ALKAWARIN JINI CHAPTER 3 BY _HAWWA MUH’D USMAN

ALKAWARIN JINI CHAPTER 3 BY _HAWWA MUH’D USMAN

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da sauri ya d’ago kansa dake sunkuye a k’asa ya kalli baffa yana masa murmushi,kafin ya d’an girgiza kai kad’an yana cewa

   “Lafiya k’alau baffa..Buh kawai dai naga lokaci yana sake k’urewa ne,shi ne nace bari nayi saurin wucewa kada yamma ta sake yi min..!”+

     “Toh to..! Ehh! Kayi gaskiya kam,gara mu hanzarta kada almuru ya riske ka baka tafi ba..”

   Sake kallon baffa yayi da sauri,kamar zai ce wani abun,dan shi gaba d’aya har ga Allah a cikin zuciyarsa bawai rakiyar tasu yafi damuwa da shi ba,buh haka nan kuma sai yaji bazai iya fitowa fili ya fad’awa baffan abunda ke mak’ale a k’asan zuciyar tasa ba,sannan kuma ganin da yayima babu lallai ace ya samu abunda yake muradin nan take ya daure yana cewa da baffan

   “Ahh! Baffa ina tunanin da kunyi zamanku ma,yanzun yamma yayi sosai,ba sai kunyi wahalar rakani ba..”

   Murmushi baffa yayi yana girgiza masa kai kafin ya amsa maganar tasa

   “A’a baza muyi haka ba,,abu da ba yau aka fara ba,bare kace ka yafe..Abu ne daya zama jiki a gurin mu,tafiya a gurinmu bama ganinta a matsayin abu mai wahala,,dan haka muje kawai kada wannan ya dame ka..Kamar yanzun ne zamu je mu dawo..”

   Wucewa yayi gaba sai dai har lokacin deeply yana jin babu dad’i aransa da rashin ganinta da bai yi ba,buh ya san tunda aka kawo yanzun zai yi wahala su had’un kafin ya wuce,,yana tafiya yana sak’e-sak’e a ransa har ya kai zauren gidan inda ya d’an sake tsayawa yana jiran fitowar sa,,,baffa kuwa a nan inda ya barshi tsaye a tsakar gida sai ya juya ga yaran dake zazzaune suna aikin b’are masara daga cikin ganyenta suna fiddata waje

   “Kai Hamudan..! Maza kai da Sule ku zo ku d’auki wannan kayan muje ko..!?”

  Baffan ya kwallawa yaran biyu kira,,cikin sauri duka suka bar aikin da suke yi sannan suka fara kiciniyar d’aukan sacks da aka masa packaging tsaraban da zai tafi da su,sannan kuma a tare dukan su suka yi hanyar fita a gidan while suna tsokanar sauran da baffa bai ambata ba,,har baffa ya waiwaya zai fita kamar wanda yayi mantuwa ya dawo da sauri yana fad’in

   “Mairo..!! Ina uwata ne..? Yau duka banji d’uriyarta ba tun safe..Anya ma kuwa sun gaisa da MUHAMMADU..!?”

  

   Duk abunda ake yi a gidan tun zuwansa da hirarrakin su babu wanda kunnuwanta basu saurara ba,buh ta b’oye kanta a d’aki a dalilin jiyowa da tayi ana cewa zai yi tafiya,,wanda itan kanta duk da bawai suna wani shahararren shiri da juna ba ko dogon hira idan yazo gidan sai duk take jin kamar tace masa kada yayi tafiyan,,tun fitowarsa tare da baffa da duk sallamar da suke yi da y’an gidan tana tsaye jikin labule tana lek’e har zuwa lokacin daya fita,ko da jin bai tambaya tana ina ba a hankalk wasu irin tears masu d’umin gaske suka fara gangarowa daga idanunta,komawa tayi saman gado ta kwanta tana ci gaba da kuka k’asa².

  Lokacin ko da baffa yake tambayar Innarta tana ina,take tayi saurin mik’ewa tana wiping tears d’inta kana tayi wuf ta fice daga d’akin cikin matsanancin jin dad’i,zuwa lokacin kuwa dama duk ta k’agu,jira kawai take taji anyi magannarta.

   Ko kafin Innar ta bawa baffa amsar tambayar da yayi mata tuni hat ta fito daga d’akin kamar wacce aka cillo waje,kallonta Inna tayi da mamaki shimfid’e a fuskarta,sai dai bata iya cewa da ita komai ba ta juya tana girgiza kai dan ita dai AL’AMARIN Sabinar a y’an kwanakin yana matuk’ar d’aure mata kai,,inda baffa yake tsaye ta nufa cikin rashin kuzari while kanta a k’asa tak’i bari su had’a ido da kowa dan gudun kada a gano damuwarta,tun bata k’araso ba baffa ya kalleta yana cewa

  “Uwata yau kuma zaman d’aki kike sha’awar yi ne..Duka ban saki a idanuna ba..!?”

  D’an kad’an tayi murmushi wanda yake daf sawa ta saki sabon kuka nd cikin muryanta mai tattare da sanyi ta ce

   “Laaa! Baffa bayan mun gaisa da kai d’azun dana dawo daga makaranta,,kuma fa har tambayar kama nayi nace zani gidan yagwalgwal anjima..”

   “K’warai..! Anyi haka..Na manta ne SHALELE shi yasa na tambaya..! Amma duk ba wannan ba,shin kinje kuwa kun gaisa da MUHAMMAD..!?”

   Duk da tasan da zuwansa gidan ambaton sunansa da baffa yayi sai da yasa taji zujiyarta tayi wani irin mugun tsinkewa,cike da dauriya mai tattare da rainin wayo,nd tana yi tamkar bata san yazo gidan ba duk da karad’in da y’ay’an gidan suka yi tayi daya zo d’in kasancewar irin sabon da suka yi da shi sai cewa tayi da baffan

  “Ehmm! Baffa yaushe ya zo..!? Ai ni banma sani ba,,buh ina jin ko lokacin da yazo ina bacci..!”

  

   Yana daga tsaye a zauren gidan nasu kunnuwansa suka jiyo muryanta lokacin suna magana da baffan akansa,buh abun daya bashi matuk’ar mamaki shi ne yadda duk ihun da yaran suka yi wai tace bata sani ba,,nan take yanayin maganarta sai ya sake d’aure masa kai,a zuciyarsa yake k’iyastawa dan yadda muryanta yake fita sam babu wani alamun dake nuna yayi kama dana mutimin daya tashi a bacci,muryan baffa ya sake jiyowa yana cewa da ita

  “To uwata kuma banda abunki ai yanzun sai kiyi sauri ki riske shi ko ku gaisa,,lokaci yana sake wucewa,bayan kinji na shaida miki yana da tafiya a gabansa..!”

   Kamar wacce bata son zuwan ta amsawa baffa a kasalance da “Toh” sannan taja k’afafunta tana nufar hanyar soron gidan,tafiya take da kyar yayin da zuciyarta duka ta shiga cikin wani irin yanayin alhini na rashin son tafiyar tasa.Tun data nufo soron yayi hanzarin sauya yanayin fuskarsa zuwa wani irin mood mai wuyar fassara,ko data k’araso kanta yana sunkuye a k’asa nd bakinta d’auke da sallama har ta riske shi,,,kamar wanda baya son yin magana ya d’ago kansa dake k’asa ya zuba mata su had’e da amsawa,,shiru Sabina ta d’anyi tana tunanin abunda ya kamata tace masa bayan sallamar,amma sai taji duk ta zama wata speechless,,duk motsin da take akan idanunsa ko da yaga tana k’ok’arin d’agowa cikin sauri ya janye idanunsa akanta,itanma sai data kalleshi sannan ta iya furta

      “Ina wuni..!?”

   Sai daya sake d’agowa ya kalleta while deeply yana fad’in

   “Lallai yarinyar nan akwaita da iya rainin hankali..”

  Buh a zahiri sai yaja wani mugun space kafin ya iya amsa mata

      “Lafiya..! Ya kike..!?”

  Dogon ajiyar zuciya ta sauke nd tana kwantar da kai sannan ta iya amsawa

   “Lafiya k’alau..”

  Shiru duka suka sake d’auka a soron babu wanda ya sake magana,ga Sabina kuwa a lokacin tambayar kanta ta shiga yi a zuci,fad’i take

   “Ohh! Ya rabb..help me..me zance masa ne…!? Aarrghh! Ya Allah.. Me ya kamata na aikata..!?”

  “U must to tell him all what u want..Or else..!?”

   A hankali ta maida idanunta ta runtse while zuciyarta na harbawa da sauri² sannan tayi jarumtar tambayarsa da cewa

  “Ashe tafiya za kayi..!? Allah ya tsare hanya ya saukeka lafiya,,nd a gaida kowa da kowa..!”

   Still idanunsa na akanta ya tsinto maganar nata har ya wuce shi,d’an siririn murmushi yayi duk da bata gani ba yana fad’in

  “Ehh! Hakane..Ameen thumma ameen.. Na gode sosai *K’ANWATA* da addu’ar ki,nd in sha Allah sak’on ki zai isa ga kowa kamar yadda kika fad’a..!”

   Haka nan ta tsinci kanta a cikin yanayin jin dad’in amsar sa wanda har yasa ta saki murmushi,,,duka sun sake yin jim ba tare da wani cikinsu ya sake cewa komai ba,a lokacin sai ga baffa ya fito,nan ya d’an kallesu duka kana yana fad’in

  “Toh..! Mai babban suna, idan kun kammala sai mu tafi ko..!?”

    “Toh baffa..”

   Abunda ya fito daga bakinsa kenan,nd tun bai kaiga gama fad’a ba tuni tayi saurin d’agowa tana kallonsa,yayin da a lokaci guda taji wani irin tashin hankali ya sake ziyartar ta,gaba baffa ya wuce zuwa waje,nan shima ya motsa daga inda yake da hannayensa zube cikin aljihun trouser d’insa,sai daya kalleta sannan ya fahimci itanma shi take kallon buh yanayin da fuskarta ta bayyanar sai yasa zuciyansa tafiya tak’aitaccen yajin aiki,,sam bata kula da abunda yake yi ba,sai dai taji muryansa daf da ita,da sauri ta dawo hayyacinta tana sake kallon yadda suka yi closer da juna,d’an ja baya tayi kad’an tana jingina bayanta da katangan soron,ba tare daya sake matsowa ba ya furta

  “Arrmm! *K’ANWATA* ni zan wuce ko..!?”

  Kai ta rausayar gefe ba tare data sake iya yin k’arfin halin yi masa magana ba,still tana tsayen sai dai kanta yana k’asa tana wasa da yatsunta,,a d’an kaikaice ya kalleta while yana sake fad’in

    “Ki shiga gida,,,sai na dawo ko..!?”

  

  Kamar zata d’ora hannunta aka tayi ta zunduma ihu haka take ji a duk sanda yace zai tafi,,ganin ta kasa motsawa a gurin sai ya sashi juyawa ya kama hanyar fita yana sake maimaita mata

   “Na tafi..nd ina son ki maida hankali sosai akan karatunki..”

   Da sauri ta d’ago kanta dake sunkuye,slightly idanunta suna tara hawaye,har ya fice akan idanunta ba tare data iya ce masa komai ba,a hankali ta shiga silalewa a gurin har ta kaiga zama kan dandagaryar k’asa,yayin da hawayenta suka sami damar fara sauka,kanta ta kife a tsakanin guiwarta tana sakin sheshshek’ar kuka mai tsuma zuciya.

     A k’ofar gidan ya iske baffa suna jiransa,dan haka ko daya k’araso fuskarsa cike take da fara’a

     “Baffa mu tafi ko..!?”

  Ya furta yana mai kallon dattijon,har baffa zai amsa masa,nan ya hango inuwarta a soron bata tafi ba,shima murmushin ya maida masa kana yana fad’in

    “K’ANWAR taka ta shiga gida ne..!?”

   Saurin waiwayawa yayi yana kallon soron ba tare daya amsawa maganar baffan ba,kasancewar kuma yafi baffa kusa da inda zai hangota d’in,ko daya juya d’in nan take ya hangota zaune dirshan,sake kallon baffa yayi kamar zai yi magana,kuma sai ya fasa ya juya da sauri zuwa soron,,tana zaune tana ta rera kuka abunta har ya k’araso kanta bata sani ba,a dai² gabanta ya tsuguna yana kallonta ba tare da yayi mata magana ba,k’amshinsa da yayi remaining a soron ne ya fara ziyartar hancinta buh this time around tana jinsa sosai ne ba kamar lokacin daya fita ba,saurin d’ago kanta tayi da hawayenta har lokacin suka gagara tsayawa,idanunta suka sauka akansa yana tsugune daf da ita,k’ik’k’ifta idanu ta shiga yitana son tabbatarwa kanta anya shi ne ya dawo da gaske..!? Ta d’auki mintuna tana kallonsa kafin ta amincewa ranta abunda idanunta suke gani,ko data tabbatar shi d’in ne a gabta da gaske,cikin sauri ta fara k’ok’arin goge fuskarta,shima cikin saurin ya zaro handkerchief yana mik’a mata,da kyar tasa hannunta ta karb’a sannan ta kai shi fuskarta tana goge hawayen,k’amshin da handkey d’in keyi a lokacin daya bugi hancinta ya sata lumshe idanunta kad’an

    “Mene ne dalilin da yasa ki kuka..!?”

   Tambayarsa ta shiga mata amsa kuwa a cikin kunnuwanta,saurin dawowa hayyacinta tayi da sauri ta fara k’ok’arin mik’ewa,malalacin kallon daya bita da shi ne yasa ta komawa ta zauna sai dai ta kasa amsa masa,a hankali ya tab’e baki jin tayi shiru bata amsa shiba sai yasa shi sake fad’in

  “Tashi ki shiga ciki..Nd kada na kuma ganinki kin zauna a nan kina wannan kukan..Kin jini ba..!?”

    Kamar zata bud’e baki ta fad’a masa dalilin ta nayin kukan,kuma sai taji ba zata tab’a iya yin hakan ba,har ta tashi zata wuce shi ba tare da tayi magana ba yayi saurin rik’o hannunta ta baya,kyam ta daskare a gurin tamkar ginannen dutse zuciyarta fal tsoro,shima a hanakli ya shiga dawowa ita baya har ya dawo da ita inda ta tashi,kallonta yake kamar bazai daina ba sai dai tuni ya saki hannunta daya rik’o

    “Mene ne yake damun ki..!?”

     Ya tambayeta

    “Nima ban sani ba.!”

   Amsan yayi escaping daga bakinta without ta shiryawa yin hakan,d’an murmushi yayi sama² kuma yana fad’in

     “I don’t think so.. Nasan kin sani buh kina k’ok’arin boy’ewa dai!”

   Saurin kallon sa tayi sai kuma ta sake saurin sauke kanta k’asa tana girgizawa,sake matsawa yayi sosai kusa da ita har numfashin su yana had’uwa

   “Ban yarda baki sani ba,,,shin zaki fad’a min ne ko kuwa sai na..!?”

   Yana maganar yana sake nufarta,idonta tayi saurin rufewa cike da tsoron abunda zai mata ta sake fad’in

   “Ka yarda da ni..Ban sani ba..!”

  Cak ya tsaya ba tare daya k’ara ko da taku d’aya ba,yana sake zuba mata idanunsa

   “Da gaske baki sani d’in ba..!?”

 

    “Ehh! Ban s…Sa..Sa ni ba..!”

   Daga yadda take magana ya tabbatar masa ba wai abunda take so ta fad’a ba kenan,sai dai haka nan yaji bazai iya takura mata ta fad’a masa ba,matsawa ya fara yi daga kusa da ita yana kad’a kai

    “Ok good..!”

   A hankali ta fara bud’e idanunta dake rufe,ko data gama bud’e su nan taga ya bar kusa da ita,ajiyar zuciya ta sauke mai k’arfin gaske,,har lokacin itan yake kallo,sai yaga ta d’an runtse idanu,a hankali kuma y’an guntun hawayen da suka mak’ale suka samu damar saukowa,hannunta da yake rik’e da handkey d’insa tasa ta d’auke su,kana ta juya da sauri ta shige gidan ba tare data sake bari sun had’a ido da shi ba,,kayataccen murmushi ya saki yana shafo moustache d’insa,sai daya shafe kusan minti biyu a gurin sannan ya juya cikin sauri ya fice,bai sake tsayawa ba bayan ya d’anyi gaba ya kalli su baffa yana fad’in

   “Baffa mu je…Ta koma gida yanzun..!”

  D’an murmushi baffa yayi masa sannan suka kama hanya dukansu,har sun d’anyi nisa kuma haka kawai sai yaji yana sha’awar sake kallon kofar gidan,a hankali ya d’an waiwayo ya kalli k’ofar gidan kafin yayi ajiyar zuciya,kana suka ci gaba da tafiya,duk hiran da su Hamudan sukewa baffa akan zuwa birni bai san suna yi ba dan shi tuni zuciyarsa tayi wani duniyar,,,har bakin titi suka rako shi,nd wannan lokacin sai basu tsaya inda suka saba ba,har tsallaken titin suka kawo shi sannan suka shiga ajiye kayan a k’asa yayin dabaffa yake fad’in

  “To mai babban suna nasan dai abun hawa bazai yi wahalar samu ba a nan tunda mun fito.”

Murmushi yayi kad’an yace

   “Haka ne baffa,,amma da mota ma na zo..”

  Kallonsa baffa yayi da mamaki sosai a saman fuskarsa,duk da hakan daya fad’a d’in ba wai abun ace yayi mamakin bane,idan har ace yayi duba da irin suturun da yake sawa,ahi kam Muhammad ba tare daya jira cewar baffa ba ya matsa kusa da mutumin da yake bawa ajiyar motansa a duk lokacin da yazo yayi masa sallama,bayan nan kuma yayi masa godiya kamar yadda ya saba had’e da yi masa alkhairi ya bud’e motan ya shiga,ko da baffa yaga ya shiga motan duk da yana cikin yanayin mamaki amma kuma hakan bai hana shi yin magana ba,a fili ya furta

   “Ikon Allah..!”

   Kafin ya matsa gurin motan,nan suma su Hamudan suka yi saurin d’aukan sacks d’in da suka ajiye suna rige² suka nufi kusa da motan nasa sai wangale baki suke murna fal zuciyoyinsu,sai daya gyara packing ya saita motan dai² yadda yana tashi zai hau kwalta sannan ya fito ya saka buhunhunan tsarabarsa a booth,,a hankali ya matsa inda baffa yake tsaye har lokacin shi dai yana cikin mamakinsa

    “To baffa..Ni zan wuce..!”

  Firgigit baffa ya dawo daga tunanin daya lula ya amsa masa

  “Tohh! MUHAMMADU Allah ya tsare,Allah ya kiyaye ko..? A gaida magabatan..Mun gode sosai,ubangiji yayi albarka kuma ya saukeka lafiya..”

   Kansa yana duk’e a k’asa yana amsawa da

   “Ameen baffa..Na gode sosai nima,ubangiji yaja da nisan kwana..”

  “Ameen” baffa ya amsa masa sannan ya kalli su Sule yana fad’in

  “Toh ku malamai sai mu koma ko..!?”

  Saurin dakatar da su MUHAMMAD yayi yana cewa

  “Sulaiman..! Ku jira ni kad’an kunji..!?”

  Motan ya koma da sauri sannan ya d’auko wasu lesser guda biyu masu kyau,yana murmushi ya sake fitowa inda suke,sai daya kalli yaran sannan yace

  “Yawwa samarin baffa..ga shi ko..!? Wannan naku ne..wannan kuma ku kaiwa..!”

   Sai yayi d’an jim kafin yace

   “Ku bawa Auntyn ku..”

   Kallon juna suka yi sannan suka kalleshi suna masa murmushi,cikin had’in baki duka suka furta

     “Aunty *SABINA..!?”*

  Kai ya girgiza musu yana lumshe idanunsa,baffa ne ya matso inda suke yana fad’in

  “Anya mai babban suna..!? Kai da zaka yi tafiya me ya kaika tsayawa siye² haka..!?”

  Murmushi yayiwa baffa sannan yace

  “Babu komai baffa,, gani nayi idan na tafi yanzun zan jima ban sake dawowa ba,,,sannan na manta da sak’on ne tun d’azun shi yasa ban kai musu ba..”

  “Toh! Ai shi kenan..An gode sosai Allah yayi albarka..”

   Da “ameen” ya amsa masa sannan yasa hannunsa a aljihu ya zaro kud’in da bai san ko nawa bane ya mik’awa baffan,nan baffa ya nuna sam bazai karb’a ba,sai da suka kai ruwa rana kafin da kyar baffan ya amince ya karb’a,, sunyi masa godiya sosai,shima yana ta yiwa baffan godiya kafin ya shiga motan yaja ya barsu a nan,basu suka tafi daga gurin ba suma har sai da suka ga yayi musu nisa sosai sannan suka yi k’ok’arin tsallaka titin suka d’auki hanyan komawa zuciyoyinsu cike da alhinin tafiyar tasa.

   Shi kansa MUHAMMAD tunda ya d’auki hanya yake ci gaba da hangensu ta cikin mirror nd yana jin zuciyarsa tayi masa wani iri,yana jin kamar ya koma gare su,,a hakan ya daure yaci gaba da driven tun yana iya hangensu suna masa waving har yayi nisa da su ya daina hangosu.

   Kai tsaye ko daya taho sai daya shiga campus inda ya bar Sultan yana ta jiransa,a lokacin kuwa a b’angaren sultan zuwa lokacin tuni ya gama zuwa wuya dan yadda ya gaji da zaman jiran nasa,gashi tun tuni sai kiransa yake amma amsa d’aya yake samu shi ne yana ta rejecting calls d’in nasa,,lokacin daya k’araso bai ko kalli sultan d’in ba ya wani had’e rai yana fad’in

   “MALAM ka taso mu wuce ko..!?”

  Kallonsa sultan yayi cikin takaici sannan ya mik’e ya shiga motan ya zauna,sai dai bai kula shiba dan yasan fad’an zai iya juyawa ya dawo kansa,,,sai da yayi reverse sannan ya sake take motar da mugun gudu ya fice a cikin makaranta,har suka d’auki hanyan cikin garin Kano sultan bai ce masa ko ci kanka ba,haka shima gogan bai bashi fuskar da zai masa k’orafi ba,yadda duk suka yiwa juna shiru sai yasa tafiyan nasu ya zama bashi da maraba dana kurame.

In less than 1 one hour suka shigo cikin gari kasancewar bada wasa yake tuk’in ba,nan da nan sai gasu akan titin mayangu dake cikin unguwar ta nassarawa G.R.A,daf da race course ya karkata kan motan inda ya tsaya bakin wani katafaren gida na gani a fad’a,,wanda take ni kaina ko da naga ya tsaya a bakin wannan katafaren gidan yasa birona sub’ucewa daga hannuna,har ban san lokacin da bakina ya furta “Ya salaam…!” Ba saboda tsaruwar gidan tun daga waje….

_Hhhhh! Fan’s kada ku gaji dani,ku dai kiui gaba da hak’uri,kwana biyun nan ne muna fama da matsalar wuta a gari sai kun k’ara hak’uri dan zaku ga bana posting akan lokaci kamar baya,,so ba daga ni bane,matsalan kusan duka gari ne.Ayi min afuwa._Horn ya shiga matsawa cike da k’aguwa yana jiran a bud’e masa ya shige,,sai lokacin ya d’an waiwayawa a hankali zuwa gefen sultan yana kallon yadda ya gimtse tamkar baya gurin duk kuwa da irin surutun sa amma yau yayi masa shiru,d’an murmushi ya saki mai sauti kafin ya furta

    “Heyy! Friend what’s up..!?”

    Wani mugun kallo sultan ya watsa masa mai tattare da jin haushin tambayar da yayi masan sai dai bai tanka masa ba,saima siririn tsaki da yaja kafin ya sake d’auke kai,a zuciyansa kuwa haushin Muhammad d’in duk ya cika shi nd yana ganin tambayar da yayi masa ma bata da maraba data rainin hankali,,wani murmushin ya sake yi masa kafin ya tab’e baki ya juyar da kansa zuwa kallon get d’in da ake bud’ewa,sai daya bari get man d’in ya gama janye masa get d’in sannan ya taka motan zuwa ciki yana d’aga masa hannu a sakamakon gaisuwar da yake masa da bai samu damar amsawa ba,,tsarin gidan wani irin had’ad’d’en duplex ne wanda tsayawa a fayyace shi zai zama k’auyanci,ta ko ina idan har mutum ya kalla ginin gidan da tsarinsa zai tabbatarwa kansa ya tsaru iya had’uwa,haka nan duk kushen mai kushewa bai isa ya kalli wannan gidan yace bai masa ba,musamman duba da yadda tun daga harabar gidan ya kasance cike da wasu irin shuke² na alfarma,,haka ma daga tsakiyar gidan daya kasance yana d’auke da had’ad’d’en roundabout wanda wasu irin fitilu suke bawa gurin haske nd still suma d’in suna zagaye da kyawawan flowers wanda suka sake k’awata yanayin gurin,hakama ta jikin walls d’in gidan daga duka sides shima ya kasance tun daga ta wajen sa kafinma mutum yayi arba da ainihin cikin gidan,,,direct carport ya nufa da su,bayan ya gama daidaita parking sannan ya fice daga motan ba tare da yayiwa sultan magana ba,shima d’in bai kula shiba ya fito dan yasan abunda shirun sa ke nufi,nan dukansu suka tasamma apartment d’in dake tsakiyar gidan,,Muhammad a gaba yayin da sultan yake biye da shi har suka tsaya bakin k’ofar apartment d’in,ba tare daya tsaya bawa kansa wahala ba ya murd’a handle d’in jikin k’ofar sannan ya tura kansa zuwa cikin k’ayataccen parlor’n yana yin sallama,,sanyayyan k’amshi mai tattare da sanyin ni’ima ne ya buge shi,nan ya d’an lumshe idanunsa a hankali yana jin wani irin farin ciki na ratsa duka veins d’insa a sakamakon tsintar kansa da yayi cikin gidansu.

   Sakkowarta kenan daga saman staircase sanye cikin Arabian gown ta yane kanta da vail d’in kayan,y’ar fuskarta nan tasha light make-up daya amsheta,sosai tayi matuk’ar kyau gwanin a saceta a gudu,,karaf sai idanunta suka sauka akansa yana shigowa,ihun murna ta saki cikin k’araji tana fad’in

     “Yah *HAMMAD..!”*

   Murmushi ya sakar mata yana kallon yadda ta kwaso a guje,ko data zo gabansa bata tsaya wata² ba ta mak’ale shi tana ta murna,sai lokacin Sultan ya saki fuskarsa dake had’e sannan ya d’an matso kusa da su yana fad’in

   “Wato shi kad’ai kika gani ko Baby.!?”

   Saurin d’agowa tayi daga jikin yayan nata ta waiga inda taji maganarsa,four eyes suka yi da shi yana sakar mata murmushi,amma sai tayi saurin sauke kai k’asa,itanma tana murmusawa nd muryanta k’asa² ta ce

  “Kaiii! Yah Sultan,,ai dai kasan ban ganka bane,,kuma ma ai a bayan Yah ka b’uya shi yasa..!”

  

   “Yeah..! Dama na san amsar kenan ai,kullum a bayansa nake mak’alewa ba..!?”

  Sake sunkuyar da kai tayi tana wasa da ring d’inta nd ba tare data sake yin magana ba sai d’an murmushi da take ta zubawa,,ga Hammad kuwa tab’e baki yayi kafin yaja hannunta suka nufi cikin tsakiyar cuitions while yana fad’in

  “Daddy’s Kiddo..! Where’s the households CEO..!? Naji gidan so quite,,shima wannan sarkin kwallon baya nan ko..!?.”

   Y’ar dariya tayi wacce ta bayyanar da asalun kyaunta,nd ta kuma bayyanar da tsananin kamarta da Hammad,tana shirin yin magana sai sultan ya rigata

  “Kai dai wollahi baka da kirki Mamma d’in ce ta koma Households CEO..!?”

   Hararan sa Hammad yayi ba tare daya kula zancen da yake masa ba,sai kasa kunne daya sake yi akan maganar da kid sis d’in nasa ke masa

    “Where’s she ne daddy’s Kiddo..!?”

   Ya sake tambaya yana zuba mata ido,a hankali ta masa murmushi kafin tayi nuni da finger d’inta zuwa hanyan staircase,hannun yabi da kallo zuwa inda take nuna masa yana murmusawa,a tsaye ya hangota ta dafe hannunta d’aya a jikin wall tana kallonsu fuskarta cike da fara’a,kallo d’aya ya isa yasa mutum ya gane cewa wannan ita ce mahaifiyarsu shi da Kid sis d’insa d’in saboda yadda suka yi tsananin kama da ita,,cikin sauri ya mik’e a gurin ya nufi inda take while itanma tana tahowa gare shi,rungume ta yayi saurin yi,duk da matar ba wai gajera bace amma duk Hammad ya kere ta a tsayen

    “Nayi kewarka yaro na..!”

   Hamshak’iyar matar ta furta tana shafa bayansa zuwa kansa nd still suna mak’ale da juna yana zuba mata zance kamar ba shi ne wannan miskilin ba,sai da suka gama murnan ganin juna kafin suka nufo cikin parlor’n tana fad’in

    “A’a..! Sultan tare kuke dama..!?”

  Murmushi yayi kafin yace

   “Ehh! Mamma,, nima abunda yasa banyi magana ba,naga wannan d’an darun naki yana rigima shi yasa nayi shiru..!”

   Murmushi tayi tana shafa kan Hammad dake mak’ale da ita kamar k’aramin yaro,while shi kumayana fad’in

  “Kaji shi wai d’an daru sai kace wani jariri..!”+

   “Uhmm! Dafa..!? Kana da maraba ne da infants..”

   Hararar wasa Hammad ya jefama sultan d’in sai dai bai ce masa komai ba suka zauna nan cikin parlor,,bayan sun gaisa da Mamma sultan yake cewa zai wuce gida,,nan Mamma tace masa sai dai ya jira anjima sai su fita da Hammad d’in zuwa gidan nasu,,ko mintuna ashirin basu yi da shigowa a cikin gidan ba,tuni har an shirya musu table da kayan abinci na alfarma,,after sun ci sun yi godiya ga Allah (S.W.A) sanna suka mik’e suka yi sama,alwala suka d’aura dukansu kafin suka fito dan a lokacin tuni har har wasu guraren suka fara kiraye²n sallah sannan suka nufi masjeed.

   A can b’angaren Sabina kuwa,lokacin ko data juya bata iya shigewa cikin gidan ba,har sai data ga fitarsa a zauren gidan,sannan da sauri kuma saita sake dawowa cikin soron,tana kallon lokacin daya tsaya suna magana shi da baffa saita lab’e daga gefe tana lek’ensu har sanda taga sun d’auki hanya,wasu irin hawaye ne suka sake zubo mata a lokacin data rasa ko na mene ne,kafin da sauri kuma ta kalli handkey d’insa daya bar mata,sai tasa ta share fuskarta tana kuma ci gaba da kallonsa,kamar kayan tsafi dai² lokacin ta ambaci sunan sa taga ya waiwayo,dan haka da sauri sai ta koma ta sake boy’ewa tana ci gaba da sauke hawaye,ta jima tsaye a cikin soron nasu har zuwa lokacin da taga sun b’ace mata sannan ta juya cikin rashin kuzari da niyyar komawa cikin gidan,,kusan karo suka yi da shi yana niyyar fitowa daga cikin gidan while itan kuma tana shirin shiga,saurin yin baya tayi tana sadda kanta k’asa dan bata son ko kad’an ta bashi fuskar da zai samu lagonta ko ya gaya mata magana,,shima d’in kallonta kawai yayi from head to toe kafin yaja wani wahalallen tsaki,yana tafiya cikin takaici yana fad’in

  “Tabb’ wannan shi ake kira aikin banza wai harara a duhu,kai dai LADO Allah yaso ka,,baka d’orawa ranka ba bare kasha wahala,,hhhh! Lallai iska tana wahalar da mai kayan kara..Idan ba mutum yaso kai kansa inda Allah bai kai shi ba,ina bak’auye ina d’an binni..!?? Lallai wani ya deb’o ruwan dafa kansa..!!”

  A hankali ta d’ago kanta daga k’asa ta bishi da kallo sai dai bata samu damar yi masa magana ba,ta wuce abunta da niyyar shigewa cikin gida tana jan ajiyar zuciya,har ta kai k’ofa zata shige ta sake jiyo shewarsa yana tafe yana fito had’e da dariya,cikin duniyanci irin nasa yake fad’in

  “Ayyee! Da rabon muyi kallo nan gaba,,hhhh! Zamu ga yadda k’arshen masu son abun duniya zai k’are,,idan an k’ika ana ganin baka da ko kobo,gobe zata yi aso ka,ko dan rufin asiri idan an kwaso kayan kunya…”

  Tsayawa tayi chak a dai² k’ofar tana saurarensa,dai² lokacin daya sake shek’ewa da dariya kafin yasa hannu ya kwab’i bakinsa da yana fad’in

  “Sshhh.! Kaji ka..! Kai dai LADON nan da kaud’in baki kake. ,ina ruwanka ne da zaka fad’i abunda zai faru..!?”

   Duka yana magana ne da kansa nd still yana ci gaba da tafiya,dariyar muguntar daya saki a lokacin ne tasa Sabina saurin shigewa tana runtse idanu dan yadda maganarsa tayi mata zafi a rai,shi kansa LADON ko da yaga ta shige da gudu² sake tuntsirewa yayi da dariya kafin a fili ya furta

  “Kad’an kika gani yarinya.. Daga ke har tsoffinki zaku san kunyi da ni..Mu zuba mu gani..!”

   Daga haka shima d’in sai yasa kai ya fice daga soron.

    Da gudu² ta wuce duka mutanen dake tsakar gidan zuwa d’aki,tana shiga ta kife akan gadonsu tana sakin kuka mai tsuma zuciya,sai da tayi mai isarta dan yadda take jin abu biyu ya had’e mata a rai a lokacin,matuk’ar idan har ace ba kukan tayi ba tana jin bazata tab’a iya samun sassaucin zafin da take ji a ranta ba,ta jima tana kukan kafin ta rarrashi ranta tayi shiru tana ci gaba da jan zuciya,a hakan nan da take a kife baccin wahala ya d’auke ta ba tare data shiryawa yinsa ba.

    Isowarsu baffa k’ofar gidan yayi dai² da lokacin da ake kiran sallah,dan haka daga k’ofar gida ba tare da baffa ya shiga ba sai ya kalli su Hamudan yana fad’in

      “Yawwa samarin baffa,maza ku shiga gida kuyi alwala ko,ku taho masallaci..”

      Da sauri suka amsa da

      “To baffa..!”

      Sannan suka yi cikin gidan da gudu suna ihun murna,tun kafin su k’arasa shiga tuni har sun fara bada labarin irin motar da Hammad yazo da ita,ba iya sa’anninsu kad’ai ba hatta da iyayen su mata dake aiki a tsakar gidan sai da suka tsaya sauraren hirarrakin nasu,,inda daga nan sai suka shashantar da batun zuwa masallaci har sai da baffa ya dawo ya tarwatsa su da carbi sannan duka suka fashe.Nan a cikin gidan yasa su duka suka yi alwala a gabansa sannan ya tusasu a gaba har massalaci suka yi sallah,bayan da suka idar duka suka fito daga duka sai suka sake nufo gida inda anan ne kuma suka d’auki ledar da Hammad ya basu su kaiwa Sabina dan su kam nasu tuni baffa yayi dividen nata wa duka yaran gidan,Sule ne ya kalli Hamudan cikin k’asa da murya yadda babu wanda zai ji shi yana fad’in

      “Yawwa! Hamudan zo muje mu kaiwa Yaya Sabina nata ko..!? Kaga ma ko nasan zata k’ara mana a nata..”

   

      “Ehh! Kuwan muje mu kai mata..amma kayi shiru to kada kasa su yaroro su ji,,kasan cewa zaiyi shima zashi,kuma bayan ba dasu muka samo ba amma duka baffa ya raba mana kai d’aya da su..”

     A sace suka tashi daga cikin sauran y’an uwan nasu suka fice,cikin sauri² suka nufi hanyan d’akin su Sabinar,,tana zaune kamar wacce aka dasa ta had’a kai da guiwa,yayin da ta zubawa guri d’aya ido tana tunani,da sallama suka shigo sai dai saboda nisan da tayi a duniyar tunanin yasa bata jisu ba har sai da Hamudan ya tab’a ta yana fad’in

      “Yaya.! Kina jin mu kuwa..!?”

     A d’an firgice ta d’ago kanta tana fad’in

      “Uhmm! Me kace Hamudan..!?”

     Baki ya fara washewa yana kallonta,yayin da yake yiwa Sule alama daya b’oye lesser,shima d’in y’ar dariya ya saki yana mayar da hannunsa baya kafin ya ce

    “Yaya..! Kin san me..!?”

    Kai ta girgiza musu tana kallonsu duka kafin ta ce

      “A’a.. Mene ne..!?”

   

     “A’aahh! Yaya ai sai kin bamu tukuici zamu fad’a miki..”

      Siririyar ajiyar zuciya tayi kafin ta kallesu tana girgiza kai

      “Shi kenan to naji,,ku fad’a zan baku..”

   

      “Kaii! Yaya kada fa mu fad’a miki kice kin fasa..!”

   

      “Bazan fad’a ba,,ku dai ku fad’a min,kunji y’an k’anne na..”

    Ta fad’a a matuk’ar k’agauce

     “Aaaa! Yaya sai idan kinyi *ALK’AWARI* zaki bamu sannan zamu fad’a miki..”

      Jimm tayi tana kallonsu cikin rabuwarta hankali,idan ta kalli wannan sai ta juya ta kalli wannan duk ta rasa yada za tayi,a hankali kuma cikin rashin wadataccen kuzari ta furta

      “Shi kenan nayi *ALK’AWARI* zan baku,,yanzun ku fad’a min mene nw..”

   Ledar dake rik’e a hannunsa ya fiddo daga bayansa yana mik’a mata,sai data kalli yaron kafin ta ce

  “Na waye wannan d’in..!?”

  Yana dariya yake fad’in

   “Uhmm! Yaya dama fa shi ne da muka raka shi ya bamu yace mu kawo miki..! Kuma ko Yaya kin san wani abu.!?”

  A hankali ta girgiza masa kai while taba amsan ledar,sake rage murya yayi can k’asa kafin ya ce

  “Da mota yazo..! wollahi ki Yaya dan baki ga motar ba,,tabb’! Kin san dame motarsa take kama kuwa..!? Cabb’ Hamudan d’an bata labarin yadda take..Nifa Allah ko Yaya,tunda nake ma ban tab’a ganin irinta ba..”

   Hamudan ne yayi caraf yana cewa

   “Ai Yaya idan kika ga motar ko,,aradun Allah sai kin kusa sumewa..Kin ganta kuwa kamar jirgi..Gata k’atuwa ga kyau kamar me..!”

   Shiru ta sake yi tana sauraren surutun nasu kafin ta ajiye ledar a gefe kana ta mik’e a gurin,naira goma² ta d’auko ta basu sannan tace suje su kyaleta bata jin dad’i yanzun,ba don sun soba haka nan dai suka fice dan su a son ransu ta bud’e ledar suga ko mene ne a ciki,,bayan fitar su har ta mik’e a kan pray mat d’in sai kuma ta dawo ta d’auki ledar sannan ta sake hayewa saman gadon,,sai data zauna dai² akai kafin ta shiga zazzage abunda yake cikin,kwalayen turaruka ne suka fara fad’owa har guda uku kafin wani kyakykyawan kwalin da yake nad’e da wani irin lesser mai kyalkyali shima ya fad’o,na turarukan ta fara juyawa tana dubawa,turaren good girl idanunta suka fara sauka akai,a hankali ta kai hannu ta d’auka kafin ta zaro shi daga ciki,tsarin kwalban kansa abun kallo ne dan bare kuma abunda ke ciki,yadda aka tsara kwalban da wani irin ado tamkar wani hill shoe,nd idan har bawai mutum ya san yadda abun yake ba koya karanta jikinsa babu lallai yayi saurin gane mene ne a ciki,ita kanta sai data juya shi yafi sau nawa a hannunta kafin ta fahimci abunda ko mene ne nan ta ajiye,sannan ta sake d’aukan d’ayan wanda yake d’auke da sunan *beyonce midnight heat* rad’a-rad’a ajikin kwali,shima kansa turaren ba baya bane,hakama tsarin kwalabansa anyi shi ne ta yadda zai ja hankali,sai kuma d’ayan daya kasance irin 2in1 gift set d’innan,daga sama an rubuta *story of love* da k’ananun rubutu,nd da manya kuma an rubuta *CELEBRATE* sosai sunan yaja hankalinta,har bata san lokacin da wani mugun murmushi yayi escaping daga bakinta ba,a hankali ta rungume kwalin a jikinta tana lumshe idanunta,ta jima a haka kafin ta mik’e ta tattara komai ta mayar cikin adakarta sannan ta dawo ta kwanta akan gado sai sakin murmushi take abunta cike da tunanin abunda ya wakana kafin ya tafi.

Fitowarsu daga masjeed suka nufi gidan,after sun iso tsakiyar parlor’n suka iske Mamma zaune ita da kid sis d’in Hammad,basu wani zauna ba Sultan yayi mata sallama,nd shi kuma Hammad yake fad’a mata zaije gidan su Sultan d’in su gaisa da Mom,,d’agowa yarinyar tayi tana kallon Hammad,yanayin ta cike da son tayi magana amma sai taga bai kalle taba,a hankali ta waiwaya gefen da Sultan yake tsaye kafin tayi magana

  “Yah Sultan nima zani..!”

Hammad ne yayi saurin kallonta kafin ya ce

“Ina ne d’in zaki je..!?”

Marairaicewa tayi tana cewa

  “Gidan su Yah Sultan d’in zan biku..”

Sai daya harareta kafin ya furta

“Da yake yawo neba zaki je,,ehmm! Bama wannan ba,kina maida hankali a skul ko kuwa.!?”

Shiru tayi tana sauke kai k’asa,siririn tsaki yaja kafin ya tab’a sultan yana fad’in

  “Man kaga mu wuce kawai.!”

  Kallonsa sultan yayi kamar zaiyi magana da sauri Hammad ya d’aga masa hannu

“Malam..kada kace komai,,wollahi kaji na rantse ko..babu inda zata bimu,,yarinya sai shegen son yawo amma karatu ta tsaya ta maida hankali tak’i,,ai na kusa dawowa ne,zamu gamu..!”

Babu yadda sultan ya iya kan dole yayiwa Mamma sallama sannan yabi Hammad d’in da yadda yake so coz yasan matuk’ar ya fad’i magana baya tab’a canjawa shi yasa ko daya rantse ma yaja bakinsa yayi shiru,nd yaga Mamma bata ce masa komai ba shi yasa dolensa shima yayi musu sallama ya fice,,a carport ya iske shi har ya shige yana jiransa,yana zuwa kuwa suka fice daga gidan,,basu wani yi tafiya mai nisa ba daga gidan nasu,dan duka a k’afa ma idan mutum ya fito daga gidan zai iya hango line d’insu Sultan d’in amma saboda ajebonci dake d’awainiya dasu duka yasa sai da suka d’auki motor,daga nan suka yi cikin Allu avenue zuwa gidan su sultan d’in

  Sai misalin k’arfe tara na dare sannan Hammad ya baro gidansu sultan ya nufo gida,bayan irin hiran da suka yi da Mom d’in sultan d’in,,lokacin kam ko daya dawo gidan still suna zaune kamar yadda ya barsu,,sallama kawai yayiwa Mamma da kid sis d’in nasa duk da ta d’auki fushi da shi a dalilin k’in tafiyar da yayi da ita,,daga nan yayi sama abunsa ya shige bedroom d’insa,ko daya shiga shirin bacci ya shiga yi dan yadda yake jin gajiya a jikinsa har lokacin,,almost 30 minutes da shigowarsa ya gama duk abunda zaiyi sannan ya kwanta,a lokacin da yanayin garin ya d’auki shiru shima gare shi hakan ne ya kasance,,yayi shiru abunsa shi kad’ai a d’akin ba tare da jin motsi ko sautin komai ba,yana daga kwancen a hankali tunaninsa ya fara yin nisa zuwa kan abunda ya faru kafin tahowar su gida,yadda komai ya fara dawo masa a kwakwalwa daki² sai ya sashi sake gyara kwanciyansa yana sake holding pillow dake manne a jikinsa,a hankali ya fara lumshe idanunsa while yana licking lip tamkar wanda yaji wani abu mai zak’i akai….

 Kyakykyawan murmushi ya ajiye a saman fuskarsa mai tattare da wani irin sukuni nd yana sake holding pillow d’in a jikinsa kamar zai tsaga jikinsa ya sashi ciki,idanunsa ya lumshe take sai ya fara tuna glamorous face d’inta mai cike da tashin hankali nd hawaye,a hankali ya sake sakin ajiyar zuciya dan yadda yake tuna moments d’insa da ita da suka ruga suka wuce,gani yake kamar yanzun ne suke kan faruwa,ya jima cikin wannan yanayin na tunani kafin wani irin bacci mai cike da nutsuwa yayi gaba da shi.

   

    Wasa² yau kwana biyu kenan da dawowar Hammad gida saboda break da suka samu,,sai dai wani abun mamaki a tattare da shi tun daya dawo d’in har kawo wannan kwanakin da aka d’iba ko da wasa bai iya yiwa Mamma maganar kayan da yazo da shi gidan ba,nd bawai kuma dan ya manta bane,sai dan kawai yana tunanin ta yadda Mamma zata fahimci al’amarin da zai fad’a mata d’in,a nasa hangen gani yake idan har dan ace ta itan ne bazai tab’a samun matsala ba,buh yadda daddyn sa zai fahimci lamarin idan har maganar ya kai kunnensa a wannan gab’ar shi ne abun jinsa,dan yadda ya tabbatarwa kansa idan har yaji wani magana sab’anin wanda ya shafi na karatunsa dole ne sai sun kai ruwa rana da shi,shi yasa duka kwanakin sai ya rasa ta yadda zai b’illoma lamarin,,kullum zai fita daga gidan cike da son neman shawaran da zai magance masa matsalar yake tafiya amma kuma idan ya fitan haka nan zai sake dawowa ba tare da ya samu masalaha ba tunda ya kasa sanar ma kowa,shi yasa a kullum ya kasance cike da tsoro yake dan bai san yadda za suyi da Mamma ba idan har taga kayan ya sani dole ne ta tambaye shi.

    Yau ma ko daya fita sun had’u da Sultan a race course wajen morning exercise,a nan nema yaso ace sun tattauna matsalar da shi buh sai kuma ya rasa ta yadda zai b’illowa lamarin,shi yasa har suka rabu da juna bai samu daman yi masa zancen ba,nd maganar kullum cinsa yake arai sai dai ya kasa fidda shi ga wani,,cikin wannan k’adamin kwanaki suka ci gaba da wucewa ba tare daya samu damar sanarma da kowa ba ciki kuwa har daita kanta Mamma d’in.

  

    Da sanyin safiya kimanin sati guda da dawowarsu,yana tsakiyar bacci ya jiyo ana knocking,a time d’in shi kam ko tashi ma baiyi ba,sai da yaji ana knocking d’in sannan ya mik’e idanunsa har time d’in cike da bacci ya nufi k’ofan nd yana tambayan waye,daga wajen Mamma ta amsa shi da cewa

  “Idan zaka bud’e ne ka bud’e sai kaga ko waye,,if not kuma ka koma kaci gaba da baccin asaran,maimakon ace mutum ya tashi amma tun d’azun abu ya gagara,kusan zuwana uku nan amma still sai da kasa ni dawowa duk da nace bazan sake dawowa tashinka ba,,Allah sa a skul d’in ba wannan shegen baccin kake zuwa kayi ba,shi yasa tun tuni na fad’awa Daddyn ka gara kayi karatu a nesa damu amma ya kafe kan baza kaika karatu waje ba kana yaro,ai ga abunda zama cikin k’asar tamu yake shirin haifarwa nan,,ni dai Allah sa ba wahalar damu kawai kake ba,kana sawa muna b’arnatar da dukiyar mu a banza..”

  Murmushi ya saki still idanunsa a rufen dai² lokacin daya bud’e k’ofar nd ya d’an jingina da ita

  “Haba Mamma..! Har sau nawa kike son na fad’a miki,,nifa idan ba wai na dawo gida ba,ko baccinma bana komawa idan nayi sallah..”+

  Hararan sa tayi tana fad’in

  “Kai tafi can, waye zaka fad’a mawa wannan zancen naka ya yarda,mutumin da idan ya kwanta tamkar corpse (gawa) shi ne zaka bani wannan labarin k’anzon kuregen naka na yarda..”

   “Yeahh! Mamma kawai dai dan baza ki yardan bane,,amma bana iya bacci a skul sosai ki tambaye Sultan tunda shi kina yarda da maganar sa..”

  Tab’e baki tayi kafin ta sake kallon shi up to down,cikin yanayin fara fusata ta furta

   “Wai Hammad wannan wani sabon iskanci ne ka koyo..?? Ina magana kana tsaye min da idanu a rufe.!?”

   A hankali ya fara k’ok’arin bud’e sleeping eyes d’insa da kyar har ya gama ware su,sai dai yana kallonta yana ci gaba da k’ik’k’ifta su alamun baccin bawai ya gama sakinsa ba kenan har lokacin,hararan da Mamma ke sake banka masa ya sashi yi mata murmushin yak’e kafin ya furta

    “Mamma what’s the problem ne..??”

  Siririn tsaki taja kafin ta ce

   “Ban sani ba,,da iskanci yasa kazo min da idanu a rufe kenan ko..!? Bama wannan ba,wancan kayan daka bari a booth na waye ne..!?”

   Wani mugun fad’uwa gaban Hammad yayi kafin cikin in’ina ya fara fad’in

   “Ammm! Ehmm! Mamma..”

  Hannu ta d’aga masa alamun ya mata shiru,shirun yayi buh bakinsa sai motsi yake yana son yin magana,duk irin yadda ya taso da bacci a idanunsa duka tuni ya neme shi ya rasa,nd a time d’in jin jikinsa yake kamar ya wuce 5 hours ma da farkawa a baccin

  “Hammad tambayarka nayi..ka tsaya min in’ina,, ina ka samo wancan kayan..!?”

  Ba bakinsa ba hatta k’afafunsa jinsu yake sun fara neman kasa d’aukan sa,amma saboda dauriya irin tasa sai ji yayi bakinsa na fad’in

    “Please Mamma..”

“Kaga bana son aikin wahalar da kai,,am just asking…Ni bance kamin dogon magana ba,,just tell me na wane ne..!? Kasan bana son wannan shashancin ko..!?”

   Kai ya gyad’a cikin sanyin jikin da bai san sanda ya same shiba while yana furta

   “Mamma na kune..!”

   “Na su waye.!? Mu wai kake magana..!? Uhmm! Hammad kenan,mu da ba muje ko ina ba,ina zamu samo wannan kayan..!? Ke dai ka fad’a min gaskiyar ko na wane ne..”

   “Ohh! Mamma i will explain how ya zama naku..”

   Fuskarsa duk a marairaice kamar zai mata kuka idan ta sake magana

  “Ehmm! Kai nake sauraro ai,,kasan ba ko wane lokaci nake son shirme ba..Ko dai ka nutsu kamin bayani ko kuma…!”

  “No Mamma..I will explain,ba sai kin sanar da Daddy ba,zan sanar miki komai fa..”

   “Ok..Go on,,buh ka hanzarta ni fita zanyi ina da aiki sosai a gabana,,nd Daddy ya sanar min suna hanya yau,ina so naje office na dawo da wuri,dan zan bada excuse nema shi yasa zan fitan,amma da babu inda zani..”

  Da kyar ya had’iye yahu kafin ya ce

  “Mamma to ki bari idan kin dawo sai muyi maganar ko..!?”

  Sai data kalleshi up to down kafin ta wuce shi tana tab’e baki da fad’in

  “Allah ya kaimu..Nd ka san bazan karb’i any excuse ba akan wannan maganar ko..!?”

  “Yeah..! I know..”

   “Good.. Sai ka kasance cikin shirin sanar min gaskiya..If not kuma i will try to inform ur Dad..”

   “Ohhh! Mamma! I told u zan sanar miki komai..I promised u..!”

  Jinjina kai tayi kafin ta wuce cikin sauri² tana fad’in

   “Ok..Na wuce aiki,buh komai yana dining duk lokacin da kula gama k’ailular sai ku duba can..”

   “Ok…Mah see u later.. Allah ya tsare..”

  Da “Ameen” ta amsa tana ci gaba da tafiya,har taje bakin staircase zata fara sauka ya kwalla mata kira da cewa

    “Mah..! Wait..”

   A hankali ta dakata,kafin ta d’an juyo tana kallonsa fuskarta d’auke da mamaki,cikin takunsa na isa ya nufo ta har ya k’araso,ko da yazo d’in sai ya sunkuya kad’an had’e da bata peck a chicks yana mata murmushi had’e da sake fad’in

    “Bye Mah..!”

   Kai ta jinjina masa itama tana masa murmushi sannan ta juya ta fara sauka,shi kam Hammad nan inda ta barshi a tsaye bai iya motsawa ba sai daya d’auki wasu y’an mintuna a gurin,kafin ya tura hannayensa cikin aljihun 3quarter d’insa yana sake binta da kallo har ta fice daga parlor’n,wani gawurtaccen ajiyar zuciya ya saki had’e da fesar da iska,a hankali kuma ya d’an runtse idanunsa while yana fad’in

  “Mamma..! Huh..! U frighten me,,da wannan safiyar duka nayi tunanin ma wani abu ya faru..Ohhh..!”

   Sai daya sake kwashe ak’alla mintuna goma kafin da kyar ya juyawa ya bar wajen,kai tsaye daga nan bedroom ya koma,da shigarsa bai tsaya b’ata lokaci ba ya shige wanka,mintuna sha biyar suka d’auke shi sannan ya fito d’aure da towel a jikinsa,a gaban mirror ya d’an tsaya ya zubawa kansa ido ta ciki nd ruwan dake kansa yanaa sauka a jikinsa ba tare da yayi k’ok’arin sa mini towel ya tsane ba,ya d’auki kusan 2-3 minutes yana kallon kansa kafin ya matsa baya kad’an had’e da rik’e waist d’insa nd continuously looking himself through mirrorn

   “What should i tell Mamma first..!?”

  Ya tambayi kansa nd yana d’an rik’e chin d’insa

     “Nayi mata bayanin komai kenan..!?”

   Sake yin shiru yayi yana kama waist

      “No! Ba haka ya kamata nayi ba..”

   Saurin kallon kansa ya sake yi kamar mai magana da shade d’insa kafin ya sake tambayar kansa

  “Ohh! Ya rabb,help me..What should i tell her ne,idan ta sake min maganar..!? Shin zan mata k’arya ne ko kuwa zan fad’a mata gaskiya..!? I don’t even halted my self akan abunda ya dace..”

  Fuskarsa duk alamun damuwa ya bayyana akai saboda yadda ya rasa gane mafitan da zai yi amfani da shi gurin kare kansa a wajen Mamman,zuwa can kuma a hankali kamar mai rad’a ya sake furta

   “No..Hammad! K’arya bai yi kama da kai ba,,u know tsakanin Mamma ko Daddy babu wanda ka tab’a yima k’arya ko..!? Why yanzun kake son fad’a mata haka duk dan ka kare kanka ne zaka yi k’aryan..!? Shin idan ka fad’a ma kana da tabbacin zata yarda da kaai ne..?? Baka saba ba,nd kada ma ka soma yau,,u know wannan dama ne ka samu da zaka fad’awa Mamma everything game da yarinyar,nd kasan zata sake yarda da kai ne,kana da daman sanar mata komai nd Mamma will help u,u just tell her the truth,kama daina batun yin k’arya,kasan zata ji zafi nefa idan ta gane…Try to explained her everything game da alak’ar dake tsakanin ku,,ita mahaifiyarka ce zata fahimci komai..!”

  Akan wannan shawaran ya tsaya dan yadda yaji zuciyarsa tayi na’am da ita hundred percent,,tun daya fara k’ullawa da warwarewa bai ji ya amince da kowane shawarra ba sama da wannan,dan haka sai ya tsayar da yak’ininsa duka akanta,da fitowarsa a wanka zuwa yanzun ya b’ata kusan one hour ba tare daya morarawa kansa komai ba sai tunanukan da yake ta fama da su,,slender breathe ya saki kafin ya juya zuwa closet d’insa,kayan da yasan sunyi dai² da ra’ayinsa ya d’auka,after ya shirya kansa ya sake tsayawa gaban mirror d’in kafin ya kai hannunsa saman unique perfumes d’insa ya shiga feshe jikinsa dasu,yana ganawa hanyan fita ya tasamma har ya sakko k’asa cikin parlor cike da son barin gidan,cikin rashin sa’a dai² lokacin daya fito yana niyyan ficewa ba tare da yayi kobreakfast d’in da Mamma ta sanar da shi yaba jiransu a dining,sai ya jiyo alamun shigowar motan ta,a parlor kawai ya nemi guri ya zauna yana kad’a car keys d’in dake hannunsan,yayin da zuciyansa ke daka har ta shigo ciki,da shi ta fara yin arba zaune kamar mai jiran wani,ko data shigo d’in har zata wuce shi sai kuma ta dawo cikin parlor’n ta ajiye bag d’inta sannan ta zauna tana kallonsa k’asa²,da fari ki tayi kamar kada ta tambaye shi coz bata son yaga kamar ta damu da son jin maganar da suka yi da shi zai sanar mata idan ta dawo d’in,buh yadda taga yayi zugum kamar wani mara lafiya sai yasa ta kallonsa after taja numfashi ta fara magana da cewa

  “Hammad..! What’s going wrong ne,u look so pale..Akwai wani abu dake damunka ka kasa sanar min ko..!?”

   Ajiyan numfashi yayi kafin ya d’ago idanunsa dake a birkice dan bai sanma ta yadda Mamma zata karb’i batun nasa ba

   “Am asking u,,kasa min idanu kamar Yane ka fara ganinta,kasan dai nak’i jinin nayi magana amin banza ko..!?”

   Gyad’a mata kai yayi sannan ya gyara zama yana fad’in

  “Am really sorry Mah.. Buh..!”

   Sai ya sake yin shiru yana jimanta abunda zai fad’a mata

  “Buh what..!? Ni yau duka na kasa gane maka,I know kana tare da damuwa,amma ban san mene ne dalilin daya hanaka sanar min ba tun wuri…Ka fad’a min mana idan ina da daman magance maka ai ka sani bazan tab’a barin ka da damuwa ba ko..??”

  “Yeahh! Mamma I know kina k’ok’arin ganin kinsamu farin ciki,buh Mah i don’t even know ta yaya ne zan miki bayanin matsalar.”

   “Ok…Ok! Na fahimta,,Kaga ne ko Hammad,ina so ka fad’a min koma ta yaya ne,,kasan zan saurareka ai nd zan fahimci abunda kake nufin..”

  Sai daya ajiye wani gauron numfashin kuma kafin ya fara zayyana mata duk abunda ya faru tsakaninsa da su baffa from the loins till an end ba tare daya rage mata ko wasali ba,ko da ta gama saurarensa itanma wani gawurtaccen ajiyar zuciya ta sauke kafin ta furta

  “Amma Hammad wani lokacin idan kayi wani abun,ji nake kamar nasa maka hannu saboda takaicin ka (which means ta doke shi),yanzun dan Allah wannan d’an abun ne dama ya faru shi ne kaketa faman b’oyewa da shiga damuwa,,i thought ma ni wani abune daban ya faru can,,,ai shi kenan sai ka saki ranka yanzun ko tunda na sani,,nd nayi matuk’ar farin ciki daya zama ka bada himma wajen ceton rayuwarta a wannan lokacin,da ace baka taimaka mata bane a yau da kake bani wannan labarin da nayi fushi da kai,saboda Allah ya baka iko ka bijere buh babu komai,komai ya wuce kaji ko,har kullum dama bamu da fatan daya wuce Ubangiji ya kare bayinsa daga fad’awa halaka da mummunan yanayi..!”

   Murmushin daya gani a fuskarta shine ya bashi k’warin guiwa,nan danan kafin kace me tuni sai ga shi ya ware sun shiga hira,nd fitar daya so yi d’azun sai ya fasa dan dama damuwa ne yasa shi jin fitar,buh ko da yaga yayi solving case d’in sai kawai ya some yinta,yayi zamansa a gidan ba tare daya ji son fita ko nan da can ba.

   Har yamma yana tare da Mamma,a hakan driver ya dawo da kid sis d’insa daga skul haka ma lil brother sa wanda daddy’s kiddo ke bi,kamar yadda Hammad d’in ke kiranta da shi wanda yasa sai sunanta ya b’ace a gidan duka suka koma fad’a mata hakan har shima Daddyn idan har yana garin kuma yana jin raha,dukansu sai suka taru suka zauna nan a parlor suna ta hira,buh ga Hammad duk da jefi² yake sa musu baki a hiran nasu,kasancewar hankalinsa duka da yayi wani nahiyan daban,sai dai yaji dad’in zaman tare da su a hakan saboda ya jima rabonsa da kasancewa cikinsu kamar wannan lokacin,har dare suka kai tare nd a gefe guda kuma suna ta saka ran ganin dawowar Dad d’in kamar yadda ya shaidawa Mamman tun safe sai dai sunji shiru,nd tun daya sanar ma da Mamma zuwan nasa suke ta baza idanu amma sai shiru har wannan lokacin,wayoyinsa ma duka idan sun kira sai dai ace musu a kashe,,kasancewar duka sun san yadda aikin Dad d’in yake sai yasa su bada uzurin ko tafiyar nasa ne bai yiwu ba,shi yasa suka jishi shirun,,nd sun riga sun san matuk’ar ace zai zo d’in to tabbas ne zai sanar musu ya taho d’in,wannan dalilin yasa sai duk zuwa lokacin yasa suka fidda rai da zuwan nasa a yau d’in,kusan 9pm bayan sunyi dinner nd sun sake tab’a hira after like 20 minutes duka suka yi sallama da juna sannan kowa ya shige room d’insa..

   Kwanaki sun sake tafiya a b’angaren Hammad da ahalinsa,yayin da rayuwarsu ya kasance gwanin sha’awa,wanda a gefe guda kuma ya kasance kullum cikin lissafin k’arewar hutunsu yake,dan yadda zuciyarsa ke azalzalarsa da son komawa zuwa garin ya gano halin da suke ciki,sai dai yana ganin kamar a hakan duk da ya d’an kwana biyu da zuwan kwanakin basa wani raguwa,,dan haka ne yau ko daya tashi da safen haka nan sai yaji shifa duk duniya babu inda yake sha’awar zuwa sama da wudil d’in,ba don komai ba sai don kawai yana jin idan bai ganta a yau ba zai iya fuskantar ko wane irin matsala a rayuwarsa….

  _Iyyyeee! Tofa fan’s kun dai ji Hammad da k’ok’ari, buh bari mu bishi muga mene ne zai wakana,,,kada ku manta yanzun ne labarin ya fara,dan haka wasan zai fara ne daga yanzun…_    A gefen Sabina kuwa musamman cikin wad’annan y’an kwanakin da suka gabata kusan ma iya cewa rayuwan ta a wannan lokacin bata tare da ko wane irin damuwa idan aka cire na tafiyarsa,wanda tun a bayan barinsa garin kawo tsayin wad’annan kwanakin duk da takan yi tunani akan har zuwa yaushe ne zai dawo.? Sai dai a mafi yawan lokuta zaka sameta zaune tayi shiru more especially idan tasan bata da wani aiki walau na gida ko na makaranta,haka nan zata zauna tayi zugum a d’aki ita kad’ai,fita kuwa idan har bawai ya zama mata dole ba,zata iya yini shiru ba tare da anji kanta da kowa a cikin gidan ba dama can asalinta ba mai hayaniya  bace (buh ba wai ina nufin idan an tab’a ta tana da hak’uri bane,itan mafad’aciya ce ta gaske sai dai wani abu bai shiga tsakaninta da wani ba,wannan hali ne na masu sunan na fad’a) wannan dalilin yasa sam zaman d’aki a y’an kwanakin baya damunta,haka nan rashin fita da bata yi,a mafi yawan lokuta kuwa idan har ta zauna tayi irin wannan shirun ba komai ne yake damun zuciyarta ba sama da tunanin duk wani abu daya shafi alak’ar su da juna,duk dama dai ba wai ace wani alak’a ne na azo a gani ba d’in ya had’a su ita kam tana yawan tunawa da hakan,,nd a kullum cikin lissafi take tun daga tafiyarsa,adadin kwanakin da yayi sannan a ranta tana sake lissafa wasu y’an kwanaki da sunan sune suka rage masa duk da bawai sunyi magana da shi ya fad’a mata ainihin kwanakin da zai d’auke shi kafin ya dawo ba,,yauma d’in kamar ko wane lokacin ne da yake zuwa mata bata da sauran abunyi banda zama tunaninsa,kamar ko wane lokaci tayi zugum yayin da zuciyarta tayi nisa da gangar jikinta,a hanakali cikin zancen zuci wanda a wasu lokutan har bata sanin lokacin da yake bayyana a fili take juya sunansa da kiransa tana tambayan yaushe ne zai zo,shiru ta sake yi ta nutsu kamar mai sauraren a bata amsa,zuwa wucewar wasu sa’o’i sai ta mik’e a hankali ta nufi adakarta had’e da bud’ewa,turaren *beyonce midnight heat* hannunta ya kai kai,nan ta d’auko shi had’e da bud’ewa tana sunsunar k’amshinsa,ta d’auki ak’alla mintuna biyu da rufaffun idanu kafin ta kai shi jikinta tayi spraying kana ta mayar ta adana,kafin cikin rashin kuzari da tun farko ta kasance a cikinsa ta mik’e ta koma saman gado ta sake kwanciya,nd tana sake dulmiyar cikin tunaninsa.

    Cikin sauri² yake komai har ya kammala shirinsa tsaf ya fito,can k’asan zuciyarsa banda addu’ah kan Allah ya taimake shi babu abunda yake,dan yadda yake sauri ko kad’an baya fatan wani uzurin yazo masa a wannan lokacin,cikin sa’a kuwa har ya gama duk abunda zaiyi ya fito bai had’u da kowa ba,a lokacin kusan 11am har ma ya soma gotawa,,kai tsaye mota ya d’auka kafin ya fice daga gidan ba tare daya sanarma da kowa inda za shi ba,gudun ma kada a samu wani matsalan shi yasa hatta da wayoyinsa sau ya kashe su ya barsu nan a gida,,shi kad’ai cikin motan yake tafiya ba tare daya nemi rakiyan kowa ba,sai dai ya kunna karatu cikin k’ir’ar Maheer Al-mu’ak’illiy cikin suratun NISA’A wanda ya sanace ya d’auke masa kewan rashin abokin taya hira da yayi duk dama dai shi d’in ba gwanin zama ayi hira da shi bane buh tafiya ko da tsakanin kurame ne yafi dad’i,yana driven yana saurare had’e da bii,a hakan har ya k’araso dai² mararraban inda ya saba tsayawa,can daga gefen yayi parking sannan ya nemi mai shop d’in da yake barwa ajiyar motansa,bayan ya shaida masa zai shiga ciki kamar ko wane lokaci kasancewar mutumin ya gane shi yasa tun daya ganshi fuskarsa cike da fara’a sai ya tarbeshi,nd daya tunma kafin ya sanar masa da abunda ya kawo shin yayi masa fatan alkhairi tare da fatan fitowa lafiya,bayan daya amsa nan ya tsallaka had’e da fara takawa da k’afafun sa zuwa cikin d’an k’auyen.

   Tafiya kawai yake yana kallon yadda amfanin gona yaui kyau,duk kuwa da kasancewar ba damuna bane,da yake gurin akwai ruwa shi yasa amfanin gona a ko wane seasons zaka tarar yayi shar gwanin sha’awa,tafiya kawai yake amma a yau sai yake ganin kamar ana k’ara masa nisanta,duk da irin dogon hanyan daya kwaso daga cikin Kano zuwa wudil d’in wanda duk bai ga nisan suba,sai wannan da yake daf ma da isa cikin d’an k’auyen nasu,shi kansa zuwa wannan lokacin duk da yana jin ya kusa isa,hakan bai hana shi fatan yayi ya tarar da castle na rugan ba,ak’alla sai da yayi tafiya mai d’an nisa daga main road na wudil kafin yayi reaching castle na rugar,ko da idanunsa suka sauka akan k’ofar gidan nasu bai san lokacin da wani irin farin cikiya fara ziyartarsa ba,a hankali ya saki sanyayyan ajiyar zuciya while a fili yana fad’in

     “Alhamdulillah.. Alaa kulli halin..!”

   Kafin yaci gaba da tafiya yana sake nufar k’ofar gidan,dai² lokacin daya iso yana niyyan tsayawa a k’ofar gidan da hangen inda zai samu yaro ya aika duk da baffa ya sha masa fad’an idan yazo ya shiga kai tsaye hakan ba matsala bane amma sam ya gagara dainawa,domin kuwa a ganin Hammad yin hakan dai² yake da rusa dokar da ubangiji (S.W.T) ya shimfid’a ne,shi yasa har kullum idan yazo d’in ya gwammace ya fara tsayawa ya nemi d’an aike,idan ya samu iso daga gurin masu gidan falillahil hand,,,dai² lokacin daya k’araso yayi dai² da fitowan su Hamudan suna daga gidan zasu je d’iban ruwa rafi,da yake duka babu wanda bai san Hammad ba a gidan walau babba ko k’arami nan da nan ganinsa tsaye sai yasa duka suka nufi inda yake suna washe masa baki,abunka da yaro baya manta alkhairi ko mai k’ank’antarsa kaza lika sharri duk k’ank’antarsa baya tab’a gogewa a zuciyar yarinta,idan ka kyautata ko akasin haka duk mun tsayin lokaci abun tunawa,(Saboda haka k’alubale gare ku jama’a masu zaluntar yara suna fad’in ai basu da hankali baza su gane ba,kana cutarsa a lokacin daka samu dama,shi kuma yana rik’e abun aransa,baza kasan kana yiwa kanka mugunta ba sai lokacin da ya kamata wannan yaron yaji k’anka yazo na tabbata a nan ne zaka ji zance ya sauya salo,,saboda haka garemu gyara ya rage namu) lokacin da suka k’araso kusa sa shi suna masa dariya shima sai ya sake sakin fuska nd yana fad’in

  “A’ahh! Samarin baffa,daga nan sai ina kenan..!?”

     Cikin hanzari Sule ne ya karb’a masa yana fad’in

    “Wollahi rafi zamu je d’iban ruwa..”

  “Ohh! To maza Allah ta tsare hanya,,sai kun dawo ma had’u ko..!?”

   Amsawa suka yi da to,har sun juya zasu tafi sai kuma yayi saurin tambayarsu

    “Hameed..! Baffa yana gida kuwa..??”

  Wani dariyar jin dad’i Hamudan yayi dan yadda Hammad d’in ke kiran sunansa a gayance,a mafi yawan lokuta yana matuk’ar k’aunar zuwansa gidan nasu dan yadda yake kiran sunansa cikin lafazi mai dad’i ba kamar y’an gidansu ba da suke kiransa Hamudan,akan wannan dalilin nema a yanzun ya tsani yaji an kira shi da Hamudan,wanda tun can da bai tab’a jin ya tsani hakan ba,sai a bayan zuwan da Hammad,,Sule ne yayi caraf ya amsa masa dan shi Hameed ko nace Hamudan tuni ya lula duniyar farin ciki

     “Ehh! Yana nan..Bai dad’e ma da dawowa gida ba.!”

   “Yawwa samarin baffa,maza kuyi min iso gurinsa kunji..”

   A guje suka koka yi cikin gidan suna rige² kowanne burinsa ace shi ne a kan gaba wajen shaidawa baffa sak’on Hammad d’in,,ko da suka shigan maimakon ace duka sunyi hanya d’aya kamar yadda suka shigo da niyya d’ayan,nan Sule ya shiga gurin baffa while shi kuma Hamudan ya sai ya shek’a agujen ya nufi d’akin su Sabina,tun kafin ya k’araso k’ofar d’akin ya shiga rafka mata kira

      “Yaya.! Yayah..!”

      Tana kwance tun bayan data gama feshe²n turaren ta jiyo karad’in sa yana kiranta,a lokacin zuciyarta tana raunane a dalilin rashin nayi,tana shirin mik’ewa ta zauna Hamudan d’in ya fad’o d’akin sai haki yake yi,nd still yana sake kiranta

      “Yayah..! Kina ina wai..!?”

     Sai data ja siririn tsaki kafin ta yamutse fuska da fad’in

      “Wai kawai Hamudan wannan wane irin takurawa ne sai kirana kake kamar naci maka bashi..Mene ne zanyi maka ne..!?”

     Abunku da yaro baya son yaji an gwasale shi,matuk’ar ace yazo da wani abu na musamman nan da nan sai hakan yasa yaji haushi,bata rai yayi kafin ya kalleta yana cewa

      “Haba Yaya..Kin sanfa bana son ana kirana da haka..Al’halin kin san Yayah Muhammad ma ya ce ba haka ne suna na ba.”

      Tsaki ta sake yi cikin takaici ta juya ta kwanta tana fad’in

      “Wahalallen banza ai sai kayi tayi..”

     

     “Yayah to albishir fa nazo miki shi ne amma zaki min haka,, shi kenan nama fasa fad’a mikin,,kinga tafiya ta..”

     Tana daga kwancen ta tab’e baki kafin ta sake juya masa baya tana fad’in

     “Idan ka gaji sai ka tafi ai..Ni bana son a dame ni..”

    

      “Shi kenan Yayah tunda kin gwale ni..Daga yauma bazan kuma zuwa na fad’a miki komai ba..”

    Har ya juya cikin jin haushin abunda tayi masa yana niyyar fita daga d’akin tayi saurin tasowa ta rik’o shi,haka nan sai take jin zuciyarta na shaida mata bata kyautawa yaron ba idan har tak’i saurarensa,cikin sanyin jiki ta kalle shi sosai kafin ta furta

      “Yi hak’uri d’an k’anina,,yanzun ka fad’a min mene ne kake kiran nawa,kaji samarin baffa..”

     Sake b’ata rai yayi nd yana ta k’ok’arin kwace hannunsa daga rik’on data masa

     “Ni ki sake min hannu na tafi,,ai bakya son na fad’a miki tunda har koratama kika yi..”

   

     “Kaii! Hameed d’in baffa nice fa..Wannan yayar taka..Mai k’aunar nan taka.Yawwa zo ka fad’a min kaji Hameed d’ina..!”

      Jin da yayi ta kirashi da sunan da yake matuk’ar k’auna nan da nan sai gashi ya saki fuskarsa yana murmusawa,itama kanta Sabinar ko data ga yayi dariya haka nan sai ta tsinci kanta da yin murmushin da bata san dalilinsa ba

      “Shi kenan Yayah.! Zan fad’a miki,amma kawo kunnenki kiji..”

     Ya fad’a yana rik’o fuskarta,sake matsowa tayi tana masa murmushi

      “To Hameed ga shi,fad’a min naji mene ne..”

    K’asa² dai² kunnenta ya ce

      “Yayah..! Ya zo fa yanzun nan..”

      Saurin d’agowa tayi da kanta tana kallonsa kafin tace

     “Waye ya zo Hameed..!?”

      Yar dariya ya saki mai sauti sannan cikin salon jan rai yace

      “Kai Yayah.. Wai baki san wanda yazo ba d’in..!?”

    Ahanakli ta kad’a masa kai alamun haka ne,ficewa yayi saurin yi a guje yana fad’in

     “Yayah Muhammad nake nufi Yaya..!”

    A hankali sunan ya fara zagayawa ta cikin duka veins d’inta har ya kai ga ya samu damar bugun zuciyarta,nan take ta fara jin wani irin fad’uwar gaba na bijiro mata a sakamakon ambaton sunansa kawao da Hameed d’in yayi,har ta daina ganinsa bata fasa bin hanyar daya bi da kallo ba,bayan wasu yan mintuna kuma sai tayi zugum sannan ta koma ta zauna tana tunani a zuciyarta,saboda wasu irin mix-feelings da suka had’u suka cure mata a guri guda,a lokacin jinta take tamkar anyi mata albishir da zuwa hajji,bata motsa ba sai ma sake dunk’ulewa da tayi ta zura kanta a tsakanin kafafuwanta tana surutai ita d’aya

      “Ya Allah shin nayi murna ko kuwa mene ne ya kamata nayi yanzun.!? Da gaske ne shi d’in ne ya zo..!? Ohh! Ya rabb help me..!”

      Duka farin ciki da jin labarin zuwansa gaba d’aya yasa ta kasa samun sukuni,idan ta motsa nan sai ta sake dawowa duk ta rasa inda ya kamata ta nufa dan tsananin murnan da take yi.

   

   Yadda suka shiga a guje haka wajen dawowa su labarta masa sak’on baffan na cewa da yayi ya shigo,suna tafe suna ture-turen juna su a dole sai d’aya ya riga d’aya fad’an sak’on duk da ba tare suka je gurin baffan ba,tun kafin su k’arasa kusa da shi Hamudan duk da ba shi ne yaje gurin baffa ba cikin karad’i yace

     “Yace wai ka shiga..!”

Hararan sa Sule yayi yana cewa

   “Dillah tafi can,,ai naga di ba haka baffa yace na fad’a ba..”

  Murmushi Hammad yayi musu duka kafin yayi magana tuni Sule ya riga shi

  “Cewa fa baffa yayi wai ba yace ka dunga shiga ba idan kazo..Shi ne ka tsaya a waje kamar bak’o.”

   Still murmushi ya sake yi kafin ya ce

  “Ok..Ok.! Na gode duka,,yanzun maza kuyi sauri ko…Sai kun dawo zamu had’u,amma banda fad’a kunji ko..?”

       “To Yayah..”

   Suka amsa masa,daga haka kuma sai suka juya cikin sauri² duk da anayi ana tsokanar juna suka d’auki hanya,shima kansa Hammad bayan da yaga tafiyarsu sai ya juyawa ya nufi hanyar da zai sada shi da cikin gida kamar yadda baffa ya bashi izini,,tun daga bakin k’ofa yayi sallama nd ko da zai shiga ciki ma sai daya sake yin wani sannan ya shiga,a tsakar gidan ya iske tsiraru daga jama’ar gidan suna ta hidin-dimunsu na yau da kullum,sai da suka gaisa da su tukun kafin ya nufi d’akin saukar bak’in na baffa,da sallama ya iske shi a kishingid’e da alamun kamar bai jima da shigowa sosai ba duba da yadda yake fifita jikinsa a jik’e da zufa.Kok’arin tashi baffan ya shiga yi ko daya zauna fuskarsa cike da fara’a yake fad’in

  “Mai babban suna,, kai ne tafe da wannan ranar..!?”

  Murmushin shima yayi masa kafin ya amsa da cewa

  “Ni ne baffa,,fatan na same ku lafiya..!?”

  “Alhamdulillah..! Kam ya ka baro manyan naka..!?”

  Dai² yana zama ya sake amsawa da

“Lafiyarsu k’alau baffa..”

  “Masha Allah..! Haka kullum muke fata.”

  D’an jimm dukansu suka yi kafin baffa ya kalleshi yana sake murmusawa da fad’in

  “Kada dai ace har hutun daka ce d’in ya k’are..??”

   “A’a baffa,,hutu kam da saura..”

  “Aihoo toh..! Nayi zaton ai ko har hutun naka ne ya k’are,nace lokaci babu wahala..”

   Murmushi kad’ai yayi kafin ya sake sunkuyar da kai k’asa,kallonsa baffa ya sake yi kad’an kafin yace

  “Amma mai babban suna,,tafiyar nan bata maka nisa ba,ka taso tun daga Kano har nan..!? Ai daka jira k’arewar hutun naka ko..?”

   Gajeran murmushi ya saki a ransa yana fad’in

  “Haba..! Baffa taya za’ayi zuwa nan yayi min nisa..!? Ai ko kullum ya kama nazo na taho..Bare dan nazo yau kad’ai..”

 

   “Amm! Baffa ai da yake na lek’o makaranta ne,shi ne nace bari na k’araso mu gaisa,, nasan idan na tafi zai d’auke mu tsayin wasu kwanakin kafin mu sake ganawa..”

  Tsintae kansa kawai yana fad’awa baffa hakan ba tare daya shiryawa yin hakan ba

   “A’aahh! Ai kam ka kyauta sosai,,yadda ka rik’e zumunci da mu haka,babu abunda zamu ce dakai sai godiya da fatan alkhairi.. Allah kuma ya saka maka da mafificin alkhairinsa..”

   “Ameen” ya amsa yana ci gaba da sunkuyar da kai dan wani irin kunyar baffan daya tsinci kansa ciki a sakamakon k’aryar daya gindaya masa wacce yake gudun ace ya gano hakan,,baffa kam bai san me yake k’issimawa aransa ba sai dai ya mik’e cikin sauri ya fita yana fad’in

  “Mai babban suna,,Ina dawowa yanzun kaji ko..?”

  

    “Toh baffa Allah ya tsare hanya..”

  Ya bishi da addu’ar fatan alkhairi har ya fice.

   Kamar wacce aka cillo daga d’akin ta fito tsakar gidan sai raba idanu take,burin ta duka a lokacin bai wuce ta gano shin da gaske Hamudan yake yi shi d’in ne yazo ko kuwa k’arya ne irin nasu..! Fitowarta dai² lokacin yayi dai² da k’arasowan baffa k’ofar d’akin nasu yana kwallawa Innarta kira

  “Mairo..! Kina ina ne..!?”

Baffan ya sake fad’a yana dudduba tsakar gidan,daga cikin d’akin ta Inna tayi masa gyaran murya alamun tana sallah kenan,jinjina kai yayi sannan ya juya ga Sabina dake tsaye sai sunkuyar da kai k’asa take

  “Yawwa uwata..! Maza zo ki samo ruwa mai d’an sanyi ki kaiwa MUHAMMADU..!”

  Cikin sauri ta d’ago ta kalli baffa,duk da da farko tunaninta ya gama tafiya ne akan Hamudan yayi mata k’arya,sai dai ko da jin sunan da baffan ya fad’a yanzun take ta fara jin nutsuwarta tana dawowa jikinta a 360,da hanzarinta ta amsawa baffan kafin ta juya cikin tsantsar murna ta koma d’akin,tsallen murna da doka kafin ta fara rawa tana yi tana dariya kamar wata sabon kamu,wanda jin fitowar Inna daga d’aki shi ne yasa ta dakatawa da dawar da take ta fara neman kofin da zata kai masa ruwan sannan ta fita daga d’akin,ko data fito kallo d’aya Inna tayi mata ta d’auke kanta daga gareta ta koma ciki tana girgiza kai,tabbas ba sai wani ya fito ya fad’a mata abunda ke faruwa ba a cikin y’an kwanakin,itama da kanta ta fara fuskantar damuwar y’ar tata,ba tare data ce mata komai ba ta juya ta koma cikin d’akin tunda ta fito bata ga baffan ba,ita kanta SABINA ganin irin kallon Inna ke yi mata sai daya sata shan jikin jikinta,amma to yaya ta iya..?? Idan har bata yi zumud’i da zuwansa ba mene ne ya kamata tayi..?? Wucewa ta sake yi ta kinkimo madaidaicin tray ta d’ora mug d’in akai,bayan ta kawo k’aramin cup ta d’ora ta nufi hanyar d’akin da yake cikin.

   Bakinta d’auke da sallama ta tsaya a k’ofar d’akin,,,shi kansa gogan tun daya zo gidan yake cike da son ganin ko da wucewar ta amma sai yaji shiru ko d’uriyarta bai babu sai yanzun da tayi sallama a bakin k’ofar shigowa d’akin,k’ayataccen murmushi ya saki kamar ance masa tana gani kafin ya amsa mata,,tsaiwa taci gaba da yi har kusan mintuna biyu kafin ta jiyo muryansa nan mai cike da nutsuwa yana amsa mata,sai dai yaji shiru tak’i shigowa dalilin da yasa shi maida idanunsa ga kallon hanyar da zata shigo d’in kenan nd cikin ransa yana ji kamar ya tashi ya janyota cikin d’akin tunda yaga bata da niyyar shigowa,,,ita kanta da take tsaye a gurin yanayin shirun data ji yayi bayan amsa sallamarta ba tare daya bata izinin shiga ba yasa nan da nan ta fara jin jikinta ya d’auki rawa,bayan a kullum tun daya tafi bata ganin shi take cikin damuwa,buh yanzun daya kasance yana kusa da ita nd take jin son ganinsa sai duk taji ta diririce tunma kafin suyi ido hud’u,da kyar ta samu ta saita nutsuwarta kafin ta kai hannunta ta d’age curtains d’in d’akin ta shiga tana sake yin sallama a ciki,,idanunsa kyar akanta tun data shigo har ta k’araso gabansa ba tare daya iya daina kallonta ba,duk da tana jin idanunsa akanta a hakan itama taci gaba da tafiyar,ko data zo dai² gabansa a hankali ta sunkuya tana niyyar ajiye tray d’in,a lokacin ne kuma  taji zuciyarta tana fad’a mata ta d’aga kai ta kalleshi

   “Shin yaya ya koma a cikin y’an kwanakin da bai zoba.?”

  Ta tambayi kanta,,duk da tana kissima yanda ya koma d’in a ranta  yanzun sai take jin kamar ya zartar yadda duk zuciyarta take sanar matan,dai² ta d’ago kai tana shirin kallonsa suka had’a ido da shi,cikin k’ank’anin lokaci tuni jikinta yaci gaba da rawa tamkar wacce aka jonawa shock,,sam bata kula da abunda take yi ba,sai muryansa data tsinto yana fad’in……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *