ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


da kuma jimamin rashin da muka yi na Www.bankinhausanovels.com.ng
Alh. Kabiru, babu wanda bai tausaya min ba, amma ni samun Maryam shi ne ya Kara dauke min damuwar, tun daga lokacin na fara fitar da rai na akan aure. Mustapha na da shekara hudu Maryam na – da shekara daya a duniya Innawuro ta samu ciki wanda tun daga samun sa take cikin matsala, ga kuma laulayi na Kin Karawa, domin kullum tana cikin larura, dole yasa aka cire Maryam daga shan Mama ganin itama ta fara yin rashin lafiya. ‘Kullum muka zauna ni da ita ta dinga yi min magana akan cikin nan, da kuma cewa. “Rehana anya kuwa wannan cikin zai barni na rayu da ku? Domin tunda nake ban taba daukar ciki mai wuya haka ba. Idan har na mutu ki daure ki kular min da Maryam da Mustapha, ki riKe su tamkar yadda za ki riKe yaran da kika haifa a cikin ki, bana so ki bar su hannun su Saude, domin ba za su riKe su tsakani da Allah ba. Domin na fuskanci tsanar da suke min ita ce ta koma kansu idan har na haifi wannan cikin shima ki hada ki riKe, domin ji na nake kamar rayuwata ta zo Karshe.

Hankalina ya yi mugun tashi domin kalamanta sun taba zuciyata, nan take na nuna mata kada ta ji komai yadda ta haifi sauran haka ma wannan zata haihu lafiya, ciwo ne kawai yasa take wannan sambatun. Kullum muka zauna sai tayi min wannan zancen, nan take na ce ni dai ta daina. Da ciwo ya yi yawa dole muka tattara muka koma Rano, watanmu kusan uku a can ta warware

sarai. Sai a lokacin harkalin kowa ya dawo jikinsa, amma kullum muka zuna sai ta ce min.  “Raihanatu, don Allah ki kula da yaranki sosai ga amanar su nan duniya da lahira”.
Haka zan nuna mata ta daina min irin wannan zancen, ganin bana so yasa ta daina yi Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun komawar mu Rano sau biyu ne zan ce ga Kafar su Saude a gidanmu, domin ni a gurina da zuwan su da rashin zuwan su duk daya.
_ Ranar da suka yi zuwa na uku ne a nan ne – Innawuro ta nemi su yafe ma juna, su kansu sai a lokacin suka ji nadamar abinda suke mata.
Cikinta wata takwas bai isa haihuwa ba rana daya wani ciwo ya tasar mata, kwananta biyu a asibiti ta ce ga garinku nan.
Tsananin rudani da rikicewa babu wanda ban shiga ba, domin ban taba dandana jin zafin mutuwa iri wannan ba. Babu yadda za mu yi dole mu dauki haKuri da Kaddara.
Alh. Nasir ya yi matuKar jin mutuwar nan, amma duk da haka saiya nuna yafi tausaya min da yaran da aka bari.
Haka kowa ya zo gaisuwa sai ya tausaya min, Mustapha da Maryam kuwa’ suna nanike dani, babu wanda suke yarda da shi sai n1. Da na kalli yaran sai naji kuka ya zo min. Ana gobe sadakar arba’in muna zaune da su Baffa da Innar su suka zo min da wani labari da ya ruda ni rudu na gaske kuwa, na cewa wai gobe a gurin addu’a za a daura aure na da Alh. Nasir a yi madadi da ni. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kuka na saka musu na ce ban yarda ba na auri mijin ‘yar uwata, aka yi aka yi dani na tsaya da kukan na ki. Nan wasu daga cikin iyayen mu maza da mata suka shiga saka baki tare fa fada min cewa Alh, Nasir nemi hakan da kansa. Ya ce, “A roKar masa gurinki, ba don komai ba sai don saboda yara sun riga da sun gama sabawa da ke, babu wanda suka sani bayan ke”.
Shiru nayi ina kuka, mahaifiyar sa ta karba tace,
. “Raihanatu ko ba don komai ba don yaranki ki daure ki maye gurbin ‘yar uwarki, domin kin fi kowa sanin zaman da za su yi a gidan ubansu idan ba kya kusa da su. Sannan kuma da ana mutuwa a dawo idan ki ka yiwa ‘yar uwarki haka ta dawo ta gani zata yi murna da farn cikin kin kula da yaran ta, na tabbata ta ‘ baki amanar yaranta a hannun ki.
Nan nayi shiru na dinga tunanin irin maganganun da muke yi da ita akan yara, tun kafin ta kwanta rashin laifyar nan. Na ci kukana na Koshi, babu yadda na iya dole na amsa musu na yarda.
Nan farin ciki ya cika su, suka shiga saka min albarka da nuna min cewa dama haka Allah Ya rubuta, shi yasa tun farko Allah bai Kaddara yin aurena ba, domin a lokacin shekaru na sun dan soma dagawa sabanin yadda akewa kowacce budurwar aure a Kauyen mu. Da daddare Alh. Nasir ya zo ya yi min godiya da taimakon da nayi masa, kuma insha
-Allahu ba zai taba barinta cikin damuwa ba, zai mata duk abinda take so ita da yaransa.
Kuka na saka mishi domin ban san da wacce kalma zan ce da shi ba, ganina cikin damuwa ya bani hakuri ya ce na tashi na koma cikin gida. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kafin na koma ciki aka kawo min yara suna kuka, a wannan lokacin naji dole ne ma na saki raina na auri Alh. Nasir domin yaran su tashi gaban mahaifinsu, don mu samu damar basu tarbiyya ni da shi.
Ganin yadda suka yi shiru a jikina sai ya samu damar cewa._
“Raihanatu ko ba don ni ba don yaran nan da suke ganinki kamar wacce ta haife su ki yarda ki maye gurbin ‘yar uwarki matuKar ba kya so su san maraici”. “Babu komai na amince, ita kuma Allah Ya jiKanta da rahama”.
Murna ya nuna sosai, ya yi min godiya, haka muka rabu na shiga ciki da yara. Maryam na rungume a kafada ta shi kuma Mustapha na rike masa hannu muka shige muka bar shi zaune a gurin. Washe gari haka aka hada daurin aurenmu
*da addu’ar arba’in din Innawuro, mutane da dama sun nuna farin cikin yin haka, addu’a aka yi sosai
a gurin. Tunda ana cikin alhini ba wani shagalin biki don haka aka tsayar sati mai zuwa zan tare a dakin ‘yar uwata hade da yara na biyu.
Sam Alh. Kabir bai sanarwa da matansa maganar auren mu ba, don bai barsu sun zo Ranon ba, haka ya ce su zauna a Kanon su yi duk abinda ya dace, sai washegari ya zo musu da labarin daurin auren, haka suka ji abin sama. Take hankalin su ya yi mummunan tashi, suka shiga ce mas yaCi amanar su ya yi aure ba tare a sanin su ba. Ganin da yayi za su bata masa lokaci ya tafi ya barsu a gurin.
Haka dai na zo na tare a dakin ‘yar uwata, gori da takaici da habaici babu abin da ban fuskanta gurin A’i da Saude ba, duk bakina amma na kasa yi musu komai, da zama ya fara zama na gaji da abin da suke yi min na fara tanka musu.
Ke na taKaita miki daga ni har yaran sai da zaman gidan yaso ma. gagarar mu, da Kyar ya tsaya akan gidansa abubuwa suka dan soma sauki, da suka ga an soma girma sai suka saduda. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haihuwa ta uku, da fari na haifi Aziza, sai Mukhtar wanda ya ci sunan Baffanmu da Allah Ya yiwa resuwa, sai Ga auita na Usman. Kafin su girma Allah Ya dauki Aziza da Usman, Ya bar min Mustapha da Maryam da Mukhtar. Ita kuma Haj. A’i tana da yara biyar su ne Bara’atu, Jafar, Lukman, Habib sai Shehu da aka sa ma sunan Usman nawa. Ita kuma ta binne uku duk mata.
Sai Haj. Saude tana da hudu, Aminu, hamza, Aminatu da Hajara. Kinji yaran nan guda goma sha biyu da na lissafa miki su ne suka hadu suka gina junan su, suka zamo ZURI’A DAYA, ta cikin ZURI’Ar su ne aka same ku, kuma cikin su har yanzu suna nan babu wanda ya rasu, sai dai ba a guri daya suke yanzu ba, za kiji dalilin da yasa duk suka watsu cikin duniya”.
“Raihanatu na faro miki labarin ne tun daga tushen ku, don ki gane komai dalla-dalla, shi yasa na yi miki haka saboda kada zuwa gaba kice ba ki gane kowa ba tunda na ware miki
daki-daki kin gani”. ‘ haana tayi murmushi cikin alhini ta ce. “Granny na tausaya miki wallahi, kuma kin yi KoKari sosai. To shin ina su Haj. Saude da Haj. A’i? Suma suna raye ko sun rasu?” Tayi murmushi ta ce, “Raihanatu kenan, ai bak1 ji komar ba, ki biyo ni a sannu domin yanzu ne zan fara baki labarin komai har zuwa yau din nan da muke ciki, domin duk abubuwan da kika ji a baya somin tabi ne, ke dai ki saurare ni”Ta gyara zama ta ce, “Tam”, ‘ :
“Kamar yadda na fara fada miki zaman kishi muka yi sosai da kishiyoyi na har sai da yara suka girma aka dasa musu ‘yan ubanci, wannan baya son wannan dan dakin, amma nawa nice kawai ake yiwa haka.
Da kansa Alh. Nasir ya gane haka, ya tara kan yaransa gaba daya da matansa ya ce matuKar ba a kawar masa da wannan muguwar al’adar ba to gaba daya zai kori matan ya sake wasu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sanin zafin sa da suka yi da kuma ganin – tarin dukiyar da yake da shi a yanzu, domin akan arziKin sa na da sai muce ya ninka zaman sa a wannan lokacin, don yanzu komai nashi ne na kansa ba tare yake da na kowa ba. Domin ba gidansa kadai ba, ‘yan uwansa na jini babu wanda bai dagawa Kafa ba ya gina kansa, kusan duk Kannen sa sai da ya dawo da su cikin garin Kano suma suka kafa kansu.
Don haka ya tsaya sosai akan iyalinsa, sai da ya kawar da wannan bambance-bambancen ya gina Kauna da soyayya tsakanin yaransa. Hakan ba Karamin dadi naji ba, domin burina kenan naga mun samu hadin kan yaranmu. Babu laifi nima mun dan samu dai daituwa da abokan zamana.
Arzikin Alh. Nasir kullum daduwa yake yi, domin ya rungumi zumuncin Allah, duk wanda ya rabe shi shima sai ya yi arziKi, domin bashi da bakin ciki matuKar zaka yi gaskiya to zai daga maka kai ma ka tsaya da Kafar ka. Da yaransa da na ‘yan uwan ya tsaya akan su, duk abin da zai wa dansa shi zai yiwa dan dan uwansa don haka duk wanda ya gama karatunsa waje yake turashi ya karo ya karo karatu tun duniya na kwance haka ya shiga gidan manya manyan campany a garuruwan arewa yana diban jama,a yana sawa aiki duk burinsa idan yaransa sun girma baida burin Www.bankinhausanovels.com.ng barinsu yin aikin gwamnati yanason su hadu wuri guda donsu zama abin kwatance a duniya bara,atu itace diyar da muka fara aurar wa a cikin Zuri‘ar domin dama itace babba kaff cikinsu itama din auren dangi akayi musu da dan yayan alhaj nasir wanda shima shine babba a cikin jikokin gidan jafar lukman aminu da hamza sune manya a ciki sune aka fara aurar wa bayan auren bara,atu duk auren gida akayi musu domin anji dadin na farko wasu sunyi na biyu wasu kuma saida akai musu aure sannan sukai digiri na biyu haka zuri’ar ta zamo ta yan boko hatta muma daba wani bokon mukayi ba sai muka taso kamar wasu yan boko domin muna auren yan bokon ga kuma yayanmu yan boko Kasancewar mu daga tushe daya muka _ fito duk dinmu Fulani ne kuma na yanki daya, sai aka dinga kiran ZURI’Ar mu da gidan farare. Maganar kyau kuwa muna alfahari da ZURI’Ar niu, don wasu suna dauka cewa muna da dangantaka da Larabawa, nan kuwa basu sani ba asalin Fulanin Rano ne”.haana tayi dariya ta ce, “Kai Granny, irin  -wannan kurakaihaka”“Ba kurara kai bane, gaskiya na fada — domin mu Fulanin na yankin mu daban muke, kuma kema kin san haka a gareki”Haana tayi murmushi ta ce, “Granny na yarda, ci gaba da labarin ki, son ki ci gaban naji an fara gangarowa don kina ta samin Kaunar ZURI’A ta har na matsu naji Karshen labarin”. Lokaci guda Zuni’ar mu ta fara yaduwa  domin ‘ya’yanmu sun fara ajje mana jikoki, haka_ muka dauki soyayyar mu duk muka dora su akansu. Sai dai kaf cikin Zun’ar babu wanda_
yayi farin jinin Abdulhameed dan Alh. Jafar, domin yaro ne abin so daga zuciyar mu_ baki daya. Ba komai ne ya jawo haka ba domin shi ne jika namiji na farko a cikin Zuri‘ar, sauran duk mata ne, don an haifi har (twins) suna mutuwa, akansa ne dai suka fara tsayawa. Shekarun Hameed biyu aka yi auren
Mustapha da Kannen sa uku, Amina, Hajara da Karamar su Maryam, duk cikin dangi suka samu Www.bankinhausanovels.com.ng mazajen su, Mustapha ne dai ya dage sai da ya auri ba ‘yar dangi ta jini ba, ita ‘yar aminin Alh. Nasir ce, mutanen Garo ne, suma Fulani ne na asali, suma haka suke kamar Larabawa.Hameed ya tashi cikin gata da soyayyar iyaye da kakanni, domin kowa da irin son da yake nuna masa, har gatan ya so ya yi masa yawa, ba ya laifi ayi masa fada. Ganin yadda ZURI’A ta soma yawa farin ciki yana ta samuwa a cikinta yasa Alh. Nasir yin tunanin yiwa yaransa gini yadda za su hadu guri daya har Karshen rayuwar sa, don baya son ya ga abin da zai raba kansu. Don haka ya samu Katon fegi (wato fili) iya ganinka ya ce anan yake son ya gina ma zuni’ar sa gidaje inda za su dunKule guri guda har zuwa lokarin da kowa zai yi nasa iyalin suma su zauna ciki. Lokacin duniya na kwance, ga filaye nan ko ta ina, kuma gashi babban mutum da suke da alfarma a wannan gwamnatin, don haka ya zuba kudinsa sosai ya samu abin da yake so don har matansa mun fara yi masa surutu ya ce mu dai
mu barshi, yasan abinda yake, kowa ya zo ya ga filin sai ya girgiza kai.Haka aka fara gini iri daya har gidaje  sama da sha biyu, kuma duk tsarinsu iri daya, sai dai guda daya da ya bambanta da sauran wurin girma. Nan ya fara gaya mana cewa gida ne zai . gina tunda yara maza har mata kowa ya dawo gurin da mazajen su, wanda kuma ba su yi aure ba gashi nan guri yana jiransu. Kowa ya shiga nuna murnar sa yiwa Allah godiya ganin inda aka tanadar musu don rayuwa guri guda. Tunda aka yi KoKarin daina nuna wariyar daki da daki sai rayuwar tayi dadi, kowa ka gani yana farin ciki da abin da dan uwansa zai samu. Soyayya da Kaunar juna ya gama kewaye zuri’ar, babu wani mai kuka da dan uwansa.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *