ZURI’A DAYA BOOK 1 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin Kunar rai Haj. Asiya ta ce, “Daddy – kada ka kuskura ka Karasa gurin yaron nan, domin gashi a bayyane zarginmu ya zama gaske”Cikin tsawa da bacin rai ya juyo ya kalleta, ya ce. “Asiya kin san irin mugun furucin da kike yiwa dan da kika haifa a cikinki kuwa? Don kawai — Www.bankinhausanovels.com.ng
Zuciyar ki tana zargin wani abu sai kawai ki zartar da hukunci kai tsaye?” Daddy idan har kuna zargina da wani abu to haka ne nine na aikata, ni ne na jefa Aziza cikin halin da take ciki yanzu”.
Tasss! Ya dauke shi da wani wawan mari, sai da ya ga (stars) suna masa yawo a cikin idanunsa, ya yi sauri ya dafe kuncin sa, ya yi taga-taga zai fadi.
“Kana da hankali kuwa? Kasan abin da kake fada min da bakin ka? Yaushe ka fara hauka ne?” . ;
“Daddy wallahi sharrin zuciya da shaidan su ne suka debe ni na aikatawa Aziza haka, Daddy ku yafe min, wallahi nayi nadama fiye da tunanin ku”
– “Inna lilahi wa inna ilaihi raji’un! Hameed zargina ya zama dai-dai kenan? Ya Allah Ka dauki raina da ganin wannan rana mai tarin takaici, yanzu dama kaine ka aikata mata haka? Amma dai ka cuce mu, ka janyo mana gori da Surutu. cikin zuri’a, ka wulaKanta mu, ka wulakanta kanka. Ni Asiya yau naga ta kaina”.
Cikin kuka ya ce, “Mommy kiyi hakuri, wallahi nayi nadamar abinda na aikata a rayuwata’.
Nan ya taho zai riKeta ta kauce itama cikin kuka, ta ce. Wallahi idan ka taba ni zan tsine maka,,. domin da ganinka gabana gwara gawar ka, domin ka
janyo mana baKin jini da gaba a cikin danginmu”.
Cikin tsawa Alh. Jafar ya ce, “Asiya kina _ hauka ne? Kin san wane furuci kike yiwa dana? . — Kada ki kuskura ki furta masa tsinuwa domin . kina tsine masa nima zan datse igiyar auren mu ni da ke ta har abada”.Jafar me kake son fada min ne?” Ta ambaci sunan sa kai tsaye cikin bacin rai, sunan da ta dade bata ambata masa ba tun lokacin da Allah Ya basu Www.bankinhausanovels.com.ng yara Cikin Kunar rai yace, “(Okay) baki ji abin_ da na fada miki ba kenan sai na maimaita?” SO ‘ Nan take ya sake maimaita mata abinda ya fada da farko. Cikin zubar hawaye ta ce, “Idan har nice na tsuguna na haifi hameed to ba zan taba yafe masa abinda ya yiwa Aziza ba har sai yaje ya bayyanawa duniya cewa shi ne ya yi mata wannan rashin tausayin, amma idan ba haka ba to na yafewa duniya shi har da kaima kanka”. Da sauri Hameed ya zo ya rungume ta yana kuka yana cewa. “(Pleasc) Momce ka da kiyi fushi dani, idan har za ki yafe min to zan je na fadawa kowa cewa nine na cutar da Aziza ba kowa ba”. “Karya ku ke yi ke da shi, babu wanda ya isa ya tona min asiri cikin zuri’a, na yarda cewa Hameed shi ne ya aikata ma Aziza wannan danyen aikin, naji ni da kaina zan hukunta shi ba tare da kowa ya sani ba. Amma ya je ya tunkari Zuri’ar mu da wannan labarin ai tamkar kun daba min wuka a ciki ne. A barni da kaina zan hukunta abuna”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Yin hakan ba adalci bane Jafar, kuma ba addini bane tsabar son kanka da zuciyar ka shi ne zai sa ka fadi haka. Bari na fada maka, idan kana tunanin wannan shi ne soyayya ga abin da ka haifa to kayi kuskure, domin ka jefa danka cikin halaka, gwara kawai ka barshi a hukunta Shi kamar yadda shari’a ta tanada, amma yin hakan babu abin da zai haifar maka sai tarin bakin ciki da nadama”.
“Asiya ban taba tunanin ba kya son danki ba sai yau, ya aikata laifi bai Boye mana ba shi ne mu kuma za mu tonawa kanmu asiri duniya da Zuri’a su zage mu, to ni ba zan yi haka ba, na yarda yayi laifi a barni na hukunta shi da kaina”Sam wannan ba addini ba ne Jafar, sannan kuma ba so bane. Me za ayi da yaron da zai gwada wannan rashin imanin? Zan iya yafe auren ka matuKar ba ka bari an hukunta Hameed ba, don na rasa wane irin so kake ma ‘ya’yan da har idon ka ya rufe baka son ganin laifin su ko da kuwa wane irin laifi suka yi? Duk cikin Zuri‘ar nan yaran gidan nan sun. fita daban’ wurin tarbiyyar su, wanda kuwa hakan duk ya samo asali ne daga irin son da kake musu. Dalilin da yasa kenan ta kai ga Hameed ya aikata wannan – rashin imanin”. ° . . – Cikin tsawa ya ce, “Asiya ki rufe min baki na ce, Hamecd dana ne, ina son shi fiye da * dukkan yaran da na haifa, don haka banga abin da zai yi na juya masa baya ba a fadin duniyar nan, matuKar nima zan iya hukunta shi da hannuna. Ki zuba idanu ki gani, ni da kaina zan yi masa abin da baki yi tunani ba”. Cikin kuka Hameed ya Karaso ya rike Kafar mahaifinsa yana cewa.
“Daddy ka barni a hukunta ni kamar yadda addini ya tanadar, domin yin hakan shi ne zai sa na samu nutsuwa cikin zuciyata da kuma samun gafarar Allah. . Daddy nayi nadamar abinda na yiwa Aziza na, ban taba tunanin dai-dai da rana daya zan Cutar da ita ba, sai gashi zuciya tasa nina yi _ aikin da na sani.(Please) Daddy ka barni ayi min abin da Momee ta ce, domin bana son tayi fushi dani, don ina son ganinta cikin farin ciki”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Baka isa ba Hameed! Ba za ku kunyata ni cikin Zuri’a ta ba da kuma idon duniya, saboda zan zamo ba komai ba a cikin su, girmana da mutuncina da daraja ta za su zube a wajen su, ni . kuwa da na rasa mutunci da daraja ta cikin ZURI’A ta da idon duniya gwara na rasa shi a idon matar da nake aure da kai dana na kaina. Na yarda ban goyi bayan abin da ka aikata ‘ba, naji ciwo sosai har cikin zuciyata. Tunda
babu wanda yasan kaine ka aikata to ni dai da hannuna ko baki na ba zan iya daukar wuka na dabawa kaina ba, ma’‘ana na fadawa duniya cewa kai ne, don haka tun wuri mu rufe zancen a nan. MatuKar kaje ka tonawa kanka asiri ni ma _ zan tsine maka, zan kuma yanke duk wani alaka a tsakanin mu ni da kai na har abada, don haka ka tsaya kayi tunani. Ke kuma na fasa sakin, kije ki fada, ina da ~ hanyoyi da dama da zan bi don ganin na hukunta ki da su, kema kiyi tunani tona asirin ko rufa shi, cikin biyu dole ki yi daya. Kai kuma wuce muje ka ga likita don ya duba maka wannan goshin naka”.Bai tsaya ya jira amsar su ba ya ja hannun – sa suka fice, kai tsaye mota suka je suka shiga sai asibiti._ a Tun da suka tafi Hameed yake kuka bai . sarara ba, haka mahaifin sa ya shiga tausar sa da ba shi baki akan ya daina daga hankalin sa, babu abin da zai faru da shi sai alheri.Bayan fitar su Haj. Asiya ta zube a Kasa ; ‘tana kuka mai isar ta, tana tunanin irin rashin adalcin mai gidanta, tsabar rashin imani da tsoron Allah ga irin abin da yake furta mata.
Tabbas tasan irin mugun halin sa da kafiya da rashin kwantar da kai a cikin abin da yasa gaba, bashi da mai sa shi haka ba shi da mai hana shi.
Tabbas tasan rabuwar kan ZURI’Ar su ya zo, domin babu wani da za a yiwa haka cikin Zuri‘ar ya dauka, domin haKurin sa da son zamuncin sa, domin wannan keta haddin ya yi yawa.
Sannan ‘shin Jafar baya tunanin cewa wannan abin da yake wa yaransa shine gata ko so? Sai kana daurewa yaranka gindi kana fifita son su akan sauran yaran duniya? Tabbas ka yi kuskure, dole idan baka daina ba wata rana da kanka zaka dora hannu ._kayi kuka. Shin’ ma _ wait ina tunaninsa da – Kwakwalwar sa suka nufa? Idan ni ko Hameed wani bai fada ba ita idan Allah Ya tashi kafadar ta zai rufe mata bakin ta ne akan kada ta fada? To wannan ne bai isa ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ta daga hannu sama tana addu’a akan Allah Ya bata lafiya don gaskiya tayi halinta. Da wannan tunani ko nace addu’ar tayi dakinta, taje ta ja ta rufe zuciyar ta da Kuncin abin da ya faru.
Sai da safe ta ganshi anyi masa (dress) a_ gurin da yaji ciwon, suna haduwa ta daure fuska ya yi naci akan ta saurare shi ta Ki, dole ya , koma dakinsa ya Kulle yana kuka. Haka yaji gaba daya duniyar tayi masa ba dadi, ya Kara jin tsanar kansa da rayuwar ma gaba daya. Haka dai ya zamo abin tsangwana a gurin mahaifiyar sa, – dole yasa ya koma rayuwar sa shi kadai a cikin daki.
Tun sanda mahaifin sa ya zo masa da labarin abin da likita ya fada musu na cewa ba lallai bane ta ‘iya tuna abin da ya faru da ita ba, domin ta samu ta yi wata irin razana mai tsanani , wanda hakan ya janyo mata fadawa_ cikin mawuyacin hali.
Da farko ya yi murna har yake fatan Allah – Yasa kada ta dawo cikin hayyacin ta domin kada ta tuna abin da ya faru a baya da ita, ta hakan ne
zai iya. bin duk hanyar da zai jaryo ya wanke laifin daya yi mata, amma fa a tunaninsa. . Amma tun sanda ya je ya ganta ya rasa ma
kansa nutsuwa haka kullum zai kebe kansa a daki , ya shiga yin kuka idan bai samu nutsuwa ba sai
ya dauki AlKur’ani yana karantawa sai yaji ya _ nemi damuwar sa ya rasa.
Sam Momin sa ta Ki sauraron sa, kullum haka zai sa ta gaba yana kuka haka ita ma za tai tayi, ita babban takaicin ta yadda Alh: Jafar ya yi mata katanga da zuwa asibiti domin yana ganin kamar idan ta je zata iya cewa Hameed ne ya aikata mata wannan al’amarin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hameed ne da kansa ya takura ma mahaifin nasa akan ala dole sai ya je asibitin ya
Sake ganin halin da Aziza take ciki, domin shi ma ya hana shi ganin yadda yake ce masa shi a bar shi ya bayyana cewa shi ne ya aikata mata haka ko ya samu ya samu nutsuwa, amma ya ce masa bai yarda ba.
Ganin kafiyar da ya nuna na son ganinta ya sa ya ce ya amince suje, amma ba zai barshi
Shi kadai ba don gudun kada ya kwanto masa kura.
Har cikin ran Alh. Jafar baya jin dadin abin da ya faru da Aziza, ya so Kwarai da farko ya dauki mataki mai arfi a ranar da abin ya faru, amma daga baya da ya gane abin a gindinsa yake sai ya yi shiru ya shiga taka tsantsan da al’amarin_ don kada abu ya fito aji kunya. Dole ya sa yake faranta ran Haj. Asiya don kada tayi fushi ta tona asirin dansu, amma duk abin da zai yi mata a banza domin kawai kallon sa take yi.
A wannan ranar ce suka je da Hameed din da tashin hankalin suka dawo gida, domin kadan ya rage Hameed ya tonawa kansa asiri. A cikin mota ya shiga yi masa masifa ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, shi kuwa Hameed shiru yayi yana dubansa, bai ce da shi komai ba.
Da suka dawo gida haka ya shiga dakinsa ya rufe kwana daya da wuni ya yi bai bude ba, hankalin Alh. Jafar ya yi matuKar tashi.
Washegari ko wurin aiki bai je ba, ya tsaya a bakin dakin yana ta roKon sa da ya bude
don da farko zaginsa yake ta yi ganin ya Ki dole ya dawo yana rarrashin sa da bashi baki akan zai masa duk abinda yake so idan ya bude Kofar. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka yayi ya gaji ya koma ya dawo, haka
ya yi tsawon ranar shi ba abinda yaje ya fadawa wani cikin ‘yan uwansa ba abin da yake gudu ya zo ya faru, domin dole ne sai sun so jin dalilin sa na yin hakan, shi kuma ba zai iya fadawa kowa ba.
Haj. Asiya tana kallon su babu abin da ta ce da su sai tsananin mamakin irin Kaunar da yake nunawa Hameed kamar ransa, wanda hakan ne ya janyo ya fada cikin wannan halakar. Don tabbas ta san Alh. Jafar yana: matukar son Hameed fiye da komai a cikin rayuwar sa, ta san zai iya aikata komai akan sa, don ya ga ya bashi farin ciki.
Sai dai kuma a yanzu yanda ake da wuya ya bawa Hameed farin cikin da yake so, domin farin cikin sa a yanzu shi ne ya bar shi ya fada cewa shi ne ya yiwa Aziza wannan aika-aikar. Amma ina! ba zai taba barin haka ya fsaru ba. Sai misalin sallar isha taje ta yiwa Hameed magana akan ya bude dakin, da yaji
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG