WATA MACE CHAPTER 6 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 6 BY SANA S MATAZU


                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Look Ramlatu kinsan dai abinda ki ke be dace ba. Ta yaya na kai kuɗi gidanku amma kuma kina tsayawa da samari kuma dan cin fuska a gabana?”

“Dakata Kabir, ni fa allura ce acikin ruwa ta yaya zan tsaya ka yi min sakiyar da ba ruwa. Na sani ko ƙarya ka ke ba aurena zaka yi ba, sai na gama sakankancewa sannan in ji wuf ka fece!”

Wani miyau ya haɗiya yana jin kansa yana yi masa nauyi,

“Be san abinda ya ja shi ga auren Ramlatu ba, duk da zuciyarsa ce ja gaban kwaɗaitar da shi cewa ita ce ta dace da shi amma kuma yana ganin kamar ya yi kuskure”

Kallonta yake idanunsa jajjur, amma kuma wata shakkarta da be san dalilinta ba tana mammayeshi. Kamar wanda aka datsema baki ya kasa tanka mata haka ta juya tana girgije-girgije. Ƙasan ransa ya na jin kewar Zahidaht da komai nata.

“Shikenan Ramlatu ki faɗa ma su Baba ji bi za a zo batun saka rana kuma wata ɗaya nake buƙata!”

Guɗa ta yi tare da kai masa hug, “amma ka biyani wallahi”

Janye jikinsa ya yi yana takaicinta, sai dai ya gaza hanata shi gaba ɗaya ma tsoronta yake ji dan wani kwarjini take yi masa.

***

Ƴan kai amarya sun ɗaukin hanyar Geza. Tafiya suke ba kama hannun yaro. Tun Labiba na ganin abin wasa ne har ta soma gajiya, ita da Tukur ya ce mata nan nan unguwar Maude za a kaita. Tazararta da gida kaɗan ne amma kuma ta ji sai lulawa ake. Gashi an ƙumsheta cikin mayafi ga zafi ana yi, ganin tafiyar ba ta ƙare ba ce yasa ta yayye rufin tana kallon yadda suke wuce hanya. Wani abu ne yake tokare da zuciyarta ganin da gaske ƙauyen Geza za a kaita. Bata manta ba, nan ne garin da ƙawarta Atine ta yi aure. Suka dinga yi mata dariya tun suna yara bare kuma yanzu? Tabbas ya yaudareta amma zata nuna masa kuransa. Sai dai wata zuciyar na gargaɗinta kan kadda fa ƙilu ta jawo bau. Ba wannan ne matsalarta ba, ta ina zata fara rayuwa a ƙauyen nan da ko service me kyau basu da shi. Kennan da gaske ƴan gidansu suke yi na cewar gidan ma da zata zauna na ƙasa ne? Da sauri ta girgiza kanta tana ayyana miliyan guda fa ta bashi ya zai kama mata gidan ƙasa?

Tunaninta ya katse daidai lokacin da suka ajiye motarsu a ƙofar wani gidan ƙasa. Kasancewar akwai sauran rana bata ƙarasa faɗuwaba. Sossai ta ware ido tana kallon ƙofar gidan. Ya sha shafe da farar ƙasa an mana irin tambarin nan na indomie da ake yi wa gidajen ƙasar ƙauyuka. Gabanta ya doka, tana saukewa Hajiya iyyah harara saboda mitar da take na taƙi rufe fuskarta. Bata damu ba, ta soma jan hannunta,

“Labiba fito mun kawo ki gidanki”

Hajiya Mawwadah ta maida dariyarta tana yin gaba, tare da cewa,

“ku sata ta yi basmallah ta saka ƙafar dama!”

“Angama Mamarmu”

Cewar Ade tana rangaɗa guɗa cike da shaƙiyanci. Su Yaya Amina da Maryam da Husnah kuwa  sakatotto suka yi dan dama su basu san dawan garin ba tunda basu zo jera ba. Duk surutan da ake a gida sun ɗauka iya shege ne. Labiba kamar mutum-mutumi haka aka dinga janta. Ta dinga binsu kamar raƙumi da akala. Yuuuu! Yara suka yi dafifi a ƙofar gidan suna shafa bango kamar sun ga wani sabon abu. Suka shiga gida sai ƙamshin ƙasa yake da yake anyi yayyafi kafin  su ƙaraso.

Ɗakuna uku ne a gidan, ɗaya ya ɗauke kujerunta gaba ɗaya da tv da fankar ƙasa Ox babbar sai firij ɗinta. Ɗayan kuma ya ɗauki gado da kwaba da mudubi. Sai kayan kicin ɗinta da aka tsubesu a cikin ɗayar kwabar saboda babu kanta. Hasalima turaku uku ne na murhun dutse da aka yi da gini babba da ƙarami kuma ciki babu daɓe. Sai rumbun hatsi a tsakar gidan, daga gefe kuma buɗaɗɗan banɗakine. Tsakar gidan ya sha irin shafa nan me tafiyar mijici da ake yi a ƙauyuka da farar ƙasa. Labiba kasa jurewa ta yi ta warce hannunta tare da lallubar jakarta hannun Yaya Amina tana ƙoƙarin kiran Tukur amma kuma yaƙi ɗagawa. Fashewa ta yi da kuka,

“Wallahi bazan zauna a wannan matsiyacin ƙauyen ba, ai ba haka muka yi da shi ba. Uw…sa ya yi da kuɗin da ya…”

Bakinta Hajiya Mawwadah ta buge tare da turata ɗakin da gado yake, ba dan komai ba sai dan ganin yadda yara suka yi dafifi suna kallonta. Daga bayansu kuma mata ne zuga guda an zo tarar amarya. Suna zama kuwa matan na shigowa. Nan aka gaggaisa suka soma gabatar da kansu, matan kawunansa ne da kannansa sai kuma yayyansa mata uku. Dukkansu anan garin suke wasu ma suna maƙotaka da Labiban. A ɗage take dubansu, tana yatsina duk ta gama ƙaguwa Tukur ya dawo ta sauke masa kwandon masifa na ha’intarta da ya yi ya kawota ƙauye. Lallai mutum mugun ita ce ne. Ƙanwar Tukur ce ta kasa haƙuri da duban da take musu, ta ga ko ƴar kunyar nan ma ta amare babu a gun amaryar tasu ta furta,

“mu dai ance mana matan birni basu da ta ido, naga kuma da alama irinsu aka kwaso masa!”

“Mene ne haka Magajiya”

Cewar matar ƙanin mahaifinsu Lantana tana umartar yara da su ajiye fantekun da suka zo da su. Nan da nan suka miƙe, Addeh ta cikasu da tukuicin dubu goma. Kamar su goyata haka suka fita suna murna. Sai dai da hanzari wasu suka zagaya suna kaiwa mahaifiyar Tukur tsegumin irin surukar da aka ɗauko mata. Sossai ta shiga faɗa tana ba zata lamunta ba kasancewarta mace me zafi. Ana haka Tukur ya ƙaraso, nan ta haushi da faɗa haƙuri ya dinga bata tare da nuna mata zai ja kunnan Labiban. Fita ya yi yana jinjina abinda ya faru duk da ya shiryawa haka domin ya san halinta amma ba zai juri ƙasƙantar da martabar mahaifiyarsa ba. Yaƙin nasa ne._Suna da yatsan ɗagawa su yi nuni wa shafin da ƙaddara ta buɗewa ɗayansu abisa kalmar sakaci. Amma kuma nasu yatsan ya kan zauna a ƙwantare wajen nuni wa nasu sakacin zuwa kalmar ƙaddara. Idanunsu na da kaifi wajen hango kuskure duk ƙanƙantarsa. Amma suna zama makafi yayinda suka hango nasu kuskuren koda kuwa kusancinsu da shi ya kai sun shafa sun ji tabbacinsa._+

WAYE TUKUR?

Ita ce tambayar da Labiba taketa nanawata acikin zuciyarta. Domin gaba ɗaya ta rikice. Ƴan kai amarya kuwa tun suna ƙunshe dariyarsu har wasu suka soma yi a gabanta sai da Hajiya Mawwadah ta tsawatar musu. Ta kira Yaya Khamis ya fi sau shurin masaƙi amma wayarsa bata shiga hakama Amne. Ƙarshe ta ajiye girman kanta ta sa Husnah ta bincika mata aka tabbatar mata network ɗin garin baya tafiya sossai sai cikin dare ko kuma ka zaga baya ka hau dutse.

  Abin ya bata mamaki dama akwai irin waɗanna ƙauyukan a cikin garinsu? Ta dai ji ana faɗar garin geza amma bata taɓa zuwa ba, hasalima akwai gonakin mahaifinsu a garin waɗanda bayan rasuwarsa duk aka saidasu. Amma bata taɓa tunanin haka ƙauyen yake ba. Tana yawan ganin ƴan garin sun kawo tallan gyaɗa me gishiri cikin Sakwato. Yanayin yadda suke wajen rashin tsafta ga rashin kunya da raina mutane, uwa uba rashin wayewa. Duk bata ɗauki lamarinsu da zafi ba, ta ɗauka kawai abu ne irin na ƴan tallah musamman a shigarsu.

***

Tukur shi ne cikakken sunansa. Matashi ne me kimanin shekaru talatin cif, amma matsi da ƙuncin rayuwa ya takureshi waje ɗaya ɗan firit da shi kamar ɗan shekara ashirin da ɗoriya. Yana da faɗin ƙirji da kuma ƙaton kai ga tagomashin tsagun magge a gefan bakinsa.

  Su takwas mahaifinsu ya mutu ya bari, babu wanda ya sami tagomashin karatun boko saboda rayuwar yau da gobe. Yayarsu Hajara sai Katume da Tsahare da kuma Indo. Duk suna aure anan Geza da ƴaƴansu. Tukur shi ne na biyar sai Auwala da Isuhule daga nan sai autarsu Mero data rage ba ayi mata aure ba.

  Auwala direba ne Lagos yake zuwa. Isuhule kuwa manomine. Sai Tukur da ubangiji ya taimakeshi aka turashi garin Sakwato almajiranci. Anan ya sami karatu na izzuf talatin cif daga nan ya faɗa buga-bugar rayuwa. Allah ya bashi nasibi kan gyaran takalma da kuma facinsu.

  Kasancewarshi babba cikin maza ƴan uwansa be bashi damar yin aure da wuri ba, duk kuwa da gorin da ake masa na ƙannansa duk sunyi aure har ma da yara biy-biyu Isuhule da Auwala. Badan komai ba sai dan yadda yake tunanin sana’arsa ba zata ɗaukeshi da iyalinsa ba amma a ransa yana son ya raya suna.

  Haka abokansa babu wanda be aure ba. Lokacin da ya riski dami a kala game da Labiba ba ƙaramin farin ciki ya yi ba, koba komai lokaci ya yi da shi ma zai raya gori. Ya kuma ci alwashin ko zata  yi hauka ba zai saketa ba. Musamman da ya ga gidan data fito.

  Ya godewa Allah da ya sa duk dabarar da ya haɗa babu wanda ya fuskanceshi ita Labiba na ɗaukar Khamis ne ya turoshi shi kuma Khamis na ɗauka Labiba ce ta aikoshi. Ko Jawwad sai ranar ɗaurin aure suka haɗu shi ma sama-sama kuma be wani tsaurara bincike ba da jin cewar Labiba ya aura. Hasalima shi ta kansa yake sakammakon kamuwa da cuta me karya karguwar jiki.

   Mahaifiyarsu Baba Harira mace ce me faɗan gaske, bata son raini. Tana sana’ar gasarar koko da wainar gero da safe. Da rana kuma tana taliyar hausa da manja da awara. Haka kuma tana sana ar saida mai da ƙuli-ƙuli. Tun suna yara sana’arta kenan.

  Baba Harira tafi kowa takaicin rashin auren Tukur, da kanta ta sha nema masa auren ƴaƴan abokanta sai ya doje. Hakan yasa ya daina zuwa gidama gaba ɗaya sai dai ya yi musu aike. Gidansu  Tukur babban gidane me wadatar ɗakuna, matan ƙannansa da ƴaƴansu duka a haɗe suke da mahaifiyarsu. Sai dai katanga da ke nuna ɓangaren wancan da wannan amma ƙofa ɗaya ce ta shiga gidan.

  Girki a cikin gidan ake basa raba tukunya, sai dai idan an gama Baba Harira ta rarraba. Idan kana san ganin fushin Baba Harira ka taɓa Mero auta, tabbas ranar zaka ga fushi da sababi dan haka surukanta suke shakarta kuma suna taka tsantsan da ita. Ƙiri-ƙiri mijinki zai siyo miki abu, koda ya bata nata ta taka ɗakinki ta ɗauki naki ta haɗa biyu. Idan kinyi magana ta ce yayanta ne ya siya kuma Baba ta goya mata baya.

Kwatsam Tukur ya zo mata da batun zai auro ƴar birni ya kawota nan, abin ya ɗaure mata kai amma bata hanashi ba a saninta ƴar birni da hankalinta bata zama a garin nan. Domin su kansu suna fatan yaransu in sun fita talla su samo na cikin gari su aura dan har murna ake zo ma uwa idan ƴarta ta samo ɗan cikin Sakwato.

  Amma ba a ƙwacewa yaro garma dan haka ta yi masa fatan alkhairi. Tun a wajen haɗa lefe suka soma haurawa, a cewarta ya tsawala amma sai ya nuna mata ƴar babban gida ce. Data turkeshi kan ina ya sami kuɗi be ɓoye mata komai ba amma ya nuna mata shi fa ba AUREN MANUFA zai yi ba in ya aureta ya aura kenan. Sossai ta goya masa baya, domin ta tsani masu yin irin auren da ya faɗa mata tana danganta hakan da yi wa ubangiji shisshigi a lamuransa.

A wajen fitarwa da Labiba sashi ma sai da suka haura, domin kaf surukanta ƙofarsu na ciki amma ya nuna mata na kwana biyu ne. Dan haka ƙofa biyu aka yi ɗaya tana cikin gida ɗaya na waje.

***

Washegari Baba Harira ta sa aka damawa ƴan kawo amarya koko, ya ji gasara ya yi kirtif ga kuma wainar gero da tasha ƙuli da man ƙuli ziryan aka yanka albasa akai. Sai aka ɗora musu farar alawa akai madadin sakari. Biredin da ya siyo musu kuwa ta rabawa jikokinta acewarta Labiba ta ja musu. Sai dai ga mamakinsu tsaf ƴan kai amarya suka lamushe waina da koko suna santi. Hakan ya ragewa Baba Harira haushin Labiba koba komai ta ci albarkacin danginta. Sai dai Labiba ƙirƙiri taƙi ci taƙi sha sai da Hajiya Mawwadah ta aika ango ya samo mata tea da biredi da ƙosai. Haka ta ci tana yatsina, su dai da ido suke binta suna ganin dole ta sauko.

Da zasu tafi har gida suka shiga suka yi wa Baba Harira godiya suka rabu kowa ransa wasai. Sai lokacin Labiba ta ƙara raina kanta. Kuka take wiwi tana riƙe Husnah ita ma Husnahr ƙwallar tausayinta take sharewa Yaya Amina kuwa ta kasa cewa komai. Da ƙyar da siɗin goshi suka ɓamɓare suka shiga motocin Ɗan saɓalo estate suka nufo cikin Sakwato.

  A mota gaba ɗaya sunyi ɗif suna jimamin wace rayuwa Labiba zata yi?

***

Lokacin da labari ya je kunnan Amne game da garin da aka kai Labiba kamar zata yi hauka. Tasa Khamis ta yi agaba ta dinga surfa masa zagi ta uwa ta uba. Abokan zamanta kuwa banda dariya babu abinda suke yi mata. Su Yaya Amina ne kaɗai masu tausarta hatta Hajiya Mawwadah ta kware mata baya. Khamis kansa ya shiga tashin hankali sai yanzu ya soma tunanin yadda auran ya kasance, yana tunanin duk da zaman ƙarantace ne amma wace rayuwa zata yi?

***

Labiba amarya kuwa, bayan tafiyar danginta ta fito ta zazzaga gidan, babu laifi kayanta sun haska gidan dan tana kallon yadda ƴan ƙauyen suke shasshafasu suna kallon fuskarsu a jikin mudubi.

Abu ɗaya ya burgeta da garin ba a cika ɗauka wuta ba. Koba komai ta samu ta cajin yin karatun novel da yin game. Sai da ta gama zaga gidan tsaf sannan ta lura da ƙofar da ta zamo mahaɗarsu. Jim ta yi kamar zata buɗe sai kuma ta ƙyale.

Da rana aka aiko Mairo ta kawo mata gero da wake, ƙerere ta tsaya mata aka kamar wata sa’arta bayan ta dire kwano. Bayanta kuma ƙawayenta ne da suke dafifin leƙa ɗakin Labiba suna kallon firij. Taƙaici ya kamata, ta tsaya kawai tana kallonsu kafin ta gama yanke abin yi Mairo ta buɗe firij ta rarraba musu pure water. Ta zarce ta ɗauki kwalbar turaren data gani gefan kujera.

   “Ina so!”

Ta furta cike da ko in kula, daga bisani ta ba wa abokanta umarnin su tafi. Fuu! Labiba ta miƙe ta bi bayansu. Janyo kwalar rigar Mairo ta yi tana huci,

  “Bani kayana!”

  “Na hana ai yayanmu ne ya siyo..”

  “Da kuɗin uwarki ya siy…”

Wani wawwan ihu Mairo ta tsalla, wanda ya janyo hankalin mutan gidan suka shiga rige-rigen nufo sashin. Kafin Labiba ta yi aune sun soma tuttuɗowa ta ƙofar da ta dinga tunanin ta me ce ce.

“Wallahi baki isa ki zagarmun Innarmu ba. Ƙarya nayi ba shi ya siya ba?”

  Ta faɗa tana cakumar wuyan Labiban wadda mamaki da takaici sun hanata kataɓus. Daidai ƙasawowar Baba Harira tana tambayar ba asi, caraf sai Mairo ta ƙara kukanta tana faɗin,

“Innarmu zaginki ta yi…”

“Zagi?”

Sauran matan suka haɗa baki wajen faɗa,

“ke kuma taki tarbiyar kenan daga zuwanki jiya?”

Wata ƴar tsamurmura ta faɗa, kafin su farga sai ga Tukur kamar anjehoshi.

“Lafiya Inna? Ke dalla malama sakar mata wuya!”

Ya faɗa yana watsawa Mairo harara. Da hanzari ta saketa. Matan kuwa da ɗai ɗaya suka soma zare jiki saboda sun san halinsa.

“Ke Ladiyo me ya faru..”

Mairo ta yi caraf,

“Innarmu amaryarka ta zaga..”

“ban tambayeki ba suda!”

Tiryan-tiryan Ladiyo ta faɗi gaskiyar abinda ya faru, duk da hararar da Mairo ta ke antaya mata. Juyowa ya yi tare da nunata da yatsa ya shiga watsa mata kashedi. Sum-sum ta ja tawagar ƙawayenta suka fita. Sai lokacin ya dubi Inna yana sassauta murya kansa a ƙasa,

“Dan Allah Inna kadda ki biye zancen yaran nan su hanaku zama lafiya. Labiba dai ƴar ki ce kamar ni…

“Dakata min Tukur ni ma a gabanta zamu yi magana da kai?”

  Ta faɗa tana tsattsareshi da idanu. Kai ya girgiza jiki a sanyyae baya san fitina ta soma tashi tsakaninsu, yasan Innarsa kuma ya san labarin Labiba tabbas ya kamata ya yi wani abu..Fuu! Ta juya ta nufi sashinta. Labiba ta bi su da idanu kawai tana jinjina lamarin.

***

Sati uku da kai Labiba ƙauyen geza, gaba ɗaya hankalinta ya tashi. Tukur ya rantse mata ya maya babu saki tsakaninsu. Kuma ya gayamata dalilinsa na auranta da hanyoyin da ya bi. A ranar ta kira Yayanta ta faɗa masa komai. Shi kansa ya girgiza amma babu yadda zai yi, in ya yi wani yunƙuri tabbas iyayansu zasu fahimci manufarsu ba kuma ya san ta ƙara wani laifin kan na baya. Dan haka hankali ya kwantar mata tare da nuna ta yi haƙuri kawai ta rungumi ƙaddara.

  Ɓangaren Amne ma dai hakane, amma zuciyarta na cike da danasani da takaicin yaudarar da aka yi musu.

Labiba fa ta shiga tsaka me wuya, da fari ta soma zuba rashin mutunci sai dai mutanan gidan suka nuna mata sun fita gogewa. Mairo kaɗai ta isheta ciwon kai. Haka zata jawo yara ta kunna kallo, ta ɗaura ƙanƙara ta saka a firij dinta wai ta saidawa idan kuma ta hana Baba Harira ta tsefet tsaf ta uwa ta uba.

   Ranar girkinta kuwa babu me taimaka mata, saboda ita ma bata taya kowa. Inda Allah ya taimaketa kwana biy-biyu ne zagayowar girki dan haka tana samun hutu na kwana huɗu. Tuwon dare sunayin kwano uku, saboda dumammen safe kuma shi za a kuma ci da rana wata rana sai dai idan muguntar Baba Harira bata tashi ba. Tukur ya so nuna mata gata ƙwarai amma mahaifiyarsa na hanawa, amma duk da haka yana yi a sace. Duk yadda taso ta yi masa rashin kunya tana shakkar mahaifiyarsa don bata ƙyalewa. Tun a satin farko da ta nuna masa ɗanyen kai ta yo waje kan karɓar haƙƙinsa ta gane wacece surukarta. Dan sunkutukum ta ɗauketa ta a kafaɗa ta maida ita ɗakin tare da saka kwaɗo ta yi tafiyarta.

  Da safe sai goma da rabi ta buɗeta, bayan tun asuba ta buɗewa ɗanta ɗaki. Lokacin data fito kuma ta sa facalolinta suka dinga yi mata dariya da habaici tana gudun miji. Tun daga lokacin ta kiyayi matar dan bata son raini. Ita kuma a duniya ta tsani ƙasƙanci. Yanzu gaba ɗaya tunaninta ya tafi ne kan yadda ɓale auran cikin ruwan sanyi.

Amma kuma Khamis ya tabbatar mata badai gidansa ba matuƙar ta kaso auranta. Wajen Amne kuma bata ga fuskar hakan ba. Babban takaicinta duk wasu kuɗi nata ta wasarairai da su. Kaya ta yi masu mugun tsada ga shi ta ƙare a ƙauye. Ko kayan kicin kuɗin da ta kashe suna da ya wa, da fari ta soma tunanin ta fitar da su ta siyar amma kuma tasan karya mata su za ayi. Duk wata kaddara tata ta rasa inda suka yi dan sai yanzu ta farga da cewa ta yi ɓarnar kuɗi ba kaɗan ba. Gidan da Yusuf yake ciki kawai ya rage mata sai tsirarun kuɗi wajen Khamis.Tun auransu da wata biyu ya fuskanci ta soma tu’amli da maganin hana ɗaukar ciki, da fari ya maida abin na marmari amma dag bisani sai ya fuskanci da gaske take bata buƙatar haɗa zuri’a da shi. Duk yadda ya fahimtar da ita hakan ta gaza fuskantarsa, hasalima dalilin hakan suka shafe sati uku suna gaba. Ƙwarai yana buƙatar haihuwa amma babu yadda zai yi ya turasasa Ramlatu. Da farko bambami ya soma, daga bisani ya ga ba ci ya koma lallashi. Ƙarshe dai tsada suka yi kan zai dinga biyanta dubu goma duk wata domin kadda ta sha maganin . Babu ja ya amince saboda haihuwar ce muradinsa a yanzu. Sun yi wannan yarjejeniya da wata ɗaya kwatsam safiyar yau yana shirin fita aiki Allah ya nuna masa kwalin maganin da ta sha ta bari kan mudubi. Ƙwarai ransa ya ɓaci har wani ɗaci ya ke ji. Kai tsaye fallo ya nufo yana ƙwalla mata kira.

Zaune take tana dana wayarta, bata amsa ba har ya  ƙaraso inda take. Wayar ya warce tare da wurgata kan kujera.

“Ni zaki munafunta Ramlatu, ba tsada muka yi dake ba?”

Ya furta yana kanga mata kwalin maganin a fuska. Ta razana amma da yake ƴar duniya ce sai ta maze. Jijjigata ya yi yana huci kamar mahaukacin kare. A zuciye ta ingijeshi, abinda da ƙarashen maye sai ya yi taga-taga zai faɗi ya cize. Wannan dmaar ta samu ta nufoshi da dukkan ƙumajinta. Masifa ta shiga surfa masa kamar ta ci babu duk da tana jin ɗar a ƙasan ranta. Ganin ya nufota kamar zai daketa ya sa ta gyara tsayuwarta. Yana ƙarasowa ta tattara duk wani ƙarfi nata ta cakumi kwalarsa.

Shaƙar data kaiwa wuyansa ita tafi komai bashi mamaki, zuciyarsa ta zo iya wuya. Ya ɗaga hannu zai kwaɗa mata mari, kamar wanda aka jonawa shocking sai ya janye. Ya yi wa kansa alƙawarin ba shi ba dukkan mace. Yana tuna silar rasuwar Zahidaht ya kan ji ya tsani kansa, tabbas ba zai sake wannan gangancin ba. Kallonsa ta yi sheƙeƙe,

“Wai Kabir da dukana zaka yi, to me ya hanaka ka dakeni?”

Shiru ya yi mata yana huci, ga hannuwanta _still_ a wuyansa ta gaza sakinsa. Jijjiga jiki ta soma yi,

“haihuwa ce da kai na ce ba yanzu ba,ka barni in yi sha’anin rayuwata. Ko zan haihu sai na mori ƙuruciyata ballantana kuma ni ba sakarya ba ce da zan yadda in haihu da mutum irinka. Wallahi ba zan haifi ‘ya’ya a dinga kawomunsu an bi su an ƙwaƙwaleba!”

Kamar saukar aradu ya ji shigar kalamanta, jikinsa ya yi mugun sanyi. Zuciyarsa ta matse da wani irin yanayi. Tabbas sai yanzu ya ke ƙara danasani da takaicin rayuwarsa ta baya, be taɓa hango abinda Ramlatu ta faɗa ba duk da yasan ta faɗa ne domin kare kanta. Murya a raunane ya furta,

“sakarmun wuya!”

Ita kanta ya bata tausayi ganin yadda kalamanta suka illatashi lokaci guda. Amma ƙasan ranta tana jin wannan shi ne makamin yaƙarsa ta huta kawai. In ya ga ba zai iya ba ya sauwaƙe mata. Wayarta ta ɗaga ta dana kira, ta bishi da idanu ganin ya dafa bango yana bi har ya kai ƙarshan fallon ya fice. Tsuka ta ja tare da furta,

“Adijee na gama da batun Man fa, na samo hanyar hukuntashi”

Daga can ɓangaren aka furta”ke fa kwalba ce wallahi”

Ba ta bata amsa ba, suka koma wata hirar da ban.+

***

Labiba ganin babu sarki sai Allah ya sa ta saki jikinta ta soma fuskantar rayuwar da ta riska. Ta karɓi duk wani sauyi da ta samu acikin rayuwarta illa abu biyu zuwa uku. Baba Harira dai tsakaninta da ita mutuntawa ce, haka ma facalolinta tuni ta taka musu birki kan izgilanci da suke yi mata kuma Tukur ya mara mata baya. Hakan ya sama mata sauƙi sossai. Tsakaninta da su gaisuwa sai in ta fito girki sun haɗu wanda babu wanda yake taimaka mata. Hakan kuwa ba ƙaramin naƙasu ya ja mata ba, duk ranar girkinta sai ta yi zazzaɓi sabida bata da mataimaki.

Mairo ma tuni ta dakatar da ita, duk masifarta da ta Baba Harira sun haƙura sun sa mata ido domin ta ƙeƙashe ƙasa ta hana Mairo ɗaukar mata ko tsinke. Idan sun yi magana amsarsu ita ce guminta ne bana ɗan uwansu ba. Jin hakan ya kan sa guiwoyin Baba Harira yin sanyi domin tana gudin asan AUREN MANUFA ɗanta ya yi a saka shi a bakin duniya. Dan ta lura ƙwarai Labiban tere take san yi musu. Wnda tana da yaƙinin matuƙar ƙaddara ta ratso ya saki Labiban babu me bashi auren ɗiya a garin dan haka suka shafa mata lafiya.

Babbar damuwarta yanzu shi ne muguwar kazantar Tukur, tun lokacin da ta yi karatun ta nutsu kan rayuwarta ta baya ta fuskancu ƙazanta da wasu ɗabi’unta suka ja mata barin gidan Yusuf ta ɗauki ɗamarar gyara kuskuranta. Komai nata tsaf yake abin sha’awa. Sai dai ga Tukur abin ba haka bane. Tukur cikakken ƙazami ne na bugawa a jarida. Ya kan shafe kwana biyar be yi wanka be yi brush ba. Hakan yasa haƙoransa suke yalaye shar da su babu kyan gani. Har mamaki take yi me yasa bata kula da duk wannan ba KAFIN AURE amma ƙaddara ta tiga fata. Kaya kuwa sai ya yi sati yana maimaita saka m

su kuma ya zo ya cusa mata cikin kwaba, kusa da wankaku su yi ta tashin tsami. Fason ƙafarsa kuwa kullum cikin janye mata zanin gado yake yi. Ta yi masifar ta yi lalashin ya kan rage akan da amma har lokacin be gamsheta ba.

***

Yusuf kam sai sambarka, arziki ya ninka na da. Allah ya sa masa albarka, bayan gidan youghurt da ya buɗe yanzu yana da wajen kiwon kaji da kuma raguna. Shi kansa har mamaki yake yi. Haka kuma be yi ƙasa a guiwa ba wajen tallawa dangi da ƴan uwa. Kowa nasane be ware ba, hidimar abinci da sutura duka ya ɗaukewa mahaifansa. Su Khamis duk sai suka raina kansu, ɗaga kai da ɗagawar da sukewa dangi sai ta tashi a babu. Babu wanda zai buɗe baki be kira mutuntakar Yusuf a dangi ba. Ya zamo wani tauraro me haskawa. Matarsa kuwa ta zamo abar kwatance domin ita take ƙara goya masa baya kan dukkan hidimar danginsa. Da jiki da zuciyarta tana tare da shi. A yanzu haka tana ɗauke da ciki wanda suke sa ran haihuwarsa yau ko gobe. Duk wata siyayya ya gamata. Wasu lokutan tasa kayan babyn yake a gaba yana kallo, wani lokacin ya yi kuka wani lokacin ya yi dariya. Yana tuna ɗiban albarkar Labiba a lokutan haihuwarta da bashi da karfin siyan komai.

***

Da gudu yaran suka shigo, tana zaune ta miƙe ƙafa saboda nauyin da cikinta ya yi mata tana dubansu. Murmushi ya suɓuce mata ganin yadda suke zaga fallon suna dariya. Da alama Khalifa na san karɓar teddyn ɗin hannun Ummi ne. Daidai lokacin mahaifinsu ya yi sallama bayansa yaya Amina ce da nata yaran. Da gudu Ummi ta tafi ta rungumeshi,

“Abba ka ga Khalifan Mommah ko”

“A’a fa ɗiyar Abba ke kika taɓamun yarona”

Cewar Shukura tana murmushi, ƙarasawa suka yi gaba ɗayansu ta yunƙura tana gaishe da yaya Amina. Faɗa ta soma yi mata kan mene zata takura kanta ta ce sai ta sunkuya bayan ta yi nauyi. A kunyace ta ɗauke kai tana murmushi, ita ma murmushin ta yi ƙwarai halin yarinyar na burgeta. Sai yanzu ta sake gasgata cewar Yusuf ya yi mata.

Hirar zumunci suka shiga yi, Shukura ta miƙe ta kawo mata abin motsa baki sannan ta basu guri su gana da ɗan uwanta bayan ta yi dabarar janye yaran. Wannan ɗabi’a tata ta ƙara mata ƙima a idanun dangi da yawa. Duk yadda kuka saba da ita matuƙar ta kula wajen Yuauf suka zo to kuwa zata basu waje su yi uzurinsu. Musamman yanzu da ya kasance Yusuf ɗin ya zama babban ƙarami a cikinsu. Buɗi da wadata sai ƙaruwa suke yi a harkokinsa. Mutane da ya wa na ganin shi ya maye gurbin mahaifin Labiba acikin zuri’arsu saboda yadda harkokin kuɗi suke zuwar masa da nasara.

Amne kanta ta shiga nadama da danasani, duk wata hidima ta gidan shi ne kama daga kan cimma zuwa sutura. Sau tari idan aka shiga taro har shaguɓe ake yi mata cewar ɗiyarta me ƙashin tsiya ce gashi nan daga rabuwarsu Yusuf ya zama wani abu. Ira-iran wannan kalaman kansa mata jin ƙyamar shiga dangi, sossai take dana sanin raba Labiba da gidan auranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *