RAI BIYU
CHAPTER 7
Inna ta kai hannu ta kwanto da fuskarta zuwa saman hannayenta tana murmushi. Haske sosai fuskar Habiba take goshinta ya soma taruwa da gumi.
“Allah ga yata nan, ta aikata kurkure kuma na yafe mata, ina roƙon ka Allah ka yafe mata, ka karɓi baƙuncinta, Allah ka zama gatanta bata da gata sai naka, yau ƴata ta koma gareka Allah kuma nasan ba ka yi dan ƴata ba, kuma ba kayi ƴata dan ni ba, Allah ga ƴata nan ta dawo gareka, ƴata mutuminyar kirki ce dukan abunda ta aikata ta aikata ne saboda mu, Allah ka yafe mata, haƙiƙa kai mai yawan gafara ne” 8
Inna ce take maganar tana shafa fuskar Habiba, hawayen idonta na zuba a fuskar Habiba. Sai kuma ta ɗago ta kalleni.
“Kin ga abunda na aikata ko Nawwara? Saboda gudun kunya na kashe ƴata, ba a tambayar Allah miyasa ya aikata abu, abunda ya ga dama shi yake aikata a sanda ya so ga kuma wanda ya so, amman da ace ni ce na mutu a wannan lokacin zai fi, ko ba komai ni naga duniya Habiba ko yanzu take tasowa, Habiba ƴarinyar kirki kin samu rana, mutane da yawa suna fatar mutuwa a cikin wannan ranar ta jumma’ah-” 2
Tsakanin Habiba da Inna sai na rasa wanda zan tausayawa, Habiba da ta bar duniya da ƙirciyarta ko kuwa Inna da zata shiga wani tashin hankalin a dalilin rashinta? 2
“Na rasa *RAI BIYU* Ran mahaufinku da kuma na ƴar’uwarku, na mahaifinku saboda zalinci na ƴar’uwarku kuma saboda talauci, Allah na gode maka” 4
Mai napep ɗin ya juyo ya kalletaa dai-dai lokacin da ya faka napep ɗinsa bakin ƙofar emergency,idonsa cike da ƙwalla ya ce
“Ta mutu ne?”
Sai ta ɗaga masa kai.
“Juya mu koma gida daman ta ce karna kawo ta asibiti”
“Da kin bari an dubata ko dogon suma ta yi”
“Jikina ya bani ƴata ta tafi har a bada, sai idan na iskota” 2
Shi ne ya matsa har aka fita da ita aka shiga da gawarta emergency, likitoci biyu suka dubata suka tabbatar mana da cewar ta mutu, sannan suka saka mana ita a motar ɗaukar gawa na asibiti saboda tausayin halin da suka ga muna ciki, mai Napep ɗin kuma ya ƙi karɓar kuɗinsa sai kuka yake kamar ƴar’uwarshi ce ta mutu. Ni dai bana iya aikin komai sai na kuka har muka iso gida. Jiniyar motar asibitin ce ta ɗago hankali kowa izuwa gidanmu, kan kace kwabo maza da yawa sun taru ƙofar gidanmu cikin har family Babanmu na babban gida, sai kuma family Inna maza da mata wanɗanda suke unguwar da kuma waɗanda bama da wata tazara mai nisa tsakanin unguwarmu da ta su. 2
“Miyasa ta? Tun yaushe ne bata da lafiya?”
Shine abunda kowa yake ta tambaya, masu kuka na yi, ciki har da kawayenta na makarantar islamiya da boko, tsakanin Sakina da Jamila bana iya banbance waye ya fi kuka a tsakaninsu, babu abunda ya fi bani tsoro kamar Noor da ya koma gefe ɗaya ya zauna ya natsu sosai ya kasa ko da guntun hawaye. Jidda ce ta shigo gidan da gudu tana ihu kamar zata tashi gidan, kuka take sosai tana kiran sunan Habiba kamar zata dawo da ita. Inna kan hawaye kawai take iya yi kamar yadda nima nake. Can kuma sai muka ji muryar Noor ya saka kuka ya yi waje da gudu yana kiran sunanta.
“Wayyo Mama Habiba-”
Ɗana ƙarami ne amman yasan mutuwa, yasan duk wanda ya tafi baya taɓa dawowa yasan ya yi rashin uwa har abada…!
Ƙanwar Bilal ta biyu ce Zulaihatu ta shigo tana kuka sai ta kama hannuna.
“Taso muje gida Bilal ya ce na zo da ke”
Bana iya uh bale uh uh tana jan hannuna na bita kamar babba da yaro ina ƙwalla ita kuma tana kuka, har muka isa gidansu. Gidansu Bilal irin babban gidan nan ne mai yalwa amman ba sosai ba, ba kuma irin na masu kuɗi ba na masu rufi asiri dai-dai gwagwado, gidane da ke cike da ƴan mata daga ƙanensa da kuma cousins ɗinsa da ake riƙo gida wasu saboda suna makaranta a sokoto wasu kuma zaman ne kawai, sai kuma Mahaifiyarsa da kishiyar mahaifiyarsa, da ƙanwar babansu wato Gwaggo Rabi.
Sun tausaya min sosai sun nuna kulawarsu a kaina, daga iyayen har ƴan matan da suke gida, a falon kishiyar mamansu aka fara shiga da ni na zauna sai kuma wata cousin ɗinsa ta shigo ta fita da ni zuwa ɗakin Bilal dake can gefen ɗakunan mazan gidan kuma a farkon shigowa gidan.
Kamshin turarene ya fara yi mana murhbun sai kuma lallausan carpet, ya gyara ɗakin kamar na mata komai akan tsari kamar na wani babban mai kuɗi. Wutar daƙin da kunna duk da kasancewar ɗaya da rabi na rana ya yi.
A saman gadonsa ta zaunar da ni har ta juya sai kuma ta juyo ta dawo ta kwantar da ni saman gadon kaina akan matashin kai, sannan ta ce
“Ya Bilal ya ce a kawo ki nan saboda gudun hayaniya”
Ta juya ta fice. Ƙaton hoton Bilal da ya yi da Noor nake kallo, a zahiri hoton na ke kallo amman hankalina yana can gurin Habiba da Inna. Zuwa can na lumshe ido bachin wahala ya yi gaba da ni.
Ko da na farka dishi-dishi na fara gani kamin na ga dai-dai, Bilal ne zaune gurin kaina idonsa na kaina Noor kuma na bayana yana bachi sai faman sauke ajiyar zuciya yake yana wani ɗaukar numfashi, da alama ya yi kukan ne har ya gaji.
Kallo kallo muka riƙa yi ni da Bilal ni na kasa tashi daga kwance da nake, shi kuma ya gagara motsawa har sai da yaga idona ya fara zubar da ƙwalla.
Sai ya yi saurin kai hannunsa for the first time ya riƙa ya tayar da ni zaune, babu wani kuzari a jikina ko ƙire ji na ke kamar ba ni ce ba, fashewa na yi da kuka sai ya yi min masauki a ƙirjinsa ya rungume tsantsan.
“Shiiiiiiiii”
Rarrashina ya ke amman ji nake kamar yana ƙara min ƙarfin kuka, ban lura da shafa baya da yake alamar rarrashi ba sai da kukan ya tsagaita min, sai na yi saurin barin jikinsa na miƙe tsaye, shi ma ya miƙe tsaye yana kallona.
“Ina zaki je?”
Ban iya amsa masa ba na juya ina kuka, sai ya y hanzarin kai hannu ya juyo da ni ya rumgume a karo na biyu, a nan na rushe da kuka muka durƙushe da a ƙasa tare ni ina kuka shi kuma yana hawaye suna sauka saman kaina.
Wata irin natsuwa da kwanciyar hankaline suka ziyarce ni, na ji daɗin rumgumar da ya yi daman i need some shoulder to cry, har ga Allah na san ba dan wani abun Bilal ya rungume ni ba sai dan rarrashi da kuma tausayi, hakan yasa na sake jiki na yi kuka iya yadda zan iya sannan yasa handkerchief ɗinsa ya goge min fuska yana shafa saman kaina kamar wata yarinya.
“Shiiiiiii karki tashi Noor, daker na samu ya yi bachi”
Gunɗe bakina na yi na lumshe ido ina sauraren bugun zuciyata, yanayin Bilal yana min kamar na tsohon mijina wato Margayi Faruk, yau a bayar tafiyarsa wani namiji mai natsuwa da kamala ya rumgume da har na samu natsuwar da na kasa samu a farkon aurena, sai dai wannan ba da ijiya uku ya rumgume ni ba. Tuna wannan yasa na yi hanzarin barin jikinsa, duk yadda ya so ya tsayar da ni sai na ƙi a dole ya biyo bayana yana min magana amman ban kula shi ba har na bar gidan.
3
JUMMA’AT MUBARAK…😘
Ko da na isa gida na tarar ƴan’uwa da masu karɓar gaisuwa suna Sallah la’asar, ashe huɗu ta yi ni ban ma sani ba kasancewar na kwanta ne a lokacin da ba a fara zuwa masallaci ba. Ba zan iya kwatantan yawan mutane da na tarar a gidanmu ba, daga ɗakinmu har ɗakin Inna da tsakar gida cike yake da ɗan adam, hakan ya tabbatar min da an kaita gidanta na gaskiya kenan. Duk yadda na so na danne kukana sai na kasa saboda raunin zuciyata, kuka na ke haƙuri ake ba ni amman kamar wuta da fetur na zama, haƙuri na ƙara min kuka, daker mutaneɓ suka rarrasheni har wasu suka samu damar yi min gaisuwa, da yawa na ji suna faɗar dole zan yi kuka saboda shaƙuwar da ke tsakaninmu da Habiba. 1
Bana iya kwatanta yawan mutane da ke ta zuwa gaisuwa ba, tsakanin ita da Baba bana iya banbance waya fi yawan jama’a, tun daga maza har mata, ta samu addu’ah da yabo sosai, kowa ya ji mutuwar Habiba har ma da waɗanda basu danta ba gani ko kuna jin ta rasu haka kawai babu wani ciwo. Ban tabbatar da na yi rashin ƴar’uwa ba sai da dare ya yi naga inda take kwantawa babu kowa sai matashin kanta, da kuma komatsan kayanta a gefe, ban san lokacin da na fashe da kuka ba sai kuma dariya ta biyo baya, wata ƙanwar Inna ce ta shigo ɗakin ta fita da ni zuwa ɗakin Inna, amman har lokacin ban bar kuka da dariya ba, ni kaina zan iya cewa na kusa na haukace ne a wannan lokacin.
Addu’ah suka riƙa min suna tofa min har sai na dawo ina kukan kawai babu dariya, kuka ne ya saka Inna kuka, ni da ita aka rasa mai rarrashin wani. Ni da Inna ba mu runtsa ba sai dai ƙannenta ne suka samu suka yi bachi, ni kuma na tashi na raya dare ina tayi ma Habiba da Baba addu’ah da kuma Faruk, sai mutuwar ta dawo min ta yi min tsaye, duk mutanen da suka da muhimmanci a rayuwata ina ta rasa su.
Ka rasa mahaifina sai kuma na ƴar’uwata, na rasa RAI BIYU masu muhimmanci a rayuwata, kuma duk a cikin shekara ɗaya.
1
Har aka yi kwana ukun Habiba aka gama bana aikin komai sai kuka, bana iya cin komai sai ruwa, a wannan babin kan na yarda Inna ta fini tawwakkali domin da kanta tana kan zauna na bani haƙuri tana min maganganu masu tausasa zuciya, amman na kasa jurewa wannan ƙaddarar kan na saka ɗaukarta, a kowa ne dare gani nake kamar Habiba zata dawo, bana da mafarki sai nata, da naja numfashi na sauke addu’ah nake mata, ƙiriƙiri bachi ya gagareni duk dare bana iya bachi har garin Allah ya waye, wani lokacin Bilal ya kan shigo har cikin gidan saboda bana fita ya riƙa min nasiha yana jana da hira wai ko zan sake amman ina na kasa kai zuciya nesa, Jidda ma ta yi iya yinta har ta gaji ta sa min ido.
Haka na kwashe sati biyu babu wani canji tsakanin ni da Noor domin shi ma idan yana bachi kiran sunanta yake, idan zai ci abinci sai ya ambaci sunanta saboda mun saba cin abinci tare, da an taɓa shi ya buɗe baki yana kiran Mama Habiba. Ranar da ta cika kwana goma shabiyar a ƙabarinta ina zaune waje ina karatun ƙur’ane Noor ya kwanto jikina yana kuka. 1
“Momy miyasa idan aka mutu ba a dawowa?”
Kallonsa na yi, da farko rasa na yi mi zaɓ ce masa sai kuma na yi ƙarfin halin ba shi amsa.
“Haka Allah yaso, kuma duk wanda ya samu lahira baya ƙaunar dawowa duniyar nan, sai dai mu iskeshi”
“Momy nima ina son na mutu naje inda Mama Habiba, kullum ina mafarkinta bana jindaɗi idan bata nan”
Ya faɗa yana kuka, sai na rufe ƙur’ane na aje gefe na kwantar da kansa saman cinyata ina shafa kansa, shi kuka ni kuka.
Na yi kuka sosai har sai dai na jawa kaina ciwon kan da ban taɓa irinsa ba, domin har cikin ƙashin bayana yaƙe sauko min, a ranar bana iya ko da motsin kirki har sai da aka kira wani nurse ya duba ni ya bani magani. Wasa wasa ciwo ya fara min yawa yau ciwo gobe lafiya tun abun be kama Inna ba har ya soma bata tsoro, sau biyar ana min ƙarin ruwa amman kamar zubarwa ake, duk nabi na rame na lalace farar fatata ta soma ɗuhu, gashi bana iya cin komai.
Haka Inna zata saka ni a gaba tana kuka tana cewa ni ma rasa ni zata yi, damuwar da nake ganin tana ciki ne yasa na ragewa kaina tunani ta yadda zan samu na riƙa cin abinci ko da kaɗan ne, domin nurse ɗin ya faɗa min matuƙar ban daina tunani ba ba zan taɓa jin sauƙi ba, kuma ba zan taɓa iya cin komai ba, idan zan kwanta sai na shimfiɗa zanen da Habiba take shinfiɗawa na yi matashin kai da fillonta hakan yasa sai ma ji kamar tana kusa da ni. 1
STORY CONTINUES BELOW
Da addu’o’i da ƙarfin hali na fara samun sauƙi, cikin sati ɗaya na koma normal sai dai ban iya maida jikina ba, lafiyata ma bata dawo gaba ɗaya ba, amman Alhamdulillah na dawo cikin hayyacina ma miƙa lamarina ga Ubangijina, har na kan fita naje gidansu Jidda saboda rage kewa, Bilal kuma ya yi min sallama na fita mu gaisa na tattara komai na adana a zuciyata, na tabbatar da ace ana buɗe zuciya da tawa zuciyar idan aka buɗe ba za a tarar da komai ba sai damuwa, baƙincikin, tunani, da kuma hudu na rashin RAI BIYU da na yi.
Walwalar da nake tasa Noor ma ya sake har yana sawarsa da yara, sai dai duk da haka idana ka masa wani abu sai ya shigo yana kuka ko ya ce da Mama Habiba na nan da yanzu ta rama masa, Sakina ce ta ɗauke halin Habiba a gidanmu duk wani aiki da Habiba take Sakina ce take yinsa a yanzu, Noor ma idan aka masa wani abun itace kan gaba wajen magana, sosai take ɗauke min kewar Habiba daman suna kama sosai da Habiba ta fuska da kuma ta magana, inda suke da banbanci Habiba tana da tsawo ya yinda Sakina take gajeruwa sai dai ba can sosai ba.
A kwana a tashi hasarar mai rai! Wasa-wasa kwanaki suka soma ja, har Habiba ta haura wata ɗaya da rasuwa, a zuwa yanzu kan mun fara sabawa da rashinta, sai dai duk da hakan kewarta bata bari na bachi har sai na kwantar akan shinfiɗarta. Ranar da Inna ta fita wanka, wato ta gama taƙaba sai mutuwar Habiba da ta Baba ta dawo mana sabuwa. Mutane da dama kama daga ƴan’uwa, maƙota abokan arziki suyi ta shigowa suna mana barka da fita wanka da Inna ta yi lafiya. Sai dai babu Family Bilal ko ɗaya da ya zo mana barka da fita wanka, hakan be bani mamaki ba daman can na san ƴan gidansu ba son alaƙar dake tsakanin mu suke ba.
Bilal kan sai dare ya zo, ya kawo ma Inna atamfa vilisco ta dubu biyar da kuma wax ita ta dubu biyar da Hijab mai kyau yadi huɗu, sai turaruka da man shafawa da kuma kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe, abunda yan uwan Babanmu suka kasa yi, ko atamfar roba ka rasa wanda zai siyo ya kawo ma Inna da suna ta saka na fitar wanka saboda rashin haɗin kai da kuma halin ko’in kula nasu.
Duk yadda Inna ta so ta rage kaya sai Bilal yaƙi yarda wai idan har ta mayar masa hakan na nufin bata ɗauke shi ɗa ba. A bakin ƙofar gida muka tsaya muna fira da shi, a nan yake min zancen aikina wanda ni har na watsar da lamarin.
“Ya kamata ki koma kin ga idan kina fita zaki fi sakewa, kuma ita kanta Inna zata ji daɗi”
“Amman Bilal ni aikin ya fita daga raina ma”
“Aiko yanzu ne ya kamata aiki ya shiga kanki domin Sakina da Jamila da Noor suna da buƙatar taimakonki, ga kuma Inna”
Gaskiya ya faɗa tun da bamu da wasu ƴan’uwa masu son taimako dole ne mu tashi mu nemi namu, daman hausawa na cewa ‘indan ma ɗan’uwa nemi naka’
Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi duk da kasancewar ba zan iya ganinsa ba saboda babu hasken farin wata, ita kan wutar nepa na manta rabon dana ganta a gidanmu domin an daɗe da yanketa, sai dai idan maƙota sun kunna wuta hasken gulob ɗinsu na haska gidanmu musamman masu gidan samman nan dake kusa da mu, sai dai yau basu kunna ba sakamakon babu wutar gaba ɗaya a unguwa.
“Amman basu kore ni ba? Na daɗe ban zo ba”
“Na basu rahoton cewar baki da lafiya, dan haka idan kin shirya zuwa kije kawai”
“I will try”
Na faɗa ina tsotsa lips ɗina. Bayan zancen aiki sai kuma muka ɗora da wani zancen na daban, ba laifi na saki jiki mun yi fira har da dariyata kamar ba ni ba, da wannan na yarda cewar zuciyata ta fara zaurancin son Bilal domin ina jin nishaɗi a duk lokacin da muke tare da juna, ko sunansa na tuna sai na samu kaina cikin hauƙi da murmushi.
Bayan kwana biyu da faruwar hakan na shawarci Inna akan maganar aikina, na yi zaton zata hanani ne ko tace wani abu sai naga ta nuna farinciki sosai har tana ce min wai na fara dawowa a mutun ɗinta, farincikin dana gani a tattare da ita ne ya ƙarfafa min guiwa na yi jimmar wanke uniform ɗina na zuwa aiki.
STORY CONTINUES BELOW
Washe gari na shirya tsaf na ɗauki Hijabina na saka, sai kuma na buɗe jakar da nake aje tarkace na na ɗauko ƙaramin hoton Habiba na saka a aljihu, hakan zai kwantar min da hankali kuma zai ƙarfafamin guiwa domin a duk lokacin da nake kusa da wani abu da ya danganceta ina jin kamar ƴar’uwata tana kusa da ni.
Sai da na yi ma Inna sallama sannan na fita bayan na yi addu’ar fita daga gida. Bana baƙinciki ba farinciki na isa gurin aikin, kamar yadda nake a baya, sai da na fara zuwa na rubuta sunana da lokaci na aje hijabina da wayata a inda aka tanada domin aje irin waɗandanan abubuwan sannan na domin sai sannan na nufi gurin aikina, ina cikin aiki na ji muryar wani namijin yana faɗin
“Khadija Musa Kafinta you’re fired”
Da sauri na juyo na kalli mai maganar yana sanye da black suit hannunsa riƙe da file.
“Saboda me?”
Na tambaya cike da mamaki.
“Saboda rashin zuwa da kika yi, shugaba baya son haka, kuma ya ce be yarda da rahoton da aka bada cewar baki da lafiya ba”
A take raina ya ɓace sosai, taya zai ce be yarda ba shi beda uzurine hala! Sai da na fara aiki za a ce an koreni, ni ko ba zan yafe haƙƙina na kwana biyu da na yi ina aiki ba.
“Na ji an koreni amman a bani kuɗina na aikin da na yi na kwana biyu da rabi”
“Kwana biyu da rabi?” 1
Ya maimaita fuskarsa a haɗe.
“Ee ai na yi aiki sau biyu a wannan kamfanin kuma yanzu na yi rabin aikin, dan haka a biyani haƙƙina”
Ta yadda na yi masa maganar ya fahimci ina cikin zafin raine, domin a hasale nake ina katsa masa tsawa, yasan duk ya yi wasan sake ce min wani abu zan haukace masa ne.
“Kije hawa na biyar bi faɗawa mai kamfanin, ba ni zaki faɗawa ba”
Ya faɗa yana juya ya fice, ni kuma na bishi da bala’i ina cewa. 1
“Ai kai ya aiko dan haka kai zan aika”
Can kuma na soma tambayar kaina, wai shi wannan mai kamfanin wane irin mutun ne, miya ɗauki mutane ne? Aiko Wallahi ba zan iya yafe masa haƙkina ba ko da be bani kuɗin ba sai na faɗa masa marar daɗi sannan na bar kamfanin.
Haka na kuɗiri aniyar sai na nuna masa ahi ba kowa ba ne, kai ina ma son ganin shi wane irin hallita ne da yake wulaƙanta ɗan adam, wato shi wannan yana tunanin kamar ba zan iya ba shiyasa na ce naje ko?
“Aiko zan baka mamaki”
Na faɗa a fili, sai na saka ƙafa na yi shuri da bokitin da nake mopping ɗin ruwan suka watse a ƙasa na fice a fusace. Kai tsaye na nufi gurin da lifted take na danna ta buɗe sai na shiga na danna 5. Gadan-gadan na fita daga lifted babu tsoro ko kaɗan a tare da ni, wannan gurin ma kamar wacan yake sai dai wannan ko wane office a kulle yake, an yi rubutu an laƙa a saman ƙofar. Ɗaya bayan ɗaya na riƙa bin ɗakunan ina duba wai ko zan ga wanda aka yi wata alama ta mai kamfani amman ban samu ba. Har na juyo sai ga wani mutume ya fito daga wani ɗaki riƙe da files, tsaidashi na yi ina tambayar office ɗin mai Kamfanin.
“Lafiya kike nemansa?”
“Shi ya aika ya ce yana nemana”
Wani kallo ya yi min daga sama zuwa ƙasa sannan na kalli sunana dake rataye a wuyana.
“Sai kin hau Excavator can, zaki ga Office guda uku jera, a na tsakiyar zaki tsaya akwai wani maɓalli a gurin sai ki danna”
Sai da ya gama min kwatancen sannan na lura Excavator ɗin dake can gefen dama da offices ɗin.
STORY CONTINUES BELOW
“Na gode”
Na faɗa inanufar gurin, shi kuma ta bi bayana da kallo. Ni ban kula shi ba na hau Excavator ɗin. Ina kawowa sai na hauye saman tile ɗin na ƙarasa gaban offices dake jera, a na tsakiyar na tsaya, dama na ni na hango maɓallin da yake magana a kai na kai hannu na danna.
Wata ƴar tsuwa na ji sai wata fitila ta hasko saman kaina.
“What do you want?”
Muryar namiji ce mai tambayar, kaina na ɗaga saman ina kallon camera dake ɗaukata.
“Ina son ganin oganku ne”
“Ur Name?”
“Nawwara”
Bayan na bashi amsa da kamar minti biyu sai ya ce.
“You don’t have an appointment with him”
“Amman shi ya ce yana son gani na”
Na faɗa a tsawa ce ina kallon camera kamar ance mutumem ne a gabana.
“Sorry Ma’am you’re not in the list”
“But he’s the one who tell me to come and meet him here”
Na faɗa cikin turancina na yan ƙaramar makaranta. Sai kawai ƙofar ta rabu biyu ta buɗe min, da ɗan tsoro na kutsa kai ciki sai na gano ashe cikin wani ɗan kumbo ne na ke ciki, sai da kumbon ya gama scanning ɗina sai muryar ta sake min magana.
“Keep your passport inside the box”
Muryar ɗazu dai ce ta yi min magana, sai na saka hannu na ciro hoton Habiba na saka cikin wani ɗan ƙaramin akwati dake gefena, sannan ƙofar ta buɗe min tana min WELCOME.
Wani ɗan madaidaicin Office ne na samu kaina ciki shi ba babba ba kuma ba ƙarami ba, an ƙawatashi da kayan alatu, da gangan na hana idona kallon wasu abubuwa na office ɗin saboda karna manta abunda ya kawo ni.
Matashin Saurayi ne zaune saman kujerar dake office ɗin, laptop biyu a gabansa a daga gefensa kuma desktop computer ce a aje, can nesa da shi kuma an jera wasu desktop computer har biyu da kujerarsu daban. Can a farko shigowa office ɗin an jera kujeru masu kyau na san ba zasu wuce na zaman baƙi ba. Matsawa na yi kusa da shi da jimma na fara masa masifa domin a haukana na ɗauka shi ne mai kamfanin, sai ya rigani magana.
“Stay where are you, i have to call him first”
Telephone ɗin dake kusa da shi ya ɗauka ya fara danna wasu numbobi, hakan yasa na yi janzarin ƙarasawa kusa sa shi sosai.
“Sir a young lady… ”
Yana fara magana na fisge telphone ɗin na fara tawa maganar domin nasan idan har ya faɗa masa zai ce shi be san da zuwana ba, ba zasu bani damar magana da shi ba.
“Azzalumi macuci, ka koreni ai sai ka bani kuɗin aikin da na yi na kwana biyu da rabi kuma kaima baka wuce Allah ya ɗora maka ciwon ba-”
“Nawwara…-” 1
Ɗaga can cikin wayar ya ambaci sunana. Tun da muryarsa take daki kunnena yawun bakina suka tsinke, kaina ya fara jiri wani abu na ji na tsikareni tun daga saman kaina har cikin ɗan yatsan ƙafata, gaba ɗaya jikina sai ya mutu. Mutunen nata ƙoƙarin fisge telphone ɗin daga hannuna sai na saka masar na juya da gudu na nufi inda na ke hango wata ƙofa dake can dama da teburin mutumen amman nesa da shi. 1
Da gudu na banki ƙofar na shiga, sai na samu kaina cikin wani irin ƙaton office mai cike da sanyin ac. Yana hakimce saman kujerar alfarma wani irin ƙaton tebur mai takardu da kayan kawata teburin office haɗi da system na gabansa.
Ji na yi kamar ana zooming ɗina a take hawaye suka fara bin fuskata, na san idona ba gizo suke min ba, ba mafarki na ke ba. 1
Daga saman kujerar da yake zaune ya ɗagawa secretary sa dake ta kokuwar fitar da ni hannu, ya yi masa alama da ya fita sai ya juya ya fice yana ja ƙofar office ɗin. Shi kuma ya taso da sauri ya doso inda na ke yana kira sunana muryarsa har rawa take.
“Naaa…Naww…Nawwarraa….”
Tafin hannuna na kama taɓa sai ya yi saurin kai shi gefen fuskarsa ya lumshe ido, sai hawaye suka zubo masa.
Fisge hannuna na yi ina yin baya-baya, Tabbas shine, shine mutumen da ya yi nasarar canja ni daga mutum zuwa mutum mutume, shine mutumen da ya ce yafi ƙaunar ganin mutuwarsa sama da ni, shine mutumen da ya kirani ƴar talakawa marar daraja, shine mutumen da daya wulakanta ni ya sani a rana kuma yasa duniya ta zargeni, shine muteme da ya yanke min duk wani jindaɗi ma rayuwar duniya, shine mutumem da ya fara saka ni a ɗakin kuka da baƙinciki. 1
Kai na nake girgizawa ina cigaba da yin baya-baya shi kuma yana matsowa kusa da ni, duk ya rikice kamar zai cinye ni, idonsa har sun soma canja kala, jikinsa na ta rawa hawaye kuma na ta aikinsu a fuskarsa.
Muna haka Mutumen da ya taɓa tambayar sunana a wacan lokacin da na ke aiki ya shigo, shi ya kai hannu ya dafe masa ƙirji saboda kar ya ƙaraso kusa da ni, ni kuma na juya da gudu na fice ina kuka, ina jiyo sautin muryarsa yana kiran.
Da kuka na sauko ƙasa na ban tsaya saka sunana ba na nufi gurin da Hijabi ya ke tare da wayata na ɗauka na saka na fice ɗaya ɗaga cikin mutanen da suke reception na ta kirana wai na zo ga saƙo amman nayi banza da shi ina ta aikin gudu da kuka.
Sai da na yi nisa da kamfanin sannan na fara tafiya ina hawaye, tare da tambayar kaina wasu tambayoyin da ba ni da amsar su.
‘Shi da yake likita miya kawo shi nan? Daman ƙamfanin na su ne? Daman shi ne mutumem da Bilal yake faɗa min, miyasa ban gane shi ba a lokacin da Bilal ya faɗa min suna da Asibiti? Na taɓa jin ƙamshin turarensa miyasa ban ga ne shi ba? Ya faɗa min yana da tattoo miyasa ban ga ne shi ba?’
“Lallai ke wawuyace Nawwara” 1
Na furta a fili hawaye na min zuba, yau kan ƙasa na kama hanyar gida duk kasancewar akwai tazara mai tsawo tsakanin unguwarmu da kuma inda kamfanin ya ke, amman baƙincikin da ke raina ba zai bari na iya tsayawa na tari abun hawa ba.
Ƙarar tsayawar motarsa ce ta riƙa ta dawo min kamar a yanzu ne abun ya ke faruwa, irin yadda ya fisgoni ya jefar gefen titi ne ya riƙa min yawo a ƙwaƙwalwa.
Wani irin jiri ne na ji na ɗibeni sai na ji ƙafafuna kamar an cankesu an ja ni, duhu na soma gani, ko kamin na kai ƙasa numfashina ya daɗe da barin jikina.Sanyi da yaji a tafin hannunta ya tabbatar masa da ita ɗin ce, hawaye ke zuba a idosa ba tare da ya san suna zuba ba, baya-baya take tana hawayen da yake jin ɗigarsu har cikin ransa, a hankali ya ke maye duk wani footsteps nata da take backwards, ga wani irin abu da ke jansa na ɗimaucewa da al’ajab ɗin ganinta kamar zai fita hayyacinsa he just can’t believe Nawwara ce yau a gabansa.
Shigowar Siraj ya bata damar fita da gudu, shi kuma ya yi hanzarin binta sai Siraj dakatar da shi, ta hanyar ɗora hannunsa saman ƙirjin Jibril. +
“Calm down Jibril”
Be saurari abunda ya ke faɗa ba ya ƙwala ma Nawwara kira da dukannin muryarsa yana mai jin kamar ya yi tsalle ɗaya na fisgota. Ya sauke idonsa da suka yi ja suka rine akan Siraj yana ambatar sunan Nawwara cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai.
“Nawwara ce fa”
“I know”
Siraj ya amsa masa yana ta matsar da shi baya har ya zaunar da shi saman tebur burinsa.
“Nasan zaka haɗu da ita tun ranar da na yi arba da ita tana aiki a kamfanin nan, ni ma dan bata san ni bane yasa ta zauna da ace ta san kamfaninka ne ba zata yi aiki a nan ba”
Cewar Siraj Hannayensa akan kafaɗar Jibril, sai ya ture masa hannaye yana masa kallon mamakin furucin da ya taɓa masa a can baya.
“Miyasa ka ce min ta mutu? Kasan iya shekarun da na ɗauka ina nemanta? Saboda ita na aminta na yi aiki nan saboda kawai ta taɓa rayuwa a nan garin, Siraj kasan yadda take da muhimmanci a gurina kuwa?”
“Na sani wannan dalili ne yasa na ce maka ta mutu, saboda ka yi focusing akan abubuwan da ke gabanka, na yi nemanta har na gaji ban samu ba, amman tun daga lokacin da na ganta a kamfanin tana aiki nasan wata rana zaku haɗu”
“So kasan tana aiki a nan kuma ka ƙyale baka faɗa min ba? Ban taɓa sanin kai maƙiyina ba ne Siraj sai yau”
“Na ganta sau ɗaya lokacin da muke duba ɗakunanan ni da Zinatu”
Miƙewa Jibril ya yi cike da ɓacin rai, ya nufi ƙofar zimmar fita, sai Siraj ya bishi da kallo yana faɗin
“Ina keka tunanin tafiya? Gurinta? Ai ba zata taɓa saurarenka ba ko ka manta irin wulaƙacin da ka yi mata?”
Tsayawa ya yi cak hawaye na ta cigaba da masa zuba kamar ba shi ba, abun ka da farin mutun har fatar idonsa ta yi ja. Tabbas ba zata saurareshi ba ba ma cancanci Nawwara ta kalleshi ba balle har ta saurare abunda zai fito daga bakinsa.
‘What can i do now? Oh God…’
Ya juyo cikin rashin kuzari ya zauna saman kujerasa ya dafe kansa yana lilo da kujerar.
“Take this”
Siraj ne ya yi maganar yana aje masa farar takarda mai ɗauke da Cocaine saman tebur. Jin ƙamshinta yasa ya buɗe ido ya kuma sauke idanuwansa akan cocaine ɗin, hannu ya kai ya yagi gefen takardar ya fara mata aiki kamar ba gobe, sosai ya shaƙeta ko da ya ɗago ƙasa da kuma gurin tsinin hancinsa ya yi ja sosai.
Yana san cocaine ne kawai saboda ta zame masa jiki ba wai dan tana masa aiki ba, tun lokacin da tunani Nawwara ya sashi gaba ya addabe shi yasa ya fara shanta, saboda ta ɓatar masa da hankali, da wasa-wasa ta kamashi har ta zame masa jiki ta yadda idan ransa ya ɓace sai ya shata yake jin sawaba, izuwa yanzu kan ta daina masa aiki ajiki saboda sabon da ya yi da ita, ko ya sha baya jin komai sai dai kawai ya sha dan ta zame masa kamar a abincin.
Miƙewa ya yi tsaye yana tsotsar pink lips ɗinsa sai wani numfashi yake kamar zakin da ya yi faɗa ya gaji, hannu ya ɗaga ya daki teburin da ke gabansa iya ƙarfinsa.
STORY CONTINUES BELOW
“Ya za’ayi na sake ganinta Siraj?”
Siraj ya ɗauke ragowar cocaine ɗin ya mayar a wani ɗan ƙaramin box yana faɗin.
“Malam ka fa koreta daga aikin ko ka manta?”
Wani dogon tsaki yaja ya fice daga office ɗin yana ciro wayarsa dake cikin aljihu, wata number ya nemo bugu ɗaya aka ɗaga.
“A fito min da mota waje”
Yana fitowa sekaterinsa ya miƙe tsaye yana faɗin.
“Sir akwai meeting tsakaninka da Managen Daherr Global Prints yanzu”
Juyowa Jibril ya yi a fusace zai jefa masa baƙar magana sai Siraj da ya fito daga office ɗin Jibril yanzu ya yi aurin karɓa masa.
“I will attend the meeting”
A fusace Jibril ya juya ya fuskanci ƙofar sai ta buɗe masa da kanta. Da ya fito be iya tsayawa Excavator ya sauko da shi ƙasa ba ya riƙa tattakowa ya sauko da sauri, kai tsaye ya fita daga harabar gurin, kamar zai tashi sama haka ya nufi lifted, Already sun saba indai zai shiga babu mai matsowa kusa da gurin har sai ya shiga ya sauka.
Kamin lifted ta dawo dashi hawa na ɗaya har ya matso sosai, sai gumi yake kamar wanda yake kusa da wuta, lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya, babu komai a cikin zuciyarsa da ƙwaƙwalsa sai Nawwara. Ina zan ganta ta ina zai fara nemanta shine abunda yake ta tunani har ya isa gurin motarsa da aka fito masa da ita aka kawo masa har gaban kamfanin, duk gaisuwar da ma’aikatan gurin suke masa be ji ko ɗaya ba saboda hankalinsa kwatakwata baya jikinsa, su kan basu kula ba tun da sunsan halinsa ayi masa magana ya ƙi amsa tun da ya maida kowa maƙasƙanci saboda kawai suna aiki a ƙarƙashinsa, idan har ka gaisheshi ya amsa maka lallai kuwa ka isa irin sosai ɗin nan a gurinsa.
Direban na tsinkayarsa ya yi saurin fitowa ya buɗe masa mazaunin baya, a tunaninsa zasu fita tare ne sai yaga ya ɗaga masa hannu ya nufi driver seat. Da sauri ya rufe masa motar ya matsa can baya yana kallon yadda ya fisgi motar kamar zai tashi sama, abun har tsoro ya bashi.
Tun kamin ya ƙaraso security guard suka buɗe masa gate, domin sun san halinsa ba tun yau ba, shi baya jira a buɗe masa gate sai dai gate ya jirasa. @360 yake gudu kamar ba a cikin gari yake ba. Minti ɗaya zuwa biyu yake furta sunanta zuciyarsa na wani irin bugawa kamar zata filo.
“Nawwara Where are you?”
Titi yake bi zuciyarsa nata raya masa zai ganta, bayan kuma be san inda ta bi ba, haka ya yi yawonsa na neman Nawwara amman har aka kira sallah azahar be haɗu da ko da sawonta ba balle ita.
“I’m very stupid human being, taya za ayi ta bi titi? Tana gidansu by this time”
Ba bawa kansa da kansa amsa, sannan ya bugi sitarin motar iya ƙarfinsa, sannan ya juya akalar motarsa zuwa sama road. Tuna hannunta da ya riƙa yasa jin relief har miskilin murmushi ya bayyana a fuskarsa murmushi da ya kasa gushewa har ya isa ƙerarren gidansa end of discussion da ke sama road.
Yau kan be yi parking a inda ya saba ba sai ya fito cikin wani irin yanayi shi ba farinciki ba kuma ba akasinsa ba ya nufi ƙofar Babban falonsa, yana shiga idonsa suka sauƙa kan ƙaton hoton Nawwara dake tsaye a falon yana fuskartar ƙofa, matsawa ya yi kusa da hoton ya kai hannu yana shafa fuskarta kamar ance masa ita a gabansa tsaye.
“I love you Nawwara i love you so much”
Hawaye ne suka zubo masa, sai ya nufi bedroom ɗinsa yana buɗe maɓallan rigarsa, saman bed ɗinsa ya zauna ya buɗe bedside drawer ya ɗauko wani madaidaicin diary mai zaganen zuciya ya yi masa kiss sannan ya bude shi. Pages da yawa ya wuce a cikin diary sannan ya bude new page da ba ayi ma rubutun komai ba ya ɗauki biro ya zana zuciya a saman zuciyar ya rubutu. _Finally i meet her today she’s still alive _ a kasan zuciyar kuma sai ya rubuta _Naj_ ya zagaye shi da biron ya yi ma yatsunsa biyu kiss ya liƙa hawayensa sannan na manna a jikin sunan da ke ƙasan heart ɗin, a take gurin ya jiƙe. Rumgume diary ya yi ya kwanata rai-rai yana bin ɗakin nasa da kallo kamar wani baƙon. Daga bangon gaban na ɗakin zuwa yamma babu komai sai hotunan Nawwara, dagana kudu zuwa arewa babu komai sai horunan Nawwara.
“After the game, the king and the pawn go into the same box, every step I took since the moment I could walk was a step towards finding you, and i find you Naj ba zan iya rasa ki ba i can’t lose you again”
Ya tashi zaune ya fiddo wayarsa daga aljihu ya kira waya number.
“A cikin waɗanda aka kora akwai wata Nawwara wacce ta zo yau, ka aika mata da saƙon neman ta dawo aiki yau, kuma ka duba addreshinta ka aiko min da shi right now”
Yana faɗar haka ya kashe wayar, yana wani irin nishi shi ba na wahala ba, ba kuma na fushi ba, ba na jindaɗi ba, kansa ya shafa yana faɗin.
“Ina son ki Nawwara, ina son ki har cikin zuciyata, idan na rufe idona ke nake gani, idan kuma na buɗe ke nake da buƙatar gani kece ruhina Nawwara ina son ki matuƙa”
Magana yake da kansa yana kallon hoton, zuwa can idanuwansa suka sauka kan gmt ɗin dake ɗakin sai ya yi hanzarin tashi ganin uku saura kwata be yi sallah azahar ba.
NAWWARA POV.
Ƙoƙarin buɗe ido nake sai na ji sun min nayi sosai, bana iya tuna abunda ya faru da ni balle har na gane inda nake har sai da nayi ƙarfin halin buɗe idona dake ciki da danshi domin bana iya gani da su sosai.
“Sannu”
Bana iya tantance mai muryar amman tabbas na taɓa jin wannan muryar ko a ina ne, da sannu idanuwana suka buɗe wasai har na iya tantance a asibiti na ke, yanzu kan na tuna abunda ya faru amman waya kawo ni asibiti? Kamar ance na kalli gefena sai idanuwana suka sauka kan Mustapha idonsa narai-narai kan nawa. Unƙurin tashi na yi amman babu wani kuzarin kirki a jikina.
“San..nu..”
Ya faɗa murya na rawa, kansa ƙasa-ƙasa kamar mai saunata. lallai ma wannan mutumem ya raina min da hankali miya kawo shi a inda na ke ma? Tambayar da na kasa amsawa kaina kenan, cikin ƙarfin hali na ɓalle drip ɗin da aka saka min a hannu, na sauke ƙafafuna ƙasa, hannun da na ɓalle cannula yana ta jini na ɗauki Hijabina da ke saman durowa na saka.
“Nawwara….”
Ya faɗa yana miƙewa tsaye idonsa a razane kan hannuna dake ta zubar da jini. Da hannun na nunasa ina masa wani mugun kallo.
“Kar sunana ya sake ziyartar laɓɓanka, kar kuma ka sake ƙoƙarin furta wata kalmar a gareni, ban taɓa tunanin kai hasararren ɗa bane sai yau, zakka marar tarbiya, Zahili dan gantali haihuwar hasara”
Tun da na fara wannan maganar kansa na ƙasa ya rumtse ido yana ta saurarena, mi kuma tuni na fara takawa zuwa gurin ƙofa to my surprise sai ga Jidda ta shigo rike da kaya niƙi-niƙi a hannunta.
“Har kin farka?”
Da ni take magana amman idonta yana kan Mustapha da kamar akwai wani abu a ƙasa. Ƙarasa ta yi ta aje kayan da ke hannunta ta zo ta dafani, sai na kaɓe mata hannu idanuwa cike da ƙwalla zuciyata kuma har wani fisga take kamar zata fito.
“Me kuke yi a nan”
“Suma kika yi a hanya, sai Mustapha ya ganki ana neman inda za a kaiki shine ya kwaso ki ya kawo asibiti”
Kai tsaye ta bani amsar, Mustapha kan tuni ya yi mutuwar tsaye saboda kalaman da na masa.
“Ya akayi kika sani?”
Na tambaya yayinda da hawaye suka sauko daga idona suka wanke min fuska. Sai da ta kalli Mustapha sannan ta kalleni ta ce
“Mustapha ne ya faɗa min”
Dauƙe kai na yi na cigaba da tafiyata na ƙi kula kiran da take min har na fice daga ɗakin.
‘Taya Mustapha yasan alaƙar da ake tsakanina da Jidda? Miyasa be kira wani daga cikin gidanmu ba kira Jidda?’
Shine abunda na ke ta saƙawa a raina ina tafiya, Jidda na bina da kira.
‘Amman kuma ai bata san illar da Mustapha ya yi mana ba, bata san aibunsa a garemu ba’
Tuna wannan yasa na tsaya har na saka Hijabina na danne Hannuna ina jiran ta ƙaraso.