BATUUL CHAPTER 19

BATUUL




CHAPTER 19





Jin muryar Ammah ya d’aga kai yana kallon Ajiddeh, a fusace Ammah tace “Kana ji na ka min shiru Aliyu” yyi kasa da kai yace “A’a Ammah ina yini?” cike da fada tace “Rike gaisuwar ka, maxa tun muna mu biyu gobe ka taho min da Batuul gida, ai tun ba yau ba nasan kai shashasha ne, uwar ka cikin ya tsare maka kake son a cire” kasa cewa komai yayi, Ammah tayi ta bambami ya bari tayi mai isarta sannan a hankali yace “Ammah tana wahala ne, ki tambayi farida in ta iso gobe” Ammah tace “Ya baxa tayi wahala ba kana xaune da makira a gida a matsayin mata sun sa min ita a gaba, ina me tabbatar maka xaka ga the other side of me idan abu ya samu Bitti, maxa ku bar asibitin nan gobe ku biyo 1st flight ka dawo min da ita Nigeria” Ammah na kai wa nan ta katse wayar, ya daga kai yana kallon Ajiddeh dake jingine jikin bango duk jikinta a sanyaye, ajiye wayar yayi yace “Why did you call her?” Bata ce komai ba ta juya ta fice daga ward din, juyawa yayi a hankali yana kallon Batuul dake bacci, dawowa yayi kusa da ita ya daura hannunsa a hankali kan fuskarta, sosai ta rame daga jiyan xuwa yau, lumshe ido yayi cikin sanyin murya yace “Get well soon wife” mikewa yayi jiki ba kwari ya koma gun likitocin don dakatar da su, A asibiti suka kwana ranan don gani yake suna komawa gida ciwon xai tashi, sai dai throughout daren ko farkawa Batuul bata yi ba, a spare bed din dake dakin Ajiddeh ta kwanta, sai dai kwata kwata ta kasa bacci ta rasa me ke damunta, Abuturrab dake xaune kan darduma a dakin yana kula da yanda take ta juye juye sai dai bai ce mata komai ba, da asuba suka bar asibitin don bai son suyi missing 1st flight kamar yanda Ammah ta bukata duk da he is not sure xa su samu, a mota yana driving ya d’an kalli Ajiddeh yace “We will be leaving for Nigeria, xan maida Batuul gida, you take care….” Bai karasa ba ta katse shi tace “Nima xan je” kallon ta ya kuma yi sai dai bai ce komai ba ya ci gaba da driving dinsa yana yi yana kallon Batuul da har ta koma bacci a bayan motar. Ba tare da bata lokaci ba duk suka shirya, Batuul dama shi ya taimaka mata tayi wanka ta shirya don yaga alamar in suka biye ta nata bacci kawai xata yi tayi, Biyar saura suka isa airport yayi masu booking, biyar da rabi suka yi set off for Nigeria, duk motsin da Batuul dake rungume jikinsa xata yi idonsa na kai don waje daya suka xauna har lokacin kuma bacci take, lkci lkci kuma ya kan juya ya kalli Ajiddeh dake gaba ta saka earpiece, sai a sannan ya fara tunanin sudden change dinta is it for real, maganganun da Ammah ta fadi masa jiya suka fado masa, wai sun sa Batuul a gaba, ya sauke ajiyar xuciya don shi bai yrda da wannan belief din ba, a hankali Batuul ta bude ido tana kallonsa, ganin yanda ta bata fuska gabansa ya fadi a hankali yace “What?” Ta rike hannunsa tace “Ya Abu cikin xai fara” hankalinsa ne ya tashi ya daura hannunsa a cikin yace “No, no baxai fara ba idan Allah ya yarda” runtse ido tayi jin kamar ana murda mata cikin ta sakar masa kuka tace “Wllh ya Abu ya fara” ya rungume ta sosai yace “Noo wife baxai fara ba in’sha Allah, ko yunwa dai kike ji…” Ta fashe da wani kukan tace “Wayyo ya Abu cikin ya fara min” Kallon su kawae Ajiddeh ke yi, can kuma ta maida kanta kan wayarta, ganin kuka sosai Batuul ke yi jikinsa tana rike da cikinta ya kalli Ajiddeh suka hada ido, dauke kai tayi, ya sake Batuul ya mike ya tafi gunta cike da damuwa yace “Babe kin ji wai cikin ya fara, how are we going to do it, gashi ba muyi rabin journey ba har yanxu fa” ba tare da ta kallesa ba tace “Ba sai kayi ta tofa mata addu’a ba” yace “Yea haka ne kuma” juyawa yayi da sauri ya koma gun Batuul da ta hade kanta da gwiwa har ta hada xufa don axaba ita kanta baxa ta ce ga yanda cikin yake mata ba, ya xauna ya dagota ya kwantar da ita jikinsa yace “Sorry wife xai daina in’sha Allah” a hankali ya dinga tofa mata addu’a tana jikinsa, sun kusa awa biyu a haka har dai yaji ta daina kukan da take a hankali, ya leka fuskarta ya ga bacci tayi, ya sauke ajiyar xuciya ya lumshe ido ya manna mata kiss a forehead dinta, yana bude ido suka yi ido hudu da Ajiddeh dake kallon su, dauke kai tayi da sauri, ya ji wani iri shima ya dauke nasa kan. Shidda na yamma jirginsu yayi land a Nnamdi Azikwe Airport, ya kunna wayarsa ya shiga kiran layin Sadeeq, yana d’agawa yace “Hello Bro, ka taho kayi picking dinmu muna airport” daga haka ya katse wayar, ya kalli Batuul dake kwance jikinsa idonta lumshe duk da ba bacci take ba and he can see how happy she is to be home, ko bata fadi ba, Ajiddeh kam nesa da su ta xauna, bude ido Batuul tayi da sauri, yace “What?” Kallon matar dake xaune daga gefensu tana cin popcorn tayi ta bata fuska tace “Bana son kamshin xai sa ni amai” mikewa yyi da sauri ya d’agata suka bar wajen, Ajiddeh ta bi su da kallo, wani gun ya koma suka xauna, boye fuskarta tayi da sauri a kirjinsa yace “What again?” Kamar xata yi kuka tace “Bana son kamshin turaren mutumin nan” juyawa yayi ya kalli Mutumin dake xaune gefensu, ya mike ya dagota suka kuma barin wajen suka koma wani gun suka xauna, plantain chips taga wani yaro na ci ta kallesa da sauri tace “Ya Abu xan ci” yace “Me za ki ci?” Ta turo baki ta nuna masa chips din, kallon ta yayi, sai kuma ya mike ya nufi inda yaron da Mamarsa ke xaune yayi masu sallama yace “Don Allah a ina ku ka siya chips din nan Anty” matar tace “Ai kam ba nan muka siya ba” yace “Toh nagode” juyawa yayi ya koma gun Batuul ya xauna yace “Ki bari idan xa mu gida in siya maki a hanya suma ba nan suka siya ba” kamar xata yi kuka tace “Noo Ya Abu yanxu nake so wllh, kila anjima baxan iya ci ba xai fita raina” murmushi yayi ya jawota jikinsa yana shafa cikinta a hankali yace “Shi babyna yake son ci yanxu koh?” Bata fuska tayi, yayi dariya ya manna mata kiss ya cheeks dinta yace “Don’t worry, it’s nothing don babynmu yasa mu roko a airport” mikewa yyi ya koma gun masu chips, yana d’an Shafa kai yace “Anty ko xaku d’an san mana chips din k’adan, matata ce wai shi ke ranta taki bari mu fita mu siya” dariya matar tayi tace “Allah sarki duk mun cinye a jirgi amma bari in dibar mata na Kamal” yayi murmushi yace “Toh mun gode” ta karbi na hannun yaronta tace “Kamal idan mun fita xan siya maka wani ka ji” ya gyada mata kai, ta d’an dibar masa k’adan ta mika ma Abuturrab sauran na ledan ya karba yana murmushi ya shafa kan yaron yace “Toh mun gode kwarai Anty da kamal” tayi dariya tace “Babu komai, Allah dai ya raba lafiya” murmushi yayi ya juya yace “Toh Ameen” duk wannan abinda suke Ajiddeh na kallon su kuma tana ji, ya koma gun Batuul ya d’ago kanta yace “Oya ga chips Maman twins” hararansa tayi ta fada kansa ta shagwabe murya tace “Ni Allah bana so” dariya yayi ya dauki chip daya yace “toh na daina, bude bakin” ba musu ta bude ya d’an gutsura k’adan ya saka mata sauran a baki. Mikewa Ajiddeh tayi ta fice daga waiting room din ba tare da ya lura da hakan ba, haka yayi ta ba Batuul chips din har tace ya isheta, wayarsa ya shiga ring ya fiddo ya ga sadiq ne, mikewa yayi ya dagota yace “Sadeeq na jiranmu” sai a sannan ya kalli inda Ajiddeh take ya ga ba ta, waige waigen inda xai ganta ya fara yi amma bai ganta ba, yana rike da Batuul suka fita.Suna cikin tafiya ta tsaya, ya juya yana kallonta yace “What?” Murmushi ta k’irk’iro ganin irin kallon da yakeyi mata tace “Am fine”, kallonta yakeyi har lokacin yace “are you sure? Ko dai ya fara?”, da sauri ta shiga girgiza kai tana sake wani murmushin da kana gani kasan ba na gaske bane, kyaleta yayi badan ya yadda ba ya tallafota jikinshi tareda kwantar da kanta kan kafad’unshi yace “okay let’s get going Sadiq is waiting”, suna d’ago kai suka hango Sadiq na waving musu da wide smile shimfid’e a fuskanshi, ya tara gashi a kanshi sai ya k’ara mishi kyau, ido ya wara ganin Batuul yace “Batuulan Aunty is that you?”, baki ta zumb’uro mishi tayi raurau da ido tace “Its Batuul ba Batuula ba”, dariya ta bawa Sadiq yace “kin ganki kuwa?, Yaa Abu mey kake bata haka, you can see her glow from a far, she has changed tayi kyau sosai”, harara Abu ya sakar mishi tareda turo mishi trolley d’in yace “Let’s get going, you are tiring her da unending surutunka”, tafiya Sadiq d’in ya fara yana dariya yace “Its okay ba sai kin fad’amin yanzu ba, we will meet ltr ko Batuulan Aunty, rabu da Yaa Abu, he doesn’t know”, ya fad’a mata yana kashe mata ido d’aya, tsaki Abu yaja yace “hand me the key, in ka gama surutun ka samemu a gida”, dariya kawai Sadiq yayi bai sake cewa komai ba, a mota suka tarar da Ajiddeh, sai lokacin ya tuna fa suna a tare tun lokacin da ta bar wajen, da unreadable expression d’in dake fuskanta ta kalleshi ganin yanda yake riqe da Batuul tace “bari in dawo baya in zauna da ita, you can sit here ta fad’a tana k’ok’arin barin gaban motan, kai ya kad’a mata yace “No you can stay back babu komai, she will be fine”, shiru Ajiddeh tayi tana kallon yadda yake handling Batuul d’in har ya zauna ya gyara mata zamanta, a hankali ta janye idonta a kansu tana jin wani abu har cikin ranta ta maida kallonta gaba jin mey Sadiq ke fad’i, da k’yar ta bud’e baki tace “Handsome you said?”, hannu Sadiq yasa a cikin gashinshi jin dad’in sunan da Ajiddeh ta k’irashi da yana murmushi yace “Naga ne kun canja Batuul totally, tayi wani irin fresh da zuwanta for months, ko nima in zo ne a rik’a bamu abinda ake batan tare” kallon Batuul dake d’an mutsu mutsu Abutturab na mata magana k’asa k’asa tayi ta mirror sannan tayi maza ta d’auke kallonta daga kansu tayi murmushi tana kallon Sadiq, ya kad’a kai yace “gaskiya UK ya karb’eta, haka sukayi ta hira yana tuk’in, suna cikin hiransu sukaji kukan Batuul d’in, a hanzarce suka juyo ganin mey ke faruwa, rungume suka ga Batuul jikin Abutturab sai kuka take tana riqe da cikinta, da sauri Sadiq ya ja brake gefen titi yace “What’s wrong with her Yaa Abu ko mu k’arasa asibiti ne if she isn’t feeling well?”, kasa magana yayi sai alama da yayi mishi da yaci gaba da driving, Ajiddeh ce tayi k’arfin hali tace “Sadiq let’s get going, she needs rest”, hakan akayi Sadiq ya tada motan sukaci gaba da tafiya, Batuul kam sai kuka takeyi tana riqe da cikinta duk ya rikice ya rasa ya zaiyi, tunda Ajiddeh taga an d’auki hanyan gidansu Abu jikinta yayi sanyi gabanta ya rik’a fad’uwa, taso a kaita gidansu ko kuma gidanta da bata tab’a sanin ya yake ba dan ba tab’a zuwa tayi ba amma tasan yanzu its already late, horn Sadiq yayi bakin k’ofa yana jira a bud’e gate daidai nan Ajiddeh ta d’ago kanta jiki a sanyaye tana kallon cikin gidan, tun Sadiq bai gama parking ba Abu ya bud’e k’ofa ya fita, duk tsayawa sukayi suka bishi da ido ganin yanda ya rikice gaba d’aya, jiki a sanyaye ta sauk’e idonta, Sadiq ne da yayi noticing uneasiness da restlessness d’in dake tattare da ita yayi maza ya bud’e ya zagayo ta gefenta ya bud’e mata k’ofa da murmushinshi mai kyau yace “Muje ko Anty?”, haka ta janyo handbag d’inta ta fito daga motar, Sadiq yace “Let me help with d bag Ma’am”, wai ko ta d’an saki jiki, batace komai ta mik’a mishi jakar ya shiga gaba ta biyoshi a baya, da sallama ya Abu ya shigo parlour dake d’auke da wani ni’imtaccen k’anshi da sanyi kamar kullum, Ammah dake zaune cikin hanzari ta mik’e tana kallon yanda Batuul d’in ke jin jiki tace “Subhanallah, Abu yanzu haka yarinyar nan ke wahala amma kaje ka zauna kaqi dawo min da ita, wane irin hali ke gareka wai?”, kasa cewa komai yayi sai kwantar da ita da yayi kan doguwar kujera, ya zauna daga gefenta ya dafa kanshi da duka hannayenshi biyu, Farida ce ta sauk’o a guje tana fad’in “Ammah na fad’amiki haka yakeyi mata kullum, koh ranan fa tana bacci kawai cikinta ya fara ciwo, Ammah mu kaita asibiti Dan Allah kar wani abin ya sameta, am with a key”, ta fad’a tana k’ok’arin jin d’umin jikin Batuul, Ammah ce ta dubi Abu tace “Abu ba magana nakeyi maka ba, tun yaushe ta fara ciwon?”, jajayen idanunshi da suka rine ya d’ago saura kad’an hawayen dake cikinsu ya zubo, ji kawai Ammah tayi ya rungumeta, cikin sanyi yake cemata “Ammah plss help her, bazan iya jure rashinta ba I need her to get well Ammah, kuyi wani abu nima bansan mey ke damunta ba, I don’t want to lose her, Plsss Ammah”, daidai nan Ajiddeh da Sadiq suka shigo parlour, kallo d’aya Ammah tayiwa Ajiddeh ta d’auke kanta ta d’ago Abu da ya kwantar da kanshi jikinta ta kama fuskanshi da hannayenta duka biyun tace “You have to be strong, babu abinda zai sameta da izinin Allah, just pray for her kaji?”, Kai kawai ya iya d’aga mata kamar wani k’aramin yaro, gaban Batuul d’in ta dawo ta rik’e mata hannaye tace “Bitti sannu kinji, kin kusa samun sauk’i In sha Allah”, Batuul kam bata iya cewa komai sai kuka da take tana k’iran sunan Aunty, Ajiddeh har lokacin tana tsaye ta rasa mey ma zatayi gashi babu wanda yabi ta kanta har Abutturab d’in, kamar dama baisan da ita wajen, wayanta ne ya fara ringing cikin jaka, gabanta ne ya shiga fad’uwa ganin mai k’iran nata, Mumm ce ke kiranta, bata d’auka ba saima sawa da tayi a silenta, tana gani haka Jainaba ma ta k’irata amma har lokacin bata d’aga ba daga k’arshe ma kashe wayan tayi gaba d’ayanshi, Addu’a Ammah ta shiga tofa mata, da kad’an kad’an kukan nata ya fara yin sauk’i sai juye juye da take, snn ta d’ago ta dubi Abu tace “kai min ita d’aki”, Sadiq dake fitowa part d’insune yaga Ajiddeh tsaye har lokacin yace “Noo, badai tun d’azu kike tsaye nan gun ba, find a place and settle yourself”, d’an murmushi ta k’irk’iro mishi ta nemi waje ta zauna bakin kujerun parlourn kamar wata mara gaskiya, ko kallonta Ammah batayi ba tayi side d’in Abui, Abu ta kalla tace “Babe ya jikin nata?”, kai ya d’aga mata tareda cewa “she needs rest”, ya haura sama da ita, a kan gadon d’akin Ammah ya kwantar da Batuul d’in, samun kanshi yayi shima da kwanciya daga gefenta, rungumeta yayi tsam jikinshi ya saka hannayenshi cikin nata, a hankali kamar wani d’an yaro ya fara mata hawaye, “Fatima I promise to give you all you ever requested for, kiyi hakuri ki tashi ki fad’amin abinda ke damunki, its gonna be hard to live with out you kinji, am used to you kinji Fatima, I will keep you and my unborn baby happy, no harm will befall you just get up and we will live happily”, duk surutun nan da yakeyi ko kad’an Batuul bata san abinda yake fad’i ba don tuni baccin wahala yyi gaba da ita, haka yayi ta surutunshi, vibration d’in wayanshi ya katse shi ya kwantar da ita a hankali yayi snn yayi receiving call d’in, “Man ba yau mukayi dakai zaka dawo ba, but Ammah ta qirani wai tana nemana snn kaima ka dawo”, ajiyar zuciya ya sauk’e snn yace “I had to comeback, Batuul batajin dad’i”, “Subhanallah mey ke damunta, how is she feeling now?”, juyawa yayi ya dubeta tana bacci snn yace “Alhamdulillah she is getting better, in kazo we talk”, da haka suka gama wayan, fuskanshi ya shafa yana salati ya mik’e, kamar kar ya barta a d’akin ya fice, Ajiddeh na ganinshi yana sauk’owa kan stairs ta mik’e tsaye, saida ya ka’araso parlour ya lura da ita, jiki a sanyaye tace “Zan tafi gida”, kallonta ya tsaya yi for some seconds snn yace “nanma gida ne, you can’t live ke kad’ai to a new home da ba a tab’a shiganshi ba”, kai ta girgiza mishi tace “gidanmu fa zan tafi”, “You can stay here in zan tafi sai mu tafi tare”, da haka ya k’yaleta nan tsaye yayi side d’in Abui.Ta kai 10mins tsaye tana jiran ganin Abu ya fito amma har lokacin shiru, jikintane ya k’ara sanyi taja k’afafuwanta ta koma kan kujeran palon, in banda masu aiki dake kaiwa da komowa bata ganin kowa, ko Farida ma bata sake ganinta ba, haka nan ta zauna jigum sai sak’e sak’e take tana warwarewa, can bayan wajen minti ashirin ta jiyo motsi, da sauri ta wartsake daga gyangyad’in dake shirin d’aukarta, k’ofan ta kafawa ido, Abui ne ya fara fitowa kamar kullum yana cikin shigarshi ta girma, murmushin nan na fuskanshi, Ammah ce daga bayanshi sai Abutturab k’arshe, kamar wata mara gaskiya tana hangosu ta mik’e tsaye, a diririce ta bud’e baki da k’yar ta iya gaishesu, Ammah kam ko kallonta batayi ba bare ta amsa mata gaisuwar, Abui ne yace “Lafiya kalau, ya gida ya kuma mai jiki, ashe y’ar uwartaki bataji dad’i ba”, murmushi ta k’irk’iro tace “Alhamdulillah, tama fara jin sauk’i”, Abui ya kad’a kai yace “Allah ya bata lafiya yasa kaffara Ne”, daga haka yayi hanyan waje tareda Abu, itakam tsayawa kawai kallonshi tayi ganin ya fita baice mata komai akan tafiya gidansu da zatayi ba, haka ta koma ta zauna jiki a sanyaye kamar ta kurma ihu, wayarta ta ciro cikin jaka ta kunna ta, kamar jira ake ta kunna nan da nan msgs suka fara shigowa kuma duk yawancinsu daga Mum ne, ignoring d’insu tayi baki d’aya ta mik’e tayi d’akin Abu.



+

Ammah kam na hawa sama bayan fitansu Abui d’akinta ta wuce kai, Batuul na kwance abinta tana bacci kamar ba itace d’azu ke kukan ba, amma da gani baccin baya mata dad’i, daga gefenta ta zauna tana kallon yanda ta k’ara haske tayi kyau ta rame, hannu ta d’aura saman goshinta taji babu wani zafi, kallon Batuul d’in kawai takeyi tana jin yadda tausayinta ke ratsata, yarinya k’arama da ita amma saida aka samu wani Mara imanin yayi mata wani abin, duniya babu kyau, babu ruwanka da rayuwar mutum amma idonshi yana kan naka rayuwar, in banda rashin adalci da rashin tausayi meye ma Batuul da har za ayi mata asiri, babu komai da izinin Allah sai aikinsu ya lalace, a hankali ta furta “sannu Fatima, Allah ya baki lafiya”, sannan ta mik’e ta bud’e closet d’inta ta ciro wani d’an kwalba mai d’auke da ruwan Zamzam ta dawo bakin gadon ta bud’eshi ta tsiyaya kad’an a hannunta ta shafawa Batuul d’in a fuska, wani irin numfashi taja jin ruwan a jikinta, juyawa tayi ta gyara kwanciyarta daga haka taci gaba da baccinta, intercom Ammah ta d’auka ta k’ira d’aya daga cikin masu aikinta, babu b’ata lokaci d’aya daga cikinsu tazo, “inaso ki wanko min Baby cucumber, ki tabbatar ya wanku da vinegar snn ki tafasa fresh milk sai ki jefa cinnamon da cardamom kad’an kada a saka sugar, ki Juyo min a flask, bada dad’ewa ba, snn a d’ora soup d’in offal’s”, yarinyar dake sanye da uniform d’in cooks tace “okay Ma, za ayi wani abin ne kuma?”, Ammah tace “No for now dai babu, ba kun d’ora lunch ba?”, yarinyar ta kad’a kai tace “Ehh Ma”, Ammah tace “toh shikenan kije ku gama wannan, and be fast”, da sauri yarinyar ta amsa ta fice abinta,




Ajiddeh na zaune d’akin Abu duk abin duniya ya taru yayi mata yawa, ta rasa mey ma zatayi taji dad’i, har ga Allah ba son Batuul takeyi ba bare ma a matsayin kishiya amma batason ta zama silar mutuwarta, ko ba kishi musulmace kuma ta san hukuncin kisa kan musulmi, ita inda yadda za ayi kawai ayi koma meye a rabata da gidan amma banda kisan kai, ko haukatata ne ayi, gabanta na fad’uwa take kallon wayan da ta saka silent na ringing, tun d’azu ake k’ira amma ta kasa d’auka, da k’yar ta sa hannu tayi sliding ta kara wayar a kunnenta, tun kamin tayi magana taji muryar Mum na cewa “Dan ubanki tunda yarinyar kanwar uwarkice dole kiqi d’aukan wayata, wlhy Ajiddeh kina jina, kada ki kuskura raina ya b’aci kanki, wani abu ya shiga kanki ne shegiyar yarinya inace akanki nayi sa’ar haihuwa ashe wahalar banza nasha, toh tun wuri kisan abunda kikeyi tun kamin inyi maganinki” Kamar wacce za a jiyo maganan da takeyi tace “Mum mey yayi zafi toh hka, naji kiyi duk yadda kike so amma fa babu ruwana inta mutu, I just want to be happy, yanzu haka mun dawo Nigeria kan ciwon nata muna gidansu Aliyu yanzu haka”, kirji Mum ta dafe tace “Naga ta kaina ni Zuwaira, yanzu dan uwarki Ajiddeh kina garin nan shine baki fad’a mana ko kizo gida ba, gidansu miji yafi miki dad’i ko, ina zansa kaina yau dan takaici ni Zuwaira, anya kanki d’aya kuwa Hauwa, lokaci d’aya ki juye ki zama wata sakarya sallamamiya, Wato Bilkisun asirce min keh tayi ko, Ta Allah ba tata ba, duk sai nayi maganinsu daga ita har y’ay’an nata, kuma ki tabbata kinzo gida yau”, shiru Ajiddeh tayi tama rasa mey zatace, “Toh” kawai ta iya cewa ta katse wayan, tashi tayi ta fito daga d’akin tayi hanyan d’akin Ammah, saida tayi sallama snn tajiyo muryan Ammah na cewa “Bismillah shigo”, tura k’ofan d’akin tayi ta shigah Ammah na zaune kan abin Sallah ta idar da Sallah kenan, waje Ajiddeh ta samu ta zauna tana kallon Batuul dake kwance, takai 5mins kamin ta iya bud’e baki tace “Ammah ya jikin nata?”, Ammah ta kalli Batuul dake kwance snn tace “Bacci takeyi tun d’azun, kuma da izinin Allah zataji sauk’i”, daga haka basu sake cewa komai d’akin shiru, Farida ce tayi sallama ta shigo, da mamaki ta tsaya kallon Ajiddeh, rabonta da ganinta a d’akin tun satin bikinsu da Yaa Abu, tab’e baki tayi ta k’arasa shigowa, daga gefen Batuul d’in ta zauna tana kallonta da tausayi tace “Ammah ya jikin nata?, ta farka tun bayan fitana?”, kai kawai Ammah ta gyad’a mata alamar A’a, Hannu tasa ta kamo na Batuul tace “Allasarki bestfriend , you will get well soon kinji, In sha Allah”, tacewa Ammah, “Ammah mu tafi asibiti mana, turawan nan duk ba aikin kirki sukayi ba, a kaita wajen Dr Zakaa tunda gynaecologist ne zai iya duba matsalarta, tunda cikinta take cewa kullum”, Har saida Farida tayi shiru kamar baza tace komai ba can tace “Ai ciwon nata bana asibiti bane, Abui sun tafi tahowa da Ashiekh Zai mata addu’a ya gane mana matsalar”, k’ululu cikin Ajiddeh yayi k’ara, gani kawai takeyi Ammah tasan abinda ke faruwa, har zufa taji yana tsattsafo mata, Farida tace “Subhanallah, Ammah Jinns ne suka tab’ata?”, Ammah tace “tashi kije ki kitchen ki dubamin ko sun gama aikin da na sakasu, kice su hanzarta, banaso ta farka babu komai a kusa”, “Toh”, Farida tace tasa kai ta fice,





Lokacin dasu Abutturab suka fita kai tsaye airport sukaje d’auko Asheikh, shike tuk’a motar Abui da malamin a baya amma gaba d’aya hankalinshi na
Kan Batuul, wayan Batuul dake wajenshi ya katse mishi tunani jin yana ringing, dubawa yayi yaga ansa Anty with all sort of hrt Emojies, baiyi picking call d’in ba har ya katse, haka a karo na biyu ma bai d’auki wayan ba, uku da rabi suka iso gida, a guest side aka sauk’eshi, saida Abu ya tabbatar komai daidai snn yayi d’akin Ammah, so kawai yake yaga lafiya, a hankali ya tura k’ofan d’akin ya shiga, babu kowa cikin d’akin sai sanyi da k’anshi mai dad’i, har lokacin Batuul na kwance tana bacci, ajiyar zuciya ya sauk’e snn ya k’arsasa shiga, bargon ya janye bayan ya zauna daga gefenta,murmushinshi mai kyau yayi ganin cute face d’inta da ya k’ara haske, a hankali ya d’aga y’ar rigar dake jikinta ya tsurawa flat tummy d’inta ido, hannunshi yakai kai yana shafawa, bakinshi ya kai ya d’ora mata kiss kai a hankali ya furta “Your Mommah will get better soon kinji Lil princess”, jin hannu jikinta yasa ta bud’e lumsassun idanunta tana scanning d’akin, murmushi ya sakar mata da yasa itama ta mayar mishi, da sauri yaga ta tashi ta zauna idonta tab da hawaye, tace mishi “Aunty”, hannu yasa ya rungumota ya zaunar da ita kan cinyarshi yace “No Fatima kar ki fara, kiyi hak’uri kinji, kinga bakida lafiya, Aunty da kanta zatazo wajenki kinji, keda zaki koma gidanta ma gaba d’aya ko kin mantaa ne”, k’ara widening smile d’inta tayi ta d’ago tana dubanshi tace “Bazan koma UK ba?”, yana kallon idonta yace “a ba haka kikeso ba, kince in kin bani Babyna zan maidaki wajen Aunty”, zumb’uro mishi baki tayi tace “Toh ai nafison gidan Aunty ne kuma kaine kace in na baka Baby zaka kaini”, kallon d’an k’aramin lips d’inta da yafiso kawai yakeyi, yadda ta zumb’uroshi tana pouting, a hankali ya d’aura d’an yatsanshi kai yana zagayesu ya kafeta da ido yace “Will you miss me in kin koma gidan Aunty?”, kai ta shiga gyad’a mishi da sauri kamar wata yarinya tace “Ehhen, sosai ma, you are kind ai, you have stopped being bad to me”, dariya ta bashi yayi murmushi yace “Was I?”, tace “Of course , but that was then ai, da fa ko bansan kana waje ba if nayi approaching wajen heart beat d’ina increasing yakeyi, it runs at a faster pace, I thought ma mayune suka kamani, Aunty kuma sai tayi ta cewa banida gaskiya, but daga baya sai ya dena, I don’t know mesa?”, matseta yayi jikinshi a kunne ya rad’a mata “Its same with me, duk Inda kike indai naje wajen toh I feel that restlessness, shiyasa I don’t want you kusa dani but nima nawa ya daina, kinsan mey ya janyo duka haka?”, jiki a sanyaye tace “A ah ni ban sani ba”, yayi murmushi ya kamo d’an k’aramin hancinta yace “Its gonna be an assignment, shima sai kin nemo reason d’in before in kaiki gidan Aunty”, ta kalli idonshi da ya fara canja kala tayi murmushi tace “Toh ai zan tambayi Aunty ta fad’amin”, ya d’age girarshi yace “okay…, yanzu malami yazo yayi miki addu’a, kinga hospital duk ba asan mey ke damunki ba, kuma kinga in ya fara kina shan wahala, so we will try na Asheikh, he is a great scholar”, tayi murmushi tace “But ai na warke, kaga I can even jump, dama d’azun kawai shine ya fara”, ta shiga k’ok’arin mik’ewa zatayi tsalle, da sauri ya jawota jikinshi ya had’e rai yace “Baby mana, you will get hurt, da Babyn dake jikinki”, ganin ranshi b’ace itama taji ba dad’i tace “Na dena toh, but ni ai ba baby bace, your other wife is baby, haka kake ce mata itama haka take qiranka”, yayi murmushi ya lakuce mata hanci yace “Okay then you are?…..”, ya tsaya kamar mai tunani, caraf tayi tace “Am Batuul”, kai ya girgiza mata yace “Yeah nasan wannan, I want a name da ni kad’ai zan na k’iranki  dashi”, tace “Ni bana so just call me Batuul d’ina, nafisonshi”, tayi maganan tana barin jikinshi, kamata yayi yace “Wait, ina zaki”, tsuke baki tayi tace “Na gaji da magana ka tafi”, ido ya wara yace “Yaushe kikayi magana, I was d one talking fa, do you know how much I missed you?”, kamin tace wani abu ya had’e bakinsu, tun tana tureshi bataso har ta hak’ura ta biyeshi, jin an tab’a k’ofa yasata saurin turashi amma har lokacin tana jikinshi, Ammah ce ta shigo d’akin, da mamaki ta tsaya kallon Abu da batasan lokacin da ya shigo d’akin ba, raurau Batuul tayi zata sauk’a daga jikinshi amma yaqi sakinta, Ammah ce tace “Kai yaushe ka shigo, yarinyar ba lafiya tana bacci shine saida ka tadata dan neman magana?”, murmushin jin kunya yayi ya shiga sosa kai yace “Ammah ki tambayeta bani na tasheta ba, zaune nazo na sameta tana game”, Batuul kam nok’ewa ta dingayi wai ita kunyan Ammah, ido ta wara jin abinda ya fad’a, da sauri ta sauk’a daga jikinshi, Ammah tace “Bitti ya jikin, yayi sauk’i kenan”, da k’yar Batuul ta iya gyad’a Kai, Ammah ta k’araso gaban gadon tace  “Tashi kici wannan zaisa kiji dad’in jikinki, tun d’azu nake jira ki tashi”, Ammah ta mik’o mata plate d’in baby cucumber da akayi slicing akayi cling filming, sannan ta tsiyaya mata fresh milk d’in dake ta k’anshin Cinnamon da cardamom, kasa karb’a tayi sai Abune ya karb’a yace “Ammah ai baza taci ba, sai na bata”, Ammah ta hararesa tace “Make sure taci, Asheikh ne yace a fara bata, tasha madaran sosai”, yace “In sha Allah” daga haka Ammah ta juya ta fita daga dakin, mikewa yayi ya kuma jawota jikinsa ta fashe da kukan karya tana cewa “Ya Abu ni bana son haka gashi kasa Ammah ta gan ni naji kunya” ya wara idonsa yace “So? Ae bari ma ta dawo ta hada mana ruwan wanka in maki” cusa kanta tayi kirjinsa ta rufe ido tana kai masa duka tana kukan karya, ya kai bakinsa a hankali kan wuyarta ya lumshe ido murya can kasa yace “I… I like you…” Da sauri ta bude ido tana kallonsa, ya wara ido ya shafa cikinta yace “Yes I like my baby”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *