BATUUL
CHAPTER 23
Lukman get the key to my house, right away”, daga d’aya b’angaren Lukman ya amsa da “Hokay Sir but which of the Ouses?”, “Mississippi Street, you should get there right now, I will soon be there”, yace “Hokay Sir Hi will do that”, ya katse wayar ya ajiye, kallonta yyi har lokacin hawaye ne idonta ya bud’e baki zaiyi magana kenan suka iso bakin gate, ya mik’owa masu gadin card d’insu ya fita daga harabar Blue cabana, kallo d’aya yayi mata ya maida hankalinshi kan tuk’in da yakeyi, hijabin jikinta taja taci gaba da goge hawayen dake zubo mata, ita da kanta ta rasa hawayen mey takeyi, attention d’in da bai bata bane ya zauna yana danna waya ko kuma matan da ta gani suna magana dashi harda dariya ya sata b’acin rai, wani iri taji da ta tuna da matan har saida gabanta ya fad’i, batayi yunk’urin goge hawayen ba dan ba daina zubowa zasuyi ba, hannunshi taji a fuskarta yasa ya shafo hawayen yana murzasu yana kallonta, a hankali ta sauk’e idonta k’asa, zaiyi magana wayarsa ta fara ringing ya duba ganin mai k’iran yasa ya d’aga tareda cewa “Sorry badai har kun fito ba”, daga d’aya b’angaren Massa ya amsa da “Yanzu haka ita na d’auko, baku dawo bane?”, d’an siririn tsaki yaja yace “God man am sorry wlhy ba yanzu zamu dawo ba, I had to but am sorry”, Massa dake d’aya b’angaren yace “For real?, I told you gobe zata koma Sokoto kuma dan Batuul zata, ita ta tsaya dubawa”, Abu yace “I know, I understand, am having issues over here so nake inyi clarifying before getting back home, bawa Rahamar waya muyi magana da ita”, Tsaki Massa yaja yace “You are a jerk kaima ka sani ko”, dariya Abu yayi yace “Not better than you, d’an bata wayar nikam, da ita zanyi magana ba kai ba”, cikin siririyar muryarta tace “Hello”, Abu yace “Hey, am so sorry, wlhy abune ya tsaida mu nan kiyi hak’uri, next time har gida zan kawo miki ita ku gaisa kinji”, ya juya ya kalli Batuul yaga har lokacin kanta a k’asa yake, a hankali Rahama tace “No fa, ba komai, there will surely be next time, Allah ya bata lafiya ya k’ara mata lafiya”, wani irin sanyi yaji har cikin ranshi jin addu’ar da Rahaman tayiwa Batuul da murmushi a fuskarshi yace “Amin ya Allah, sorry once again and Thank you”, murmushin tayi itama tace “Ba komai fa”, yace “Yawwwa mun gode Allah ya kiyaye hanya”, ta amsa da Amin snn ta mik’awa Massa wayan, Abu yace “Ita mai zuwa dubiyan da kanta ta hak’ura, ka dawo goben ka dubata”, Tsaki Massa yaja yace “Kaga ni kai ta sani, zan kaita ta gaida Ammah in kuma ka dawo daga gantalin naka ka samemu, fine”, Abu yayi dariya yace “kaima zaka fito gantalin ne anytime soon, just get married”, Massa yace “My regards to her, kayi mata ya jiki pls”, Abu yace “Sure zataji”, ajiye wayan yayi ya d’ago kanshi suka had’a ido, da sauri ta d’auke nata idon tana twitching d’an k’aramin bakinta, murmushi yayi ya kamo hannunta yana murzawa a ranshi yace “She will b the death of me”, bata yi yunk’urin k’wace hannunta ba kuma batace mishi komai ba, yace “Rahama tace inyi miki ya jiki?, they wanted coming now kuma nace musu bama gida”, d’ago kanta tayi tana kallonshi tanaso ya fad’a mata wacece Rahama dan batasanta ba, yayi murmushi ya sak’e damtse hannunta yace “Mustapha’s fiance”, batace komai ba ido ta lumshe kawai hawayen da ta kasa riqewa na dad’a taruwa, shima bai sake cewa komai ba amma yana riqe da hannunta d’aya yaci gaba da driving d’inshi, bakin wani baqin gate taga sun tsaya, horn yayi aka wangale musu gate d’in suka shiga tunda suka shiga gidan take k’arewa gidan kallo , ba wani babba bane sosai, duplex ne amma yayi kyau sosai, fitowa yayi daga mota, Lukman dake tsaye jingine jikin tashi motar ya k’araso wajenshi, saida ya gaisheshi snn ya mik’a mishi key d’in, Batuul ya hango zaune cikin mota yace bari su gaisa da Madam, Abu ya girgiza kai yace “No Lukman not now okay, next time”, Lukman da murmushi fuskar shi yace “Hokay Sir, Hi will leave now”, daga haka ya koma motarshi ya shiga ya tafi, Abu ya zagaya ta wajenta ya kamo hannunta sukayi gidan, parlour ne mai girma sosai, sosai tsarin gidan yayi mata kyau, bai sake mata hannu ba har saida ya zauna bakin gadon bedroom d’in gidan dake sama, Wani fridge ya bud’e ya fiddo ruwa roba d’aya kamin ya dawo ya zauna daga gefenta snn yasa hannu ya juyo da ita tana fuskantarshi ya bud’e ruwan ya mik’a mata, a hankali tasa hannu ta karb’i ruwan tasha kad’an, sai kallonta yakeyi yana lumshe ido ya bud’e, Miko mishi tayi yace “Ya isheki?, ta d’aga mishi kai alamar ehhh, shima shan ruwan yayi ya ajiye gefe snn ya rik’o hannayenta duka biyun, wani irin bugawa kawai zuciyarta keyi, a hankali ta lumshe ido, kamar daga sama taji muryanshi yace “Do you need to see a therapist?”, bata san lokacin da ta bud’e ido ta kalleshi ba jin abinda yace”, wara ido tayi a sanyaye ta fara k’ok’arin janye hannunta ya riqe da k’arfi, rungumeta yyi yana d’an rocking d’insu yace “sorry its okay baza ki ga wani therapist in baki so,”, a hankali ta d’ago kanta da wani irin smile fuskarta tace “I look mental huh?, ta goge d’an hawayen dake fuskarta, kai ya girgiza mata ya sake rungumeta yace “ko kad’an Fatima, I just want you to be happy, banason ganinki kina wannan kukan, you barely spend 5hrs batareda kin zubda Hawaye ba, and yana damuna, gani nakeyi kamar ban kyauta miki ba, its hurting me nima”, kallonshi takeyi har yayi shiru batace komai ba, yace “Say something, bana son kallon nan, I just want you to be happy, I love you sosai Fatima”, kamar yanzu ta fara jin kalmar I love you d’in bakinshi, abin nan da takeji kullum shi taji yauma, a hankali tace “Then why where you ignoring me if so d’azun?”, wara mata manyan idonshi yayi yace “Dagaske?, I did that?”, kau da questions d’in tayi ta sake cewa “those ladies da suka zauna suna maka magana suna dariya fa?, who were they?”, sai yanzu ya lura da kishi ya sata kukan nan, shi sam ya ma manta da dasu wlhy, dariya ya fasheda da ya sake kufular da ita, rai b’ace ta tashi daga kan gadon zata bar wajen yayi sauri ya fixgota ta fad’a kanshi, idonshi yasa cikin nata da yasa tayi saurin rintse su zata mik’e, hannu yasa ya zagayeta ya matseta jikinshi har yana jiyo heartbeat d’inta, cikin wata iriyar murya tace “Nikam let go of me, ba dariya kayi min ba”, dariyan ya sakeyi yace “ashe kina kishina tinda har kikayi kuka dan kin ganni da wasu”, tsuke baki tayi tana son barin jikinshi yaqi saketa, ya tsagaita dariyan yana k’arewa fuskanta kallo yace “You have changed me Fatima, you have changed me a lot cikin k’ank’anin lokaci, ban tab’a kawo zama ina rarrashin mace ba sai gashi kin sani na fara, I get emotional anytime nayi tunanki”, “your eyes”, ya d’an hura mata iska a fuska, “your lips”, ya fad’a yana zagaye lips d’inta da k’aramin yatsanshi, “your cute chiseled nose”, ya fad’i tareda had’e hancinsu, “I like everything about you, duk wani uneasiness da nakeji a da yanzu nasan mesa nake jinshi, inasonki but I couldn’t realize”, hawaye yaga ya ziraro mata a ido, d’an murmushi yayi yace “Bana son zama sanadin zubar precious hawayen nan pls kinji, anytime nayi miki abu just yell, shout, tell me na b’ata miki rai amma banda kuka kinji?, kuka sosai tasa tana son ta tashi daga jikinshi ya sake matseta yace “fad’amin kukan mey kikeyi?”, kasa motsi tayi zuciyanta na tsananta bugu, tsorata yayi jin yadda zuciyanta ke bugu ya mik’e tareda zama yana kallonta yace “Fatima are you okay wai, meke damunki ya Allah?”, a hankali kamar mai koyon tace “I… love…. you”, kamar wani shigewar iska haka yaji maganan ta daki dodon kunnenshi, kallonta yakeyi yanason tabbatar da abinda yaji ya fito daga bakinta, idonta yake nema ya gani dan ko zai tabbatar mishi da abinda ta fad’an, hab’arta ya d’ago yana kallon fuskarta, sauk’e ido tayi tanajin nauyin abinda ya fito daga bakinta, ta d’auka iya zuciya kad’ai ta fad’eshi saida ta gama furtwa tasan a fili ta fad’eshi, yace “Look at me Fatima, pls”, da k’yar a hankali ta iya d’ago kai ta kalleshi, suna had’a ido tayi maza ta kauda nata, wani irin runguma taji yayi mata, tare suka sauk’e ajiyar zuciya, a kunnenta yace “son nawa ne ya saki kukan da kikeyi?”, a hankali ta girgiza mishi kai, ya d’agota kamar da damuwa a ranshi yace “Toh mey ke saki kuka?” Cikin sanyin magana tace “The very first day i met you, i know something in me has changed da har uanzu bai koma daidai ba, You came into my life lokacin da banyi zato ba, na d’auka you are just here to snatch my happiness, na d’auka duk wani farin ciki da zanyi ragagge ne tunda ka shigo rayuwata, I never thought I could fall for anyone so easily but then I realised kullum anytime nayi tunaninka, I get emotional, anytime I see you, I feel happy, anytime you come in contact I feel shivers down my spine, that feeling that I can’t express, tsoro nakeji Yaa Abu, am scared”, ta rik’o hannayenshi duka biyu ta rik’esu da k’arfi, kallonta kawai yakeyi, Batuul ce zaune gabanshi tana expressing mishi son da take Mishi, jiya ya gama expressing mata but bai tab’a kawowa kanshi anytime soon Batuul will fall for him, ta fad’a mishi itama heartbeat d’inta is never stable when ever they are close amma ya d’auka tsoronshi ne duka ya janyo hakan, ya sake damtse hannunta ya sunkuyo yana kallon fuskarta yace “Kalleni, mey ke tsorataki, tsoron mey kikeyi when you have me?”, ido ta lumshe ta bud’e tayi d’an murmushin jin dad’in abinda yace, mey zai bata tsoro bayan tana dashi, ajiyar zuciya ta sauk’e da tayi tunanin ba nata bane ita kad’ai, she have to share him da wata, “Fad’a min mana, tsoron mey kikeji?”, a sanyaye tace “Of losing you”, wani irin farin ciki yaji har ranshi, ya sake tabbatarwa dagaske take tana sonshi, wani lallausan murmushi ya saki ya d’ago hab’arta da tak’i yadda su had’a ido yace “And you think this will happen?, kin rigada kin sameni Fatima sai yanda kikayi dani, I don’t need to remind you how much you have changed me, but zan fad’a miki cewa you have gotten Aliyu sai yadda kikayi dashi, Aliyu nakine ke kad’ai, baza kiyi sharing d’insa da wani ba”, batason yana mata irin wannan alk’awrin, tun kamin ta sameshi tasan wata ta sameshi kuma babu yadda za ayi ya zama nata ita kad’ai, tasan ba mantawa yayi ba, badai yasone yayi ruining moment d’innan shiyasa yaketa wannan zubar haka”, hannu tasa tayi cupping faces d’inshi tace “Ka dena fad’an haka, before me there was someone a rayuwarka, she got you before me”, tayi wani irin murmushi tace “am okay with it, just love me, kar ka dena sona that’s I want”, sai lokacin ya lura da maganan da takeyi, sai lokacin hankalinshi ya nuna mishi cewa da Ajiddeh take, wani irin b’acin raine yaji ya ziyarce shi lokaci d’aya, ya kai hannu kan hannyenta dake fuskarshi ya riqe yace “ki riqe a ranki ke kad’ai keda ni and no one else”, kallonshi take tana dad’a tabbatar da what he is saying, from his eyes tana ganin he meant what he is saying, kai ta girgiza mishi zatayi magana yace “I promise, ke kad’ai kike dani nima ke kad’ai gareni”, ajiyar zuciya ta sauk’e ta lumshe ido zuciyarta na bugawa tana kokonton abinda zuciyarta ke shirin sata tayi, a hankali tayi leaning ta cikata gap d’in dake tsakaninsu ta had’e bakinsu waje d’aya, wani irin dogon numfashi yaja kamin ya amshi bak’uncin abinda yakeji yanzu, a hankali yayi parting lips d’inshi suka shiga kissing junansu with so much affection, kamar wacce ta tuna abu tayi maza ta janye bakinta daga nashi, a raunane ya d’ago ya kalleta da puppy eyes yace “Plssss”, had’e rai tayi tace “Su waye y’an matan d’azu da suka zauna suna maka magana harda dariya?”, ajiyar zuciya ya sauk’e tareda lumshe ido ya sake kamota ya had’a bakinshi da nata, saida ya gaji don kanshi ya k’yaleta ya cire mata hijab tareda da kwantar da ita jikinshi ya na yamutsa mata gashinta da yake a tsefe, ya bud’e baki zaiyi magana daidai lokacin wayarsa tayi ringing, dubawa yayi yaga Ammah ke k’ira, jiki ba k’wari ya d’aga, muryar Aunty Amnah yaji tana cewa “Sannunka Abu, ina ka kai y’ar mutane ana zuwa dubata bata nan?, Massa da Rahama tun d’azu suke zaune baiwar Allah kasa ta zaman jira, ka dawo da ita”, murmmushi yayi yace “She is my wife, nafi kowa buk’atarta, suyi hak’uri su barni da ita, I need my wife”, baki Aunty Amnah ta bud’e tace “Lallai Abu, yanzu ko kunyata baka ji kake cewa a bar maka matarka you need her ko?, toh ga Ammah nan kayi mata bayani”, muryar Ammah yaji tana cewa “Abu bana son wasa, ina ka kai yarinyar mutane?”, a hankali yace “Ammah she is my wife kuke magana kamar wata nayi kidnapping”, Ammah tace “Kana jina ko, Batuul d’in da bata da lafiya ko k’warin jiki bata gama samu ba shine zaka d’auketa ka tafi da ita gantali?”, kallon Batuul dake kwance jikinshi yayi suna had’a ido ya sakar mata murmushi har lokacin hannunshi d’aya na cikin gashinta, itama ta maida mishi murmushin a ranta tana tunanin yadda zatayi facing Ammah, yace “Ammah relax, dagaske babu inda na kaita, muna gida fa, she will be safe, I promise” tace “Ban gane gida ba, yanzu haka k’annen nata zasu tafi basuyi sallama da ita ba?”, yaja numfashi yace “Ammmaaahhh, we will be back soon, ayi mana hak’uri, kuma ma zan kai ta ta gaishesu ai some other time”, Ammah taja tsaki tace “inace jikinta lafiya babu matsala?”, yace “She is fine, yanzu zamu dawo”, da haka ta katse k’iran, yaja numfashi ya sauk’e ajiyar zuciya, da sauri ta mik’e ta zauna tace “Kaga mu tafi, su Ammah na nemanmu”, ya maidata position d’inta na da yace “We are staying here for the night”, ta wara ido tace “No Yaa Abu, inajin kunyan Ammah fa”, ya d’aura hannu kan flat tummy d’inta yana shafawa yace “Kin manta ma da tambayar da kika min, well those ladies da kika gani, all I can remember is we had classes together when I was in college”, tace “toh shine suka zauna har kuka dad’e kuna magana dasu”, yayi pouting lips d’inshi yace “Bake kika tafi kika barni ba, you unveiled me kika barni ni kad’ai, they thought banida mata shiyasa suka zo wajena”, D’auke ido tayi da sauri, a ranta tace “Subhanallah”, wani irin kyau yayi mata da yayi pouting, he will be the dead of her in har taci gaba da kallon face d’inshi da yayi pouting da girarsa da suka had’e waje d’aya, tace “su basusan mey mata bane Kai, I cried because of that, my heart was aching da na ganku a tare”, ya sake tab’are fuska yace “Noooo, karki damu baki sake ganinsu anywhere close to me, kema promise not to leave me”, pouting d’in tayi itama tace “I can’t even do that, I love you”, wani farin ciki na daban ke ziyartarsa, ya sunkuya yayi pecking d’inta “You know I do more”, lumshe ido tayi tana jin wannan sabon yanayi da ta samu kanta ciki, a hankali tace “kaga fa kukana shi da kanshi yake zuwa, bani keyi ba”, ya d’agota yace “And you know it hurts me ba?, I hate to see you cry”, a hankali kamar zatayi kukan tace “I promise not to again”, yace “Thank you, tashi muje kiyi alwala muyi sallah, its Magrib, ita ta fara yi snn ta jirashi ya fito shima yayi suka dawo ya jasu sukayi sllh, zama yayi bayan sun idar yace zai musu ordering abinci su dan nan zasu kwana, da k’yar ta samu ya yadda suka koma gida, gabanta har fad’uwa yakeyi tana tunanin Ammah zata gane komai ga kunyarta da takeji yau, da Aunty Amnah suka fara had’uwa da ta bishi da harara tayi hugging Batuul tace “kika yadda kika bishi yawo?, gantalinshi fa ba mai k’arewa bane da kike ganinshi”, murmurshi kawai tayi ta sunkuyar da kai, ya kalli Aunty Amnah yace “Nima haka zanje in samu uncle ince mishi ya dena zuwa ko ina dake, dama gashi kin fara tsufa, sai a d’auka yayarsa ce”, Aunty Amnah ta wara ido tasa salati tana tafi tace “Abu ka gama rainani, zamu had’une da kai har gida zakazo ka sameni”, dariya kawai yayi dai dai lokacin Ammah ta k’araso ta harareshi tace “ai ka kyauta”, murmushi yayi yana sosa kai yayi mata k’asa da puppy eyes d’in da yayi alamar tayi hak’uri, Ammah ta kama Batuul tace “muje kisha magani, ga soup d’in kifin tun d’azu Amnah taxo dashi”, ta manta sam da tacewa Aunty Amnah ma tana son soup d’in kifi, a kunyace tabi Ammah a baya, k’arfe tara Uncle yazo suka tafi da Aunty Amnah bayan ya yiwa Batuul ya jiki tareda yi mata alk’awrin kawo su Nawal kamin su koma Paris, wanka Batuul tayi ta shirya ta sulale d’akin Farida, hiransu sukeyi abinsu sukaji an bud’e k’ofa, duk suka dubi k’ofan a tare suka ga Abu ne, bai cewa kowannensu komai ba ya shigo yad’auki Batuul cak, tace “Yaaa Abu kayi hak’uri ka sauk’eni, kaga fa akwai su Ammah a gida”, yace ba guduwa kikayi kika barni ba?”, tace “naga fa kana wanka ne shine na tafi kamin ka fito”, bakinshi ya d’aura wuyan da yasata kasa yin wata maganr, ranan kwanan farin ciki sukayi , sosai Abu ya gwadawa Batuul irin son da yake mata da missing d’inta da yayi a daren. Tunda Dad ya fita ya barta d’akin Kulthum Ajiddeh bata sake cewa komai ba, angle ta samu daga gefe ta zauna a takure, duk bayan minti d’aya sai ta duba wayarta tana jiran tsammanin k’iran, a hankali siraran hawayen ke bin fuskarta, rayuwarta a baya take tunawa, tun ranan da ta fara ganin Abutturab a school Allah ya d’aura mata sonshi, babu irin wahalar da batasha ba dan kawai ya fara koda kallonta ne amma yaqi, babu irin nacin da batayi akanshi ya nuna duk baisan abinda takeyi ba, gashi ko aboki d’aya bata tab’a ganishi tareda ba, shekarar da zai gama ita tana third year, sosai hankalinta ya tashi ganin har zai gama ya tafi, shawara ta yanke kawai na ta sanar da Mum, at first mum bata biye mata ba saida taji ko d’an waye shi d’in, lokacin ne Mum tace mata ko sau d’aya ta samu ya bud’e bakinshi yayi mata magana daga nan zasusan abin yi, baza ta manta ranar da suka shirya itada friends d’inta akan in taga ya shigo makaranta ran sunday ta shige gaban motarsa ba ya bigeta ko dan yayi mata magana ne, tunda duk Sunday a school yake yinta kuma babu mutane da yawa, hakan kuwa sukayi ranan Sunday babu mutane da yawa school, daidai ta hango motarsa ta tashi ta shiga drive way shikam da ya taho sam bai lura da ita ba, kiiiii ya taka brake, da hanzari ya fito, ranshi b’ace zai fara yiwa maishi fad’an rashin kula, sai a lokacin ya gane mace ya kad’e, duk nacin da take mishi baisa ya gane wacece ita ba, baki ya bud’e zaiyi magana ta fashe da wani irin kuka, babu sautin da yafi tsanar jin irin kuka bare na mace, duk masifar da ya kwaso kasa k’arasa yin ta yayi, kuka take sosai tana yarfe hannuwa dukda ba wani ciwo taji ba, d’aukarta yayi ya sata mota, friends d’inta na daga gefe sukayi mata signalling zata wuce, ido d’aya ta kashe musu alamun taji dad’in accomplishing mission d’inta, murna fal cike ranta tana jin ta jikinshi kamar lokaci yayi ta zama a haka, a mota ya sakata yace mata sannu daga haka ya fara driving, asibitin da yake zuwa can ya kaita aka dubata sukace bata wani ji ciwo ba amma sam taqi yadda ta taka k’afar, ya tausaya mata ganin yadda take kuka, Wheel chair yayi requesting da a bata, badan taso ba ta zauna Kai, sai da suka fito yake tambayarta makaranta zai kaita?, tace mishi kada ya damu ya kaita gidanta, yana tsaye bai shiga gidan ba yasa tayi waya aka zo aka shigar da ita, yana barin wajen da mortarsa
ta daka wani uban tsalle, tayi hugging kawayenta, take ta bugawa Mum ta fad’a mata duk yadda abin ya faru, tun daga lokacin suke asiransu kanshi, wasu suyi tasiri wasu baza suyi ba, lokacin da yazo mata da zancen aurensu suma ne kawai batayi ba sbd dad’i, kamar a mafarki takejin lbrn, tasan Aliyu baya mata son da har zaice zai aureta, son da yake mata baifi 2% ba cikin 100% d’in da take mishi, tsoron kada wani abu ya sa ta rasashi ta shiga neman maganin mallaka, duk inda tasan za a bata abinda zaisa Aliyu ya sota ita kad’ai har abada saida suka zagaya itada su Mum da Aunty Jainaba, wani hawaye mai d’umi ta share daga fuskarta tana ci gaba da tunani, tunda ta zauna Kulthum ke kallonta, a hankali taji muryarta tace “Komai yayi zafi maganinshi Allah, ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki shi zai miki jagora”, wani iri taji maganar kamar ma ba da ita akayi maganan ba amma sanin su biyu ne kad’ai d’akin yasa ta gane da ita take, bata kulata ba har lokacin, da dare ma haka Ajiddeh bacci kad’an tayi, washe gari ne ganin yanayin Ajiddeh duk ya canja tace “Hauwa tunane tunanen nan da kuka duk da kikeyi matsala zasu k’ara miki, ki samu ki sassautawa kanki, bance ni ba ko inason sanin matsalarki ba, a ah, ki samu wani amintacce da kika yarda dashi kika san zai baki shawara mai kyau ki fad’a mishi matsalarki zaki samu sauk’i a ranki, ko da mahaifiyarki ce ko mahaifinki, zasu fahimceki ko da wacce iriyar matsala kikazo musu, kallonta kawai Ajiddeh keyi ta kasa ce mata komai, batasan komai game da matar ba amma daga yanayinta tasan bazata cutar da ita ba, tashi tayi ta fice daga d’akin tayi side d’in Mummy, masu aiki ne sukace mata Mummy tun da asussuba ta fita amma tace kada a bari ki fita ko inane, wani kallo ta jefeshi dasu kamar in tayi niyyan fitan zasu iya hanata, juyawa tayi ta koma side d’in can, a hankali ta fara magana ta shiga zayyanowa matar abinda ke damunta, matsalarta da kuskuren da duk ta aikata, batace dai asirin kisa sukayiwa Batuul ba, tace kawai na zubda ciki ne da kuma barin gidan sukayi mata
+
STORY CONTINUES BELOW
Da asuba shi ya fara tashi, bai tada Batuul ba dan yasan bacci bai wani isheta ba, kwanciyarta ya gyara mata snn yayi wanka ya zira jallabiya ya fesa turarukanshi masu sanyin k’anshi ya fita zuwa masallaci, a masallaci ya had’u da Abui da Sadiq, Bayan an idar da Sallah snn suka gaisa, Abui yana tambayanshi ya jikin Batuul ya amsa mishi da “Alhamdulillah taji sauk’i”, Sadiq ma ya gaisheshi yayi mata ya jiki daga haka suka shigo gida kowa yayi side d’inshi, a hankali ya turo k’ofar d’akin, da mamaki ya kalleta ta kunna bedside lamp tana zaune kan abin Sallah riqe da Qur’an tana karanta Suratul Qasas cikin muryarta mai dad’i, Ido ya lumshe ya bud’e snn ya shigo d’akin tareda mai da k’ofar ya rufe, tunda yake da Ajiddeh bai tab’a ganin ta tashi Sallah batareda ya fad’a mata ba, ko ya fad’a sai lokacin da ta ga dama take tashi tayi, da sauri ya kawar da tunanin Ajiddeh yayi da sauri, daga gefenta yazo ya zauna, godiya ya dinga yiwa Allah cikin ranshi da ya bashi Batuul, a zuci yana bin duk ayoyin da take karantawa, kamar yau ya fara jin Qissoshin Annabawa dake cikin surar jin yadda take karanto shi, har saida tayi kusan rabi snn ta rufe ta shafa addu’o’inta ta maida Qur’anin kan bedside drawer, a hankali ta juyo ta kalleshi tace “Ina kwana”, wani farin ciki yakeji a ranshi da ganinta, ji yakeyi kamar ya d’auketa ya kaita wajen da babu kowa, inda babu abinda zai sameta sai farin ciki, ido ta d’an wara ganin yana kallonta bai amsa mata gaisuwarta ba tace “Yaa Abu ina kwana”, sai lokacin ya lumshe ido ya bud’e yace “Waye malamin da ya koya miki Qur’an?”, cike da farincikin tuna mata malamin da baza ta tab’a mantawa dashi ba tace “Malan Ahmad shine malami na, mey yayi?”, ta fad’a tana d’an yatsina fuska yace “Har Tajweed duk shi ya koya miki?”, ta kad’a kai tace “Har komai ma shi ya koya mana dukkanmu dasu Ahmad da Sa’eed”, yace “Ya complete sunanshi yake and yana ina yanzu?”, tunanin mesa yake son sani a hankali tace “Sunanshi Ahmad Abu Hamira Daiba, su Ahmad sun san inda yake, nasan har yanzu yana koyar dasu”, a hankali ya janyota jikinshi yayi wrapping duka hannayenshi jikinta yace “In na bashi kujerar Hajj da Umara this year yayi?”, da sauri ta shiga k’ok’arin juyowa taga dagaske yake nufin abinda yake fad’i amma bai saketa ba saima k’ara gyara mata zama da yayi ya d’aura fuskanshi kan wuyanta, duk da hijab a jikinta bai hanata jin d’umin numfashinshi dake sata jin wani a iri a jikinta ba, da k’yar ta iya bud’e baki tace “Dagaske?”, yace “Kuma a bud’e mishi Tahfeez, inaso in princess ta girma ya koya mata”, ya fad’a tareda sauk’e hannunshi kan cikinta, “Inaso in ta girma itama tana min irin k’ira’arki”, wani irin juyawa tayi ta rungumeshi sosai, yana jin yanayin bugun zuciyarta, shima d’in sake rik’ota yayi, kamar mai jin tsoron abinda zata fad’a tace “I love you”, ido ya lumshe ya bud’e yana jin kamar kullum ta zama magana da zata fito daga bakinshi, ta d’ago da sauri tana kallon fuskarshi tace “Yaaa Abu tun yanzu ka fara sani farinciki, am scared yayi min yawa and mayb you might change nan gaba”, kallonta kawai yakeyi for seconds ya kasa ce mata komai, da k’yar ya iya samu yace “Baki yadda da son da nake miki ba ko?, baki yadda I can forsake duk wani farin ciki nawa for you to be happy ba ko?”, kunya ce taji ta kamata, lafewa tayi jikinshi hannunta kan k’irjinshi tana jin yadda yake heaving a hankali tace “Na yadda, bana so ne yayi min yawa”, bakinshi ya d’aura kan nata ya rufe mata baki, saida ya d’ago yace “You deserve all happiness, ki kwantar da hankalinki kinji, you have got me for yourself”, shiru tayi lafe a jikinshi, d’agata yai cak ya kwantar kan gado yace “You need sleep, kwanta kiyi bacci”, ya shiga k’ok’arin cire mata Hijab d’in dake jikinta zai gyara mata kwanciya, kai ta girgiza mishi tace “Yaaa Abu da sanyi, I don’t want to remove the hijab”, bai ce mata komai ba har saida ya cireshi sannan ya rungumota jikinshi ya ja musu duvet yace “I will keep you warm”, murmushi kawai tayi tana tuna ranan da sukaje gidanshi a London yanda yayi keeping d’inta warm har ta gama duk abinda zatayi, a hankali ta matsa jikinshi ta gyara kwanciyarta, cikin kunnenta ya rad’a mata “are you still cold?”, juyowa tayi tana fuskantarshi da kyau tace “Will you always keep me warm all the time?”, ya saka hannayenshi duka biyun yana zagayeta yace “Always and forever”, daidai lokacin ta tuna da Ajiddeh, tana son ta tambayeshi ina take tana tsoron kada ya sake mata fad’a kamar na ranan, a hankali taji yace “Yaushe zamu koma gida?”, idonta a lumshe batareda ta bud’esu ba tace “Nanfa?”, yace “This is Ammah’s house”, ta zumb’uro baki tace “Ni I want to stay here”, yace “No gidanki kuma fa, wa zai zauna ciki?”, tace “Inada gida ne ni?, d’ayan ai gidanta ne, d’ayan Kumar kace na love of your life ne”, dariya yayi yace “So baki manta ba?”, tureshi tayi daga jikinta tace “Ni kam ka dena min dariya, a nan zan zauna”, yace “Toh bud’e idonki in fad’a miki wacece love of my life d’in?”, kamar yana ganinta ta murgud’a mishi baki, juyo da ita yayi yace “Plsss mana, ki bud’e idonki in fad’a mki gidan waye?”, a hankali ta bud’e idonta suna had’a ido tayi maza ta rintse su, dariya yayi ya d’agota yace “Fatima get up and listen, gidan nanfa nakine, I built it for the woman I will love, I designed everything for her, banida ra’ayin k’ara aure, I want to live with just a single wife and then Allah yayi Hauwa baza ta zauna gidan ba, then it was you, tun lokacin da akace zan aureki a raina nasa gidan zai zama naki, I then programmed everything ya koma naki, censor and all but God so kind you turned out to be the love I wanted, the love I wanted to give and take and there the house is yours, kinga sai mu koma ko tunda kinada gida, only I and you have access to wannan gidan”, jin shirun yayi yawa a hankali ya k’ira sunanta bata amsa ba, da wayarshi ya haska yaga bacci take, murmushi yayi tareda pecking goshinta ya gyara mata kwanciya suka kwanta bacci
3
Tunda Ajiddeh ta fara Magana Kulthum ke karanto Innalillahi wa inna illaihi raji’un, sosai ta tsorata da jin lbrn snn ta tausayawa Ajiddeh, tasan duk so ne ya sata aikata abinda take nadama a yanzu, ta jima kamin ta bud’e baki da k’yar “Kuskure kikayi Babba, shirka ba k’aramin laifi bane, da lokacin kin mik’awa Allah lamuranki da ko baki had’a da kowa ba yaron nan zai zama mijinki tunda Allah ya kaddara da aure tsakaninku, amma da yake komai rubuttace ne babu yadda za ayi ki tsallake hakan, gashi nan yanxu koda ya hak’ura bazai dena kallonki da abinda kika aikata ba, kada ki gaji da bashi hak’uri koda yana korarki ne, itama yarinyar da ki nemi ta yafe miki dan ita akafi zalinta, batada haqqin kowa sai dai nata da kuka d’iba, ni bansan Mummy d’inki ya take ba da zai yiwu sai kije ki sameta kuyi magana da ita, yanda na fuskanci mijinki yana sonki har yanzu, ki sameshi ki sake bashi hak’uri”, d’agowa Ajiddeh tayi da idanunta da suka rine tace “Baya sona, ya dena sona, cemin yayi in fita kada in sake nuna mishi fuskata”, ta fad’a tana share hawaye, Kulthum da har ranta ta tausaya mata tace “Fushi yayi, in ya huce zai saurareki, ki bashi lokaci ya sauk’o, snn ki fad’awa Babanki cewa bazai yiwu ki koma gidanshi ba, sbd yace baya son ganinki”, a tsorace Ajiddeh ke kallonta, batasan da ya Dad zai d’au zancen ba,haka tayi ta rarrashinta tareda kwantar mata da hankali, da yamma Dad da ya dawo duba ya jikin Kulthum da mamaki yake kallon Ajiddeh yace “baki tafi ba Hauwa?”, hawaye ne ya fara zirya idonta, da kyar ta samu ta iya cewa “Dad ya koreni, yace I should not show my face to him ever”, kallonta kawai yakeyi har ta gama magana, bayason raising family issue gaban Kulthum duk da hankali ya kwanta da ita amma baijin yin magana gabanta, Kulthum ya duba yace “ya jikin yayi sauk’i ko?”, wani awkward haka take jinta, ce mishi tayi “Alhamdulillah tana jin sauk’i”, yayi mata sannu da jiki snn yace in tana buk’atar abu ta fad’awa masu aikin a sama mata, ya juya kamar Ajiddeh bata d’akin ya fice, da gudu Ajiddeh tabi bayanshi, wani kallo da ya bita dashi yasa ta tsaya with pleading eyes tana so ya barta ta mishi bayani tukunna kamjn ya yanke kowane hukunci kanta, jiki a sanyaye ta durk’ushe wajen ta fasheda kuka, Daddy kam a ranshi yake tunanin irin tashi kaddarar, ko jiya da daddare saida Mum ta gama mishi tijara harda cewa mey ya tab’a mata duk zamansu, da yake ba mai son hayaniya bane bai biyeta sunyi surutu, masifa ta dinga yi akan zaman kulthum gidan, ganin yaqi kulata ta fice ta banko mishi tana cewa zai gani, duk sai tayi maganinsu, kanshi ne yaji yana sara mishi Dan abin yayi mishi yawa, Ajiddeh da yake ganin gara ita itama gashi tana fad’a mishi wani zancen daban, nan inda Ajiddeh ta durk’ushe ta jiyo k’arar wayarta, addu’a take a ranta Allah yasa Abutturab ne, da k’yar ta mik’e taje ta d’auki wayan, ganin Mum ce yasa ta maida wayar ta ajiye dan batasan mey zatayi mata ba in banda k’arin b’acin rai, har ya katse bata d’aga ba aka sake k’ira, d’auka tayi tasa a kunnen tana jiran jin mey zata fad’a mata, kamar a mafarki ta dinga jiyo abinda ake fad’a Mata, ta kasa yadda da Mum d’inta ce ake cewa tana Illorin, yaushe ta bar Abuja har ta tafi Illorin, wayar ce ta kubce mata daga hannu itama ta sulale tayi k’asa.Gabanta ne ke fad’wa, batason son tabbatar da abinda kunnuwanta ke jiyo mata, yaushe Mum ta bar gida har ta tafi Illorin, so take ta k’aryata zancen amma tunanin da wayar Mum aka k’irata ya sata saurin mik’ewa, a guje kamar wata mara lafiya tabi bayan Daddy, ba tareda tasan ta inda zata fara ba ta isa gabanshi tace “Daddy Mummy”, Kallonta yayi yanason jin mey ya samu Mummy, a ranshi yace mey ma zai sameta, a daburce cikin kuka tace “Daddy wai Mummy ce wai sunyi accident”, duk da maganar tazo mishi a ba zata bai nuna ba, dakewa yayi yace “Hauwa mey kuma kikeson sake aikatawa bayan wanda kikayi, burinku ne a kullum ku kunyata ku tozartani ku sani magana, dake da y’ar uwar taki duk kunyi nasarar cikar burinku, kun biyewa son zuciya, ki koma kiyi zamanki tunda shi d’in ya fiye miki shi kika zab’a”, wani sabon kukan ta fasheda hawaye d’aya na bin wani tace “Dan girma Allah Dad kayi hak’uri ka saurareni, wlhy ba k’arya nake ba, yanzun nan aka min waya da wayar Mum akace tayi accident hanyar Illorin, Dad dagaske ne dan ko da naje side d’inta bata nan, kayi hak’uri kasa a bincika muji ko itance dagaske”, kallon Ajiddeh kawai yake a ranshi yana tunanin abinda zai kai Zuwairah Illorin, wa ta ajiye wa take dashi can garin da har zata tafi bada sanin shi bs”, juyawa yayi ya tafi Side d’inshi a Ajiddeh na biye dashi a baya tana hawaye, yana k’arasawa d’aki ya d’auki waya yasa a bincika mishi ko dagaske ne abinda Ajiddeh ta fad’a mishi, ba a jima ba aka k’irashi aka tabbatar mishi da “Ehhh gaskiyane, matane uku da Driver d’insu sukayi accident d’in”, ajiyar zuciya ya sauk’e dan ya rasa tak’amaimai abin fad’a, tashi yayi zai fita Ajiddeh dake zaune tana hawaye gefenshi ta taso tace “Kaji ko Daddy, an tabbatar maka da Mummy ce ko?, Na shiga uku Dan Allah Dad muje mu dubata, wayyo Mummy na”,wani irin kallo da ya watsa mata ne ya sata saurin had’iye maganar dake bakinta, tun da take harara Dad bai tab’a yi mata shi ba sai yau, jiki a sanyaye ta koma ta zauna, fita yayi shida driver yana neman yanda za ayi a dawo dasu gida dan sai an had’a da police, baisha wahala sosai ba kasancewarshi d’an siyasa ko ina sunada mutane, +
Wanka tayi ta zauna bakin gadon daga ita sai d’an towel, shima lokacin ya fito daga toilet d’in yace “Bata kawo kayan ba har yanzu?”, kallonshi tayi ta zumb’uro mishi d’an k’aramin bakinta tace “Nace fa zanje In d’auko ka hana, nasan bacci takeyi ka tada ta”, bai kulata ba ya d’auko wayarshi ya k’ira Farida a waya, yana bugawa ta d’aga yace “Har kin kawo kayan kenan ko?”, kamar tana gabanshi ta girgiza kai tace “Yanzu nakeson in k’irata ta fad’amin wanda zata saka fa”, yace “Get the whole box here”, ido ta wara kaman yana gabanta tace “Kai Yaaa Abu, da nauyi fa”, bai jira mey zatace ba ya katse wayan”, kayanshi dake ajiye kan gadon ya d’auka ya sanya, kinkiman akwatin ta shiga yi a ranta tana mitar tada da yayi daga bacci, gefen Batuul ya zauna ya shafi gefen fuskarta tareda juyota ta fuskanceshi yace “Fushin meye ne wai har yanzu haka?”, ya fad’a yana shagwab’e mata fuska, d’auke kai tayi tace “Ni fa sanyi nakeji ka hana kuma inje in d’auko kayana”, kallonta yayi cikin ido da ya sata tayi saurin sadda kai k’asa yace “bana son kina stressing kanki, am there all the time”, ya kamo hannunta ya damtse cikin nashi, daidai lokacin Farida tayi knocking tareda turo k’ofan ta shigo da akwatin tana haki,Batuul na jin k’arar tab’a k’ofa dama ta janyo hijab d’inta ta saka, jan akwatin tayi har cikin d’akin ta snn ta dubi Abu tace “Ina kwana”, daga gani daga bacci ta tashi yace “Baki iya jiran izini ba kawai you barged into d’akin mutane ko?”, zumb’uro mishi baki tayi a ranta tace “Hmmmm ai saidai idan ba Yaa Abu ba”, a fili kuwa cewa tayi “yayi nauyi ne shinefa na shigo kuma saida nayi knocking”, idonta ne ya fad’a kan Batuul dake zaune daga ita sai d’an towel da hijab, duk ta shagwab’e fuska kamar zatayi kuka, batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba, dariya takeyi harda hawaye snn ta tsagaita dariyar tayi pointing Batuul tace “Ya Allah, you have started gaining weight, Affan have to hear of this, kin ganki kuwa?” Abu da ya tsaya kallonta da mamaki ya daka mata tsawa yace “kina da hankali kuwa?, c’mon get out kamin in tashi in sameki”, kallon Batuul da tayi raurau da ido yayi, yasan kuka take shirin mishi, Farida da ke tsaye wayarta ta ciro cikin aljihun rigan baccinta zata k’ira Affan, tsawa ya sake daka mata yace “Na fara wasa dake ko Farida?”, kamin tace wani Abu ya tashi ya fizgota ya karb’e wayan ya turata waje, dawowa yayi bakin gadon yana kallon Batuul dake jiran k’iris ta fashe da kuka baki a tab’e, a hankali tace “Dagaskene av gained weight?”, in banda iskanci irin na Farida babu ta inda yaga Batuul ta k’ara jiki, dalilin da yasa ma kenan bayason kaita gida sbd yadda duk ta rame, ya d’aura hannu kan wuyanta yana tab’a collar bone d’inta yace “I want you to, kin rame dayawa kuma banaso ni”, tasan bazai fad’a mata ba, cire hannushi tayi ta mik’e ta isa gaban human size mirror dake d’akin tana kallon kanta, itama d’in babu ta inda taga ta k’ara k’iba, tasowa yayi ya biyota gaban mirror ya rungumota ta baya tareda tareda sauk’e ajiyar zuciya yana shak’an k’anshinta masu dad’i, ido ya lumshe ya bud’e dai dai nan hawayen da take ta rik’ewa suka gangaro, da sauri ya juyo da ita yana girgiza kai yace “Glitter noo, kar kiyi kuka plss”, muje kisa kaya yau sai Farida ta fad’amin yadda akayi kikayi gaining weight” ya fad’a tareda kamo mata hannu, d’ayan hannunta ta saka kan nashi, juyowa yayi ya dubi fuskanta yaga duk sai glittering d’in hawaye suke, rungumota yayi, bai tab’a ganin mutumin da hawaye bai mishi wuyar zuba kamar Batuul ba, jawota yayi suka koma bakin gadon, a hankali tace “Nasan ban k’ara jiki ba but nan gaba in nayi fa?, you will stop loving me ko?”, yanzu ya sake tabbatar da harda yarinta cikin lamarin Batuul, dan kawai tayi jiki sai ya dena sonta?, he love her for whatever she is and whatever she will become of, wani light peck yayi mata a goshi ya rik’o hannuta cikin nashi yace “Hey look at me”, kasa d’agowa tayi ta kalleshi saida taji yace “Glitter look at me”, d’azu ma taji word d’innan daga bakinshi sai yanzu ta san da ita yake, sunaye biyu kenan ya saka mata yanzu, Haya da Glitter, har cikin ranta takejin sunan, a hankali ta d’ago ta dubeshi, Hannu yasa ya share hawayen dake shirin zubo mata yace “what will make you change the way you feel about me?”, shiru tayi ta kasa cewa komai saida yace “Uhmm ina jinki”, jiki a sanyaye ta girgixa mishi kai, yace “Ki bud’e baki kiyi min magana a hankali tace “Babu”, yace “mesa kike tunanin gaining weight zaisa in dena sonki, wa yace miki jikinki nakeso Haya, wa yace miki structure d’inki nakeso?, Ina sonki for who you are da kuma what you are yet to be, banason sake jin kin sake fad’an haka, zamuyi fad’a kinji ko?”, kai ta gyada mishi yace “Good” yana sa hannu cikin gashinta da bai bushe ba yace “zakiyi mura fa kina barin gashinki da ruwa”, tace “yanzu fa zansa kaya inyi drying d’inshi”, ta fad’a tana k’ok’arin tashi ya rik’ota yace “No ki bari in mun sake jik’ashi sai kiji dad’in drying da kyau”, sarai tasan abinda yake nufi da hanzari ta mik’e tana dariya tace “A ah nikam, I can dry it haka nanma”, dariyan yayi shima ya kamata ya zaunar kan stool ya shiga drying mata dogon gashin kanta mai santsi da shek’i, sai da ya gama snn ya taimaka mata ta shirya cikin navy blue lace mara nauyi mai k’ananan jan patterns yace su sauk’a ya fara jin yunwa, ya rik’o hannunta suka sauk’o dinning area, suna k’arasowa tayi maza ta janye hannunta cikin nashi, kallonta kawai yayi baice komai ba har ta zauna snn ya zauna, daga kitchen Ammah da Sadiq suka fito, da alama daga exercise yake saboda kayan jikinshi, yana riqe da apple yana taunawa biye da Ammah yana mata magiya, juyawa tayi ta dubi Sadiq tace “Kana jina fa Sadiq nace bansan zancen ba, ka samu Abui kuyi maganan dashi”, ta k’arasa dinning d’in, Da sauri Batuul ta tashi ta karb’i pan d’in dake hannun Ammah tace ” *Ammah Nda wattu* Ina kwana Ammah”, “Ammah da murmushi fuskanta tana goge hannunta tace ” *Bitti k3lewa selai, k3lewan fanema? Lafiya Kalau Bitti, kin tashi Lafiya?”, ta tambaya tana gyara tray d’in fruits, a kunyace Batuul ta ajiye pan d’in dake hannunta tace “Alhamdulillah”, ta dubi Abu tace “Ya jikin nata?”, Saida ya gaisheta snn ya amsa da Alhamdulillah, ya dubi Sadiq da duk ya shagwab’e fuska yana tauna Apple d’inshi yace “Shi kuma wannan mey ke damunshi?”, ya fad’a yana tambayan Ammah, Ammah ta zauna ba tareda ta dubi Sadiq ba tace “Ka tambayeshi gaka gashi, kunfi kusa inajin”, kallon Sadiq yayi yace “Whats wrong?”, a hankali Sadiq yayi wata magana da babu wanda yaji, Abu da ya had’e fuska yace “In ka shirya fad’an matsalarka ka biyoni ka fad’amin”, Ammah tace “Shima da kanshi yasan hauka yake shirin yi shiyasa bazai iya fad’a makan ba, ni bara in fad’a mishi yaji yasan rashin hankalin da yake min”, Ammah taci gaba tace “Wai aure yakeson a mishi”, daidai lokacin Abui ya k’araso dinning d’in yana cewa “wakeson ayi mishi auren?”, Sadiq da sam baiso Abui ya Karaso at this time ba yayi maza ya sadda kai k’asa, Abutturab tsabar mamaki kasa cewa komai yayi sai baki da ya bud’e yana kallon Sadiq d’in, Ammah tace “Wai Sadiq keson a mishi aure”, murmushi Abui yayi yace “Har ka shirya kenan, ka shirya kula da y’ar mutane”, d’agowa yayi suka had’a ido da Abutturab, Abutturab yayi mishi kallon you are not okay yace “wace yarinyar ce zata aureka bakada aikin yi?, Serving d’inma ba gamashi kayi ba bare ka fara maganan settling “, D’an kafad’a ya d’aga alamun am due fa snn yace “But ai inada gida, what else?” Sosai Sadiq ya bawa Abui dariya, Ammah da Abutturab kam ko kad’an abun wasn’t funny to them, Farida ce ta sauk’o sanye da kayan bacci da hula kanta tana danna waya, jin maganan da akeyi ya sata k’arasowa da sauri tana maida wayar cikin aljihu tace “Laaah Ammah ku baku San ma yarinyar bafa, wai fa Layla k’anwar Uncle d’in Aunty Amna yakeso, ina jinshi yana waya da ita kullum, ko wallpaper d’inshi picture d’inta ne, bara ma ku gani” taja kujerar gefen Abui ta zauna tana mik’a hannu zata d’auki wayarsa dake ajiye gefe, Hannu Sadiq yasa y make nata hannun, b’ata rai tayi ta zumb’uro baki ta kalli Abui tace “Abui kana ganinshi ko”, tunda Abu ya harareta tayi shiru ta d’auki plate ta d’ebi pomegranate tana sha, Sadiq ma harara ya sakar mata, Abui yace “Sadiq ba gida bane aure, it takes a lot fiyeda wannan, you are just 22, kana buk’atar time da kuma nutsuwa kamin kace zakayi settling, ka bari in ka gama Service ka samu aiki then you talk of settling amma banda yanzu, parents d’in yarinyar da kanta ma ba yadda zasuyi da zancen ba in ba aiki ka fara ba”, Ammah da tayi serving Abui soup tana mik’o mishi tace “Sadiq in baka rabani da shirman nan ba ranka zai b’aci, itama Laylan da ta biye maka”, Wani kallo ya jefi Farida dashi da ta tona mishi asiri, d’auke kanta tayi tana jin haushin make mata hannu da yayi, Sai da kowa ya nutsu yana cikin cin abinci Abu ya kamo hannun Batuul ta k’asa yana kashe mata ido, kallonshi tayi na ya sakar mata hannu, bai sake ba saima sunan Abui da Ammah da ya k’ira, a tare kowa ya kalleshi suna jiran suji mey zaice musu, Batuul dai gabanta sai fad’uwa yakeyi tana tunanin abinda zaice musu tana k’ok’arin kwace hannunta amma ya dad’a k’arfin rik’on, jin yayi shiru Abui ya maida hankalinshi kan abincin da yakeci, Ammah ce tace “Muna jinka”, a nutse yace “Ammah inaso mu koma ne, inada aikin dayawa that are pending”, tace “Dama can kai ne kayi zamanka, tunda taji sauk’i ka tafi abinka ka rik’a dawowa kana dubata, ido ya lumshe ya bud’e jin abinda Ammah tace snn yace “Ammah tare fa nakeson tafiya da ita, ba nan zan barta ba”, Wani kallo Ammah tayi mishi a taqaice tace “baza ta koma gidan nan ba, ka barta nan in ya so ka riqa dawowa kana dubata”, marairaice fuska yayi ya kalli Abui da puppy eyes d’inshi, yace “Ammah ba gidan nan zata zauna ba, tun kamin ta fara ciwo take d’aya gidana, Plss Ammah”, Abui yace “Anytime you are ready ka d’auki matarka ku tafi”, Kallonshi Ammah tayi zatayi magana yace “Meye amfanin barin nata da zaiyi a nan, ko ya tafi hankalinshi ba kwanciya zaiyi ba, su koma kawai zai ci gaba da kula da ita In sha Allah babu abinda zai sameta”, Badan ta yadda ba ta hak’ura, Abu kam dariya yayi yace “Nagode Abui, Allah ya k’ara girma da d’auka, Allah ya k’ara Nisan kwana, Allah ya gafartawa magabata yasa a gama da duniya lafiya”, “Amin” dukkansu suka amsa, dariya ma ya bawa Abui Dan kawai yace zai iya tafiya da matarsa shine duka wannan addu’a haka, yace “Kaje ka dubo Hauwa?”, gaban Batuul sai da ya fad’i jin sunan Ajiddeh, take expression d’in fuskan Abu ya canja jin sunan Ajiddeh, har idonshi ya fara canja launi yace “Abui am not ready, bana so inyi taking decision out of anger, kar inyi abinda we all will regret”, kai kawai Abui ya gyad’a mishi alamar he understands him, Batuul dai gaba d’aya kanta ya gama d’aurewa, mey zaiyiwa Ajiddeh da har zaisa suyi regretting, kuma meye sa tunda ta farka bata gidan, tana sak’e sak’enta har suka gama cin abincinsu,
9
Da yamma aka dawo dasu Mum asibiti aka wuce dasu kai tsaye, ita Jainaba, sai wata mata da Dad d’in bai Santa ba, babu wanda baiji mugun ciwo ba cikinsu, Da ya dawo gida suka taho tareda Ajiddeh, in banda kuka babu abinda Ajiddeh keyi, ta rasa bakin cewa komai, Zainab ma sai da Daddy ya qirata snn ta taho, itama kukan ta saka ganin yanayinsu, Dad baice musu komi ba ya tafi wajen Doctor, Doctor yayiwa Dad bayanin cewa Mum ta sami raunika hannu da k’afa da kuma spine d’inta, babu ita babu tafiya a yanzu, d’ayar matar kuma Brain d’inta ya tab’u amma suna fata in ta farfad’o a samu a sake dubawa, sai Jainba ita kuma hannayenta ne kawai suka ji raunin sai kuma kafar ta da sai an yanke sbd ya lalace, tunda doctor ya fara magana Dad ke danne zuciyarshi yana addu’a sbd wani irin abu da yakeji yana taso mishi, saida likita ya gama bayani yayi mishi godiya ya fita, gida ya wuce kai tsaye dan bayajin zai iya komawa cikin d’akin, har ya isa gida yana tunanin abinda ya kai Zuwaira Illorin.