ABDULLKADIR CHAPTER 1

ABULLKADIR




CHAPTER 1






DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI 1

*

Tsaye yake jikin bangon wajen, lokaci zuwa lokaci yakan saka hannun shi cikin sumar kan shi, bazai iya tuna ranar karshe da wani abu ya daga mishi hankali haka ba, yanayin yake ji ya zame mishi bako. Kayan da yake jikin shi yabi da kallo, gajeran wando ne na kakin sojoji da ko gwiwar shi bai taba ba, sai rigar wandon mai yankakken hannu, wuyan shi da alamar sarqar da baka ganin kota mecece, sai shi da take wuyan shi, wani dan dogon karfe ne maqale a jiki da yake dauke da sunan shi da kuma lambar aikin shi, dan lokutta da dama idan mutuwa ta gifta, sarqar ce kawai shaidar gane waye da waye ta runtsa da shi.

Duk da kalar kakin bai hana shi ganin jinin daya bata kayan ba, jinin da kallon da yake mishi yasa wani abu tsinkewa a cikin shi, baida kalmar dazai dora abinda yake ji, saboda jini baya daga mishi hankali, ko kafin aikin shi yana da wata irin dakakkiyar zuciya taban mamaki, yau shine yakejin alamun zufa a goshin shi da ganin jini a jikin rigar shi.

“Paapi zan sha ruwa…”

Muryar Fajr ta doki kunnuwan shi tana tuna mishi cewar bashi kadai bane a wajen. Dan juyawa yayi yana kallon su, Fajr da yake cikin shekarun shi na biyar yanzun, dan dai yana da girman jiki da tsayin da zaisa kai tunanin ya wuce shekara biyar din da baima karasa ba, yana zaune da kanwar shi da duka watan ta hudu a duniya, yanda ya riketa dam yana sa Abdulkadir leqa yarinyar yaga ko tana numfashi.

“Wanne irin riqo kai ma Ikram haka?”

Kallon shi Fajr yayi yana shagwabe mishi fuska, dan shi ya gaji da rikon yarinyar.

“Ni ina so in sha ruwa. Paapi, Omma fa?”

Hannu Abdulkadir ya mika yana karbar Ikram din daga hannun Fajr, bacci take hankalinta kwance, dan daquna fuska yayi yana son tuna ko ya taba jin kukan yarinyar tun dawowar shi, bata da rigima ko kadan. Idanuwan shi yake hangawa ko zai hango inda zai samo ma Fajr din ruwa batare daya bar wajen ba, bayason motsawa daga inda yake ko likitan zai fito da wani bayani. Kasan zuciyar shi yake ji wani abu tamkar bargo da yake ta haduwa yana kara kauri, yasan shi yake so ya lullube da rashin gaskiyar da yake yawata mishi a ko ina na jikin shi.

“Fajr ina zan ga ruwa anan?”

Ya fadi, yana gyarama Ikram kwanciya akan kafadar shi, yanda ta kwantar da kanta a jikin shi na nutsar da kadan daga cikin abinda yake ji. Daga idanuwa ya sake yi ya kuwa sauke su kan Mami da ta turo kofar glass din wajen tana takowa, yanzun yake dana sanin kiranta da yayi, amman lokacin daya kira din a rikice yake, baisan abinda ya kamata yayi ba, ita tace ya dauko Waheedah din ya kawota asibiti, daya tashi saiya kwaso harda su Fajr.

Aminu ya hango ya rufo mata baya, sai kuma Salim da Zainab. Ya manta yanda yan gidan su suke, yanayin aikin shi ya manta yanda ko kurjewa kayi indai za’a kaika asibiti mota daya tayi kadan, dan kusan rabinsu sai sunje, in kuka jima baku dawo ba zakuga sauran rabin da aka bari a gida sun biyo bayan su, yana tunanin duk wani asibiti da suke da file a garin Kano sun san Yan gidan Bugaje da wannan al’adar tasu, ba’a ma hanasu shiga. Suna karasowa Zainab ta mika hannu tana karbar Ikram daga hannun shi, baiyi musu ba ya mika mata ita.

“Ya jikin nata?”

Mami ta tambaye shi, idanuwan shi ya sauke kasa yana tsintar kan shi da kasa hada idanuwa da ita. Sai dai kafin ya amsa Fajr ya riga shi da fadin

“Mami Omma ta fadi, jini mai yawa a kanta…”

Hannu Mami ta miqa ma yaron daya taso yana kama hannunta hadi da zagaya dayan hannun nashi jikin kafafuwan ta, daga idanuwan shi yayi yana saukewa cikin na Abdulkadir da yake tsaye, harshen shi yake ji ya mishi nauyi, dan ya kasa amsa ma Mami tambayar da tai mishi. Rashin gaskiya ne shimfide a fuskar shi. Da wani irin yanayi da yake ji ya mishi wani iri Fajr yake kallon shi, sosai yaron yake kallon shi yana kara shigewa jikin Mami, idanuwan shi na cikin na Abdulkadir yace

STORY CONTINUES BELOW


“Paapi ne yai pushing (Turewa) dinta ta fadi… Mami Paapi ne…” 7

Wani irin shiru ya biyo bayan maganar yaron, shiru ne da hayaniyar shi tafi ta surutu, dan ko wani yazo wucewa shirun da yake wajen zai iya taba shi, dakuna fuska Abdulkadir yayi yana son nemo kalmar abinda ya lullube shi.

‘Kunya’

Wata murya ta furta can kasan kwakwalwar shi, sai dai shida kunya nada wata irin tazara da bazata misaltu ba, bata taba kamo shi ba ko acan ba, baisan ma ya akan jita ba, kai tsaye yake dukkan al’amuran shi, yau kam ba kamoshi kawai tayi ba, lullube shi tayi ruf, bargon rashin gaskiya mai kaurin gaske na bin bayanta, numfashin shi ma kamar a lissafe yake jin fitar shi.

“Mami kinga abinda nake ce miki ko?”

Aminu ya fadi yana korar shirun da yake kewaye da wajen.

“Aminu…”

Mami din ta kira cike da kashedi, akan ce yaro baya karya, musamman mai karancin shekaru kamar Fajr, sai dai yaran yanzun kuruciyar su cike take da abin mamaki, bakomai daya fito daga bakin su bane abin yarda, hakan shine take ta fadama kanta dan karta yarda da abinda Fajr din ya furta, duk da yanayin Abdulkadir din ya gasgata maganganun yaron nashi, amman batason ta yarda da hakan. Sam bata kula da girgiza mata kai da Aminu yake ba saida yace 4

“Karki ce inyi shiru wannan karin ma, kina jin abinda Fajr ya fadi, Wallahi na jima da sanin Hamma Abdulkadir ne ajalin Adda Wahee…”

Cikin tashin hankali Mami ta kalli Aminu din, yanayin kallon na sakashi kasa karasa maganar da yake, dauke idanuwan shi yayi daga kanta yana watsa ma Abdulkadir da yake tsaye wata irin harara, wani daci Aminu yake ji a kasa makoshin shi, ba tun yanzun Abdulkadir ya gama ficewa daga ranshi ba, Mami nace mishi Waheedah ta fadi ta fasa kai ya san Abdulkadir nada hannu dumu-dumu cikin faduwar tata, sai dai ko kadan bai hango sanadin zai zamana da hannun shi ba, ya dauka bacin ranshi ne ya sata faduwa tunda duk sun san tana da hawan jini.

Da yana da iko kan igiyar auren Waheedah da Abdulkadir da tuni ya sa almakashi ya datse ta, datsar da babu hanyar da za’a abi a sake daurata har abada.

“Hamma…”

Zainab ta kira cike da wani yanayi dayasa Abdulkadir din sake kasa da kan shi, dan koya dago ma bashi da kalaman dazai musu amfani dashi, baisan me zaice musu ba, yawan magana ba dabi’ar shi bace ba tunda can, ko da yana da abin fadi kuwa, ballantana yanzun da babu abinda yake so kamar kasa wajen ta bude dai-dai inda yake tai kasa dashi. Kafin ta sake cewa wani abu likitan ya fito daga dakin da Waheedah take, wasu Nurses guda biyu na biyo bayan shi. 1

Idanuwan shi ya sauke kan Abdulkadir, sai dai kafin yace ya bishi office kamar yanda Mami tasani ta riga shi magana da fadin

“Ni mahaifiyar tace, wannan kannen tane, duk abinda zaka fada mishi zai mai-maita mana ne, gara ka fada anan din kawai…”

Abdulkadir din dai likitan ya sake kallo, kai yadan jinjina mishi a hankali yana bashi izinin yin magana, numfashi ya sauke tukunna yace

“Babu wata matsala In shaa Allah, munyi mata karamar tiyata saboda buguwar ta shiga sosai…badai yanzun zata tashi ba, amman zaku iya shiga ku ganta, banda yawan surutu dan Allah, kar a tasheta, tana bukatar hutun sosai ko dan jininta da ya hau fiye da na da…” 1

Kai Mami ta jinjina tana mishi godiya tukunna ya wuce, hannun Fajr ta kama tana raba Abdulkadir ta shiga cikin dakin, daga inda take tsaye tana hango ramar da Waheedah tayi, tayi wata irin ramewa da duk da idanuwanta a rufe suke kana ganin ramin da yake kasan su, kanta nannade yake da bandeji, hannunta daure da karin ruwa. Wani irin abu Mami taji ya matse a cikin zuciyarta, a hankali ta taka tana jan kujera ta zauna, ta dora Fajr kan cinyarta. Hannu yaron yakai kan jikin Waheedah

STORY CONTINUES BELOW


“Omma…”

Ya fadi, Mami na kama hannun shi ta janye

“Karka tashe ta Fajr, bacci take kaji…”

“Ni zan sha ruwa…”

Fajr ya fadi yana sa Mami din juyawa ta kalli Aminu da suma duk sun shigo dakin. Kafin tayi magana Salim yace

“Bari in karbo… Ruwan kawai ake bukata? Ko zan taho da wani abin…”

Waheedah ta kalla, tasan babu abinda Abdulkadir ya dauko, hakan yasa ta fadin

“Ka fara kawo ruwan dai, sai kazo kuje gida kai da Zainab akwai yan abubuwan da zaku dauko mana…”

Kai Salim ya jinjina mata yana juyawa ya fice daga dakin. A bakin kofa yaga Abdulkadir a tsaye, kallon shi kawai Salim yayi yana girgiza kan shi, tukunna ya wuce, kan kujerun da suke wajen Abdulkadir ya karasa yana zama, yau gabaki daya nasa shi jin abubuwan da yake tunanin yayi bankwana dasu shekaru da dama da suka wuce, yanzun kallon da Salim yai mishi yasa shi jin wani irin abu na lullube shi, so yake yaga halin da Waheedah take ciki, amman ya kasa shiga dakin, kunyar hada idanuwa da Mami yake ji, bazai iya shiga in tana nan ba. Kanshi ya saka cikin hannuwan shi yana dafewa. Tunanin barkatai na soma kawo mishi ziyara.

*

Salim na kawo ma Fajr ruwan suka juya su duka ukkun, harda Aminu, dan Fajr dinma manne musu yayi, dole ta karbi Ikram daga hannun Zainab, towel din da yarinyar take ciki tayi amfani dashi ta goyata. Tukunna ta danyi dabara ta zauna kan kujerar dakin, tunda ta rubber ce. Shisa tace har babbar darduma a dauko musu. Sosai ta nutsar da hankalin ta kan Waheedah, hannunta da ya kara zama siriri, daman abinka da ba qibar kirki ba, yanayin kaddarar yarinyar nasa idanuwan Mami din cika taf da hawaye.

Tana da hakuri da kauda kai tasani, amman na Waheedah yayi yawa, ita ko baki ba zata iya budewa tace ana mata abu ba, in kuma ka tambaya murmushi kawai takanyi

‘Mami rayuwar duka babu yawa, komai zai wuce kamar bai faru ba’ 3

Shine maganar ta a ko da yaushe idan kaso sanin halin da take ciki, da ba’a ganewa in baka kula da yanayin ramewar da take a tsaye, ko murmushin ta da baya kaiwa cikin idanuwan ta ba, to ita dai kam Mami zata iya cewa tun yawon arba’in din Ikram da tazo musu rabon da ta sakata a idanuwan ta, sai dai a waya, ta kuma hana su Aminu kawo mata zancen gidan Waheedah din, dan haka ko sun kula da wani abin in sunje ba zuwa suke suna fada mata ba.

Batasan iya lokacin da ta dauka a zaune a wajen ba, sai da taji sallamar su Zainab din, amsawa tayi a hankali, yawan su na bata mamaki, kusan su duka gidan suka dawo, kasa-kasa suke magana, tarkacen da taga sun kwaso zaka rantse watanni zasuyi a asibitin, da alama abincin ranar da duk basuci bane ba zasuci shi yanzun a asibitin. Kujera Zainab ta mikoma Anty, dan a wajenta ma sukaje suka amshi abinci suke fada mata Waheedah na asibiti, ta biyosu suka taho tare.

“Haj. Halima wai dagoki sukayi kenan”

Mami ta fadi, Anty na zama da fadin

“Ai baki kyauta mun ba, ko ba zaki shigo ki fadamun Waheedah na asibiti ba ai saiki aikomun ko? Ke ce zaki kwana da ita?”

Murmushi kawai Mami tadan yi, daman tayi niyyar Zainab ta kwana ne, ita da dare saita tusa su Aminu a gaba, kirkin Anty bazai gaji da bata mamaki ba.

“Ya jikin nata?”

Anty ta tambaya

“Gata nan dai bata tashi ba har yanzun…”

Mami ta fadi, su Nabila da suka fara fada da Salim Anty ta kalla

“Zanci ubanku wallahi, ku kamar kaji bakwa zama waje daya?”

Harara Salim yake watsa ma Nabila

“Anty hannuna ya fara taba plate din…”

STORY CONTINUES BELOW


“Ni na riga gani, Anty kice yabarmun suci dashi da Aminu…”

Nabila ta fadi a tabare, Salim na samun damar fisge plate din.

“Kuci tare ke da shi…”

Shagwabe fuska Nabila tayi, idanuwanta na cika da hawaye

“Ni bazan ci dashi ba”

Numfashi Anty ta sauke

“Na sake magana akan ku saikun koma gida, tunda ba yara bane ku, da ina sanyin surutu dana taho da Albarkah…”

Sanin halinta yasa suka nutsu, tare suka zuba abincin, tana kallo suna kaiwa cokulan juna karo, dauke idanuwanta tayi daga kansu, dan sun saba, kullum cikin fada suke, ko makaranta zasu je haka suke kamar kaji, kuma ta rasa kalar fadan nasu, randa ya jibgeta kuma tana kuka haka zata bishi su tafi tare. Indai kace zaka shiga rigimar su kaine zaka sha kunya.

“Ikram ce kika goya haka?”

Anty ta tambaya tana daga hijab din Mami, taga yarinyar ta farka tana ta kalle-kalle.

“Idon ta biyu ma…”

Cewar Anty

“Ikon Allah…”

Mami ta fadi tana mikewa ta kwance goyon tana sauko Ikram

“Ke baiwar Allah babu magana…”

Inji Mami tana gyarama Ikram din zama, da alamu hakurin mahaifiyarta ta biyo, sam yarinyar bata da rigima, ruwa ta karba ta zuba a murfin tana ba Ikram din

“In kuma basa ba yar su ruwa fa?”

Anty ta bukata

“Nidai ai na bata, wannan shirmen nasu na zamani ba dani za’ayi shi ba, cikin su babu wanda ba’a bama ruwa ba, meya same su?”

Dariya Anty tayi

“Ni kaina bazan iya ba wallahi, gani nake daukar alhaki ne…”

Hira suke a hankali a hankali, Anty ita tasa Mami dan tsakurar abinci, dan damuwa ce fal ranta.

“Ba za’a zuba a mika ma Abdulkadir ba kuwa? Yana wajen nan”

Mami ta fadi tana sa Anty kallon ta

“Ni rabani da wannan dan Allah, ya koma gida yaci wajen dayar matar shi, ban zubo abincina da shi ba nikam”

Shiru Mami tayi, sai dai duk yanda taso ta nuna halin ko in kula da Abdulkadir din sai ta kasa, Ikram ta mikama Anty tana mikewa ta taka zuwa kofa tasa hannu ta bude dakin tana leqa kai, yana zaune kuwa ya hade kanshi cikin hannayen shi.

“Abdulkadir…”

Ta kira a hankali tana kallon yanda ya dago kai, idanuwan shi sun sauya launi. Yanayin kaddarar su na mata nauyi

“Ba zaka shigo kaganta ba?”

Abinda yake son yi kenan, amman ya kasa, yanzun dinma kunyar Mami tasa shi sadda kanshi kasa yana kasa cewa komai.

“Ka shigo ka ganta…”

Mami ta umarta, sai da taga ya mike tsaye tukunna ta dawo da kanta cikin dakin, a hankali ya tako yana shigowa, daga bangon kusa da kofar ya tsaya yana jingina bayan shi a jiki, inda Mami take zaune ta koma tana zama, idanuwan shi ya tsayar kan Waheedah da nata suke a rufe da alamun bacci, duk da haka yana jin gabaki daya idanuwan su na yawo a jikin shi, ya zabi yaki kallon sune kawai dan bayason yaga kallon tuhumar da suke mishi.

Zuciyar shi yaji tayi tsalle tana shirin dawowa cikin makoshin shi, kafin ta koma mazauninta tana ci gaba da wata irin dokawa da yake ji ba cikin kunnuwan shi kawai ba, har a ko ina na jikin shi, bai tsammaci Waheedah zata bude idanuwan ta data sauke cikin nashi ba.

STORY CONTINUES BELOW


“Waheedah… Alhamdulillah…”

Yaji muryar Anty ta fadi, yana kuma jin motsin kannen shi da suke mikewa suna tahowa sukai ma gadon Waheedah din rumfa, yadai daina gane me suke ta fada, saboda har lokacin idanuwan Waheedah na cikin nashi, kallon shi take da wani irin yanayi da yasa zuciyar shi rawa. Yasha ganin yanayi da dama cikin idanuwanta, kaunar shi na daya daga cikin yanayoyin da suka rinjayi sauran, suka rinjayi lokuttan da ko a kasan bata mata ran da yakan gani akwai kaunar shi. Wannan yanayin bakone, kuma bazai ma kan shi karya ba, ya soma ganin alamun shi wajen kwana hudu da suka wuce. Sai dai duk idan yaga giccin yanayin yakan ga alamun kaunar shi da yake son rinjayar ko meye din yake gani.

Yau kam kallon ta yake, duba idanuwanta yakeyi sosai yana neman alamar kaunar shi a cikin su ya rasa, a hankali yake girgiza mata kai, akwai inda ta boye soyayyar shi, ba zatai mishi haka ba, Waheedah ce yasani, kaunar shi bangare ce na rayuwarta da bata boye mishi, ba zata fara ba yau, bakin ta yaga ya fara motsawa kafin yaji dirar muryarta cikin kunnuwan shi da fadin

“Mami dan Allah ku ban waje inyi magana dashi…”

Bazai ce ga asalin abinda yake ji ba, amman yasan bayason subar dakin, bayason fuskantar ta, a karo na farko da yake son gujema fuskantar wani abu, bai taba hango zuwan ranar nan ko a mafarkin shi ba.

“Ko ruwa ki sha…”

Anty ta fadi, yana kallo Waheedah ta girgiza mata kai, har lokacin shi take kallo da yanayin nan cikin idanuwan ta.

“Ina son magana da shi dan Allah…”

Ta sake furtawa, yana kallon daga Mami har Anty suna mikewa, su Salim suka fara wucewa suna fita daga dakin. Anty ce karshe, bata fita ba sai da ta dan tsaya tana mai wani irin kallo kamar tana son yawo da idanuwanta cikin zuciyar shi ne taga abinda yake boyewa kowa, tukunna ta fice tana turo musu kofar.

“Ka zo ka zauna…”

Waheedah ta fadi, daga inda yake taga ya girgiza mata kai. Zuciyarta take jin ta daskare a kirjinta, ta dunqule waje daya kamar dutse, ta dauka datai hakan ba zatai mata ciwo ba, ba zata ji yanda take dukan kirjinta da wani yanayi da yake barazana da numfashin ta ba.

“Magana zamuyi Abdulkadir…”

Ita kanta saida taji sunan ya dira cikin kunnuwanta da wata murya da tasa jikinta bari, balle Abdulkadir da yake jin kafafuwan shi na rawa, yaune karo na farko a tsayin rayuwar shi data furta sunan shi kai tsaye haka.

“Waheedah…”

Ya kira da bayanannen mamaki a fuskar shi da muryar shi.

“Idan ba zaka zauna ba shikenan”

Cewar Waheedah cikin sanyin muryarta din nan, da yau yake taba shi a wajajen da baisan akwai su a jikin shi ba.

“Waheedah…”

Ya sake kira yana jiran hakan yai tasiri a kanta kamar ko da yaushe. Sai dai cikin idanuwanta yake ganin katangar daya kasa ko motsi balle yayi wani abu akanta tana ginuwa a tsakanin su, kai yake girgiza mata a hankali, kamar hakan kadai ya isa ya hana abinda yake faruwa ya faru.

“Aurenka zaka saukake mun!”

Maganar ta jima tana mishi yawo kafin ta samu wajen zama tana sa shi kokawa da shaqar numfashin da yakeyi ta hanci, bude baki yayi yana soma shaqar iskar ta bakin shi ko zata wadace shi, yakai mintina biyu a haka kafin yaja wani irin numfashi, budaddiyar muryar shi na sake budewa da wani yanayi yace

“Karki sake mun irin wasan nan, bana so, karki sake” 3

Wata dariya tayi da sautin ta yai mata wani iri har a cikin kunnuwanta, kafin wasu hawaye masu dumi da bata da iko dasu suka zubo mata

STORY CONTINUES BELOW


“Ba wasa nake ba, Sadauki ba wasa nake ba”

Lumshe idanuwan shi yayi yana bude su, Sadaukin da ta kira shi na rage bugun da zuciyar shi take yi, yana kuma bashi karfin raba jikin shi da bangon wajen yana karasawa inda take yaja kujerar ya zauna gab da gadon nata, hucin numfashin shi da taji kan fuskarta na sata runtse idanuwan ta, wani irin abu na tsirga mata har kasan zuciyarta, sanannen yanayin da takan ji duk idan yai kusa da ita haka take jira ya dirar mata, amman shiru, babu ko alamar shi, hakan yasa ta bude idanuwan nata tana jan jikinta ta mike zaune, bayanta ta jigina da gadon da take kai tana kallon shi.

A duk jikin ta take jin lokacin da take jira yayi, lokacin da batasan ta dibarma zama dashi ba sai yanzun take ji har a kasusuwanta ya cika

“Ka saukakemun auren ka”

Ta sake maimaitawa, wannan karin shi yai wata yar dariya yana kallon ta kamar ta samu tabin hankali

“Doctor din nan yace babu wata matsala, haka yace baki samu wata matsala ba…”

Abdulkadir yake fadi, maganganun Waheedah din na tabbatar mishi ta samu matsala a kwakwalwar ta, da hankalinta ba zata furta mishi wannan kalaman ba, bazai kusa da ita haka ta sake maimaita kalaman ya saukake mata auren shi ba. 1

“Ki kwanta ki huta sosai kina jina?”

Yai maganar yana daga mata girar shi, cikin yanayin da take jira hannunta da taji ya motsa ya sauka akan fuskar shi, sai taji shi akan tata fuskar tana shafa kuncin ta, cikin yanayin daya sashi saurin fadin

“Waheedah…”

Wasu hawayen taji da suka fi na dazun dumi sun sake zubo mata.

“A gaban yarana, Sadauki a gaban yarana…” 4

Take fadi tana jin wani daci na taso mata daga kirjinta, kalmar hakuri na daya daga cikin kalaman da baya amfani dasu, shisa yanzun da yake neman ta inda zai fara furtawa ya kasa, indai abinda take son ji kenan zai kokarin furta mata ko zata dawo cikin hayyacinta.

“Ka saukakemun auren ka, dan Allah ka saukakemun auren ka”

Take fadi tana kamo hannun shi, da sauri ya rike hannun nata yana dumtse wa, yanajin siraran yatsunta da suke barazanar ballewa kowanne lokaci cikin nashi, suna saka shi sassauta rikon dayai mata

“Bakisan me kike fadamun ba ko? Baki san kalaman da suke fitowa daga bakin ki ba”

Abdulkadir yake maganar yana yawata idanuwan shi kan fuskarta, yana so tagan shi, yana so taga shine Abdulkadir. Kamar tasan hakan yake nufi ta furta

“Nagan ka…ka yarda dani naganka, na kuma san me nake fadi. Ka saukakemun auren ka nace, kuma wallahi da gaske nake… Dan Allah sadauki”

Waheedah ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata, ji take in ta kara kwana daya da igiyar auren shi a kanta hauka zatayi.

“Kaji dan Allah…”

Hannun ta ya saki yana jan kujerar shi baya, kai yake girgiza mata, baisan akwai wani waje mai laushi daya rage a zuciyar shi ba sai yanzun da Waheedah tasa kalaman ta dai-dai wajen tana dannawa. Yana alaqanta wannan hargitsin da yake ji da yanda ya jima baiji tashin hankali ba. A gaban shi abokan aikin shi babu adadi suka tarwatse, wasu daga sassan jikin su na dukan jikin shi harda fuskar shi, a gaban shi harsashin bindiga yasha fasa kan abokan aikin shi, mutanen daya yarda dasu da rayuwar shi, mutanen daya kwashi shekaru yana kwana waje daya dasu a karkashin kasa ko a samanta. Bayajin akwai sauran tashin hankalin dazai gani ya taba shi, asalima ya dauka ya jima da katange zuciyarshi da faruwar hakan.

Sai yanzun da Waheedah take karyata shi, take nuna mishi raunin katangun daya gina.

“Dan Allah Waheedah…kinji… Dan Allah ki daina mun wasan nan”

STORY CONTINUES BELOW


Da mamaki take kallon shi, take hango raunin da bai taba bari tagani ba, da sati daya daya wuce ne taji taushi irin wannan a muryar shi, ta hango rauni haka a cikin idanuwan shi, da tana da tabbacin zuciyarta ta gama narke mata da soyayyarshi da ta jima tana dawainiya da ita, da yanzun tana jikin shi ta rike shi cike da tsoron kar tabar kofar da wani abu zai sake shiga tsakanin su fiye da yanda ya riga da ya faru, amman yau babu abinda hakan ya kara banda sa zuciyarta yin wani taurin fiye da yanda takejin ta a kirjin ta.

Ganin da gaske bai dauka cikin hankalinta take magana ba yasa ta fadin

“Mami…”

Cikin wani sabon hargitsin Abdulkadir yake kallon Waheedah da take hawaye kamar an bude wani abu.

“Mami!”

Ta sake fadi da karfin da yasa Mami turo kofar babu shiri, ganin kukan da Waheedah take yasa Mami fadin

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un….Waheedah? Me yake faruwa haka?”

Salatin da Mami tayi yasa Anty biyo bayanta tana ma su Salim alamar dasu tsaya nan inda suke karsu biyo su, ita ta karasa da sauri gefen Waheedah din ta zauna tana rikota jikinta. Kuka Waheedah take kamar numfashin ta zai dauke, kallon ta Abdulkadir dake zaune yake yana jin shi kamar a mafarki, yana jin shi shirun da yaji lokacin da bomb ya fara tashi da abokan aikin shi a karo na farko a gaban shi, shiru ne da bai taba fatan ya sake jin irin shi ba, bai dauka akwai abinda ya isa ya sake saka shi jin irin shi din bane bama, sai yanzun.

“An…Anty…”

Waheedah take fadi tana jin numfashin ta na mata wani sama-sama.

“Waheedah dan Allah ki daina kukan nan… Kinji…duk gamu nan, ko ma menene, muna nan tare dake, kina jina?”

Kai Waheedah take girgiza ma Anty tana ci gaba da wani irin kuka da yasa jikin Mami yin sanyi, dan ita kam tana tsaye ta rasa abinda ya kamata tayi

“Anty kuce ya saukake mun, dan Allah kuce Sadauki ya sakeni!”

Ba Abdulkadir din ba, har su Mami saida suka girgiza da kalaman da Waheedah din ta furta

“Kunji, kuce karya fita daga dakin nan bai rabani da auren shi ba…”

Wannan karin Anty nata idanuwan cike yake da hawaye, fuskar Waheedah din ta dago tana kallon ta

“Waheedah kinsan me kike fada?”

Anty ta tambaya cike da tashin hankali, tasan auren Waheedah da Abdulkadir wani irin aurene da yake cike da hargitsi, ta hango mutuwar shi a watannin kusan takwas da suka wuce, amman bai mutu ba, batasan dalilin da yasa sai yanzun ba. Duk da zatai karya idan tace a watannin baya bataso mutuwar auren ba, ko dan kwanciyar hankalin Waheedah din, amman yanzun da take ganin abin na shirin faruwa a gaban idanuwanta, tashin hankalin da take ciki bazai misaltu ba.

Mikewa Abdulkadir yayi

“Ina zaka je? Ka dawo fa, karka fita baka rabani da auren ka ba… Ka dawo”

Waheedah take fadi tana kai hannu ta fisge karin ruwan dake jikin dayan hannun nata. Mami kallon ta take tana da tabbacin ba a cikin hayyacinta take ba. Hannu Abdulkadir yadan daga yana kasa magana, kafin dakyar yace

“Iskar dake dakin tamun kadan… Zan fita in shaqi iska ne”

Yai maganar muryar shi can kasan makoshin shi.

“Ka saukake mun saika fita kasha iskar…”

Waheedah ta fadi tana sa hannu ta share hawayen dake fuskar ta, tana tsayar da idanuwan ta akan fuskar shi da wani irin yanayi da yasa bugun zuciyar shi karuwa. Juyawa yayi

“Sadauki… Sadauki!!”

Baiko juya ba, tafiya yaci gaba dayi yana ganin kofar dakin ta mishi nisa, kafin ya samu ya fice, ko kofar bai ja musu ba, Anty ta rike Waheedah gam, dan shirin sauke take daga kan gadon tabi Abdulkadir

“Anty ki sakeni, kuna kallo fa ya fita, Mami ki bishi ki karbomun takardata, idan bazai rubuta ba ya fada miki da bakin shi ki dawo ki fadamun…”

Kallon ta Mami takeyi

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Ta furta a hankali tana ci gaba da maimaitawa, dan batasan wani abu daya kamata ta fadi ba. Wannan tashin hankalin da yake faruwa a gaban idanuwanta yafi karfinta.

“Anty dan Allah ku kira shi, kinji… Ku kiraa sh…”

Bata karasa maganar ba, ta sulale jikin Anty data saki wani irin sakati a firgice, cikin tashin hankali ta ke girgiza Waheedah

“Haj Sakina ba kallona zakiyi ba,ku kira likita mana…”

Da sauri Mami ta fita tana ma su Aminu magana dasu kira likitan, kafin kace meye saiga likitan da gudu, wani ma yana biyo bayan shi, dayan ne yace ma su Anty su fita daga dakin, ya rakasu har bakin kofa yaja kofar.

“Me yake faruwa wai? Anty me yake faruwa?”

Zainab ta tambaya cike da damuwa.

“Meya sameta? Naga Hamma ya fita a hargitse shima… Dan Allah kuyi mana magana”

Cewar Nabila muryarta na karyewa. Hamma da ta fadi yasa Anty kallon su Aminu da fadin 1

“Ku bishi dan Allah, kar yace zaiyi tuqi a yanayin da yake ciki…”

Tsayawa sukai suna kallon ta cike da rashin fahimta, tsaki ta saki tana kama hanya cikin sauri ta fita daga wajen, sai dai bata ga Abdulkadir din ba, ko alamun shi bata gani ba, har wajen asibitin ta duba amman bata ganshi ba, wajen da taga an ajiye motoci ta nufa tana duddubawa, duk da batajin tasan wacce irin mota Abdulkadir din yake da ita, kawai dai ta duba ne ko Allah zaisa tagan shi. Dan dafe kai Anty tayi tana fadin

“Oh Allah na…”

Kasan zuciyarta take addu’ar Allah ya kaishi gida lafiya idan can din ya nufa, kafin ta juya tana nufar hanyar da zata mayar da ita cikin asibitin Aminu Kano din, a duk jikinta take jin wannan abin bana lafiya bane…!A nutse yake tuqin shi, dan ba ranar bane karo na farko daya taka mota cikin rashin kwanciyar hankali, yana dai kula da yanda ake kauce mishi saboda katon tambarin bajon sojoji da yake manne jikin gefen motar, sai kuma sticker dinsu a gaban motar, ko babu kayan da suke jikin shi, kallo daya zakai ma motar kasan cewa ta soja ce. A haka harya kara gidan shi da yake Rijiyar Zaki, kasancewar shi muqamin shi na Captain,akwai sojoji guda biyu masu tsaron shi a gida. Daya daga cikin sune ma ya bude mishi gate, bai damu da ya tsaya ya gyara parking din ba, kawai kashe ta yai ana harabar gidan yana fitowa, mukullin ma a jiki yabar shi bai cire ba. +

Cikin gidan ya karasa, har saida ya wuce tsakiyar falon da takalman shi, kaman daga sama yaji muryarta na fadin

‘Babu sallama Sadauki? Takalmi har tsakiyar daki, ina sallah a wajen fa’

Bai kokarin cire takalman nashi ba, sallamar dai ya tsinci kan shi dayi. Jin shiru babu wanda ya amsa yasa shi takawa cikin gidan yana karasawa bangaren Nuriyya, hadi da sake yin wata sallamar, yasan tana can tana bacci, idan akace batai sallar Azahar ba bazai musu ba, ranar girkinta ma tana bacci, balle yau da tasan ba itace dashi ba. Karasawa yayi bangaren dakin baccin ta yana kwankwasawa, tukunna ya tura ya shiga, tana zaune kan gado, kunnenta liqe da earpiece, ta tusa system a gaba, da alama kallo takeyi.

Jin shigar shi yasa ta zare earpiece din guda daya tana kallon shi a kasalance da idanuwanta da suka fi komai a tattare da ita jan hankalin shi. Miqa tayi hadi dayin hamma tukunna tace

“Masoyi…”

Kamar yanda take kiran shi ko a gaban waye. Ganin yayi tsaye yasa ta mika hannunta tana mishi alama daya karasa, tana sakeyin wata hammar

“Bacci nake ji Allah, jikina namun ciwo”

Tsintar kan shi yayi da tambayar

“Me kikayi?”

Daquna mishi fuska tayi

“Kallo nayi… Me Waheedah ta dafa dan Allah?”

Zuciyar shi yaji tayi wata irin dokawa da sunan Waheedah din da Nuriyya ta kira. Bai iya amsa ta ba ya wuce kan shi tsaye yana nufar bandaki. Da ido Nuriyya ta bishi tukunna ta tabe baki tana mayar da earpiece din data cire daga kunnen ta daya taci gaba da kallon da shigowar shi ta katse mata. Rigar jikin shi ya fara cirewa yana mamakin yanda akai Nuriyya bata kula da jinin da yake jikin kayan shi ba, bata ma kula da damuwar da take shimfide a fuskar shi ba. Kan washing machine din da yake cikin bandakin ya ajiye kayan daya cire.

Ruwa ya bude ma kanshi yana yin tsaye, sanyin ruwan na nutsar da wani abu a tattare dashi, idanuwan shi ya kankance saboda bayason rufe su gabaki daya, baisan meya faru ba, baisan ya akai ba, yana da wata irin zuciya ta fitar hankali da bata da alaka da aikin shi, tun kafin shigar shi aikin soja yake da wannan zuciyar da har Abban shi yakan mishi addu’ar samun saukin ta a can baya, bayason rufe idanuwan shi ballantana yaga me zuciya ta saka shi aikata ma Waheedah yau a karo na farko tun auren su. Bazai bata lokacin shi tunanin abinda ya rigada ya wuce ba, wannan ba halayyar shi bace sam, yau bazai zama na farko ba, idan abu ya wuce mishi ya riga ya wuce tunda ba zai iya komawa ya sake ba, gaba kawai zai duba ya kiyaye. Da wannan tunanin a ranshi ya karasa wankan ya fito.

Baibi takan Nuriyya ba, kamar yanda bata bi ta kan shi ba, da towel din daure a jikin shi ya fito daga bangaren ta yana nufar bangaren Waheedah, dan nan yake da tabbacin zai sami kayan shi a nutse, dakin baccinsu ya shiga, kamshin ta na cika mishi hanci, tana son amfani da turarukan larabawa, sai dai bazaice ga wannne da wanne takan hada kamshin su ya bada kalar da yake bayarwa ba. Kan gadon ta ya hango kayan shi data fito mishi dasu, ya karasa ya dauka, riga ce fara qal, sai wando iya gwiwa baki mai wasu igiyoyi. Sai da ya fara saka singlet din da take ta zabga kamshi tukunna ya saka sauran kayan yana daukar towel din ya koma bangaren Nuriyya dashi.

STORY CONTINUES BELOW


Idan yace ga asalin abinda yakeji karya yake, kan shi dai yayi mishi wani irin nauyi.

‘Ka saukakemun auren ka’

Maganar Waheedah ta dawo mishi tana saka shi kai hannu dai-dai kirjin shi inda yake jin wani abu na mishi kaikayi ya murza. Bandaki ya koma ya mayar da towel din ya rataye, tukunna ya karasa kan gadon yana kwanciya gefen Nuriyya da ko inda yake bata kalla ba. Hannun shi ya mika yana zare earpiece din kunnenta, ya sake miqawa ya zare dayan, juyowa tayi fuskarta babu walwala

“Kallo fa nake…”

Idanuwan shi ya kankance mata, yana sa ta fadin

“Dan Allah mana Masoyi, kuma wallahi yunwa nakeji, nace me matarka ta dafa muku kayi banza dani” 5

Runtsa idanuwan shi Abdulkadir yayi, duk idan yana tare da ita yakan sha wahala, komai saiya fito fili yayi magana tukunna zata gane, ba surutu yake so ba.

“Bata da lafiya… Tana asibiti”

Sai yanzun tagane dalilin dayasa ya shigo mata, inda Waheedah din nan bata tunanin jarabar nacin ta zai sa tabari Abdulkadir ya shigo bangarenta haka kawai batare da wani dalili ba. Tabe baki tadan yi

“Allah ya bada lafiya…”

Ta fadi da wani yanayi a muryar ta da tasa Abdulkadir mikewa

“Me kikayi yanzun?”

Ya bukata muryar shi can kasan makoshi, ware mishi idanuwa Nuriyya tayi

“Me nayi nikuma?”

Hannun ta ya damqo yana janta kamar bata da wani nauyi zuwa gab dashi

“Abinda kikayi da bakin ki yanzun nake nufi”

Wani irin yawu Nuriyya ta hadiya, tasan halin shi, tun kafin dan zaman nan na auratayya ya hadasu, tunda kusan fiye da rabin rayuwarta a gidan su tayi ta, ta kuma san raini na daya daga cikin abinda baya dauka ko daga wajen yayyen shi, iyaye ne kawai Abdulkadir yake dagama kafa, sai dai ita din takan mishi abubuwa da yawa sai dai ya kalleta ya wuce, sosai ta shagwabe mishi fuska tana matsawa hadi da shigewa jikin shi. 1

“Yunwa nake ji Masoyi…dan Allah karkai mun fada… Ni banyi komai ba, addu’a nai mata”

Yanda ta narke mishi yasa shi sauke numfashi, a hankali ya janye ta daga jikin nashi, yana dafe kan shi da hannu.

‘Karka fita baka saukemun auren ka ba’

Maganganun Waheedah ne suke ta dawo mishi. Tsintar kan shi yayi da saukowa daga kan gadon, asibitin yake son komawa ya tabbatar da bata samu matsala a kwakwalwar ta ba, bayajin zai samu wata nutsuwa in bai tabbatar ba

“Ina zaka je?”

Nuriyya ta bukata

“Zan koma asibitin ne”

Ya amsa ta, yana jiran yaji ko zata ce mishi su tafi tare ta duba jikin Waheedah din. Baisan wani abu taji ya taso mata tun daga kirjinta har cikin wuyanta yana mata tsaye ba. Bata son nuna mishi kishin da taji, dan haka tace

“Zaka dawo da wuri? Kayo mun take away dan Allah…” 1

Kallon ta Abdulkadir yakeyi

“Me yake damun ki Nuriyya?”

Itama kallon shi takeyi

“Bangane me yake damuna ba, kar ince ka taho mun da take away idan zaka dawo da wuri? Jikina yamun nauyi bazan iya girki bane shisa, kuma laifinka ne daka qi dauko mun yar aiki…”

Kai Abdulkadir yake girgizawa

“She was your BestFriend (Aminiyarki ce a baya)…” 13

Ya furta a hankali, yana mamakin Nuriyya din, yanda yake kallon ta yasa ta cire earpiece din daga kunnuwanta tana ture system din, saukowa tayi daga kan gadon tana takawa ta karasa inda take, ba zaka kirata gajerar mace ba, amman tsayin Abdulkadir na kwatance ne, ga girman da yake dashi kasancewar baya wasa da motsa jiki, sai ta ganta yar karama a gaban shi, matsawa tayi tana riko hannun shi, hadi da daga kanta tana sauke idanuwan ta cikin nashi.

STORY CONTINUES BELOW


“Masoyi yau kam laifina kake ta gani, bansan me nai maka ba”

Ta karasa maganar tana tattaro hawaye dakyar ta cika idanuwan ta dashi

“Karki mun kuka Nuriyya… Karki mun kuka”

Dayan hannunta ta saka tana share kwallar data taru a gefen idanuwan ta

“Bansan me nayi maka ba…”

Yanda tai maganar cike da rauni ya taba shi, numfashi ya sauke, baisan me yake damun shi ba yau. Ganin ya fara saukowa a fuskar shi kawai yasa Nuriyya dora kanta a kirjin shi tana sakin wani guntun murmushin da take da tabbacin baya gani, batasan meya faru ba yau, idan zatai fada dashi Waheedah ba zata zama sanadin hakan ba, yaune karo na farko daya jefeta da kalmar alaqar dake tsakaninta da Waheedah a baya, ba zata bari hakan ya faru ba, tana sane sarai saboda ba tace zataje duba Waheedah din bane. 4

“Kome nayi kaina a kasa Masoyi…kar a sauke sojan a kaina yau… Umm?”

Tai maganar tana kara narkewa a jikin shi, dagota yayi yana sumbatar gefen fuskarta batare da yace komai ba ya juya yana ficewa daga dakin, bin bayan shi tayi tana leqawa ta tabbatar da yayi nisa tukunna ta dawo dakin tana turawa hadi da fadin

“Ni na dora mata ciwon… Yanzun haka karya take… Bansan yaushe Waheedah ta koyi munafunci da bakin hali ba…” 1

Da kan gadon zata koma taci gaba da kallon da take, sai kuma ta fasa saboda cikin ta dayai wata irin murdawa da yunwa. Babu shiri ta koma tana ficewa daga dakin, kitchen din ta ta nufa, a dispenser ta dibi ruwan zafi ta hada shayi, kwalin biscuit ta dauka tana wucewa ta koma daki, ta kasa daina zagin Waheedah a cikin zuciyar ta, yau da safe Abdulkadir din ya koma bangaren ta, shisa ta zauna tana kallon film din ta a system dan kartai tunanin yanda Waheedah take manne dashi kamar mayya, yanzun ma ba zata bari tunanin Waheedah ya bata mata rai ba, hakan take maimaitawa kanta harta samu wajen zama tana gyara system din ta dauki earpiece din ta mayar a kunnuwanta ta kunna film din, tukunna ta dauki kofin shayin data ajiye tana janyo biscuit din gabanta. 1

**

A hanyar shi na zuwa asibitin yaga Apple, dan harya wuce yayi parking yana fita daga motar ya taka da kafar shi zuwa wajen masu Apple din, hannu ya saka a aljihunshi duk da yasan bai zuba kudi ba, amman Waheedah ta dauko mishi wandon, yana da tabbacin duk wani abu dazai bukata tasa a ciki, akwai kudin kuwa, biya yayi ya karbi ledar yana komawa mota. Zai iya rantsewa da Allah duk idan ya dawo gida ya ganta, yakan manta yanda yake iya yin komai batare da ita a kusa dashi ba. Dayan aljihun yakai hannu ya laluba yaji I.D cards din shi na ciki yana kuma da tabbacin har da ATMs din shi duk suna ciki.

Sai da ya sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba tukunna yaja motar yana nufar asibitin. Parking din motar shi yayi a inda akeyi yana takawa zuwa cikin asibitin, hannun shi rike da ledar Apple din daya siya, indan tashi ba za’a ci Apple ba, dan yana cikin kayan marmarin da baya kan shi sam-sam. Zama da Waheedah ya sashi koyan ci, duk da haka badan yana jin dadin shi ba, duk idan ta yayyanka yanda takan yi ta miqo mishi bayaqin dauka, ko idan tana ci, data gutsura take miqa mishi shima ya gutsura saita sake karba, ko ruwa zata sha saita bashi shima. Baya tunanin Waheedah na iya cin wani abin yana zaune ko yaci nashi bata bashi ba.

Sosai yake shiga cikin asibitin harya karasa bangaren da Waheedah din take, dan sun kama dakin da ita kadai ce, kan shi tsaye ya nufi dakin da yake lamba ta sha biyu, kwankwasawa yayi hadi da murza hannun kofar ya shiga batare daya jira an bashi izinin ba. Baiga kowa a dakin ba sai Anty, da sallama ya karasa ta amsa shi a sanyaye. Ledar Apple din ya ajiye a gefe kan abinda akan ajiye kayayyaki, tukunna ya kalli Anty da take zaune tana goye da Ikram yana fadin

“Ke kadai? Ya jikin nata?”

Cikin sanyin murya ta amsa shi da

“Sun koma gida, ba’a son hayaniya ne ko kadan, saboda jininta yayi wani irin hawa. Abdulkadir me yake faruwa?”

STORY CONTINUES BELOW


Kujera ya janyo yana samun waje ya zauna, fuskar shi da bata cika fara’a ba ya sake hadewa waje daya. Tambaya na daya daga cikin abubuwan da bayaso, musamman wadda ta shafi matsalar iyalin shi.

“Tambayar ka nake, me yake faruwa?”

A daqile yace

“Tsakanin mune… Komai zaiyi dai-dai…”

Sakin baki Anty tayi, na dan lokaci ta manta waye Abdulkadir, yanzun yake tuna mata.

“Tsakanin kune take rokon mu da mu karbar mata takardar saki a hannun ka?”

Dago da kan shi yayi yana kallon Anty

“Kaman yanda nace, tsakanin mune. Anty karki wuce hurumin ki dan Allah” 7

Ya karasa yana mayar da kallon shi kan Waheedah da take bacci, hannun ta da yake daure da ruwa ya kama yana gyara mata zaman shi, baibi takan Anty da take kallon shi ba, rashin kunya ce Abdulkadir ya saba batun yanzun ba, batasan me yasa tai tunanin iyalin daya fara tarawa zasu saka halayyar shi canzawa ba. Bata sake cewa komai ba, tasan halin rashin hakurin ta, kaca-kaca zasuyi ita dashi a asibitin nan, dan bakinta bazai shiru ba, Abdulkadir kuma ba zaiqi datsa mata duk maganar data fito daga bakin shi ba. Yanke hukuncin tashi ta koma wajen dakin tayi, idan ya gama zaman shi ya fita ta dawo.

Yana jin bude kofar ta da rufewa, juya idanuwan shi yayi, yana kara matsawa kusa da Waheedah sosai, sam bayason baqar tambaya, baiga meya shafi Antyn da matsalar gidan shi ba, dayan hannun Waheedah ya kama yana zagayo dashi takan cikin ta hadi da riqewa.

“Wahee kinga me kika ja mana ko?”

Ya furta a hankali, yanzun yake kara samun tabbas akan ba cikin hayyacinta ta furta mishi kalaman dazun ba. Numfashi ya sake saukewa, sosai ya ja kujerar yana kwantar da kan shi a cikinta, kan kuncin shi haggu ya kwanta yanda zai iya kallon fuskarta, har lokacin dayan hannun shi na cikin nata. Wani numfashin mai nauyi ya sake ja yana fitarwa hadi da lumshe idanuwan shi. Babu tunanin komai cikin kan shi, kallon ta yake wata irin nutsuwa na saukar mishi, a hakan bacci mai karfi ya dauke shi shima.

*

Kan ta takejin kamar an dora mata katon dutse, idanuwan ta dakyar ta iya daga su, nauyi taji saman cikin ta, a zaton ta Fajr ne, dan haka yakanyi mata, komin baccin da takeyi zata jishi yazo ya kwanta a jikin ta, bazai taba kwanciya kan katifa ba, ko ta sauke shi daya farka yake sake koma kan jikin ta ya kwanta. Hannu takai tana dorawa kan cikin ta inda take jin nauyin, zata rantse dumin shi ya banbanta dana sauran mutane. Dan dago kanta tayi, shi dinne ba magagin bacci takeyi ba. Hannu takai tana murza kirjinta inda take jin yana mata wani irin ciwo.

A hankali komai yake dawo mata, hannu takai da nufin tashin shi ya furta mata abinda take son ji, saita tsinci kanta da kasa yanke mishi baccin nashi, tunda tasan bako da yaushe yake samu ba, duk da yazo hutune bayan shekara biyu sai yanzun ya sami hutu mai dan tsayi. Kallon shi take, zuciyarta a dunqule waje daya take jinta, shisa bata motsa mata da duk wata kaunar Abdulkadir din. Zufa taga yana yi, a hankali jikin shi ke bari, tasan yana cikin duniyar mugayen mafarkan dakan hana mishi samun wadataccen bacci. Ganin yanda yake zabura yasa takai hannun ta kan fuskar shi tana shafawa a hankali.

“Sadauki…”

Ta kira a tausashe, hannunta taji ya damqa kamar zai karyata kafin ya bude idanuwan shi yana sake matse riqon dayai ma hannunta da saida ta runtsa idanuwan ta saboda azaba, sosai ta dauka ya karyata yau dai.

“Sadauki hannu na…”

Ta fadi, tana saka shi dago fuskar shi daga kan cikin ta yana karema dakin kallo, kafin da sauri ya saki hannunta yana fadin

“Bansan sau nawa zance ki daina yo kusa dani inkin ganni a yanayin nan ba…”

Dayan hannun ta mai daure da ruwa ta dago tana murza wannan din, idanuwanta harsun tara hawaye

STORY CONTINUES BELOW


“Yau dai ka karyani, kayi maganarka ta karshe a bakin yan Amin, an amsa, ka karyani Sadauki…”

Karamin murmushi yayi yana kamo hannun nata data fisge, karfi yadan saka ya riko hannun

“Kokawa zakiyi dani?”

Ya tambaya yana daga mata girar shi guda daya. Turo mishi labbanta tayi, hannun yake dubawa, farar fatarta tasa hannun ya fara tara jini, shafa mata wajen yayi

“Ban karyaki ba, in kina tabani ina bacci dai zai faru wata rana, na fada miki bakyajin magana”

Fisge hannun ta tayi tana murzawa.

“Ina yarana?”

Ta buqata a hankali, tana jin kewarsu na danneta

“Fajr na tare dasu Mami nake tunani, Ikram na wajen Anty…bari in karbo miki ita…”

A hankali ta girgiza mishi kai duk da hakan take so, batasan lokacin data dauka a kwance ba, tasan yarinyar taji yunwa ba kadan ba, amman a karbota daga wajen Anty, abin ya mata nauyi. Abdulkadir bai saurareta ba ya miqe yana nufar kofar dakin ya bude ya fita, Anty yagani zaune tana danna waya, da alamar game ne daya kalli screen din.

“Ta tashi Anty, ki bata Ikram wai…”

Batare da tace mishi komai ba ta ajiye wayarta a gefe tanaa kama goyon yarinyar ta kwance ta mika mishi ita, karbarta yayi yana kallon ta, idonta biyu, ta tsoma hannuwanta guda biyu a bakinta tana tsotsa. Gyara mata zama yayi a hannun shi daya tukunna ya bude kofar yana shiga yana mayar wa ya rufe, sai da ya saka Ikram a hannun Waheedah din tukunna ya zauna inda ya tashi, yana kallo ta miqe zaune tana jingina bayanta da abin gadon, tukunna ta gyarama Ikram din zama sosai tana soma shayar da ita.

Dago kanta tayi tana kallon shi, zuciyar shi yaji ta doka ganin yanayin nan baibar idanuwan ta ba.

“Kai nake jira…”

Ta furta a hankali, kallon ta yake yana son fahimtar ma’anar kalaman da ta furta mishi.

“Abinda na fada maka dazun, bana ce ka saukake mun auren ka ba? Ko baka jini ba in sake maimaitawa?”

Yanzun ya gama tunanin ta dawo hayyacin ta, ashe bata dawo ba har yanzun, wacce irin buguwa tayi haka. Dole zai magana da likitocin nan, inma barin kasar ya kama Allah ya mishi rufin asirin da baya tunanin zai gagare shi.

“Kayi shiru…”

Waheedah ta fadi tana sake tallabo Ikram din jikin ta, wani irin yanayi taje ji da batasan yanda zata misalta shi ba, har wani kaikayi take ji a jikinta da son jin ya furta mata kalaman da zasu datse igiyar da ta qulleta dashi.

“Kin buga kanki da yawa…”

Abdulkadir ya fadi can kasan makoshi, shine kawai bayanin dazai fassara abinda yake faruwa yanzun. Idan ba kanta ta buga ba Waheedah ba zata nemi saki a wajen shi ba, karma azo maganar saki ba zata kalle shi cikin ido tana mishi magana da yanayin rashin kunya haka ba.

“Ban buga kaina ba, sakina nake son kayi…”

Ta fara bata mishi rai, yana jin yanayin na barazana da hakurin shi.

“Kibar mun maganar nan, ki bari, nace kin buga kanki da yawa ne…”

Ya karasa yana jan kujerar shi baya ya miqe tsaye

“Ina zaka je?”

Dan dafe kanshi yayi yana sauke hannun shi

“Zan magana da likita…”

Wani murmushi Waheedah tayi, tana rasa meyasa kalamanta suke mishi wahalar fahimta haka.

“Kayi magana dashi, idan ya tabbatar maka lafiyata kalau, saika dawo ka saurareni”

STORY CONTINUES BELOW


Kallon ta Abdulkadir yake yi, maganganunta na zauna mishi, a hankali ya girgiza kai, idan ya zaman bata buga kanta ba, idan ya zamana tana cikin hayyacinta baisan me zaiyi ba, baisa ina take so ya ajiye kalaman ta ba. Babu shiri ya koma ya zauna yana kiran sunan ta

“Waheedah…”

Kallon shi kawai tayi batare data amsa ba, wani abu daya zo wuyan shi ya tsaya yake kokarin hadiyewa amman hakan ya gagara.

“Saboda hakurina ya kwace a karo na farko a zaman mu yasa kike furta mun kalaman nan?”

Kai ta girgiza mishi a hankali

“Kamun abinda yafi nayau, kasani kuma, nayau dinne dai zai zamana na karshe In shaa Allah…”

Wata gajeriyar dariya yaji ta kubce mishi

“Kin san girman kalaman da kike furta mun?”

Ikram ta janye daga jikinta dan hartayi bacci, tana gyarawa tukunna ta jinjina mishi kai.

“Ba zai yiwu ba to, idan ma da gaske baki buga kanki ba, ba zai yiwu ba Waheedah…”

Ya fada da wani yanayi a muryar shi da yasa ta tambayar

“Meye bazai yiwu ba? Sakin nawa?”

A hasale Abdulkadir yace

“Waheedah…kina son sake gwada hakurina ba?”

Cikin idanuwa ta kalle shi

“Meye zai faru? Zaka sake dagamun hannu ne yanda kayi? Nace idan na gwada hakurin ka zaka sake dagamun hannu ne Abdulkadir?”

Yanda taja sunan shin kamar ta kafa abin gurza kwakwa a zuciyarshi taja haka yaji ta karce wajaje da yawa a cikin kirjin shi. Ko a mugun tunani bai taba hango Waheedah zata taba yi mishi rashin kunya ba, mamaki yake har kasan ranshi daya kai karshe wajen baci, ya mata kuskure bawai bai mata ba, amman hakan bashi bane dalilin dazai sa ta kalli kwayar idanuwan shi tana fada mishi son ranta, bai tsaya kalmar neman saki ba, harda rashin kunya tana daga mishi murya.

“Saukake miki a hannuna yake ko? Ba zai faru ba to, kina jina bazai faru ba”

Wasu hawaye taji masu zafin gaske suna zubo mata, ji take wani abu yana yamutsawa cikin kanta, rashin hankalin da yake mata tunanin take ji yana gab da cimmata idan bai saukake mata auren shi ta huta ba yau.

“Wallahi baka isa ba”

Ta fadi muryarta na karyewa da kukan da takeyi, kujerar shi yaja baya yana mikewa, wani irin tuquqin bacin rai yake ji har idanuwan shi ke lumshewa

“Ki kalleni…”

Ya furta ta tsakanin hakoran shi, kukan ta taci gaba dayi

“Ki kalleni Waheedah!”

Ya fadi cikin wata irin murya data sata sauke idanuwanta da suka fara rinewa da kuka cikin nashi

“Na isa…Ni Abdulkadir Ahmad Bugaje na isa har nayi yawa. Bansan me yake damunki ba, ki kwanta kiyi bacci, bana bata lokacina akan abinda ya riga da ya wuce ke kin sani, zanyi kamar komai bai faru ba…”

Ya karasa maganar yana juyawa dan jikin shi ya soma bari da bacin ran da yake ciki

“Sadauki karka fita baka saukake mun ba…”

Waheedah ta furta kamar baiyi magana ba, kamar bata ji abinda yace ba, bai juyo ba, saboda baida tabbas kan abinda zai iya faruwa idan baibar dakin ba, yanda ya doko kofar saida ya firgita Ikram data zabura tana fashewa da wani irin kuka, riketa Waheedah tayi tana jijjigata cikin alamar lallashi dan itama kukan takeyi. Yana fita Anty ta shigo tana kallon Waheedah dake faman share hawaye. Dan haka ta karasa tana karbar Ikram din daga hannunta ta goya yarinyar da dakyar ta samu tayi shiru.

“Dan Allah kubi komai a hankali, kinji Waheedah? Kinga baki da lafiya…”

Saida ta share hawayen da sunqi daina zubar mata, da wani daci a makoshin ta tace

“Ni bance wani abu ba Anty, ko a musulunci an bani damar neman saki idan naga bazan iya zama dashi ba… Me yasa bazai mun abinda nake so ba?”

Yanayin karayar dake muryarta yasa Anty karasowa ta dafa ta, itama tana jin idanuwan nata sun ciko da hawaye dan Allah yai mata wata irin zuciya da ko bata sanka ba taga kana kuka itama tayaka takeyi, balle kuma Waheedah da hankalin yarinyar yasa take jinta har ranta. A raunane tace

“Ku dai bi komai a hankali, karki yanke hukunci cikin fushi…”

Wasu sabbin hawayen na zubar ma Waheedah tace

“Anty ki aramun wayarki dan Allah”

Batare da wata gargada ba Anty ta cire lambobin sirrin data rufe wayar dashi ta mika mata, wajen kira ta shiga tana fara saka lambobin mutum dayan da take da yakinin shi kadaine zai iya saka Abdulkadir yai mata abinda take so, shi kadaine kuma bazai ce tayi hakuri ko abi abun a hankali ba. Danna kira tayi tana kara wayar a kunnenta, ringing daya tayi a na biyun ya daga da sallamar data kasa amsawa sai ma wani sabon kukan da taji ya kwace mata. Dakyar ta iya cewa

“Abbah…”

Tana jin muryar shi daga dayan bangaren ya amsa da

“Waheedah?”

Cikin son tabbatar da ita dince, kai take daga mishi kamar yana ganin ta, wasu hawayen na zubar mata

“Abbah…”

Ta sake kira cikin kukan ta

“Subhanallah… Waheedah me yake faruwa ne? Lafiya dai ko?”

Kai ta girgiza mishi

“Abbah kai ma Abdulkadir magana ya sauwaqe mun… Dan Allah Abbah”

Ta karasa maganar kuka mai sauti na kwace mata, jim yayi daga dayan bangaren da alama yana juya zancen tane, kafin yace

“Hajiya Halima na kusa dake?”

Dakyar ta iya cewa

“Eh…”

“Ki bata wayar…”

Anty dake tsaye Waheedah ta miqa ma wayar, tana jan kafafuwanta ta hade su da jikinta hadi da dora kanta saman gwiwoyinta hawayenta naci gaba da zuba…!Tunda ya shiga gida bangaren Waheedah ya wuce, dakin baccin su ya shiga, yana zama gefen gadon. Kan shi sarawa yake tunda ya fito daga asibitin, baisan ta inda zai fara tarar matsalar da Waheedah take son janyowa rayuwar su ba, dan baisan meya shiga kanta ba, kafafuwan shi ya janyo da nufin dorasu kan gadon yaga takalman shi dabai kwance ba. +

“Bazan cire ba…” 8

Ya fadi a fili, da Waheedah yake, dan ita ce bataso yana shigo mata da takalma har daki, abinda take so shi take mishi yau, shima abinda yake so zaiyi, hannu yasa ya dafe kan shi, yana kuma saukewa hadi da ajiye numfashi mai nauyi. Idan matsalar kwakwalwa ce ta samu Waheedah, yaga alama harshi takw son gogawa tunda ya fara magana shi kadai. Hoton su dake durowar gefen gadon ta ya dauka yana tsayar da idanuwan shi akai. So yake yagane wanne kalar kayane a jikin Waheedah din, yadai ga farare ne, dankwalin da ta nade kanta dashi ma farine, zai iya tuna da wayarta ta dauke su hoton, tana lafe a jikin shi, ya zagayo da hannunshi daya kan cikinta data dora nata hannun akan nashi, ya kankance mata idanuwan shi daba girman kirki ne dasu ba daman, da dariyar nan tata a fuskar shi.

Dan yatsan shi ya saka ya shafi dai-dai fuskarta, yasha ganin hoton a ajiye a gurin, hade da sauran hotunan shi da bazaice ga lokacin data dauke su ba, amman zai karya idan yace ya taba tsayawa ya kula da hoton da yake hannun shi, balle ya tambayeta lokacin data kai aka wanko hoton har aka saka shi a frame hakan, baisan meyasa sai yanzun yake son tambayarta ba. Sake shafar fuskarta yayi

“Me yake damunki yau? Me kike son janyo mana Wahee? Me kike son janyo mana haka?”

Ya tsinci kan shi da tambaya, shirun dakin na saukar mishi da wani irin yanayi daya saka shi ajiye hoton inda ya dauka. Baisan abinda ya kamata yayi ba, wani abu makamancin wannan bai taba faruwa da shi ba, asali yau ce rana ta farko da rikici ya soma hadashi da Waheedah, shisa yake jin komai ya kwance mishi, ba zaice baya fada da ita ba, ita dince dai bata taba biye mishi, komin fadan dazai sauke mata hakuri kawai zata bashi, baisan me yake damunta ba yau.

Aljihun shi ya taba, wayarshi bata ciki, waige-waige ya fara yana neman inda ya ajiye ta, babu shiri ya mike, duka inda tunanin shi zai iya kaiwa cikin dakin saida ya duba amman bai ganta ba, takawa yayi zuwa falon su, zuciyar shi na wani irin dokawa da ya sauke idanuwan shi kan table din da Waheedah ta fada kai, ga jini da harya fara bushewa kan kafet din, kafafuwan shi da yake ji sun soma rawa yaja zuwa hanyar kitchen, wani karamin bokiti yagani ya dauka ya tara ruwa a ciki, kan window din kitchen din ya dauki omo ya zazzaga a ciki. Abin goge-goge yake nema, bai gani ba sai wani towel karami.

Shi ya dauka ya saka cikin bokitin yana daukowa ya fito daga kitchen din, gefen da jinin yake akan kafet ya ajiye bokitin yana tsugunnawa, towel din ya fiddo ya matse yana soma gogawa a wajen, sosai jikin shi ya dauki dumi da alamar zazzabin da yake da alaqa da dana sanin da ya lullube shi, yana mayar da towel din cikin bokitin yaga yanda ruwan ya sake launi yaji wani abu na tattarowa daga zuciyar shi ya hadu a wuyan shi ya shaqe shi, a hankali kuma shige da ficen numfashin shi ya fara canzawa. Towel din yake gogawa a wajen da dukkan karfin shi.

‘Jinin Waheedah ne duka anan’

Wata karamar murya ta furta cikin kunnuwan shi, numfashin shi na fita da sauri-sauri kamar wanda yai gudu.

‘Bana bata lokaci akan abinda ya riga ya wuce, bana tunani akai saboda bazan iya komawa in canza ba’ 1

Yake fadi cikin kwakwalwar shi ko zuciyar shi zata taimaka ta bashi hadin kai. Iya abinda zai iya gogewa daga jikin kafet din ya goge yana daukar bokitin ya mayar kitchen, wajen wanke-wanke ya juye ruwan, kalar shi nasa cikin shi yamutsawa, baisan lokacin da jini ya fara daga mishi hankali haka ba, fanfo ya bude kan ruwan dan ya wuce da wuri, bayason ganin shi, ya tara hannuwan shi a jiki ya wanke, har fuskar shi ya wanke ko zata rage mishi zafin da yaji tanayi, ya kashe fanfon ya fito. Tunawa yayi wayar shi yake nema, yaci gaba da duddubawa, baisan lokacin da yace

STORY CONTINUES BELOW


“Waheedah! Ina wayata?” 2

Idanuwan shi ya runtsa, bai gama tunanin yanda shima yake gab da samun tabin hankali ba yaji karar wayar. Hakan na sashi bude idanuwan shi babu shiri, inda yake jin karar wayar yake bi, harkan kujera daga gefe, hannu ya saka ya janyo wayar da rabin ta ya fara shigewa cikin lokon kujerar, sai dai kiran harya yanke, dangwala jikin gilashin wayar yayi tunda babu wani mukulli a jiki ta kuwa bude, mamakine bayyane a fuskar shi ganin Abba ne ya kira, bawai dan baya kira ba, lokacin daya kira dinne yaji ya mishi wani iri.

Yana shirin bin kiran sai gashi ya sake shigowa, amsawa yayi yana kai wayar kunnen shi da fadin

“Abba…”

Daga dayan bangaren Abba ya amsa

“Abdulkadir, kome kake kazo gida yanzun”

Zuciyar shi yaji tai wata irin dokawa

“Abba lafiya?” 2

Ya bukata yanajin sautin muryarshi daya fito a tsorace

“Ka dai zo…”

Kai ya girgiza

“Ni dai ka fara fadamun ko menene a waya tukunna”

Abdulkadir ya fadi, dan yanda zuciyar shi take bugawa sam bai aminta da kiran Abban ba.

“Abdulkadir…”

Abba ya kira cike da kashedi

“Ba zanyi tuqi a nutse bane idan bansan meye dalilin kiran ba Abba, ni dai ka fadamun dan Allah. Kaji”

Ya sake fadi

“Bari in aiko a dauke ka to”

Cewar Abba da alamun ranshi ya fara baci, kai Abdulkadir ya girgiza yana jin komeye yake shaqe da wuyan shi yana kara shaqe shi.

“Akan Waheedah ne ko?”

Ya tambaya muryar shi can kasa, yana kuma jin bugun zuciyar shi har cikin kunnuwan shi, idanuwa ya runtse yana jiran amsar Abba, a ranshi kuwa rokon Waheedah yake

‘A’a Waheedah, bakimun wannan tonon asirin ba, baki mun haka ba, ba zaki taba mun haka ba’

Bude idanuwan shi yayi dajin Abba yace

“Akan ta ne, kazo yanzun ina jiran ka”

Kafin ya furta wani abu Abba ya kashe wayar, tayi yar karar alamun an kashe daga dayan bangaren cikin kunnen shi, sauke wayar yayi yana fadin

“Abba mana, Abba banaso ana kashe mun waya cikin kunne, da gaske bana so…” 21

Ya karasa maganar da furta

“Yaa Ilahee…”

Komai yake ji ya kwance mishi, takawa yayi yana fita daga dakin, gurin motar shi ya nufa, budewa yayi yana jefa wayar a ciki, harya daga kafarshi daya ya saka cikin motar yaji an kira sallah

“Ni sai nayi Sallah wallahi” 10

Ya furta kamar wani yace kar yayi sallah, cikin gida ya koma ya daura alwala, sai dai bayajin yana da nutsuwar da zai iya zuwa masallaci, anan dakin baccin su ya nemi darduma ya shimfida yana tayar da sallah. Sai dai ga mamakin shi kokawa ya soma yi sosai da nutsuwar shi, dakyar ya samu yai sallar tunani fal cikin ranshi, ko addu’a baiyi ba ya mike yana barin dardumar anan. Fita yayi ya shiga motar yana kunnuwa hadi da janta ya juya, maigadin kofar nashi ya bude mishi gate ya fice ya nufi hanyar da zata kaishi da gidan nasu da yake a kofar ruwa.

**

Dakyar Anty ta samu likitan yabar su suka taho gida, shima da alkawarin cewa zata dawo da Waheedah a ranar, komai a asibitin suka baro shi. Ita kanta Antyn taso koma menene abar shi sai Waheedah ta samu sauqi sai ayi, amman ita da Abbanta sunki yarda da hakan. Har suka shigo gida addu’ar Allah ya kawo musu sauqi takeyi. Waheedah da kanta ta fara jan Anty zuwa bangarenta, badan bata son ganin Mami ba, bata son kowa yace tayi hakuri ko tabi komai a hankali, batason jin duk wannan. 2

STORY CONTINUES BELOW


Kujera ta samu tai zamanta a dakin Anty, lokaci zuwa lokaci take saka hannu ta share hawayen dake biyo fuskarta, Ikram ma data qara bata tasha Anty ta miqama yarinyar. Tana nan zaune Abba ya shigo da sallama, tana sauke idanuwan ta cikin nashi wani irin kuka ya kwace mata, a hankali Abba ya karaso cikin falon yana neman waje ya zauna.

“Waheedah…”

Abba ya kira sunanta muryar shi cike da rauni, kanta da yake nade da bandeji ya fara bi da kallo, tukunna ya tsayar da idanuwan shi kan fuskarta da duk kumburin da tayi da alamun kukan da tasha bai hana yanda ta rame matuqa nunawa ba. Kukan da take yasa ta kasa amsa shi

“Waheedah kiyi hakuri kinji…”

Abba ya furta yana jin yanda zuciyar shi take a jagule, muryar Waheedah a dishe ta dago jajayen idanuwanta tana kallon Abba, kai take girgiza mishi tana sauke ajiyar zuciya a hankali

“Dan Allah Abba…”

Ta soma fadi tana jin zuciyarta kamar zata fado

“Dan Allah… Karkace in koma… Karka ce inyi hakuri Abba… Wallahi nagaji… Inajin idan na koma zuciya ta Abba…”

Tai maganar tana kai hannunta a kirji inda take jin zuciyarta kamar zata fashe, numfashi take ja tana fitarwa amman iskar bata kai mata inda take so, dakyar take iya magana

“Abba zuciyata ina jin kamar zata fado, dan Allah karkace inyi hakuri, karka tambayeni me ya faru… Bansan ta inda zan fara maka bayani ba, kawai nagaji ne, nagaji sosai” 5

Anty dake tsaye hannu tasa tana share hawayen da taji suna shirin zubo mata, a muryar Waheedah take karantar kuncin da Allah kadai yasan tun yaushe take danne shi, a muryat Waheedah take jin ciwon da take ciki, ya kuma taba zuciyarta ba kadan ba, sosai tayi niyyar lallaba yarinyar takoma dakin mijinta domin shi aure dan hakuri ne, kowa kaganshi zaune a gidan mijin shi komin dadin zaman su akwai hakurin da suke da juna ta fannin da bazai bayyanu ba.

Sai dai kuma batasan har yaushe za’a dinga labewa a bayan hakuri ana cutar mata a zamantakewa ta auratayya ba, batasan sai yaushe mutane zasu fahimta shi kan shi hakurin yana da qa’ida ba, a al’adance ma hakuri na da iyaka, balle addini daya sauqaqa matakin komai, batasan lokacin da mutane zasu fahimci duk da hakuri jigone na zaman aure bai sa ya zama ibadar auren gabaki dayan ta ba. 1

“Dan Allah Abba…”

Roqon da Waheedah tayi ya katse ma Anty dogon tunanin da takeyi, wani radadi takeji zuciyarta nayi, kuncin Waheedah na tuna mata da duk hakurin da tayi a nata gidan auren, yana sa tana tuna rashin sauqin da yake tattare da hakuri, sai mai matuqar karfin zuciya ake yiwa ya kauda kai. Abba kan shi numfashi ya sauke yana furta

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Abdulkadir…Halima kinga yaron nan saida ya kure hakurin ta ko?”

Abba ya karasa maganar yana jinjina kanshi, a raunane Anty ta amsa shi da

“Ai shikenan, ya kyauta, ya kuma yima kan shi wallahi”

Hajja ce ta shigo dakin da sallama, tana kare musu kallo, dan sallah take lokacin da Abba ya aika a kirata. Mami daman da Anty taje da kanta catai duk suna wajen ita kam bataga zuwan me zatayi ba, ta san zasuyi yanke duk abinda ya kamata akan Waheedah din. Duk kawaicin Mami, Anty tasan Waheedah ta ninka ta, yau kam tura takai bango.

“Allah dai yasa lafiya…”

Hajja ta fadi bayan Anty ta amsa mata sallamarta, kafin ta zagayo ta samu waje gefen Abba ta zauna, sai lokacin ta kula da Waheedah da tun shigowar Abba ta sauko daga kujerar da take ta zauna kan kafet din dakin

“Subhanallah, Waheedah? Ashe dai ciwon da yawa haka… Zainab tazo tana fadamun, yanzun nake shirin in idar da sallah saimu koma asibitin gabaki daya. Amman kamar bai kamata su baki sallama da wuri haka ba…” 1

STORY CONTINUES BELOW


Anty ce ta amsa Hajja da

“Basu bayar da sallama ba suma, zamu koma zuwa anjima…”

Da mamaki Hajja tace

“Ikon Allah… Lafiya dai ko?”

Tai tambayar tana kallon Abba daya girgiza mata kai

“Abdulkadir ne…”

Zuciyarta Hajja taji tayi wata irin dokawa jin sunan dan nata

“Yau kam dai ya kure hakurin yarinyar nan. Saki take nema…”

Cikin tashin hankali Hajja tace

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…saki kuma Alhaji? Meya faru? Me yai mata?”

Dan rausayar dakai Abba yayi, dan baida wannan amsar, ba kuma shi da karfin zuciyar da zai tambayi Waheedah din tunda har roqon shi tayi dakar ya tambaya. Waheedah dake share kwalla Hajja ta kalla

“Waheedah me ya faru?”

Batare data dago ba ko hawayenta ya daina zuba tace

“Dan Allah Hajja karki tambayeni meya faru, kiyi hakuri, duk kuyi hakuri, takardata kawai nake son a karbar mun a wajen shi…”

Maganar daga zuciyar ta takejin tana fitowa, ta dauka rashin Abdulkadir a kusa da ita zai barazana da rayuwarta, bata taba tunanin zama dashi ne abinda zai haifar da hakan ba, in baya kusa da ita ko numfashi batajin tana fitarwa dai-dai, amman yanzun tunanin kusanci dashine yake barazana da dai-daiton numfashin ta. Ba tasan lokacin da rayuwa ta bude musu wannan shafin ba, sai dai ko ba zata iya wuce shi ba, zatai duk wani kokari da zata iya ko dansu Fajr. Salati Hajja take tana kara wani 1

“Ke kam Waheedah kiyi hakuri mana, kinji tunda duk muna nan kibari a kira shi in shaa Allah koma menene yake faruwa zamuji sai a dai-daita ku…tunda haihuwa ta shiga tsakani ko dan yara sai a duba lamarin…” 7

Kai Abba ya girgiza ma Hajja

“Karkuyi amfani da yaranta ku danne ta…” 1

Rai a jagule Hajja ta kalle shi

“Karka cemun kana tunanin yin abinda take so ne batare daka duba lamarin ba?”

Kafin ya amsa Abdulkadir ya shigo dakin, kallo daya zakai mishi kasan babu nutsuwa a tattare dashi ballantana ai maganar kwanciyar hankali. Ko sallama baiyi ba, zagayowa yayi yana zama kan hannun kujera, zuciyar shi kamar zata fito daga kirjin shi saboda tsallen da takeyi

“Abba me tace na mata?” 7

Ya tambaya, rashin gaskiya shimfide a fuskar shi. Kallon shi kawai Abba yakeyi, Hajja ce ta watsa mishi harara

“Me kai mata Abdulkadir? Me ka sake yi mata?”

Cike da rashin fahimta yace

“Bangane me na sake mata ba Hajja? Na mata wani abune banda nayau?”

Girgiza kai Anty tayi tana fadin

“Hmm…”

Dan batason tayi magana, Abdulkadir rashin kunya zai mata tasan shi sarai

“Dan ubanka baka san me kai mata ba?”

Fuskar shi babu walwala yace

“Hajja mana…”

Ko kadan bayaso a saka shi a gaba ana mishi fada, ko dacan ma bayaso balle yanzun da ba yaro bane shi, sai dai baiga laifin su ba, Waheedah ce, duk laifin nata ne da tai mishi wannan tonon sililin, tafi kowa sanin yanda yake son sirri a rayuwar shi, abinda ya faru yau din tsautsayine da zasu iya magance shi tsakanin su, baisan me yake damunta da ta kwaso matsalarsu tana fadama su Abba da baiga ta inda abin ya shafe su ba. 1

STORY CONTINUES BELOW


“Ka kyauta Abdulkadir… Ka ji… Ka kyauta”

Hajja ta karasa muryarta na karyewa, idan ranta yai dubu a bace yake. Abba ya sake kallo

“Dan Allah Abba me tace nayi mata?”

Kai Abba ya girgiza mishi

“Batace kai mata wani abu, aurenka ne kawai ta gaji dashi”

Cikin wani irin tashin hankali Abdulkadir ya kalli Waheedah da ta sauke mishi rinannun idanuwanta. Da nashi idanuwan yake tambayarya me take? Me take yi musu haka?

“Abba zanyi magana da ita… Kaji… Hajja kunji…” 1

Ganin suna kallon shi yasa shi dorawa da

“Dan Allah…”

Abba ya fara miqewa, shikam batun yanzun ya sallama da lamurran Abdulkadir ba, tsakanin shi da yaron idone da addu’a, amman shikam yace yayi ko kar yayi bakin shi ya daina wannan asarar. Ganin da gaske bar musu dakin zasuyi yasa Waheedah fadin

“Abba dakun zauna… Kome zaice bazai canza komai ba… Takardata kawai nake so ku amsar min tunda ni na mishi magana yaki…”

Basu ce komai ba suka fita, ko karasa barin dakin Hajja batai ba, Abdulkadir ya bar inda yake zaune yana dawowa kusa da Waheedah ya tsugunna, hannu yasa yana tallabo fuskarta

“Me nayi miki da zafi haka Waheedah? Dan Allah me nayi miki haka? Hankalina kike son ganin ya tashi? Nutsuwata kike son rabani da ita? Duk kinyi nasara, wallahi kinyi nasara, kibari haka ki tashi mukoma gida… Idan ma kina so raina ya baci ne kamar yanda na bata miki rai duk ya faru…” 3

Saida hawaye suka zubo mata tukunna tasa hannuwanta tana zame nashi daga fuskarta, kallonta yake yana ganin kamanninta nata ne, amman gabaki daya yanayinta yasa ta zame mishi baquwa, bai taba sanin tana da wannan bangaren bama balle yai tunanin ganin shi wata rana.

“Aurenka nake so ka saukake mun”

Ta furta da wani irin yanayi daya sashi zama. Ko dai Waheedah nada aljanun da baisani bane sai yau, ko kuma watakila batasan yanda kalmanta suke mishi kamar ta watsa mishi garwashin wuta bane shisa

“You are hurting me…Waheedah dan Allah… Kiyi hakuri… Shikenan? Hakuri kike so in baki?”

Kalaman suka kwace mishi batare daya sani bama, kallon shi take, yaune rana ta farko a tsayin shekarun data sanshi da taji kalmar hakuri ta neman afuwa akan labban shi, sai dai zuciyarta kamar dutse take jinta, babu abinda hakurin shi ya motsa a kirjinta balle yai tasiri. Muryarta na rawa tace

“Ka sakeni… Shi nake so”

Ciwon kan da yake ta fama dashi yaji yana karuwa, ya kasa gane kanta, ko kadan ya kasa gane kanta balle yasan ta inda zai bullo ma abinda yake faruwa.

“Kinsan girman kalmar da kike fada? Kinsan babu kyau mace ta furta ma namiji kalaman nan?”

Duk da hawayen dake zubar mata saida murmushi ya kwace mata

“Zakafi kowa bada tabbacin naje islamiyya Sadauki, kaman yanda zan bayar akanka, an halarta mun neman sakina idan bazan iya zama dakai ba… Zan biyaka sadakinka karka damu…”

Ta karasa tana sa wata irin dariya kubce mishi, ya lallabata, yayi duk iya abinda zai iya, baisan me take son samu daga wajen shi haka data zabi wannan hanyar ba, mamakinta yake sosai, ance kana sanin halayen mutum fiye da ko yaushe idan zamantakewa ta aure ta hadaku, Waheedah nason karyata kowaye ya fara fadin kalaman, dan yanzun bazai iya bada shaida akan halayyarta ba, da wani yanayi a muryar shi yace

“Me kike so daga wajena?”

Dan in bayau ba, shi bai mata komai ba, wata rigima bata hadasu da zata zabi daga mishi hankali haka ba. A gajiye ta amsa shi da 2

STORY CONTINUES BELOW


“Sau nawa zan maimaita? Ka saukakemun auren ka”

Tashi yayi daga kasa yana komawa kan kujera, yaga alamar tashin hankalin shi take son yi, nata kuma babu yanda za’ai ya kwanta, baisan kalar wasan da takeyi dashi ba, amman zai biye mata harya gane kan wasan, sai yasan hanyar dazai bi yai nasara akanta.

“Ko meye yake fada miki zaki samu abinda kike nema yaudararki yake yi…”

Ya fada mata yana tabbatar da kalaman sun zauna mata, zaiga wanda ya isa yasa shi sakinta tunda igiyoyin a hannun shi suke. 4

“Abba…”

Waheedah ta kira idanuwanta cike da hawaye, zaman shi Abdulkadir ya gyara kan kujera yana jin shigowar su. Suka zazzauna banda Anty datai tsaye inda take kafin ta fita daga dakin. Kallon su Abba yayi, fuskar Abdulkadir tana tabbatar mishi basu cimma wata matsaya mai kyau ba, duk da yayi wannan addu’ar, bayason Abdulkadir ya rasa Waheedah din, amman ba za’a hadu dashi aci gaba da zaluntar marainiya ba. Baida karfin daukar zunuban nan kam.

“Abba ku fada mata, ni ban shirya rabuwa da ita ba… Ku fada mata”

Abdulkadir ya fadi yana kara gyara zaman shi, karyar hauka Waheedah take, aure yanzun yakejin ya fara yinshi da ita, dan bai amsa karbar aurenta a masallaci ba saida niyyar mutuwa ce kawai abinda zai raba igiyoyin da suka qulle su a ranar. Baiga meye zai canza wannan ba. 1

“Kaji shi ko Abba? Bazan iya komawa gidan shi ba nikam… Dan Allah ku bashi hakuri ya saukakemun…”

Waheedah ta fadi cikin tashin hankali, cikinta har yamutsawa yake da tunanin komawa gidan shi, karfinta ya gama karewa gabaki daya.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Anty ta fadi, tana sa Abdulkadir juyawa ya kalleta

“Kifa daina salati tunda auren bai mutu ba, ba kuma mutuwar zaiyi ba” 3

Idanuwan Hajja a waje tace

“Abdulkadir…”

Ranshi a bace yake, sosai ranshi ya jima bai baci irin na yau ba

“Salatin me take yi to Hajja? Ni banma san me takeyi anan ba wallahi” 11

Abba ne ya kalle shi yana girgiza kai

“Ai ba zaka taba sake halin ka ba, ba zaka sake halinka ba Abdulkadir…ni bazan bata hakuri ba, Allah kadai yasan me take qunsa a zama dakai…tunda ta nemi ka bata takardata ai shikenan…”

Wata yar gajerar dariya Abdulkadir yayi da bata da alaqa da nishadi, yasan Abba ba sonshi yake wani yiba, ba tun yanzun ba, yanda ya goyi da bayan Waheedah bai bashi mamaki ba, baibi takan Anty ba, ra’ayinta ko abinda take tunani bashida muhimmanci a wajen shi. Hajja ya kalla da yake ganin hawaye cike da idanuwanta

“Abin nan baimun dadi ba sam…ni dai ko meye ya faru dan Allah kuyi hakuri, kuba abin kwana biyu tunda duk kun hau dokin zuciya… Idan kuka sauko sai ayi magana”

Kai Waheedah ta girgiza ma Hajja

“Ko an kwana biyu bazai canza wani abu ba…gara nidai yaban takardata yau, Abba zan mayar mishi da sadakin shi…”

Rai a bace Abdulkadir yake kallon ta

“Zakuma ki bani yarana…”

Wannan karin zuciyarta taji ta motsa, da karfin gaske, idanuwan shi ya tsayar cikin nata

“Ba Fajr kadai ba, har Ikram…”

Da wani irin tashin hankali take kallon shi

“Alhaji kana jinsu, a gabanka suke wannan rashin hankalin…”

Hajja ta karasa maganar wani hawayen bakin ciki na zubo mata.

“Kasan me kake fada Abdulkadir? Jaririyar kake cewa zata baka? Kayi yaya da ita to?”

Abba yake tambaya yana kallon shi

“Wallahi har ita saita bani, Abba kaji ita me take furta mun ai bakai magana ba, saini dan nace taban yarana zai zamana rashin hankali?” 8

Numfashi Abba ya sauke

“Karka kara batamun rai fiye da wanda nake ciki, banason furta wasu kalamai marassa dadi a kanka Abdulkadir, batun yanzun kake kure hakurina ba…”

Jikin shi Abdulkadir yake ji har bari yake saboda bacin rai, wani irin kallo ya watsa ma Waheedah da duk ita ta ja mishi wannan tijarar, ya kuma kudurta ranshi bazai baci shi kadai ba, tashin hankali take nema ta kuma samu, yaga alamun duka laifin komai suke so su dora mishi, da yayi wani abu mai girma ne ma ranshi bazai baci har haka ba, babu abinda yayi da za’ai saka shi a gaba haka. 2

“Abba nasan ba wani sona kake ba daman, ba tun yanzun ba nasani, amman duk da haka ya kamata aimun adalci, saika tambayeta idan na mata wani abu” 1

Da mamaki Abba yake kallon shi, cikin yaran shi zaice daga shi sai Waheedah yafi kula da lamurran su, yake kuma jin shaquwa taban mamaki dasu, Waheedah saboda hakuri da hankalinta, Abdulkadir saboda yawan kawo mishi karar shi da akan yi, da kuma zuciyar da Allah ya halitta mishi ta saurin fushi, yasa babu ranar da yake gidan da baya kiran shi dakin shi dan sulhunta tsakanin shi da wani a cikin gida, ko kuma yi mishi fada kan koyon hakuri, amman shi yau yaron zai kalla yace baya son shi, wanne kalar soyayya ce bai nuna ma Abdulkadir ba.

“Abdulkadir…”

Hajja ta kira, Abba na katse da

“Ki kyale shi Hajiya Furaira….ki kyale shi”

Mikewa Abdulkadir yayi yana kallon su gabaki daya

“Ni dai ku fada mata, zata bani yarana…” 1

Wannan karin hawayen da Waheedah taji ya zubo mata daga abinda yai saura mai motsi a zuciyarta ya fito, dan saida taja kafafuwanta tana hade su da jikinta ko zata samu sauqin ciwon da fitowarsu ya bar mata, idanuwanta ta sauke cikin nashi da suke fal da kwantanccen rikici, muryarta dauke da wani irin yanayi tace

“Wannan shine sharadin ka? Yarana kake son amfani dasu Sadauki? Shikenan…naji na dauka, ka saukakemun, ga Ikram nan bayan Anty ta baka ita, Fajr na cikin gida nake tunani saika dauke shi, Allahu ya rayasu cikin aminci…” 7

Anty da take tsaye batasan lokacin data juya tana nufar hanyar dakin baccin ta ba, dan wani kuka ne ya kwace mata, zuciyarta ta gama karyewa da abinda yake faruwa, Hajja ma mikewa tayo tana kallon Abba kamar shine sanadin komai tunda yaki musu magana, ba a gabanta zasuyi wannan rashin hankalin ba. Ficewa tayi daga falon, Abba ma mikewa yayi yana basu waje ganin kallon da suke ma juna da alama sunma manta basu kadai bane a dakin.

Tunda ta fara magana, yanayin muryarta yasa ko numfashin shi a hankali yake zarya, iskar wajen kanta tsaye Abdulkadir yaji tayi, kamar itama tana son tayashi mamakin Waheedah, dan ya tabbatar ba shi kadai yake mamaki ba, bazai hada yanda yake ganin soyayyar shi da ta yaransu a idanuwanta ba, tasha nuna mishi yanda yake da muhimmanci akan komai na rayuwarta, sai dai bai taba tunanin zata iya ce mishi ya dauki yaran dan ya rabata da auren shi ba, girgiza tayi kadan ya dora halin da yake ciki a yanzun, a cikin idanuwanta yake ganin yanda komai ya fara.

TUNA BAYA…!!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *