BATUUL
CHAPTER 24
Da yamma suna zaune garden itada da Farida da take ta mata iya shege kan ta k’ara k’iba, bata kulata ba dan Yaa Abu ya fad’a mata babu wani k’iba da ta k’ara, gaba d’aya hankalinta yana kan fruit Bump game d’in da take bugawa, Juyo mata da Macbook d’in dake kan cinyarta Farida tayi tace “Kinga nacewa Affan in zaizo ya taho min da wannan cradle d’in, its cute ai ko?”, sai a sannan ta d’ago ta kalli cradle mai kyau dashi snn ta kalli Farida with confusion fuskarta tace “Huh?, cradle nefa, kwana zaki koma yi kai?”, Farida ta d’ago ta dubeta tayi mata kallon you ain’t okay ta girgiza kai snn tace “Babynmu na siyawa, the newest niece/ Nephew, kinga fa unisex nace ma tunda bansan mey zaki haifa ba, Dan Allah kicewa Yaa Abu kuje a duba cuz in san irin kayan da zan riqa keeping”, ta fad’a with soo much excitement a muryarta, Sai lokacin Batuul ta fahimci ina ta dosa ta tsuke fuska tace “Ni nace miki zan haihu toh?”, Farida ta kyalkyale da wani irin dariya da ya bawa Batuul haushi tace “Wake jiran sai kin fad’a mishi, tun da naje wajenki UK na gano, shiru kawai nayi maki ina kallonki kawai”, Jin ambaton sunan UK ta tuna da Ajiddeh, jiki a sanyaye tace “tun yaushe ne bata nan, ni tunda naji sauk’i ban ganta ba”, ba tareda ta dubeta ba Farida tace “Wa kenan?”, a hankali Batuul ta furta Ajiddeh, kafad’a Farida ta d’aga tace “Oho, da yake she is not my cup of slush”, Batuul ta dawo kusa da Farida tana k’ok’arin rufe System d’in tace “Riri mana, dagaske fa nake, she was nice to me da banida lafiya, har Addu’a fa tayimin”, wani irin kallo Farida tayi mata, kallon lallai you are not okay, har ta bud’e baki zatayi magana ta fasa, ta sake janyo System d’in zata bud’e, Batuul tayi maza ta riqe tace “dagaske nake I could remember everything har da kukanta, she insisted mu dawo fa ayi min magani a nan, amma tunda na warke ban ganta ba, kuma d’azu naji Abu na cewa bayason ganinta cuz bayason taking decision out of anger, mey ya sameta Dan Allah?”, Sai yanzu Farida ta tabbatar da Lallai Batuul batasan mey ke faruwa, kuma baza taji daga bakinta ba, gyara zamanta tayi tana fuskantar Batuul da kyau kamar wacce zatayi wani maganan kirki tace “Kina jina dai koh?”, Batuul ma ta gyara zama dan ta fad’a mata, Farida taci gaba “Naga kin fi kusa da Yaaa Abu, just ask him about her, baza kiji daga bakina ba”, had’e rai Batuul tayi tareda kaiwa Faridar duka a kafad’a tace “You are a jerk Allah, shine kika b’atamin lokaci kamar wacce zata fad’i abin kirki”, mtewww taja tsaki daidai lokacin wayanta ya hau ringing, dubawa taga unknown number ne, har baza ta d’auka sai kuma ta fasa tayi recieving tasa a kune, cikin masculine voice d’inshi taji yace “Are you ready?”, lumshe ido tayi ta bud’e tareda cire wayar ta sake kallon screen d’in da kyau snn ta maida kunne tace “Hello?”, yace “Glitter you there?”, a hankali cikin siririyar murya tace “Inace fa sai dare zamu tafi kuma”, yace “Nah get ready yanzu zanzo mu tafi kinji?”, tace “Okay”, yace “Yeah sai na k’araso, take care”, a hankali ta lumshe ido, this is the first time Yaaa Abu ya k’irata, ko ina ya samu number d’inta, ko dai dama yana dashi ne, kauda tunanin tayi ta d’ago taga Farida ta kafeta da ido tana wani irin smirk tace “And you will later tell me kefa baki iya soyayya ba, dubi yadda kika wani kashe murya kina magana, badan shegen son jin gulmana ba da bazanji ma mey kike cewa ba”, Harararta Batuul tayi ta mik’e tace “You have a problem these days kin sani ko, ni matsa min in tafi, kya ji dashi, I pity best friend”, ta fad’a tana mik’ewa zata bar wajen, da sauri ta ajiye Macbook d’in hannunta ta biyota tana dariya tace “exactly why he can’t do with me”, tsaki Batuul taja taci gaba da tafiya abinta Farida na biye da ita tana ta zuba, ko da suka shigo a parlour suka tarar da Ammah, Ammah tace “Bitti badai baki shirya ba kam, inace da yamma yace zaku fita”, sauk’ar da kai tayi k’asa tace “Shine nazo in shirya yanzu Ammah”, Ammah tace “Toh shikenan” Farida tace “Ohhh ashe fita zakiyi shine kike shamin k’anshi dan kada in biki, toh nikam sai naje bara inje in shirya nima”, dariya kawai Batuul tayi dan tasan in ta biyewa Farida sai ta hanata shiryawar ma gaba d’aya, tana shiga d’aki ta fad’a toilet tayi wanka snn ta fito, akwatin da Farida ta shigo dashi d’azu ta bud’e ta ciro wani swiss voile purple had’e da underwears suma purple, saida ta shafa mai snn ta saka kayan, turarukanshi dake gaban vanity table d’in ta fesa wad’anda taji sun kwanta mata, Farida na zaune parlour suna hira da Ammah wayarta tayi ringing, da sauri ta d’aga ganin Yaa Abu rubuce jiki takai kunnenta tace “Hello Yaa Abu ina wuni”, bai amsa ba sai cewa da yayi “Kina jina?”, ta kad’a kai tareda cewa “Ehhh”, yace “Har ta gama shiryawan ne?”, sarai tasan wacce yake nufi amma ta dake tace “waye kenen?”, yace “I mean Fatima, ta shirya ne?”, daga yadda yayi maganan tana jiyo how stern muryarshi take, murmushi tayi tace “Yeah ta dai hau sama shiryawa, inaga ta gama by now”, yace “ita kad’ai ce saman nan ko?”, kamin tayi magana yace “Anyway, kina jina koh?, inaso ne ki taimaka mata ki shiryamin ita yadda duk wannan ramar da tayi zata koma, I mean she should look all presentable, har wannan make up d’in naku na mata if possible kiyi mata”, murmushi kawai takeyi tace “Tohh Yaa Abu, lemme check on her rn”, ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Okay Plss do, Thank you” cikeda da murna yau Yaa Abu yace mata Thank you ta ajiye wayan ta dubi Ammah tace “Wai Yaa Abu ne yace in taimaka wa Batuul ta shirya”, batareda ta kalleta ba Ammah tace “Toh shine kike zaune?”, mik’ewa tayi ta haura sama ta tura k’ofar d’akin da tasan Batuul na ciki, gaban vanity table ta tarar da ita zaune tana faman taje dogon gashinta da yake gajiya mata da hannu, hannu tasa ta anshi comb d’in tana cewa “Kedai har yanzu baza ki fara retouching ba”, bakinta ta tsuke dan in da abinda ta tsana bai wuce a tab’a mata gashi ba ace za ayi mata kitso ko taji amma da yake yanzu yana bata wahala babu yadda ta iya, dariya Farida tayi tace “Hey chill!, bafa ni na kar zomon ba, rataya aka bani, start retouching zaki bar k’uncin nan da kikeyi yanzu”, d’an tsaki taja tace “Nikam kiyi shiru ki tajemin”, haka ta gama taje mata tayi bun dashi ta baya snn tacewa Batuul “ina zuwa”, ta fita daga d’akin bata dad’e ba ta dawo riqe da Makeup kit kan madubin ta fara jera komai, Batuul ta dubeta da kyau tace “You also going”, Farida ta kad’a kai tace “Nah, ke zanyi wa d’an touch up”, Batuul ta yatsina fuska tace “dayake nace miki inason yi koh”, Farida tace “Nifa am trying to help, babu ruwana in kukaje yaga y’anmata masu kyau wajen, kuma kinsan dukkansu y’an matan nan yanzu abinda sukeyi kenan ko”, da kyau Batuul ke kallon Farida gabanta na fad’uwa jin abinda take cewa, gyara zama tayi kan stool d’in tace “Toh kiyi min”, murmushi kawai Farida tayi tazo ta fara shafe shafe fuskar Batuul, d’an touch up tayi mata da ya k’ara fito da kyan Batuul d’in snn ta fita, bata jima da Fita ba taji an turo k’ofar d’akin, batareda ta damu ta juyo taga waye ba taci gaba da rataya towel d’in da take ratayawa, shikam tun daga corridor yakejin k’anshin turaruka masu dad’i, ido ya lumshe ya bud’e ganinta tsaye tana k’ok’arin rataye towel, a hankali ya shigo d’akin ya rungumeta ta baya tareda sauk’e ajiyar Zuciya, itama abinda tayi kenan jin k’anshin shi da d’umi jikinshi, ajiye towel d’in tayi dan yana neman fad’uwa jin d’umin lips d’inshi a wuyarta tana jin sauk’ar numfashinshi, a hankali ya juyo da ita tana fuskantarshi idonshi na zagaye ko wane angle d’in fuskan, hab’arta ya d’ago yace “Kinyi kyau Glitter”, duk da rashin haskenta zaka iya ganin blush d’in da Farida ta shafa mata na dad’a turuwa, a hankali tace “Thank you, kaima ai kayi kyau”, hannu yasa ya lakuto purple ombre lipstick d’in da aka shafa mata yana yatsina fuska yace “wa yace mata ta shafa miki wannan?, I can’t take wani ya kallemin keh har idonshi ya kai kan lips d’inki”, kamin tace wani abu ya sunkuya ya had’e bakinsu waje d’aya, sai da ya tabbatar ya tsotse dukan lipstick snn ya saketa yana maida numfashi raurau tayi da ido tace “ka b’ata min fa kenan”, ya rik’o hannunta yace “Na gyara dai, ni kad’ai za ayiwa irin wannan kwalliya ba in zamu fita ba”, agogon shi k’irar Hublot ya duba yace “Glitter muje, its getting late”, ya mik’o mata mayafinta dake ajiye kan gadon, sauka sukayi k’asa har lokacin Ammah na zaune falo, tana ganin Batuul tace “Masha Allah Bitti, ya babu d’an kunne kuma bare sarqa, Farida maza jeki ki d’auko mata d’akina”, Da hanzari Farida ta tashi taje ta d’auko wani gold chain da earring d’insu da agogo, ita ta taimaka mata ta saka Ammah tace “Masha Allah, yayi daidai yanzu, ki gaida min su in kinje Bitti”, 3
23
ta amsa da toh dukda batasan inda zasun ba, ta kalli Farida tace “Muje mana?”, Farida tace “Wa zai biku?, keda ma bakisan inda zaku ba, marairaice mata tayi tace “I have assignment kuma gobe zanyi submitting, kuje kawai sai kun dawo”, juyawa kawai tayi ta bi bayan Abu, shi ya bud’e mata k’ofar mota snn ya zagaya side d’inshi ya shiga ya tada motar, hira sosai ya dinga yi mata yana driving, har mamakinshi takeyi yadda yake ta magana, gidan Yaa Mera suka fara Zuwa, basu wani jima ba suka yi mata sallama suka tafi tana ta saka musu albarka snn suakje gidan Yayan Abui dake unguwarsu d’aya da Yaa Meran, sai gidan Aunty Amna, sosai taji dad’in ganinsu ta bawa Batuul abubuwa dayawa tareda bayanin yadda zatayi amfani dasu, bayan sun bar gidan Aunty Amnah taga sunyi hanyan gidansu, with so much excitement ta juyo ta dubeshi, ido d’aya ya kashe mata yace “Surprise”, cikeda murna ta kamo hannunshi d’aya tayi kissing tace “I love you”, murmuahi yayi this time ya kai hannuta bakinshi yayi kissing yace “I love you too Glitter”, a hankali tace “Thank you”, har tausayi ta bashi ganin murnar dake fuskanta yace “Shhh anything for you”, daidai bakin gate d’in gidansu Batuul wayarshi tayi ringing, dubawa yayi ganin mai k’iran nashi take expression d’in dake fuskarshi ta b’ace, Batuul dake ta murna bata ma lura da yanayinshi ba, yana parking ta bud’e k’ofa da gudu ta fita, bayanta yabi ya had’e rai yana mata wani kallo tareda d’aura hannunshi kan cikinta yace “Gudun mey kikeyi?”, rau rau tayi da ido tace “Am just happy ne zan ga Aunty fa”, yace “Na fad’a miki bana son kina tsalle, my Baby”, ya fad’a yana kallon idonta,sai lokacin ta fahimci inda maganar ta dosa, ita mantwa ma takeyi da wani halitta cikinta, puppy eyes tayi mishi tace “Tohh, toh ka sakeni sai in shiga gida”, bai saketa ba saida ya koma ya rufe k’ofar motan snn ya kamata suka shiga ciki a tare, suna shiga ya saketa, tana son gudu tana tsoron fad’anshi , Sunan Aunty ta shiga k’ira, jawota yayi yace “Glitter meye haka kikeyi?, zamu koma tunda haka zaki rik’ayi”, kai ta girgiza mishi tace “Na daina fa”, Daidai nan Aunty ta fito side d’in Baba, da gudu taje ta rungumeta ta fashe da kuka, Aunty da mamaki ya cikata ta d’ago tana kallonta tace “Aa a, Batuul daga ina haka ke Kam harda kuka?”, sake kwanciya tayi jikin Aunty tace “Aunty I Missed you, 4months ban ganki ba fa”, dariya ta bawa Aunty, itama tayi kewar y’ar tata sosai tace “Keda yanzu kin girma, ba kullum zaki na ganina ba dama”, Ta shagwab’e fuska tace “nikam wane girma nayi?, am still your kid Batuul”, Aunty tace “naji toh, keda waye haka da magrib d’inna?”, juyawa tayi ta kalli inda Abu ke tsayawa ya zuba musu idanu yana kallon bond da affection d’in dake tsakaninsu yana murmushi”, Aunty ta fad’a murmushinta tace “Aliyu ashe tare kuke tafe shine ta k’yaleka a tsaye, shigo ka zauna”, bai ce komai ba ya k’arasa shigowa ya zauna snn suka gaisa da shi, Aunty ta juya zata tafi Batuul ta bita a baya, text ne ya shigo wayan Abun ya duba yaga, bai damu da ya karanta ba sabida ko ganin maishi bayason yi bare kuma har ya kai ga karanta text d’in, yana gogewa k’ira ya sake shigowa wayan, bai d’auka ba ya ajiye wayar gefenshi, Batuul da ta fito riqe da tray ta kawo mishi ruwa ta tsiyaya mishi cikin tumbler ta mik’a mishi, yayi mata murmushinshi mai kyau ya karb’a yana sha, wayarshi ce ta sake ringing, duban wayan tayi gabanta na fad’uwa ganin sunan da ta gani rubuce, wani irin curiosity ke fizgarta da yasata d’aukar wayar tayi receiving ta kai kunne, muryar Ajiddeh taji tana cewa “Aliyu Dan girman Allah badan halayena ba ka taimaka kazo Mum tayi accident ko sau d’aya ka ganta ta nemi yafiyarka”, ido ta lumshe hawaye na taruwa idonta lokaci daya jikinta yayi sanyi, yana sauk’e cup d’in yaga wayarshi kunnen Batuul, da sauri ya karb’e wayan yana kallonta yace “Do you have to?”, ido ta rintse hawayen da suka taru suna zubowa.Da mamaki yake kallonta ganin hawaye idonta, wayar ya d’auka ya duba da wa sukayi magana, kallonta yayi snn ya sake duban wayan yace “Glitter mey tace miki?”, ido ta lumshe ta bud’e hawayen na sirarowa, da sauri ya sauk’o daga kan kujerar yana fad’in “Subhanallah, Glitter talk to me mey tace miki?, kar kiji tsoro tell me all”, “Ina take?”, abinda kawai ta iya fad’a mishi kenan, so yake kawai yaji abinda Ajiddeh ta fad’awa Batuul a waya, ganin baza ta fad’a mishi ba yasa shi d’aukan wayan zai k’irata, a hankali tana share hawayenta tace “She said Mum had an accident tana son ganinka”, ajiyar zuciya ya sauk’e jin abinda tace snn ya juyo yana kallonta yace “Toh kukan mey kikeyi Glitter?”, “kaje ka duba Mum d’in, in ka dawo sai mu tafi”, He is not ready to tell her duk wani ciwo da tayi da sa hannun Ajiddeh ba, yana jiran right time ne ya fad’a mata amma yanzu he is not ready, hannunta ya kamo ya riqe yace “shine kike zubar min da precious hawayenki bayan nace banaso?”, ya fad’a yana kawar da maganan, kallonshi ta tsaya yi ganin ta fad’a mishi Mum d’in Ajiddeh tayi accident kuma baice komai ba, hannunta ta karb’a daga wajenshi tace “Yaa Abu nace fa Mum na Ajiddeh fa batada lafiya”, idonshi ya d’aura cikin nata yace “Naji, mey zanje inyi mata Glitter?, I don’t wanna see her, I don’t wanna talk to her”, ya fad’a muryarshi becoming stern,da tsoro da mamaki sosai take kallonshi jin abinda ke fitowa daga bakinshi, anya wannan Yaa Abu ne da ta Sani har yake cewa bayason ganin Ajiddeh, koma meye tsakaninsu dai yaje duba Mummy tunda itace tayi accident d’in ba Ajiddeh da bayaso ba, ya bud’e baki kenan zaiyi magana ganin mood d’inta ya canza yaji takun tafiya, da sauri ya kai hannu fuskar ya shafe ragowar hawayen dake shirin zubowa yace “Kina so Aunty ta ganki kina kuka tace nayi miki wani abun ko?”, itama hannu takai ta shafe hawayen, tashi yayi ya koma kan kujerar da ke Zaune, Aunty ta k’araso parlour zatayi Side d’in Baba ta ganshi zaune tace “dama kana nan Ashe, inace ma ka juya, shiyasa na jiki shiru kenan”, duk kunya ya kamata suna had’a ido da Abu ta langab’ar da kai, yayi murmushi tareda shafa gashin kanshi yace “Yanzu nake shirin fita zan barta inje in dawo anjima”, Aunty tace “Toh shikenan sai ka dawon”, daga haka tayi wucewarta, pie d’in da ya fara ci ya k’arasa snn ya ajiye sauran tareda mik’ewa yace “Glitter I will b going, 9 zan dawo sai mu tafi, yayi miki ko?”, kai kawai ta gyad’a mishi ya dawo ya matso gabanta ya d’aga hab’arta yace “ki kalleni kimin magana, yayi miki?”, a hankali tace “Ehhh”, yayi murmushi yace “that’s my baby, muje ki rakani”, tare suka jera har suka fita waje, saida ya shiga mota snn yace “ki koma gida I will b back shortly”, ya shafi gefen fuskarta, yana ganinta har ta shige gida snn ya sauk’e ajiyar zuciya ya koma cikin mota ya d’auki wayarshi daketa ringing da ya maida silent d’agawa yayi yace “Kai shikenan dan bakada family sai kayi ta damun mutane”, tsaki Massa yaja yace “Kai d’an duniya nefa, da anyi magana kace kai Family, gashi family naka ke damuna ai, kaifa d’an iska ne wlhy, yarinya nata k’iranka kaqi d’aga waya”, girarshi ya had’e ya dubi hanyar da Batuul tabi yace “a ina ka gantan har take damun naka?”, yace “Am in Tripods, let’s meet there”, juya motar yayi ya fita daga gidan, a tripods suka had’u, Massa yayi musu ordering abin sha snn yace “Ajiddeh, she called me like thrice yau wai tana son ganinka banma gane whole abin ba but tace tana k’iranka you weren’t picking”, har saida yayi shiru Abu ya dubeshi yace “is this why am here?”, harara Massa ya sakar mishi yace “nifa wulakanci ne bana so, in gama maka bayani kana tambayata dalilinka na zama a nan?”, Abu ya lumshe ido har sai da Massa yayi shiru ya bud’e ido yace “Mustapha kasan ni yanzu tsoro take bani, seeing her infuriates me”, kallonshi Massa keyi na lallai kaima the saying goes with you, maza bakuda tabbas yace “Dan kayi amarya shine har zaka manta da matarka, I wasn’t expecting this from you Aliyu, ka bani mamaki, har tsoronta kakeji sbd kana da wata matar kuma kana sonta ko, tana ma inane haka take ta nemanka bata samu d’in?”, Abu da ya fahimce sam Massa bai gane mai yake nufi ba yace “kasan rashin lafiyan nan da Fatima tayi was all because of her?, su suka kwantar da yarinyar mutane sukayi ta bata wahala, they wanted killing her Mustapha, the mere thought of it weakens me inji na tsanesu gaba d’ayansu, am sure setting eyes on her again bazai mana da dad’i ba daga har ita shiyasa bana son ganinta, Massa da gaba d’aya kanshi yayi nauyi jin abinda Abu yake fad’i yace “For real?, Innalillahi wa inna illaihi raji’un×2, badai akan ka akayi duka wannan abin ba?” Abu ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Har yau ni bansan dalilinsu na aikata hakan ba, all I know is itada da Mamanta da Aunty sukayi conspiring to end Batuul’s life, su sukayi causing mata duka wannan pain d’in sbd rashin tausayi, kuma har yau yarinyar bata sani ba”, Massa yace “Subhanallah, amma mata ma dai wani sa’in matsala ne dasu, what on earth could make you try such shit, akan so koko meye?”, Abu ya d’age kafad’a tareda yarfe hannayenshi duka biyun yace “Ita ta sani yanzu, kai kafi kowa sanin yanda nake tausayin yarinyar nan, I married her badan ina sonta ba, she was never my type of woman, it was just a compromise, son da take min yasa nake ganin yeah zan sota and maybe even change her but i was wrong, you were a witness tunda na aureta everything changed abt me, sai da nayi shekara without visiting home, my siblings, dukkkansu sunyi kewata, Abui, he needed me to be his support a business, Sadiq wasn’t matured enough bare yayi handling business d’in Abui, Ammah cried because of me, tayi enduring wannan ko fad’a min batayi cewa shima bayin kaina bane asiri akamin ba, amma su bar kaina su koma kan y’ar mutane kaga that is insane, ya rigada ya zama hauka, in sonta take so inyi am trying on that, bata tab’a tambayana kud’i na rage koda single penny bane cikin abinda ta buk’ata, If she were an ideal wife da su Ammah basu sani auren Batuul ba, cuz ko ni banida ra’ayin mata biyu, but she caused it all, hakanma bai isheta ba sai sunbi y’ar mutane da jafa’i?, No am not taking it, I have no problem with her saidai inma gafara ne ta roqi wacce suka cutar, wacce sukaso halakawa”, Massa ya sauk’e ajiyan zuciya mai nauyi yace “Allah ya rufa asiri, yanzu hakan tana ina?”, “I don’t know, gidansu ta tafi maybe”, wayar Massa tayi message tone, dubawa yayi snn ya mik’awa Abu wayar, karb’a yayi ya duba msg d’in snn yace “Da take damuwa da zuwana in naje zan bawa mahaifiyar tata lafiya ne?, Whatever but I know she is paying for her crimes, alhakin baiwar Allah nan ba barinsu zai yi ba su zauna lafiya”, 11
STORY CONTINUES BELOW
Cikin gida ta koma kai tsaye ta wuce kitchen tana kokarin mance duk abinda ta gama ji yamzun, Freezer ta bud’e ta ciro wani babban rubber assorted ne soye ciki duk sunyi block, plate ta d’auka ta d’ibi kad’an ta saka ciki snn ta saka a micro wave zatayi warming, kan freezer ta koma ta zauna bayan ta ciro ta d’auki fork tana cin kayan cikin, ta Bawa dake wanke fruits tace “Yaa Batuul naga baki nemi yaji ba kuma akwai su iri iri”, Batuul ta d’an yatsina fuska tace “Aunty ta Bawa kinsan a can bamuyi wani aikin nama ba, masallaci kawai mukaje muka dawo, ya dai yi mana yanka”, Ta bawa ta riqe baki tace “kai haba, toh ina aka kai ragunan?”, Batuul ta tab’e baki tace “Ehhhm, Sadaka akeyi dashi kasashen mabuk’ata”, “Ahhh lallai an gaisheku, ai koda za ayi sadaka ba duka ba, nan gaba kice a bar miki naki ko nan kya turo na gyara miki in aikace shi, wa yace duka ake sadakar?”, Batuul tayi dariya tace “Toh shikenan”, ta dubi Janet dake ta faman goge plates d’in da ta wanke tace “Janet miqo min yajin na tafarnuwa, da sauri ta kawo mata shi ta koma bakin aikinta, tana zaune tana ci Aunty ta dawo kitchen d’in taga Batuul zaune kan freezer tana take
kayan ciki tace “har ya tafi?”, kai ta gyad’a tareda amsawa bayan ta cinye wanda yake bakinta, Aunty tace “in kin gama ki sameni sama”, Aunty bata gama bama ta sauk’o kan freezer tana ajiye plate d’in ta biyo bayan Aunty, sosai sukayi having mother daughter time d’insu, ta bata addu’o’i da shawarwari masu kyau, tace ta shiga tayi wanka bayan ta had’a mata ruwan da sinadarai masu yawa, bayan ta fito ta taga wata da ganinta y’ar Tchad ce zaune, gyaran jiki Aunty tasa matar nan tayiwa Batuul tayi mata, cikin lokaci kad’an Batuul ta canja sai shek’i takeyi, saida aka gama suka sauk’o dining cin abinci, sai lokacin taga Baba da y’an k’annenta, da murna shima ta rungumeshi, koda zata fara mishi shagwab’a wayo yayi mata yace ai ta girma yanzu sai dai su Yusra suyi, haka suka zauna cin abinci murna fal ranta, har wani emotionally ta rik’a ji a ranta, bayan sun gama cin abinci mai gyaran nan kuma. tayi mata kitso, k’arfe goma daidai ya dawo, tun da ya shigo gidan idonshi ke kanta, babu abinda yake furtawa cikin ranshi sai “Subhanallah, Masha Allah cikin ranshi”, har ya k’araso cikin parlour, da murmushinta mai kyau ta juyo ta dubeshi, a nutse suka gaisa da Baba ya sake gaida Aunty, yaran ma dukkansu suka gaisheshi, a nan yake sanar da Baba gobe sha d’aya jirginsu zai tashi, Albarka Baba yayi ta saka musu tareda Nasihohi, Aunty ta cikata da abubuwa dayawa da wasu ma bata san amfaninsu ba, kamar kar ta tafi haka tayi sallama dasu suka wuce, yana barin compound d’in gidan yayi parking gefen titi ya ciro wayarshi yana haskata yace “Glitter kinyi kyau da yawa”, murmushi tayi tace “Aunty tasa aka min duka, kaga har kitso anyi min”, ta cire d’an kwalinta tareda nuna mishi sabon kitson nata, gaba d’aya motar k’anshinta mai dad’i yakeyi, hannu yakai yana shafa kitson yana lumshe ido a hankali ya dunga furta wasu addu’o’i da shikad’i yakeji snn ya bud’e idon yace “Glitter plss ki tayani addu’a ki haifa min Baby girl mai kama dake”, tayi dariya tace “nikam baby boy nakeso, kaga I want to name him after this fav name” hararanta yayi yace “wane sunane favorite d’in naki?”, batareda tunanin komai ba tace “I have loved the name tun ina yarinya, I wanted marrying someone with such a name ko kuma in haifi mai sunan, I just have a thing for the name ALIYU”, ta fad’a kanta tsaye, ajiyar zuciya ya sauk’e jin sunan da ta ambata, sai da ta ambata ta tuna mey ya fito daga bakinta, ta tun. a shima fa sunanshi kenan, ido ta rintse tana dariya, hannu yasa yana cupping fuskarta yace “Every Aliyu have his own Fatima, it happened you are mine, I can’t imagine life without you now, I love you”, itama tayi murmushi tace “I love you too”, da haka yaja mota sukayi gida, koda suka isa har Ammah tasa an gama shirya musu kaya, d’an hira suka tab’a snn sukayi sama suka kwanta, washe gari tunda suka tashi da asuba basu koma sun kwanta ba har suka gama shirin tafiya, 9 Sadiq ya fita dasu airport, Batuul dai sai kallon ikon Allah takeyi jin babu mai zancen Ajiddeh, Sadiq na dropping d’insu bai jima ba ya juyo, duk motsin da zatayi idonshi yana kanta, candy floss ta hango wani d’an yaro naci, a hankali ta juyo ta dubeshi tace “Yaa Abu inaso”, ya kalleta yaga inda take kallo yace “we should go nd get”, tayi raurau da fuska tace “Nifa na gaji, ka samomin kai zan jiraka a nan, in na tashi zan gaji dayawa”, yayi murmushi tareda lakuce mata hanci yace “okay take care, bara inje duty free nan in duba”, har ya juya yaji tace “da spicy French fries plss”, murmushi yayi mata kawai ya tafi, baifi five minutes da tafiya ba ya dawo, baisan lokacin da murmushi ya k’wace mishi ba ganinta zaune k’ark’ashin wasu manan rose Petals a wani perfume stall, sosai tayi kyau sbd kayan dake jikinta suma pink ne, abubuwan dake hannunshi ya ajiye ya ciro wayarshi daga aljihu yayi snapping d’inta pictures batareda ta lura ba,
16
15
har ya isa wajenta yana murmushi, gabanta ya tsuguna tareda mik’a mata floss d’in, da wide smile ta karb’a tayi mishi mouthing “Thank you”, kai ya girgiza mata yana nuna mata cheeks d’inshi, wara ido tayi tana blushing tana girgiza mishi kai, baza ta iya ba, kunyan shi duk ya gama cikata, ganin taqi yi ya zumb’uro mishi bakinshi ya miqe zai bar wajen, hannu tasa ta riqoshi, saida yayi murmushi snn ya juyo yana kallonta, a hankali tace “da mutane anan, in munje gida pls”, hannunshi zai sake karb’a tace “toh close your eyes”, lumshe ido yayi a hankali ta dawo gabanshi, d’age tayi sbd tsawonshi, ji tayi ya d’aura hannu waist d’inta ya d’agata sama, pecking kumatunshi duka biyu snn ta maida kanta ta sinnewa jikinshi, tafi taji duka wajen ya d’auka, tsabar kunya kasa d’agowa tayi, tana jikinshi ya mayar dasu wajensu sukayi zamansu, 11 daidai sukayi boarding jirgi, in banda bacci babu abinda takeyi, lokaci lokaci take tashi, murmushi kawai zai mata ko kuma ya tambayeta in tana da buk’atar wani abin, har suka isa UK Hawayen da kanshi nema take ya zubo ko zataji dad’i ta rasashi, ido ta k’urawa Mummy dake kwance duk jikinta anyi bandaging gwanin tausayi, tunda taga yaqi d’aga k’iranta tasan babu yadda za ayi yazo, tunanin Abutturab yasa ta jin silalowar hawayen da take ta neman zubowarsu ko zata samu y’ar nutsuwa, amma Sam abun ba haka yake ba, saima rad’ad’i da ya k’arama zuciyarta, tun da Dad ya fita bai sake shigowa ba har yau, a hankali taga Mum na k’ok’arin bud’e ido, da kyar ta bud’esu tana k’arewa d’akin kallo, kan Jainaba dake kwance ta d’aya b’arin idonta ya fad’a, hawayene kawai ya dinga silalo mata, a hankali ta maida dubanta ga Ajiddeh dake zaune, rintse ido Ajiddeh tayi ta bud’e snn tace “Mum wani irin fitina ne wannan nake gani a rayuwa?, duk wata masifa ta rayuwa na gama ganinta, Mum kece silar duk wani tashin hankali da nake ciki yanxu, tun ina k’arama tun Dad baiyi arzik’i ba, tun kamin inyi hankali na fahimci duk abinda kike so sai kin sameshi ko da ya kaucewa shari’a, tun bamuda arziki kike cewa mucewa k’awayenmu mufa y’ay’an wane da wanene, tun ban fahimta ba har na gano ma’anar inda kika dosa muka fara biye miki, babu yanda Dad bai nuna k’ok’arisnhi kanmu ba dan mu gyara amma kan ya faskara saboda kullum tare dake muke, zamanmu dake yafi yawa dole mu d’au ak’idarki, Mum kece uwa ta farko da na fara ganin bata tab’a yiwa y’ay’anta fad’a kan abinda babu kyau ba, baki tab’a tsawatar mana akan laifinmu ba, Dad ne kad’ai ke mana fad’a, ana haka Dad yazo ya samu arziki, d’an time d’inshi da muke samu yazo ya zama bama samu, duk wani jin dad’in rayuwa mun samu saboda irin son da yakeyi mana, amma ko shi Dad naga ba time d’inshi kikeda ba sai abinda yake dashi, kin koya mana son abin duniya da muka d’auka muka girma da, nima nasa a raina zanso mutum amma saboda kud’inshi”, tayi shiru tana shesheka ta kalli Mummy da ta rintse ido tana kuka, taci gaba, “Allah mai yi yadda yaso da bayinshi ya had’ani da Aliyu da kallo na d’aya naji duk duniyar nan babu wanda nakeso kamar shi, babu possible ways d’in da ban bi dan yasoni amma ko zamana baisan da ba, a haka na tareki da zancen, tashin farko Mum cewa kikayi zamuyi maganinshi, haka mukayi ta bin bokaye, duk basuyi tasiri akanshi ba har saida na samu nayi plan d’in da ya bigeni da mota, ni nasan Aliyu bai tab’a sona ba, amma saboda son da nake mishi yasa bazan iya barinshi ba, ya aureni bawai dan yana so ba, nasan ya rasa abin yine saboda matsa mishi da akayi a gida, na samu fatana ya cika, my dream came true na zama matar Aliyu amma son zuciya da tsoron rasashi suka rinjayeni, babu abinda na tashi saka mishi da sai rabashi da nayi da iyayenshi da danginshi har tsawon shekara, Allah da yake shi ba azzalumin bawanshi bane ya saka mishi, iyayenshi sanin da sukayi ba haka kawai zaiyi haka ba, ba zasu zauna suna gani d’ansu ya halaka ba suka nema mishi aure”, dariyan takaici ta saki tana girgiza kai taci gaba tace “Dole ma Allah ma yayi mishi sakayya ta alheri, mey na tab’a yi mishi na zamantakewar aure?, ko tsinke ban tab’a dagawa gidana ba bare inje ga zancen girki, a haka ya dawomin da yarinyar gida, tun had’uwata ta farko hankalina bai kwanta da ita ba, dukda kullum ina admiring duk wani abu nata, nutsuwa, kunya, k’awaici amma hakan baisani ganin gaskiya ba sabida son zuciya, Baiwar Allah jikina dama yana bani da wani abu a tattare da ita mai girma, amma son zuciyata yasa na cutar da ita, da na tab’a sanin akwai ranan da zan bud’i ido inji Aliyu na korata kan yarinyar nan da ko kallon banza ban jifarta dashi bare mugun kaba’iri, gashi a dalilin cutarta da nayi yasa yace ko kallona bai sakeyi, am not putting all the blame on you Mum, I have a commision a ciki, in kinyi abu mara ai nima nasan daidai zan iya gyarawa, shiyasa Allah ya bani hankali amma naqi aiki dashi, gashi we are accounting for all our deeds, we are reaping what we sow, Mum ni bansan mey kikaje yi har illorin ba amma nasan ba alheri bane ya kaiki, gashi nan Allah yana nuna mana ishararsa, Na kirashi yazo mu nemi yafiyarsu Mum yaqi d’agawa, ko yafiyarshi ne yazo in roqa”, Sai lokacin Mum ta bud’e idonta da suka kad’a da k’yar tace “Hauwa duk wani abu da nayi dan Ku nayishi, babu wanda nakeso da k’auna duk duniyan nan sai ku da Allah ya mallakamin, banida kowa sai y’ar uwata Jainaba, mun taso cikin k’unci nida Jainaba da nayiwa kaina alk’awarin y’ay’ana bazasu fuskanta ba, ba haka naso rayuwa ta juya mana ba, kuyi hakuri Ajiddeh, nafiku jin ciwon duk abin nan da yake faruwa, tafiyan nan da nayi duk dan nema muku farin ciki na fita yinshi, farin cikinku shine nawa, ku yafemin, ta fashe da wani sabon kukan
STORY CONTINUES BELOW
Suna sauk’a cab ya tara suka wuce d’ayan gidanshi, ko da sukaje Bacci Batuul keyi, ita kawai ya d’auka a hannu cak ya shiga cikin gida ya kwantar snn ya dawo ya kwashi Luggages d’insu ya shigar, saida ya fara wanka ya rama sallolin da ake binshi kanshi kamin ya dawo gefenta ya zauna, hannu yasa ya shafi gefen fuskarta tareda matsar da kitsonta dake kwance kan fuskartata, baccinta har dariya yake bashi, slight opportunity take jira ta rufe ido, a hankali ya furta “Glitter”, kamar ma bataji ba sai juyawa da tayi tana gyara kwanciyarta, hannu yasa d’agota yace “Sleepy head tashi kiyi Sallah kici abinci”, zumb’uro mishi baki tayi tana sulalewa saga jikinshi tace “um um, bacci nakeyi nikam”, ya d’agata ta zauna snn ya hura mata iska a fuska yace “Its getting late Glitter, kinga kuma bakiyi Sallah ba, and my Baby needs to eat”, a hankali ta bud’e ido tana mik’a, tashi yayi ya tsayar da ita taje toilet, saida tayi wanka snn tayi alwala ta fito d’aure da towel, yana zaune gaban Desktop yana danne danne, ido ya kafa mata ko k’iftawa bayayi yana roaming dukan jikinta, duk kallon da yake mata bata lura saida ta zauna zata shafa mai ta ga idonshi a kanta, zumb’uro baki tayi tace “ashe kai ke kallona shine naji towel d’ina yana so ya fad’i?”, murmushi yayi yace “ai inma bai fad’i ba ni da kaina zan cireshi”, dariya kawai tayi ta janyo hijabi ta saka dan tasan zai iya cirewan shiyasa batace komai ba, saida ta idar tukunna ta tayi shafe shafenta ta saka kaya, y’ar sweat doguwar riga ta d’auka ta saka navy blue, tashi yayi ya dawo kusa da ita yana girgiza mata kai yana isa wardrobe d’inta yace “we are going out to eat, sai mu wuce hospital, kinada appointment, kayan nan basu min ba, change into something light, waje akwai sanyi”, kaya ya ciro mata ya mik’a mata, karb’a tayi ta saka kayan, straight gown mara hannu da beach kimono peach mai brown patterns snn ta d’auki brown veil ta yafa, tare suka fita ya bud’e mata front seat ta zauna ya zagaya d’aya side d’in ya shiga, asibitin ya fara zuwa suka ga doctor, bayan ya gama dubata yace itada Babyn are all fine, shawarwari ya basu sosai akan abinda ya kamata tanayi da wanda zatayi avoiding, snn yace ta fara Exercises ko da kad’an na 30 minutes ta na kuma wasu sporting activities ko indoors ne, tun suna zaune office d’in take yatsina fuska tana jin yunwa ta k’osa subar wajen taje taci abinci, suna fitowa ta marairaice mishi fuska tace “Yaa Abu”, shi da kanshi yasan yunwar takeji amma, a hankali ya rik’o hannayenta cikin nashi yace “Yunwa ko?”, kai ta gyad’a mishi yace “sorry yanzu zamuje kici abinci, okay?”, a hankali tace “Ehen”, saida ya zaunar da ita a mota snn ya zagaya ya shiga side d’inshi, driving yakeyi yana ta mata hira duk dan ya d’ebe mata damuwar yunwar da takeji, duk inda taga restaurant sai ta kalleshi taga ko zai tsaya amma sai taga ya wuce har taga sun d’auko hanyan gida, a gaban Orwell’s restaurant taga ya tsaya da motar, ajiyar zuciya ta sauk’e amma ganin kamar babu kowa wajen ta dubeshi tace “kaga bafa su bud’e ba”, baice komai ba sai hannunta da ya kamo sukayi bakin restaurant d’in, gaba d’aya wutan a kashe yake kamar ba a aiki a restaurant d’in, bakin k’ofan taja ta tsaya, raurau tayi da ido tace “mey zamuyi a nan?, nikam tsoro nakeji, mu tafi”, hab’arta ya d’ago yana kallon idonta dake glittering yace “The trust?”, idonta ta sauk’e k’asa tace “toh fa cikin duka duhu, basu bud’e bama yau naga”, hannunta ya kama suka kutsa ciki, dukda duhun da wajen keda wani irin k’anshi mai dad’i ke tashi a wajen, a hankali taji ya sake mata hannu, sai nemanshi tayi ta rasa a wajen, gabantane ya shiga fad’i ta shiga lalubenshi, har idonta ya fara tara hawaye jikinta ya soma rawa, a hankali kamar wacce bataso a ji abinda take cewa tace “Yaa Abu”, sau biyu tana maimaitawa taji shiru bai amsa ba, da k’yar ta iya d’aga k’afa zata juya kenan taga haske ya dallare ko ina, wani irin view take gani ko ina na hall d’in sai glittering sukeyi, komai na wajen peach ne da brown, yunwar da takeji ma gaba d’aya nemanshi tayi ta rasa, sosai wajen yayi mata kyau ba kad’an ba, daga tsakiya ta hango isle dayake da wani irin haske, Abu ta hango daga gefen isle d’in jingine yasa hannunshi cikin wandon riganshi yana mata murmushinshi mai kyau, sai lokacin ta lura da itama murmushin ne a fuskarta, a hankali ya tako inda take tsaye ya mik’o mata hannayenshi duka biyun, har ta mik’ar da nata zata kama nashi ko meye ta tuna ta zumb’uro baki ta fasa, a hankali ya juyo da fuskarta ya rik’e kunnuwanshi duka biyun yace “am sorry Glitter”, idonshi kad’ai bazai barta ta iya fushi dashi ba, space d’in dake tsakaninsu ta cike tareda yin d’age ta zagaye hannayenta duka biyu ta bayanshi, shima hannayenshi yasa ya zagayeta, sun kusa minti d’aya a haka snn ta janye jikinta ta kalleshi tace “This is beautiful”, hawaye ya gani tare a idonta, kai ya girgiza mata alamun kada ta bari hawayen su zubo, dariyan da tayi yasa su zubowa a tare, shima dariyan yayi yasa hannu ya goge mata duka hawayen snn yace “Anything for you”, ya rik’o hannunta suka taka takan flower petals suka k’arasa isle d’in, suna zama wasu mutane da kana gani kasan waiters ne sukazo wajen, da hannu Abu yayi musu alama da su koma, kujerarshi ya matsar kusa da da nata ya warware mata veil d’in dake kanta ya maida matashi turban snn ya d’auki plate yayi serving mata abinci, da kanshi ya d’auki spoon ya d’ebi abincin ya kai mata bakinta, kallonshi kawai takeyi a ranta tana yiwa Allah godiya da ya sa Abu ya zama mijinta, a hankali ta bud’e bakinta ya saka mata, murmushi yayi mata yace “Yayi miki?”, ta gyad’a mishi kai tace “sosai”, sake d’ebowa yayi zai kai mata baki ta riqe cokalin ta juyar bakinshi , bai musa ba ya bud’e ta zuba mishi abincin, haka sukayi ciyar da junansu cikeda farinciki, sai suka gama cin abinci ya zagaya ta bayanta, a aljihunshi ya ciro wani diamond pendant sark’a, da kanshi ya saka mata snn ya sumkuya daidai wuyanta yayi tareda kwanto ta baya yana kissing wuyarta, ido ta lumshe tana jin d’umi da laushin lips d’inshi a wuyanta, saida ya d’ago yace “For Everything Fatima, I will forever Love you”, snn ya dawo ya zauna kan kujerar, hannunta ya kama ya zaunar da ita kan cinyanshi, wani plate ya bud’e, shima zobe diamond ne ciki sai glittering yakeyi, ido ta wara ganin kyan zoben, she wasn’t expecting it, ta kalleshi taga murmushi yakeyi tace “This too”, girarshi dake cike ya d’aga mata tareda kamo yatsanta, tace “You are not proposing to me right, we are married”, yace “You will b the girlfriend I will always want to hear from your melodious Voice, the fiance I will always dream of and the wife that will be be my responsibility to care for, my strength and weakness, a wife that will help me complete my life”, bata tab’a voicing wa kowa dreams d’inta ba amma gashi Yaa Abu kamar zuciyarta ya shiga ya gano komai, wani irin murna takeyi da tunda ta dad’e batayi irinshi ba, kai kawai ta gyad’a mishi dan bakinta ya kasa bud’uwa, shima cikeda murna yayi slipping zoben cikin d’an yatsanta na dama, ya sunkuya yayi pecking zoben, batasan mey zatace mishi ba ya nuna cewa itama mai sonshi ce, ta nuna mishi cewa shine completion d’in duk wani mafarki nata da takeyi tun tana k’arama, a hankali tayi leaning ta had’e lips d’insu, yau ita tayi dominating, sosai tayi kissing d’inshi saida ta gaji dan kanta ta zama submissive ta bashi entrance, kwanciya tayi lamo a jikinshi ta maida numfashi, a hankali ta furta “I love you more”, goshinta yayi pecking snn shima yace “I know and I love you more”, haka suka zauna suna savouring each moments tareda nunawa junansu yadda suke son juna, sai yamma suka tashi tafiya, ganin basu shiga motarsu yasa ta tambayeshi yace “Let’s walk down tunda babu nisa, I need a walk with you, zasu kawomin motar har gida”, murmushi kawai tayi ta sak’ala hannunshi cikin nata suna tafiya cikeda farinciki, a hanya take tambayanshi yaushe duka ya shirya wannan Romantic Lunch d’in, yace ya dad’e yana son yayi but yafi son sai tayi confessing tana sonshi itama, ranan da tayi confessing ranan ya fara shirye shiryen komai, ta kad’a kai tana dad’a jinjina mishi tace “Orwell’s fa babban restaurant ne, one of the best in Uk, you paid for it all?”, dariya yayi yace “tunda na fara gina wannan gidan naga yadda ake partronising na sayi franchise d’insu, wanda yake Manchester nawa ne, so we are partners, inda kud’i anything is possible” kai ta kad’a sai yanzu ta sake sanin lallai mai kud’i ne shi tunda ya iya siyan franchise d’insu ya bud’e branch a Manchester, suna hira har suka k’arasa gida da k’afa, suna tafiya yana ta d’aukanta hotuna
, farinciki fal ransu basuda wata damuwa, itace ma lokaci lokaci take tuna Ajiddeh duk sai taji babu dad’i
Washe gari tunda sukayi Sallah asuba ya sata shiryawa wai doctor yace tana yin exercises, yau zasuyi ball tare, batayi baccin asuba ba ta saka bak’in jeans da jar rigar Adidas, sosai tayi kyau abinta, face cap d’in na NY ta saka shima ja
, ita ta fara sauk’owa k’asa ta had’a teashi kuma ta had’a mishi coffee, bayan ya gama sha suka fita filin gidan daga baya akwai recreational fields iri iri, football pitch sukayi, dariya ya dinga mata ganin yanda take wasan har suka gama, duk ta gaji, ita ta fara wanka snn ta had’a mishi ruwa ya shiga shima yayi, kamin ya fito har ta shirya ta sauk’o kitchen ta dama mishi kunu ta had’a fish roast a oven tq kunna snn ta ciro bread d’in da zatayi musu musu toasting, snn ta koma sama bayan ta gama kamin ya dahu, zaune ta tarar dashi dagashi sai towel, taimaka mishi tayi ya shafa mai ya shirya snn suka sauk’o sukaci gaba da aikin tare, in ka gansu gwanin sha’awa basuda wata damuwa