon mata balle wannan Karamar yarinyar”
Jan kunnensa tayi “zaka ma fadi gaskia ne”
Sai kusan biyar na yamma suka Kama hanyar Bauchi yayin da Yarima da Sadiq abota mai karfi ta shiga tsakanin su da alkawarin Sadiq zaixo Bauchi kwanan nan Mami har da kukan ta Hafsa ma ji tayi kamar kada tabar gidan don sosai take kaunar ahalin Bestyn nata
Suna isa gida suka fara shirya kayansu kuwa Ummi tasha lbrn Gombe sosai
Washe gari Sunday suka koma Schl suka bar Ummi cike da kewar su
Haka suka cigaba da rayuwa a Schl komi da Yarima sukeyi babu ruwansu yayinda Xee sam ta fita harkar su duk da cewa tanajin haushin yadda yake nan² dasu amman Saudat ta bata shawaran cewa ta gwada basa gabanta tunda har Daddy ya tabbatar mata Yarima Mijinta ne
Shakuwa ne ko kuma ince soyayya mai karfi ya shiga tsakanin Mami da Yarima ita kam Hafsa tana ankare da duk wani motsin su ita daman ba son shi take ba balle tayi kishi sedai ta amince da aurensa ne kawai don biyayya kuma tasan shima hakan take a wajensa
3rdterm yazo sauran students sun fara Exams su kuma SS3 aka basu hutun 2 weeks kafin su fara WAEC
Ranar da sukayi Hutu Sadiq ne yaxo tafiya da Mami suna tare da Yarima har Mami suka fito da kayansu kamar hadin baki Yarima ya nufi Mami ya karbi akwatin ta shima Sadiq ya nufi wajen Hafsa ita dai kanta na kasa don sam bata son kallonsa gabanta faduwa yake sosai in suka hada ido mika hanu yayi ya riko akwatin da hanzari ta sakar mishi ta matsa gefe yy murmushi dan y lura kamar tsoronsa take ya bude motar Yarima ya saka mata sukayi sallama tare da rugume juna ita da Mami suma mazan hakan sukayi kafin kowa ya shiga motarsa suka bar Schl din…
Yau satin su guda Mami tana kwance duk kewar Mus’ab ya dameta ynx kam ta gama tabbatar da cewa son shi ya gama mata babban kamu domin ‘yan kwanakin nan da bata ganinsa duk hankalin ta ya tashi Ammi tayi tmbyr duniyan nan tace babu komi da ta damu sai tace ciwon kai take a dole tasa tasha magani duk da lfyrta lau
Yau ma tana kwance abin ya damu Ammi ta kira Sadiq cewar yaxo y kaita asibiti ya shigo yana amsa waya sai dariya yake
“Prince zan kira ka anjima bari in Kai Baby asibiti”
Jin an ambaci Prince tayi zumbur ta tashi zaune shi kanshi Sadiq saida ya bita da kallo
Daga daya bangaren kuma Yarima hankali tashe yake tmbyr Sadiq me ya sameta coz yasan ita Sadiq ke kira Baby
STORY CONTINUES BELOW
“Wlh Bro tun dawowarta take fama da zazzabi kuma taki zuwa asibiti da an mata mgn sai kuka ynx dai dole zan kaita” Sadiq ya bashi amsa
Yarima dake zaune gefen Ummi har ya fara zufa don hnklinsa ya tashi yace “Bro tana ina please bata wayan”
“Okay gata” Sadiq ya mika mata wayar tare da ficewa don ya shirya
Kara wayar tayi a kunne tare da sakin wani marayan ajiyar zuciya
“Hello Baby me ya same ki?” Shi har ga Allah ma ya manta yana kusa da Ummi
Ta kasa magana kawai sai tasa masa kuka jin kukanta hankalin Yarima ya sake tashi mikewa yy ya fita daga dakin ya nufi nashi yana lallashin ta
“Haba Baby so kike hankali n ya tashi ne please ki fada min me ya same ki kukan nan yana daga min hankali”
Ta share hawayenta a hankali ta fara magana “ni bb abinda ya sameni fa kuma wai sai Yaya ya kaini anmin allura kace masa bana so ni na warke”
“To kiyi hkr an fasa kaiki amman kimin alkawarin bazaki sake kuka ba”
Tayi murmushi “to na daina ina Besty?”
“Taje gida kinason ganin ta ne?”
Ta ce “Eh ka Kai mata waya to gobe sai muyi magana”
“To ranki shi dade ni ynx ma zan kai mata amman sai kin fada min ni da ita wa kika fi son gani” Yarima ya fada cikin tsokana
“Dukan ku” ta fada Innocently
“A’a daya zaki zaba gaskia”
A hankali tace “Kai” sai kuma tayi saurin rufe fuskar ta kamar yana ganin ta
Murmushi mai sauti yayi cikin jin dadi yace “yaushe kike son gani na ko minti daya ban karawa ynx ki ganni dakin Ammi”
Tayi daria tasan wasa yake shiyasa tace “Yau”
“An gama Baby ki shirya tarba ta”
Nan suka cigaba da tadi sai daria take Sadiq da ya shigo su tafi yaga har ynx ba’a kashe wayan ba ya ce “Baby tashi mu tafi kar rana tayi”
Noke kafada tayi “ni barinje ba fa”
Da ya zare mata ido sai tasa kuka “Yarima ka ganshi wai sai ya kaini”
“Bashi wayar kinji”
Ta mika masa
“Hello Baaba ya”
Yarima yace “Haba mana kasan da ya nayi tabar kuka kuwa please ka kyaleta ai ta warke”
Hangame baki Sadiq yayi yana kallon Mami dake sauka daga kan gado har da dan tsallen ta ga kuma Yarima dake masa magiya cikin waya
“To shikenan ku kuka sani barin wuce Kasuwa”
Sukayi sallama ya fito Ammi dake fitowa daga kitchen tace “Wai me kuke jira ne kace sai kun dawo ku karya ina take Mamin”
Zama yayi a tabarman dake shimfide yana fadin “Ammi bani abinci kawai ni yunwa nake ji”
Taliya ta zubo mai ya fara ci zata sake tmby suka ga fitowar Mami daga bandaki daure da zani alamun wanka tayo bata ko shiga daki ba tazo ta saka hanu cikin taliyar suna ci tare
Ammi binsu tayi da kallo tana neman karin bayani Sadiq ya daga kafadu “Ammi tace ta warke”
“Karya take kawai bata son allura ne sai ka tafi ta narke min” Ammi ta fara fada
“To aide gata nan Yarima harda yimin warning kan cewar in barta” inji Sadiq da ya mike yana wanke hannu
Kallo Ammi ta bi Mami dashi baki bude itama tashi tayi ta wanke plate din ta wuce daki tana “Yaya Jirani mu tafi tare”
“Yau kuma kasuwan zaki bishi ko me?” Inji Ammi
“A’a ni Jeka da Fari zai kaini kuma chan zan kwana”
Ammi ta tabe baki “Allah gayas nima na huta”
Kaya ta saka ta dau karamar jaka da kayanta kala biyu ciki suka kama hanyar gidan kakannin su inda ya sauketa ya wuce sbd yana sauri yasan in ya shiga ba fitowan ynx ba
Da gudun ta ta shige ciki nan gida ya dauka ga Mami ga Mami da shike yau Saturday duk jikokin gidan suna nan sbd daman duka gidan suke Weekend har ita idan tana hutu
Kowa farin cikin ganinta yake don an dade ba’a hadu ba kuma kaf ahalin gidan suna matukar sonta yadda mahaifiyarta ta kasance mafi soyuwa cikin ‘ya’yan gidan musamman wajen Malam wato mahaifinsu
Da dare tana dakin Malam suna ta hirarsu taji Muryan yayanta a tsakar gidan suna gaisawa da matan yaran ma kowa yana ta gaidashi bata fito ba taji Sallamar shi a kofar dakin amsawa tayi ta tafi da gudu ta rugume shi yaja hancin ta
“Yaya na I missed u”
Ya harare ta “bb wani nan bayan kun hade min kai da Prince ynx ai Hafsa ce Baby na”
Daria tayi jin ya ambaci habibin ta jin motsi a bayansa yasa ta lekawa tamkar a mafarki ko kuma gizo ya fara mata domin Yarima ta gani tsaye yana mata murmushi
Hannu ta mika ta taba shi taga dai da gaske shine nan ta zaro idanu tana mamakin ganinsa
Malam ne yace “wai Hafsatu baza ki barsu su karaso bane?”
Matsawa tayi cike da farin ciki da murnan ganin hasken ranta
Gaban Malam suka durkusa suka gaidashi ya amsa yana zolayar su irin dai na kaka da jika
Banda kallon Yarima ba abinda Malam yake don tabbas ya taba ganin fuskar nan ko kuwa mai kama da ita in ko kamace to kamar ta baci sosai
Sadiq ne yake fada masa abokin shi ne yaxo daga Bauchi to da yake Sadiq a ATBU yayi karatu sai Malam bai wani tmby ya akayi suka hadu ba
Kusan karfe tara suka tashi zasu tafi Mami tace “Ya Mus’ab yau zaka tafi gida?”
Ya girgiza kai “a’a gidan Ammi zan kwana sai gobe”
Take tace itama binsu zatayi goben ta dawo babu wanda ya hanata sbd sun san rikicin ta
Suna kan hanya wayar Yarima tayi kara ya dauka “Hello Ummina”
“Na’am Yarima kana hanya ne?”
“A’a Ummi sai gobe zan dawo In Sha Allahu”
“To ka gaida su Ammin naku da mai sunan Kani na”
Sukayi sallama ya kashe wayar sai kallon Mami yake yadda alamunta suka nuna farin cikin ganinshi kiri kiri
Mami karamar yarinya ce bata wuce shekaru 16-17 ba so bata iya boye soyayya cikin rantaHira suke tayi a falon Ammi Sadiq kam har ya gaji da surutun su ya zuba musu ido damun sa tayi ya kira mata Hafsa dole ya kira wayar Abba Sadiq yace zaiyi mgn da ita Abba ya kira ya bata wayar jin ta amsa Yarima ya mika wa Mami+
“Hello Besty na”
Cike da farin ciki Hafsa ma ta amsa “Laa Besty daman kece Abba yace Ya Mus’ab”
“Ni ce amma wayarsa ce yaxo Gombe ne”
“Auu haba ya kike da Ammi na da My Dad?”
“Ammi lfy lau waye kuma Dad”
Hafsa tayi dariya “Yaya Sadiq mana ba sunan Abba na bane”
“Auu Yaya gashi nan zaune ko in bashi ne?”
Sadiq jin an ambace shi ya murmusa daman tun da aka kira ta ya kasa kunne yana jin Mami
“A’a rufa min asiri ke wlh kunyarsa nake ji” cewar Hafsa
Dariya Mami ta kwashe dashi “Yaya wai Besty kunyar ka take ji”
Kyat Hafsa ta kashe wayar tsabar kunyar abinda Mami ta mata
Mika wa Mus’ab tayi tana dariya
“Kedai magulmaciya ce wlh Baby” inji Sadiq
Tashi tayi tace “Sai da safen ku”
Suma mikewa sukayi suka tafi dakin Sadiq suka kwanta suna dan taba hira har bacci ya daukesu
Washe gari Mus’ab ya koma Bauchi cike da kewar Masoyiyarshi duk da cewa Sadiq promised dat kafin su koma schl da kwana biyu zai kawo Mami Bauchi shima ya masa 2 days din a nan
Mus’ab yaso ya fada ma Sadiq yana son Mami amman yayi tunanin ya fara sanar da Ummy tukun sbd baida matsala da Mami yasan itama tana sonsa amman yana tunanin yadda zai fuskanci Hafsa ya fada mata cewar yana son Kawarta yasan abin da kunya amman babu yadda zaiyi abinda zuciarsa keso ne
A gefe guda kuma Sadiq shima ynx y gama tabbatar da cewa ya fada soyayyar kanwar abokin nasa kuma a ko yaushe yayi yunkurin sanar dashi sai ya kasa sbd haka ya yanke shawarin tuntubar ita Hafsan da zaran yaje Bauchi bazaiyi kasa a guiwa ba
Mami ta koma gidan Kakansu ynx ma zaune suke suna hira Malam yace “ni kam Hafsatu wannan yaron da yaxo jiya Ina kika sanshi naga sai zumudi kike da yaxo?”
Ta murmusa an tabo inda yake mata kaikayi “Malam ai in fada maka Uncle dinmu ne a Schl kuma yayan kawata ne Hafsa da nake baka lbr kullum”
“To ya akayi ya zama abokin Sadiqu kuma?”
Ta ce “ai lokacin da ya kawo mu ne da muka sami Midterm Break shine suka hadu suka kulla abota”
Malam ya gyada kai “kenan a makarantar idan anyi hutu malamai ke kaiku gida?”
“A’a Malam munje gidansu ne da Hafsa shine sai ya kawoni inga Ammi kuma ranar muka koma”
Malam dai yana son sanin wani abu akan Mus’ab kuma tabbas ya lura jikarsa tana son yaron duk da cewa yana zargin wani abu musamman in yayi dubi da garin da Mus’ab ya fito yasan wani abu na shirin faruwa duk da bai tabbatar ba amman yana fatan hakan ko sbd ya sauke nauyin da ke kansa domin kullum kara tsufa yake kuma Mutuwa tana kusanto shi ko yau ko gobe so burinsa a ynx ya saita komi kafin ya mutu dan gudun kar yabar baya da kura
Mus’ab zaune suna hira da Ummy bayan sun gama cin abincin dare Hafsat na gefe itama ta dawo daga wajen mahaifinta don zamanta a fada yafi yawa kasancewar tun lkcn da mahaifiyarta ta rasu Abban ta bai sake aure ba
Gyara zama yayi don yasan dole ya fadi abinda ke ransa “Ummi nd Wifey ina son fada muku wani mgn nasan za kuji abin wani iri amma don Allah ku fahimceni wlh ba haka naso ba nima kawai sbd babu yada na iya ne” sai kuma yayi shiru yana kallonsu
STORY CONTINUES BELOW
Ummy tayi murmushi daman tasan wannan ranar tana zuwa “Muna jin ka Auta”
Ita kuwa Hafsa ido kawai ta zuba tana sauraren shi bata ce komi ba
Sadda kai kasa yayi “daman so nake in fada muku cewar Ina son Mami kuma so nake in auresu duka tare”
Murmushi Hafsa tayi tana jin wani farin ciki a ranta ko kadan babu kishi domin ita ba son Yarima take ba kawai zata auresa ne don cika burin iyayensu na son hada zumunta domin su kadai suka rage basu da kowa daga zuri’ar mahaifiyarsu amman ita ynx ta tabbatar zuciyarta ta kamu da soyayyar wanda bazata taba samu ba
A nata tunanin
Ummy ta gyara zama “daman na dade da lura da hakan Auta kuma ni banda matsala da Mami yarinyace mai tarbiya na kuma tabbata ta fito daga gidan mutunci amman ni ba maganata bace ina dai so ka tuna cewar yaran nan aminai ne kuma sannan ga ‘yar uwarka nan kuyi mgn da ita idan ta amince shikenan”
Tun kafin yayi magana ta yi Dariya “Ya Mus’ab indai nice wlh banda matsala nafi kowa farin ciki kuma ni ce da godia domin zaka hadani zama da Besty na”
Wani numfashi ya sauke yana t murmushin samun nasara tare da furta “Alhamdulillah”
Ummy ta numfasa “amman Auta kana yaro dakai har zaka iya rike mata uku kuwa?”
Bai wani damu ba shidai farin cikinsa sun amince ya ce “babu abinda zai gagara Ummy tunda haka Allah ya kaddara min”
Ya juya ga Hafsa “yauwa Wifey ke zaki shawo min kan kawar ki duk da cewar tana sona amman tana fada min kullum cewar ba zata taba auren Mijin Bestyn ta ba”
Hafsa tayi dariya “kar ka damu Yaya amman fa sai ka bada cin hanci in kana son kaga aiki kamar yankan wuka”
“Laa Wifey a mulkin Baba Buharin? to amman dai ba komi me kk so?”
“Gombe za’a kaini nima gobe” ta fada cikin tsokana
“Eyyah ba rabo ba wifey ai kin makara gobe zasu taho Sadiq zai kawota” Yarima ya fada yana mata dariya
Cike da farin ciki Hafsa tace “Kai amma naji dadi wlh shima Ya Sadiq zai zo gidanmu kenan”
“Yes har kwana biyu ma zai mana sai ranar da zaku koma Schl zai tafi” cewar Mus’ab
Wow take fada cikin ranta ko ba komi zata ga sanyin idaniyar ta
Stop did Hafsat
Matar wani fa kike shirin zama
Kar ma ki fara sawa zuciyanki wannan tunanin
Baki da damar son wani sai Yarima
Zuciyanta ke sanar da ita wadan nan kalaman amman ta basar ta cigaba da murna a haka tayi bacci ranar cikin farin ciki she can’t wait for 2moro
Karfe 11am su Mami sukayi sallama da Ammi suka kama hanyar Bauchi Ko wanne ckin ransa yana mai farin cikin ganin masoyinsa suna ta hirar su har suka shigo garin Sadiq ba bako bane a Bauchi tunda nan yayi karatu so ba sai ya tambayi hanya ba Kai tsaye ya nufi fada suna kofa ya kira Mus’ab ya sanar dashi isowan su fitowa yayi da kafarsa har bakin kofa
“Amma dai kai banxa ne kamar wani bako zaka tsaya a nan” Yarima ya fada yana hararan shi
“Eh naji dai mara kunyar In law haka zan baka auren?”
Zaro ido Yarima yayi yana mmakin yadda akayi Sadiq ya gano shi Sadiq yayi dariya ganin yadda yake raba idanu “Oh ka dauka ban sani ba dallah muje”
Mami dake cikin mota ta leko “Allah in tadi zaku tsaya yi zan shiga in barku”
Kunne Yarima ya kama “Sorry Princess Blacky muje” ya fada yana shiga wajen driver Sadiq ya shiga baya
STORY CONTINUES BELOW
Harara ta balla mai “nidai bani bace Blacky sedai Matar ka Mayyar baccin nan”
Dariya yake mata harda gwalo ta lura yau ‘yan tsokanar na kusa sai ta kyale sa
Suna shiga Mami ta fice da gudu tayi ciki tana kiran Besty da Ummy
Hafsat dake tsara kwalliya a dakin ta amman kunnenta na falo tana kuma faman duba agogo tana shirin daura dankwali taji muryar Bestyn ta da gudu ta fito suka hadu a falo suka rungume juna
Sadiq da ke biye da ita suka kariso yana fadin “Kedai Baby bansan yaushe zaki girma ba sam har….” Maganarshi ta makale ganin kyakkyawar halittan data dago take zuciyar shi ta fara bugu irin wanda ko sunanta yaji hakan yake ji itan ma hakan take ji cikin zuciyar ta ta kasa koda motsawa har su Yarima suka zauna Sadiq ne yayi dauriya yace “Kanwata ba gaisuwa ne?”
Jawota Mami tayi har gabansa tace “Yauwa Besty zo nan daman Yaya yace ya canza ni wai kece Babyn shi ynx”
Murmushi Kawai tayi ta gaidashi Yarima yace “to sai me rabu dasu bama gayyarshi daman ke Baby na ce ni kadai”
Ummi dake fitowa hayaniyarsu ya tado ta tace “to meeting din yaare akeyi ne banda ni?”
Duk suka mike suka gaidata tana ta saka musu Albarka tare da tambayarsu Ammi nan sukaita hira har zuwa azahar bayan sunci abinci ne suka tafi don su huta Mus’ab yace da yamma su shirya zasu je yawo
Dakin Hafsa suka shige suka kwanta suka fara hirar su ta kawaye a nan Hafsa ke sanar da Mami yadda sukayi da Yarima ai bata karasa ba Mami ta mike “amman Besty bansan bakida hankali ba sai yau tunda har kika yarda to nikam ba dani ba wlh”
Suka fara musu daga karshe Mami tayi fushi ta juya mata baya a haka bacci ya daukesu
Kiran sallar la’asar ne ya tada Mami wanka tayo tare da alwala ta tarar da Hafsa ma ta tashi itama shigewa bayin tayi bayan sunyi sallah ko wacce ta shirya suka fito falo ko magana Mami taki mata wai a dole fushi take amman cikin ranta taji farin cikin cewar ba ita kadai ke sonsa ba shima yana sonta
Cikin shirin kananan kaya suka shigo falon ‘yan matan biyu ke zaune kowacce da abinda take Hafsa tana danna wayar Ummy ita kuma Mami kallo take gefen ta Yarima ya zauna yana kare mata kallo cikin doguwar rigar Atamfa bata daura dankwalin ba don ba gwana bace wajen saka dankwali sai ta yafa mayafi kalan pattern din rigan tayi kyau har ta gaji duk da babu kwalliya a fuskar ta
Shima Sadiq gefen Hafsa ya zauna yana dubanta “Baby yadai naga kamar fushi kike?”
Ta dan yi yake “a’a Yaya babu komi mun shirya”
Ba don ya yadda ba ya ce “oh haka kunyi kyau kuma” ya fada yana murmushi
“Maza muje ko” yana duban Yarima
“Ohh okay muje”
“Ina Ummy?” Sadiq ya tambaya
“Tana bangaren Abba” cewar Hafsa don Mami taki kulasu sam
Bangaren Mai martaba sukaje bayan sun gaidashi ya sa musu Albarka nan suka musu sallama suka wuce
Zaga gari sukayi sosai kafin suka yaada zango a Havila don shan Ice cream Jawo Sadiq Yarima yayi “Please Yaya jeka ka zauna wajen Hafsa zanyi rarrashi naga Baby kamar fushi take”
Hararsa Sadiq yayi “dan air kawai ni kk cewa yaya wa yasan ma ko kaine yayan” bai jira amsar shi ba yayi gaba suna zaune yaje kusa da Hafasa “Kanwata taho muyi wani sirri mana”
Babu musu ta tashi ta bisa suka zauna dan nesa dasu
Sam Hafsa ta kasa sakewa tasha Ice cream din don ya lura kunyarsa take “Baby look ni fa Yayanki ne miye kk jin kunya ta ko kinga haka kawar ki take yiwa Prince”
Tayi murmushi “ai shi saurayinta ne shiyasa” da sauri kuma ta rufe baki bata san maganar ta kwace mata ba
Gira ya daga mata alamar tambaya sai kuma yayi daria ganin yadda tayi “to shikenan nima sai in zama saurayin ki ai indai zaki daina haka”
Ta dauka wasa yake amman shi har cikin ranshi yake fada mata maganar tayi dariya
“Cafdi lallai ma ka taba ganin matar aure tayi saurayi ne?”
“Matar aure kuma waye mijin?”
Ta nuna mai Mus’ab dake zaune tare da Mami “ai tun yana makaranta aka cemin idan ya dawo za’a hadamu aure sbd haka ma kar in yadda in kula wani” ta karisa a hankali ganin yadda yake binta da kallo
Cikin ransa ya fara kokarin danne abinda ke taso masa don ya tabbata zaisha wahala kafin sonta ya fita cikin zuciyar shi sbd sone a farkon gani haka ya jure ya mata murmushin dole
Mikewa yyi ya isa wajen su Yarima dake ta famar tambayar Mami amman tace babu komi yaso sanar da ita yana sonta da yadda sukayi da Ummy amman ya fasa zai bari sai ta gama Exam sam yau ko daria taki tamai dole ya hakura suka tafi gida motar shiru kowa da abinda keci mai raiA daddafe Sadiq yayi kwana biyu domin a koyaushe yaga Hafsa sonta karuwa yake cikin zuciyarsa a haka dai ya daure har Schl ya rakasu da zasu koma ya kuma jaddada masu cewar suyi kokari yanason ganin result mai kyau ya musu sallama ya koma Gombe
Haka su Mami ke ta faman rubuta Exam Hafsa dai bata sake tada maganar Yarima ba sbd gudun fushin Bestyn ta har suka gama Jarrabawar Mami bata koma Gombe ba sbd kwana biyu aka saka Speech nd Prize giving day ranar kuwa har Ammi Sadiq ya dauko suka zo su Mami sunsha kwalliya taji dadi sosai ganin Ammin ta nan Ummy suka hadu da Ammi kowaccen su taji kaunar ‘yar uwanta cikin ranta tashi daya wani abinda Sadiq ya lura dashi shine Ammi da Ummy da suka zauna waje daya yaga haka nan sun masa kama but bai kawo komai a ransa ba a haka aka gudanar da abubuwan a nutse ba hayaniya yayinda Hafsa da Mami suka karbi kyaututtuka da dama musamman ma ita Mamin domin ita ce Best student a shekarar
Bayan an tashi ne Ummy ta matsa wa Ammi cewar sedai su kwana gobe su wuce duk da cewar taso su koma a ranar amman haka dai ta hakura babu yadda zatayi a ranta tace Ina laifin me sonka
Sun sha hira sosai kamar wadan da suka san juna haka washegari aka rabu cikin kewa itama Ummy tayi alkawarin zata kai musu ziyara Gomben soon
Bayan sati biyu da yin Candyn su Mami Daddy wato Waxiri ya kira Yarima kan cewar sun gama magana da Abbansa nan da wata biyu za’ayi bikinsu shidai ya amsa da to sbd ynx baida matsala da auren Xee tunda zai sami muradin ranshi har yayi magana da Abba Sadiq ya tabbatar masa nan da Sati daya in sunyi magana da Mai martaba za’aje tambayo masa auren ta wajen Baffa Auwalu
Ya tashi zai fita a hanya suka hadu da Zee ta tsaya baiyi niyyar kulata ba yaji tace “sannu Yaya ina wuni?”
Dan dakatawa yayi ya juyo “lafia ya hutu”
“Alhamdulillah” ta amsa tare da shigewa falon Dad dinta
Bayanta yabi da kallo yana mamaki sbd tun lkcn da suke Exams ya lura da canzawa da tayi ko Staffs ma suna maganar ynx an daina yawan kai karanta duk da ba duka ta daina ba kuma ta daina yawan shigemai da takeyi gashi yau harda gaisuwa ya dan tabe baki yayi tafiyar sa zuwa wajen Ummy
Actually ita Zainab bawai wani halin banza ne da ita ba daman dai sangarta ce irin ta yaran masu kudi sai kuma rashin wayo wanda hakan yasa haduwarta da Sauda ya kara bata ta da rashin ganin girman na gaba
A kullum burin Umman ta shine ta kasance ‘ya ta gari ko yaushe takan mata misali da Hafsa wanda hakan shi ya jawo tsanar Hafsan cikin zuciyarta kuma kawarta Sauda take zugata suke takura rayuwar ita Hafsan kasancewar ta shiru² bata kuma son hayaniya to sai bayan zuwan Mami lkcn suna JSS 3 kafin suka sarara mata don Mami akwai zafin rai da masifa wannan yasa suke tsoronta
Umma dai bata fasa yiwa Zainab fada ba akan hakan har sabani suke samu da Waxiri domin ko cikin Yayyenta Maza babu wanda ya isa ya tsawatar mata to a haka da Umma ta lura Zainab tana matukar son Yarima sai tayi amfani da hakan wajen nutsar da ita kullum tana nuna mata yadda yake kula da su Mami sbd suna da nutsuwa ba irinta ba da kuma cewar ta daina yawan shige masa tunda ya amsa cewar zai auretan to Alhamdulillah da alamu dai ta fara daukn maganar Umman
Mus’ab yayi waya da Sadiq cewar ya sanar da Ammi akwai me son Mami daga Bauchi kuma yana son ya turo a nemar masa auren ta amman sun kulla kada ya fada mata shine har sai yaxo din to itama bata wani ja ba tunda Bappa Auwalu ya takura tun dawowar Mami cewar sedai ta fidda miji ko ya aurar wa duk wanda yaga dama mutane sun dameshi ita ta gode wa Allah ma da ya basu dama baiyi radin kansa ba don haka da amince da batun Sadiq don ya tabbatar mata cewa sanda yayi bincike kuma ya amince da tarbiyyar yaron
STORY CONTINUES BELOW
Ranar Asabar kuwa Abbah Sadiq,abokinsa da Waxiri suka nufi Gombe direct Jeka da Fari suka wuce gidan Malam don Bappha yace acha zasu hadu sbd duk iya shegen Bappa Auwalu yana shakkar Malam abokin mahaifinsu ne kuma Malaminsa
Yarima ne ke jansu suna isa Gombe ya biya ta Kasuwa ya dauko Sadiq don ya musu Jagora
Mami dake gidan tazo Weekend tana kwance dakin Inna taji ana maganar yau za’a xo neman aurenta bata wani daga hankali ba saima dadi da taji a ranta watakila hakan zaisa ta daina son Mus’ab don ko an rasa maza duniyar nan bata auren Mijin Bestyn ta
Tana jin Sallamar Yayan ta yaxo yayi wa bakin iso kafin ya fita ya shigo dasu Manyan ne kawai suka shiga falon Malam yayin da su Sadiq suka gaida matan yana tsokanar su Inna tace “Kai tafi chan ynx bamayi dakai ga Takwarar Yaya nan zata kawo mana sabon Ango me zamuyi dakai”
Sadiq yy daria “kedai kice kinga dan fari zaki canza ni to aradu na zama takalmin kaza mutu karaba”
“Ni ina naganshi ma yazo dai Inga ko yakai ni haduwa”
Yarima ya nuna yana fadin “ai shine wannan a gabanki”
Zaro idanu tayi “Kai banson shakiyanci wannan ai abokin Kane”
Murmushi sukayi dukansu Sadiq ya tabbatar mata shine dai suka fice cewar zasu tafi gidan Ammi
Mami tana jin ana ga angon Cousins dinta ‘yan mata suna leqensa sai santin kyaunsa suke suna fadin gaskia kun dace Mami sosai wlh dayar su tace “nikam ma don kar kuce nayi karya da sai ince Kama suke wlh dimples dinsu iri daya”
Sukayi dariya ita kam jin ance dimple Yarima kawai ta tuno don ko a jikinta bata damu da tasan ko waye ba Angon ba indai su Malam sun amince dashi shikenan bata da ja domin ko Amminta ma shi ya zaba mata Miji kuma kullum Ammi takance batayi nadamar biyayyarta gareshi ba sbd itama shaidace koda bata tashi ta ga Abban ta ba kullum mahaifiyarta tana bata labarin kyawawan halayensa
Ammi tayi mamaki kwarai jin cewar Mus’ab keson auren diyarta da suka fada mata shi da Sadiq taso kin amincewa ganin daga gidan da ya fito amman ya nuna mata shi tsakani da Allah yake son Mami kuma ai dukansu daya ne wajen Allah sbd haka ta amince a nan suka ci abinci kafin suka koma shagon Sadiq suna jiran kiransu Abba Sadiq idan sun gama
A dakin Malam kuwa bayan ‘yan gaishe² suka gabatar da kansu matsayin wadan da suka zo nema wa dansu auren diyarsu Hafsa nan Malam ya fara musu tambayoyi da kuma inda suka fito
Waxiri ne ya gyara zamansa ya fara bayani “da farko dai ni suna na Isma’il Mu’ayyad Dembo ni kanin mahaifin Mus’ab ne kuma Waxirin shi,wannan kuma Kanin mahaifiyarsa ne Abubakar Sadiq Lamido sai amininshi gashi nan Alhaji Bashir daga Bauchi muke kuma shi yaron shine da namiji tilo wajen mahaifinsa Mubin Mu’ayyad Dembo wato Sarkin Bauchi”
Jinjina kai kawai Malam yake yana fadin “Allahu Akbar! Allah buwayi gagara misali, Ubangiji maiyin yadda yaso, tabbas tun farkon gani na da yaron na kasa mntawa dashi a kullum sai wani abu ya fado min amman nayi shiru duk da cewa sanin inda ya fito ya sake tabbatar min hasashena kan iya zama gaskia amman na kasa tabuka komi duk kuwa da sanin cewar dole watarana sai na fadi abinda nake boyewa cikin zuri’a ta” yadan dakata tare da duban Abbah Sadiq na ‘yan wasu dakikai suma shi suke kallo don maganganunsa sun jefasu cikin duhu sam basu fahimce shi ba kafin kuma waninsu ya tambaya yaci gaba da magana “tun shigowar ku nake kallon wannan bawan Allah domin kamanninsa da yaron zatona shine mahaifinsa ashe kawun sa ne to amman jin cikakken sunan ka yasa na gne cewar zatona gaskia ne akan wancan al’amarin kuma wannan abu tabbas Allah ne ya hada yaran nan domin warware wani kullallen al’amari da nake fatan warwareshi kafin mutuwa ta iskeni nabar baya da kura”
Abbah Sadiq ne yayi karfin halin katse shi tare da fadin “Alhaji hakika kalaman nan naka sun jefamu cikin duhu kuma baka ce komi ba kan maganar dake tafe damu”
Murmushi Malam yayi “kwantar da hankalin ka kaji maganar dake tafe daku bazance komi ba ynx a kanta a yau amman ina son sanin ko mahaifinka yana raye”
Sunyi mamakin tambayar amman Abbah ya bashi amsa da cewar tabbas yana nan da ransa
“Shikenan kuje gida ka sanar dashi cewan gobe yana da baqi daga Gombe in Allah yaso” Cewar Malam
Sudai basu fahimci komi ba Alh. Bashir yace “Ranka shi dade muna fatan dai komi lafia?”
A karo na biyu Malam ya murmusa “lafia lau sai Alkhairi kar ku damu goben da yardar Allah muna tafe”
Mikewa yayi ya fita ya barsu kowa na sake² cikin zuciyarsa abinci aka kawo musu dakyar ma suka ci kadan da Malam ya matsa kafin suka kira Yarima yazo sukayi sallama da Malam suka kama hanyar gida
Bappa da bai fahimci komi ba ya tashi zai tafi Malam yace ya shirya shima dashi za’ayi tafiyar
Waya Malam yayi wa Sadiq yace su shirya shida Ammi gobe da safe suxo zasuyi tafiya haka ma Inna uwargidansa ya sanar da ita gobe zasuyi tafia ita da Mami su shirya…..
Nima barinje na shirya kar a barni a baya wajen tafiya Bauchin Yakubu jiyo muku abinda za’ayi ko Masa zan dan ci