ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
ba kowa bane illa abokin fadanta a bakin (gate), mutumin da ya buga mata motar ta ne. Bude baki tayi domin nuna tsananin ~ mamakinta da ganinsa, ashe dama shi ne malamin nasu da ake fada ne? Yau ta shiga uku, ya zata yi da tarin tsaurin idanun da tsiwar da tayi masa dazu?” Shima kallon nata ya yi mai cike da mamaki, to amma sai ya Boye ya nuna kamar bai ganeta ba. Shiru (lecture hall) din ya yi sannan ya yi gyaran murya, ya shiga ya yi dan dube-duben sa cikin I-pad dinsa, sannan ya ce.
“Salam alaikum (class)”.
Duk aka amsa cikin sakin” fuska, sannan – ya soma da cewa. .”Don Allah ina neman afuwar ku na rashin zuwa na da wuri, wata ‘yar tangarda na samu hakan ya janyo na makara”.Nan take aka amsa da, “Babu matsala Sir”. Amma ban da Haana, domin duk jikinta. ya yi sanyi don bata san da wane ido zata iya dubansa ba, domin zai yi tunanin bata da kirki, ya zata sam bata da tarbiyya kamar yadda wannan (student) din ya fada. Lallai tunda take bata taba fadawa cikin wannan jin kunyar ba, to ita kuwa da wanne ido zata iya zuwa ta bashi haKurin tarin laifin da tayi masa? Domin tayi masa furuci masu zafi kuma. tabbas tasan bai ji dadin su ba, to yau ta ga ta
kanta, da wanne ido zata iya zuwa gurinsa don bashi hakuri? Zungurar da Zahra tayi mata shi ne ya dawo da ita daga zangon tunanin da ta tsunduma, sam bata san ya fara (lecture) din ba. ‘ Tana daga idanunta sai suka sake hadawa a tare, nan ya ci gaba da bayaninsa amma kai da ganin irin kallon da yake mata kasan na tuhuma ne Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta bude baki da niyyar zata yi ma Zahra magana sai ta ga idanunsa akanta, sai ta dake ta fasa ta shiga duban wani guri daban, nan ya dauke hankalinsa daga kanta ya ci gaba da bayanin sa.
Cikin murya Kasa-Kasa ta fada ma Zahra cewa shi ne mutumin da take basu labarin ya buga mata mota, cikin sauri Zahra tayo waje da idanunta don mamaki, yana juyowa suka yi sauri suka basar. Ya jima yana kallon su babu wadda ta daga kai ta kalle shi, shima basarwa ya yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Can dai ya dinga jin tashin surutu KasaKasa, wannan karon yana juyowa ya hangi Haana ce take masa surutu kuma ya tabbata labarin sa take bawa Kawarta don ya fuskanci har yanzu fuskarta na dauke da mamakin ganinsa a matsayin malamin su.
Tsayawa ya yi tsak da yin bayanin, cikin daurewar fuska ya ce.. . “Ke, zo ki fitar min daga aji, domin hakan ya nuna min cewa jiya ba ki yi (attending lecture) dina ba, maza zo ki bace min, za ki raba min aji gida biyu”, Gabanta ne ya fadi, daga idanunta ta yi taga ita yake kallo, dama ta sani da wuya idan bai koreta ba, Mikewa tayi ta fara daukar jakarta, haka itama Zahra ta mike a zaton fa su biyu ya kora tunda da ita suke maganar. Ke kuma ina za ki? Ko kema kin gaji da sauraren (lecture) din za ki fita?”
Zahra ta gane da ita, yake, sai ta koma ta zauna ba tare da ta ce da shi komai ba.
Gaba daya Haana taji wani iri ganin yadda duk idanun mutane ya yi kanta, duk suka. yi mata ca. Karfin hali tayi ta ce, “Sorry Sir”. Out of my class!”. Ya fada cikin daga_ -.. murya.
Nan da nan ta dan razana don bata soma jure irin wannan tsawar ba, domin abin da yasa take tsanar mutum shi ne ya yi mata tsawa. –
Ranta ya yi mugun baci, ta suri jakarta ta taho zata wuce, tana zuwa gabansa ya ce. “Kowa ya yagi takarda ya rubuta sunansa – da (number) dinsa na bashi (five mark) maki — biyar”.Www.bankinhausanovels.com.ng
Bata tsaya ta ji abinda zai Karasa fada ba . cikin fushi tayi sauri ta fice cikin bacin rai, cikin ranta ta ce. “Tabbas mutumin nan ya yi haka ne don ya rama abin da nayi masa, ko don ya cusa min haushi. To maganar gaskiya ya yi nasara akaina, domin kuwa na ji haushi sosai, domin lokaci guda ayi rabon maki babu ni a ciki. Maki biyar fa? To gaskiya malamin nan bashi da tausayi da mutunci, amma dai duk tsiyar sa sai nayi duk – yadda zan yi naga ban fadi (course) dinsa ba, sai idan muguntar zai ci gaba da nuna min”.
. Cikin 6acin rai ta Karasa gurin da suke zaunawa idan basu da (lecture) duk abin duniya ya yi mata yawa, ta tuna irin baccin da take yi mai dadi amma don kada tayi (missing lecture) dinsa haka ta katse ta taho. Da tasan haka ‘ne zai – faru da ita da bata shigo (school) din ba. Haka ta zauna tana ta zancen Zuci. – Sama da awa guda da wani abu tayi a wajen tana jiran fitowar su Zahra, tana zaune a gurin ya zo ya wuce ta gabanta ya yi kamar bai ganta ba. ,.
Itama din ta hango fitowar sa, tana ganinsa ta wani-share ta shiga danne-dannen wayar ta, bayan ya dan wuce ta kadan ta dan saki wani tsaki.
Da har ya yi kamar zai tsaya sai kuma ya. fasa don sarai yaji tsakin da tayi, ita kuwa dama da biyu tayi don yaji ko zai tanka maka, amma a banza don ko waiwayawa bai yi ba, sai tayi tunanin bai ji ta ba.
Zahra Kabir ce ta hango ta a gurin da suke zama ita da Salma da Kulthums, suka yi sauri suka Karaso gurinta, rai Bace suka same ta a zaune. ‘
Salma Harun ta ce, “Haana kinga irin baudadden halin mutumin namu ko? Ai bayan fitar ki ya kori mutane ba adadi”.
Tsgaki ta saki ta ce, “Bar min mutumin nan dai, rainin hankali ne, dama nasan sai ya yi min haka. Ni wallahi naji na fara tsanar sa cikin rai na, tsana mai zafi ma kuwa”. Haana ba a haka, ki dai yi hakuri, a hankali komai zai wuce don sai mu hadu muje
mu bashi hakuri tunda dai komai cikin rashin, sani aka yi”. Zahra ta fada. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan take jikin Haana ya yi sanyi, ta ce, ,’ “Kuma fa gaskiya ne Zahra, don ko kadan ban – zata cewa shi ne (lecturer) dinmu ba”. “Gaskiya Haana nima nayi mamakin da ki ka fada mana cewa kin yi masa rashin kunya, abin da ba halinki ba sai gashi yau kin aikata”. Kulthum ta fada tana mai kallon Haana.. Haana ta yi ajiyar zuciya, sannan ta ce,
“Gaskiya ne nima sai yanzu nake tunanin abin da nayi masa ban kyauta ba, to amma Bacin rai ne ya janyo nayi masa haka, duk kuma akan kada na rasa (class) dinsa ne”.
Zahra ta ce, “Ku mu tashi yanzu muje (office) mu hadu mu bashi hakuri, sannan mu nuna kin yi kuskure, ina ganin zai haKura, daga can sai ki karbi (key) din motarki ki ce kin ~ hakura ba sai ya gyara miki ba”.
-Murmushi Haana tayi ta murda hannunta ya yi das! Ta ce. “Zahra, (nice idea) ku tashi muje”
Su hudu suka rankayo zuwa (office) dinsa don Haana bata ma san sunansa ba bare (office) dinsa, tun jiya ya yi bayani da komai nashi. Suna tafiya Haana ta ce, “Ku tsaya, meye sunan sa tukunna? Ko kuma ba ku nike ba?” Salma ta ce, “Na rike, sunan sa M.J Naseer”, “(Okay) muje, amma fa tare zamu shiga da ku don ba zan shiga ni kadai ba, to me zan fara cewa da shi idan naje?”Tsaki Zahra tayi, ta ce, “Ki tuna lokacin da ki ka yi matsa tsiwa me ki ka ce masa? Don haka idan mun je da kanki za ki san abin da za ki fada masa, bakin da ya yi rashin kunya da kansa zai san abin da zai sake fada na hakuri don ya fanshi kansa”.
“To masifatu naji, muje nasan me zan ce da shi”.
– Dariya Salma da Kulthum sukai musu, haka suka tankayo zuwa (office) din nasa, suna zuwa (office) din suka iske jama’a sosai a ciki wannan yana shiga wannan yana fita. Sun kai kusan minti sha biyar suna jiran ya gama da wadanda suke ciki,
Suna shiga yana ganin su hudu ya daure fuska kamar bai taba yin fara’a ba.Barka dai Sir”. Haana ta fada bakinta yana rawa. Daka mata tsawa ya yi, ya ce, “Ke fice min daga (office), me ki ka zo yi min? Ko kin zo ki Kara yi min wata rashin kunyar ne tunda ke din ishasshiya ce?” Ta bude baki da niyyar sake yin magana ya ce. (I say get out of my office)”. Sannan ya kai duba ga su Zahra, yace. . “(And you) me yake tafe da ku?” Zahra ta ce, “Tare muke dukkan mu”.
“(Okay) to ku fice dukkan ku, ban son ganin Kurar ku gaba daya”. Rai bace Haana ta baro (office) din, su kuma suka biyo ta a baya. . Www.bankinhausanovels.com.ng
Zaune suka suna tattauna yadda za ayi a — sake zuwa bashi haKuri idan ya huce, Haana tana jinsu don da bata yi niyyar sanya musu baki ba, sai da suke tambayar ta anjima zata zo su koma kan sannan ya huce. ‘
Hararar Zahr tayi, te ce, “Wa kike tunanin _Zai sake kula wannan dan girman kan? Wallahi Malami na ne amma tunda ya fara nuna min shi dan zafin kai ne nima zan nuna masa, ba dai batun mota zan je na bashi haKuri akanta ba? To – ya je ya riKe shi ne matsiyaci, da naje na bashi_ __ hakuri ya Kara wulaKanta ni gwara naje gida na ce na ajje motar an sace ta”, Zahra ta bude baki ta ce, “Haana yaushe kike son canza halayyar ki lokaci guda bayan idan anyi shari’a kema kina da naki laifin me yawa shi ne zaki.dinga yin irin wannan furucin? Gaskiya bai dace dake ba”. “Zahra kin san tun ba yau ba maganar gaskiya bani da raini ko wulaKanci,; amma akan wannan mutumin zan fara, don yana malamina bai isa ya wulaKanta ni ba, don sai na haKura da (class) dinsa (next year) na zo nayi (carry over)”.
Salma riKe bakita ce, “Ya Salam! Haana lallai kin dau zafi amma ai duk abin bai kai na fushi haka ba, ki dai yi haKuri domin babu wani riba idan tsama ta hada ku da malamin ki”.
“(No) Salma, mutumin ne akwai zafi kina jin yadda yake yi min tsawa don ni bana so, ina jin tsoron tsawa da yawa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haana hakuri za ki yi a dai rabu lafiya da shi, shima dai bai kyauta ba da ya tsaya ya karbi uzurinmu”. Cewar Kulthum.
. Ta bude baki da niyyar cewa wani abu, kawai sai-ta ga mutum ya nufo gurin su, shiru tayi tana kallon sa, suma sai suka juya suna kallon abin da ya hana ta fadin abin da zata ce. * ” Suna juyowa sai ‘Suka ga Mal. M.J ya nufo ‘ gurin su, duk sai suka nutsu. Sallama ya yi musu duk suka amsa cikin’ sakin fuska, sama-sama ya ce. , “Hajiya mai mota ki jira ni zan je a gyara miki motar ki, to amma Karfe nawa za ki gama _ . (lecture)?” .Duk mamaki ya kama su ganin yadda ya sakko lokaci guda, nan suka kalli junansu, Zahra ta yi sauri ta ce.”Sir biyar za mu gama komai”. Murmushi ya yi ya ce, “(Okay) to lokacin kan sannan na dawo, idan kin gama kije wajen
za kiga motar, idan ba ki gani ba ki dan Kara min minti biyar zan zo na kawo miki”.
Baki ta bude da niyyar zata yi magana, ya daga mata hannu yace.
“Bana son ki ce komaike da kanki ki ka ce na gyara miki kuma zan gyara”.
Yana gama fadin haka ya sa kai ya bar wajen.
Gaba dayan su abin mamaki ya basu, kowa ya rasa bakin magana ganin yadda lokaci guda ya juye kamar ba shi ne yake musu tsawa dazuba.
Nan take kunyar abin da tayi masa ya kamata, nan kowa ya shiga yabawa da saukin — kansa, domin yadda suka zace shi ashe ba haka yake ba. Ita kanta Haana nan take kunyar duk irin furucin da tayi duk ya kamata.”
_ Sun jima suna mamakin labarin, nan suka tabbatar da cewa al’amarin Malam M.J mai wuyar ganewa ne, sun jima suna hira daga nan suka tashi suka koma (class) don yin (lecture) dinsu na gaba.
Sun gama komai misalin biyu Salma da Kulthum tare suka fice, suna fitowa domin suna –
da wani uzuri, Zahra ta jira Haana akan cewa su «dan jira kadan sai su Karasa bakin (gate) din ko Malam M.J din ya dawo. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna cikin jira aka bugoma Zahra waya a gida idan ta gama abin da take ita suke jira, dama sun yi za su fita da Ummansu.
“Haana Umma ta kira ni, to yanzu ya za ayi? Ko mu Karasa bakin (gate) ko ya zo mu yake jira? Don kin san ba shi da wayar mu bare ya kira ya ce mana mu zo ya dawo”.
“Gaskiya ne kuma, mu Karasa kada na fara yin wani laifin da ba nawa ba ya ce na shanya shi, don ni na kasa gane kalar sa wallahi”.
Haka suka Karaso suna zuwa ba su ga kowa a gurin ba-sai iya motar sa kawai da wani mutum a tsaye kamar mai gadin motar, Haana ce tace. Www.bankinhausanovels.com.ng
” – “Zahra ga dai “‘motarsa can*muje ma tambayi wancan mutumin ko ina ya shiga”. “.“ Kashe motar ‘suka yi suka nufo’ “shi, sallama suka yi masa ya amsa nan suka tambaye – shi ina mai motar don Allah? Nan ya basu amsa ~ da cewa.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG