AMAL CHAPTER 6

AMAL



CHAPTER 6






Usman nufa d’akin yayi amma yaji a kulle, jin k’aran tana fasa abubuwa yasa ya fara buga kofar da sauri tare da kiran sunanta yana fad’in sadiya ki bud’e kofar

Amma ina ko sauraranshi batayi ba, sai k’ara jifa take ta kayan d’akin

Usman Jin yayi bugun duniya ta’ki ta bud’e kofar gashi yana jin k’aran tana fashe fashe yasa yama kofar wani mugun bugu ta balle

Tsayawa tayi turus yana kallonta gaba d’aya ta fashe show glass din dake d’akin tare da mirror d’inta da TV din dake manne a jikin bangon bedroom din

Kuka takeyi Sosai, ganin ya shigo yasa ta Fara k’okarin yin gaba Aiko tasa kafarta akan kwalba tuni ya fashe jini ya Fara fita, wani irin razanannan ihu ta saki

Da sauri usman ya nufeta tare da d’aukanta yayi d’akinshi da ita, inda ya kwantar da ita akan gadon d’akin, wajan kafarta ya nufa ya saka hannunshi ya fara cire mata kwalban dake kafarta

Bayan ya cire still jinin yana zuba, dan haka ya d’auko wata riganshi ya d’aura mata a wajan, jinin ya tsaya, ya daina zuba

Tashi yayi ya koma kusa da ita, tare da zama ya kura mata ido wacce hawaye ke zuba a cikin idonta

Sunanta ya kira da sadiya

Bata amsa ba sannan bata kalleshi ba

Bai damu da hakan ba, burinshi dai shine ta saurareshi

Yace sadiya ban taba tunanin haka daga gareki ba, da Farko Nayi tunanin zaki supporting d’ina a duk abunda na Kawo miki, zaki Mara min baya, sai gashi ba haka ba, Allah shine shaida bani da niyan kuntata miki ko kad’an, ban taba tunanin cutar dake ba, wannan Abun daya faru ban kwana dashi ba, ban San Zai faru ba, hasali ma naje ne taron biki, sai Abun ya canza, ina son ki sani ban taba tunanin cutar dake ba, sannan ina son ki d’auka komai ya faru daga Allah ne

Sadiya kuka takeyi Sosai, amma wannan maganan na Usman jinshi kawai take bawai tana sauraro ba, domin gaba d’aya zuciyarta tana fad’a mata Usman ba gaskiya yake fad’a mata ba, dan idonta ya rufe a wannan lokacin, tana bala’in son USMAN tare da kishin shi, zuciyarta wani irin zugi yake mata tare da rad’adi

Usman jin har yanzu tana kuka yasa ya d’agota tare da fad’in sadiya kibar wannan kukan dan Allah, kinga duk kin fasa abunda ke cikin d’akinki gashi Kinji ma kanki ciwo, kinki kibar wannan kukan kuma, plz ki bari haka, kanki zaiyi miki ciwo 

Cikin kuka tace ai komai ciwo yake min, wlh Usman komai dake jikina ciwo yake, wani zunubi na aikata haka? Da zan fuskanci wannan sakayyan, yau ko wata uku banyi ba amma ace har anyi min kishiya, taya jikina bazaiyi ciwo ba?? 

Usman jikina yana bani y’ar soyayyar da kake min zaka daina, yanzu shikenan na rasa ka……. Kuka yaci karfinta Sosai 

USMAN gaba d’aya tausayin sadiya ya kamashi Sosai, rungumota yayi Sosai jikinshi sannan ya fara fad’in sadiya bazan daina sonki ba, karki manta ni mijinki ne, sannan abunda mata bakwa ganewa shine idan namiji ya k’ara aure sai kuga kaman Wai baya sonku ne, which ba haka bane, namiji bazai zauna da macen da baya so ba, k’arin aure bashi bane Idan namiji yayi ba za’ace baya son Uwar gidansa ba, yana son matarshi kawai k’arin auren kaddara ne wanda Allah yasa dole saiya k’ara, kuma Allah ya rubuta mishi dole saiya ajiye mace fiye da d’aya 

Story continues below


Sadiya bazan taba wulakantaki dan Nayi aure ba, ina son ki san da hakan 

Zuciyar sadiya ta Fara sanyi daga rad’adin da takeji, domin jin kalaman Usman tasan Usman Indai ya fad’i abu Toh hakane, amma da yake shi kishi kumallon mata zuciyarta ta kasa yarda da wannan auren nashi 

Domin tana ganin Akwai abunda Alh Sulaiman yake nufi da Usman, dama ba’a Banza ba, wannan abubuwan da yake masa ashe y’arsa yake son bashi, Allah kad’ai yasan abunda zaice mishi gaba, tunda yaga usman din yana jin magananshi 

Usman jin tayi shuru yasa ya d’agota tare da kallon fuskanta yace tashi muje kiyi wanka kinji 

Bata Musa mishi ba, ta tashi Tana d’an dingishi domin ciwon dake kafarta 

Gefen su Amal kuwa, tunda ta shiga dak’i take kuka tare da tsanar duniya, Wai yau itace matar driver d’inta 

Lallai kaf duniya babu wanda aka taba tozartawa kaman ita, lallai USMAN ne ya shirya wannan Abun, domin tasan fahad yana Sonta, gashi usman din dama ya tsani fahad tun Farko, tashi tayi tsaye tare da fad’in tabbas shine yasa fahad yayi abunda ya aikata  koma ince sharri yayi mishi domin na tabbata fahad bazai taba gudu na ba, kalli irin dukiyar daya kashe min cikin akwati taya zai juya min baya, komai ya faru dasa hannun Usman…. 

Shigowan mahaifiyarta yasa ta kalli kofar d’akin 

Hjy Rabi tace Amal Ina fatan Kinji abunda mahaifinki yace, dan Allah kiyi hakuri kiji maganan mahaifinki, in baso kike ya fad’i ya mutu ba, kiyi biyayya, yau mahaifinki harda kuka saboda abunda fahad yayi mishi a bainan jama’a, wlh Amal Usman ya cancanci godiya domin inda badan yana jin maganan mahaifinki ba da sai dai wannan dubbannan Jama’an su watse domin babu ango 

Ya kamata kaman yanda Usman yayi ma mahaifinki biyayya, Kema hakan ya dace dake, domin wanda bai haifa ba yayi mishi biyayya keda ya haifa Kece za k’iki mishi?? 

Amal wani irin kuka ta saki mai cin rai 

Hjy Rabi tace maza kije kiyi wanka, kizo ki shirya domin tafiya dake gidanki 

Amal bata ce komai ba, sai nufa toilet da tayi ranta babu dad’i, lallai yau Gaba d’aya amal bata gane komai dake cikin wannan duniyar koda ta shiga toilet ruwa ta Saki a kanta, ta dade bata fito ba, jin haka hjy Rabi tazo tana Mata nocking akan tayi ta fito 

Jin bata fito ba har yanzu yasa hjy Rabi shiga cikin toilet din inda ta ganta ko kaya bata Cire ba, ta saki shower yana ta zuba a jikinta 

Hjy Rabi kai ta girgiza tare da kashe shower din, sannan ta Fara k’okarin cire mata kayan, Bayan ta cire mata, ta d’auko mata wasu Bayan ta d’aura mata towel sannan tasa mata kayan 

Gaba d’aya Amal bata iya komai, ita a halin da take ciki yanzu bata san inda kanta yake ba, domin gaba d’aya ita gadai ta nan ne 

Haka Hjy Rabi ta gama shiryata sannan ta feshe mata jiki dasu turare tare da body spray, sannan ta d’auko wani hijab cikin kayan Amal ta saka mata 

Amal hawaye ne ke zuba cikin idonta 

Karfe 8 dai dai aka fara shirin kai Amal gidanta, ba’a damu da tayi sallah ba, domin sanda hjy rabi ke cire kayan jikin Amal din taga pad cikin pant dinta alaman tana period 

Y’an uwan hjy rabi dana mahaifin Amal ne suka zo, domin tafiya da ita gidan mijinta wato Usman 

Amal ganin haka yasa ta Saki kuka mai sauti tare da kankame Hjy Rabi alaman bata son tafiya 

Hjy Rabi duk yanda taso ta dake ta kasa, itama sai da ta Fara kwallan 

Alh Sulaiman yana sama yana kallonsu 

Ango bai turo mota ba, domin bama sa bukata an d’auke Mai tunda bai San da auren ba 

Hjy Rabi ta Fara banbare Amal a jikinta domin ta shiga mota a tafi da ita gidan mijinta 

Jin hayaniya a bakin kofar gidan yasa hjy Rabi da da mutanan dake wajan yasa hankalinsu ya dawo wajan, inda hjy rabi tayi waje da sauri sauran mutanan suka Mara Mata baya suma 

Alh Sulaiman shima fitowa yayi domin yaga maike faruwa 

Koda su hjy rabi suka fita suka ga fad’a akeyi da tsohowan Dattijon dake musu gadi da kuma wasu mutane, wanda mace dana miji ne suke fad’a da Mai gadin, daga gani dai mata da miji ne 

Hjy Rabi tace lafiya maike faruwa?? 

Mai gadin yace hjy wai ihu suke akan dole sai Sun shiga sunga y’arsu Fatima.
M
Na fad’a musu babu Fatima a wannan gidan amma sunki yarda, wai dole sai Sun shiga 

Mutumin ya matso kusa da Hjy Rabi yana fad’in hjy Munzo muga y’armu dake cikin wannan gidan…… 

Dai dai lokacin Alh Sulaiman ya fito shida Amal 

Mutumin ya nufi amal yana fad’in Fatima. 

Itama matar dake tare dashi ta Fara fad’in Fatima, sai kuma ta saki kuka tana fad’in dama baki mutu ba, kina Raye?? 

Kuka take Sosai tare da nufan Amal tana k’okarin rungumota tana kuka 

Amal da sauri tayi baya tare da manne mahaifinta alaman tsoro bata son matar ta taba ta , 

Domin ganin matar tayi kaman wata mahaukaciya, Allah sarki ba hauka bane kawai tsabar talauci ne yasa Amal take Mata kallon mahaukaciya 

Alh Sulaiman kam gaba d’aya zufa ne ke keto masa, domin ya tabbata su mutanan basu sanshi ba amma shi yasan mutumin shekaru goma sha 17 da suka wuce domin bazai taba manta fuskan wannan mutumin ba….. 

Mutumin yace Fatima nine mahaifinki 

Hjy Rabi tace Kai malam hauka kayi ko me??  Akan wani dalili zaka dinga kira mana y’a da y’arka?? 

Mutumin yace Wlh wannan y’ata ce Fatima, duk inda zamu y’ata ce wacce ta rasu ashe ba mutuwa tayi ba sai kuma yasa kuka 

Gaba d’aya y’an uwan Alh Sulaiman da yan uwan hjy rabi Sun shiga rud’ani 

Uwa ub,  Amal din wacce gaba d’aya gabanta ke faman fad’i sosai, musmman da idonta ke kan matar da suke tare da mutumin inda taga matar tana Kama da ita Sosai 

Hjy Rabi tace Wlh ko Kubar nan ko insa ayi  muku duka…… 

Wata daga cikin y’ar Uwar Alh Sulaiman tace a’a nifa wannan Abun akwai alaman tambaya domin haka kawai bazai ce y’arshi bace, sannan jama’a ku kalla matar nan ku kalli Amal basa Kama?? 

Kowa shuru yayi yana kallon matar da Amal shi kam Alh Sulaiman kasa magana yayi 

Matar tace kinga saiki fad’i gskiya muji su Waye wa Innan mutanan 

Hjy Rabi tace Mai kike nufi?? 

Y’ar Uwar Alh Sulaiman tace abunda kike tunani, domin dai ga kama nan sak……. 

Alh Sulaiman ya daka mata tsawa tare da fad’in ki iya bakinki hjy rabi Bata san komai ba akan wannan Abun ba, dan uwanki ne mai laifi babba…….. 



Alh Sulaiman yace kuzo mu shiga ciki in fad’a muku komai, yau zan fad’i abunda na dad’e Ina boyewa wajan shekara da shekaru 

Yana fad’in haka yaja hannun amal sukai ciki, wacce jikinta gaba d’aya ya saki 

Gaba d’aya su hjy Rabi sun shiga cikin rud’ani tare da damuwa, domin gaba d’aya basu gane Mai yake nufi da abunda ya fad’a ba, dan haka suma suka bishi har cikin gidan 

Harda mutanan da suke kiran Amal da y’arsu suka shiga cikin gidan, inda gaba d’aya suka zauna a cikin babban falon gidan 

Amal kallon fuskan mutumin tayi inda ta tuna shine dai wannan tsohon Wanda ya kirata da y’arsa Sanda take zuwa skul 

Mutumin ne ya d’auko hoto yana nuna ma Alh Sulaiman yana fad’in ka ganta nan wlh y’armu ce Fatima wacce ta rasu 

Alh Sulaiman yace wannan ba Fatima bace y’ar uwarta ce 

Hjy Rabi tashi tayi tsaye da sauri Tana fad’in Mai kake fad’a haka??  Taya amal zata zama y’ar Uwar y’arsu Bayan bata had’a komai dasu ba, nice nan na haifeta bamu had’a komai d…… 

Alh Sulaiman ne ya dakatar da ita tare da fad’in hjy Rabi ki gafarce ni, sonki da kuma rashin son in rasaki yasa gaba d’aya na koma mai son zuciya, yasa na aikata babban zunubi na raba yarinya da iyayenta ba tare da sun sani ba, daga ni sai Dr muka San wannan Abun….. 

Amal gaba d’aya ji tayi dum dum cikin kanta, Mai Dad d’inta yake nufi??? 

Saboda tashin hankali da damuwa gaba d’aya ta kasa magana 

Dad din yaci gaba da fad’in in baki manta ba, lokacin da nayi accidents a lokacin aka gano kina d’auke da ciki, nayi farin ciki Sosai da wannan labarin 

Kwatsam sai Dr yazo min da mummunan labari akan accident din da Nayi na samu matsala akan bazan k’ara haiyuwa ba 

Inata ro’kan Allah wannan cikin dake jikinki Allah yasa ki haifa lafiya domin Ina matukar jin tsoran abunda zaisa in rasa wannan cikin dake jikinki 

Kuma wani ikon Allah sai gashi bai zube ba, harya isa lokacin haiyuwa, inda na’kuda ya kamaki, mukai asibitin shima a ranan wa Innan bayin Allah aka kawo wannan matar asibti Domin haiyuwa, Wanda wani mai mota ne ya bugeta shine ya kawota asibitin ita da mijinta Wanda a lokacin tare suka fita 

Koda suka zo a lokacin Dr yace bazai amshe suba, tunda ba’a nan suke Awo ba, kuma da duka alama zata haiyu ne 

Dakyar dai Dr din ya yarda ya amshi matar inda aka kaita d’akin theater domin aiki aka mata a lokacin 

Lokacin da kika haiyu kika haifi mace Yarinyar tazo da rai amma wajan gyarata yarinyar ta rasu a wajan nurse Kai tsaye waje tayi inda ta fad’ama Dr 

Story continues below


D’akin yazo ya duba yaga yarinyar ta koma  wato ta rasu, nan take yace a kawo yarinyar a dubata 

Kina kwance baki San yarinyar ta koma ba 

Koda Dr ya fito da yarinyar binshi nayi ina tambaya lafiya 

Nan ya fad’amin abunda ke faruwa, sannan yace bai Bari kin sani ba dan yasan irin condition d’inki domin  asibitin muke zuwa, yasan komai 

Hankalina ya tashi sosai tare da gudun kiji wannan mummunan Labarin 

Lokaci d’aya na kalli Dr nace tunda baki San yarinyar ta rasu ba, zanje Gidan marayu in d’auko miki yarinya tunda ana samun jarirai 

Nan Dr yace a’ah basai Naje ko ina ba, a nan zan samu 

Jana yayi mukai wani d’akin da babu kowa, inda yake shaida min matar da aka kawo anyi Mata aiki ta haifi y’an uku, zai d’auko d’aya ya bani domin yaga basu da hali sai a basu y’ar da kika haifa 

Ba tare da wani tunani ba na amince Dr yaje ya saka wata nurse tayi wannan aikin, inda aka d’auko yarinya d’aya a cikin y’arsu aka ajiye musu y’arki data rasu 

Inda kike ta murna kin haiyu lafiya, Abun yana damu na, ganin irin farin cikin da kikeyi yasa nima na saki tare da cire komai cikin rai na 

Haka aka sallamemu muka koma Gida 

Inata tunanin in nemi mutanan in taimaka musu, amma dana koma hspt din suma akace an sallamesu, tun daga lokacin na cire Abun inda tsoran kar wata rana Asirin ya fasu yasa nace mubar garin Kano mu dawo abuja 

Nasan bani na haifi Amal Ba, Nasan bata da gado na, sai yasa na rubuta komai wajan barrister d’ina kona mutu wanda shine mutum na uku da yasan Amal ba y’ata bace 

Na d’auki kud’i na bata just to see her happy, ina Mata duk abunda takeso domin Ina matukar jin tausayinta domin na rabata da iyayenta da suka haifeta….. 

Shuru yayi wani hawaye mai zafi yana k’okarin fita daga idonshi amma yasa hannu da sauri ya kare hawayen domin bai son ya zubo 

Amal kam gaba d’aya tunda taji wannan Labarin  taji komai ya tsaya Mata cak….. 

Alh Sulaiman ya kalli iyayen Amal yace bawan Allah dan Allah ka yafe min Nasan na cutar daku wlh 

Mahaifin Amal yace Alhmdlh Alhmdlh na gode Allah, tun sanda matata ta haiyu bata K’ara haiyuwa ba, koda Dr yazo yaga yaran ya cire daya yace ta mutu, haka aka sallamemu 

Muka koma Gida, aka birne d’ayan, ya rage saura guda biyu har Akayi suna inda yaran sukaci sunan Fatima da hauwa, Bayan suna da sati d’aya hauwa ta rasu 

Haka mukai ta renon Fatima harta girma inda ta Fara karatu, Fatima yarinya ce mai biyayya ga ilimi Da sanin ya kamata, ga hakuri, bikinta ya rage wata d’aya Allah ya d’auki rayuwarta, hankalin Mai d’akina ya tashi haka dai muka d’auki kaddara, da yake ni bana zama waje d’aya tunda Sana’a ta inayin abunda yazo lokacin Ma’ana in lokacin yalo ne shi zan siyar, in lokacin gwaiba ne shi zan siyar, in lokacin rake ne shi zan siyar 

Nazo garin habuja inda iyalina take zaune a Kano tunda bamu da halin kama gida a nan, ina zuwa makaranta makaranta da kasuwa, ranan naje makaranta sai naga wannan yarinyar sak Fatima inda nake kiranta da Fatima Ashe ba fati na bace itama wannan y’ata ce, sai kuma ya fashe da kuka yana fad’in Allahu Akbar Allah babu yanda bayayi mun Cire rai da samun haiyuwa, domin mun manyanta, sai gashi ashe muna da wata y’ar Allah Mai iko 

Alh Sulaiman yace hakane, lallai haiyuwa tana da dad’i wanda Nima gashi saboda rashinta yasa na rabaku da y’arku gashi yanzu zata barni…… 

Gaba d’aya Amal kasa magana tayi amma zuciyarta wani irin bugu take Mata, yanzu dama ita ba y’ar Alh Sulaiman Bace, dama basu bane iyayenta ba, wa Innan ne iyayenta….. 

Hjy Rabi kuka ta saki Tana fad’in yanzu dama y’ar dana haifa bata zo da rai ba??  Innalillahi’wa inna ilaihirajiun Mai yasa ka boyemin, ko kasan wannan Abun yafi min ciwo akan rashin fad’amin da kayi, yau gashi y’ar da nake kallo y’ata na dauki son duniya na d’aura mata, ashe ba y’ata bace, na bata nono na tasha, na Mata komai na rayuwa a matsayin d’iyar dana haifa, ashe ba y’ata bace Wlh zuciyata baka ji yanda nake jiba, ko kasan yanda nake jin Amal kuwa?? Y……  Sai kuma ta saki kuka cikin kunan rai, lallai mijinta bai taba bakanta mata rai irin wannan abunda yayi ba, duk da yace saboda ita yayi amma hakan da yayi  yafi mata komai muni da d’aci,  zaifi mata dad’i da sau’ki ace ya fad’a mata tun Farko y’arta bata zo da rai ba, akan wannan Abun, yanzu gashi tana kallon Amal tasan dole iyayenta zata zaba akanta 

Alh Sulaiman ya fara fad’in hjy Rabi kiyi hakuri Wlh Nayi hakan ne saboda farin cikin ki badan komai ba 

Gaba d’aya kowa dake falon ya tausayawa ma halinda da Hjy Rabi ta shiga 

Ita kam Amal gaba d’aya kunnanta a doshe yake yanzu, domin ta kasa gane komai dake mata dad’i, lallai duniya yau ta juya mata yanzu wa Innan mutanan wanda ita harga Allah tasha matar hauka take yanzu sune iyayenta, gaba d’aya jinta take wani iri, wanda sai yanzu ta k’ara ganin mugun kamanta da matar wanda inda za’a Mata gyara wani zai d’auka Amal dince 

Mahaifin Amal yace hjy karki damu, bazamu rabaki da Amal ba, domin daku ta saba, bada mu ba, gashi ance yau aka d’aura mata aure, kunga ba zama zatayi damu ba, gashi mu mutanan Niger ne zama muke a Nigeria yanzu dole zamu koma Niger amma ina neman alfarman muje tare da ita Amal din…… Shuru yayi yana tunani lallai yasan in suka koma Niger akwai babban Abu inya had’u da zuri’arsa Wanda suka gudu wajan shekara ishirin da biyar basu sake waiwaya k’asar ba sai a wannan karan , amma komai zasu Tarar dole su koma kodan su nemi gafara daga iyayensu akan babban laifin da suka aikata….. 

Alh Sulaiman ne ya katse mishi tunani da fad’in karka damu zaku je tare Nasan mijinta zai amince, bari in kira Usman din yazo ma 

Nan take Alh Sulaiman ya doka ma usman kira 

Usman wanda yake ta rarrashin sadiya saiga kiran Alh Sulaiman ya shigo wanda yasa dole ya tashi ya fita sannan ya d’auka 

Sadiya ganin haka yasa ta tabbar ma kanta Amal ce ta kirashi….. 

Tana cikin wannan tunanin saiga usman yazo yana fad’in zai fita yaje ya dawo 

Sadiya kuka ta saki Sosai, ganin haka yasa ya fita domin yaga kaman bata jin rarrashi 

Kai tsaye gidan Alh Sulaiman ya nufa, koda yaje shiga yayi inda ya iskesu a falo, idonshi sauka yayi akan Amal wacce take kallon k’asa, lokaci d’aya ya kawar dakai tare da gaida mutanan dake cikin falon 

Alh Sulaiman ya kira Sunan USMAN tare da fad’in zauna mana 

Zama Usman yayi inda Alh Sulaiman ya fad’a mishi komai 

Gaba d’aya Usman shima ya shiga cikin rud’ani da wannan Abun, dama Amal ba y’ar Alh Sulaiman bace?  Ikon Allah 

Usman yace babu damuwa, zasu iya tafiya Da Amal din……… 


Amal wani hawaye Mai zafi ne ya zubo daga idonta lokaci d’aya ta tashi Tana k’okarin barin wajan amma jiri ya d’ibeta ta fad’i k’asa luuuuuuu tim 

Da sauri suka nufeta cikin tashin hankali, usman ya riga kowa zuwa wajan inda ya fara Girgizata amma ina bata ko motsi 

Nan mahaifinta na gaskiya yace Suma tayi a d’auko ruwa 

Da sauri wata daga cikin y’an uwan Alh Sulaiman suka nufi kitchen sai gasu Da Ruwa inda aka yayyafa mata tayi firgit ta tashi cikin tsoro Tana kallon su, lokaci d’aya kuma ta fashe da kuka tana kallon hjy Rabi tana fad’in mum dama bake kika haifeni ba??  Ko mafarki Nayi?? 

Hjy Rabi itama kukan ta kuma saki cikin tausayin Amal din, inda ta kamo hannunta tana fad’in Amal….  Sai kuma tayi shuru kuka yaci karfinta sosai 

Amal idonta ya sauka akan matar da itace mahaifiyarta, da sauri ta lumshe ido, zuciyarta na Mata wani iri, atamfa matar tasa amma duk ya kod’e, alaman tasha ruwa, shiko mahaifin Nata wani kodaddan Yadi ne a jikinsa, hawaye ne yake zuba a idonta, yanzu wa Innan ne iyayenta?? 

Matar da take mahaifiyar Amal ta fara ma mijinta magana da French inda shima ya fara bata amsa da duka alamu dai suna magana ne akan Amal din domin Suna kiran sunanta 

Bayan sun gama magana mahaifin Amal ya kalli Alh Sulaiman tare da fad’in munyi magana bai kamata muje da ita ba yanzu, gashi yau akayi aurenta, kawai a kaita d’akin mijinta, mu zamu tafi Idan muka je zamu dawo 

Nan Alh Sulaiman yace babu damuwa duk yanda suka tsara hakan yayi 

Tafiya sukace za suyi inda Alh Sulaiman yace su kwanta a gidan, da safe sai su tafi, hakan koh ta faru inda aka kaisu wani d’aki 

Ita kuma Amal Alh Sulaiman da kanshi yace zai kaita d’akin  mijinta, kuka Amal take Sosai cikin tashin hankali haka Alh Sulaiman ya tafi da ita 

USMAN shida kanshi ya wuce inda ya nufi gidan shima 

A tare suka k’arasa gidan, Dan haka suka shiga cikin gidan kai tsaye 

Amal tana manne jikin mahaifinta Tana kuka wanda shima Alh Sulaiman dauriya kawai yake domin shi d’aya yasan abunda yake ji, dan kirjinshi ji yake kaman zai fito Dan azaba 

Haka dai suka shiga Bayan sun shiga suka zauna, gidan amsa komai a cikin sa, kuma gidan yana da girma 

Nan Alh Sulaiman ya fara magana kaman haka, Usman ina son ka ri’ke Amal tsakani da Allah, sannan ka zama Mai adalci tsakanin matanka biyu, karka zama d’aya daga cikin maza azzalumai marasa adalci 

Nan dai yaita ma Usman nasiha Mai ratsa jiki Wanda yana maganan ne dakyar 

Kallon Amal yayi sannan yace Amal Kema ki zama mace Mai biyayya domin Aljannanki tana karkashin kafar mijinki, sannan ki sani aure ba wasa bane, sannan komai kika ma mijinki yaji dad’i zaki samu lada, ina son ki sama ranki bauta kikeyi Kinji??  Dan Allah karki bani kunya kinji Amal 

Amal bata ce komai ba sai kuka da takeyi haka Alh Sulaiman yaita musu nasiha sannan ya musu sallama inda Usman ya fita rakashi 

Bayan Alh Sulaiman ya tafi koda Usman ya dawo a falon ya tarar da Amal tana ta kuka wani irin son Amal dinne yake fusganshi tare dajin tausayinta Sosai 

Story continues below


Yana son yaje ya rarrasheta Amma zuciyarshi tana k’okarin hanashi, kwakwalwanshi kuma na fad’in yaje ya rarrasheta, watsi yayi da maganan zuciyarshi inda ya d’auki na kwakwalwanshi ya nufeta tare da zama kusa da ita yana fad’in Amal dan Allah kibar wannan kukan…. 

Bata kulashi ba haka bata bar kukan ba, 

Usman yace Amal Ina son ki sani komai na duniya jarabawa ne, sannan komai ya faru da bawa kaddara ne, kuma babu Mai kaucewa kaddaran shi, ina son kibar wannan kukan…… 

Tashi tsaye tayi tare da watsa mishi wani irin tsinannan kallo sannan tace Kai har kana da bakin fad’amin magana, karka manta koni wacece yau koda ba Dad bane ya haifeni kayi aiki a karkashina Wlh bazan taba Sonka ba, zan zauna dakai ne saboda mahaifina domin naga hakan kawai zanyi yasa yayi farin ciki, kaine ka shirya komai, kaine kasa fahad bai aureni ba 

I hate you Usman I hate you, ina son ka sani zan zauna dakai amma zuciyata bata tare dakai domin fahad nake so har gobe ba Kai ba, kayi nasara ka aureni amma baka da iko dani W…… 

Jiri ya d’ibeta ta fad’i da sauri ya tarota ta fad’o jikinsa 

Idonta na kanshi shima nashi yana kan nata, suna kallon juna, a hankali ya fara fad’in Amal ban taba tunanin saminki a rayuwa ba, Nasan kinfi karfina sannan ina son ki sani bani na nemi aurenki ba, mahaifinki ya bani, Kinga ban San komai ba, ki daina zargina akan laifin da ban aikata ba…. 

Ido ta lumshe tana ri’ke a jikinsa 

Lokaci d’aya ya d’agota ya tsayar da ita dakyau still dai bai saketa ba, yana kallon kyakyawan fuskanta, Amal tana da kyau ga dan k’aramin bakinta wanda mutum zai iya rantsewa bazata aikata abunda takeyi ba 

Lokaci d’aya ta bud’e ido wanda suka sauka akan na Usman, wani irin Abu taji Domin ji tayi bata san kallon idon nashi dan gabanta taji yana fad’i 

Lokaci d’aya ta tureshi tare dayin baya tana fad’in who give you the right….. How dare you…. Shuru tayi sannan taci gaba da fad’in who give you the right to touch me?? 

Karka k’ara tunanin tabani har Abada, domin namiji Kazami irinka bai Isa ya taba jikin Amal ba 

Nufanta ya farayi ta Fara yin baya harta manne da jikin bango 

Hannunshi biyu yasa ya kare bangon ta yanda bazata iya barin wajan ba 

Sannan ya fara magana, Idan zan taba jikinki bana bukatar izini daga wajan kowa, haka bana bukatar tambayan kowa, because you are my wife….. 

Ido ta lumshe da sauri Tana takaici 

Yaci gaba da fad’in even me nayi accepting d’inki saboda mahaifinki, badan ina sonki ba….. 

Ido ta bud’e wanda ya sauka akan nashi 

Tana k’okarin juyar da kanta yasa hannunshi ya juyo Mata da fuskan tare da fad’in just think once in your life Mai yasa lokaci d’aya abubuwa suka canza….. 

Yana fad’in haka ya barta tare da bud’e d’akunan ya shiga guda d’aya domin ya kwanta, harya shiga ya tuna kayanshi a mota dole ya k’ara fita still tana falon a tsaye yanda ya barta, koda ya fito Bai kulata ba, direct waje yayi ya d’auko kayansa sannan ya dawo d’akin 

Amal jiki a sanyaye ta bud’e d’akin dake kusa dashi ta shiga inda tana shiga ta saka key tare da fashewa da kuka lallai abubuwa sun canza mata gaba d’aya 

ita bata jin komai akan iyayenta, kaman auren Usman, bata son wannan auren kaman yanda bata son mutuwarta lallai usman yana da saka hannu wajan fasa aurenta da fahad, domin tasan Usman ya tsani fahad…. 

Wayanta ta Fara dubawa, lokaci d’aya kuma ta saki kuka tunawa da tayi wayar tata tana gida, bata tawo dashi ba 

Kanta ciwo yake mata Sosai, ga yunwa tana ji kaman cikinta zai fita, sai yasa take ta jin jiri saboda yunwa 

Shiko ta gefen Usman ya rasa wani irin so yake ma Amal haka, yarinyar da bata ganin kimarsa da darajan shi, amma gashi ya mutu akanta  ido ya lumshe yana tunanin abubuwa da dama, koya zamansu zai kasance oho 

Washe gari da safe Amal bata fito ba har wajan karfe 10 USMAN d’akinta ya nufa ya fara Mata nocking 

Tana ji tayi banza dashi ta’ki tashi ta bud’e, ga yunwa Tana ji amma saboda isa irin Nata tak’i tashi ta bud’e Mai kofar 

Jin ta’ki bud’e kofar yasa yace ki bud’e an Aiko miki da sa’ko 

Jin haka yasa ta tashi ta bud’e kofar ta fito 

Kallonta yayi fuskanta duk ya kumbura saboda kuka, idonta ya shige ya kankance saboda tasha kuka 

Ita kam wani irin kallon tsana take mishi hango kayanta tayi cikin akwati da sauri ta nufi wajan domin tana bukatar canza kaya 

D’aukan wani akwati tayi ta nufi d’akinta Jim kad’an sai gata ta fito ga duka Alamu wanka tayi ta canza kayan jikinta, abincin da aka Aiko musu ta d’auka ta Fara ci 

USMAN na zaune yana kallonta baice komai ba, lokaci d’aya ya fara danna wayarshi 

Amal wani irin mugun harara ta sakar mishi, wai yanzu shine mijinta, ko ina fahad yake oho 

Usman na zaune yana danna wayarshi aka turo mishi message na wani aiki da Alh Sulaiman yasa dole ya nema akin a NNPC ne sai gashi an turo mishi message akan ya samu aikin 

Usman wani irin murmushi yayi tare da godema Allah, lallai Allah yana sonshi, tashi yayi tare da kallon Amal yace zan fita Mai kike bukata in kawo miki 

Banza dashi tayi ganin haka yasa yayi gaba abunsa har yakai ba’kin kofa tace wait….. 

Tsayawa yayi tare da waigowa yace inaji 

Shuru tayi na wani lokaci sannan tace ina son phone d’ina, shi nakeso a kawo min a gida 

Bai bata amsa ba ya fita, wani irin Abu taji ya tsaya Mata a wuya, tare da fad’in mai yake nufi Toh…. 

Tana cikin wannan tunanin sai gashi ya dawo, 

Kallonshi ta tsayayi harya k’araso gabanta sannan yace Amal get ready muje ki gaisa da iyayenki 

Da sauri ta Fara k’okarin shiga dak’i, hannunta ya ru’ko tare da fad’in just 5 minute na baki, yana fad’in  haka ya saketa 

Haka ta shiga cikin d’akin rai a bace domin bata son taba mata jiki da yakeyi ko kad’an 

Bata dad’eba sai gata ta shirya cikin wata doguwar riga Yar kanti, tare da saka wata hula akanta 

Kallonta Usman yayi sama da k’asa sannan yace wannan dressing dinfa?? 

Kaman kar tayi magana sai kuma tace na shirya 

Murmushi yayi wanda ya k’ara Mai Kyau, yace a haka?? 

Cikin isa tace eh 

Hannunta yaja sukai d’akinta inda suna shiga ya saketa tare da bud’e wardrobe d’inta yaga babu wasu kaya, kai tsaye falo ya nufa inda ya fara shigo mata da akwatinta saida Ya gama shigo mata dasu duka sannan ya fara bud’ewa, saiga wayarta cikin akwati ansa Mata, da sauri ta nufi akwatin zata d’auka wanda shima USMAN yakai hannu zai d’auka Aiko sukai caraf hannunsu ya had’e 

Da sauri ta kalleshi shima ita yake kallo cikin so da k’auna, sai dai ita ban San wani irin kallo take mishi ba 

Sun d’auki lokaci Mai tsawo a haka, kafin ta cire hannunta daga nashi tare da komawa baya tana kallonshi 

Ido ya lumshe lokaci d’aya kuma ya bud’e tare da d’auko wayarta ya bata 

Amsa tayi ba tare data kalleshi ba 

Ciro mata wani doguwar rigan atamfa yayi tare da wani hijab yace tasa 

Kallonshi tayi tace wannan kayan zan sa??  Murmushi ta saki tare da fad’in never babu wanda ya isa yasa Inyi abunda Banyi niya ba…. 

Nufanta yayi gabanta ya fara fad’i ganin yana nufota 

Har inda take yaje tare da fadin gashi kisa na baki minti uku in baki fito tare da kayan ba zan tafi…. 

Yana fad’in haka ya fita yabar mata d’akin yana dan murmushi 

Wani irin tsaki ta saki tare da furta Kalman I hate you wai yau ita yake bama umarni……  Wani irin kuka ta saki mai cin rai, lallai ya kamata ta d’auki mataki tun Kafin Lokaci ya k’ure Mata……



Bayan ta gama kukan tasa ta shiga toilet ta wanke fuskanta, sannan ta fito tasa rigan 

Bayan ta gama shiryawa ta fito jikinta sai kamshi ke tashi, tunda ta fito yake kallonta amma ta gefen ido, yana son Amal sosai 

Bata kulashi ba, shima bai damu da hakan ba, ya tashi ya fita, itama binshi tayi a baya bayan ta sakar mishi wani irin harara ta baya, lol Amal manya wannan shi ake kira harara a cikin duhu, tunda kinyi bai gani ba 

A mota ta iskeshi ya shiga yana jiranta 

Bayan motar ta nufa zata bud’e 

Ganin haka yasa yayi luck din motar ta baya, ido ta lumshe tare da cije lebe, lokaci d’aya kuma tayi tsaki tare da fad’in mai yake nufi?? 

Gaban motar tayi inda ta bud’e ta kalleshi tare da fad’in ka bud’emin baya in shiga 

Bai ko kalleta ba, idonshi na kan wayarshi yace am not your driver now, tunda ba salary zaki bani ba, and wannan mota nane not yours 

Amal wani irin Abu taji ya tsaya Mata a wuya dan ba’kin ciki, haka dole ta zauna a gaba, tare da tamke fuska….. 

Kai tsaye gidansu ya nufa inda ya tsaya a bakin gate ya kalli Amal tare da fad’in anjima in nazo daukanki Zan shigo 

Amal bata kulashi ba, sai bud’e motar da tayi ta shiga cikin gidan kai tsaye 

Shi kam usman Kai ya girgiza tare da fad’in ko yaushe zata canza daga wannan halin Nata oho, motarshi yaja Domin zuwa gidan sadiya 

Koda Amal ta shiga gida a falo ta iske iyayenta da Mum suna zaune suna fira kaman Sun saba 

Amal fuskanta babu yabo babu fallasa ta k’arasa falon sai dai idonta nakan iyayenta, zama tayi kusa da Mum tare da lumshe ido 

Mum tace lafiya?? 

Ido ta bud’e tare da fad’in Ina kwana Mum? 

Bayan Mum ta amsa 

Sannan ta kalli iyayenta ta gaidasu 

Suka amsa cikin fara’a 

Amal ta kuma kallon Mum tace shiya saukeni inzo in gaidaku 

Mum tayi murmushi tare da fad’in ai yau budan Kai, harda gidansu zaki, ki gaida mahaifiyarshi 

Amal bata fuska tayi domin ita kaf duniya babu wanda bata so kaman Usman musamman da take ganin shine yasa fahad bai aureta ba 

Ita yanzu bata jin komai akan iyayenta domin tasan babu yanda ta iya sune suka haifeta 

Hmm rayuwa kenan, lallai Allah shine mai badawa Mai kuma amsa, yau Ina dukiyar Alh Sulaiman wanda yana d’aya daga cikin masu jerin kud’in Africa amma yau an Wayi gari ya koma babu abun, waye zai taba kawo wannan dukiyar tashi zata k’are ba, Allah kenan babu yanda bayayi, saiya kwace Abu daga hannun wani yaba wani 

Gadai mahaifin Amal wanda take ganin bazai taba talaucewa ba, domin yana da mugun kud’i sai gashi Allah ya nuna mata 

Amal tashi tayi ta haura Sama inda d’akinta na gidan yake, dialing din number din fahad tayi taji switch off, mamaki abun ya bata haka taita kira taji akashe dole hakura tayi badan taso ba 

Story continues below


Gin yunwa yana damunta sosai yasa ta fito inda ta iske harda Alh Sulaiman a falon gaidashi tayi cikin girmama 

Murmushi yayi tare da fad’in ina usman din??.. 

Wani iri taji cikin ranta amma saita daure tace yace anjima Idan yazo d’aukana zai shigo 

Alh Sulaiman yace Allah ya kaimu, 

Amal ta amsa da Ameen tana d’an Satan kallon Alh Sulaiman wanda taga ya rame sosai har dan duhu saida yayi 

Gaba d’aya tausayin mahaifin Nata take Sosai, tasan ba komai yasa shi cikin wannan halin ba sai na rashin dukiyar da yayi wanda ba kowa zai iya dauriyan da shi mahaifin Nata yayi ba, wani hawaye ne taji ya zubo mata wanda tayi sauri ta goge domin kar a gani….. 

Amma ina lokaci ya k’ure, domin mahaifin Nata ya gani Alh Sulaiman  yace Amal lafiya kike hawaye?? 

Tambayan da yayi mata kaman yace ta saki kuka, Aiko ta Fara kuka Sosai gaba d’aya kallonta suke cikin mamaki 

Lokaci d’aya ta nufi Alh Sulaiman tana fad’in Dad kayi min komai a rayuwa, duk da kasan niba y’arka bace Ta cikin ka, Wlh Ina ji kaman saboda irin halina Allah ya jarabce ka S……. 

Alh Sulaiman yace Subhanallah Karki k’ara fadin haka Kinji?? 

Bakya nan sanda na k’ulla yarjejeni da mutanan da suka damfareni dan haka karki k’ara Dan ganta kanki da wannan Abun kinji?? 

Amal hawaye take Sosai cikin kuka tace Dad mai zan maka a rayuwa kaji dad’i wanda zan biyaka saboda irin soyayar daka nuna min?? 

Alh Sulaiman yayi murmushi wanda yasa hannunshi ya rufe idonshi domin wani hawaye yaji yana son zubo mishi 

Bayan ya cire hannunshi daga fuska ya kalli Amal yace Amal Abu d’aya zaki min in kasance Ina alfahari dake koda yaushe, shine ki zauna da mijinki lafiya, kiyi mishi biyayya, ban son inji kinyi wani abu da zaki saka mijinki cikin kunci, Amal Ina miki wannan maganan ne a matsayina na mahaifinki Mai son ganin farin cikin ki, wlh Amal na tabbata Usman bazai bari kiyi kuka ba, domin shine wanda ya dace dake 

Ina miki wannan maganan ne domin ganin yanda kike ma Usman a baya, yanzu Ina Son ki sani yanzu da, dah ba d’aya bane, inda kina kallonshi a matsayin maiyi miki bauta, kina biyanshi Toh yanzu kid’a ya canza ya dawo mijinki 

Sannan aljannanki yana k’arkashin k’afar mijinki, wlh Idan kika saba ma mijinki ko kika cutar dashi Allah bazai barki ba 

Amal wannan kad’ai nake so Kimin a rayuwa, ki ri’ke mijinki hannu bibbiyu 

Amal da tunda mahaifin Nata ya Fara magana tayi shuru tana hawaye, lallai mahaifinta yana son wannan Usman din da yawa, a hankali ta furta Kalman dad zanyi duk abunda kace 

Alh Sulaiman murmushi yayi tare da furta Kalman Allah yayi miki albarka, yasa yanda kika faranta min Kema in kin haifa a faranta miki 

Amal hawaye take sharewa Tana amsawa da Ameen cikin ranta 

Gaba d’aya taji jikinta yayi sanyi ga maganan mahaifinta, lallai dole taji magananshi musamman yanzu da taga ita da Usman din babu Ban banci, Toh sai dai abu d’aya taya zata amshe shi a matsayin miji???  Wannan ne babban abunda take gani shine Tashin hankali a gareta 

USMAN kam direct gidan sadiya ya nufa, inda ya ganta fuska duk a kumbure alaman taci kuka harta gode Allah, wani irin azababban kishin usman take Sosai, wanda take ganin zata iya aikata komai akan shi, Domin tasa ma ranta ita d’aya ce matarshi, Toh amma sai dai a yanzu tana k’okarin ta boye kishinta amma ta kasa domin kuka ta kuma saki data ganshi ya shigo, domin sai take ganin kaman an kwace mata shi, tunda tace Alh Sulaiman ya mallake shi sai abunda yace USMAN din yakeyi 

Shi kam usman tausayin sadiya yakeyi domin yasan tabbas ko wacece a matsayinta zatayi hakan koma tayi abunda yafi hakan, shi ya maga hakurinta sosai, bai fita da niyan auren wata ba, sai gashi ya dawo mata da zancen auren wata, Usman nufanta yayi yana fad’in haba sadiya miye amfanin wannan kukan da kikeyi yanzu??.. 

Aikin rarrashi ya fara tare da fad’a  mata magana masu dad’i wanda yasa zuciyarta ta d’anji sanyi sanyi, amma ba Sosai ba,  domin tana matukar kishin mijinta sosai 

Kaman yanda hjy Rabi tace hakan ko akayi k’arfe biyu aka shirya kayan su cin cin dasu dai kayan gara, yanda al’ada ya tsara 

Hjy Rabi kiran Usamn tayi ta shaida mishi za’a kawo Amal gidan mahaifiyarshi, sannan za’a kawo ta gidan matarshi ma 

Usman yace Toh, 

Hjy Rabi tace sai dai ba’a San gidajen ba.. 

Usman yace zai turo, Bayan ya gama waya ya kalli sadiya wacce fuska ke tamke, domin tana jiyo maganan da ake fad’a mishi 

Murmushi yayi tare da fad’in sadiya sai kinyi hakuri, ina son ki sani komai na duniya hakuri ne, dan haka ki tashi ki shirya kar suzo suga irin halinda kike ciki.. 

Sadiya bata ce komai ba, lokaci kad’an kuma ta tashi, ta kalli Usman Tana fad’in yaushe zasu zo?? 

Yace Nasan yanzu, ni Bari in fita za muyi magana, kud’i ya ciro ya bata tare da mata peck kiss a goshi yace plz ki shirya saiki kira friends d’inki Kinji Uwar gida.. 

Murmushi tayi tare da fad’in Toh, fita Usman yayi sadiya ta d’auki waya domin kiran kawayenta guda biyu ta kira, domin suzo su tayata tarban Amarya 

Usman ya tura wani yaro, inda ya nuna masu Amal gidansu mahaifiyar USMAN 

Y’an uwan Alh Sulaiman da na hjy Rabi ne suka rako Amal, mata uku, sai Amaryan su hud’u 

Mahaifiyar USMAN ta tarbesu ita da y’an uwanta cikin mutunci da girmamawa, inda Amal fuskanta ke rufe da gyale amma tana ganin komai,  gaida mutanan falon tayi 

Suka amsa, Amal cikin ranta tace mahaifiyar USMAN kaman ba ita ta haifeshi ba, domin taganta kaman ba wata babba ba, duk da kuwa basu da hali a baya amma jikinta Mai Kyau, Amal ta gane mahaifiyar usman domin ganin kamansu sak, inda kanwar alh Sulaiman ta tambaya Ina Maman ango??  Matar dai da Amal take tunani itace din dai, Bayan an gama shigo da kayan gara na iyayen ango suka musu sallama inda aka bama Amal tukwicin dubu ishirin 

Kai tsaye gidan Uwar gida aka nufa, inda Amal dai shiga tayi amma tana tunanin koya matar zata tarbesu, amma abun mamaki sai gashi ta amshesu hannu bibbiyu ita da kawayenta, itama an bata kayansu soye soye  inda taba Amal atamfa dasu hijab Kala biyu 

Nan suka tafi, inda y’an uwan Amal suke fad’in kai Amma matarshi tana da kirki Kalli yanda ta tarbemu hannu bibbiyu 

Haka dai suka koma Gida, inda suka bama hjy Rabi labarin abunda ya faru 

Iyayen Amal sun so, tafiya yau, Alh Sulaiman yace su Bari gobe hakan suka hakura badan sun soba.. 

Hjy Rabi ta kalli Amal tace kije kima iyayenki sallama domin gobe zasu tafi, Niger kuma zasu wuce 

Amal jiki a sanyaye tayi d’akin iyayen Nata, inda ta samu mahaifiyarta ita d’aya tana zaune 

Amal kallonta tayi lokaci d’aya taji k’aunar mahaifiyar Nata a cikin ranta, Hmmm Anya Amal ce kuwa??  Koda yake uwa uwa ce koda kuwa a bola take kwana, duk iskancin mutum yana kaunar mahaifiyarshi so ina tunanin itama hakan ne ta gefen Amal 

Zama amal tayi kusa da mahaifiyar tata, bayan ta furta mata Kalman Barka da hutawa, cikin muryanta dake dashe kaman tana mura, amma ba mura bane tsabar kukan da tasha ne 

Mahaifiyar tata ta amsa da yauwa cikin sakin fuska tare da fad’in Amal har kun dawo?? 

Amal tace eh mun dawo 

Mahaifiyar tata cikin jin dad’i take fad’in sannu 

Amal Dan shuru tayi sannan tace yauwa mama ban San labarinki ba, harta su Mum basu sani ba ,domin gaba d’aya kowa baya cikin hayyacinshi….. 

Wani guntun hawaye ne ya zubo daga fuskan matar tare da fad’in labari na, ba Abu bane Wanda zanji dad’in fad’anshi, mun aikata kuskure tsawon lokaci Mai Nisa Wanda lokacin ba muyi tunanin y’ay’an da zamu haifa za suso Susan labarin mu ba, sai daga baya, Bayan lokaci ya k’ure mana……… 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *