YAR NAJERIYA CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAR NAJERIYA CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR 

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

A duka kwanakin da suka biyo baya da Hasna’u yake kwana yake tashi a ran sa. Don haka bayan kwana uku da zuwan Hasna’u clinic ya bi kwatancen da ta yi masa ya shiga cikin garin Kachako. Karo na farko da ya taba shiga garin tun fara service din sa. Gwamnatin Tarayyah ta turo shi asibitin ‘Unity College Kachako’ domin hidimtawa kasa, a matsayin sa na wanda ya karanci MBBS.+

Da tambaya da kwatance kuma dama aka ce zabiya baya taba buya a cikin mutane, musamman a karamin gari kamar Kachako, don haka bai sha wahala ba ya gano gidan Kawu Sama’ila.

Ya sauka daga kan machine din okada da ya kawo shi ya taka zuwa kofar gidan sannu a hankali, abinda ya dau hankalin sa shine cincinrindon mutane kamar ana daurin aure, sai da ya lura kuma ya gane fuskokin su duka babu walwala kuma kowa alwala yake yi, alhalin ba lokacin kowacce sallahr farilla bane, ba jimawa kuma kafin ya yanke shawarar abin yi ya ga an fito da gawa cikin makara an fara daidaita sahu.1

A matsayin san a musulmi sai ya ambaci “innalillahi wainna ilaihi rajioun” duk da bai san waye ya rasu ba, ya kuma bi sahu don dama da alwallar sa, akayi sallahr jana’izar tare da shi. Koda aka idar kowa ya wuce makabarta banda wani dattijo da ya zauna akan kututturen iccen darbejiyar kofar gidan. Sai ya karasa gare shi yayi masa sallama.

“Sannu samari, daga ina? Wa kake nema?” Dattijon ya tambaya cikin mutumtawa.

“Na zo neman gidan su Hasna’u-Zabiya, wadda take makarantar kwana”.

Dattijon sai ya dube shi da dukkan alhini ya ce “nan ne gidan, bari maigidan ya dawo sun tafi makabarta kana gani” “Allah ya jikan musulmi Allah ya bada hakuri, ai ba wurin sa na zo ba, na zo ne wajen Babar Hasna’u in isar mata da sakon diyar ta, ni likitan su ne na makaranta”.

Dattijo sai ya ce “Allah sarki dan nan, Allah sarki Hasna’u – Zabiya. Da rabon bazaku gana da Inna Zulai ba, ita aka tafi kaiwa makwanci, yau watannin ta biyu kenan a kwance tana jinya sai yau Allah ya hutar da ita”.1

Saheeb sai ya durkushe a wurin yana fadin “Innalillahi wainna ilaihi rajioun”. Ya nemi waje gefen dattijon nan ya zauna ya rasa abinda ke masa dadi. Tausayin Hasna’u ya kara ninkuwa a ran sa and he vowed to himself to become her guardian and also a shoulder to lie on (bango abin jingina) ko da wannan shine abu na karshe da zai gabatar a rayuwar sa.

Yayi hawaye ya share har babu adadi. Ba jimawa su Kawu Sama’ila suka dawo. Dattijon nan yayi masa nuni da Kawu Sama’ila “ga Yayan ta can ya dawo, je ka yi masa taaziyya”.

Ya karasa har gaban Kawun ya tsugunna ya gaishe shi yayi masa gaisuwa, sannan ya gabatar da kan sa matsayin likitan ‘Unity College’ da abinda ya kawo shi wato duba ma Hasna Innar ta da kuma abin alhinin da ya tarar. Ya kare da yi masa ta’aziyya. Kawu Sama’ila ya ja shi suka zauna tare a gindin bishiya yana ta gode masa tare da sanya masa albarka.

“Wato dan nan ina tausayin Hasna’u, bata saba da kowa ba sai uwar ta, ga ta da kebe kai daga cikin al’umma (alienation), idan ka ga irin shaquwar da suka yi sai ka ji cewa lallai Hasna’u yanzu ne zata yi maraici na baya ba komai bane tunda ko sanin uban bata yi ba.

Ko barci baya raba su, sai in ta koma makaranta.

Kullum zancen ta shine, “ranar da babu ni, Yaya Sama’ila ko yaya Hasna’u zata yi?” Sai in ce mata Allah da ya halicce ta shi zai bata yadda zata yi”.

Hirar mu ta karshe bayan masassara ta kwantar da ita shine ta ce ta san Hasna’u na cikin damuwa na rashin zuwan ta ganin ta a makaranta, tunda bata taba fashin zuwa ba, nace mata ni zan je in gano mata Hasna’u” sai cewa tayi “yanzu ta kusa cika shekaru sha bakwai, na san ba miji zata samu ba, ko yaya rayuwar ta zata kare?” Nace mata “Zulai ki daina irin wannan tunanin Allah shi yake komai, kuma muddin ina raye Hasna’u zata yi aure kamar kowa tunda dai na haifi ‘ya’ya maza, in ‘ya’yan kowa sun ki ta ‘yan uwan ta Hassan ko Hussaini bazasu ki ta ba.

STORY CONTINUES BELOW

Sai ta yi murmushi tace “gara kowa da su in dai a kan Hasna’u ne”

nikuma nayi mata alkawarin muddin ina raye, to Hassan ko Hussaini wani cikin su zai auri Hasna’u”.

Tunda Kawu ya fara bayanin sa yake saurare attentively har Kawun ya dasa aya. Bai ce komi ba, don bai da abin cewar amma hakika Hasna ta gaya masa Hassan da Hussaini ‘ya’yan Kawun ta sun fi kowa kyamar ta. To ina ga an aura musu ita? Amma su kadai suka dace da auren nata ko babu komi jinin ta ne ‘yan uwan ta ne, but Hasna is talented a karatu despite her disability, talent din da ke bukatar nurturing ba wai auren wuri ba, auren da za’ayi ne kawai don a rufa mata asiri ba don ana son ta ba.

To amma shi wanene da zai hana Kawu yi wa ‘ya’yan sa aure in shi ba auren ta zai yi ba?

Rasss! Ya ji gaban sa yayi mummunan faduwa. Abu daya zai yi in har yana so ya taimaki rayuwar Hasna’u shine YA AURE TA!!!

To amma ya aureta ya kai ta ina? What of the genetic factor? Mama will NEVER allow him to bring ALBINO to her family talkless of matar data riga ta yi masa wato Fa’izah diyar aminiyar ta.

“Kawu ina rokon alfarmar kada a fadawa Hasna mutuwar Innar ta sai ta dawo hutu, saura kwana goma su dawo”. Ya fada da wata murya kamar ta wanda ya sha duka hawaye na kundumbala cikin idanun sa. “Sannan ina neman alfarmar a bar ni in kaita asibiti a yi mata gilashi ranar da suka yi hutu ni da kaina zan dawo da ita har gida cikin amana, idan har ka amince da ni. Gilashin zai ceci ganin ta da take gab da rasawa”.

“Samari na amince maka ka ji? Ka kaita ayi mata ka dawo min da ita, Allah yayi maka albarka, in iyayen ka na raye Allah ya kara musu lafiya da nisan kwana, idan kuma sun rigaye mu Allah ya kai ladan taimakon da kake da niyyar yi wa Hasna’u kabarin su”. “Amin ya Allah Kawu, ubana ya rasu mahaifiyata ke raye, sai kanwata daya Nusaiba.

Sunana Abubakar Saddiq amma ana kira na SAHEEB”

“Sannu ka ji Sahabi? Sahabi abokin Manzo, Allah ya baka masu yi maka kai ma”.

Da wannan suka yi sallama da Kawu Sama’ila, yana shirin barin kofar gidan wani saurayi na tahowa dukun-dukun da shi idanun shi jajawur, in ba shaye-shaye ba ba abinda zai maida idon namiji haka, ya kalli Saheeb ya watsar, yasa kai zai shige cikin gida.

“Kai Hassan don jakar ubanka baka san kanwata ta rasu bane? Ban ganka a makabarta ba kuma yanzu zaka wuce mu baka yi mana ta’aziya ba, ga bako kana gani amma ko ka gaishe shi?”

Bai tsaya ba ya cigaba da tafiyar sa yana fadi cikin kunkuni “to Baba ina ruwa na don uwar zabiya ta kwanta dama? Bakon ka kuma meye gami na da shi? Garin kwashe-kwashen ka sai ka janyo wadanda zasu yi kidunafun din ka”.3

Da haka ya shige cikin gida, kunya kamar ta kashe Kawu Sama’ila, sai da ya gwammace bai kula shi ba. Saheeb yayi kamar bai ji su ba ya sa takalmin sa ya wuce don gab yake da fashewa da kuka da ya gane wannan ne mijin Hasna’u. Mijin da sai wani babban ikon Allah ne zai hana ta auren sa.

Mr. Samson ne a cikin ajin yana bada darasin sa na lissafi. “Set Theory” is our today’s topic. Who can tell me what is set in mathematics?”

Kamar ko yaushe ya san ita kadai ce zata daga hannu, kasancewar ta masoyiyar darasin sa na lissafi, saboda tsabar son ta ga subject din kafin a yi musu topic ta je labirare ta dubo shi ta yadda in ya zo ya fara koyarwa sai dai ya zama kamar tishi a gare ta. Amma ga mamakin sa yau bata daga hannu ba. Ta hada kai da tebir bata ma san me ake a ajin ba.2

Har Mr. Samson ya zo gaban tebirin ta ya tsaya, ya kuma kira sunan ta bata ji shi ba. Sai ga sallamar Saheeb wanda baya zuwa classes area sam, amma yau sai gashi har ajin su Hasna’u, gabadaya a hargitse yake kamar bai samu barci sosai ba kuma bai yi wanka ba, bayan ya dauki iznin hakan daga principal ya kuma gaya mata abinda yasa yake son ganin Hasna’u din, ba wani abu bane lafiyar ta zai bincika don tana gab da fadawa depression kuma ga rasuwar mahaifiyar ta ba tareda ta sani ba. Ya gaya mata Kawun ta shi ya bashi iznin kulawa da ita har zuwa asibitin Murtala da zasu je ranar hutu.

Principal Haj. Maimuna Dikko, ta yi mamaki kwarai, what is special a kan zabiyar nan da kowanne malami bai da zance sai nata? And now Dr. Saheeb, yayi tattaki har cikin kauye sabida Hasna’u zabiya, lallai ne there’s something unique, something special associated with Hasna’u Dabo, wanda su Malamai da suke tare da ita suka yi noticing.

“Samson what’s wrong with her?” Ya fada hannayen sa biyu zube cikin aljihu, sounding worried, gaban sa na faduwa, cike da tsoron ko wani yayi masa riga malam masallaci ya gaya mata mutuwar Innar ta.

“I don’t know Dr. But she’s absent-minded”.

“Hasna! Hasna!!”

Saheeb ya kira sunan ta da dan karfi, tare da kwankwasa tebirin nata. Firgigit ta tashi ta hada gumi kashirman idanun ta sun kada sun yi jazir. Mafarkin da ta yi jiya da inna shi ya daga mata hankali. Sai ta ji uncle Saheeb na fadin.

“taso ki biyo ni clinic”.

Duk attention din ‘yan ajin sai ya dawo kan su, masu kyabe baki nayi, masu mamaki nayi. Dr. Sahib Bello Wamakko, ya kasance mai farin jinni a wurin ‘yammatan Unity Kachako duk da kasancewar bai dade a makarantar ba kuma ba mai sakin fuska bane.  A rashin sanin sa 70% na ‘yammatan unity masu ji da kan su yana matukar burge su.1

Ya riga ta shiga ofishin sabida tafiyar data ke yi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Nurse Saratu na gyara kantar magunguna ta gan su sun shigo. A yadda ta ga Hasna’u sai ta tabbatar ba lafiya ba, ga fuskar ta kara yin jajawur kamar da ka taba jinni zai yi tsartuwa.

“Have a seat” in ji Saheeb. Ya fada yana gyara mata kujerar gaban sa. Ta zauna, amma ta kasa ko duban sa.

“What happened Hasna’u?” Girgiza kai ta yi alamar babu komai. Shi kuma ya cigaba da lallashi yana tambaya. “Ni ba Yayan ki bane yanzu? Baki san har gidan ku na je ba? Kowa da kowa yana gaishe ki, ga wannan Inna ta ce na kawo miki” ya fada yana mika mata wata katuwar Ghana must go shake da kayan masarufi na alfarma. Kallo daya ta yi wa kayan ta hau girgiza kai.

“Ba Inna ce ta aiko da wadannan kayan ba”.

“Why do you say so?” ya tambayeta cikin rashin jin dadi, feeling somehow yau yayi karya don ya farantawa Hasna’u.

“Ina ta gan su? Da dai kanzo, kwaki da kuli da mai da dunkule ka kawo shine zan yarda Inna ce ta aiko” “to naji na yi karya Hasna’u, shikenan, har zuwa gidan ku dana yi shima karya ne ko? In baki sani ba har Hassan na gani da malam Audu makocin ku da Kawu Sama’ila  da ita Innar kan ta”.

A take fuskar Hasna’u ta washe, jan ya ragu, har ta yi murmushi. Ganin hakan ya cigaba da yi mata bayani.

“na je na karbo iznin Kawu ne na in kaiki asibiti ranar hutu, daga nan in maida ke gida. So ki shirya da wuri ranar hutu don mu samu ganin likita a cikin Kano”.

Bata san meyasa shi ta yarda da shi ba, bata san me ya sa kome ya gaya mata sai zuciyar ta ta yi amanna ba, haka bata san me yasa shi SAHEEB take da kyakkyawan confidence  da trust  a kan shi ba.

Ta ji ta yarda zata iya bin sa ko Birnin Sin ne, ba tare da ta ji ko darr ba, ta amince ba zai cutar da ita ba. Ta kuma yarda ya je gidan su, wadannan kayan ne dai bata yarda daga hannun Inna suka fito ba, they are solely from Saheeb, yace inji Inna ne don yayi mata wayo ta karba.

“Kai dai uncle ka gaya min gaskiya, cewa kai ka yi provision din nan, ai ba zan ki karbar kyautar Yaya na ba. Amma ina kudin surfen Inna zai sayi wannan? Jarin abincin ta ya dade da karyewa”.

Ta fada with so much love and affection ga Innar ta cikin sautin muryar ta.

Saheeb, sai ya ji hawaye na son zubo masa, yayi maza ya juya yana lalube a cikin loka yana hadiye hawayen sa. Ba zai yarda ya zama wanda zai labartawa Hasna’u mutuwar Innar ta ba in ba haka ba har abada bazata daina ganin bakin sa ba. Gara ya bari suje lafiya su dawo lafiya in yaso Kawu Sama’ila ya fada mata da kan sa.

“Naji-naji ni Saheeb shikenan Wamakko na yi wa Hasna karya, kwashe ki tafi hostel ki aje su ki koma aji”. A raunane tace.

“I’m sorry uncle, ba nufi na ka yi karya ba, tuntuben harshe ka yi” Saheeb ya saki wani kasaitaccen murmushi yana duban ta yace “Hasnah? To shikenan naji tashi je ki, kuma kwana bakwai na baki ki cinye su. Kafin hutu ya kare zan karo wasu” “a’ah Uncle. Ko cikin zani gare ni ban iya cinye wannan a kwana goma”. “Yar dariya yayi wadda bata taba ganin yayi irin ta ba. Sannan yace “pls go with your BAGCO, na sallame ki”.

Barci yake so yayi amma ya kasa, sai juyi akan gado. Scenes din yau a clinic ke dawo masa filla-filla. Why is things happening like that?  His heart taking another direction, WHY? For Allah’s sake ina zuciyar sa ke son jan sa? She is Albino wadda in ya aure ta duka rabin ‘ya’yan sa sai sun zama albino. Amma akwai abubuwa masu dimbin yawa da suka fizgi hankalin sa a kan ta, abubuwa da yawa da suka gabata sun yi attracting din zuciyar sa, kwakwalwar sa da ruhin sa akan HASNA’U regardless of her skin, hair and eyes colour. There’s something beyond BEAUTY that haunted him as a man, wadanda tausayi shine jigon su. Sai kuma extraordinary characteristics na Hasna wadanda mazan kwarai kadai ke duba su, mazan jiya ba na yau ba, masu dattaku da ilmi. As a medical doctor wanda ya gama shekaru bakwai na MBBS, a yau sai ya ji ba abinda yake so yake buri irin yayi specializing a ‘Dermatology’ ba don komai ba sai don ya din ga kula da fatar HASNA’U!!!

-Takori

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *