ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 6 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

tsawon shekarun da suka gabata, kuma naji dadin damar da na samu na bayyana miki komai, domin Abban ki bai son ana tuna masa baya, hakan yasa baya son a fada miki duk abin da ya faru.
Shi yasa ko hotunan Aziza bai bari an aje su inda za ki gani ba bare har ki yi tunanin kina da wata ‘yar uwa, duk don gudun kada ya saki damuwa domin a duniyar nan bai son abin da zai daga miki hankali, hakan yasa duk yadda zai yi sai ya ga abin da kike so shi zai yi miki, yana

KoKarin ganin ya baki dukkan farin ciki don yana ganin nishadinki. Tsananin son da ya yiwa ‘yar uwarki shi ne ya hade shi biyu yake miki shi mai tarin yawa. *
‘Don haka zan dauko hotunan na baya ki gani don ki Kara tabbatar da irin kamannin an Boye komai don kada ki gani ki tuna baya ki tashi hankalin ki, wai ya bari sai kin yi aure kin haihu, lokacin kin girma kin yi hankali shi ne zai sanar da ke komai”.Murmushi Haana tayi ta ce, “Abba na kenan, (he is the best father) shi kullum haka yake ganin bani girma ba”. Granny ta mike taje ta bude dan wani Karamin (box) daga

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG ganinsa ka ga tsohon akwati da aka jima ba a taba shi ba, nan ta dauka ta zo gaban Haana ta zauna ta bude matsakaicin (box) din nan, sai ga wasu tarin hotuna dadaddu. Hotunan da Haana ta gani ya yi mugun daga mata hankali da mamaki, domin tsananin kamar da ta gani suna yi da ta jikin hoton, don ganin kayan da suke jikinta ta tabbata bata da su ba don haka ba cewa zata yi ita ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
_Da sauri ta karbi hoton ta“ce, “Granny wannan ita ce Ya Aziza na kamar (photo copy) na?” Daga mata kai tayi cikin sanyi jiki, nan da nan hawaye suka zo ma Haana da sauri ta runtse idanu ta sumbaci hoton, tace. “Allah Sarki Ya Aziza na, Allah Ya jiKanki, Ya kai rahama kabarinki, ‘har yanzu ina jin kewar ki a raina ‘Haka ta rungume hoton tana kuka KasaKasa mai tsuma rai, Granny ta dafa ta, tace, “Raihana ban baki labarin nan don na daga miki hankali ba, na fada-miki ne don ki taimaka min ko zan samu cikon burina don kullum addu’a ta Allah Ya hada Zuri’a dinmu guri DAYA kamar yadda muka faro a baya, don haka ki share hawayen ki, ki daina kuka’. Nan take ta share hawayen, ta Kirkiro murmushin, Karfi da yaji don itama bata san ta bawa Granny damuwa kamar yadda itama bata son ganinta cikin damuwa, ta ce.
(Okay my sweet Granny) na daina, bani sauran hotunan na gani”.Nan ta sake miKa mata wani hoton, ta ce, “Wannan shi ne Yayanki Hameed”.
Da sauri ta karbi hoton tana gani cikin murmushin yake, kallon sosai tayi masa dan gaye da shi na wancan lokacin nasu. Nan take taji tausayin sa da Kaunar sa, don gashi nan kyakkyawa da shi.
‘ Allah Sarki Ya Hameed, Allah Ya jikanka Ya yi muku rahama, Ya yafe muku dukkan laifin. ku. Nayi muku alKawarin saka ku cikin addu’a na na sallah kullum, Allah Ya yafe muku, Yasa kuna cikin aljannar Firdausi kai da Ya Aziza na” Nan take wasu hawaye suka zubo mata, tayi sauri ta goge su. Nan Granny ta sake nuna mata wani (picture family) gasu nan Kwansu da kwarkwatar su WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Haana tayi saurin zaro idanu, ta ce, “Granny wadannan duk family dinmu ne da gaske? Daya bayan daya tayi mata bayanin su har da yaransu da suke jikin hotunan. Tsananin doki da murna da Kaguwar son danginta nan take ji duk tana Kaunar su, ta so ganin sun kasance a cikin su.
Lokaci guda kuma jikinta ya yi sanyi da ta tuna irin yadda suka rabu da iyayenta, tabbas sun yi musu wulaKanci na Kin Karawa. Nan take taji haushin su ya kamata, ta yi sauri ta ajje hoton, sai dai ta dauki na Aziza da Hameed ta rike a gurinta.
“Granny ki dauki hotunan nan ki boye, amma ki bar min wannan a gurina, bana son ganin wadannan.
Maganar gaskiya (family) din Abba basu yi masa adalci ba, ganin tarin yawansu ya sa naji haushin su tunda ba sa son Abbana to nima bana – son su, Ya Hameed kadai nake so kuma zan yi ta masa addu’a Allah Ya yafe masa abin da ya yi a ~ rayuwar sa, don haka ki bar min wannan hoton a gurina”. Tana sake duban hotunan, nan take hawaye suka zubo mata. .
Da sauri Granny ta mika mata hannu, ta ce, “Raihana bani hoton nan kada ya zamo abin da zai ke daga miki hankali, don da na san haka za kiyi min da ban fada miki komai ba a game da abin da kike son ji”.
. Da sauri ta ce, “(Please) Granny wallahi babu abin da zai faru, kuma naji dadi da ki ka sanar dani komai, a yanzu ban huce da (family) din Abba ba, amma nan gaba ban sani ba ko zan huce. Kuma nayi miki alKawarin babu abin da zai faru dani game da damuwar da ki ke tunani zan shiga.
Kuma ba zan fadawa Abba komai ba, ki bari na huce zan ga abin da zan yi miki na ‘burinki (for now) na tsani (family) din Abba tunda suka yi masa haka, idan kinga na yafe musu to Abba ma ya yafe musu”.
“Shi kenan, babu laifi Raihana, kije ina jiran ran da za ki huce domin nasan kinsa buri na, na tabba ba zaki barni cikin saurare ba. Idan -kuma har Allah Ya dawo min da Abba lafiya nasan shima zai yi wani abu akai, domin ya san abin da nake so”.To Granny mu WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG bari naga zuwa Ya Abban, zai yi tunanin zuciyata tayi sanyi domin duk mai Kin Abba na ba zan so shi ba ko ma wane”. “Raihana tuni Abban ki ya manta da rayuwar ‘yan uwansa, ya manta da cewa yana da wasu dangi da suka guje shi, tunda Allah Yasa ya samu wasu suka dawo gurinmu ya saki ransa ya basu dukkan Kaunar da zai bawa wadancan, yana samun duk abin da wadancan za su bashi, hakan ya janyo baya wani tunanin su ko son jin labarin su tunda ya manta da su har yau babu wanda ya Kara yi masa maganar su, ko ni da da nake masa ‘don nice amma ina ganin irin damuwar da yake shiga shi yasa na daina domin .ina son ganin farin cikin sa. Sai dai ni kuma bani da wani buri da ya wuce naga an yafi juna an dawo gun guda kamar da, wannan shi ne burina nake kuma fatan ganin ya kasance kafin na bar fadin duniyar nan”. Tana gama fadin haka nan take hawaye . suka zo mata. Nan da nan hankalin Haana ya tashi, da sauri ta dawo ta duka gabanta domin Allah ne kadai Yasan irin tsananin so da shaKuwar da suka yi da Granny dinta. . Saka hannu tayi tana goge mata hawayen tana cewa. “Granny na don Allah ki daina saka wa kanki damuwa, ki kwantar da hankalin ki, duk ban san damuwar ki da son ZURI’A dinmu ya kai haka ba, tunda haka ne nayi miki alKawarin zan yi iya KoKari na naga mun cika miki burinki, amma mu jira Ya Abba na ya dawo shima ki haska masa mu ji shime zaice”” take farin ciki ya kama ta, ta‘ce, “Na ° gode sosai Raihana tashi kije abinki, Allah Ya – nuna mana lokacin. Jin _wannan furicin, naki sai naji komai ya yaye na bakin ciki cikin zuciyata”. ..
Wannan shi ne labarin yadda ZURI’A DAYA ta_ dare ta zamo biyu tsawon shekaru ‘ babu wani da yake da labarin dan uwansa. Burin Granny shi ne Allah Ya bata ikon samun mataimaka da zata samu su dawo da zumuncin da ya shude ba a yi. Alh. Mustapha Allah Ya azurta shi fiye da tunanin mutum, arziKin sa na yanzu sai dai godiyar Allah. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
. Tun bayan rasuwar Aziza ya. dauki son – duniya ya dora shi kan Haana, tsawon shekaru basu sake haihuwa ba sai daga baya Allah Ya basu haihuwar ‘ya’ya har hudu, Aziza, Imran, isham sai auta Nur. Amma duk tarin su babu wadda ta kai matsayin Haana a gurin mahaifinsu, domin yana matuKar Kaunar diyarsa fiye da komai, domin ita ce farin cikinsa duk abinda take so shi ne yake so. Tsananin saka ido ido akan tarbiyyar _da yake-bata yasa ta zamo nutsatstsiya da kamun kanta, haka kowa yake ji da ita tamkar tsoka daya a miya, musamman yayanta Abba da yake matuKar ji da ita a duniyar nan. Tsananin shakuwa da Kaunar da suka taso suna yiwa junan su tun suna yara, domin Ya Abba shi ne komai dinta, itama bata da wani burin. da ya wuce ta sa yayan nata farin ciki kamar yadda kullum take ganin yana sa ta tunda ta taso daga rayuwar ta bata taba ganin ranar da Ya Abbanta ya yi fushi da ita ba. Tsananin shaKuwar su da sabon su ya-yi mugun tasiri a cikin zuciyoyin su, domin Haana  bata iya yin komai da kanta matuKar Ya Abba yana nan, tun tana Karama har ta fara girma. –
A lokacin da ya fice karatu can waje ta shiga muguwar damuwa har da kwanciya gadon asibiti, Allah dai Ya taimaka ta warware. .
Kowa yana farin ciki da yadda yaran suka ta so da wannan zumuncin, ta hakan ne Allah Ya saka Kaunar Ya Abba a zuciyar Alh. Mustapha . mai tsanani, yadda yake Kaunar diyar sa tilo gashi kuma dama dan Kanwarsa ne da tayi masa takwara. Tun wancan lokacin ya dauke shi ya zamo tamkar shi ne mahaifinsa har kawo yanzu, idan. mutum bai sani ba babu wanda zai ce ba dan da ya haifa da cikinsa bane.
Domin haka suka hada kansu suka zamar da junansu babu wani bambanci tsakanin yaran .., su, don kawai ba sa son tuna wani abu da ya faru baya. Dan Fillo Estate yanzu ya yi suna a cikin garin Kano, domin estate ne mai dauke da ZURI’A DAYA, duk kuwa WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG girman da yake da shi duk yawan gidajen na ZURI’A daya ne, domin sai da Alh. Mustapha ya raya estate din da danginsa na uwa da na wajen uba, domin duk
wani abu da yake nema na farin ciki Allah Ya taimake shi Ya bashi, kuma Yana farin ciki ga yadda ya samu ya hada wata ZURI’A da suke matuKar Kaunar sa da girmama shi, ta hakan ne ya dauke kansa ga su, domin su ma wadanda yake tare da su a yanzu duk jini daya suke, don haka sai yake ganin kamar bai rasakomaiba, Babban burin sa dai a yanzu shi ne ya matsu da Alh. Mukhtar ya bar zaman Kasar wajen nan ya dawo gida da zama shi da iyalansa, domin yana buKatar sa a kusa da shi. Kullum maganar sa akan shi ya daure ya dawo gida su. zauna guri daya, haka shima kullum zai ke cewa yana nan kan hanya.

**************

Tsanan cincirindo na = yawaitar abubuwan hawa da suka hada gagarumin (goslow) a bakin gate din shahararriyar jami’ar Bayero University Kano (B.U.K) dake Kano. sakamakon wani mai Karamar mota da ta sha jiki ya bugawa wata matashiyar budurwa cikin .sabuwar motarta fil a cikin leda, kuma ya yi mata bara. Tsabar takaici da jin Karar yadda ya buga mata motar yasa ta kasa fitowa don bata san me zata iya cewa ba, kashe titin da tayi shi ne ya janyo wannan tashin gwauron zabin (go-slow) da ake. Ban da Karar (horn) babu abin da kake ji, ita bata yi gaba ba shi kuma wanda ya yi laifin yaki fitowa daga cikin tashi-motar don yaje ya bata haKuri. Motar Kirar Peogoat ce C350 ash colour, sabuwa fil da ita sai daukar ido take. Cikin mutanen da suka matsu suna gaggawa nan take suka shiga Korafi ganin babu – mai motsi cikin su, kai tsaye wasu suka nufi bakin motar tata, nan suka fara mata ihu da hayaniyar ta kauce ta basu guri idan bata da abin yi susuna da shi. Kashe motar tayi daga (slow) din da take, ta bude Kofar motar ta fito.
Kyakkyawar matashiyar budurwa ce ajin farko, jajir da ita kamar ta hada jini da jinsin

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *