YAR MAKIYAYA CHAPTER 6

YAR MAKIYAYA






CHAPTER 6




Matsowa yayi daf da Suraj gami da had’a masa lafiyayyun Marika har uku a fuska had’awa da kalmomin “Am very ashamed of you!” Harara ya watsa wa Mom cike da b’acin rai ya nufi sashen sa, Suraj na d’ago kai suka yi ido hud’u da Ameer ya nad’e hannuwan sa a k’irji ya jingina da bango yana Murmushi. Fice wa Suraj yayi a zuciye idanuwan shi sunyi jajir ,Habeeb dake tsaye cike da mamaki ganin Suraj ya fice shima ya yunk’ura zai bi bayan shi amma sai Ameer ya katse mishi hanzari ta hanyar shiga gaban sa yace “Haba d’an uwa! Long time no see! Gaskiya duk ka chanja welcome back nasan kaji dad’in zuwa Belel ko?” +

Murmushi Habeeb yayi mai nuna alamar *go to hell* ya ture Ameer gefe ba tare da yace komai ba ya fice.

Cikin mota ya hango Suraj kai had’e da stirring mota , k’arasa wa yayi ya bud’e motar ya shige ba tare da ya furta ko kalma ba ya zuba wa Suraj ido.
Ya dad’e sosai kansa a kan sitiyarin kafin ya d’ago yayi wa mota key cike da zafin nama ya fisgo motar har saida ta sauya k’ara, a d’ari ya fita ,lamarin da yayi matuk’ar tsorita Habeeb wanda babu abunda yake buk’atar yaji kamar explanation akan abun da ya faru tsakanin Dad da kuma Suraj.

*Oh hoho! Dad kuma? Me ma ya dawo da shi? Mutumin da zai yi wata guda? I know that’s the question in everyone’s mind Amman amsar tana wajen Dad shi kad’ai*

Tun ficewar Suraj da Habeeb mom bata motsa daga inda take tsaye ba har Ameer ya fito daga sashen Dad ya fice sannan ta kwashi jiki tayi sashen Dad. Tsaye ta iske shi ya nad’e hannuwan shi ta baya ya d’aga kai sama yana fuskantar window.

A sanyaye ta ce “Barka da dawowa, actually we are not expecting you today ,sam bamu san zaka zo ba gash…….
Bata kammala maganar ta ba ya d’aga mata hannu chak ta dakata tana kallon shi

“Razia am disappointed in you! Kin bar yaro yana abunda ran shi yake so don kawai kina so ki ja min raini , Ashe wadancan talakawan sun fini da magana ta muhimmanci? Suraj har zai iya d’aga wa Saeed hannu saboda wani talaka? Wannan duk laifin ki ne, kina da bakin tambaya ta Yaya hanya? Toh ba lau ba domin ko wanne numfashi, kowanne second,minute da kuma Awa nayi shi ne d’auke da bak’in cikin wannan yaron kin ji dad’i? Ina tambayar ki are you relieved? Ko kun d’auka aikin wata guda bazan iya yin shi cikin Mafi k’ank’antar lokaci bane? Now if you don’t mind Razia I need some space ina so na huta ,and Idan kin samu daman ganin d’an naki ki sanar da shi ina son ganin shi in yana da lokaci now please leave”.

Bakin ciki irin wannan Mom bata tab’a jin shi a rayuwa ba, a iya zaman ta da Abdul-malik yau ce rana ta farko da ya yi mata kalamai da suka k’ona mata zuciya, iya sanin ta bata san takamammen laifin da tayi ba. Suraj ba yaro bane babu aibu don ya yi cudanya da talakawa? Su kansu talakawan miye aibun su, we all are humans , kuma dukkanin mu bayin Allah ne babu wanda yafi wani a wajen Ubangiji.

Ba tare da ta sake magana ba ta fice daga d’akin tana kwalla, jin fitar ta yasa Dad ya juya yana kallon k’ofar.

*******************

“Suraj pls speak to me, at least say something, jiya ka ce min Dad baya gari all of a sudden se gashi kuma ma daga zuwa se mari saikace wanda ka aikata babban laifi? Sannan miye wancan Ameer d’in yake yi? Kasan shi in ka ganshi a guri tabbas akwai wata kullalliya da yake kullawa”

Suraj ya d’ago kai a hankali yana kallon waje ta gilashin motar yace “Duk abunda ka gani Toh ka tabbata a tsakani akwai Ameer, he’s been against me tun da Nazo”

Daga farko har k’arshe Suraj ya kwashe labarin abunda ke faruwa ya sanar da Habeeb, tsabar takaici bai san sanda ya doki k’ofar motar ba wanda tuni ta bud’e ya fice yana shafa gashin kansa da hannuwan shi biyu, fitowa Suraj yayi ya jingina da da motar yana kallon how frustrated Habeeb is. Juyo wa Habeeb yayi ya k’arisa daf da Suraj ya rik’e kafad’un sa yana jijjiga wa ” You have to be a man, dole ka mayar wa Ameer da martani ,teach him a lesson, bazai yiwu ace kullum yana yin nasara ba a kanka yanzu tunda ina nan I won’t let him win not anymore!”

Had’e rai Suraj yayi gami da d’aga gira sama yace “wait a minute! In na tanka mishi it will sound as if he wins,kawai ka rabu da shi in the end bazai ci ribar komai ba”.

Habeeb ya yi dariya ya dubi Suraj cike da kulawa sannan ya ce

“Kawai a rabu da shi? You mean to let him be! Come on Suraj! Ameer is busy tarnishing you image a gun mahaifin ka, someone who should be proud of you is very disappointed in you! Kawai dalilin tuggun da yake shirya maka, yana kwace maka duniyar ka in fact he has taken your world from you and is ruling it yadda yaga dama, dole ka motsa kafin ya taka rawar shi na gaba, Suraj kai d’an uwa na ne kuma bazan bari wani Yayi maka yadda yaga dama ba.”

Murmushi Suraj yayi ya dafa kafad’ar Habeeb yace “I know Bro , thanks for your concern and care.”Tun daga saman tsauni ta hango motar sa, da gudu ta gangaro tana dariya , cikin dogin ciyawi ta dinga bi ko a jikin ta. +

    Tana isowa wajen ta Sunkuya tana haki hakan yasa Suraj da Habeeb suka juyo a lokaci guda Habeeb ya kalli Suraj yaga sai Murmushi yake ya nad’e hannu a k’irji Tab’e baki Habeeb yayi yana shafa hab’ar sa , a hankali ya d’an matsa kad’an kusa da ita yana k’ok’arin ganin fuskar ta.

   Karaf d’aya ta d’ago tun k’arfin ta har saida suka yi gware da Habeeb da sauri ya ja da baya ya k’ank’antar da idon shi yana mulmula goshin sa ita ma haka. Saida suka gama jin zafin sannan ta juyo rik’e da kunkumi cikin had’e rai tace

*waye kai!!*?  Habeeb ya dubeta har zai yi magana ya kasa baki ya hangame maganar ta k’i fitowa se cewa yake “mam… Mam…maam.”

   Matsowa tayi kusa da shi tace “dallah kayi magana ka tsaya se mamammm kake yi tamkar kurma”

Da kyar Habeeb yayi k’ok’arin cewa *maciji* yayinda suka had’e baki tare da Suraj a karo na biyu *Maciji*

    Laila bata ankara ba taga maciji bak’ink’irin dashi ya fasa mata kai ai kuwa kafin kifta ido sai hangota nayi ta k’ank’ame Suraj gami da nad’e hannuwan ta a Wuyan shi tuni shima macijin yayi hanyar sa Habeeb kuwa ya jingina da mota ya nad’e hannuwa a k’irji yana kallon su.

  Ganin basu da niyyar sakin junan su yasa Habeeb gyaran murya yana duba agogon hannun sa
  “Macijin ya  kai kamar mintina biyar da tafiya ai mannewar ta isa haka sai ki sake shi ai”.

  Da sauri ta sake shi ya gyara zaman rigar sa ,kowa ya nemi Kalmar fad’a daga baki amma sun rasa sai Kame Kame suke 
  Habeeb ya matso kusa da su ya ce

“Kai ya isa haka nan Kame kamen kawai kai mata bayani a kai na saboda d’azu ma naga ba don maciji ba da shaqe ni zata yi kuma wannan kana ganin ta haka  Ba k’aramar madakiya za’a yi ba wallahi yanzu se ta kassara ni.”

  Wani mugun harara ta watsa ma Habeeb ,da gangan ya b’oye a bayan Suraj yace

“Kutmelesi! Kaga wasu idanuwa,? Kai Suraj amma wannan baturiya aka so yi ko?”

  
Suraj ya make shi a hankali yace “come on buddy you are irritating her stop it please”.

   In a serious tone Habeeb ya ce “Yi hak’uri, suna na Habeeb d’an uwan Suuuuuuraj” ya fad’a ne a yanayin zolaya hakan ya bata dariya sosai Suraj ya d’an gyara murya yace “me kike yi a nan ke kad’ai.
  “Kiwo nake daga saman tsauni na hango motar ka shine na taho, yau tun safe naji ka shiru, Zubaina sun je Mubi tare da baffan ta, Yaya Junaidu kuma yana aiki”

   Kai Suraj ya yi  gyada yace ” Toh kawai ma mu tafi mu sha kiwo! Ya kashe mata ido Habeeb ya Mak’e kafad’a ya ja da baya yace

“Ku kuje babu yadda za’a yi naje kusa da saniya ma balle na kiwata ta, kaje ka dawo ina mota ina jiran ka. Harara Suraj ya watsa masa tuni Habeeb ya ja y’ar tsaki “mtsew! Toh muje d’in Amma fa ka sani sam bazan tafi ina farin ciki ba ,kuma nishad’i da annashuwa na duk zasu ragu wallahy”

  Suraj da Laila ba su da aiki se dariya  suna gaba yana bin su kafin ya isa inda suke zai kai tsawon taku goma sha biyar ko sama da haka…

  ******    ****** 

      Tana fita d’akin ta tanufa zuciyar ta fal bak’in ciki tana kwalla, wani zuciyar na ce mata ta koma Egypt wani kuma na hana ta, haka ta zauna cikin k’unci har Kusan La’asar.

  Tun daga main entrance na gidan yake kwala mata k’ira kai kace makaho, wata maid ya tambaya 
“Hey Ena Mom take? Yau naga bata falo”
“Tana d’akin ta yallabai” ta amsa cikin rusuna wa, tare da Habeeb suka haura staircases zuwa sashen Mom Suraj har lokacin k’iran ta yake.

    Daga jingine da take a jikin gado ta jiyo k’iran Suraj da kuma takun k’afafu wanda ta tabbata nashi ne, 
“In har Suraj ya ganni in this state za’a samu matsala” 
Da sauri ta mik’e ta nufi bayi tana share hawaye, wanke fuskar ta tayi, sannan ta
fito tana goge fuskar ta da towel ,hango shi tayi tsaye a bakin k’ofa Habeeb kuwa yana waya kan resting couch dake wani gefe a d’akin. Tura k’ofar yayi ya fara takawa yana kallon fuskar ta wanda tayi pale , tuni yanayin Suraj ya sauya coz he knows when Mom is in a bad mood. Hannun ta ya rik’e yace

“What happened? Your eye’s ! Have you been crying? Mom! You look pale and…..” Bai k’arisa ba ta dakatar da shi

“Yeah, ciwon kai ke damu na gashi ma na kasa barci, shine na sha magani yanzu haka bacci nake ji zan kwanta.”  Pillow ya gyara mata ba tare da yace komai ba, ta kwanta sannan ya ja blanket ya rufe ta da shi ,Habeeb yayi mata sannu  shi kuwa Suraj bai ce k’ala ba ya nufi k’ofa zai fita bayan Habeeb ya fice.

  “Suraj” ta k’ira sunan shi juyo wa yayi yana kallon ta ba tare da ya furta kalma ba.
“Baban ka yana neman ka yace ka same shi any time in ka shigo”.

Murmushi  Suraj yayi ya dawo yana kallonta kafin yace “daman na sani, babu wani ciwon kai, idanuwan ki basuyi kama da na mai ciwon kai ba ko na me jin bacci ,kama kawai suke da na wanda ya dad’e yana kuka , a desperate person, ba zan tambaye ki dalili ba saboda na san dalilin  amma zan rok’e ki dan Allah kiyi hak’uri, let go please”

Kai ta girgiza kawai shi kuwa ya tashi ya fice cike da jin rashin dad’i a rai. Kai tsaye ya nufi sashen Dad….Da sallama ya shiga, Dad ya amsa ba tare da ya d’ago kai ba idanuwan shi kafe kan system nashi. Kujerar dake gaban shi ya nuna wa Suraj yace ” Sit, we need to talk” 
Ba b’ata lokaci Suraj ya ja balance a kan kujera ya zauna yana kallon Dad wanda har bayan mintina biyar bai ko d’ago kan sa ya dubi Suraj ba sedai yakan kurb’i Shayin dake kan table d’in, a nitse yake harkar gaban sa Suraj ya zuba masa na mujiya har ya kammala ya rufe laptop nashi sannan ya kurb’e ragowar Shayin sa.

   “Ammm…. Suraj, na k’ira ka nan ne don muyi magana man to Man, mu ajiye individual differences a gefe, to be frank nan da watanni uku masu zuwa na yanke shawarar aura maka Khadija y’ar aboki na, Amma ina so in ji opinion naka in akwai wanda kuke tare coz I don’t want to be the bad Dad in the end.

   Zuciyar Suraj Saida tayi bugun da bata tab’a yin irin sa ba har ya mik’e  “Dad ina da wanda nake so”
Ya fad’a a tak’aice bai ma san yayi maganar ba domin ya girgiza.
“Wacece ita is she from Egypt? “A’a a nan take sunan ta Laila”

   Mik’e wa Dad yayi cikin tashin sense yace “A nan Belel? Y’ar waye a Belel da har zata samu matsayin auran irin ka?

  Suraj ya tabbata in har Dad ya san da y’ar makiyaya suke soyayya Toh akwai matsala, baya son rabuwa shi da Laila ,kuma in yayi shiru dad zai aura masa khadija wanda bai tab’a so ko k’auna ba, he wants Laila badly kuma rasa ta zai janyo masa illa dan haka ya yi k’arya yace 
  “No Dad Laila ba y’ar Belel bace , y’ar k’anin baban Habeeb ne da ya rasu kuma a gidan su Habeeb take a KADUNA Mun had’u tun a school kuma Ka tambayi Habeeb ma kaji”

Shiru Dad yayi na d’an wani lokaci yana nazari “Gidan su Habeeb? How comes ban sani ba? I should have known her, Y’ar k’anin baban Habeeb?” Kai Suraj ya gyada zuciyar shi na tsere da bugun ta, yana jiran jin abunda zai fita daga bakin Dad amma se Dad yace “shikenan, zaka iya tafiya sedai ina so yarinyar ta zo Belel I want to meet her.
Zuciyar Suraj saida ta yi bugun da bata tab’a yi ba babu shiri ya damk’e k’irjin sa gaba d’aya yaji wuta ta d’auke a idon shi, Dad ya dafa shi yace “Are you alright?” Kai ya gyada kamar k’adangare bakin shi ya kasa furta komai , se yanzu

“Ammm Dad ina ga bazai yiwu ka ganta ba da wuri haka don last week mukayi waya wai zata tafi Istanbul tare da mahaifiyar ta ,dake ma a can take karatu, kuma yanzu zai kai four months kafin su dawo amma in ka damu zan iya mata magana sai ta zo in yaso se ta koma daga baya”.

  “A’a, baza ayi haka ba, Allah ya kai mu nan da four months d’in in ta dawo se ta zo coz I want to see my daughter in law” kai Suraj ya jinjina ya mik’e Allah Allah yake ya bar sashen Dad kafin ya sake fad’a masa abunda hankalin sa bazai d’auka ba balle ya k’irk’iro k’aryar da zai masa.
Dad kuwa ido ya zuba wa Suraj har ya fice sannan ya jingina kan sa jikin kujera yana maimaita sunan Laila cike da mamaki bai tab’a jin sunan ba bayan yasan cewa gidan su Habeeb ba bak’on sa bane, har ya d’auki waya zai k’ira Dad d’in Habeeb wayar sa tayi ringing ya d’auka, k’ira ne daga business partner d’in shi wannan k’iran kad’ai ya isa yasa Dad ya manta da k’iran da zai yi wa Baban Habeeb saboda yana dad’e wa a waya when it comes to business.

  Sauri yake kamar k’afar sa zata fita daga jikin sa direct ya shiga kitchen da kyar ya lalubo ruwa a fridge ya bud’e, kafa baki yayi ,qut qut qut, ya kwankwad’e duk da haka zufa ya dinga karyo masa,sai kace an riga an aura masa khadija, tashin hankali ne k’arara a fuskar sa.
Wata hadima ce ta k’araso inda yake tana tambaya ko akwai abunda yake buk’ata ,girgiza mata kai yayi kawai ya duka’d da kai k’asa tuni har idanuwa sun yi jajir.

  Har bayan isha Suraj bai shigo gida ba Habeeb babu inda bai duba ba har sashen mai martaba kuma gashi motar sa tana nan, dawo wa yayi sashen Mom inda ya iske ta kan sallaya tana addu’o’i ,saida ya jira ta idar sannan ya ce

” Mom ban ga Suraj ba ,I taught yana nan ne ma dan babu inda ban duba shi ba amma baya nan kuma ba fita yayi ba, tun d’azu da na bar shi a d’akin ki”  
“Baya nan kuma? Ta tambaya surprisingly dan tasan k’arfe Tara bai yi masa a waje yawanci”

  Habeeb ta tura d’akin Dad ya duba ko Suraj d’in yana nan,  ba b’ata lokaci ya nufi chamber d’in Dad.

“Habeeb! Come in please, bamu samu zama ba tun da ka zo, take a seat”
Maganar Dad kenan wanda yasa Habeeb ya rusuna ya gaida shi sannan ya zauna.

“Tell me! akwai wata matsala ne? You look disturbed”.

Eh daman nayi zaton Suraj yana nan ne nayi ta neman shi ban ganshi ba.
“Tun d’azu ya fita ina tsammanin har yanzu yana masallaci don shi kad’ai na bari d’azu bayan kowa ya fita go check him out” mik’e wa Habeeb yayi ya nufi k’ofa 
“Habeeb!” Dad ya kira shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *