SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 15
Mansur Part din mahaifiyarshi yaje, Yaganta zaune tana kallon T.V da remote a hannunta, da gudu yaje yai hugging dinta yace” Mum I’ve miss you sosai tace nima haka son ya hanya? Yace Alhamdulillah +
“Tace Masha Allah, ga abincinka chan kaje kaci kai wanka kai sallah sai kazo kaban labari, Yace” OK Mum, Bari natafi dashi part dina Kallonshi tayi Tace” why not here anan fa ka saba cin abinci komun dare, yace mum kinga I’m exhausted, so I need some rest, Kallonshi tayi cike da tsantsan So da kauna tace” OK Take Care, Kwasan abincin yayi da kanshi ya wuce part dinshi, budewa yayi yaganta zaune a tsakar gidan Kallonta yayi yace meye haka kuma meyasa baki shiga cikiba? Zunburo baki tayi, yace Hmmmmm
Dire kayan abincin yayi a parlo, sannan yaje ya kwaso sauran, Bayan haka ya bude bot na motar Ya kwaso kayan daya siya Mata, Zama yayi a kan kujera itama tana zaune akan kujera, kare Mata kallo yayi tsab, Nazeefa tai tsaki tace meye Dalilinka na kawo ni nan gidan? Kici abinci 1st yace” Sannan ya sake cewa kinganni nayi kama da masu cutar da mutane? Tsintar kanta tayi cikin jin kunya meyasa tamai wannan tambayar, Samo plate yayi ya zuba abincinshi sannan ya shiga room dinshi yaci ya koshi, sannan ya shiga toilet yai wanka daganan ya dauro alwala yai sallah ya roka Allah ya karesu daga sharrin shaidan, shima Sam yasan beda ce ba ya kawo mace dakinshi duk da taimakonta zaiyi, but he has no optins dolene tasa haka
Ya kusan 1 hour a daki Nazeefa taji shuru, ta fara tinanin kodai aljaninin ne dan ko alamun motsin mutun batajiba, mikewa tayi ta bi dakin daya shiga taganshi a tsaye gaban wardrobe dagashi se gajeren wando, yana lalubo rigar da zaisa, Kwalla ihu tayi tace Na Shiga uku, Da sauri ya waigo yai maza yasa rigan shaddan da baiyi niyya ba Dan jallabiya yaso dakkowa Gabanta yazo yace” ke bakida hankali KO? Yanzu badan karar generator dinnan ba dame kike tinanin zai faru da kikai ihu? Indai kinaso in temaka miki kar ki abun da zaki janyomun magana cos naga alamun akwai yarinta a tare dake, Sorry tacemai ta koma falo sume sume ta zauna,
Fitowa yayi, yaga abinci daya ajiye mata KO ci batai ba, hade rai yayi yace me yasa baki Ciba? Tace bakomai Ya kafe ta da ido yace oya serve yourself yanzun nan ki faraci, Yana magana ta dakko plate ta Fara zuba hadadden Shinkafa da miyan naman kaza, Ga wani pineapple juice a gefe, ci tayi sosai yace KO kefa? Hope dai kin koshi, ta daga Kai alamun eh, yace OK Ga room Chan ya nuna Mata yace ga kaya nan ki tafi dasu kije ki wanka ki Salla, ka sa duk kayan da kikeso sai gobe zamui magana KO kina bukatan wani abune? Girgiza Kai tayi Tace” No bana bukatan komai Kwashe kayan tayi ta shiga dasu taga bed room din kamar a kasar waje, Sannan ta Fara bude kayan taga Manyan dogayen rigunan da take gani a Film, Wanda Su Hadiza gabon da sauransu suke sawa, ta dafa kirji Tace oh ni Nazeefa hardasu kayan kwalliya? Ji tai kamar andasa Mata mashin Sonshi aranta Tace inama ya aureni, anya ba mafarki nakeyiba!
Dasauri ta shiga toilet tai wanka tazo ta gwada kayan duka ba Wanda be mata kyau ba kaman Dan ita akai kayan Dan sunyi fitting dinta sosai Alhamdulillah tace aranta se taji tanason Ganin Mansur din! Kwanciya tayi bacci me karfi ya kwasheta Dan rabonta da bacci irin wannan harta manta, Mansur na zaune a daki har kusan 11 yana tinanin Yanda zaiyi ya furta yana sonta, Dan gaskiya auranta yakeso yayi, shuru yaji alamun tai bacci, ya shugo dakin kamar barawo ya kare Mata kallo, kamar ba ita ba Dan wani haske ta kara ga gashin kanta ya kwanta, kana ganinta kasan bacci take hankalinta kwance, I love you yace yana murmushi, daga wayarshi yayi kirar iPhone ya dauketa hoto tana bacci, yai ma wayar kiss sannan yabar dakin Koda ya shugo dakinshi pluging phone dinshi yayi a chaji sannan yahau bed yana tinaninta, da tinaninta yai bacci Around 3:AM Nazeefa itama ta farka, tana farkawa d first thing that comes to her mind shine Mansur, kasa baccin tayi se juyi takeyi a kan gadon, taji bazata Iya kwanciyar ba, Sakkowa tayi kamar barauniya ta nufa dakin Mansur, bacci ta sameshi yanayi, kunna fitilar dakin tayi ta karemai kallo itama, tace Allah yama bawan Allah nan kyau
Mansur na bacci yana mafarkin Nazeefa, wani smiling yayi a cikin baccinsa tace ikon Allah, da sauri Nazeefa ta kashe wutan dakin tai dakinta, tinaninta Allah yasa ba ganinta yai ba Dogon tinani tayi taji aranta Tace inason bawon Allah nan but lamuranshi tsoro suke bani kodai ba mutun bane! Addua take tayi, Da yake a gajiye dake baccine ya kwasheta me karfin gaske Asuba nayi ya tashi yai sallah ya tasheta itama tai sallah Around 7:AM Mansur ya tafi part din mahaifiyarshi ya gaisheta Take cemai she has been waiting for him yester night bezoba
Yace wlhi mum nagaji Ina shiga daki nai bacci na gaji, Tace nai tinanin haka, Face din shi ta kalla taga yana murmushi Tace” what’s the secret my love? Sosa kai yayi yace mum bakomai, nan sukai wasa sukai dariya Ta bashi breakfast still yace bazaici a part dinba sedai ya tafi dashi part dinshi tace Alright bakomai …… Haleemace zaune tayi tagumi, tana Mai bakin cikin rashin zamar mahaifiyarta a gida, kullun yawon siyasa, tsaki tayi ta Kira kawarta mamashow tana sanar da itafa sunsama matsala da Mubeen, yanzu hakama tana gida, Toofa tace gatanan zuwa + Tazo suna hira sosai saiga mahaifiyar haleeman ta dawo, tagansu a gidan! Tace yadai Allah dai yasa lafiya Haleema duk tai wani iri Tace mum inako lafiya mubeen ya sakeni! Gyara zama tayi tace yame? Tace ya sakeni Mahaifiyarta tace me kikaimai kodai wulakancinshine ya tashi zai sakar mun ya’ta, Tace Eh mum banmai komai ba tana magana kamar Mara lafiya Dan wasu kuraje sun fiffito Mata Tace” karki damu za’ai uwar watsi kuwa Dan sunja ma Kansu tonan silili, duniya saitaji kosu waye sirrin da ake boyewa kuwa ya kusan fitowa, Haleema tai murmushi tace OK Mum that’s why I love you ***** Bangaren Su Mubeen kuwa hankalinshi kwance Dan yayi kyau, Mata sekaimai hari sukeyi tunda sukaji ance ya sake matarshi, Shi kam basa gabanshi *** Mansur ne zaune a daki, Yaga dai gaskiya bazai Iya zama da mace daki daya ba Dan tsoranshi sharrin shaidan, Ya Kira Nazeefa yace yace zo muyi magana! Ta ziro hijab dinta har kasa tazo ta zauna a kasa
Kallonta tsab yakeyi Dan wani Sonta kara shigarsa yakeyi! Ce Mata yayi tell me more about you wai ke bakida iyaye ne? Hawayene masu zafi suka zobo Mata tace inadasu mana Dasauri yace suna Ina? Fashewa da kuka tayi, yana lallashinta, Yace ta Dena kuka tunda Allah ya hadasu inshaa Allah komai zaizo da sauki Fara magana tayi kamar haka Tace” nima yarinyace kamar kowa amma Mara gata, saboda tun tasowa na tsintar kaina nayi kaskantarciya saboda yanayin dana sama kaina a ciki, iyayena basuji tausayi na ba tun Ina karama suka kaini aikatau, anan na hadu d gwagwarmayar rayuwa, bashi labari tayi har alakarsu da Mubeen, Daka Mata tsawa yayi yace dakata malama, kawai kicemun bakida kamun Kaine Kukan tane ya tsananta tace” ba haka bane inda kasan waye ni bazaka fada hakaba, kawai yana cikin kaddarar rayuwatace, Kuma ba laifin kowa bane na iyayenane da Ina tare dasu wani abun bazai faru da niba Taci gaba da bashi labarin Silar barin Gidan aikinta har izuwa jiya da suka ganta Hawaye sosai Mansur yayi yace gaskiyane ko karya Dan bincike sosai zanyi tana kuka Tace wallahi Kai bincike kaji gaskiya na fada maka Nan take yaji yana sonta, kishinta da tausayinta, Kallonta yayi yace sannu lalle kinga rayuwa Kala Kala Kallonta yayi yace zaki Aure na!! Mikewa tsayi tayi Tace” aurefa kace No bazan Iya aurankaba saboda bandace dakaiba Kallonta yakeyi yanda take magana daki daki Kara burgeshi, yace yes inshaa Allah I’ll marry you, rufe idonta tayi ta tashi ta shiga room dinta wai kunya takeji Mansur kuwa fita yayi, direct gidan Abdallah ya nufa, ya samesu tare da matarshi suna zaune gwanin sha’awa, suna buga soyayya, Abun ya burgeshi sosai Ya kalle Abdallah yace inason magana dakai, muje waje yace.OK Fita sukai Abdallah ya kalleshi yace lafiya kuwa? nan Mansur ya kwashe labarin Da Nazeefa ta bashi kaf
Sake Baki Abdallah yayi yace are you serious? Yace wallahi that’s what she told me kuma nasan bazatai karyaba “Ikon Allah Abdallah yace” Ya kamata kam muyi kokari Mu kaita garinsu ta hadu da iyayenta, Mansur yace nima haka nace Yace Masha Allah zamui magana idan na koma Nagode abokina Mum Mansur zaune taci kwalliya kallo daya zakai Mata kasan tana cikin kwanciyar hankali, Mansur ne ya shugo ya zauna kusa da ita yana Mata shawaba, tace Beloved son wai meke damunkane kwata kwata baka zama kana cin abinci a part dina yanzu ka girma KO? “Noo mummy yace” tace eh mana meye ne to ka fadamun yace mum bakomai fa, Tana murmushi tace ai shikkenan! Kasan yau dad dinka zaidawo kuwa? Yace yes munyi waya Dashi this morning Tace” Masha Allah **** Bangaren Mum Haleema kuwa duk abun duniya ya isheta, se jimamin an sak’o mata yarta takeyi, Ta kalle Haleema tace karki damu Ina jiran wani sakone bayan kwana biyu zamuje chan gidan Dan tashin hankali za’ai Haleema Tace OK Hajiyata Bayan Kwana biyu Dad din Mansur ya dawo anmai tarba mekyau, ya siyowa Mansur kaya Kala Kala, abunka da da daya tilo, duk abunda Mansur yakeso suna Mai, Dan yana dawowa washe gari ya chanza mai mota, ji dashi sosai sukeyi, basuda buri illa suga jikokinsu Alhaji ne zaune ya kalle Maman Mansur yace” ya naga these days beson zama damu anan? Ko akwai wani abune? Tace nima bansaniba Alhaji namai magana se yace bakomai, Alhaji ya nunfasa yace” I think aure yakeso, Ko besoma ya kamata mumai saboda age mate dinshi kusan duk sunyi aure, kinga kiramunshi ma mui magana Wayarta ta dakko ta kirashi Tace Dad dinshi nason ganinshi, fita yayi ya wuce part din sallama yayi suka amsa, ya shugo ya zauna a kasan carpet, dad dinshi yace Son, me kke jira da har yanzu bakai aureba? Kosai na zaban ma dakai nane? Da sauri ya dag’o ya kalle dad dinshi yace” No dad Zan nemo matar aure inshaa Allah “Dad Yace very good na baka nan da 2months idan har ya wuce sekasha mamaki, Zaune yake yaji wata zufa na ketomai yace” dad 2months fa kace! Yace” exactly 2month’s kasan nai magana ban chanzawa Mik’ewa Mansur yayi ya nufa part dinshi, koda ya shiga shi Sam ma ya manta akwai mace a dakin, Oh God yace” ya fada kan kujera
Nazeefa ce ta mik’e da sauri tace bakada lafiyane? Kallonta yayi bece komai ba, Daki ya mik’e ya shige itadai ta bishi da kallo Haka wunin ranar yayi beyi walwala ba kwata kwata ba, yasone Yaje yaga iyayan Nazeefa, Dan yanzu ko yace akwai matar da zai aure zasuce Ina iyayanta suke sai yasa yakejin wani iri a mind dinshi, Tsoronshi daya ma kar ace bazai aureta ba! Nazeefa ce ta Lura dashi Tace” wai ya Mansur lafiya kuwa, Yanda ta fada _yaa Mansur_ yabi labenta da kallo, a mind dinshi yace she has an angelic voice, smiling yai mata yace tinaninki nake Kara magana tayi tace ni kuma bayan gamunan muna tare, kasa magana yayi irin yanda take magana irin she don’t care dinnan “Yace yes bakyso ne na dinga tinaninki? Ta rufe ido tace inaso mana, Zata gudu kenan yace tsaya zamui wata magana ne tace OK ya mansur Ce mata yayi zaki gane garinku? Wani murmushi tayi tace Kai yaaa Mansur da Zan Iya da ba tuni nakai kaina ba, amma da dai inada number babana amma yanzu ya bace Yace ehhmmm bangane ya bace ba! Tace” da akwai cikin jakar ghana na amma yanxu banganiba Yace Ki duba jakar akwai number yananan Tace yaaa Mansur benan fa Kafeta da ido yayi yace do as i said, bata sake magana ba ta nufa dakin ta Fara binciken kayanta sosai, lungu da sak’o cikin ikon Allah saiga number a Yar takarda da gudu ta fito _Tace yaaaa Mansur gashinan wlhi na gani_ Kyalkyalewa da dariya yayi yanda ta fito kamar wata yarinya, yace good girl, ta zumbura baki tace nifa ba yarinya bane Kara bashi dariya sosai tayi cos kome tayi burgeshi takeyi Saboda characters dinta kamar na yara, Bangaren su mum dinshi kuwa suna jiran feed back dinshi, shuru sukaji mamanshi tace your excellency Bari naje na duba yaron nan Mansur da Nazeefa Suna falo se hira sukeyi, Sallamar Mum din mansur sukaji bude kofar da zatai kenan taga Mansur da wata A cikin Dakinshi Mansur mik’ewa yayi, mahaifiyarshi Tace wacece wannan? Mace dama ka kawo daki? Kiran dad da karfi tayi, Dad da yaji seda aranshi yace daga gani kiran nan bana lafiya bane Tashi yayi ya nufa part din Mansur saigashi ya shugo shima yagansu a Dakin, innalillahi wa Inna ilaihir rajiun yace, Mansur kaci amanar mu, ka cutar damu wato abunda kkeyi kenan yasa bakason yin aure ko ya Salam ya dafe kanshi Nazeefa kam mutuwar tsaye tayi tana kuka Mum tace rufemun baki, Mansur kuwa tsuru tsuru da ido yayi zufa sai ketomai yakeyi Dad da mum se innalillahi wa Inna ilaihir rajiun sukeyi Mum tsaye take tana kallon ikon Allah, Tace Son har kayi wayon da zaka kawo wata? “Yace I swear to Allah mum Is not what you mean sannan ya fashe da kuka!