FETTA
CHAPTER 12
Suraj ya tashi yaji gidan sam baya masa dad’i, unlike before, Ruwan tea kad’ai ya sha, Ya kira Sabeer ya umarce sa ya mishi booking flight na yamma, da ya gama ayyukan sa na yau zai wuce, baya jin zai iya k’ara kwana, +
Yaba Kamal 200k yace ya siyo masa laces masu kyau, Ya amsa da ladabi.
Shiri yayi, Ya fice zuwa sabgogin sa.
Fetta da tunanin yadda zata taimaki Suraj ta tashi, Zuciyarta ta gama amince mata ta taimake sa ko dan Hajiya, idan ya samu kariyar arzik’i zai shafeta, Yasmeen tazo mata a rai, ita zata taimaka mata, Wayarta ta d’auka tayi dialing number ta, bugu d’aya ta d’auka, Bayan sun gaisa tace “Please if you are free kizo, I need your help”, ” Ina da lecture 10-12 idan na fito, zan zo”, “Sai kin zo”, ” Olryt”, Tayi hanging up.
Pass 12 ta kammala ayyukan gida, Tana zaune falo tana lazimi, Taji knocking, Ta kalli agogo 12:30pm, Tasan Yasmeen ce, Ta tashi ta bud’e, “Amaryar Suraj”, Tace ” Hmm”, Ta mayar da k’ofar ta rufe bayan Yasmeen ta shigo,
Ta zauna kan kujera tana fad’in “Wash wallahi na gaji”, ” Sannu”, “Yawwa yunwa nake ji”, ” Gashi banyi girki ba”, “Fetta bakya son cin abinci, shiyasa kuke fad’a da Suraj”, ” Uhmm yunwar ce bana ji”, “Allah ya baki ciki mai sa cin abinci”, Ta zaro ido tace ” Ciki”, Yasmeen ta d’aga kai tace “K’warai”, ” Yanzu kina mun fata na haihu da mutumin da ba zama na har abada zamu yi ba”, Yasmeen tayi murmushi tace “Samar mun abunda zanci, cikina kuka yake”, ” Ko na dafa miki indomie”, “Eh”
Kitchen ta shiga ta had’a indomie, Cikin minti 30 ta kammala, ta juye a plate ta kawo mata, Da lemo mai sanyi, Loma d’aya tayi tace “Fetta Allah ya baki baiwar girki, indomie ma ta fita daban”, Tayi dariya tace ” Santi kike”, “Allah kuwa, idan zan yi aure zan zo koyon girki”, ” Allah ya kaimu, ya nuna mana”, “Amin Amin”
Bayan ta gama ci ta natsa, Fetta ta nisa tace “Kinsan Alhaji Tambari?”, Yasmeen tayi nodding kai tace ” K’warai kuwa farin sani, a garin nan waye zai ce bai san Alhaji Tambari ba”, “Ba sani na suna da fice ba, ina nufin personal sani”, ” Na san shi k’warai, abokin Daddy ne kafin ya rasu, yana zuwa gidanmu, Matarsa Aunty Amina itama tana zuwa, tana da kirki sosai har gobe tana kawo mana ziyara”, “Mashaa Allah” Ta furta tare da jin alamun nasara, “But why asking?, meye had’in ki dashi?”
Ta zayyane mata komai bata b’oye mata ba, Yasmeen tace “Tabbas akwai shirin da ya shiryawa Suraj, yana matuk’ar son Tasleem da farin cikin ta, he will do everything for her, ko rayuwarsa zai iya sadaukar mata”, Fetta ta jinjina kai tace ” Yanzu ina zaki samu mana information”, “Through PA d’insa”, ” How?”, “Yana matuk’ar sona, nice bana wani kula sa, zan yi k’ok’arin shiga jikinsa ko zan samu wani bayani”, ” Yawwa ki taimaka Yasmeen please, ki shiga jikinsa, zan dinga fad’a miki yadda zaki yi”, Tayi murmushi tace “Baki da damuwa, burina na taimake ki a ko da yaushe, Ki k’ara k’ima da martaba a idon Suraj”, Fetta tana mamakin son alak’arsu da Suraj da take, ina ga Hajiya kad’ai ta fita son auren su.
Ta jima suna tattaunawa kafin ta wuce, Fetta na nagode ma Allah da ya kawo Yasmeen cikin rayuwarta, ta zame mata tamkar yar’uwa ta jini.
*6:15pm*
Jirginsu Suraj ya d’aga from Lagos to Kano.
Fetta ta idar da sallar magrib, Tana zaune kan sallaya tana karatun Qur’ani cikin k’ira’arta mai dad’i.
STORY CONTINUES BELOW
Suraj da sallama ya shigo falon, Ya sauke ajiyar zuciya sakamakon k’amshin da ya daki hancin sa, wanda ya kama falon permanently, Gidansa tsaf, Duk dawowar da yake unexpected bai tab’a tarar dashi kaca-kaca ba, Ya yarda tana da tsafta, Driver sa yabi bayansa da ledar laces, da briefcase, Bai tafi da kaya ba, haka bai dawo dasu ba, Yana da kaya a can.
Zama yayi a falo yana sauraren karatun ta, Yana matuk’ar son k’ira’arta, Har lumshe ido yake.
Kiran sallar isha’i yasa ta tsaya, tayi addu’a ta mik’e dan gabatar da isha’i,
Jin tayi shiru ya mik’e ya shiga, Sam bata ji shigowar sa ba, Ta mik’a dukkan hankalinta wurin bautar Allah, Briefcase d’insa ya ajiye ma’ajiyar sa, ya zauna gefen gado, yana zare safa, Har ya kammala cire kaya, ya shiga toilet, bata idar ba.
Ta sallame sallah, juyowar da zatayi suka yi ido hud’u, Fad’uwar gaba taji “Yaushe ya dawo”, Ta tambayi kanta, Juyawa tayi ta cigaba da lazimi, sai da ta kammala, Tace ” Sannu da zuwa”, “Yawwa”, ” An dawo lafiya?”, “Lafiya” Ya amsa a dak’ile.
Tana shirin nad’e sallaya, Yace “Barta”, Ta ajiye ta fice, Kitchen ta nufa ta had’a masa girki tasan zai buk’ata, Bata san wane irin mutum ne shi da baya sanar da dawowar sa, sai dai a gansa kamar aljani, Ta kawar da tunanin ta hanyar fara kayan miya.
Jollof na taliya da kifi ta masa, shine mafi sauk’i da zata iya, Cikin k’ank’anin lokaci ta kammala, Daga falo ta jiyo muryarsa ” Ki zuba a plate ki kawo mun bedroom”, “Ka hutar dani” Ta fad’a a ranta, Ta zuba masa a plate, ta rufe da wani, Ta ajiye a tray ta saka fork, ruwa, lemo da cup.
Da sallama ta shiga d’akin ya amsa, murya k’asan mak’oshi, Ta ajiye abincin gabansa, Yace ta jira ya gama ta fita da kwanukan, bata so haka ba, ba musu ta zauna k’asan carpet, ta jawo wayarta ta shiga whatsapp.
Yana ci but hankalin sa na kanta, Chatting d’in ya tafi da dukkan tunanin ta, tana ta murmushi,
“Dawa kike chatting?”, Ya jefo mata tambayar da bata zata ba, ” Friends “, Ta bashi amsa, Ya cigaba da cin abincin sa tamkar baya shi yayi tambayar ba, kuma bai ji amsar data basa ba.
Wayarsa tayi ringing, Ya umarceta ta mik’a masa, Alhaji Tambari ta gani a saman screen, Ta tsurawa wayar ido, sai da ta tabbatar ta haddace number, Tana mik’a masa ta tsinke, Mugun kallo ya watsa mata Yace “Me kika tsaya?”, ” Ba komai”, Ta bashi amsa murya sanyaye, tana zama, number ta rubuta a wayarta tayi saving,
Wani kiran ya sake shigowa, Yayi receiving,
A speaker ya saka, saboda abinci da yake ci, Bayan sun gaisa.
Alhaji Tambari Yace “Ban ji ka ba”, ” Tafiya ta kamani, yau na dawo, akwai kud’in da nake expecting, jibi In Shaa Allah zan bayar a fara”, “Toh Madallah ayi aikin da kyau fah, yadda gwamnati zata ji dad’i though bani da fargaba akan ka”, ” Kar ka samu damuwa”, “Toh Shikenan”, Sukayi sallama ya kashe wayar,
” Mayaudariya kana so kayi manipulating nashi”, Fetta ta fad’a a ranta, Zuciyarta na ingizata tace masa me zai hana yayi bincike kafin ya bayar, wani b’angare na gargad’inta zai iya gwaleta ko yace ta masa shishisshigi tana sauraren wayarsa, kuma hasashe take bata da tabbas.
“Zo ki d’auka”, Ya katse mata tunani, Ya cinye tass, ta d’auka a ranta tana fad’in ” Baya wasa da ciki”,
“Zaki ga Leda a falo, ki d’auka”, ” Na d’auka nayi me dashi?”, Ta tambayi kanta, “Kije kiga ledar meye”, Ta kai kwanukan kitchen ta wanke, bata son tara wanke-wanke.
Laces masu azabar kyau ne cike da ledar, Ta shiga fiddo su cike da murna, She couldn’t believe ya siyo mata, ” Ashe zai siyo mun, kai amma naji dad’i”, Cike da murna ta d’auki ledar ta nufi d’aki,
STORY CONTINUES BELOW
“Nagode k’warai sunyi kyau, nawa ka siyo na baka kud’in”, Wani mugun kallo ya jefata mata yace ” Nace miki ina buk’ata, ko na miki kalar mabuk’aci”, Yace kyauta ya siyo mata yake jin nasara, Taji dad’i sosai na siyo mata kyauta, bata damu da furucin sa, ta soma sabawa da halinsa, Haka yake naturally, she is hoping ya canza, “Allah ya saka da alkhairi”, Cikin zuciyarsa ya amsa da ” Amin”, Yaji dad’in addu’ar.
Washegari da zai fita, ta tambaye sa tana son zuwa gida, Ya amince ba musu yace Driver ya kaita, kuma ta saka hijab, “Salon takura, dama shi zansa ai nasan darajar aure”, Bata san maganar ta fito fili, ” Ni kike fad’awa magana, wallahi zaki karb’i hukunci kuma na hana ki zuwa”, Tayi narai narai da ido tace “Yi hak’uri” Bata shirya karb’ar hukunci ba, kuma tana son zuwa gida, wata biyu da aurenta bata je ba.
Banza yayi da ita ya fice.
Cike da murna da zumud’i ta shirya, Cikin kud’in sana’arta ta zari dubu ashirin, Ta bud’e akwatin lefenta ta d’auki roll na sabulu, da turare guda biyu,
Ta fito cikin shirinta na atamfa, da hijab iya gwiwa, Kallo d’aya zaka mata kasan ta samu hutu.
Aliya da Mallam sunyi farin cikin ganinta, Suna ta yaba kyan da tayi, Ali da ya dawo makaranta, da gudu ya rungumeta, Ta shafa kansa tace “Dan’ makaranta”, ” Aunty kullum ina cewa Umma ta kaini wurin ki, sai tak’i tace Uncle allura yake”, Ta turbune fuska tace “Kai Umma shine bakya kawo mun shi”, ” A’ah ba zaku iya da k’iriniyar Ali ba”, “Allah zan iya, ni dai a rik’a kawo mun shi”, ” Toh naji”
Rumaisa ta shigo gidan, Mamanta ta aikota, Tace “Amarya saukar yaushe?”, ” Ban dad’e da shigowa ba”, “Kinga kyan da kika k’ara”, Tayi dariya tace ” Yaushe kika dawo?”, “Jiya wallahi mun zo hutu”, ” Allah ya bada nasara”, “Amin”, Rumaisa na makaranta ABU ZARIA, Sun tab’a hira da karb’i sak’on da aka aikota ta fice.
Fetta sai bayan sallar la’asar ta kira driver yazo ya maida ita, Yace mata Maigida yace kar ya sake ya barta ta koma a k’asa, da ta koma abunta ba nisa.
Dubu goma taba Mallam da turare, Aliya dubu goma da sabulu, Sunyi farin ciki sosai, suna tasa mata albarka, Da ganin amfanin rik’on maraya, Sun kuma yaba da hankalinta da bata wofantar dasu ba.
Yasmeen ta d’auki kiran Mukhtar(PA Alhaji Tambari), Kullum sai ya kira ta, bata d’auka, Cike da murna ta d’auka, Ya shiga tambayar lafiyarta ta amsa, Ya tambayi dalilin da bata d’aukar wayarsa tace school ya sakata gaba, Ya buk’aci zuwa ganinta, Ba musu ta amince, Cike da murna yace zaizo bayan isha’i.
Ana idar da sallar isha’i, Mukhtar yasha wanka sai zuba k’amshin turare yake yazo gidansu Yasmeen, Ya kira wayarta yace gashi bakin gate,
Ta fito sanye da mayafi na doguwar rigar jikinta, ya zuba mata ido yana jin kamar ya had’iyeta, Da sakin fuska tace ” Sannu da zuwa”, “Yawwa gimbiyar mata”, Ta masa iso cikin gida suka zauna a fararen kujeru na roba, Ta kawo masa ruwa da lemo, yasha yana ta bayyana mata sirrin zuciyarsa.
Ta danna recorder na wayarta ta nisa tace ” Wai da gaske gwamnati taba Alhajin ka kwangila”, Ya kurb’a lemo yace “Kwangila kuma”, ” Eh haka naji labari na gidajen marayu”, Yayi dariya yace “Ba gaskiya bane, duk wata kwangila da aka ba Alhaji ina da labarin ta dani yake shawara, Yanzu kusan shekara ba’a bashi kwangila ba”, ” Kuma shine ake ta rumor a gari ya basa”, “Kinsan mutane, da kuma harkar siyasa sau da yawa za’a ce abu ba gaskiya bane ” Allah yasa mu dace”, “Amin”, Ta kashe recorder,
” Wash kai”, Ta fad’a tana dafe, “Subhanallah! kanki ke ciwo?”, Ya tambaya a rud’e, Ta d’aga kai sama, ” Sannu, ki shiga ciki, kisha magani Allah ya baki lafiya”, “Amin”, ” Zan dawo gobe”,
Ta shiga gida tana dariya, da jin dad’i sun samu evidence na farko.
Suraj a gajiye ya dawo gida, sai da Fetta ta masa tausa ya samu bacci.
Washegari tare suka yi breakfast, Suna kammalawa ya fice.
Fitar sa ba dad’ewa Yasmeen tazo, Ta zayyanewa Fetta yadda suka yi da Mukhtar tare da kunna mata recorder taji, “Zargin mu ya zama gaskiya”, Yasmeen tace ” Meye abun yi?”, “Naji yana maganar bayar da kud’in goben a fara aiki”, ” Kiyi yadda zaki yi ki hanasa bayarwa”, Cewar Yasmeen, Fetta tayi nodding kai.
Wunin ranar tayi sa babu kuzari, da tunanin hanyar da zata b’ullowa Suraj, Ya lura da yanayin ta kamar akwai abunda ke damunta, yana son tambayar ta, yana ganin ba huruminsa bane, Ya fita sabgarta.
A gado sai faman juye-juye take ta kasa bacci,
“Motsin ki na damuna, idan ba baccin zaki yi ba ki tashi ki fita”, Ya nuna mata k’ofa, ” If only kasan akan ka ne”, Tayi saurin kwab’ar kanta “Akan Hajiya dai”, ” Shine jigo dukiyarsa ce” Tacewa kanta, Siririn tsaki taja tana jin tamkar tayi wancakali da sha’anin sa.
*7:30am*
Tana ganinsa ya rubuta cheque na 500million, Zuciyarta ta kasa natsuwa, ta rasa ya zatayi ta hana sa, Ya shiga toilet wanka, ya bar cheque d’in akan gado, Ta d’an hankad’a bargo ta tura.
Ya fito, ya shirya a gaggauce ga dukkan alamu sauri yake, Ba tare da yabi ta kan cheque d’in ba ya fice, Tabi bayan sa, sai da taji tashin motocin sa ta sauke ajiyar zuciya.
D’aki ta koma, ta d’auki cheque d’in ta saka hijab da niqab, Ta fice, masu gadin basu gane ta ba, saboda niqab,
Napep ta tara tace ya kaita GT bank, Tana zuwa ba b’ata lokaci, ta basu cheque suka bata kud’in cike da Ghana must go, Ta kira Yasmeen tace ta sameta bank,
Cikin mintuna kad’an tazo da motar ta, Suka saka booth,
“Kud’in meye?”, Ta mata bayani, ” Meyasa kika cire?”, “Itace kad’ai hanyar da zan hana shi bayarwa, idan babu kud’in wurinsa ai bazai bayar ba”, ” Kinyi dabara mai kyau”, “Ki wuce da kud’in gidanku, ni zan koma”, Ta amsa da ” Toh”
Napep ta sake shiga ya mayar da ita, Tana jin natsuwa a tare da ita, bata dad’e da shiga gida ba, Ya dawo ta tsinci da fad’uwar gaba, D’aki direct ya nufa ya duba bai ga cheque d’in ba,
“Baki ga cheque na kud’i ba”, ” A’ah”, Ya fice yana tunanin ya yar’, Dama ya sake rubuta wani ya bashi yaje ya ciro, Kiransa ya shigo wayar sa
“Ranka ya dad’e anyi withdrawing kud’in nan fah”, ” What you must be kidding”, “Wallahi ka duba alert d’in ka”, Wayarsa ya lalubo ya duba, Yaga alert an zare 500million, Ya duba branch da time ya gani, ” Ko waye sai na nemo sa, bai isa yaci kud’in nan ba, and wallahi sai yayi paying for doing this”, Ya bugi sitiyarin mota.Ya fisgi motar sa a 360, bai zarce ko’ina sai GT bank, Rough parking yayi ya fito, Fuskar sa a d’aure tamkar wanda aka aikowa da sak’on mutuwa, Ya shiga bankin, Manager bank d’in ya buk’aci gani, ba b’ata lokaci aka sada shi dashi. +
Cike da girmamawa ya tarbe sa, Ya nuna masa seat ya zauna, Suraj ya zauna, yana cije lips na k’asa, Suka gaisa, Ya zayyane masa abunda ke faruwa, Manager ya jinjina kai yace “Abu ne mai sauk’i, zamu duba suna da time d’in da aka cire, su Cashiers d’in bara su kasa rik’e face na waye and akwai cameras”, Suraj yace ” Do your possible best”, “OK Sir”
Ya samu Cashiers ya tambaye su a wurin wa aka yi withdrawing 500m yau, Chioma tace “Am the one Sir”, ” Waye yazo?”, “A lady with niqab”, ” Muga record “, Ta d’auko littafin ta basa, Ya shiga dubawa Aisha Lawal ya gani, 9:30 na safe,
Ya koma yayi wa Suraj bayani, ” Lady with niqab kuma Aisha Lawal”, Ya furta, Manager yace “Yes Sir”, ” Toh wacece?, ko namiji ne yayi shirin mata dan ya b’atar da kama?”, “It can be”, Cewar Manager, ” Thank You Manager, idan akwai buk’atar wani bayani zan dawo”, Ya fad’a yana mik’ewa, “OK Sir”,
Ya shiga mota, ya zauna tare da d’aura kansa kan sitiyari yana nazari, ” Waye zai yi wannan aiki?, Wallahi I won’t spare him”, Ya fad’a cikin karaji.
“Kai ban fita da cheque ba, na tuna da na fito wanka ina sauri ban d’auka ba”, Ya tabbatar wa kansa, ” Fatima has something to do with it”, Wata zuciyar tace “Why will she do so, tayi yaya da kud’in wanda basu kaisu bama, ta nuna bata so, maybe wata ta shigo gidan, i have to find out”, Yaja kan motar sa zuwa gida.
Yasmeen na zuwa gida da kud’in, K’atuwar akwati ta samu, ta zuba duka kud’in da kulle da padlock, ta d’aura can saman drawer, ta d’aura wasu akwatuna a kai, babu wanda zai d’auka akwai kud’i a ciki.
” Ya Allah ka shigewa Fetta gaba, Allah ya daidaita su da Suraj, kasa musu soyayyar juna, Allah ya d’aura mishi zazzafar k’aunar ta”, Ta furta tana sauke ajiyar zuciya, Ta fice zuwa kitchen taba ciki hakk’in sa.
Securities na bakin gate, Ya tambaya “Wata ta fita da niqab?”, Habu yace ” Eh Ranka ya dad’e”, “K’arfe nawa”, ” Da safe wuraren tara”, “Ta dawo?”, ” Eh”, “K’arfe nawa”, ” Goma ta wuce”
Ya k’arasa ciki kamar zai tashi sama, “Fatima”, Ya furta yana squeezing hannun shi,
Tana zaune falo ya shigo, Ta tsorata da ganin yanayin sa, Ta dake tace ” Sannu da Zuwa”, “Yawwa”, Ya amsa ba tare da ya nuna mata wani abu ba, ” Waya zo wurin ki d’azu?”, “Ba kowa”, ” Kin tabbata?”, Ta d’aga kai sama, Ya wuce d’aki ba tare da ya sake cewa komai ba.
Jikinta yayi sanyi “Ya Allah ga baiwar ka, bani da nufin sharri a kansa, Allah kayi mun jagora”
D’akin ya shiga bincike, duka drawers, da akwatunan ta sai da ya duba, bai ga wata alama na ita bace.
Wayarta dake jikin chaji ya d’auka, bata saka mata password ba, Yaji dad’in hakan, Ya fara bincike WhatsApp da text messages bai ga komai ba, Har zai ajiye wayar, ya shiga contact, d’aya bayan d’aya yake bin numbers d’in, Idonsa ya kai kan sunan Alhaji Tambari,
“Alhaji Tambari”, Ya furta, ” Meye alak’arta dashi?, ko sun shirya cuta ta ita dashi?”, Ya shiga girgiza kansa yana fad’in “Noo”, Yayin da zuciyarsa ke k’ara tabbatar masa ” Had’in baki ne ita da Alhaji Tambari”
STORY CONTINUES BELOW
Ya fito rik’e da wayar a hannun sa, Ya jefa mata a jikinta tare da fad’in “Meye had’in ki da Alhaji Tambari?”, Fuskar sa babu alamar wasa, Hanjin cikinta suka kad’a, Ya daka mata tsawa ” Zaki fad’a mun ko sai na shak’e ki”, Tasan tunda ya jefo mata wayar yaga number sa, Tayi wauta na saving da sunan sa,
K’afa yasa ya take mata yatsa, “Answer me”, Cike da azaba tace ” Yasmeen ce tayi saving ta kira sa, abokin babanta ne”, “Waye babanta marigayi Alhaji Adamu”, Ya d’an yi jim, Yace ” Wallahi na gano akwai sa hannun ki a d’auke mun kud’i, na lahira sai yafi ki jin dad’i”, Ya koma d’aki,
“Ki fad’a masa gaskiya, yasan meke faruwa?”, ” A’ah this is not the right time, kina buk’atar wasu shaidu akan Alhaji Tambari “, Ta tabbatar wa kanta.
Hajiya ke ta maimaita ” Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, meyasa baka nemi shawara ta ba kafin kayi tunanin aiwatar?”, Ya sauke ajiyar zuciya yace “Ina da niyyar fad’a miki, idan komai ya kammala, a tunanina zaki fi jin dad’i”, ” Kayi kuskure Suraj, addu’a kad’ai da zan maka sai kaga Allah yasa albarka”, Yayi shiru cike da dana sanin rashin neman shawarar ta, “Yanzu meye abun yi?”, ” Zan cigaba da bincike, Mama ki sani addu’a”, “In Shaa Allah”, ” Ina cikin damuwa, idan na rasa su zan samu kariyar arzik’i ba kad’an ba”, Ya fad’a tamkar zai yi kuka, “Allah yasa rabon ka ne”, Ya amsa da ” Amin”
Feena da Su’ad jin an ambaci kariyar arzik’i hankalin su ya k’ara tashi, Idan Ya Suraj ya talauce basu san ina zasu sa kansu ba, basa fata hakan ta kasance.
Aunty Jummai ta karb’o maganin wurin Malam, Yace ta jefa a tsohuwar rijiya, wani k’ulli kuma Bilkisu ta saka masa a abun ci ko sha, Da anyi haka zasu rabu, Tuni ta aikata na rijiyar, Wanda Bilkisu zata saka ne take tunanin taya, Ta umarce ta taje gidan, tasan yadda tayi ta saka a abincin sa, Bilkisu ta shirya ta nufi gidan Hajiya Tumba,
Direct sashen Suraj ta nufa, Fetta na jera abincin kan dining table ta shigo ba sallama,
“Sannu ko”, Ta fad’a tana yatsina fuska, Ko kallo bata isheta ba balle ta amsata ta shige d’aki,
Bilkisu ta shiga waige waige, Ta nufi dining table, Ta bud’e cooler wacce take kyautata zaton abincin Suraj ne, ta barbad’a ta motsa yadda ba za’a gane ba, Ta mayar ta rufe,
Ta fice da sauri, ta bar gidan ba tare da ta shiga wurin Hajiya ba.
” Har kin dawo”, Cewar Aunty Jummai, “Eh, nayi nasarar sawa”, Washe baki Aunty Jummai tayi tace ” Saura k’iris, mu jira labarin rabuwar su”, Suka tab’e kamar k’awaye.
Suraj damuwar da yake ciki ta kore mishi yunwa, sam baya jin cin abinci.
Fetta ganin wunin ranar bai ci abinci ba, Ya bata tausayi, a ranta tace “Da ace Alhaji Tambari yayi nasara a kansa haka zai shiga damuwa”,
Da sallama ta shiga d’akin, Yana waya da Alhaji Tambari, Yace yaji sa shiru, Nan yake fad’a masa matsalar da aka samu, Jin damuwar da ya shiga, da yadda yake jimamin al’amarin, ta bashi shawarar ya tsananta bincike, Hakan ya tabbatar masa babu sa hannun sa.
Sukayi sallama ya katse wayar, Yana bin ta da kallo, Zuciyarsa na k’arya mishi zarginta da yake, Bara ta aikata ba, Murya a sanyaye tace ” Komai yayi zafi maganin shi Allah, addu’a bata bar komai ba, kada kasa damuwar da zata zame maka matsala”, Da kallo yabi ta yaji dad’in nuna kulawarta gare shi, Da hannu ya mata alama is ok,
Ta koma falo, ta d’auki wayarta tana chatting da Yasmeen, akan su hanzarta su samu shaidu, a mik’a masa kud’insa yana cikin matsananciyar damuwa, Yasmeen tace “Ko dai kin damu da damuwar sa ne”, ” Meye nawa a ciki, am feeling guilty na nice silar damuwar”, Yasmeen ta turo mata murmushi, Sukayi sai da safe, bacci ne sosai a idonta.
Har bacci ya d’auketa tana jin sa yana mutsu-mutsu ya kasa bacci.
*3:00am*
Yayi alwala, Ya gabatar da k’iyamul laili, Ya rok’i Allah ya bayyana wanda ya d’auki kud’in, Ya bayyana duk mai son cutar dashi.
Ya idar, Yayi folding sallayar, Yazo ajiyewa yaga yar’ k’aramar takarda a k’asa wanda ya kyautata zaton fad’uw tayi daga cikin sallayar(suna da yawa) dake wurin, Ya duk’a ya d’auka,
Receipt ne na bank, A matuk’ar razane ya sake karantawa, Receipt na kud’insa da aka cire, “Fatima ta cire kud’ina, so she is responsible”, He couldn’t believe, Ya matuk’ar girgiza, ” Ashe green snake ce”,
Kamar a mafarki taji saukar ruwan sanyi a jikinta, “Tashi mayaudariya, azzaluma, mai fuska biyu”, Taji saukar kalamansa cikin k’wak’walwar kanta, Kafin ta mik’e ya fisgota da k’arfi, Ya jefar k’asa,
” Kin aureni ne dama dan ki mallake dukiyata, kin kwantar da kai kina mun ladabi dan ki cuceni, kina pretending bakya son kud’i, Allah ya tona asirin ki”, Ya nuna mata receipt, Ta rasa me zata ce masa, Tana tunanin abun cewa, Taji ya shak’eta, “Ina kika kaimun kud’ina”, Ya saketa ta bugu da gado,
Sam bata ji zafin buguwar ba, sai rad’ad’i da zafin maganganunsa, da takaicin zargin da yake mata, wajen taimako ta d’aure kanta, Ya d’aga k’afar sa sama ” Zaki yi magana ko sai na taka ruwan cikin ki, betrayer, Hajiya ta taimaka miki, but sakayyar da zaki mata kenan”,
Hawaye ne ya wanke fuskarta, “Crocodile tears, wa zaki yaudara da hawayen munafunci”, Kanta ta had’a da gwiwa ta shiga rera kuka,
” Ko ki kama mun bakin ki, ki fad’i ina kika kai kud’ina ko wallahi na sab’a miki kamanni”, Ta d’ago idonta da suka fara ja saboda kuka tace “Ban d’auki kud’in ka da niyyar yaudara ko cuta ba”, Wata dariya yayi mai cike da takaici yace ” Ba zaki tab’a wanke kanki a wurina, muradina ki mayar mun da kud’ina, na yad’a ki duniya dan mutane suyi hantara da irin ku, sannan na baki takardarki”,
“Allah da yasan manufata shi zai wanke ni”, ” Two face, mai bak’ar zuciya, banda kwad’ayi da had’ama ina zaki kai 500m”, Ya d’agota, Ya kama hannun ta ya murd’e, “For the last time ina kud’ina suke?”,Ganin yana neman karya mata hannu, Ta shiga k’ok’arin fisgewa, Ya kama shi gam ya murd’e, “Kiyi magana ko wallahi na karya miki hannu” +
Ganin da gaske yake, Ta zayyane masa komai ta k’ara da “Nayi ganganci na aiwatar da abunda zuciya ta sak’a mun kai tsaye ba tare da nayi shawara ba”,
Sakinta yayi, Yayi murmushi mai cike da takaici yace ” Taya kike so na yarda da zantukan ki”, “Kayi bincike, idan ka sameni da laifi, na yarda ka yanke mun duk hukuncin da kaga dama”
Ya jinjina kai “Hukunci na ba mai dad’i bane, idan na kama ki da laifi sai kin gwammace mutuwarki and make sure you return my money kafin na dawo”, Yana fad’ar haka ya fice daga d’akin.
Ta durk’ushe k’asa, Tana sauke ajiyar zuciya da rok’on Allah ya kawo mata mafita, Yasa ya gane gaskiya, wayarta ta lalubo ta kira Yasmeen, Tace tazo da kud’in, Ta buk’aci jin k’arin bayani, Tace idan tazo taji.
Suraj zuciyar sa ta kasa amince masa da zantukan Fetta, muradin sa ta maido masa kud’insa, shiyasa ya tsaya ya saurare ta, Mutum kamar Alhaji Tambari zai yaudare sa, 500m ta mishi me, a irin dukiyar da Allah ya bashi, Wata zuciyar tace ” Trust no one, zai iya yaudarar ka, think twice”, Haka yayi ta sak’e-sake a ransa, Har ya shigo sashen Hajiya.
A d’aki ya sameta tana gyaran kayanta, “Mama da kanki kike gyara”, ” Eh”, Ta bashi amsa, “Ga masu aiki”, ” Bana so suna tab’a mun kayan sawa”, Ya jinjina kai, Tace “Ya maganar kud’in ka?”,
Yayi niyyar b’oye mata, Ya tuna yadda wancan karan ya kasance, ” Kayi shiru”, Ta katse mishi tunani,
“Fetta ta d’auka”, Hajiya a razane tace ” What! Fetta”, Yayi nodding kai, “How and Why”, Ya fad’awa Hajiya yadda ta gaya mishi ya k’ara da ” Ban yarda da ita ba, tana son ta k’ara b’atar dani ne, intentions d’inta a kanmu is bad”,
Hajiya ta nisa tace “Na yarda da Fetta, akwai abunda ta hango, na tabbata ba zata tab’a cutar mu ba, Ka binciki Alhaji Tambari”, ” Mum meyasa kullum kike backing d’inta, Meyasa kika yarda da ita haka?”,
Tayi d’an murmushi mai cike da ma’anoni tace “Fetta mutuniyar kirki ce, alheri ce a rayuwar ka da tamu baki d’aya”, Yayi shiru dan baya so ta d’ago zaman da suke, Sam zuciyar sa ta kasa yarda da ita, Yayin da wani b’angare ke son cusa mishi yarda da ita, idan kuwa ta d’auka ne saboda selfish interest d’inta, ba zai k’ara yarda da kowacce mace ba bayan Mahaifiyarsa har abada.
” Zanje gidan gona”, Ya fad’a yana mik’ewa, “A dawo lafiya, Allah ya bada nasara”, Ya amsa da ” Amin”
Cikin hanzari direban sa ya taso, ya bud’e masa k’ofar baya, Ya shiga, ya mayar ya rufe, Ya koma driver’s seat,
“Ranka ya dad’e ina zamu?”, ” Gidan gona”, Ya bashi amsa a tak’aice.
Minti 20 ya kawo su gidan gonar sa dake Nasarawa GRA, Direct office d’insa ya nufa, Ya kira wani abokin sa Hafeez wanda d’an siyasa ne dashi ake damawa cikin gwamnatin, Yace yazo yana buk’atar ganin sa.
Ya jinginar da kansa jikin kujera, Ya lumshe ido yana nazari.
Kusan minti 30 yana haka, duk wanda ke da burin sun dank’wafar dashi ba zai d’aga masa k’afa ko na second d’aya ba, Shigowar Hafeez ya katse shi,
STORY CONTINUES BELOW
“SS manyan gari”, Ya fad’a yana bashi hannu, Sukayi musabbaha, ” Ai kune manyan gari ku da gwamnati ke hannun ku” , “Kune masu kud’in garin ai”, Suraj yayi dariya yace ” Ya harkoki?”, “Wallahi Alhamdulillah, ya naku?”, ” Alhamdulillah “, ” Allah yayi mana jagora”, “Amin”
“Naji kamar ance gwamnati ta bada kwangilar gyaran orphanage”, Hafeez yace ” Kai bani da labari”, “Yaushe ta bayar?”, ” Almost a week, taba Alhaji Tambari”, “Ba gaskiya bane, babu wata kwangila da aka bayar”, ” Ka dai bincika”, “Ina da tabbaci, but zan sake bincika maka zuwa gobe”, ” Yawwa nagode”, “But meyasa kake son ji, ko kana so asa da kai ne”, Yayi murmushi yace ” K’warai”, “Toh Allah ya taimaka”, Ya amsa da ” Amin”, “Ni zan koma akwai meeting da zamu yi da governor”, ” OK thank you for ur time”, “Haba anything for you”, Sukayi sallama ya wuce.
” Ban ji dad’i da haka ta kasance ba”, Cewar Yasmeen cike da damuwa, Fetta tace “Haka Allah ya k’addara”, ” Hakane but bana so ko kad’an Suraj ya zarge ki”, “Allah da yasan manufata ta alkhairi shi zai wanke ni”, ” Allah ya yarda” Ta furta a fili, “Amin”, Ta amsa, ” Ya Allah ka nuna mun ranar da Suraj zai fahimci wacece Fetta”, Tayi addu’ar a zuciyar ta,
“Idan ya dawo ki kunna mishi VN na PA, hakan zai saka mishi shakku da k’arasa ya bincike Alhaji Tambari”, Fetta tayi nodding kai cike da gamsuwa, Sam bata jin dad’in jikinta, Kanta ke masifar ciwo, tana jin sanyi a cikin k’ashinta, Yasmeen ta taya ta da aikin gidan, Tayi girki white rice da miyar kabeji, sai coconut juice, Kamar kullum ta jera masa a dining table, Bayan sallar azahar Yasmeen ta tafi.
Kwanciyar k’asa taji na mata dad’i, Ta kwanta k’asan carpet na d’aki, ta lullub’e da bargo, Damuwa da zullumi cike da zuciya da gangar jikinta.
Suraj ya shigo gidan a gajiye, tamkar wanda yayi aikin k’arfi, Kallo d’aya zaka masa kasan yana d’auke da damuwa.
Har ya nufi hanyar d’aki, Cikinsa yayi kukan yunwa, Tun faruwar abun bai saka ma cikinsa wani abu ba sai ruwa, Dining area ya nufa, Yayi serving kansa, yaba ciki hakk’insa, Damuwar da yake tattare da ita, bata hana masa jin dad’in girkin ba, Yana mamakin baiwa ta girki da Allah ya bata.
Bata ji shigowar sa, Kallo d’aya ya mata ya kawar da kansa gefe, Ya nufi toilet, Yayi wanka ya shirya,
Bargon da ta lullub’e ya janye, “Ina kud’ina?”, Ya fad’a yana tsare ta da ido, Ta d’ago kanta tamkar zai fashe, ” Sannu da zuwa”, Ta furta, “Ban buk’aci gaisuwar ki ba, kud’ina nake buk’ata”,
Mamakin son kud’i irin nasa take, Dama ance mai arzik’i yafi talaka son kud’i, but yana cewa wani nada son kud’i bayan yafi kowa, ” Zaki tashi ko sai nayi ball dake”, Kujerar dake gefe ta dafa ta mik’e, ta jawo wayarta,
“Kafin na baka ina so ka saurari wannan”, Ta fad’a tana mik’a masa, Ya bita da wani shegen kallo, tamkar ba zai amsa ba, Ya fisga kamar zai yi k’wace,
” Bai isa ya zama hujja da zaki kare kanki ba”, Ya fad’a yana mik’a mata wayar, Ta karb’a ranta taji ya b’aci, A zuciyar ta tayi alk’awarin janye hannun ta, ko taka zai ba Alhaji Tambari ba zatayi yunk’urin hana shi ba, “My money”, Da hannu ta nuna masa wurin da bagco yake.
Bud’ewa yayi ya duba, ga dukkan alamu complete ne ba’a tab’a ba, Ya sauke ajiyar zuciya.
” Am sorry da na shiga rayuwar ka, nayi kuskure”, “Ba zaki san kinyi kuskuren shigowa rayuwata ba, sai zargin da nake akan ki ya tabbata”
Kwanciya tayi taja bargo ta rufe ba tare da tace masa komai ba.
Kiran Alhaji Tambari ne ya shigo wayar sa a karo na ba adadi, bai d’auka ba har ta tsinke, baya son magana dashi, sai yaji daga Hafeez, Wayar ma ya kashe gaba d’aya yabi lafiyar gado, Bacci ya d’auke sa( Dole kayi bacci kud’i sun dawo)
“Sweety ina kika samu kud’i haka”, Bilkisu ta fad’a tana kallon tulin kud’in dake gaban Zulaihat, Tayi murmushi tace ” Yanzu harka ta cigaba”, “Ban gane ba”, “Wata Hajiya na had’u da ita mai harka irin tamu”, ” Sai akayi me?”, Ta tambaya tana hararar ta, “Mukayi harka ta biya ni”, Bilkisu ta mik’e a fusace tace ” Kan bala’i ni zaki ma kishiya”, Ta rik’o hannun ta “Haba sweety zauna ki saurare ni”, Ta fisge hannun ta, ” Ba abunda zai saurara, kin yaudareni wallahi”, Rungumeta tayi tace “Ban yaudareki ba, ke kad’ai ce tawa, wannan kud’in ta zamu ci”,
Bilkisu ta d’an sassauto tace ” Taya?”, “Matan manya ne dake harkar mu, su kawai su samu yara suyi dasu, su biya su, Yi d’aya fah 100k”, Bilkisu ta zaro ido tace ” Rantse”, “Wallahi, ki shirya gobe muje, na had’aki da wata Hajiya kema”, Cike da farin ciki tace ” Sweety kice munyi kud’i”, “K’warai kuwa”, ” Dama ina zaune na kati ma ya gagare ni”, “Komai yazo k’arshe”, Ta rungumeta tace ” I Love you”, Tare da manna mata kiss.
*5:40am*
Fetta da k’yar ta gabatar da sallar asuba, kanta ke mata masifar ciwo, Ta jingina da kujera tana lazimi, A haka ya dawo masallaci ya tarar da ita, Ya wuce da niyyar fita iskar ta, Ya dawo saitin ta, “Are u OK?”, ” Kaina ke ciwo”, Ta bashi amsa, “Dole yayi ciwo, anga samu anga rashi”, Kalmar ta mata zafi, ta dake a ranta tana fatan ya gane gaskiya,
Bedside drawer ya jawo ya d’auko panadol ya mik’a mata, Kamar kar ta amsa, ganin kanta zata cuta, Ta karb’a, Falo ta fita, ta bud’e fridge ta d’auki ruwa, Tasha maganin, Ta kwanta a kujerar falo.
Yana shirin komawa bacci, Kiran Hafeez ya shigo, Yayi receiving, bayan sun gaisa Yace ” SS maganar kwangilar nan k’arya ce, Governor ma ya tabbatar mun babu wata kwangila”, “Thank you”, Kad’ai ya iya furtawa ya kashe wayar, Jikinsa yayi sanyi sosai,
” Hakan na nufin Fatima taimako na tayi niyya?”, “Meye manufar Alhaji Tambari a kaina?”, Ya jefowa kansa tambayoyin da babu mai bashi amsa.