ABAR SO CHAPTER 5 KARSHE BY NAFISAT MA’ARUF SHEHU💋(WURARH)💋
Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin tashin hankali ya bi bayan ta da mugun gudu shi ma cikin son ya cimmata amma abin ya faskara saboda har ta sauka daga matakalar benen tayi waje cikin mugun speed daga gani ma stairs uku-uku take tsalakewa ,straight boys quatars ta nufa,
+
Dadynsu da kuma Alhaji dake zauna suna tattaunawa akan yanda Dadynsu dakuma Nadhira zasu tafi India saboda sun samu papers din da ya ke hannun ta dukda uban mamaki da zulumin da zuciyarsu ke ciki game da inda Nadhira ta samu papers din!
Gani suka yi an wucesu fhew kaman guguwa, nan suka Kara ganin Amin shima ya taho da gudu yana faɗin
“She’s Harmed! “
“Waye? “Suka tambayesa cikin haɗin baki amma ko amsawa bai yi bah asalima ko juyowa bai yi bah, suma basu yi kasa a guiwa bah suka mara mai baya!
Gani ya yi ta fito daga wani ɗaki tana shirin buɗe dayan daga gani neman Nadhiran ta ke yi
“Dan kaza Kazan ki Ina ki ke? “Ta faɗa cikin karaji hawaye masu zafi na silalo ma ta saboda kishin da ke addabar zuciyar ta, wuff ya yi ya rike ta ta baya tare da fara kiciniyar kauce kwalban a hannun ta wanda hakan ya yi daidai da shigowan su dadynsu
Yana karɓan kwalban ya juyo da ita tare fizgewa ta yi tana ihu har san da antynsu da Nadhira suka fito a tsorace, tana haɗa ido da Nadhira ta yi kan ta tana mai jijiga kafadarta
“Wai yar ke dinnan neh daman ki ke neman kwace min miji? Waye ya baki wannan confidence din? Kin san ni kuwa? Wlhy Ina iya kai sunan ki wajen malamai su haukatar mun da ke! Ke bama haukataki zan sa su yi bah kashe ki zan sa suyi in yaso daga iyayenki har shi mijina suyi rashi! “
Afirgice dukkan su suke kallon ta barinma Nadhira da idanuwan ta su ka yi jazir kaman garwashin wuta.
Zata sake magana kenan ta ji saukar wata gigitacciyar Mari a kumatun ta! Ai a saba’in ta saki Nadhira hawaye na zubo mata kaman an buɗe famfo
“Ka Mari ni? Ko da yake ba yau ka fara duka na a kan ta ba! Wani tsaya ma tukunna laifi miye na yi maka? Fine na san ba ka taɓa sona bah! Yes nasan da hakan amma Ina laifin me son ka? Laifi ne don naso ka? Tell me” ta fad’a gwanin ban tausayi haɗe da zubewa a kasa tana fashewa da kuka mai cin rai
Gabadaya wajen babu wanda jikin sa bai yi sanyin ba hatta ita Nadhiran
Zama suka yi inda Kursum sai share unstoppable hawayen fuskar ta ta keyi, ita kuwa Nadhira kaman wata mage haka ta kanainaye Antynsu cike da tsoro ga idanuwan ta da suka yi ja saboda har yanzu tana jin sautin muryan Kursum a cikin kunnenta
“Gaskiya lamarin da ya farun nan ban ji dadin sa ba ko kaɗan!”Alhaji ya faɗa cikin Nuna rashin jin dadin sa kaman yanda ya faɗa a zancen sa
Juyawa wajen da Kursum ke zaune ya yi yace”Kursum wannan da kika gani kanwa ce a gareki! Kuma ba cikekkiyar lafiya gare ta ba saboda matsalar kwakwalwar da ta ke d’auke da shi wanda mu ke adduan Allah ya dawo ma ta da tunanin ta nan kusa! Kuma shi ƙarin aure ba haramun ba ne! Ya hallata saboda fiyeyyen hallita Annabi Muhammad (SAW) ma ya kara aure kuma ya kuma umartan mu da mu kara in har zamu yi adalci a tsakanin s.. “
Katse Alhaji Kursum ta yi da faɗin”Amin ba zai tab’a yin Adalci ba! Tin kafin nasan ta ido da ido ya ke nuna mun cewan ita ya ke so! Tin ban san ta ba ya ke duka na saboda ita Ina kuwa ga ya aure ta? Na tabbata kashe ni zai yi saboda ita daga karshe kun ga kuwa in na fara kashe ta ban yi laifi bah!I hate her right from the begining! ke Abar so ko? Aww na tina ma kunce mahaukaciya ce it…
“Watch your mouth!”ya katse ta cikin tsawa wanda ya sata firgita bama ita Kadai ba har da mutanen wajen gabadaya, cikin kuka ta miƙe tana cewa
“Allah,kasan ba zaka hana ni magana bah! Kuma na faɗa Allah duk ranan da wannan mahaukaciyan ta tare a gidan ka to ka tabbatar washe gari za’a yi jana’izar ta! “
Miƙewa ya yi da sauri tare da nufan in da ta ke wanda hakan na nuna alaman mazge ta zai yi,Muryan Dadynsu neh ya katse sa da faɗin
“kar ka kuskura ka taɓa ta!”
“Barshi ya taɓa ni wlhy da babu abinda zai hana ni ramawa a kan wannan mahaukaciyar sa!”
“Fita a nan!”Ya faɗa yana nuna ma ta kofa trying to be calm,hanyan waje ta nufa tana magana kasa-kasa, sanda ta isa bakin kofa sannan ta juyo cikin ɗaga murya ta ce
“Ke mahaukaciya!wallahi kika kuskura tsautsayi ya sa ki ka shigo gidana to sunan ki Sorry!” Ta faɗa haɗe da ficewa da gudu
Murmushi Dadynsu ya sake saboda sai yanzu ya gane matsalar dukkansu biyun!ya gane cewa Kursum ko kadan bakin ta baya mutuwa ko da kuwa wuƙa za’a sanya a wuyar ta ,shi kuma Amin ba shi da hakuri ,murmushi ya sake sakewa a karo na biyu lokacin da ya haɗa ido da su Antynsu da ke kallon sa barinma Nadhira da ke kallonsa kaman eyes na ta zasu faɗo! yasan duk kuri Kursum ta ke yi saboda yasan halin ƴarsa
Alhaji ne ya sauƙe ajiyar zuciya mai karfi saboda sosai maganan kisan da Kursum ke cewa zata yi ya addabe zuciyar sa,kallon Amin da kan sa ke sunkuye ya yi ya ce
“Gabadaya ban ji dadin abin da ka yi yanzu ba”
“Babynmu, muje ko!”Antynsu ta fad’a saboda ganin bai dace ace su zauna sauraren faɗan da za’a yi ma Amin bah
Bayan sun tafi ne Dadynsu ya ce”Wa ya ce ma ka ana dukan mata!gaskiya na sha mamaki! kuma nima ban ji dadi bah! yanzu haka ka ke son na baka auren ƴata? anya za ka yi adalci kuwa?”
Mikewa Alhaji ya yi fuskar sa na nuna seriousness a kan maganar da zai yi,cikin isa da nuna cewan shi din uba ne a wajen Amin ya ce”Maganar auren an soke sa har sai sun sasanta da matar sa! kuma sai ta yarda ta karɓi Nadhira da hannu biyu a matsayin a bokiyar zama”
wani irin faɗuwar gaba da tashin hankali ne ya ziyarci zuciyar Amin nan gaban sa ya hau dukan fat fat fat kaman zai fasa kirjin sa ya fito,wani yawu mai ɗaci ya haɗiye yana kallon inda baban nasa ya ke wayam ya ga baya wajen nan ya fahimci ashe ya fice ne!
Kallon wajen da Dadynsu ke zaune ya yi,murmushi Dadynsu ya sakar mai ya ce “do as he say!”
Wani huci ya sake yana lumshe idanuwan sa saboda yasan abu ne mai matukar wuya Kursum ta yarda da batun sa ,he’s so confused
“kar ka bada maza mana Aminu!”
“bansan ya zan yi ba ne ta amince wlhy da wuya ta amince!”ya faɗa kaman zai yi kuka
Dafa sa Dadynsu ya yi ya ce”ni zan faɗa ma ka yanda za ka yi kuma ta amince”
waro idanuwansa ya yi ya ce”dagaske?”
“inshaAllah!”
wani farin ciki ya ji ya lullube sa nan ya hau washe bakin sa kaman gonar auduga , a wajen kafar dadynsu ya zauna tare da kallon fuskar sa yana jiran jin abinda Dadynsu zai faɗa….Magana dadynsu ya mishi a kunne wanda ni ban ji shi na sam! Murmushi naga ya sake yana shafa kansa Kafin ya ce+
“Thank You so much! Wallahi na ji dadin wannan batun! “
Kafadar sa Dadynsu ya tab’a ya ce”oya je da sauri kar lokaci ya kure! “
Mikewa ya yi da sauri tare da ficewa yana Adduan Allah yasa ya iya shawo kanta har ta yarda….
“Ni babu abinda zan ji!”ta fad’a cikin shesheka, zama ya yi tare da rik’e kansa da hannayen sa a hankali ya ce
“Ya za’ayi na nuna miki ina son ki! “
Dariyan irin ka raina mun wayo ta yi, cikin takaici ta ce”Karma kasoma mun dadin baki saboda Wallahi ni din ba yar yau bace! “
“Haba! Wallahi inasonki! Ina sonki sosai!! Ya ma za’ayi nace bana son ki! Ke ce fa na fara kasancewa daita! Ko kin manta ke ce kika b’are ni nima na b’are ki! Allah da bana sonki da tin lokacin da aka ce ke aka zab’a mun to wallahi dana bi matan banza! Please ki yarda dani wallahi ina son ki sosai! “
“Toh miyesa baka proving cewan kana sona! Baka tab’a behaving kaman wanda yake sona ba!”ta fad’a cikin d’acin rai saboda abin ba karamin damun ta yake yi ba
“Don’t worry! InshaAllah daga yau zan chanxa! “Ya fad’a cikin lallashi!
Kallon irin are you sure dinnan ta mishi, a hankali ya d’aga kan sa tare da sumbatar kumatun ta, tab’e baki ta yi tare da wucewa abin ta
Wani ajiyar zuciya ya sauk’e ganin bai wani sha wuyar shawo kan ta ba!…
“We’re going for dinner tonight by 8:00 get ready! “Shine abin da ke yawo a saman screen din ta, wani iri ta ji dukda abin ya ma ta banbarakwai
Cikin jin dadi ta hau shiryawa, kwalliya ta chanchara kaman wacce zata je gasa, tana gamawa call din sa na shigowa, sanda ta ja aji tukunna ta d’auka
“Hey dear ina jiran ki a mota! “Shine abinda ya fad’a tare da katse Kiran, wayar ta bi da kallo tana jin farin ciki na ratsa ta
Clutch din ta tad’auka sannan ta fice, yana hango ta yayi flashing wutan motan da yake ciki, a hankali ta taka wajen cikin sauri ya fito ya bud’e ma ta kofan motan ta shiga sannan anima ya zaga tare da tayar da motan suka fice.
A hankali ta fito daga bayan bishiyan da ta ke kallon su, tsayawa ta yi tare da hard’e hannayen ta a kirjin ta, tsaki ta ja wannan ta juya b’angaren su….
A cikin kwana biyun nan sosai Kursum ta ga gata a wajen Amin, sai yanzu ta ke jin ta a asalin mai aure,
Shima Amin abin ya mai dadi sosai saboda wata rana manta da babynsu ya ke in fact baya tashi tuno ta sai sun had’u a hanya
Zaune suke a kan kujera suna kallo ga popcorn a gaban su suna ci, gyaran muryan da Amin ya yi ne yasa Kursum miyar da hankalin ta kan sa
“My dear! “Kallon sa kawai ta yi ba tare da tayi magana ba, hannun ta ya hau murzawa chan ya ce
“Zamu yi magana ta fahimta ne da ke kuma bana son ki fassara ta wani wajen daban! “
Gyada kai ta yi cikin sanyin jiki”ban tab’a jin zan iya sonki sosai kaman yanda na ke sonki yanzu ba! Gabadaya kwanan nan ji nake kaman ba ni ba saboda irin kulawan da nake samu daga gare ki! Ji na yi ma bana bukatan Karin aure saboda daman saboda bukata zan yi auren! Please dear karki chanza daga yanda muke a yanzu! “
Shafa fuskan sa ta yi cikin shauk’i, a hankali kaman ba ita ce wannan Kursum wacce bata san abu kaxa ne ba’a fad’i ba ta ce”haba love! InshaAllah bazan chanza ba!”
Murmushin jin dadi ya yi chan yanayin fuskar sa ya sauya zuwa ta damuwa, cikin kulawa ta ce” Miye faru!? “
“Tunanin babynmu na ke yi da kuma babanta! “Annurin fuskar Kursum ne ta d’auke, chan ta had’e rai tana jifan sa da kallon karma ka fara, hannun ta da ta cire a nasa ya sake kamowa yana cigaba da fad’in
“Wallahi tausayi suke bani! Taimakon su zanyi kuma kin ga yarinyan ba ta da isheshiyar lafiya! Asalima duk abin da aka ce tayi zata dinga yi kinga kin samu mai tayi ki aiki! “
Ganin yanda take kallon sa kaman zata rufe sa da duka yasa shi had’iye wani yawu mai d’aci, lips din sa da suka gama bushewa ya lashe,
Kaman zaiyi kuka ya ce”Dear please alfarma kawai zaki mun saboda babanta! Tana warkewa zan sake ta! “
“Are you sure Zaka sake ta in ta warke? “Ta tambaye sa ganin yanda ya wani marairace ma ta, gyada kai kawai ya yi yana jin farin ciki na ratsa shi
“Ba damuwa Allah ya kaimu lokacin amma ka sani yar aiki zaka kawomin ba kishiya ba! “
“Zaki san yar aiki! “Shine abinda yake fad’a a zuciyarsa, a fili kuma dariya ya yi ya ce”as you wish dear! “…
A hankali ta juya saboda daman shiga zata yi taji suna magana, suna ganin ta suka sakar ma ta dariya itama dariyan ta musu tare da shiga cikin mota
“Ina yake!? “Shine abin da suke tambayan ta amma ko cikan ku ba ta ce ba, ganin bata amsa musu ba yasa Alhaji kiransa a waya, chan sai ga shi ya fito kuma daman Hajiya bata nan ta tafi Dubai had’o kayan lefe
“Ai tin d’azu muka aiko babynmu sai kuma muka ga ta dawo ita kad’ai! “Gabansa ne ya yi mugun bugawa dalilin jin abinda dadynsu ya fad’a
“Karmu b’ata lokaci nan da hour daya jirgi zai tashi kuma kusan tafiyan minti talatin ne a gabanmu! “Alhaji ya fad’a yana shiga cikin mota
Suma cikin motan suka shiga kasancewan motan sieana ne, tare da driver Amin ya zauna sannan aka ja su….
“Gaskiya kayi kokari sosai Inspector! Kuma gaskiya kwakwalwar ka na ja sosai! Amma ka sani kullum sawa nake a raina babu wanda zaiyi beating intelligence dina shiyasa kaga na maka haka saboda mugun shishigin da kake da shi! Alhmdllh ko mai yazo karshe tinda yanzu haka Muna kokarin shiga cikin jirgi kuma ni da dawowa… Hhhhhhh ba yanzu ba maybe ma bazan sake dawowa ba kuma kasan you have no right da zaka zo har inda na ke kayi arresting dina saboda kasan sarkin wani guri bawan wani waje ne!…. You really impressed me saboda kasan aikin ka kuma samun irin mu wahala garai! Ina farin cikin sanar da kai ni _Nadhira_ ba ni ce na jawo komai ba! Asalima ramakon gayya nayi saboda gaskiya kaman yanda ka tab’a jin abinda Antymu ta fad’a all I know is do me I do you!… Oops am sorry for playing with your intelligence! Bye _Nadhira!_”Wani irin kukan kura Inspector ya yi lokacin da ya gama karanta sak’on da aka turo mai, safa da marwa ya fara yi a cikin office din sa, nan da nan ya jik’u da zufa!….
+
_India…_
Duk iya kacin binciken da ya kamata a yi wa Nadhira anyi sa kuma result daya ke fitowa, wato lafiyan ta kalau babu abinda ke damun kwakwalwar ta! wanda hakan ya yi mugun basu mamaki!
Babu yanda ba’a yi wajen sa Nadhira dawowa daidai ba amma abun ya faskara har su Dadynsu sun fara tunani ko dai iska ne suka shafe ta….
Antynsu ce ta bada shawaran komawa da ita bayan an gama mawa daddynsu gwaji, amma kuma sai Likitan ya d’aura ta a kan magani kuma yen uwan Margayiya Momma sun ce abar musu ita zasu mata magana irin na su na indiyawa!
Dakyar da dadynsu ya yarda kuma akan sharadin bayan wata daya zasu dawo su d’auke ta! Wannan batun ba karamin dadi ya mawa Nadhira ba!….
Bayan shekaru biyar!…
Tsaye na hango wasu yenmata uku a cikin aji kowa da abin ya ke rike da shi , daya daga cikin su ce ta ja tsakin da ya jawo hankalin daliban da suke zaune, girgiza kai kawai suka kowa ya cigaba da abinda yake yi saboda inda sabo yaci ace sun saba da halin su yen group din Baby Nadhira!
Cikin indiyanci Nadhira ke cewa”wai miye ne kika ishe mu da tsaki ne? In kin sa nan bai miki ba zaki iya tafiya saboda daman bada igiya muka janyo ki ba! “
Harara Fatima ta maka mata tana turo bako “kutt ni kike harara? “
Nadhira ta tambaya cikin hasala da b’acin rai, ganin yanda Nadhira ta jefo mata tambayan yasa ta aza murmushi akan fuskar ta tana cewa “haba dai my dear sisto, wacce ni na harare ki”
Nadhira zata sake magana kenan wayar ta ya dau ruri, “My Husband! shine sunan dake yawo a saman screen din wayar ta
Hanyar waje kawai ta yi tana receiving call din kaman b’ata so! Sai uwar harara da dangwali da take kai wa fuskar wayan kaman wanda yake kiran ta ne a wajen
“Abar so na! “Taji ya fad’a daga dayan bangaren, jin bazata amsa ba yasa shi fad’in
“Antynki bata da lafiya fa! Tin last month akayi admitting din ta a asibiti “
Cikin tashin hankali take fad’in” miye kake cewa? “
“Baby Antynki babu lafiya sosai! “
“Shine sai yau kuke fad’a mun? Ina take yanzu!? “Ta tambaya cikin d’auriya saboda dab take da fashewa da kuka
“Ga ta nan! “Ya fad’a
“Babynmu! “zama tayi akan dakali cikin mutuwar jiki dalilin jin yanda antynsu ta Kira sunan ta Dakyar
Cikin kuka take fad’in”Miye ke damunki antynmu?”
“Babynmu danAllah ki dawo na miki kallon karshe kafin na mutu! “
Kuka ta fashe dashi tana cewa”ki daina fad’in irin wannan maganan antynmu! Bazaki mutu ba insha Allah ai cuta ba mutuwa bace! “
“Nasani Babynmu danAllah kece last wish dina please ki dawo hakan nan babu mai miki komai wallahi yanzu baki ga yanda su big daddy suka dawo ba wallahi ke karan kan ki sai kin tausaya musu! “Antynsu ta fad’a kaman ba ita a kace bata da lafiya ba
Shuru Nadhira tayi tana son gano wani abu daga muryan Antynsu, jin yanda Nadhira tayi shuru yasa antynsu sakin wani nishi mai nuna cewan tana jin jiki
Nan da nan Nadhira ta rude sai haukin sannu take yi hankali tashe, zata yi magana taji muryan Amin yana cewa”baby please ki dawo she really need you by her side! “
Kashe wayan kawai tayi tana share hawayen fuskar ta, zaman Jakarta ta gyara bayan ta mike sannan ta bar wajen batare da ta koma cikin aji ba!…
Lumshe idanuwan ta tayi bayan ta zauna acikin jirgi gefen wani matashin saurayi, tinawa da tayi da bata sa seatbelt ba yasa ta fara kiciniyar sawa idanuwan ta rufe,
Tsaki taja tare da bud’e idanuwan ta da suka danyi ja saboda rashin samun bacci dalilin jin Antynsu bata da lafiya! Ita karan kanta bata san adadin son da take mawa Antynsu ba!
Tinda take bata tab’a d’aukan ta amatsayin matar babanta ba sai a matsayin mamarta, lips din ta ta ciza kadan tare da sake sakin wani tsakin kaman wata tsaka
Shi dai wannan banda kallon ta babu abinda yake musamman ma karamin cute bakin ta, sai tasbihi yake yi a zuciyar sa dalilin ganin baiwar kyan da Allah ya mata
“Kallon nan ya fara wuce ka’ida fa! “Ta fad’a da turanci tana ya mutsa fuska,
“masha Allah! “Ya furta jin sweet voice dinta, tsaki tayi tana bashi hararan gefen ido batare da ta ga fuskar sa ba
“Am Ramadan by name”ya fad’a yana bata full attention dinsa, fuskar sa ta kalla sannan ta sake tab’e baki
Cikin turanci ya ce”Ke fa”
Ganin bazata amsa ba ya ce”you’re really beautiful! “
“I know! ” ta bashi amsa a takaice wanda hakan ya yi daidai da tashin jirgi
Dariya ce ta sub’uce mai jin abinda ta ce, “I like it! “
“Am a married woman! “Ta fad’a cikin takaici, dariyan kinma raina mun hankali ya fara, headphone dinta ta sa tare da lumshe idanuwa ta, tinawa da tayi yanda ta musu wasa da hankali yasata sakin murmushin da bata shirya ba…
Lokacin da suka dawo komawa da ita tak’i sai a lokacin suka yarda da abinda Inspector ya fad’a musu a kanta Wanda hakan ba karamin mamaki ya basu ba
Daga karshe ma guduwa tayi ganin in bata yi wasa ba zasu koma da ita Nigeria kuma tasan akwai matsala in ta shiga Nigeria
Yen uwan mamanta ne suka bawa su Dadynsu hakuri akan a barta zuwa wani lokaci kafin nan ta fara karatun ta a wajensu daman kuma already har an d’aura aurenta da Amin shiyasa Dadynsu ya nema mata uzuri a wajen mijin ta nan ya nuna ba damuwa a barta…
Sosai ta dinga musu wasa da hankali wanda hakan yasa Dadynsu yin fushi da ita amma zuwa wani lokaci ya hakura…..
_BAUCHI, NIGERIA…_
Fitowar su daga jirgi kenan taga wannan guy din ya biyo ta, tsaki taja tana nufan wajen wata mata dake zaune da alaman tazo tarban wani ne
“Assalamu alaiki! “
Amsawa matan tayi cikin murmushi, “nace danAllah ki dan taimaka mun da aron wayan ki zan Kira gida azo a d’auke ni”
“Oyoyo Ammi! “Taji an fad’a daga bayan ta, batare da ta juya ta dan matsa inda matan kuma ta mike cikin farincikin ganin tilon d’anta
Cikin ladabi ya gaishe ta inda yace”Ammi yau nasha mamaki! “
“Miye faru uban surutu!”
“Hmmm wallahi Wai ni wannan yarinyan ta dinga sha wa kamshi a cikin jirgi Allah ban ma d’auka ta jin Hausa ba sai yanzu! ” ya fad’a yana kallon bayan Nadhira saboda har lokacin bata juyo ba
“Babynmu! “Taji an fad’a, kai ta d’aga ta kallesa, ganin Amin dinne yasa taji wani kwalla na shirin zubo mata, Amin kam takowa yayi har wajen da take yana Kare mata kallo ai kuwa baisan lokacin da taji ta rungume shi ba
Mamaki ne ya kama sa saboda ya d’auka balbale sa zata fara amma kuma yaga sab’anin hakan, wani farin ciki ne ya lullubesa nan Shima ya rungume ta da hannun sa
Ita kuwa tayi hakan ne saboda wannan parrot guy din acewarta, daga idanuwan ta da zata yi ya sark’e cikin na inspector
Gabanta ne yayi mugun fad’uwa wanda hakan yasa jikin ta ya dau rawa, cikin sauri ta sake sa tare da ture sa daga jikin ta
Kai tafara girgiza wa wani uban bakin ciki na turnuke ta”you lied to me! “
Ta fad’a cikin son ganin batayi kuka ba, Shima kan ya girgiza, kafin ya yi magana har inspector ya karaso yana cewa
“Welcome back to Nigeria the master planner! “
Wani mugun yawu ta hadiye tana buga kanta da hannun ta wanda hakan yasa Ammi karasawa wajen ta tare da rik’e hannun ta tana fad’in”haba ai sai ki jiya kanki ciwo”
Fixge hannun ta tayi da mugun karfi wanda hakan ya basu mamaki amma banda Amin da Inspector wanda suka san halin ta
Tab’e baki inspectorn yayi Cike da tsanan ta ya ce “Zamu iya tafiya kokuma har yanzu baki gama gudun ba? Duk nan wajen zagaye yake da polisawa don haka cikin sanyi ki biyo ni Kafin ayi disgracing din ki acikin jama’a “
Mamaki ne yakama su Ammi da jin abinda Inspector ya fad’a
Cikin tsiwa ta ce”aikin birit inji tusa! Kai kuma ko!?…. Dariya tayi tace…. Kun bani mamaki! Amma bakomai duniya ce” tana gama fad’in hakan ta buge Amin tare da wucewa inda su kuma suka mara mata baya harda su Ammi….
Ba’a wuce da ita ko ina ba sai police station babu yanda su Ammi basu akan a fad’a musu miye tayi ba amma suka ce in suna son jin abinda ya faru su had’u a kotu….
Isan su police station yayi daidai da karasowar su Antynsu, ko iskan da ta kwaso su ba ta shaka ba ta wuce su duk da Kiran ta da suka dinga yi…+
Babu yanda basu yi da ita akan tayi magana ba amma ta k’i asalima ko kallon su bata yi ba har yen sandan suka koma da ita cikin cell….
Sosai ranta yake konewa in ta tina harda Antynsu acikin masu mata karya dama kuma ta riga ta san shi Amin makaryaci ne amma antynsu fah?
Ihu tasaka kafin ta fashe da kuka mai cin rai saboda yanda take ji, tinda take a rayuwan ta bata tab’a tunanin zata shiga police station ba balle a zo ga cikin cell!
Washe gari…..
Kotu ya cika mak’il da jama’a saboda hukuncin da ake son yankewa, yen uwan Maimuna har da su big daddy da familynsa, Kaii in takaita muku mutane da dama sun hallara
Gefe guda antynsu ne idanuwan ta duk ya kumbura tsantsan kuka ga Amin ma ya dawo wani kalan tausayi dashi a wajen,
Malama Kursum kuwa ido ya raina fata da jin abinda aka ce Nadhira ta aikata amma wani b’ari na zuciyan ta farinciki ne fal a cikin jin za’a yanka mata hukunci ga kuma tunanin cewan Hajiya zata sa Amin ya sake ta saboda ita a yanda take ganin take-taken sa tasan da wuya ya sake ta kuma tasan ko Karen hauka ne ya cije ta ba zata iya mata ko kallon banza ba balle kuma a zo ga tasa ta aiki!
“Hmm wane ni kalan ta Kashe ni! ” shine abinda ta fad’a a sarari, juyowa Maman Ramadan da suke jiran jin laifin da Nadhira aikata tayi
“Ta tab’a kisa ne?”
Sanda ta ya mutsa fuska kafin ta ce”yo miye maraban dambe da fad’a tinda daman kisan taso yi Allah bai bata sa’a ba! “
Cike da mamaki Maman Ramadan ta kalli kofan da ake shigowa da ita,
Ganin ta da suka yi yasa antynsu fashewa da kuka cike da tausayin yarinyar ta, ko inda suke bata kalla ba aka wuce da ita cikin bar din da suke tsayawa
Shigowar alkali ne yasa kowannen su yin shuru, batare da b’ata lokaci ba Alkali ya nemi jin ba’asin zance
Nan aka fad’i komai, d’agowa Alkali yayi cike da mamaki inda kowannen a cikin court din suka fara kus kus nan Alkali ya buga guduman su
Gyaran murya yayi ya ce”Nadhira Shariff kin dai ji abubuwan da ake tuhuman ki da su! Shin kina da abin da zaki iya cewa don Kare kan ki ko kum…
“Na amince da duk abubuwan da ake tuhuma ta da shi! “Ta katse Alkalin, mamaki ne ya karo akan fuskokin mutane inda antyn su ta fashe da wani siririn kuka
“Oh Allah! “Shine abinda wannan gayen wato Ramadan wanda suka had’u da shi a filin girgi ya fad’a cike da dimbin mamakin ta saboda daman shine mai kare ta amma tinda ta riga ta amsa laifin ta babu abinda ya rage da za’a k’are!
Girgiza kai Alkali yayi yana jinjina bushashiyar zuciya irin na Nadhira! Sake gyaran muryan sa ya yi ya ce”this is my judgment! “
Ai nan ka ji Kotu ya dau shuru kaman graveyard, kowa ka gani ya zura wa Alkali ido ana jiran a ji wani hukuncin zai yanke
“Kotu ta yanke miki zaman gidan yari na tsawon shekara guda saboda kwayoyin da kike amfani da shi da Kuma miliyan biyar wa iyayen yarinyar da kika haukatar!”
Lumshe idanuwan ta tayi Chan Kuma ta bud’e tare da sakin Murmushi wanda hakan yayi daidai da bud’e inda take tsaye,fitowa tayi still da wannan murmushin a fuskar ta,Suna had’a idanuwa da mutanen gidan su ta tsuke fuskar ta Kaman bata tab’a dariya bah.
Suna isowa wajen su ta ja burki ta tsaya “kun ban mamaki,Amma ba damuwa gwanda da kuka dawo dani din!
Dan takawa tayi har gaban Kursum da Murmushin ta ya d’auke dalilin ganin ta tako zuwa gaban ta,nan da nan Wani irin tsoro ya shige ta!
Murmushin ta mai d’auke da ma’ana daban daban ta sake tana kallon Kursum da tsoro ya bayyana a fuskar ta
“Kin tina miye kika tambaye ni ranan da kika mare ni?…murmushi ta sake sake wa ganin Kursum ta girgiza kai alaman a’a…”ko zaki Rama ne? Don na ga alamun Marin ya shiga” toh bari na baki amsa ta!
Kaman daga sama suka ga Nadhira ta kifa wa Kursum wata gigitacciyar maruka a kowani side na kumatun ta,Zaro idanuwa suka yi inda polisawan suka riketa, ko barin wajen basu yi ba suka ga Kursum ta sume a wajen sumammiya
Man da nan aka rufa a kanta , polisawa Kuma suka yi waje da Nadhiran da ke ta zuba murmushi….
Hannun ta da suka yi Sab’a ta kalla tare da ya mutsa fuska lokacin da ta Tina fatar maciji ta shafa a hannun ta na musamman saboda Marin Kursum….Rushing din ta suka yi zuwa asibiti cikin tashin hankali, nan aka fara bata taimakon gaggawa saboda gabadaya numfashin ta daukewa ya yi chak,in ba don jikin ta da ya dau zafi radau ba da zasu iya cewa ta mutu.+
Basu gama tsinkewa ba har San da suka ga fuskar ta na sab’a nan suka shiga mamaki al’amarin
San da tayi kwanaki biyu chur kafin ta farka a lokacin har ta sha ruwa ya kai 6 harda su Karin jini saboda yanayin jikin.
“Wayyo Model face dina!”Kursum ta fad’a cikin kuka saboda ganin yanda fatar fuskar ta ya b’aci da sab’a har wani ya mutse wa yafara Kaman wacce ta shafa ruwan kwai a fuska
“It’s ok dear!”Amin ya fad’a cikin tausayawa,rik’o hannu sa tayi da sauri tana cewa
“Wannan yarinyan zata iya kashe mutum DanAllah ka sake ta wallahi da wuya na iya zama da ita”
Girgiza kan sa ya hau yi had’e da share ma ta hawayen da suke silalo mata wanda Sam ita bata ma San da su bah,
“Kiyi hakuri dear nima da so samu me nasan yanda zan yi da ita Amma kuma kin ga iyayen ta Suna da Wani waje daban a zuciya ta wallahi bazan iya bah!am so sorry” ya fada gwanin ban tausayi
Jan hanci tayi cikin gajiya wa da sanyin jiki,”toh DanAllah ko zan zauna da ita ba gida daya ba!karka had’a mu saboda nasan it will be a hell for me”
Gyada kan sa yayi yana mata kallon tausayi ganin yanda ta koma lokaci guda…
Gidan Yari…
Zaune take akan gadon su tana karanta littafi,gefe guda Kuma wata ce take yin kneeling da alamun tayi laifi ne
“Ga shi nan zuwa!”wata ta fad’a da karfi da alaman tana musu gargadi ne,kokarin mikewa wacce take kneeling tayi Kaman daga sama taji Nadhira ta ce
“Kar yarda ki Mike!”
Cikin sanyin jiki ta koma tana matsan hawaye saboda daman shishigi me ya kai ta inda take yanzu duk da uwar kashedin da ake mata akan Nadhira
“Miye ke faruwa a nan?”Wani bagidaje ya tambaya lokacin da ya hango mai yin kneeling,
“Hukunci nake mata saboda haka zaka iya tafiya “Nadhira ta fad’a ba tare da ta daga ido daga karatun da take yi bah!
Girgiza kai kawai mutumin yayi tare da yin gaba saboda daman haka take,satin ta 2 a gidan yarin ammakaff wajen babu wanda bai San da zaman ta ba saboda yanayin ta….
BAYAN SHEKARA DAYA….
Sosai take cin duniyan ta Kaman ba agidan yari take bah! Iko kuwa babu wanda basu gani ba, gashi babu wanda ya isayayi complain! Asalima tsoronta suke ji saboda an basu labarin abin da yakawo ta gidan yari , kuma tin da ta shiga bata sake fita ko gaisar da mutanen gidan su bah Kaman yanda in aka kawo musu ziyara ake fita Dan Hiram mintuna goma sha biyar….
“Yau sai gida ko?”wata warder ta tambaye ta,murmushi ta sake had’e da girgiza kan ta
“Wallahi na miki murna sosai,Kuma kar ki manta da addreshin dana baki,Insha Allah zaki ga chanji sosai”
“Nagode sister!”ta fad’a had’e da ficewa daga office din.
A bakin gate ta tarar da duka mutanen gidan su harma da mutanen gidansu Amin,mutanen gidan su Big dady ma ba’a barsu a baya ba
A hankali ta taka zuwa gaban su , hawaye fal idanuwan Antynsu saboda tsananin tausayin Babynsu,girgiza wa Antynsu kai tafara alamun kar tayi kuka amma inaa abin ya fasakara ai kawai ta rungume ta tare da sakin siririn kuka itama
“Nayi missing din ki Antynmu!”
“kiyi hakuri babynmu am sincerely sorry!”
Tapping din bayan antynsu ta hau yi cikin tausayawa,ciro ta tayi tare da share mata hawayen ta tana cewa” bana son wa’inan hawayen antynmu! Karyar mun da guiwa suke yi idan na gani”
Murmushi antynsu ta sakar mata cikin farinciki, gyaran muryar da suka ji ne ya hankarar da su inda suke
“Dadynmu!” Ta fad’a kaman Mai tsoron magana ,ware mata hannu yayi ita kuwa babu kunya ta Isa gare sa tare da rungume sa
“Baki ga surakanan ki bane mara kunya?” Antynsu ta katse su
“Ohh ji son kai! Ke da kuke kukan yaushe gamo baki tina da surakan ta na nan ba sai da kika ga ta rungume ni?”dadynsu ya fad’a cikin ya mutsa fuska
Dariya dukkansu suka sa inda ta gaishe su nan su dunguma cikin mota
Girgiza kai Amin ya yi ganin yanda ta miyar da shi invisible a wajen…
Abinci kala kala aka shirya mata saboda sun san abinda zata bukata kenan a halin yanzu
“Kai Aminullah!”dadynsu ya Kira sunan sa ,cikin girmamawa ya amsa
“Je ka d’aki ka same ta naga ko gaisawa baku yi ba kuma dare na yi !”
Sosa keyar sa ya yi tare da mikewa ,hanyar inda ya ga ta shiga yayi
“Na d’auka kai jarumi ne ai ashe abin ban sani ba acikin lusaran ma kaine na farko!don dabarun ka ya kare shine zaka sa masoya na sumin karya! Ko ban fad’a maka ba nasan kasan yau wa’adin da ka d’iba mun ya kare, so duk hanyan da kasan zan iya haduwa dakai ka gaggauta tare wa in kuma ba haka ba hmmmm and karka d’auka alfarma ko umarni nake baka gargad’i nake maka! Lusarin banza kawaii..”We thought kin chanza! Ashe we’re all mistaken!ina fatan kinsan Wanda kika gama magana dashi yanzu? Amma kuma kike threatening din shi?why won’t you change fisabilillah ehen? Wallahi ina jiye miki ranan da zaki mawa wata wacce ramokon ta ya Fi naki ne!” Amin da ya gama Jin abubuwa da ta ke cewa akan waya ya fad’a mata cikin takaici da b’acin rai+
Ganin zata yi magana ya sa shi ficewa daga d’akin cikin fushi inda ta bishi da Kira amma ko amsawa Bai yi ba
Koma wa tayi tare da zubewa akan gado tana furzar da iska Mai zafi
Amin kam ko sallama Bai samu ya musu ba ya fice abinsa saboda B’acin rai…
After a week….
Nadhira ta murmure har k’iban ta ya dan dawo,
Ganin Amin Bai kara zuwa ba ya sa abin damun ta sosai ,kuma in ta Kira wayan sa baya d’auka don haka yau ta kuduri niyyan zuwa gidansu
“Antynmu! Zanje gaida su Hajiya!”ta fad’a daidai ta fito cikin shirin ta na fita anguwa
Kallon ta antynsu tayi cikin mamaki ta ce”Ban gane zaki je gaishe su ba ke da muka saka ran mika musu ke nan da sati”
Zaro idanuwa tayi tace” what?”
Girgiza kai antynsu tayi, zata yi magana kenan suka ji dadynsu na cewa”kar dai kin manta da auren Aminullah da ke kan ki!”
Ya mutsa fuska ta hau yi cikin takaicin jin wai ta manta da auren masoyin ta dake kan ta
“Maza-maza ki shige cikin gida yanzu!” Dadynsu ya fad’a cikin bada umarni
“Ohh Allah ai wannan gaisuwan na daban ne saboda a yanzu ba’a matsayin surka zan je musu ba! Zan je musu a matsayin babyn da suka sani don in nuna godiya ta Gare su a kan abubuwa da suka mana”ta fad’a cikin marairaice fuska
Da hannu dadynsu ya rike kai alamun ya gaji kafin ya ce”ki Kira mijin ki ki fad’a mai toh!”
Murmushi ta sake tana cewa”ai na Kira sa kuma ya ce nazo!”
Ganin antynsu na bin ta da kallon rashin yarda ya sa ta Fara kokarin fita tana musu sai ta dawo…
Sosai suka yi mamakin ganin ta amma suka basar, har kitchen suka shiga ta taya Hajiya girki kuma Hajiya tayi making sure bata fita ko d’aga ido daga kan Nadhiran ba saboda acewarta bata yarda da Nadhira ba!
“Ni wai su Kursum ba sa nan ne?”Nadhira ta katse shurun su tana kallon yar aikin gidan
“Anty Kursum bata nan!”
“Amin fa?”ta tambaya da sauri ganin Hajiya ta bar wajen
Cikin ladabi ta ke cewa”Yana d’akin sa ,shine ma ya aike ni na had’o mai tea”
“Tea da uwar ranan nan?”ta tambaya cikin mamaki
Girgiza kai tayi tare cewa”Don’t worry kawo na kai mai!”
Ba tare da musu ba ta mika mata tray din ita kuma da amsa da murmushi a samar fuskar ta
Sanda ta gama daidaita nutsuwar ta kafin ta shige d’akin ba tare da ta kwankwasa kofa ba
Fitowar sa daga bayan gida kenan ya fito daga wanka,daga shi sai towel a kugun sa
Mamakin wacce ta shigo babu sallama ne ya kama sa saboda a iya sanin sa Kursum sai dare zata dawo
Jin kaman ana kallon sa ya sa shi fadin “ke yaushe na Fara irin wasan da ke da har zaki shigo dakinmu kai tsaye”
Murmushi ta sake jin yanda ya wani juya mata baya,ajiye tray din hannun ta tayi tare da cire khimar din jikin ta(karku manta Khimar sister ce)
A hankali kaman tsoron kasa ta Fara takawa zuwa wajen sa
Bai hankara ba kawai yaji hannu na yawo a jikin sa, zabura ya yi tare da juyowa da sauri
Caraf idanuwan su ya sark’e a na juna, matsawa yayi baya kadan yana kare mata kallo saboda sam ba shi da labarin tana cikin gidan su
“I really miss you” ta fad’a tana kokarin runguman sa,matsawa ya yi baya da sauri yana bin ta da kallon da ke da wuyar fassara
Cikin tsare gida ya ce”Why are you here?”
Rola idanuwan ta tayi tace” wannan wani irin tambaya ne Amin?”
Ganin ta sake nufo sa ya sa shi dakatar da ita da hannu yana sake fad’in” na ce miye kawo ki”
“Am s…”
Cikin tsawa ya katse ta da cewa”just answer me”
Kuka ta fashe mishi dashi tare da zubewa a kasa tana fad’in” bana son ana min tsawa bana so!”
Tsaki ya ja tare da shige wa cikin d’aki abin sa nan kuwa ta kara volume din kukan ta ganin ko rarrashin ta Bai yi ba
Mikewa ta yi tare bin sa d’aki cikin kuka, a zaune ta same sa akan gado ya dafa kan sa da alamun akwai abin da yake damun sa
“Kayi hakuri mijina!”
“Ba ni zaki bawa hakuri ba! Wa wannan mahaukacin zuciyan naki zaki bawa hakuri! Haba baby abin naki yayi yawa ai! Baki ganin zan iya hakura da ke akan wannan al’amarin?”what did you say?”ta tambaye sa cikin rawar murya+
“You heard me right ba sai na sake maimaita wa ba!”ya fad’a cikin kawar da kai saboda yanda maganan take mai d’acin furtawa
Numfashi mai zafi ta furzar a ranta tana fad’in yanzu akan wannan karamin abun xai iya hakura da ni!
“Dama na dad’e da sanin baka Sona! Na san baka Sona ai kawai dai nayi shiru ne amma ba damuwa nagode tinda ka iya fitowa fili ka ce zaka hakura dani”ai kawai sai ta fashe da kuka mai tsuma rai
Zaro idanuwa yayi jin sharrin da take neman d’aura mai na cewa wai daman baya son ta
Hanyar waje ta nufa cikin kuka “Nadhira!”
Tsayawa tayi cak tare da juyowa dalilin son gaskanta ko shi din ne ya kira asalin sunan ta
“Nadhira!!”ya sake fad’a yana kallon cikin idanuwan ta da suka soma kumbura saboda kukan da ta fara
Hawayen fuskar ta ta soma sharewa saboda jin yanda zuciyar ta ke yin wasai dalilin sunan ta da ya kira for the first time of his life
“Ba wai bana son ki bane, wallahi ina mugun sonki amma wannan halin naki na rashin son yafiyan nan na damuna sosai! Yanzu misali da wannan yarinyan da kika haukatar ta mutu fa?”
“Kenan kwanan ta ne ya kare sai mu bita da Allah ya jikan ta!”ta fad’a cikin turo baki
Cikin takaici ya ce”Can you hear what you’re saying?”
“Toh fisabilillah taya mutum xai mutu in kwanan sa bai kare ba?ba ga su Momma da sisto na ba! Ai da kwanan su bai kare ba babu abinda xai sa su bar ni!”ta fad’a cikin rawar murya
“Yauwa re that’s exactly where I wanted you to land!ke karan kan ki kinsan kwanan su Momma ne ya kare so why kika yi abinda kika yi?? What you need to understand is that ba komai Aka mawa mutum ake ramawa ba,wani sa’in mukan bar abu ba dan bamu san yanda zamu fuskanci abun ba, mu kan bari ne don mun yafe ko kuma mun bari zuwa sakayyar Allah!”
“Amman dai kasan _Rama cuta ga Macuci Ibada ko?_”
Rik’o hannun ta yayi,tare da jawo ta jikin shi cikin nutsuwa yake cewa”amma baby there is limit to everything ai!”
Turo baki tayi idanuwan ta nayin rau rau alamun tana son kuka,cikin rawar murya ta ke cewa”ai limit din kenan tinda ban kashe shi ba!”
“Bana ma miki fatan kiyi kisa!amma dai kin san iyayen wannan yar aikin babu abinda suka miki amma kika haukatar musu da y’a! Yanzu misali idan su ma irin ki ne miye kike tunanin zasu miki a matsayin ramuwa?ina ga haukatar dake zasu yi kema ki sa mu a cikin matsala ko wannan tunanin bai zo miki ba?”
“Haukatar dani?”ta tambaye sa da alaman mamaki a muryar ta
Kura mata idanuwa yayi ya ce”Kwarai dagaske ko kin manta ke da kan ki ki ka ce Rama cuta ga Macuci Ibada?”
Gyada kai tayi cikin sanyin jiki,”kin ga wannan yarinyan har yau bata gama warke wa ba!Allah nasan dakyar a samu mai auren ta, please ki chanza ways din ki in ba haka ba akwai matsala babba!”
“Ku tayani da Addua ,inshaAllah bazan sake ba,komi aka min in na ga bazan iya hakura ba zan bar shi da Allah” ta fad’a cikin sanyin murya saboda gabadaya haukatar da ita da ya ce ya gama rudar da kwakwalwar ta
Murmushi ya yi tare da rungume ta a kirjin sa yana mai sauke ajiyar zuciya musamman lokacin da tudun nonowan ta ya had’u da kirjin sa
“Am so sorry!”ta fad’a a hankali,ciro ta yayi tare da cupping din fuskar ta yana fad’in
“It’s okay dear”
Murmushi ta yi tare da cewa”I missed you”
Dan zaro idanuwan ya yi ya ce”Oya show me how much you do!”
Rungume shi ta sake yi amma wannan karan ta rik’e sa sosai
“Is that how much you miss me?”
Gyada kai tayi tana sa kan ta akan fadaddar kirjin sa,girgiza kai ya yi yana cewa
“Ni bari na nuna miki yanda na yi missing din ki”
Bata hankara ba kawai taji bakin sa a nata…..Ganin suna shirin kai wa kasa ne ya sa ta ture sa kadan tana mai kawar da kan ta gefe+
“C’mon!”ya fad’a cikin shakeken murya
Matsawa baya tayi tana cewa”zan tafi kar Antynmu taga na dad’e!”
Ko magana bata bari yayi ba ta fice da sauri,zubewa yayi akan kujera tare da cusa hannun sa a cikin gashin kan sa….
Ranar Asabar…
A ranan ne ake shirin kai Nadhira gidan mijin ta, ko ina ka gani cike yake dam da jama’a
Hasanan Nadhira ce ta fito daga cikin d’aki sanye da wani dan uban su less mai shegen kyau da d’aukan ido
“Antynmu yarinyan nan fa tak’i shan komai sai wasa take mun da hankali”Hasana ta fad’a wa Antynsu
Wata yar uwan Antynsu mai suna Zuwaira ce tace”barni da ita abin ki!”
Murmushi tayi tare da cewa” gwanda kam bari na je na kai akwatunan ta saboda mijin ta ya ce za’a wuce mata da wasu zuwa Abuja anjima kadan”
“Toh adawo lafiya!”Antynsu ta fad’a inda A.Zuwaira ta wuce d’akin da Nadhiran ta ke….
8:00pm…
Kuka take yi sosai kaman zata shid’e ,yayin da fad’a da ake mata yake dad’a shiga cikin kunnen ta yana mai circulating a cikin kwakwalwar ta…
“Antynmu ki yafe mun!”ta fad’a cikin wani sabon kuka
Itama Antynsu fashewa tayi da kuka tare da rungumo Nadhira jikin ta sosai
Magana Antynsu take son yi amma gabadaya babu abinda ya ke da niyyan fitowa daga bakin ta
“Haba Amatullah wannan wani irin abu ne, kin wani zauna kina taya ta kuka! Ke kuma in baki mik’e sun tafi dake ba wallahi sai nayi maganin ki yanzu”Anty Zuwaira ta fad’a cikin fad’a saboda har ga Allah abun nasu tin yana burge ta har ya fara bata haushi
Dakyar aka banb’are Nadhira daga jikin Antynsu aka fitar da ita
Da driver da dadynsu sai kuma Hasana tare da Anty Zuwaira aka wuce da ita acewar dadynsu shi baya son hayaniya
Sanda aka damka ta a hannun Hajiya tukunna suka tafi tare da barin Hasana a wajen ta,dama kusan ba kawaye gare ta ba.
Angwaye na shigowa Hasana ta fara shirin tafiya saboda mijin ta zata bi su tafi gidan su…
9months later….
Lafiya kalau suke Zama da Kursum duk da dukkansu ba mai kula wani kuma babu yanda Amin baiyi da su ba amma basu chanza ba,yanzu kuma ya zuba musu ido yana son ganin iya gudun ruwan su…
Fitowa tayi da bulelen cikin ta wanda haihuwa yau ko gobe , sai yatsine fuska take yi
“Ya aka yi maman biyu?”Amin ya tambaye ta ganin yanda take ya mutsa fuska
“Wallahi sakwara nake son ci!”
Zaro idanuwa yayi ya ce”Sakwa miye?”
Turo baki tayi ta ce ” sakwara”
Kallon Kursum da ta wani Sha mur akan kujera tana kallo yayi
Mikewa Kursum tayi tare da wucewa bangaren ta, da kallo suka bita inda Nadhira ta tab’e baki tana cewa
“Ni fa na ce maka zan ci Sakwara!”
“Bari nayi ordering din shi ko”ya fad’a a hankali saboda yasan zata iya cewa ita shi take son yayi da kan sa ga mamakin sa kuma yaga ta zauna tare da cewa
“Toh kayi sauri!”
Ai bai san sanda ya sake murmushi ba, wayan sa ya d’auka tare da yin ordering din sakwaran a eatry
30minutes later…
Shigowar Kursum da tray a hannun ta yasa su miyar da hankalin su kanta
“Anan zaki ci ne kokuma na kai miki kan dining??”
Kallon kallo aka hau yi tsakanin junan su, ganin zasu b’ata mata lokaci ya sa ta ajiye wa a kan silk rug tare da ficewa
“Zo ki ci!”ya fad’a yana jan hannun ta, fixge hannun tayi tana cewa
“In ci miye? Kasan miye tasa a ciki zaka cemun na ci? Allah ya kiyaye! Na ma fasa cin abincin “
“Wallahi nasan Kursum bazata tab’a cutar da ke ba”ya fad’a in a defensive tune
Da kyar ta mike tare da wucewa tana zuba uwar masifa, cikin takaici ya mike shima tare da wucewa part din Kursum dama kuma chan yake da kwana yau
Akan gado yasa mi Kursum na share kwalla,cikin sauri ya karasa wajen ta tare da rik’o hannun ta
Runguman sa tayi da sauri tana cewa” wallahi bazan iya sa mata ko da maganin bacci a abincin ta ba!”
Cikin rashin jin dadin abin da Nadhira tayi yace”I know!”…
Banda safa da marwa babu abinda take yi a cikin d’akin ta, duk uwar ACn dake d’akin hakan bai hana zufa karyo mata ba
Wani siririn ihu ta saka lokacin da taji kaman an zura mata allura acikin cikin jikin ta…
Fitowan ta kenan daga d’akin ta tana son dubawa ko abincin na nan ita ta cinye kar yayi waste
Kaman daga sama taji kuka-kuka, kasa kunnen ta tayi cikin tsoro saboda dare yayi sosai kuma tasan da wuya in Nadhira bata yi bacci ba
“Wayyo Allah na!”taji an fad’a cikin wahalalliyar murya
“Innalillahi” ta fad’a a rikice tare da wucewa d’akin Nadhira
Turus tayi dalilin ganin ta a kasa, kaman wacce kwai ya fashe mata a ciki haka ta karasa wajen
“Wayyo mara ta zata balle!”ta fad’a cikin kuka sosai
Ganin yanda take yi yasa Kursum rud’ewa nan itama ta fara nata kukan…
Tsaki Amin dake jiran dawowar Kursum ya ja ganin yanda ta Jima
“Daga d’auko abinci shine taje tayi zaman ta”ya fad’a tare da sauka daga kan gadon da yake…
Tin daga kofan parlour yake jin kukan su sama-sama,cikin tashin hankali ya karasa shiga cikin parlourn a zaton sa ko fad’a suka yi
Ganin basu falo yasa shi shigowa cikin d’akin,
“Miye faru?” Ya tambaya a rikice ganin dukkansu a kasa suna kuka kaman an musu rasuwa
“Ka taimake ni danAllah zan iya mutuwa inna cigaba da Zama a haka!” Ta fad’a cikin sark’ewar murya
Cikin sauri ya karasa gare ta tare da d’aukan ta yana cewa Kursum ta d’auko khimar
Wawuro khimar guda biyu Kursum tayi tare da bin bayan su da gudu…
Tin jiya ake abu daya har washe gari, banda kuka babu abinda Nadhira take yi gabadaya karfin ta ya soma karewa
“Wai ni haryanzu ana abu daya!” Wata nurse wacce daga gani babba ce a wajen ta fad’a lokacin da ta karaso wajen
“Wallahi sai raki take mana tin dazu kaman ita zata fara labourn duniyan nan”
“Erh din! Anyi rakin ,mugaye kawai!”ta fad’a cikin kuka sosai
Basu hankara ba suka ji saukan mari, zaro idanuwa Nadhira tayi cikin kidiman jin an mare ta
Wani irin nishi mai karfi tayi ai sai ga yarinya ta fad’o wani nishin ta sake yi sai ga wata ma ta sake fad’owa
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke yayin da Hawaye masu zafi suka fara silalo ma ta, a hankali a hankali idanuwan ta suka rufe ruff….
Zaune take akan gado tana bawa daya daga cikin babyn ta nono, gefe daya kuma Kursum ne zaune rik’e da dayan babyn+
Amin da bakin sa yak’i rufuwa tin jiya ne ya shigo cikin d’akin da paper a hannun sa
Kallon su yayi ya ce”Mu tafi in kun gama shirya wa”
“Ga su ka fitar sai ka dawo ka karb’i babyn”Kursum ta fad’a tana kallon babyn hannun ta, d’aukan bags din su yayi waje dasu
Ji ta ke dama y’ar ta ce,sosai take cike da nadama, dawowar Amin ne ya hankarar da su
“Muje ko”Ya fad’a daidai ya karb’i babyn daga hannun Nadhira, sannan suka fice daga ward din
“Oops danAllah ina zuwa!”ta fad’a lokacin da suka iso gaban motan
Cikin mamaki Amin ya ce”Ina kuma zaki je?”
“Zan duba wata ne”ta fad’a tana kokarin barin wajen,
Straight inda tasan zata same ta ta nufa, a zaune ta same ta tana duba abu a takadda
Bata yi wata-wata ba ta karasa wajen tare da d’auke ta da wata gigitacciyar mari
Zaro idanuwa mutanen wajen suka yi cikin kidima,bata gama d’agowa ta kara mata wani marin
A razane matan ta karasa d’agowa tana kallon wacce ta mare ta, kun san kuma mari daya ake iya ramawa saboda in biyu aka maka firgici da mamaki bazai bari ka rama ba
“A lokacin da na ke nakud’a kin san wani irin wuya na ke sha da zaki mare ni?daga gani ma baki san zafin haihuwa ba! Saboda da kin san zafin haihuwa da ba zaki mun koda tsawa ba!”tana gama magana ta fice daga wajen inda ta bar mutanen wajen a freeze
Runtsa idanuwa matan tayi cikin tsananin firgici, a hankali ta bud’e idon inda mutanen wajen suka hau jimamin abinda ya gama faruwa yanzu…
Da murmushi ta tare su tare da shiga cikin motan, sannan suka wuce
Ko kwana biyu basu kara ba suka wuce Bauchi saboda daman su Antynsu sun so zuwa tin kafin ma ta haihu amma suka ce da zaran ta haihu zasu dawo…
Anyi suna lafiya inda yara suka ci sunan Momma da Nafhira,
After 6month…
Yara sun kara girma Masha Allah har sun koma Abuja ma
Abin da yake basu mamaki bai wuce yanda Momma bata kuka ba kuma bata fara rarrafe ba kaman yanda sisto take yi ba(Momma ake cewa Nargis, Nafhira kuma ana Kiran ta da sisto)
Gabadaya yanda yarinyan take yi bai yi kama da wanda normal mutum ke yi ba
Sosai abun yake basu mamaki nan suka garzaya da ita asibiti inda doctors suka ce basu ga abin da yake damun ta ba
A haka suka koma gida cikin rashin jin dadi
“Miye likita ya ce??”Kursum dake zaman jiran su da Sisto ta tambaya
Dan kwallan daya taru mata ta d’auke cikin rashin jin dadi take cewa”wai basu ga abinda ke damun Momma na ba!”
“Sai ku shiga ko?”Amin ya fad’a….
Bayan Shekara daya….
Duk maganin da ake yi wa Momma babu wanda yake aiki saboda yarinyan bata kara girma kullum a kwance take , bata kuka bata komai sai dai dariya kawai
Nadhira kullum cikin kuka take gashi ta Riga da ta bada Sisto ga Kursum wato Halak Malak wanda hakan ba karamin faranta ran mutanen familyn su yayi ba saboda ganin Nadhira ta yi turning into new leaf
“Baby miye zai hana akai yarinyan wajen malamai a mata Addua?”Kursum dake mawa Sisto kalaba ta fad’a a hankali gudun kar a gwatsale ta
“Ohh wallahi kin kawo shawara, bari in ya dawo sai na fad’a mai” Nadhira ta fad’a
Amin na dawowa kuwa ta fad’a mai nan yayi na’am da shawaran
Ba b’ata lokaci ya fad’a wa Alhaji a gida akan a je musu wajen Malamai….
“Wai fa dole sai sun ga maman yarinyan kafin a iya yin komai”yaji Alhaji ya fad’a daga dayan bangaren,cikin ladabi ya ce
“inshaAllah gobe zamu taho”
Nan suka yi Sallama inda ya ce wa su Nadhira su shirya washe gari zasu koma Bauchi
_BAUCHI_
Bayan sun isa Alhaji ya gayyato Malamin har gida, ba b’ata lokaci ya nemi ganin Nadhira
Cikin nutsuwa ta yi Sallama tare da gaishe da su cikin ladabi inda su kuma suka amsa mata
“Baiwar Allah miye kai ki?”shine tambayan da Malam ya jefe ta dashiKallon juna aka hau yi a cikin palourn cikin mamaki abin da Malam ya fad’a
Ita ma Nadhiran zaro idanuwa tayi tana girgiza kai alaman bata gane miye yake nufi ba
“Ki tuna da kyau akwai wani abun da kika yi wanda sam-sam bai dace ba!”Malam ya fad’a ganin she’s confused
A hankali ta ce”Ni babu abinda nayi sai ko acikin rashin sani ne!”
“Da sanin ki kika aikata abinda yayi sanadiyar ciwon wannan yarinyan!”
Cikin kidima take kallon sa barin ma yanda taga Amin ya kure ta da ido yana kallon ta
Cikin rawar murya take cewa”taya za’ayi nayi abinda zai yi sanadiyar jefa diyata a wannan halin?”
“Zaki bada amsa ne kokuma zaki tsaya tambaya!”Amin ya fad’a cikin takaici da b’acin rai
Malamin ne yayi gyaran murya yace”zaki iya tuna lokacin da kike nakud’an wa’inan yaran dakuma ranan da aka sallame ku?”
Wani yawu mai d’aci ta had’iye tana kokarin saisaita kan ta, ga wasu zafafan gumi dake karyo mata
“Hmm , mari na tayi!”ta fad’a cikin rawar murya tana kokarin miyar da hawayen ta
Runtse idanuwa Amin yayi saboda ya gane sauran abin da ya faru
“Da ta mareki sai akayi Yaya?”Malam ya sake tambayan ta
“Ramawa nay…”
Bata karasa ba taji an rufe ta da wani shegen duka,
Dakyar aka samu aka kwace ta a hannun Amin da ran ranshi ya kai kololuwa wajen b’aci
“Haba dai ! Ai bakamata ace ka dake ta ba!”
Hawayen takaicin da zubo Masa ya share cikin d’auriy yace
“Da kun bari na koya mata hankali, fisabilillah ace babu abinda ta sani sai ramuwa haba!”
“Ya isa Aminullah, abinda yakamata yanzu shine muji abinda Malam zai fad’a saboda wa’inan abubuwan da kake yi will not solve anything”Alhaji ya fad’a a hankali
Nadhira dake rakub’e a jikin Kursum ne ta kara sautin kukan ta saboda dukan ba karamin shigan ta yayi ba! Har wani ciwon ciki ta fara ji saboda ya same ta a cikin
“Shin kinsan wacce kika mara kuwa?kinsan wace ita?”Malam ya tambaye ta
Girgiza kai Nadhira tayi cikin tsananin tsoro da tashin hankali
“Toh wannan matan nada Iskokai wanda basu da sauki ko kadan,in ta matan ne babu matsala saboda mai yafiya ce, dakyar a mata abu ta rama, amma lokacin da kika je mata, akwai iska a jikin ta lokacin , ke kuma cikin rashin sa’a kika maresu ke azaton ki ita kika mara!”
“Wayyo Allah na!”ta fad’a cikin kuka sosai,
“Alhmdllh dai nasan a yau komai zaizo karshe da yardar Allah” Malamin ya fad’a yana bud’e jakan sa
Nuna kan sallayan da shimfid’a yayi tare da cewa”A mik’o min yarinyan nan”
Cikin rashin kwarin jiki Hajiya ta mik’a ta wajen da Malam ya nuna
Ruwan Addu’an dake cikin goran Malam ya bud’e tare da watsa mata da Bismillah dakuma Addu’oi d’auke a bakin sa
Wani irin kuka yarinyan ta sa mai kama da wanda ake yankawa naman jiki
Ko minti biyu ba’a yi bah jikin yarinya ya fara yankwanewa kaman jikin tsohuwa har wani furfura gare ta
Zaro idanuwa suka yi gabadayan su suna mamakin abinda suke gani a tattare da Momma
“Zaki fita ko kuma?”Malam ya fad’a cikin bada umarni
Cikin muryan tsofi Momma ke cewa” zan fita! Amma yanda kuka hana ni jin dadi nima bazan bari ta rayu ba!”
Cikin tsawa Malamin ya ce”Kiyi maza-maza ki fita yanzu!”
Chan suka ga Momma ta saki Attishawa mai karfi, kafin daga baya jikin ta ya fara dawowa daidai
Cikin sauri Nadhira ta rarrafa wajen ta, da hannu Malamin ya dakatar da ita alaman ta tsaya
Dakatawa tayi tana kallon yarta cikin mawuyacin hali,
Abu kaman wasa kumfa ya fara fitowa ta bakin Momma kankace miye yarinya ta birkici da shure-shure ko minti daya ba’a kara ba , ta ce ga garin ku nan(Allah yasa mai ceto ce)
Wani irin kuka mai cin rai Nadhira ta sake tare da karasa wajen tare da rungume ta a jikin ta
“Wayyo Momma kar ki mun haka, ki yi hakuri ki tsaya, Momma karki tafi “shine abinda take maimaita wa cikin kuka sosai
Kowa a wajen sanda jikin sa yayi sanyi barin ma yanda suka ga Nadhira na yi
Kankame Sisto Kursum tayi a jikin ta sosai zuciyar ta na tsinkewa ga hawaye shar itama a fuskar ta
“Inaaa bazan iya bayar da sisto ba! She’s mine “Shine abinda Kursum ke fad’i a cikin zuciyar ta
Alhaji ne ya karb’i Momma dakyar daga hannun Nadhira da ke turjewa wai ita bazata bayar da Momma ba
Mikawa Hajiya Yayi yana cewa aje ayi abinda ya dace,rike kafan Hajiya Nadhira tayi tana cewa
“Don’t let me lose her for the second time please, nasan Momma bacci kawai take yi,danAllah ki bani ita in goye ta”
Amin da ya zama mutumin-mutumi ne ya ce”zaki bar ta ne ko kuma?”
Jin yanda yayi magana yasa ta kara volume din kukan ta,cikin sauri Hajiya ta fizgi kafar ta tare da yin gaba saboda wani irin haushin Nadhira take gashi kuma wani irin mugun son Momma suke yi gabadayan su
Fitar da gawan Momma akayi inda Nadhira ta zube a wajen tana kuka
Sauran ma fita suka yi suka bar ta a wajen,da kyar ta lallaba ta fita daga main palourn itama
Cikin dan kankanin lokaci yen uwa da abokan arziki suka fara zuwa , harda su antynsu wanda maganan yazo musu a bazata
Ba b’ata lokaci aka sallace ta tare da tafiya da ita makwancin ta….
After 3 days…
Zaune take akan kujera ta takure kan ta a guri daya, idanuwan nan suntum kaman wacce aka daka a wajen
Ga kuma gefen bakin ta da ke d’auke da ciwon da Amin ya ji mata lokacin da ya dake ta
Shigowar Amin ne ya sa ta rufe idanuwan ta kaman mai bacci
Kallon ta Amin yayi kafin ya ce”Ke fito!”
A hankali take bud’e idanuwan ta tare da sauka a hankali saboda ita kadai tasan ciwon da take ji
Gyara zaman wuyan khimar dinta tayi saboda daman ko da yaushe shi zaka samu a jikin ta ga kuma charbi tana ja
Ganin ya wuce wajen mota yasa ta tsayawa saboda a zaton ta wasu ne suka zo mata ta’aziya
Juyowa yayi tare da hauna mata hararan da ya sata sunkuyar da kanta, kafin ya ce”Zaki tsaya a wajen ne kokuma??”
Cikin sanyin jiki ta karasa wajen tare da shiga cikin motan tana jin gaban ta na fad’uwa…
Bai tsaya da ita ko ina ba sai a gaban gate din gidan su, sauka yayi tare nufan wajen booth ya fito mata da travelling bag wanda ta taho dashi daga Abuja
Tana sauka idanuwan ta ya sauka akan bag din cikin kidima take kallon sa ,ba tare da ya bari tayi magana ba ya ce
“Ki je har sai na neme ki!”
Arazane take kallon sa tana mai jin wani irin zazzabi na kokarin rufe ta
Cikin rawar murya take cewa” kar ka mun haka Amin! Da me kake son naji? please ka taimake ni nasan abinda nayi bai dace ,danAllah kayi hakuri!”
“Hakuri zai dawo da Momma ne??”ya tambaye ta cikin takaici
“Allah zai bamu wani please karka mun haka”ta fad’a cikin kuka
Tsaki kawai yaja tare da wucewa abin sa ya shige cikin motan sa
Tsugunawa tayi a wajen tare da sakin kuka wanda hakan ya jawo hankalin mai gadin su
Fitowa yayi cikin mamakin ganin ana musu kuka a kofar gida
Turus yayi mamakin sa na dad’uwa ganin Nadhira a tsugune
Inba ya manta ba kwana 3 da suka wuce tare da shi aka sallaci yar ta, amma miye dawo da ita,Cikin sauri ya juya cikin gida don Kiran su Antynsu,
Da mamaki suka firfito amma basu bari hakan ta nunu a fuskar su ba
“Miye kike yi anan?”Dadynsu ya tambaye ta cikin kaushashiyar murya wanda yasa Antynsu runtsa idanuwa saboda yanda taji babu dadi
D’agowa tayi ta kalle sa nan ta sake fashewa da wani kuka, had’e da fara kokarin mik’ewa
Wani irin kara tasa wanda yasa su zabura saboda firgici
“Wayyo cikina!”ta fad’a da kyar tana rik’e cikin ta
Cikin sauri antynsu tayi wajen ta daman she’s pulling ne saboda kar Dadynsu ya ce ai ita ta b’ata ta
Cikin tsananin kulawa Antynsu ta ce”Miye ke damun ki a cikin?”
Wani ihu ta saki wanda yasa Antynsu matsawa baya da sauri
“Je ka fito da Mota!”ta fad’a a rikice ganin yanda suka wani tsaya suna kallon su
Cikin sauri mai gadi ya fito da motan, da taimakon Dadynsu aka samu aka shigar da ita mota wanda izuwa wannan lokacin har jini ya balle mata
Taimakon gaggawa aka hau bata lokacin da suka isa asibitin
Dakyar aka samu aka tsayar da jinin da yake zuba ajikin ta
“Alhmdllh da kuka kawo ta da sauri ai da yanzu babu labarin cikin jikin ta!”doctorn ta fad’a cikin nutsuwa
Ajiyar zuciya Antynsu ta sauk’e tana hamdala aranta…
“You don’t look happy sister!”wannan doctorn ya fad’a wa Nadhira dake kudundune akan gado
“Why would I?? Yau kwana biyar kenan da rasa y’a ta , mijina kuma ya ce naje har sai ya neme ni, how do you think I will be happy!”Nadhira ta fad’a a hankali while wani iriyan nadama ke cin ta
Rik’e hannun ta Doctorn tayi cikin tausayawa a hankali tace”shouldn’t you be grateful??”
Kallon baki da hankali Nadhira ta gefe ta dashi kafin tace”why should I?”
“Unbelievable! Last Five days kika rasa babyn ki amma baki godiya don Allah ya baki wani cikin”doctorn ta fad’a cikin mamaki
“Ciki?..”
Gyada kai tayi tana mamakin cewan Nadhira bata sani ba
“You mean ciki gare ni?” Ta sake tambaya cikin rawar murya
Gyada kai tayi mata tana murmushi,
“Thank you so much doctor,Allah na gode maka” ta fad’a out of joy
“Toh ni na tafi kafin mijina ya dawo!”
“Daga gani you really love your husband sister!”Nadhira ta fad’a cikin sha’awa
“Hmm ya na iya duk da bawai yana Sona bane amma he’s also really trying his best to make me happy and am grateful!”ta karasa fad’a da murmushi a saman fuskar ta
Cikin tausayawa Nadhira ta ce”Sorry!”
“Ni fa babu abinda ya Fi damuna sama da matar auren da yake so?”
“Matar aure kuma?”ta tambaya cikin mamaki , cos tashi daya taji gabadaya bakin cikin ta ya kau
“Erh mana, tin kafin muyi aure yake son ta!”ta fad’a sounding so free
“Ayyerh!”
“Ke don’t let me feel like that saboda mijina yana iya bakin kokarin sa a kaina and I like that cos nima bawai inason sa sosai bane kinga kuwa taimakon juna mukeyi!”ta fad’a had’e da mikewa tare da mata sai anjima….
2years later….
Sosai abubuwa dayawa suka chanza a rayuwan Nadhira duk da haryanzu Amin bai waiwaye ta ba amma she’s living good ita da twins din da ta sake Haifa da kuma iyayen ta saboda suma tin suna fushi har suka hakuri saboda basu son abun ya mata yawa
Dadynsu ma bai nemi su Amin ba saboda acewarsa ai ajiye Masa Diya kawai suka yi kuma yana da tabbacin zasu waiwayo su
Hakuri kam yanzu ba’a magana a wajen Nadhira saboda ko miye zaka mata bazata tab’a ramawa ba sai dai tayi murmushi kawai ta ce” kun ci sa’a duniya ta koya min hankali!”
Kawancen ta da doctor Maryam sai abinda ya Karu dukda sun san ita ce mijin Dr Maryam wato Ramadan wanda suka had’u a cikin jirgi
Sosai suke dawainiya da ita da twins din ta nasu shiga rai, kuma Maryam bata wani damu ba saboda a sanadiyar ta suna hira sosai da mijin ta kuma hakan yana mata dadi…
Zaune suke akan kujera dukkansu ana hira da raha
“Sister, wai miye wannan Amin din yake nufi da mu ne wai? Wallahi nida mijina mun gaji da Jira!”Maryam ta fad’a cikin raha tana kuma turo baki
“Kul yarinya ko shi mijin naki yayi karya ya ce yana Jira na, moreover har yanzu ina son Amin dina kuma nasan shi ma yana Sona, saboda haka you guys should back off!”ta fad’a tana murmushi, aranta kuma tana tunanin irin kykyawan zuciyar Dr Maryam
“Ku dai yi ku gama, nida yarana zamu je shan ice cream!” Ramadan ya fad’a had’e da mikewa yana mai Kiran twins din ta akan su zo su tafi
Nan kuwa sai ga wasu cute babies, mace daya namiji daya sun fito cikin tafiyan su da bai kama kasa sosai ba
D’aukan su yayi yana cewa “say bye-bye to your Mommies!”
Nan suka yi waving nasu suna dariya saboda yaran akwai son yawo babu karya…
Ko awa daya basu yi da tafiya ba aka aiko Kiran a waje
“Bari na zo sister!” Ta fad’a tana gyara khimar din ta wanda yake har kasa saboda gabadaya bata yarda ta zauna babu khimar a jikin ta koda kuwa a cikin d’aki ne
Tana fita gaban ta yayi mugun fad’uwa saboda wanda ta gani a tsaye ajikin mota
Ya kara kyau sosai har wani tumbi ya ajiye wanda hakan yasa murmushin farincikin sub’uce mata
Wayan sa da yake dannawa ya sa acikin aljihun jampan sa yana mai cizon labban sa
Ganin yana shirin yana kallon ta yasa ta had’iye murmushin ta
Kallo daya.ya mata ya d’auke kan sa yana dad’a tsuke fuskar sa dukda uban kyan da ta masa
Cikin mutuwan jikin ganin yanda yayi ta karasa wajen sa
“Ina wuni!” Ta gaishe sa cikin nutsuwa
Ba tare da ya amsa ba ya mik’a mata takaddan hannun sa
Gaban ta ne yayi mugun fad’uwa cikin tashin hankali take cewa”miye wannan din?”
“Takaddan sakin ki ne!”ya bata amsa tare da cilla mata papern sannan ya shige cikin motan sa
Girgiza kai ta fara yi tana kokarin daidaita kan ta wajen motan ta nufa tana cewa
“Ka taimaki rayuwa ta ka tsaya Amin! Wallahi am now a changed person ka tambayi ko ma waye zai fad’a maka please don’t do this to me !”
“Zama dake ne Naga bazan iya cigaba da yi ba Allah ya had’a kowa da rabon sa saboda saki uku chur na miki!”
Gabadaya notin kan ta ne suka soma tsincewa wanda hakan yayi daidai da shigowan su Ramadan da Twins dinta
Ai kaman Jira take kawai ta fashe da kuka wanda yasa suka karaso wajen ta da sauri
Ramadan kuma ya d’auki takaddan da ya gani a kasa tare da warwarewa…
“Mumy!”shine abinda da yaji an fad’a,dakatawa yayi daga tada motan tare da kallon waje
Caraf idanuwan sa ya sauka akan su twins da alokacin suma sun fara kuka dalilin ganin mama su na kuka
Gaban sa ne yayi mugun fad’uwa ganin kamannin Late Momma da kuma shi atattare da yaran
Nan ya fara tambayan kansa y’ayan waye wa’inan yaran…
“Sister!”Nadhira ta fad’a cikin kuka lokacin da dr Maryam ta karaso wajen ta
Cikin mutuwan jiki dr Maryam ta tsuguna a gaban ta tare da rungume ta , cike da tausayin ta wani babin na zuciyar ta kuma cike da farinciki mara misaltuwa ganin mijin ta zai sami Nadhira kuma ita ma zata samu yar uwa da kuma abokiyar zama
Antynsu dake tsaye a bakin kofa tana kallon su ne ta karaso wajen
“Antynmu,Amin ya sake ni!wayyo Allah na yarana danAllah kar a rabani da su !”ta fad’a cikin kuka
“Babu wanda ya isa ya raba ki da yaran ki a fad’in duniyan nan sai dai wani ikon Allah”Antynsu ta fad’a cikin tausayawa tare da mikar da ita
“Za ka iya barin mana gida tinda ka gama abinda ya kawo ka!”Antynsu ta fad’a wa Amin dake kallon su ta windown mota
Cikin mutuwan jiki ya tada motan sa tare da wucewa, ikon Allah ne kawai ya kai sa gida, saboda ganin yaran ba karamin hargitsa shi yayi ba, he was so shocked kuma yana da tabbacin cewan yaran sa ne.
Kursum ce ta dafa shi tana cewa”Miye faru?”
“Na rasa ta!”
Sakin sa tayi tare da zama akan kujera tana cewa” miye sa ka sake ta?”
“Gani nake bazan iya facing nata da duba ga irin lokutan da na d’auka ban neme ta ba”ya fad’a cikin rawar murya
“We don’t have to run away to solve problems, we ought to face the problems to solve them!”Kursum ta fad’a cikin kwantar da murya
“Ashe she was pregnant! Na same ta da yara!”
“And you still went ahead to give her the divorce letter!”
“I wasn’t aware of babies until after I gave her the divorce letter!”ya fad’a cikin takaici
Cikin mamaki tace”Babies!”
Ba tare da ya amsa ba ya shige cikin d’aki yana mai tunanin yanda zai yi facing Alhaji game da batun cewan shekara na biyu kenan da Nadhira bata wajen sa kuma ya sake ta!…
Tashi daya Nadhira ta rame wanda hakan ba karamin damun su yayi ba,
Alhaji har zo kuma ya basu hakuri sosai game da abin sa ya faru , kuma shi bai da masaniyar abinda yake faruwa sai kwanan nan
Dadynsu nuna mar yayi akan babu damuwa har da gayyatan sa d’aurin auren yarsa wanda sam-sam Alhaji bai d’auka Nadhira ba ce…
Zufa ce ke karyo masa ta koina na jikin sa , he’s so out of words jin wai har an d’aura auren Nadhira da wani daban bayan sakin da ya mata mai Fi sati biyu ba
Ai nan ya tada borin cewan dole.sai an basa yaran sa saboda bazasu je agolan ci gidan wani ba
“Baka da kunya ma! Bayan baka ma san tana da ciki ba! Baka san wahalan da tasha ba amma don kaga ta sake wani aure ka ce a baka yaran ka!”Maryam ya fad’a cikin takaici
Cikin fushi Ramadan”Mu had’u a kotu saboda nasan nan ne kawai za’a kwatar mata y’ancin ta!”
Jin ansa kotu acikin zancen yasa jikin Amin yin sanyi
“Kuyi hakuri bai san abinda yake fad’i bane shiyasa”Alhaji ya fad’a ya hararan Amin
Da kyar dai Ramadan ya yarda aka bar maganan zuwa kotu din saboda a ganin sa wannan bakaramin rainin hankali Amin yake shirin bullo musu da shi…
A gida kuwa tattas aka mawa Amin harda cewan yaje ya basu hakuri
Tare da Kursum suka je bada hakurin inda a lokacin ne ake shirye shiryen kai Nadhira d’akin ta
“Ai komai ya wuce yanzu kam , balle ma nice architect din jawo duk abinda ya faru! Allah ya yafe mana gabadaya!”
Ameen suka amsa mata gabadayan su
“Ai mune da godiya daman ance matar wani bata auren mijin wata kuma rabon za’a sami yara ne ya kai Nadhira d’akin Amin so yanzu kuma sai dai mu ce Alhmdllh mu kuma Allah ya bamu zaman lafiya a tsakanin mu!”
Cikin farinciki suka amsa da Amin.!
Alhmdllh!!!A nan na kawo karshen littafi na mai suna ABAR SO,