AUREN FANSA CHAPTER 5 BY ✍🏾 NIMCYLUV

AUREN FANSA CHAPTER 5 BY ✍🏾 NIMCYLUV

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kallon yadda jikinta ya saki Ya Heemu yay ga kuma jinin dake zuba daga jikinta, bai tsaya jiran komai ba ya Miƙe da ita a jikinsa kai tsaye ya nufi hanyar fita daga shashin nata, yana gab da fita daga babban Parlo yaci karo da Anut Lubna kallonsa tayi da mmki tace “Ya Heemu me kuma ya samu mahaifiyar taku?” Da gajiyayyun idanunsa kawai ya kalleta ba tare da yace komai ba sanin ba lallai yay mata mgn yasa tace.

“Ok barta a nan bari na kira Family Dr namu”

Fararen idanunsa ya juya ya kalli Anut Lubna dasu kana ya kalli Mannal dake jikinsa sai kawai ya fice da ita da sauri ba tare daya aikata abinda Anut Lubna tace ba.

Yana fita Excorts suka miƙe kallo guda yay masu suka ja baya tare da bashi waje, da kansa ya sanya (Mumy) a baya kana ya amshi key car da wani irin speed yaja motar tare da barin gidan gaba ɗaya.

*Aminu teaching hospital*

A nan yay parking nurses da yawa suka zagaye motar sa tare da gadon marasa lafiya, yana tsaye yana lumshe idanunsa tare da fesar da iska daga cikin bakinsa time to time hakan shafa lafaffan cikinsa, yana kallo har suka nufi Emergency room da ita.

Cikin nutsuwa da kamala ya juya zai shiga reception wanda daga nan zai ƙarasa emergency room ɗin da aka nufi Mumy dashi yaji hayaniyar mutane, tsayawa yay cak tare da juyawa a hankali ƙara ware manyan idanunsa yay sbd wanda ya gani abun har mmki yake masa, ba aikin sane bane kama masu laifin amma a yau zai fara domin idan tunaninsa ya bashi dai-dai wannan shi ne guy ɗin da suka jima suna nema.

Fesar da iska yay da sauri kuma ya zaro lafiyayyiyar wyarsa cikin ƙwarewa ya fara latsa ta.

Not too long yay dailing wata number, ringing ɗin farko akai pic sauke numfashi yay idanunsa akan mutumin a hankali cikin bada umarni yace “Uhm, You guy’s duk inda kuke kuzo nan” ya faɗa yana gaya masu inda yake a yanzu yana faɗin haka ya buɗe motarsa tare da cilla wayarsa ciki.

Fuska ba walwala kamar ko Yaushe ya fara tafiya inda ake hayaniyar yana zuwa yaja ya tsaya tare da kallon wani da yake cewa.

“Wannan mutumin duk sanda yazo Asibitin nan sai an nemi jariri sabuwar haihu an rasa, yanzu haka wani babyn ya ƙara ɗauka dan ban yarda da wannan jakar ta bayansa ba” .

Ɗaya mutumin yace “Haba Musty ance zato zunu bine baka da hujjar faɗin haka ai,tunda ba’a taɓa kamasa da jariri a hannu ba” kafin Musty yay mgn wani mai suna Omar yace “Haba Lawan, ai kallo ɗaya zakaiwa mutumin kirki kasan cewa na gari ne, kana kallon Wannan bawan Allan kasan cewa shi ɗin student ne, ka kalli  shigar mutunci da kuma kamala a tare da shi” Wanda aka kira da Lawan yace “Uhm! Ɗan yau ne fa? Nidai wlhe ban yarda da shi ba” Wanda ake ta mgn a kansa yana tsaye sai raba ido yake,sanye yake da riga da wando na shadda ruwan madara ya ɗura hula a kansa ga kuma handcovers ba wasu littattafai a hannunsa yace “Nifa nazo practical ne a wannan Asibitin ne ba wani abu ba” taɓe baki Ya Heemu yay domin duk surutun su ya cikasa ga wani bacci daya keji.

Tashin farko ya ƙara ware manyan idanunsa akan guy ɗin yace “What’s your name?” Kusan mutuwar tsaye matashin yay domin sai yanzu ya kula da Ya Heemu ha faɗa girman halittar jikinsa ya zautar dashi ga kuma kwarjininsa.

Lokacin ɗaya kuma ya fashin ci wani Ya Heemu, juya kai ya fara ya rasa me zai ce ta ina kuma zai fara, A karo na biyu Ya Heemu ya saki Murmushi wanda kana ganinsa kasan cewa bai saba yi ba wannan ba iya jajayen laɓɓansa ya tsaya, Cike da kuzari ya ɗauko I.D card ɗinsa ya nunawa matashin yace _” Ibrahim Khalel Muhammad Jalal my name”_ sai kuma yay Shiru tare da jan numfashi ya ɗura da faɗin _” It’s my I.d card I’m the chief of Army staff (COAS)_ dan haka last question what’s your name and where is your I.d card?” Gumi ne ya fara yan kowa matashin ya juya ya kuma juyawa yaga dai no way da zai gudu dan haka yace “Sunana Anas anace min Nas” sai kuma yay Shiru Ya Heemu kallonsa kawai yake domin duk wani jami’in tsaro kallo guda zaiwa Nas ya san cewa bashi da gsky.

Ganin kamar Ya Heemu baya ganinsa yasa ya ɗaga ƙafa zai gudu cikin zafin nama Ya Heemu ya ta ɗesa tare da riƙe hannunsa ya lanƙwasa bayansa nan take hannun Nas yay ƙara ƙassss alamar karyewa, wani ihun a zaba Nas yay a dai-dai lokacin kuma Sauran Soldiers wanda suka kasance Excorts a wajan Ya Heemu suka ƙarasu wajan, kai tsaye jakar bayansa Ya Heemu ya cire tare da miƙawa na kusa dashi yace _”Check it_  da sauri ya buɗe jakar abunda ya gani ba ƙaramin tsora tasa yay ba domin jariri ya gani wanda ko cibiya ba’a cire masa ba, an ɗaure masa baki da plaster sai ɗaga hannu yake sbd Numfashinsa da baya fita sosai.

Captain Daniel yace _”Oga it’s a Baby”_  Ya Heemu sam bai mmki sai kallon Nas da yay yace “Wa kakema aiki?” Shiru Nas yay Ya Heemu ya ƙara cafkar ɗaya hannun nasa nan take shima ya karye cikin tsawa Ya Heemu ya ƙara maimaita masa tambayar bakin Nas na rawa zai faɗi wanda ya kewa aiki nan aka sakarwa Nas harbi a gadon bayansa.

Da sauri Excorts ɗin Ya Heemu suka fidda guns ɗin su abin mmki ba mai harbi sannan ba alamar ta inda harbin ya fito.

Ya Heemu kallon gawar Nas yay da sauri ya juya zuwa cikin motarsa dan harga Allah ya kanta cewa Mumy (Mannal) ya kawo asibiti, kai tsaye hanyar Abuja ya ɗauka ba tare da Excorts ɗin ba,su kuma Excorts ɗin gawar Nas suka ɗauka suka nufi headquarter Kano ita.

Lokacin da aka shigar da Mumy cikin room ɗin kai tsaye Dr dake dubata ya gano matsala, da ƙyar ya samu jinin ya tsaya amma duk ƙoƙarin da yay sai da gudan jinin ta ya fita, daman ba wani ƙwari yay ba dan haka tuni cikin jikinta yabi jini shima ya fice, drip suka sanya mata tare da blood suka ɗauki dai-dai jininta, daman Ya Heemu yace suyi mata komai duk abinda ya dace.

Anut Lubna da mmki tabi Ya Heemu da kallo idan da sabo yaci ace tuni sun saba da halin Ya Heemu, amma a yau sai taga kamar bashi ba.

Cire komai tayi na mmkin Ibrahimul Khalel ta ɗauki key car ɗinta ta shiga mota kai tsaye Hospital ɗin ta nufa dan tasan ba lallai ya kaita wani ba.

Bata wani sha wahala ba ita special room ɗin da aka kwantar da ita, tana kwance samɓal ruwa da jinin na shiga jikinta a hankali, cike da tausayinta Anut Lubna ta ƙarasa wajanta tare da zama a gefenta, sosai taji tausayin Mannal musamman da likita yay mata bayanin ɓarin da Mannal tayi.

Wayar Anut Lubna ce ta fara ringing da sauri ta ɗauka ganin sunan _MY HEART_ Na yawo akan screen ɗin wayar.

Answering call ɗin tayi cikin ƙasa da murya tace “My heart Baban Mannal fatan ka kwantar da hankalinka, babu abinda ya samu gudan jininka sai ƙaddara” daga can ɗaya ɓangaren yana cikin mota dattijon mutumin mai shigar kamala da haiba kana ganinsa kasan shi ne Mahaifin Mannal sbd kamar da sukai cikin nutsuwa yace “On my way dear zan zo naji abinda ya sanya farin cikin Nuraddeen damuwa” da mmki tace “Wai aikin naka ka bari ka tawo?” Murmushi yay yace “Kina wasa da mijinki dear, tayaya hankalin Nuraddeen zai samu nutsuwa bayan farin cikinsa na cikin ɗimuwa da tashin hankali? Ki bari tuni na siyi online ticket na dawo yanzu haka ina hanyar zuwa Asibitin” Jinjina girman so da ƙaunar dake tsakani uba da ƴarsa tayi kana tace “Allah ya dawo mana dakai lfy cikin Aminci” ya amsa da “Ameen” kana sukai sallama. 

Ya Heemu kai tsaye Abuja ya nufa ransa a matuƙar ɓace, a yau ya ɗauki niyyar nemu dukkan mutanan da suke aikata irin wannan aikin dan haka zai ajjiye matsayinsa na Army staff ya koma nrml captain kamar kowa yadda zaiji daɗin binckensa hankali kwance da wannan tunanin yay parking motarsa a babban compound na gidan su, cikin nutsuwa yake taka ƙafafuwansa cike da jarumta kamar wani babban mutum nan kam ko 26 bai kai ba.

A parlon ƙasa ya samu Anut Meera kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, Murmushi tayi tace “Wlcm back son” haɗe fuska Ya Heemu ba tare daya kulata ba, Anut Meera na sane ta ƙara cewa “My son yaya akai naga ranka a ɓace?” Marai-raice fuska yay tare da dawowa wajanta da sauri yana zuwa ya zauna daf da ita tare da ɗura kansa a shoulder ɗinta cikin ƙasa da Murya kamar sangaltacce yace “Ke kam baki sanin ana ɗaga maki ƙafa uhm?” Dry Anut Meera tayi sosai tana shafa sumar kansa tace “Wacce ƙafa kake ɗaga min ɗan nan? Nida ka raina baka gani na matsayin Uwa bayan inda wacce ta kusa kamaka tsayi” lumshe idanunsa yay yana jin yadda take surfa masa mgn kana ya buɗe narkakkun idanunsa yace “Uhm ko? Nawa ne shekarun ƴar taki?” Kai tsaye tace “Moha wai?” Taɓe yay idanunsa akan jaririn hannunta mai kama dashi sak har baƙin yace “idan akwai wata bayan ita to” Murmushi Anut Meera tayi tace “A’a ita ɗaya gareni sai Lil Khalel, sai kuma Babban yayansu Ibrahimul Khalel” miƙewa yay tsaye yay ba tare daya kalleta ba yana tafiya yana faɗin “Soon or later zaki gane ina respect naki, banda haka babu wanda ya isa ya kalli idon Ibrahimul Khalel yace ya haifesa” yana faɗin haka ya haura upstairs kai tsaye ya nufi part ɗinsa,bai wani daɗe ba ya shirya cikin ƙananun kaya wanda suka amshi baƙar fatar jikinsa wacce take wani ƙyalli sbd baƙin ta, System ɗinsa ya buɗe nan da nan ya tura Muhimmin saƙo ta email ɗinsa, yana gamawa ya miƙe ya ɗauki lemon power horse a fridge ɗinsa ya fara sha a hankali yana lumshe idanunsa wanda suka ɗan janye sbd yanayin da yake ciki, a hankali ya kalli zanan Tattoo ɗin jikinsa kana ya lumshe idanunsa yana yadda mood ɗinsa ke sauyawa, banda shi babu wanda zai iya gane rubutun dake tsakiyar Tattoo ɗin da aka rubuta I&A shafa Tattoo ɗin yay kana a fili kuma yace _”My Shatuu”_ sai kuma yay saurin girgiza kansa shi kaɗai yasan me zcyarsa take raya masa, a duk sanda mutum ya sanya mace cikin lamuransa sai ya zama lazy very lazy ma weakness ɗin sa su bai yana a zahiri cikin ƙaramin lokaci a fahimci rauninsa,sam bai shirya hakan ba, saman bed ya faɗa tare da ɗaukan pillow ya rungome a ƙirjinsa. Ummi ce ta fito daga cikin part ɗinta ta samu Anut Suwaiba da Anut Meera zaune suna hira, kallonsu tayi tace “Ku shirya tafiya gida bikin an gama ai, Amarya kuma Ya Heemu zai kai ta” kwaɓe fuska Anut Meera tayi kamar yarinya tace “Nifa Daddyn Moha baya nan gsky sai na ƙara kwana Ya Ruma” Anut Suwaiba kuma tace “Ya Ruma nifa na tambayi kwana uku daman, kuma bani da matsala da mijina tunda mu biyu ne matansa dan Allah ki ramu damu” Murmushi tayi tana jinjina sakalcin ƙanan mijin nata tace “Bazan sake mgn mai maganin ku na nan ai” Anut Meera tace “Ai shi Ya Heemu matsala garesa, sai ta haɗewa mutane rai kamar shine gaba damu bayan muna da shekaru masu tazara” dry Anut Suwaiba tayi tace “Ai yana duba da ƙirar jikinsa irinta samudawa shiyasa yake bawa mutane umarni son ransa” Ummi murmushi kawai take masu dan ita kanta halin Ya Heemu mmki yake bata, Miƙewa Anut Meera tayi tace “Ya shigo yana ta zanyyana min surutu,yadda wani yana ɗaga min ƙafa ne” Ummi tace “To kada ku cinye min ɗa da baki ƙilan ko ruwa baku bashi ba bare abinci”  ta faɗa tana nufar part ɗinsa,tana shigewa Su Hanna ba haurawa upstairs ɗin da sauri Hanna ce farko sai Moha sai kuma Shoona kusan kansu ɗaya amma gaba ɗaya cikinsu Moha ta fisu fari domin har wani yellow take sbd fari kusan ita ta ɗauko farin Baffa sai kuma Safa. Da murna sosai Moha ta faɗa jikin Anut Suwaiba tana faɗin “I missed you so much Mom, wlh shiyasa bana son boarding school ɗin nan” ta ƙare mgnar ƙwalla na taruwa a idanunta, Shafa kanta Anut Suwaiba tayi tace “Haba daughter daga mgn sai kuka sbd baya yi maki wahala ko?” Maƙale Anut Suwaiba Moha tayi tace “Mom!” “Sorry! My Moha ai kun kusa” sharr hawaye ya zubu mata tace “Mom! Shi Ya Heemu boarding yay ne dazai takura mutum sai yay boarding school” Anut Meera tai saurin make bakin Moha tace “To rasai, bai isa yace kuyi abu bane na sake jin bakin ki wlh sai kin sakin daku” Moha an taɓa mata inda yake mata ƙaiƙayi ta zube saman carpet tana mirgima tare da fasa ihu, Hanna da Shoona tuni sunyi part ɗin Safa sbd an gama shiryata tsaf za’a aikata ɗakin mijinta, Miƙewa Anut Meera tayi ta ajjiye Lil Khalel ta nufi wajan Moha, Ummi tayi saurin faɗin “Kul kika taɓa min yarinya” Anut Meera tai ƙwafa tace “Ya Ruma kalli haukan da yarinyar nan take kamar wata ƙarama” Murmushi Ummi tayi tare da miƙar da Moha ta rungome ta tare da lallashinta tace “Stop cry Little Baki son makarantar?” Da sauri Moha ta ɗaga kai tana ƙara shigewa jikin Ummi sbd akwaita da son jin mutum kusa da ita kamar mage, shafa kanta tayi tace “Zanwa Yayan naku mgn kinji ko? Maza jeki shirya kisa sabbin kayan Safa Ya Heemu zai huce daku” tsalle tayi tana juya hips ɗinta Anut Meera ta riƙe baki tace “Yau na shiga uku ni Hafsat” dry Anut Suwaiba tayi tace “Malama Allow her to enjoy gaba ɗaya kin rikita mana yarinya” An shirya Safa cikin wani light blue ɗin lace wanda ya haska farar fatar jikinta tai kyau sosai, ita bata cewa komai sbd yanayin data shiga gaba ɗaya wani iri take jinta kamar ba ita ba, Moha kam ta sanya abaya red tai kyau sosai sai juya idanunta take daman mgn ba aikinta bace sai ƴan rigimar suna kusa. Anut Suwaiba ta riƙe hannun Safa wacce take ta kuka domin daman tun safe Ummi ta ƙara yi mata faɗa da kuma nasiya sosai haka ma Anuties ɗin nata, Ummi ce ta kalli Moha tace “Little rakata wajan Ya Heemu” kwaɓe fuska tayi tace “Ummi Hanna taje mana” kafin Ummi tai mgn Hanna ta riƙe hannun Safa suka nufi part ɗin Ya Heemu. Yana zaune a Parlo’n a karon farko daya sanya manyan kaya wani tattausan blue ɗin voyal ne a jikinsa mai mayan zane, rigar half body ce sai short hand yay kyau sosai ya ɗura ƙafa ɗaya kan ɗaya gama cin abincinsa kenan wanda Ummi ta kawo masa, idanunsa a Lumshe yaje an Turo ƙofar Parlon an shigo, narkakkun idanunsa ya buɗe tare da juyawa suna haɗa ido da Hanna tai saurin janye idanunsa a hankali ya miƙe yana zuwa daf dasu ya kalli Hanna kama ya sanya hannunsa ya kama hannun Safa yace “Kada ki sake shigowa without my permission ok?” Kai ta ɗaga masa tana fita Safa ta faɗa jikin yayan nata ta saki kuka. bai su san me Ya Heemu yaywa Safa ba ya fito da ita tana dry ta riƙe masa hannu, fuskarsa ɗauke da lallausan murmushi  yana zuwa parlo ya haɗe rai, Ummi tana ganinsu ta sauke ajjiyar zcy ta sassarfa ta nufi wajan yaran nata ta rungome su tana fargaba na shigarta, da ƙyar Ya Heemu ya zare Safa daga jikin Ummi kana ya suka fice daga gidan. Lokacin da Suka isa makeken gidan Abban Arman yana tsaye a compound sai kai komu yake yana ganinsu ya sauke wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, Ya Heemu ko kallansa ba haka kuma yace ta fita kawai basai su Hanna sun shiga ba, kuka ta sanya masa kashe motar yay kana ya fito ya riƙe hannunta ya shiga har gidan dake ba baƙonsa bane, part ɗin da yaga an tsara sosai yakai Safa kana ya ƙara bata hqr da kuma ribar biyayya shi kansa sai da jikinsa yay sanyi sbd kukan da yaga Safa nayi, da ƙyar ta barsa ya fice daga gidan, a Babban Parlo suka haɗu da Arman wanda kallo guda zakai masa kasan cewa ya faɗa damuwa ta baiyana a fuskarsa, Murmushi ƙarfin Arman ya sauke tare da nufar Ya Heemu suka rungome juna, sosai suke ƙaunar junansu sbd tasuwar da sukai tun suna yara, hey² sukai sama² kana suka fice daga cikin gidan dan Arman shima ba zama zai ba motarsa ya shiga suka fita a tare dasu Ya Heemu. Kai tsaye Ya Heemu gidan Baffa ya nufa Tun a hanya Moha ta fara tura baki yana kula da ita sanin yarinyar tana da matsala idan ya biye mata tsaf zai ƙaryata shiyasa ko inda take baya kalla. Suna isa ta fice da sauri tana faɗin _”Baffa! Inna! Gani nazo”_ sai kuma Shoona ta mara mata baya dake gayyar duk ɗaya ce, Hanna ce kawai ta tsaya ta kallon Ya Heemu daya manna baƙin glass a idanunsa yana operating wayarsa, a jikinsa yaji ana kallonsa ya ɗaga daradaran idanunsa kana ya saki tsaki tare da shigewa cikin gidan. A parlo ya samu Baffa zaune yana shan kunun tsamiya wanda yaji suger Moha maƙale a jikinsa tana masa suturu yace “Haba matar wannan ƙaton har ya isa ya baki tsoro?” Kwaɓe fuska tayi tace “Baffa ko baƙar fatarsa ai ta tsorata mutum bare manyan idanunsa da yake zarewa mutum ka wani ƙaton jiki” dry Baffa yana bawa Moha kunun bai ce komai ba, ita harga Allah bata kula da Ya Heemu dake tsaye a bakin ƙofa ba ya haɗe fuskar nan kamar hadari, girgiza kansa a ransa yace “Za kici Ubanki bari nayi maganinki” yana faɗin haka ya shigo yana ɗan sakin murmushi yace “Baffa kayi baƙo a waje” Baffa ya ƙara bawa Moha kunun tasha tana ƙara rikesau sbd tsoran Ya Heemu, Baffa ya zareta a jikinsa tare da miƙewa da sauri itama ta miƙe zata bi bayan Baffa Ya Heemu yay sauri riƙe hannunta cikin ƙasa da Murya yace “Baffa jeka bari ta tayani Shira” Baffa yace “To yau kuma?” Yana faɗi hakan yana barin Parlon da sauri Ya Heemu ya rufe ƙofar Parlon kana yaja tsaki yana kallon Moha wacce jikinta ya ɗauki rawa kamar ana buga mata ganga, kafin kace me ta saki kuka ta nayin baya, kai tsaye ya nufi inda take tsaye a jikin bangon yay mata rufe da faffaɗan ƙirjinsa yace “Dan Ubanki dawa kike? Shiga fuska kamar an silala kazar gona ba abinda kika iya sai rashin ta ido” shiru tai masa tana sakin kuka tare da kulle idanunta wata gigitacciyyar tsawa ya daka wacce tsabar tsoro da firgita da tayi yasa ta faɗa jikinsa baki ɗaya tana ƙanƙamesa tare da sakin kuka, lumshe idanunsa Ya Heemu yay yana jin yadda jikinta ke rawa da yadda ta riƙesa, zareta yay a jikinsa ta buɗe baki zatai magana yasa hannu ya ɗalle mata baki wanda nan da nan wajan yay jaa albarka da fata ba ƙwari, zafi da azabar da taji haɗi da raɗaɗi yasa tai saurin faɗin “Wayyoooo Baffa, wayyoooo Ummi, Inna zai kashe ni Wlh ban yafe ba kuma sai na haɗaka da Ummi wayyoooo ya fasan baki” ta faɗa tana birgima a ƙasan carpet, mmki ya kusan kasjey Ya Heemu wai bata yafe ba dole sai yayi Maganin yarinyar nan rasa me zai mata yay sai kawai yasa hannu ya miƙar da ya tsaye tare da haɗata da jikinsa yace “Ke ni kike cewa baki yafe ba?? Dan Ubanki har nawa kike? Shige ƙwailar banza zai rashin kunya fal ciki empty head kawai” ya faɗa yana rungome ta sbd kukan da take da kuka kumburin da leɓanta yay, kuka ta ƙara saki tace “Ni ka sake ni wlh sai na haɗaka da Ummi ka fasan baki kuma sai na rama?” Mayan idanunsa ya ware yace “zaki iya ramawa?” Kai ta ɗaga masa tace “Wlh sai na rama kuma kaje kai da Allah bazan yafe ba in sha Allah Baƙaƙen ƴar ƴar zaka haifa irinka” wani lallausan murmushi yay yana shafa cikinsa yace “Idan kuma uwar yaran fara ce fa?” Turo baki Moha tayi tace “Wacce farar macance zata aure ka wlh Ya Heemu na tsaneka kai mugu ne” hannunsa ya ɗaga ya zabga mata mari ya ƙara sauke mata wani, wasu taurari Moha ta gani sun gilma ta gefen idanunta tama rasa wanne kalan kuka zatai, sai da ta buɗe duka muryarta ta buɗe baki zata kurma Ihu Ya Heemu yay saurin sanya bakinsa cikin nata..

Idan naga COMMENT da SHARE kuga posting da wuri if not kowa yaje ya riƙe abinsa🥲🤒

Bana da grps so share it please fisabilillahi🤲🏼.

NIMCYLUV✍🏾⁹ ¹⁰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *