UKU BALA’I CHAPTER 9

UKU BALA’I CHAPTER 9

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Saura kadan Hafsat ta bangaje Umma lokacin da ta karasa cikin gidan. domin a soro ta tadda ita, tana faman leken duk abin da ke faruwa.+

Dubanta tayi kafin ta girgiza kai, ta wuce ta cikin yanayi na kunci da bakin cikin halin-ko-in-kula da halin ƙi da suke nunawa ga ‘yarta musamman Hafsat da ƙiri-ƙiri ba kunya ba tsoron Allah take fitowa fili ta fadi mugun nufi akan Mariya da wannan tunanin ta isa ciki gidan.

zaune ta hango Goggo Marka kofar dakinta tana faman ɓarar gyaɗa tana tauna tana wakar barmana coge ganin Umma ta shigo ya sanyata yin shuri tana dubanta.

“Ai kawai aje a sanar da jama’a da Malam Nata’ala, domin yin jana’izarta tunda an shuri burji”.

Wani tuƙoƙine da bakin ciki ya tokarewa Umma wuya lokaci guda a rana daya yau taji bazata iya shanye wannan cin zarafin da cin fuska da ake yi mata ita da ‘yarta ba dubanta tayi ƙwalla cike da idanu.

“ai ƙaddarar mutuwa tana kan kowa kuma wanda ya mutu da da yanzu duk ba hanzari sukayi ba wajan barin duniya”.

Wani uban ashar Goggo Marka ta danno kafin ta miƙe jikinta har ɓari yake yi saboda tsabar masifa kamar jira take yi tayi mici-mici da idanu zanin jikinta har yana kokarin kwancewa ta watsar da gyaɗar dake hannunta.

“Ni kike fadiwa haka Habeeba eh lallai duk mai sauran rai a duniyar nan yana DA SAURAN KALLO ke har kin yi bakin da zaki yaɓa mani magana ke har kin isa”.

Ta shiga sababi har ta isa gare ta tana dungure mata goshi a daidai lokacin Hafsat ta iso cikin gidan jin hayaniyar Goggo Marka ganin abin da ke faruwa ya sanyata hanzarin karasowa tana duban Umma uku ahu tana faman yatsine fuska kafin ta ja dogon tsaki kamar harshenta zai tsinke ta ja hannun Goggo Marka suka bar wajan tana mai fadin.

“yo ana tara kartan mazaje ba dole mutuwa tayi hanzarin zuwa ba tunda jaraba da masifa ta cika zuciya ko wani kare da doki nata ne mu dai Allah ya tsare mu da kamayamaya kar ajona mana mu tafi wajan likita yayi ta aunamu kamar yadi”.

Mamaki ne ya cika Umma jin furucin da ‘yar cikinta kamar Hafsat take fadi mata duk da dai bashi ne karon farko ba da ta fara dubanta tana mata izgilanci da kalamanta amma taji maganar yau sosai har kokwan ranta girgiza kai kawai tayi ta ja

kafafuwanta da taji suna kokarin gagarar daukarta ta shiga cikin daki cike da tashin hankali mara yankewa abun ya zame mata GOMA DA ASHIRIN a filin duniyarta.

*******

Kai kawo kawai suke yi a Reception ɗin asibitin gabadaya hankalin su a tashe yake in ka zare Dr.Karami da yafi kowa fidda tsammani dafatan samun Mariya a yarda ya dauko ya saka a mota ya tukota zuwa asibiti ba tare da ta yi ko da motsin ba  hakan ya kara hautsina masa tunanin

kwanya ya firgita masa duk wani fata da burin da yake dashi akanta yayi dana sani da takaici kuma akan abin da yayi na rashin bayyanar da abin dake zuciyarsa tun kafin lokaci ya kure masa sannan ya ga bakin kansa akan yarda komai ya hautsine komai ya dakule duk a gabansa ba tare da yayi wani fata ko yinkurin yin wani abu ba ya sani Mariya zata tsane shi tsana mai tsanani a filin duniyar nan dalilin kin bata dama da yayi abin ya zame masa goma da ashirin ya

tabbata har da zancen Baseera ya so kashe ta yasani zata dauke shi a wani dan ta’adda makashin rai cikin wahala ba tare da cuta ko samun matsala ba.

STORY CONTINUES BELOW

Bai san ya lamarin zai zo masa ba amma ya tabbata sai yafi kowa shan kashi a cikin su dole ya fuskanci kalubale mai tsaurin gaske dole ya fara tanadar makaman yaki domin guntule duk wani abu da zai kawo masa hari na kalubalen da zai fuskanta.

Numfashi yake ajjewa a hankali kamar wanda ranshi yaso barin jikinsa daga baya ya tsaya kuma yake mai da numfashi duban su yake yi daya bayan daya yana ajjewa

kowannen su kallo na irin yarda yake jin kowannan su a zuciyarsa da Dr.Aqeel suka hada ido ya jefa masa kallon takaici kafin ya kau da kai lokaci guda cike da bugawar zuciya.

Motsin buɗe kofar da akayi ne ta dakin da aka kargame Mariya a ciki ya sanya dukkaninsu mikewa kan kafafuwansu cikin hanzari da firgici na rashin abinda za a zo dashi a matsayin sakamako a junansu.

Dr.Karami ya fara tarar likitan da ya fito yana faman sharce gumi kafin ya dubesu su duka da yanayi na rauni na sosai.

“Kai ne Dan’uwanta?”.

Likita ya fadi yana mai duban Dr.Karami da ya iso gareshi a hargitse kamar mahaukacin da ya balle daga gidan mahaukata.

Gyaɗa kai ya shiga yi yana faman nishi kamar wanda akayi wa dole.

Sosai likitan ke dubansa yana son gane tashin hankalin da yake ciki bai gama yanke hukunci ba yaji an kwala masa kira kamar daga sama da sauri ya juya Nurse din da suka shiga tare ne ta yafito shi da dan razana a

fuskarta da sauri ya juya cikin sassarfa yana kokarin tura kofar Dr.Karami ya sanyo kai shima zai shigo amma sai likitan ya dakatar dashi ta hanyar yi masa kallo gami da girgiza kai sa’annan ya mai da kofar ya rufe.

Dr.Karami ji yayi kamar ya kurma ihu inda yana da raunin zuciya ba abin da zai hanani shi rushewa da kuka domin yanayin da yake jin zuciyarsa ahalin yanzu yafi komai ciwo ji yake yi zuciyar kamar ba tashi ba ba abin da yake yawo a ciki illa wani irin

tausayi da mahaukacin son Mariya ji yake yi kamar ya kwato duk wata cuta da take kokarin kashe masa ita ya dawo da ita jikinsa ko zai samu burinsa da fatansa ya tabbata a filin duniyar nan haɗe kai sa yayi da bango yana faman numfashi kamar wanda yayi gudun ceton rai ko da yake za a iya kiran hakan da gudun ceton rai don yarda yake wassafa abin kamar tashin alkiyama yake kallo duk wani tashin hankali da yanke tsammanin farin ciki ya tabbata akansa a daidai wannan lokacin.

Ji kawai yayi kafafuwansa na kokarin kasa daukarsa bai san lokacin da ya sulale zuwa kasa ba ya zauna kamar wani kayan wanki idanuwansa yaji suna wani yaji-yaji zuciyarsa na zafi da raɗaɗi a hankali ya fara ambaton sunan Allah a bakinsa yana faman sakin huci mai zafi.

Shigar likita cikin dakin ya tadda Nurse gaban na’urar da take tafiyar da yanayin wanzuwan numfashin mara lafiya da sauri ya isa wajan ganin numfashin da ya samu ya kwato da kai da taimakon Allah yana kokarin kufcewa aka karo na ba adadi da sauri ya isa wajan yana duban na’urar kafin ya sauke dubansa kan Mariya dake kwance sambal wacce bata da mara da gawa ga Oxgyen da yake kargame a hancinta a hankali ya kai hannunsa saitin makoshinta da kirjinta yana tabawa komai yaji ya sauya ba a yarda ya barshi ba idanu ya zaro kafin ya sake duban na’urar wacce take nuni da numfashin yana kara samun ragwanta da sauri ya zaro abin auna mara lafiya ya jona mata a kirji kafin ya soka abin a kunnuwansa lokaci guda ya zare ya isa ga na’urar yana tabe tabensa tun yana yanke tsammanin samuwar komai har ya fara firgita da yanayin numfashin da sauri ya isa ga Mariya yana dubanta ita kanta Nurse din abin ya fara fidda mata da tunani daga kai da sauri ta iso wajan tana duban likitan kafin tayi wani yinkuri wanda take fatan samun daidaituwar komai likitan ta kalla wanda ya gama firgita sosai a hankali takai hannayenta saman kirjin Mariya ta shiga dannawa da sauri-sauri a daidai lokacin Na’urar tayi dan kara tafiyar numfashin ya fara canzawa cikin yanayi na

STORY CONTINUES BELOW

farfadowa daga suman da yayi hakan da Nurse din ta ga ya bata daman saurin cigaba da danna kirjin Mariya kamar zata burmasshi ita da gadon shi kuwa likitan gaban Na’urar ya isa ya shiga dube-dube yana kokarin saita komai.

Lokaci mai tsayi suka dauka suna abu daya gabadaya sun gama hada gumi da fidda tsammani da fata akan Maryia domin tafiyar numfashin ma yaki gaba yaki baya iya kokarin su sun yi amma abun ya ci tura lokaci guda fuskar Nurse din tayi rauni kamar wanda zata fashe da kuka danna kirjin Mariya take yi zuciyarta na kara karyewa da rauni mai girman gaske hawaye lokaci guda suka shiga zubo mata ba ta bi takan su ba illa kokarin na ganin ta ceto numfashin wannan baiwar Allah a hankali ita kanta numfashin nata da kirjinta su fara sauyawa da bugu ganin

numfashin ya fara yin kasa ta tabbata yayi kadan gabadaya sai dai wata amma ba Mariya ba kokari ta kara kalatowa da jarumta ta shiga dannan kirjin Mariya tana duban Likita da komai yake shirin wargaje masa kamar ƙyafta idanu Na’urar ta saki wani sauti lokaci guda numfashin ya shiga tafiya da sauri-sauri yana cike gurbin da bai kai ba lokaci guda ya dawo yarda ake so Mariya dake yashe Nurse na danna mata kirji wani yin kuri tayi kamar wacce aka bugo kasan gadon tayo sama sannan ta koma ta sake yin wani yinkurin kafin nan ta koma da sauri Nurse ta shiga rirrike ta.

Gwauron ajiyar numfashi likita yayi yana dauke gumin da ya tsatsafo masa a fuska kafun ya iso ga Mariya da take ta faman jan numfashi ta hanyar Oxgyen dubanta ya shiga yi kafun wani lokaci yayi kokarin ganin komai ya daidaita duban Nurse yayi tare da yi mata jinjina ganin yarda tayi firgai-firgai da ita kamar wacce ta kwato kanta daga bakin kura.

Ya jima yana bakin kokarinsa kafun ya saita komai sannan ya fice daga cikin dakin.

Da hanzari Dr.Karami ya mike daga yashen da yake gefen guda yana faman cizon laɓɓa kamar mace mai nakuɗa sosai yake duban likitan cikin yanayi na tabbacin abin da zai fada masa mai dadin ji ne ko sauraro sosai tsoro da firgici su ka bayyana a idanuwansa kirjinsa da zuciyarsa sautin bugunsu yana ansa wa cikin gangar jikinsa ruhinsa kuwa ji yake yi kamar ya shuri burji ya bar jikinsa ya zama matacce.

Sai da ya gama firgicinsa yana ta faman jan numfashi magana yake so yayi amma ya kasa sai haɗe hannayensa yake yi waje guda yana matsewa yana faman mazari kamar wanda ake kaɗawa gangi shi kansa likitan tsayawa kallonsa yayi sosai ya fuskanci akwai wata alaƙa mai karfi tsakaninsa da Maras lafiyar wanda hakan ya kasa boyuwa a gareshi.

“Doctor don Allah…”.

Furucin da Baseera take kokarin yi kenan lokacin da ta hango fitowar likita gabadaya ta gama firgicewa sai faman jan numafshi take yi bakinta na ɓari ta hadiyi yawu mai tauri kafin taja fasali ta sake dubansa tana goge hawayen da suke ta faman ambaliya a fuskarta.

“Karka ce mani ta mutu domin kuwa ba wai ita kadai ta mutu a filin duniyar nan ba akwai rayuka masu muhimmanci a duniyarta da za su salwanta wanda kuma har dani bana tunanin zan iya juri da yin

TAWAKKALI in Mariya ta zarce in da ba a dawowa domin na tabbata ba zata yafe mani ba na tabbata ina da laifi mai girma wanda na san zuciyarta ta kunsa kuma ba zaya yafen ba…”.

Nishi tayi tana faman hade hannayenta waje daya alamun roko kafun ta dubi Dr.karami da ya runtse idanu kana hango yarda kirjinsa ke dokawa kau da kai tayi tana kara jin zuciyarta na karye da tsananin tashin hankali mai girman gaske.

“Karka ce mani ba zan sake jin sautin Muryarta ba karka ce mani ba zan sake cigaba da rayuwa da ita a filin duniyar nan ba don Allah Doctor kace wani abu”.

STORY CONTINUES BELOW

Dubansu yake yi daya bayan daya har da su Dr.Aqeel da Huzaif da suke ta faman kokawa da numfarfashinsu tashin hankalin su na daduwa gabadaya sun gama firgicewa sun gama yanke tsammani da numfashin Mariya a doron duniyar nan.

Nisawa yayi kafun ya dubi Baseera dake ta faman rusar kuka.

“Ki tsaurara kalaman ki kamar ba ‘yar musulma ba ko Mariya mutuwa tayi bai kamata ace kina irin wannan maganganun ba dole ki saka tawakkali a zuciyarki dole ki anshi ko wacce irin ƙaddara ce ta faɗo duniyarki…”.

“Ya isa haka Doctor”.

Dr.Karami ya tare shi yana faman jan numfashi ya buɗe idanuwansa akan sa sosai sun kaɗa sunyi jajir jijiyon kansa duk sun fito sunyi ruɗu ruɗu.

“Ya kamata kayi abin da zai kawo kwanciyar hankali da natsuwa a garemu duk wani dogon turanci ba zai tsayar da kalamin da kake cewa bai dace ba abu daya zaka fadi wanda duk zai kau da rashin hayyacin da muke ciki”.

Magana yake amma da ka kalle shi zaka gane akwai dauriya da juriya a zuciyarsa amma in ba don haka ba da tuni ya zube akasa a hankali ya shiga lumshe idanuwansa ya na matsawa jikin bango ji yayi kafafuwansa na kokarin zubda shi kasa jingina yayi da bangon zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri.

“Ban san wa zan fuskanta ba”.

Likitan ya fadi yana dubansu domin gabadaya sun gama rikita shi da rashin hayyacinsu.

Dr.Aqeel ya tako gareshi da hanzari ya roko hannunsa sosai.

“Fada min ni ne makusancinta me ke damun ta…”.

Wani haushi ne da zafin zuciyata ya turnuke Baseera jin abin da Dr.Aqeel yake fadi dubansa take yi da idanuwanta duba na raina hankalinka cizon laɓɓanta tayi kafin ta kara dubansa sosai.

“Mukusanci fa kace?…”.

Ta fadi tana dariyar da ta fi kuka ciwo kafin ta sake cewa.

“kawai cewa zakayi kana cikin yan ta’addan da ke kokarin salwantar mata da rayuwa”.

Da sauri ta dubi likita.

“Don Allah na rokeka karka saurare shi kar kace dashi komai game da Mariya domin ba amfanin da zai iyayi akanta illa ya kara turbudata cikin tashin hankali duk da sun yi ajalinta”.

“Doctor Please Rabu da su don Allah ni ne mai kaunar ta nine masoyinta na asali…”.

“Karya kake yi..wai don Allah me kuke son mai da ita ne ta shuri burjin ma ba za ku daina hauka kuna saka mata bala’i ba”.

Baseera ta sake katse Huzaif da ya iso shima yana cewa wani abu.

“Yaa Allah wai anya kuwa kalau kuke anya kuwa ba kune kuka saka zuciyar baiwar Allah nan take kokarin bugawa ba haba mana menene haka kuke yi gabadaya kun rikita ni na rasa wajan da zan duba na fuskance shi”.

“Doctor ni zaka fuskanta”.

Kamar daga sama suka tsinkayo muryar Dr.Karami cin sauti mai ansa amo sosai da sosai a hankali ya fara takowa da wani irin yanayi tattare dashi karkasahinsa da mazantakar da yake tattare da ita jarumta da zuciyarsa ta gayyato masa duk ya ajje su saman fusakarsa lokaci guda duk wata kwalla da take kokarin samun gurbi a idanuwansa  ya haɗiye su yanayin takunsa da sautin da takalmarsa ke bayarwa ya sanya likitan dubansa duba na sosai da sosai zuciyarsa ta yarje masa da cewa wannan shine makusancinta na kut da kut.

STORY CONTINUES BELOW

Gaban likitan ya zo ya tsaya sosai kan kafafuwansa duk da raunin da suke kawo masa hakan ya jajir ce yana jin yarda yake tsoro da kuma fargabar ansar abin da likitan zai sanar dashi zuciyarsa narkewa take yi da tashin hankali wani fili mai girma da ya jima da gina shi ya ajje Mariya a ciki ji yake yi yana kara buɗewa da wani yanayi na so mai girma sai yau sai yanzu a daidai wannan lokaci ya ya gama AMANNA akan son da yake yi wa Mariya sai yau ya gasgata da gaske yana sonta so mai ansa suna so sosai yake jin zuciyarta ta gama ajje GURBIN SO ako wani sashi da fanni na cikin ta ya yarda ya kuma amince son Mariya A JININSA YAKE a jikinsa yake son Mariya shine farincikin rayuwarsa son Mariya ya gama tafiya da duk wani imaninsa na filin duniyarsa.

Likitan da yake can kasa da Dr.Karami ya dago kai ya ajje idanuwansa akan nasa sosai yake hango wani lamari mai girman gaske lamarin da a lokaci guda ya ba shi suna da SO sone aciki son wanda son yake tsammani ita ce akwance ita ce wacce aka kawo bata da lafiya…

“Ni ne makusancinta ni ne dan’uwanta ne ni komai nata a filin duniyarta ni ne farincikin rayuwarta ni ne…”.

Kau da kai yayi da sauri jin zuciyarsa na kokarin harbawa da wani irin so mai girma ba ya tunanin zai iya daukar abin da likitan zai fadi a wannan lokaci yana tsoron yace masa da gaske ta mutu yana tsoron yace masa AN KASHE SO don ya tabbata son sa za aka kashe farin cikinsa zai kare a filin duniyarsa Mariyaaa ce.

“Akan wani dalilin zaka dauki wannan lamarin ka jingina wa kanka a matsayinka na wanda bai san WACECE ITA ba akan mi zaka ce kai ne makusancinta akan me zaka ce kai ne kafi kowa kusanci da ita”.

Dr.Aqeel yake fadin haka a zafafe yanayin sa kawai zaka kalla ka gane danyen so da yake ji na Mariya sosai zaka fuskanci zallar so mai ansa suna so a filin fuskarsa har da gurbin zuciyarsa.

Nishi yake ajjewa yana kallon Dr.Karami da wani irin yanayi kafin yayi taku daya zuwa uku ya daga dan yatsarsa daya ya nuna Dr.Karami dashi.

“Ka sani in akwai wanda yafi cancanta ya zama makusancinta da komai nata ni ne nan!”.

Ya fadi yana nuna kansa yana dukan kirjinsa da karfi cikin sauti mai ansa amo sosai har jijiyoyin kansa na fitowa duk da duhun fatar da yake da ita.

“Bana tunanin a filin duniyar nan akwai wanda ya dace da ita kamar ya ni ka sani Dr.Karami ta dalilina kasanta ta dalilina kansan wacece ita kafin kasanta ni ne nan na fara saninta kuma tare ka ganmu!”.

Ya sake fadi cikin hargagi kamar zai kaiwa Dr.Karami duka ya juya ya dubi likitan yana kokarin yin magana Baseera ta daga masa hannu cikin tsananin haushi da takaici.

“duk wannan abin da kake yi IHU BAYAN HARI  ne mutuniyar da kuka kashe har kake da karfin zuciyar da zaka zauna kana dambe akan ta mutuniyar da kuka zama ajalinta har kake ikirarin kai ne makusancin ta mutuniyar da ku ka birkitawa rayuwa har kuke tsammanin akwai wani lalen kati da za ku buga akanta kaico!”.

Ta kareshi da murmushin takaici a fuskarta kafin ta shiga nuna dakin da Mariya take kwance.

“ko wannan ku ya kamata yaje ya tanaji duk wani kaya da ya sani ana jana’iza dashi domin shine kadai abin da ya kamata a daidai wannan lokaci Bala’in da kuka daurawa rayuwarta ya zama ajalinta..ko da yake dama ta fadi tun da dukkanku son ta kuke sai ku je ku dandatsata ko ya dauki ka sonsa”.

kuka ne ya kawo mata hari amma ta hana zuciyarta karaya ta hana idanuwanta zubda kwalla ta hana kanta yin rauni so take yi ta kwatarwa ƙawarta ‘yancinta sai yau ta kara tabbatar da so bala’i ne so masifa ne sai yau ta kara tabbatarwa ba komai bane a cikin so sai tashin hankali duk wani kauɗi da ganɗoki da ake fadi da kambawa so na dashi na kayan jindadi da kwanciyar hankali ta karyata a so in dai haka so yake to gwanda ta zauna batayi aure ba in har sai anyi soyayya za ayi aure.

STORY CONTINUES BELOW

numfashi take ajjewa idanuwanta izuwa lokacin sun gama cika da kwalla jingina tayi da bango tana zamewa har ta zube a kasa kamar wata kayan wanki nishi take yi so take yi hawaye su zo mata amma ina zuciyarta taki aminta mata wani zafi da raɗaɗi take ji tausayin Mariya yana kara ratsa jinin jikinta sosai take ji a jikinta in har mutuwar Mariya ya tabbata to ita kam ba zata taba yarda tayi so da wani ba domin ta tabbata SO AJALI ne ba komai ba.

“Bata mutu ba”.

Runtse idanuwa tayi jin sautin kalmomin da suke ansa kuwwa a kunnuwanta ji take yi kamar a mafarki ji take yi kamar kalmar ta fito ne don kar ta sanya wa kanta abin da zai nakasta mata rayuwa laɓɓanta duka ta tura cikin bakinta tana cizawa zafin da taji ne ya sanyata buɗewa idanuwanta da saurin abin da ta ganine ya sanyata  mikewa da hanzari.

Dr.Karami, Dr.Aqeel,Huzaif gabadaya taga sun cikwuikuye likita kamar zasu raba shi gida Uku.

Wani murmushi ne mai tafe da hawaye ya kufce mata kamar wata zautacciya haka ta tunkaro inda suke sai faman jinjiga shi suke ‘wai ya tabbatar musu da gaskiya’ duk kansu ta shiga duba da mamaki gami da wani irin farinciki mai girma gaske hadiye miyau tayi mai tauri kafin ta shiga nuna shi likitan da yatsa tana kuma nuna dakin da Mariya take.

“Are You Sure?”.

gyaɗa mata kai yayi runtse idanu tayi.

“Yaa Allah…wayyo Allah na me ma ya dace nayi..yawwa….likita kasan mi…kawai mu je na ganta…please”.

Ta hade hannayenta bayan ta gama rawar baki wajan furta kalaman rokon ja da baya yayi domin kwace kasan daga rikon da firgitattun mazajen har uku sukayi masa sai faman ajiyar numfashi yake yi.

“Sosai take cikin matsala ba zan boye muku ba zuciyar tace ta kusan bugawa saboda tsananin damuwa da tashin hankali da take ci ban san mai yasa a kananun shekarunta ba ta fuskancin wannan matsalar har haka sosai naji tsoron yanayin da na ganta bani da tabbacin a halin da ake ciki a yanzu yarda zata farfado numfashinta dai yana harbawa nayi irin kokarina yanzu dai tana bukatar hutu sosai kafun muga yarda Allah zai yi”.

Dukkansu ajiyar numfashi suka saki mai karfi gabadayansu har sai dashi likitan ya dube su da mamaki Baseera ce tayin hanzarin dubansa.

“Please Doctor zamu iya zuwa muganta?”.

Dubanta yayi kafin ya dube su Dr.Karami ya girgiza kai.

“A,a wannan ta’addacin da naga anayi a nan in kuka shiga tayar mata da hankali zakuyi har abin da ake gudu ya afku”.

Yanayin da yayi maganar a dake ya sanya su zuba masa idanu suna kallon ikon Allah juyawa yayi ya koma cikin dakin kafun cikin mintina ya fito ya kama gabansa ba tare da yace da su komai ba.

Nan suka shiga kai komo a tsakaninsu Baseera kuwa sai kwaɓa take yi da tsaki kamar zata tsinke harshenta tana faman zabga musu harara kamar idanuwanta za su fado kasa lokaci-lokaci take isa kofar dakin tana lekewa amma bata hango komai dalilin labulan da yayi wa kofar shamaki.

Cikin wannan yanayin suka ji sautin takun takalma akan tayal din da yake malale cikin asibitin dukkansu suka jiyo jin sautin wajensu yake tunkarowa gabadayan su sakin baki sukayi musamman Huzaif da yayi fakare da idanu kamar wani gaula Hafsat ce take taku cike da isa da yanga sai faman taunar cingam take yi kamar wata Magajiyar karuwai daidai inda Huzaif yake tsaye ta tsaya ita ma ta karewa su Dr.Karami kallo kafin ta dubi Baseera da ita mata ta kalle ta ta watsar cikin nuna ban san ma Allah yayi halittar mai kama dake a nan ba hakan yayi wa Hafsat zafi domin dama can basa jituwa sam! a tsakaninsu duban Huzaif tayi wanda shima ita yake duba gabadaya jikinsa yayi la’asar sosai sai faman gyaɗa kai yake yi kamar wanda aka kama da laifin da bashi ya aikata ba.

STORY CONTINUES BELOW

Dage laɓenta na sama tayi kamar wacce taci karo da kashi tana wani dakune hanci kafun ta hura cingum din bakinta tayi katon kwai ta fasa masa a fuska.

“ban san mi yasa in ana gayyar tsiya nake ganin ka ba ban san min da yake sanyawa kake gangancin shiga ciki ba kai gabadayanka ba ka hada hanya da tsiya ba amma in ka ganta jikinka har wani ɓari yake yi kamar tsoho ya samu danyen jini budurwa danya sharaf a daren farko”.

Gyaɗa kai yayi cikin rashin abincewa Dr.Karami jin abin da Hafsat take fadi sai abin yayi matukar bashi mamaki ba yau bane farkon haduwarsa da ita da kuma yarda take rashin kunyarta amma yau yayi matukar mamaki da yanayin da ta nuna musamman ganin halin-ko-in-kula da ta nuna akan ‘yar uwarta Mariya da halin da take ciki wani yawu mai tauri ya hadiye kafun ya kau da kai cikin kunar zuci.

“Ban san mai yasa kake wahalar da kanka a inda ba a yin ka ba ance ba a sonka an tsaneka amma kaki daukar zuciyarka kayi nisa da inda ba ayi da kai haba sai kace mai MATACCIYAR ZUCIYA wanda ya yada kare ya dauke ya cinye tas!”.

Kuri yayi mata da ido ba tare da yace komai ba kuma da alamun bashi da niyar cewa din.

Murmushi tayi na wulakanci kafun ta dora da cewa tana nuna shi da dan yatsa.

“Wai kai ma so kake yiwa biyayya ko? ka biyo wannan zugar ta mara sa zuciya kai ma ka yaɗa hajar son ka ko za a saya kaico!”.

“ni ban san wata ƙaddara bace ta sanar dake ki dauko shanyayyun kafafuwanki ki zo wajan nan ba in ban da rashin zuciya da rashin aikin yi me ye naki a ciki ko akwai wani wanda kuke alaƙar mutunci dashi ne a nan da kika zo?”.

Baseera ta fadi cikin takaicin kalaman da Hafsat din ta fadi dubanta tayi shekeke kamar taga kashi.

“Ke kuma a soyuwa zaki sako min kazamin bakin ki mai dan banzan wari”.

“Ke dalla rufewa mutane baki yan fashi da makami kawai ke ko kunya baki ji ba ko da yake dama ba a gaje ta ba shiyasa tunda ba aji kunyar kwacen saurayi ba ai ba za aji kunyar biyo saurayi ba”.

Baseera ta sake fadi tana kau da kai daga kallon Hafsat da ta gama cika da bakin ciki da kalaman Baseera  din duban Huzaif tayi wanda gabadaya kallo daya zakayi masa kasan yana cikin rashin hayyaci da kwanciyar hankali tsaki tayi rai a bace ta wurga masa wani kallo kafin ta juya cikin sassarfa ta bar wajan.

Ba wanda ya bi ta kanta nan suka ji gaba da jajen zuciyoyinsu har zuwa wani lokaci mai tsayi da ya kwasar musu awanni uku cir!.

Sannan likita ya sake zuwa zuwan nasa da ya kasance na biyar kenan yana dubata ba tare da ya bari sun shiga ba tausayin su yaji matuka da yanayin da ya gan su a ciki hakan ya ba su damar zuwa ganinta amma a bisa sharaɗin ba wanda zai yi ko da magana ne ta a zo a gani hakan suka yarda suka shiga yarda take haka take sai Oxgyen da yake taimakawa

numfashinta yana kai kawo kirjinta na faman dagawa kamar zai faso waje sosai suka tsorata da yanayin da suka ganta don Baseera sai da ta toshe bakinta kuka ne ya kusan kufce mata kallon Mariya take cikin tausayi

wacce lokaci daya duk ta zube dama yaya lafiyar kura balle kuma ta balle da gudawa duk fuskarta faɗa sai kwarmin idanu ruwan da aka saka mata sai faman tafiya yake yi Dr.Karami ne ya isa gareta

idanuwansa na zagayawa a kanta da wani irin yanayi na rauni da tausayi gami da matsanancin so kau da kai yayi jin zuciyarsa na tsalle kamar zata faso kirjinsa ta fito gaban na’urar da take nuni da yanayin tafiyar

numfashinta ya isa ya shiga kallo na dan lokaci yana faman ajiyar zuciya kafin likitan ya shiga yi musu bayani akan komai da yake afkuwa da ita na damuwa da kuma bugawa da

zuciyarta take kokarin yi sharuɗa ya kafa musu sosai akan matsa mata da ake yi da kuma sanya mata damuwa da sanyata gaba ana mata rigimar da zata firgita mata zuciya sosai suka anshi sharuɗar kafun ya ba su dama kowanne yayi waje Baseera da

Dr.Aqeel da Huzaif ne suka tafi gida amma shi Dr.Karami ya zauna akanta a matsayin wanda zai kula da ita duk wani abun da za a bukata duk da likitan yace ba sa bukatar mai kulawa daga wajan majinyaci amma ya ki yarda akan haka dole likitan ya kyaleshi bayan yayi masa ikirarin shima likita ne.Sunkoyawa yayi da zubar debo ruwa a gorarsa har ya nitsar da ita sosai yana kokarin dagowa yaji ta maƙale gabadaya taki daguwa hakan yayi matukar daure masa kai shiru yayi kamar mai tunani wani abu kafin ya sake dago gorar tasa amma ina! sai yaji kamar an kara daura mata gingimeman dutse.+

“Ja’e zo ka taya ni gorata ta ki hidduwa daga ruwa”.

Ja’e dake tsaye yana gabzar danyen Mangwaro ya juyo ya dube shi kafin yace.

“Ban fahimce ka ba me kake nufi?”.

“Zo ka gani mana don Allah”.

Ba tare da ya sake cewa komai ba ya tako zuwa wajen ya dube shi sannan ya dubi gorar da tayi kasa amma ga bakinta nan.

“Jayota mana kai ma sai kace wani sakakke ya za ayi gora ta makale a ruwa?”.

Sake janyota yayi amma ina taki daguwa da karfin gaske ya fizgota gabadaya yayi baya ya zube a kasa gorar tayo waje sagale da ruwan rigar mutum hadi da kansa duk sunyo waje Ja’e dake tsaye bai san lokaci da ya kwala ihu ba ya ari na kare ya falle kamar wani zomo da yan farauta suka biyo shi Iro da ya baje cikin ciyayi mai taɓo ganin abin da Ja’e yayi ya tabbatar masa akwai abin da ya gani shima cikin tsorata da firgice ya k’urma da gudu shima ko tsayawa ganin abin da ke faruwa bai yi ba gudu ya shiga yi da yake irin siraran mutanan nan ne marasa jiki ga tsayi nan da nan ya kamo Ja’e da ke ta fama haki kamar wanda ya ɓalle daga lahira ya fado duniya.

Ba su tsaya tambayar juna ba suka sake arcewa gudu sukayi sosai har sai da suka fara hango bunkokin rugar su kafin su tsagaita suna mai da numfashi Ja’e ya sunkoya riƙe da kafafuwansa yana duban Iro da yake gabansa.

“Aradun Allah Iro lahira na hango”.

Ya fadi yana mai waige-waige cikin tsananin firgici da razana Iro da yake can nesa dashi ya dube shi cikin rashin fahimta.

“Ban gane ba kaifa baka da hankali wa yace maka ana hango lahira daga nan duniya”.

Nishi Ja’e ya saki na wahala kafin ya tashi tsaye sosai ya dubi bayansa sa’an nan yace.

“mutum ne fa kamar gawa na gani rike da Gorar…wai hala kai baka gani bane?”.

Iro da yayi shiru yana sauraron Ja’e jin abin da yace ya sanya shi ware idanu waje.

“Aradu ban gani ba kawai biyo ka nayi don na tabbata abin da ka gani bala’i n…”.

A guje suka sake kwasa suna zunduma ihu kamar wasu zararru sai faman tsalle-tsalle suke kawai don sun ji motsi abu cikin ciyayin da suke kusa da ita da wannan yanayin suka karasa cikin rugar ihun da suke ya firgita mutanan cikinta nan da nan kowa ya shiga kallon su ana tambayar dalili amma ba wanda yayi kokarin tsayawa balle ya basu ansar abin da ya jefa su cikin firgicin da suka samu kan su.

Da yake rugar ba mai girma bace kallo daya zakayi mata ka gane ZURI’A DAYA ce ta hadu a wajan don bunkokin na su tsilli tsilli suke a lissafe ba za su haura goma ba.

“Iro wai kalau kuke kuwa? Wannan wani irin wauta ne da girman ku da komai amma kuna wannan shiriritar”.

Tsohon da suka gilma gindin wata bunka ya shiga fadin haka cikin yanayi na jin haushin abin da ya ga sunayi don mafiyawancin lokaci haka suke indai suka dawo kiwo sun dinga nuna yarintar su ke bayan kuma a shekaru ba wanda bai haura ashirin ba kuma ko wanne da matarsa ta aure.

STORY CONTINUES BELOW

Ba su bi ta kan sa ba sai da suka karasa shiga cikin jerin bunkokin da suke kafun kowa ya faɗa bunkarsa cikin halin firgici nan da nan matan da suke wajan su ma suka tashi suna kokarin kwasa da gudu amma tsohon nan ya hana su .

“Mariye jurɗe don Allah karku biyewa shiriritar su Iro kun san dai halin su ba sai na fada muku ba indai daukar hakki ne sun iya shi wajan tayar da hankalin mutane”.

Cak! Suka tsaya suna duban sa zuciyoyinsu na harbawa domin sun tsorata da yanayin da suka ga su lron.

“Amma Baffa kamar wannan yanayin da suka shigo dashi ya bambanta da sauran lokuta alamu ya nuna kamar akwai dai abin dake faruwa”.

Gyaɗa kai yayi yana murmushi kafun ya gyara tsayuwar malfarsa akai yana duban surukan nasa.

“Nikam zan ga ranar da za ku daina daukar lamarin su Ja’e…”.

Ihun da suka ji an kurma ne gabadayan su suka juya da sauri suna duban Bunkar Ja’e Asiya ce ta yo waje a guje kai ko dan kwali babu zani na kokarin kwance mata sai faman mazurai take gabadaya ta firgice.

Jurɗe ce tayi sauri isa gareta tana rukota sosai a hannunta ganin yanayinta da firgici.

“Lafiyarki kuwa Asiya meke faruwa mai ya samu Ja’e?”.

Jikinta na mazari ta shiga nuna bunkar kafun taja numfashi mai karfin gaske.

“wai gawa suka gano a bakin kogi”.

Ta ida tana mai kokarin rike zanin jikinta dake kokarin subuce mata.

“Gawa!!!”.

Su ka fadi su duka cikin yanayi na zaro idanuwa waje Baffa da ke tsaye tun dazu da sauri ya kwaɗawa Ja’e kira yana tunkarar bunkar cikin hanzari.

Ja’e dake makale cikin bunka sai faman mazurai yake yi jin muryar Baffa ya sanya shi takowa a hankali kamar wanda aka ce gawar tana biye dashi sai da ya leko kafun ya fito wani kallo Baffa yayi masa kafun ya dube shi sosai.

“Wai shin me ke faruwa ne naji matarka tace wai gawa kuka gano bakin kogi ya abin yake ne ina shi Iron yake?”.

Cikin yanayi na firgici Ja’e ya hadiye numfashi mai tauri kafun ya dubi Baffan nashi.

“Aradun Allah Baffa Gawa ce Iro yaje debo ruwa a garo kawai sai ya ganta”.

Cikin rashin fahimta Baffa ke duban sa kafun ya kwalawa Iro kira cikin hanzari ya fito shima yana faman mazurai har yafi Ja’e firgici ya tako ya iso matarsa na biye dashi sosai da sosai Baffa ke dubansa cikin yanayi na nazarinsa kafun yace.

“Ina jin ka me ya firgita ku?”.

Rarraba idanu ya shiga yi kamar mai tsoron yayi magana gawar ta riko shi numfashi yake ja a hankali kafun ya dauke gumin da ya tsattsafo masa a goshi.

“Baffa gawa ce na gano bakin kogi naje debo ruwa to shine gorar tawa ta makale nayi-nayi ta fito amma takiya sai da nayi daƙyar sannan na jayo ta a nan ne sai ga gawar mutum ta biyo gorara”.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!”.

Gabadaya suka dauki salallami suna duban Iro da yayi firgai-firgai kamar wanda suka karawa firgici Baffa yayi ajiyar numfashi mai kwari cikin rashin aminta da zancen domin shi dai ba ya ganin wannan lamarin zai tabbata tunda ba yarda za ayi ace a tsinci gawa a bakin kogi shi dai ya san tun da yake zaune a nan sama da shekaru ashirin kogin nan bai taba cin mutum ba balle yace gawar wani dan rugar tasa ce sake duban su yayi ganin har yanzu suna cikin firgici ya sanya shi nazarin son zuwa ya je ya gani domin tabbatarwa idanunsa abin da ke faruwa numfashi ya sake ajjewa kafun yace.

STORY CONTINUES BELOW

“Mu je na gano ni dai zuciyata ba ta gasgata maganar taku ba bana tunanin haka zata faruwa domin tunda nake ban taba ganin kogin nan yaci mutum ba amma dai…”

Sai yayi shiru yana nazarin wani abu kafun ya sake dubansu yana mai cewa su je amma cikin su ba wanda ya motsa sai mazurai suke da mamaki yake kallon su ganin ba wanda ya motsa balle yace dashi wani abu.

“Magana nake yi daku fa cewa nayi muje ku nuna min ko?”.

Nan ma ba wanda ya motsa sai dakuna fuska suke yi kamar za su fashe da kuka kamar wanda ba mazaje ba  sosai Baffa ke mamakin halayensu na tsoro tun da yake haihuwa bai taba haihuwa ‘ya’ya maza masu bakin tsoro kamar su ba ko don suna tsakiyar mata ne oho! shi wani lokacin abin mamaki yake bashi sannan kuma ya bashi takaici musamman in yayi lakari da har iyali suka ajje amma yarinta bata bar su ba.

Tsuke fuska yayi cikin yanayi na rashin wasa muryarsa da sauti mai nuna bacin rai ya shiga nuna su da hannu.

“ku wuce muje tun kafin ranku ya baci bana son sakarci kun ji ko”.

duban juna sukayi kafin su ja jiki su fara tafiya wannan ya tura wannan wannan ma ya tura dan uwansa Baffa ya shiga bunkansa ya dauko sanda sannan ya sauya riga ya fito ya dubi surukan nasa dake tsaye cirko-cirko sannan ya juya ya tafi tun da suka fito daga sashin su yawancin matayen rugar suke bin su da kallo don sun tabbata ba lafiya tun da suka ga Baffa da kan sa.

Tafiya suke yi kamar wanda ba sa son zuwa Baffa na biye da su da sun tsaya sai ya daka musu tsawa cikin wannan yanayin suka tunkari kogin  zuciyoyinsu suka fara lugudan bugu suka fara tirjiya kamar dabbar da ba ta son zuwa inda za a kaita ganin da Baffa yayi ba su da niyyar karasawa sai ya raɓa su ya wuce yana mai watsa musu kallon na raina muku wayo.

Tun daga nesa Baffa ya fara tsinkewa da lamarin hango abu da yayi bakin kogin ruwa sai wuce yake yi ta wajan amma ba alamun motsi bakinsa dauke da addu’o’in neman tsari ya tun kari wajan zuciyarsa na harbawa amma haka ya dake ya isa wajan ba karamin razana yayi ba sosai ganin mutum zube a kasa rabin sa a waje rabinsa a ruwa turkewa yayi daga nesa yayi nazarinsa sosai ya tabbatar da cewa ‘eh’ gawa ce dagaske domin ganin yarda fuskar ta kumbure sosai ba ma ka iya gane halintarsa ta asali da hanzari Baffa ya isa har zuwa lokacin zuciyarsa da bakinsa ba su daina karanto addu’o’i ba ya tsorata sosai tsoron da ya kusan sanya zuciyarsa firgici har ya fara shakkan zuwa wajan gawar domin bai san abin da ya faru da wannan mutumin ba bai san mai ya kashe shi ba sannan yana tsoron abin da zai je ya komo musamman a halin rayuwar da ake ciki na yanzu baka san hawa ba baka san sauka ba fada TARKO da zai kashe maka rayuwa shi kuwa ba zai so haka ba baya fatan rayuwarsa ta kare da tashin hankali wanda zai hana zuri’arsa samun nutsuwa suma sosai zuciyarsa take karanto masa shafi-shafi na matsalolin da zai iya fadawa amma duk da hakan zuciyar tasa ba tayi tasiri ba domin wani bangare na cikin ta yana kwadaita masa ribar TAIMAKO a rayuwa numfashi yaja mai karfi kafin ya hadiye wani yawu mai tauri ya juya ya dubi su Iro da suka kara yin nesa dashi suna hangensa daga nesa murmushi yayi duk da halin da yake ciki bai taba ganin matsorotar maza irin su ba.

Sai da ya kwashe mintina masu dan dama kafun ya karasa wajan gawar ya durkusa yana karewa fuskar kallo mai cike da suma kallo daya yayi masa ya gane babban mutum ne zuciyarsa yaji ta bugu lokacin da fuskar mutum tayi masa gizo da wata fuska da ya taba sani duk da dai ya manta a ina ya san ta amma fuskar tana yi masa kamanceciniya a hankali ya sanya hannu yana jayo shi daga cikin ruwan gabansa na cigaba da bugawa sosai gefen kogin ya ajje shi yana kare masa kallo zuciyarsa na ta nazarinsa kafun ya mike cikin yanayi na JARUMTA ya dubi su Iro da suka kara matsawa can nesa tun lokacin da suka ga ya fara kokarin fiddo da gawar da hannu yayi musu alamu su zo amma ba wanda ya motsa ganin in ya biye musu ba abin da zai yi hakan  ya sanyashi takawa ya isa garesu.

STORY CONTINUES BELOW

“kuje ku taho mani da amalanken shanu yanzun nan ina jiran ku”.

Duban sa sukayi cin rashin fahimta kafun Iro ya motsa laɓɓansa a dan tsora ce.

“Baffa Amma…”.

Hannu ya daga masa cikin alamun yayi shiru.

“kuyi abin da nace muku kawai bana son jin komai”.

Yanayin da yayi maganar rai bace ya sanya su jan jiki suka bar wajan da sauri domin yin abin da ya umurce su.

Nan ya tsaya yayi shiru abubuwa da yawa suna masa yawo akai zuciyarsa sai kai komo take yi akan lamarin nan sosai da sosai abin ya daure masa kai bai san yarda zai kwatanta lamarin ba bai san ya zai dauke shi a zuciyarsa ba sosai yake jin wani iri a jikinsa abin da bai taba faruwa dashi ba tun da yake a rugar nan tashi sama da shekaru ashirin kenan amma abun ya zo masa kamar almara numfashi yaja kafun ya ɗaga kai ya dubi gawar daga inda take kwance mamaki al’ajabi duk sun baibaye zuciyarsa.

Bai san me duniyar nan take so ta zama ba, bai san ya zamanin nan yake so ya zama ba, bai san me al’ummar nan ta wannan karnin suke so su zama ba, sosai yake tsoron duniyar nan a wannan zamanin sosai al’ummar cikinta suke firgita shi komai ya sauya tashin hankali an mai dashi kamar abin ado kisan kai abu mai sauki a yanzu kamar ran kiyashi zuciyarsa kuka take yi sosai in ya tuna al’ummar nan yarda suka ɓace a wannan zamani zai iya yuwuwa wannan bawan Allah kashe shi akayi ba tare da laifin sa ba kila yana da iyali a yanzu haka Allah kadai ya san matakin da suka kai na tashin hankali haka rayuwarsu zata dauwama kullum zuciyarsu na kuka tana kunci na rashin tabbacin inda yake…

Karar amalanken da yaji ne ya katse masa dogon tunanin da ya faɗa da sauri ya juya ya dube su sannan ya nisa.

“Meye yasa kuke abu ne kamar ba masu hankali ba, mai yasa kuke abu ne kamar ba ‘ya’yan musulmai ba, mai yasa kuke abu ne kamar ba masu imani ba, mai yasa kuke abu kamar ba masu tausayi ba, mai yasa kuke gudun dan’uwan ku, ban san dalili ba? ko shakka bana yi duk da dai ban san waye wannan mutumin ba amma na tabbata yana da alaka da addinin musulunci ko ba ku da dangantakar komai da za ku iya taimakonsa dashi ya kamata ku dubi dangantakar addinin da kuka hada dashi shin ba kwa tunanin irin wannan lamarin ya faru da ku ko wani naku shin ba kwa tunanin ku faɗa halin rayuwa irin haka shin za ku so a bar ku cikin irin wannan mawuyacin halin ko wani dan uwa naku ya kamata ku sani duk zuciyar da bata taimako sannan bata tausayi to bata cika mai imani ba ya kamata ku sani shi wannan bawan ba shi ya saka kansa cikin wannan halin ba ina mai gargadin ku ku fidda tsoro a zuciyarku ku ajje komai na sakarci ku dauki hankali da natsuwa ku daurawa kan ku fisabillalahi yanzu in aka bar wannan mutumin a haka me kuke tsammanin zai faru dashi a amtsayin na matacce amma ba ayi masa suttura ba dabbobi ne da tsintsaye za su zo fa suna cin namansa wanda ba haka aka so ba ku kan ku na sani nan da dan wani lokaci in dai yana nan wajan wallahi ba za ku iya zuwa ba a yanzun ma kuna tsoronsa a haka ina ga kuma suffarsa ta fara canzawa ya kamata ku canza rayuwarku ku da zuciyoyinku tun wuri!”.

Shiru sukayi suna jin abinda Baffa ke fadi lokaci guda jikkunansu sukayi sanyi zuciyoyinsu suka mika su wani mataki na daban wanda ba su san suna dashi ba sosai suka ji wani yanayi mai girma ya dalsu a zuciyoyin su tsoro da fargaba ya shige su sosai dangane da maganganun Baffa sai faman rauyasa kai suke bai ce da su komai ba ya fara kokarin karkata akalan amalaken yana kora shanayen ganin haka ya sanya su sauri zuwa suka anshe shi duban su yayi kafun ya kau da kai sosai yaji dadi a zuciyarsa ganin maganganunsa sun yi tasiri a garesu a hankali ya fara takawa suna biye dashi har suka isa wajan gawar hannu ya saka yana kokarin daukarsa duk da a zuciyarsa yana ji ba zai iya shi kadai ba amma bai so yayi musu magana so yake yi ya ga halin da suke ciki sannan da yanayin da suka shiga a game da maganar tasa bai gama tunaninsa ba yaji su a kusa dashi a tsaye suna faman bin gawar da kallo sannan suna bin shi shima da kallo kafun su saka hannu duk da zuciyoyinsu suna harbawa amma duk da hakan sai da suka raruma jarumta suka sakawa kansu suka taimaka suka saka gawar a amalanken kafun suka hawan suka fara kokarin kaɗa shanun amma ya tsayen dasu isa yayi wajan wata bishiyar dogon yaro  ya sanya hannu ya katso reshe mai girma  da yake bishiyar ba tsayi gareta ba sosai kuma shi dama mai tsayi ne zuwa yayi ya lullube gawar dashi kafun ya hau su ja su tafi zuciyar sa cike da tausayi da jin ƙai ga wannan gawar abubuwa sosai yaji suna yawo akansa da zuciyarsa.

STORY CONTINUES BELOW

A wannan yanayin suka shiga cikin rugar duk aka shiga bin su da kallo cike da yanayi na dan firgici a daidai saitin bunkarsa suka tsaya su Mariye duk sun fito daga bunkokin su sun yi tsarko-tsarko sai faman mazurai suke yi kamar wanda za ace musu kes! su kwasa da gudu.

“Taimaka mu shigar dashi daga ciki ko”.

Ya fadi yana duban Iro da yake duban Baffa tun dazu yana son sanin abin da za ayi sun dauko gawa sun kawo gida bai san kuma abin da za ayi yanzu ba numfashi ya ja kafun ya dubi Ja’e sannan suka kama ba tare da sun buɗe gawar ba suka tattara har ganyen suka yi cikin Bunkar dashi ajje shi sukayi kan tabarmar dake shimfiɗe a tsakar bunkar duk suka saki ajiyar numfashi kafun Iro ya sake numfasawa a karo na biyu.

“Baffa yanzu me za ayi masa to?”.

Murmushi yayi kafun ya shafa kasumbar fuskarsa wacce ta fara zama fara fat!.

“Kokari zamu yi mu yi masa suttura mu kai shiga gidan sa na gaskiya shi kadai ne gatar da za muyi masa”.

Gyaɗa kai sukayi dukkannin su suna masu sakin ajiyar numfashi mai girman gaske.

“Amma Baffa kana ganin haka ya dace ba fa mu san shi ba, ba mu san daga ina yake ba kana ganin in muka yi haka ba wata matsalar?”.

“Ja’e kenan yanzu ya kake so muyi in ba mu yi masa gatar kai shi gidansa ba in muka ce sai mun binciko wanene kasan lokacin da zamu dauka ba fa RAI gareshi ba, ba ma wannan ba yanzu in muka ce sai mun binciko yan uwansa ta ina zamu fara ba da wani haske ko tsani da za mu bi ya kai mu matakin da muke so lalube kawai muke a duhu hanya daya ce kawai muyi masaa suttura duk da dai ba mu san alkiblar da yake ba amma a zuciyata nayi amanna musulmi ne”.

Da mamaki suka dube shi.

“Baffa kai ma dai da wata magana kake ai da ka kalli wannan zaka gane musulmi ne duk da dai ba a fuska ake rubutawa ba amma yanayin suffar mutum ma Allah na nuna yanayin sa da kuma zaton da za ayi masa na alkiblar da yake kalla”.

Ficewa sukayi gabadayan su waje suka tadda matan rugar da tsirarin maza sun yi dandazo suna jiran fitowar su Baffa kallon su kawai yayi lokacin da ya fito ya san za ayi haka dama dole su ne mi ba’asi ta yarda suka ga an shigo da mutum wanda suka tabbatar ba kalau ba kuma suka ga sabon abu da ba a tabayi a rugar ba.

Cikin son fitar da su daga kokwanto nan Baffa ya shiga sanar da su abin dake faruwa ba karamar razana da tsoro suka nuna ba musamman matan masu tausayi wasu har da hawaye nan dai ya ja mazajen cikin su gefe duk da yawancin sauran sun fita kiwo ba sa nan musamman manyan ‘ya’yan Baffa.

Nan dai suka ba shi goyan bayan akan shawarar da ya yanke nan cikin kankanin lokaci ka shiga kokarin suttur tashi Baffa da kan sa ya shiga yi masa wanka cikin wannan yanayin wani al’amari ya so daurewa Baffa kai koma yace ya daure masa ya sanya shi tsayawa akan abun da yake yi domin ya lura cikin gawar na dan motsawa kadan-kadan alamun numfashi da farko bai yarda ba ya dauka juyawar da yake yi masa na wakan yake motsa cikin nashi amma sai yaga akasin haka da sauri ya mai da komai gefe ya ajje yana kallon sarautar Allah.

Abu kamar wasa cikin hukuncin Allah sai ga motsin ya cigaba dayi har hannyensa sun fara motsawa nan da nan Baffa ya fita ya kira su Ja’e ya nuna musu abin da ke faruwa sosai suka nuna tu’ajibinsu.

“Baffa ko dai yana da rai ne bai mutu ba?”.

Cewar Ja’e.

STORY CONTINUES BELOW

“Akwai alamun ran  a jikin sa kasan mi yanzun kamata yayi mu taimaka masa tunda alamun ya nuna da ransa”.

Cikin hanzari Ja’e ya mike yana duban Baffa.

“Bari na kira Malam Jauro Mai Magani Baffa”.

Ba tare da ya jira ansar su ba ya fice jikinsa na ɓari dama ya matsu ya bar dakin domin gani yake kamar FATALWA ce ba wai sahihin mutum bane ya farko.

Ya jima kafin ya dawo tare da Malam Jauro din irin mutanan nan ne masu maganin gargaji na kauye kafaɗarsa rataye da jaka ta fata kallo daya zakayi masa kasan ya tsufa sosai fuskarsa duk ta tattare abin ka da bafulatanin mutum ba kauri sai tsawo ga wani gemu da ya ajje yayi masa tsiri a haɓa yayi fari tas! dashi.

Taimkon gangawa ya fara yi masa magani ya hada na sauyoyi ya murtsuke su kafun ya tsiyayi ruwan ya baiwa Baffa ya dura masa duk da izuwa wannan lokacin jikin nasa ya daina motsi hannu Baffa na k’yarma ya kai maganin saitin bakin sa yana mai furta Addu’ar neman dacewa ya shiga dura masa amma hakoran sunki buɗewa sai zubewa maganin yake yi a jikinsa ajjewa yayi gefe kafun ya sanya hannu ya buɗe bakin sosai wanda ya kunbure sosai jini duk ya taru masa laɓɓan nasa sun canza kala sunyi bakinkirin alamun mataccen jini a hankali yake dura masa wani na zubewa wani na wuce har ya gama ya mikewa Malam Jauro kokwan yana mai ajiyar numfashi kusan awa guda ana abu daya amma ko motsi bai sake yi ba amma Malam Jauro ya tabbatar musu da cewa yana da rai in Allah ya yarda zai tashi nan ya basu magunguna wanda za a dunga shafa masa da wanda za a dinga bashi na tsawon lokacin da zai farka domin ba karamar jika yayi ba jikinsa duk a kunbure yake ta ko ina sosai da sosai rigar jikinsa Baffa yayi kokarin cewa wacce gabadaya ta gama rine da jini.

Sosai Babba ya tsorata lokacin da ya gama cire masa rigar dak’yar wacce sai da ya yage ta ba dai ya fidda ita ta wuya ba saboda mannewa da tayi da ciwon dake jikin nasa hannunsa na dama da ya kumbura ya suntume Baffa ya kurawa ido sosai yana nazarin sa kafin wani lokaci ya gane harbi akayi wanda ya same shi a hannun nan ya shiga kwaɓa wani magani wanda Malam Jauro ya bashi ya shafe masa wajan dashi kafun dukkannin su su fice daga cikin dakin zuciyoyinsu cike da fargaba da yanayin da suka gan maras lafiyar a cikin in ba don Malam Jauro yace akwai numfashi ba ba su yarda ba musamman Ja’e da Iro wanda sukayi zaton kawai dama can a mace yake ganewa ne ba suyi ba suke ganin kamar motsi yake yi duk da wani ɓari na zuciyoyin su na sanar da su da sauran numfashin sa.

******

“Anya Baffa wanna mutumin zai tashi kuwa?”.

Cewa Ja’e dake faman gasa masa jiki da tafasheshen ruwan magani wanda izuwa wannan lokacin jikin nasa ya sabe sannan kuma numfashin sa na fita a hankali.

Baffa wanda ya kure shi da ido tun dazu yana kallonsa  yau kwana biyu kenan zuciyarsa na damuwa da lamarin mara lafiyar nan da ya tsinta sosai ya damu sosai yake son ya ga ya tashi kan kafadun sa yana so ya san ko waye shi yana son ya san wani abu game dashi sosai yake ji a zuciyarsa wani lamari mai girma yana tattare da shi zuciyarsa da idanunwansa suna nazarin fuskarsa wanda har zuwa wannan lokaci bata dawo daidai ba ko idanun nasa bai iya buɗewa.

Numfashi ya ja kafun ya dube Ja’e.

“zan so ace ya tashi kan kafafuwan sa sosai nake bukatar haka ina so ya dawo duniyar nan ya cigaba da rayuwa sosai nake ji a jiki akwai wani al’amari da zai faru a game da wannan mutumin ko da dai ban san sa ba amma ina ji a jikina akwai wani abu a boye”.

Shiru yayi yana duban Baffa jin abin da yake cewa wai akwai wani abu da yake zaton zai faru anya kuwa meye zai sanya kansa damuwa akan mutumin da bai san shi ba bai san daga ina yake ba…

STORY CONTINUES BELOW

Motsin shigowa haɗe da sallama da akayi ya tsinke musu zaren tunanin da suke yi Asiya ce ta shigo hannunta dauke da kwarya cike da damammiyar salala mai dauke da hadin magani a ciki durkusawa tayi har kasa.

“Sannu Baffa gashi an gama”.

Ta fadi tana mai ajjewa gefe guda tana mikewa kan kafafuwanta bayan ta karewa mara lafiya kallo zuciyarta da tausayi sosai a ciki sannan ta fice tana mai dauke kwallar da suka kawo idanuwanta hari.

“Baffa!”

Ja’e ya fadi da sautin murya yana mai zaro idanuwa waje cikin yanayi na firgici da sauri Baffa ya dube shi kafun ya sauke idanuwansa kan maras lafiyar jini ne ke fitowa ta bakin sa bakikkirin kirjisa sai faman harbawa yake yi cikin sauri-sauri ko ina na jikinsa sai motsawa yake yi kamar wanda aka jonawa wayar nepa da hanzari Baffa ya mike ya isa wajansa yana dafeshi cikin yanayin fargaba ganin jinin sai bulbulowa yake yi yaki dainawa.

“Maza Ja’e maza tashi ka kirawo Malam Jauro yi hanzari”.

Tun kafun ya rufe baki Ja’e ya fice daga gudu cikin kankanin lokaci suka iso a tare Malam Jauro na kallon abin dake faruwa bai wani damu ba ya dubi Baffa.

“Ba wata matsala bace buguwar da yayi ne jini ya tarun masa shine yake amayar dashi hakan ma duk cikin samun sauki ne”.

“Haba Malam Jauro ya zaka ce haka ka ga mutum na aman jini amma kace ba komai anya kuwa”.

“Ni na fada maka ai in ka lura da jinin ai ba lafiyayye bane ya rigaya ya lalace ko ya tsaya masa a jiki ba abin da zai haifar masa sai wata matsalar cutar ka kwantar da hankalin ka in Allah ya yarda zai farko kuma cikin sauki”.

Ajiyar zuciya Baffa yayi mai girma kafun ya koma gefe yana sharce gumin dake ta faman tsantsafo masa a goshi.

Jini sosai ya zubar kafun wani lokaci ya lafa nan Malam Jauro yayi masa yan daburansa kafun ya dura masa wani magani da ya ciro daga jakar sa sannan ya bukaci wani abu mai dan dumi mai ruwa-ruwa domin ya bashi nan take Baffa ya mika salalar da Asiya ta kawo sai da ya kare mata kallo kafun ya dubi Baffa.

“Dama ba a bashi ba tun dazu da nace”.

“Yanzu aka gama ina kokarin bashi sai ga wannan lamarin ya afku”.

Ba tare da ya sake magana ba ya shiga dura masa salalar a hankali cikin ikon Allah ya buɗe baki ya mikawa cikinsa sakon abincin da yaji yana saukar masa amma duk da hakan idanuwansa a runtse suke ba su buɗe ba sai da ya sha sosai sannan Malam Jauro ya dubi Baffa.

“In Allah ya yarda komai zai zo da sauki tun da hakan ta kasance yanzu dai ku bar shi zuwa wani lokaci muga yarda Allah zai yi”.

Gyaɗa kai sukayi suna yi masa godiya kafun ya mike ya sabi jaƙarsa ya fice daga bunkar.

Haka su Baffa suka cigaba da jinyarsa a hankali yana samun lafiya jikinsa na komawa daidai sai dai magana ce ba ya iyayi sam! sannan idanuwansa sun buɗe sai dai  mutane ma dishi-dishi yake gani a haka har sati guda ya shuɗe Baffa bai gajiya da taimaka masa ba shan maganinsa cin abinci har makewayi shi yake taimaka masa ya kai sa da kan sa daidai da rana daya bai gajiya ba da kansa yake za gayawa dashi cikin rugar domin motsa jiki shi ya zame masa DAN JAGORA lokaci lokaci yana tambayarsa waye shi? Amma ba ya bashi ansa sai dai idanuwansa suyi ta zubda hawaye yayi ta kokarin yin magana amma ba dama sai dai yayi ta jan numfashi a haka har suka saba da Baffa sosai da sosai mutanan gidan ma haka rugar gabadaya ba wanda bai san DAN MAKAHO ba sunan da suke kiransa dashi kenan ko DAN KURMA a haka ake ganewa amma ba sa fadi gaban Baffa domin fada yake yi sosai ya nuna bacin ran shi akan haka domin komai ya samu bawa na dadi da akasin sa DAGA ALLAH NE kuma tun fil’azal ALKALAMIN ƘADDARAR bawa ya rubuta hakan sai ta faru dashi a duniyarsa.

Shakuwa sosai Baffa yayi dashi domin a zuciyarsa yana jin wani bakon yanayi game dashi lokaci lokaci yake jin gabansa na faduwa wanda ya rasa dalili musamman in yana kallon fuskarsa sai ta dinga yi masa gizo da wanda ya taba sani amma ya rasa tunanin da zai kara masa haske akan fuskar cikin wannan hali suka shafe wata guda izuwa lokacin idanuwansa sun buɗe sosai yana ganin kowa da kowa ranar da ya fara ganin fuskar Baffa ba karamin yanayi na fargaba ya shiga ba  zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri-sauri lokaci guda ya firgice sai mazurai yake yi ji yake kamar ya kwashi kafafuwarsa ya zura da gudu ko kuma ya nutse cikin kasa jikinsa sai ɓari yake yi Baffa dake gefensa yana ta faman bashi labarai sam bai lura da abin dake faruwa ba motsin mikewa da yaji yayi ne ya sanyashi dubansa ganin yanayi da yake ciki ya sanya shi mikewa ya riko masa hannu.

“Lafiya me ke damunka?”.

Baffa ya fadi yana mai dunduba jikinsa kafun ya sauke idanuwansa a saitin nasa hakan ya kara fadar masa da gaba shi kansa Baffa ji yayi gabansa ya yanke ya fadi lokaci guda…Sosai zuciyarta take bugawa a duk lokacin da Al’amarin Auranta da Dr.Erena ya zo mata filin tunaninta komai nata kwancewa yake yi komai nata take ji yana canzawa kamar ba nata ba.+

Ta rasa ya zatayi ta rasa mai ya kamata tayi zuciyarta na zafi zuciyarta na raɗaɗi raɗadi mai girman gaske kudirin zuciyarta kawai take hangowa da ta dauka akan

wannan azzalumin mutumin bata so abin da zai hadata dashi a inuwa daya sam-sam ko zaman da take yi a Company sa kawai tana yi ne  don cinmma burinta amma ga yarda lamarin ya kasance har ya kai ga zancen aure a tsakaninsu.

Bata san wata irin rayuwa zatayi a gidansa ba bata san ya zata zauna ba zuciyarta na zafi tana shiga kunci duk lokacin da tunanin aurenta ya fado mata ba ta shirya masa ba ko da na kwana daya ne amma ba yarda za tayi tunda Hajiya Layla ta nuna kaunar ta akan lamarin kuma ta wannan hanyar ce kawai za su samu abin da suke so.

Sosai take mamakin yarda Hajiya Layla ta dauki lamarin da girma ta bada lokacinta da komai da ta san zai taimaka wajan tafiyar da komai yarda ya kamata.

“Areefa bawai ina son ki auri Dr.Erena bane a son raina a,a wallahi in da zan buɗe miki zuciyata ki ga bakinciki da takaicin da take yi akan wannan lamarin zaki ce naki ba komai bane amma na daure na mika zuciyata wani mataki na hakuri domin ganin ta yarje wannan lamarin ya kasance”.

“Maama ban san ya zan koyi zama da makiyina ba ban san ya zan koyi zama da mutum kamar Dr.Erena ba daidai na sakan daya ne wai da sunan a idanuwa daya a matsayin mata da miji”.

Wasu hawaye suka zubo mata a kunci masu dumi bata yi kokarin dauke su ba domin ko ta yi hakan ba daina zuba za suyi ba.

Hajiya Layla ce ta saka hannu ta dauke mata tana mai kwantar da ita kan cinyarta.

“Areefa ina so ki san wani abu guda san nan ki saka shi a zuciyarki auren Dr.Erena ba yana nufin kashe miki rayuwa bane auren Dr.Erena ba yana nufin numfashin ki ya daina wanzuwa bane a doron duniyar nan ki sani rayuwa ce zaki yi ta daukar fansa a gidansa wacce nake tsammani ita ce hanyar da tafi dacewa sannan ke dai ki zuba ido kiyi kallon komai zaki sha mamaki akwai ranar da zata zo da kan ki zaki zo kina bukatar al’amarin da yake wanzuwa a daidai wannan lokacin ba zan sanar dake komai yanzu ba amma duk ranar da komai ya tabbata zaki san komai”.

Tashi tayi tana duban Hajiya Layla cike da mamakin furucinta sai faman juya idanu take yi tana rausayar da kai tana kokarin yin magana wayarta ta dauki Ring juyawa tayi ta dubi wayar a cikin jakarta dake yashe tun da ta dawo aiki yau gabadaya ta kasa sukuni ta kasa zaune ta kasa tsaye Hajiya Layla ce ta kai hannu ta dauki jakar ta fiddo da wayar ta mika mata ba musu ta ansa ganin mai kiran ya sanyata saurin dagawa don dama kamar ya san ta na cigiyarsa don sun kwana biyu ba su hadu ba gabadaya ta shiga wani irin yanayi na tashin hankali musamman yarda Dr.Erena ya sako ta gaba akan ta bashi dama ya turo domin neman aurenta.

Numfashi taja jin muryar Alhaji Abdulwahaaab ya ambaci sunanta.

“Areefa ina kika shige kwana biyu ne?”.

Numfashi ta hadiye mai tauri kafin ta dubi Hajiya Layla.

“kai dai kawai bari al’amarin duniyar nan ne yake neman sha mini kai wallahi akan maganar mutumin ka ne Dr.Erena”.

Murmushi yayi mai sauti wanda har sai da Areefa taji sosai kafun yaja numfashi.

“kisan na kusan barin duniyar nan kuma ba wanda na daurawa sai Dr.Erena kisan an tare ni a hanya akayi min dukan tsiya har sai da na rasa kai na…”.

STORY CONTINUES BELOW

“What! Me kake cewa Alhaji Abdulwahaab duka fa kace Yaa Allah!”.

Ta fadi tana mikewa a razana lokaci guda ta ji kanta ya buga ta sanya hannu ta dafe shi sai numfashi take saki da sauri sauri kamar wacce tayi gudun ceton rai.

“kenan sai da yayi abin da yace zai yi ko wai shin me ke damun wannan mutumin ne na lura gabadaya shi cinnaka ne bai san na gida ba”.

“Rabu dashi kin ji yanzu ya maganar ku ina kuka kwana akan batun auren naku don ya kamata ace kin ajje duk wata fargaba da tsoro a zuciyarki kin fuskance shi sosai ki yarda ki bashi hadin kai a yi aure nan wannan dama ce sosai a gareki da zaki cika burin ki gami da kudirinki”.

“bana tunanin zuciyata zata aminci bana tunanin zan ita zama da shi bana tunanin burina da  KUDIRINA za su tabbata in dai ta hanyar aure ne tsakanina da Dr.Eren…”.

Fizge wayar taji anyi da sauri ta juya ganin Hajiya Layla taga fuskatar ta sauya da bacin rai ya tabbatar mata da bata so abin da take fadi ba.

“Alhaji Abdulwahaab”.

Hajiya Layla ta fadi bayan ta daura wayar a kunnanta kafin ta nisa bayan ya ansa.

“Karka damu da duk abin da take ce maka Alhaji Abdulwahaab zuciyar Areefa ban san abin da ke damun ta ba amma ka bar komai a hannu na ni dai taimakon da nake so kayi mani a wannan tafiyar a yanzu ka neman min mutanan da za su kasance a mtsayin iyayen Areefa ina son cikin watan nan bikin nan ya tabbata…”.

“Maama!!!”..

Areefa ta fadi tana zaro idanu waje kamar wacce ta ga mugun abu wani kallo Hajiya Layla tayi mata tana sauraron abin da Alhaji Abdulwahaab yake sanar da ita akan komai zai gudana ba matsala sauke wayar tayi ta cillar da ita kan kujera kafun ta dubi Areefa.

“ya kamata ki san wani abu guda daya lamarin nan fa sai ki ajje duk wata kiyayyer da kikewa Dr.Erena a gefe ke kin sani mutum ne dan duniya in har  kika bada matsala wallahi tsaf zai kashe ki har ni da ma duk wanda ya san suna hada hannu damu don haka tun wuri ki san abin yi kuma ina so in kin fita aiki gobe ki sanar dashi kin aminci nan da sati guda ya turo”.

Baki ta saki tana kallonta cikin mamaki da takaici a zuciyarta komai take ji yana canza mata duniyar taji tana juya mata da tashin hankali mai girma wani ciwo taji mai girma zuciyarta na kara shiga kiyayyar Dr.Erena na daɗuwa girgiza kai ta shiga yi kafun ta yi hanyar dakinta da gudu tana sakin wani numfashi mai wahalar gaske.

Wannan rana haka Areefa ta wuni cur! ba wani akayan farinciki har zuwa dare ko runtsawa ba tayi ba Hajiya Layla ta zo ta bata baki amma ina tashin hankalin da take ciki ya zarce a kwatantashi gabadaya a firgice take ba ta shirya ba bata da lokacin yin wannan aiki zuciyarta ba zata aminci ba.

Haka tayi ta saƙe-saƙe har zuwa wani lokaci kafun wani barawon barci yayi gaba da ita a nan zube tsakar daki.

*****

A sanyaye take shiryawa gabadaya jikinta ya mutu sosai take jin zuciyarta na mikata wani mataki mai girma gaske yana haifar mata da wasu lamaruka masu girma a zuciyarta numfashi take dak’yar ji take yi kamar wacce ake toshewa hanci da baki.

Turo kofar da akayi ne ya sanyata hanzarin mikewa Hajiya Layla ce ta tokare bakin kofar tana binta da kallo kafun ta kau da kai.

STORY CONTINUES BELOW

“Kisan karfe nawa yanzu kuwa Areefa? Wai mai yasa bakya jin magana ne Areefa ya kamata kiyi hanzarin shiryawa ki tafi aikin nan rashin zuwa aikin nan zai iya canza tunanin mutumin nan ta inda baki taba zato ba wallahi ke da kanki kwanaki kike bani labarin abinda wata ta zo tana gaya masa akan ki na cewa ba don Allah kike aiki a Company din sa ba akwai KUDIRI da kike dashi a zuciyarki ba ki tunanin wannan tunanin ya fara tasiri a

zuciyarsa bakya tunanin in bakya nan ta sake zuwa ta sanar dashi har akai matakin da zai yarda yanzu ya dace ace kina nan nan dashi ya gane eh da gaske auran sa zakiyi sannan karki sake ya gano ko yar karamar hanyar da za ta bashi dama ne ya fahimci wani abu wallahi in baki iya kama barawo ba to tsaf! barawo zai ka maki Dr.Erena da kike gani ba karamin kwallon shege bane…ko dayake ba sai na fada miki ba ke kan ki kin san waye”.

Tana gama fadin haka ta juya da hanzari ta bar dakin ta bar Areefa tsaye tana kokarin sanya dankunne cak! ta tsaya tana jin maganganun Hajiya Layla nayi mata yawo akai tunanin faruwar wani abu daban da yarda zata kasance ya dire mata a zuciya tabbas ta sani dole wani abu ya faru in har tayi sake musamman yanayin da Mufeeda take kokarin sanya Dr.Erena ya so ta ta sani ko wani hali kuma komai zata iyayi don cin ma burinta.

Cikin hanzari ta karasa saka dankunne ta saka takalmi kafun ta kara gyara fuskarta sosai da sosai ta dauki jakarta bayan ta duba kanta a MADUBI sa’annan ta fice daga cikin dakin bata samu kowa a falon ba hakan ya tabbatar mata Hajiya Layla na daki bata yi yinkurin zuwa gareta ba illa saurin ficewa da tayi.

Tana shiga motarta ta fizgeta sosai tana zabga guda gabadaya kwanyarta ta mikata cikin  wani yanayi a yanzu da take hango Mufeeda tare da Dr.Erena tana karantar dashi komai akan Areefa gabanta taji ya tsinke duk da dai ta tabbata Mufeeda ba za ta sake dawowa wajansa  ba sannan kuma shima yana nuna rashin so akanta sosai.

Da wannan tunanin ta isa Company din sai da ta tsaya bakin Get tayi kokarin saita numfashin ta kafun ta karasa ciki tayi Parking nan ma sai da ta dau mintina tana karewa motocin da suke zube a wajan kallo kafun ta dire a ta Dr.Erena wani numfashi ta ja mai tauri kafin ta buɗe motar ta fito a hankali ta shiga takawa kamar mai tausayin kasa  har ta kai bakin kofar da zata shigar da ita cikin Reception din bayan sun gaisa da Security tana kokarin sanya kai ciki sai ga Dr Erena shima ya sanya kai zai fito saura kadan su yi gware da sauri taja da baya tana mai da numfashinta da take ji yana fizga runtse idanu tayi kafin ta buɗe su lokaci guda ta dube shi wanda shima gabadaya ya shagala da kallonta sai faman zabga murmushi yake yi sosai ta ji gabanta na bugawa kafun tayi kokarin kirkiro yaƙen dole tayi masa tana kokarin raɓashi ta wuce amma yarda ya tsare kofar ya sanya dole yin maganar da bata so yi ba.

“Barka da safiya Sir”.

Ta fadi ba tare da ta dube shi ba bai ansa taba kuma da alamun bashi da niyyar ansa ta din sosai ta matsu ta bar wajan yarda take jin kafafuwanta na wani iri lauyewa kamar za su zubda ita a kasa sai da ya gama shan sharafin kallonta sannan ya kau da kai ya na mike mata wani abu dake hannunsa.

“in kin shiga ki karasa min dashi cikin Office”.

Ya fadi ba alamun wasa sosai take kallonsa da abun da yake mika mata lamarin ya shiga tsingular mata zuciya wanda take kallo a matsayin raini eh mana raini ta yaya za ace mutumin ya fito da abu daga ciki sannan kuma ita da zata shiga yanzu ya bukaci ta mai da masa mai  yasa ya fito dashi bata san abin da yake hawa kan Dr.Erena ba a yan kwanakin nan yana shige mata sosai ita kuma bata son haka ansa tayi sannan ta wuce ciki binta yayi da kallo yana sakin murmushi harda taɗɗar baki kamar  namijin da ya shekara hamsin gidan yari ya fito ya ga mace kafun ya juya da sauri ya isa wajan motarsa ya bude abu ya dauko sannan ya rufe ya kama hanyar kowama cikin reception din.

Ita kuwa Areefa tana shiga bangarenta ta isa ta ajje jakar da sauran tarkacenta kafun ta dubi abinda Dr.Erena ya bata ta shiga juya shi ba wani abu bane na azo a gani kawai neman shiga rayuwarta ne da  hanzari tayi hanyar benan cikin sauri don bata so ya zo ya tadda ita a ciki don tasan kadan daga aikin sa ne.

Tana hawa wajan Office dinsa ta tadda sakatariyarsa ko ta kanta bata bi ba ta karasa ta shiga Office din can wajan Table ta isa ta ajje masaa kafun ta juya tana karewa Office din kallo tana yatsine fuska sa’anna ta ja kafafuwan ta tana kokarin fita mutum ta gani tsaye bakin kofar harɗe da hannaye a kirjisa wani irin dokawa taji gabanta yayi kafun ta daure fuska tamau!

“Ina zuwa ko”.

Ta fadi cikin rashin son kawo mata wasa murmushi yayi kafun ya tako kamar zai shige mata jiki hakan ya sanya ta saurin ja da baya.

“Areefa ban san me zan miki ba kuma nayi iri bakin kokarina don ki bani dama amma kin kiya ban san dalili ba?”.

Ya fadi yana mai kare mata kallo kafun ya dora da cewa.

“Ina so a yanzu ayi komai ya wuce don wallahi ba zaki fice daga Office din nan ba sai kin fada mini matsayata a gareki”.

Wani irin dokawa zuciyarta tayi amma bata bari hakan yayi tasiri a fuskarta ba kau da kai tayi.

“Areefa ya kamata ki ce dani wani abu ki baiwa zuciyata dama ta so ki ta kauna ce ki ta daɗe tana daukon son ki amma ke kin ki yarjewa dagaske nake ba da wasa ko yau ki ka ce na fito akan zancen aure wallahi ko awa daya ba za a kara ba”.

Yaa fadi kamar wani karamin yaro sosai maganganunsa suka taba mata zuciya amma sai ta nuna halin ko in kula sai ma kokarin raɓashi ta wuce take yi amma yaki bata dama sun jima haka kafun ta yanke hukunci da taga yafi cancanata wanda take ganin illa ce mai girma gareta numfashi taja kafin ta saita kanta sosai ta dube shi.

“Dr.Erena ni ban ki ta taka ba..ko da yake kawai abin da za ayi mu bari nan da sati daya lokacin na sanar a gida sai ka turo”.

Ta fadi ba a son ranta ba tana jin yarda zuciyarta ke yayyagewa da tashin hankali sosai taji jikinta na ansa bakon lamari mai girma da sauri ta rabashi ta wuce ganin ya saki baki yana kallonta kamar wani butum butumi.Sosai ta shiga tashin hankali cikin lokaci kankani ta rasa mai yake mata dadi a filin duniyar nan komai ya kara kwance mata tashin hankali ta ya kara hawa mataki mai girman gaske bata san me za tayi ba bata san mai ya kamata tayi ba lokaci tafiya yake komai kara kusantowa yake yi har zuwa wannan lokacin ta rasa mafitar da zata samu don cimma burin ta ba tare da auranta ya tabbata da Dr.Erena.

Numfashi take ja cikin sauri-sauri tana faman juyi saman faɗaɗɗen gadon ta wanda take jin sa kamar kan garwashin wuta take kwance komai na duniyar take ji yana yi mata k’iwa baya son ta da farinciki ko yaya ne.

Zuciyarta na ta hasaso mata cewa ‘ta kashe shi ba tare da kowa ya sani ba’ amma ta kasa tana tsoron haka ba kisa a tsarin daukar fansanta bata so ace wani abu ya gifta a tsakaninta da shi wanda zai sanya ta zama sanadin kashe shi tsoro take ji tsoron abin da zai je ya dawo tsoron yawan zunubansa da zai dawo kanta tana tsoron mutuwarta bata shirya ba ba zata iya ba.

‘to ki kashe kanki tunda baki shirya auren dashi ba’.

Zuciyarta ta sake bata wani zaɓin na daban wanda yayi matukar girgizata lokaci guda ta shiga girgiza kai kamar wanda ya fada mata maganar a gabanta yake ba zuciyarta ba wasu hawaye ne masu dumi taji sun zubo mata sosai take jin kunci da matsi cikin zuciyarta sosai take jin zuciyarta na mikata wani mataki mai tashin hankali sosai take jin zuciyarta na buɗe wani wagegen ciwo mai girman gaske.

Runtse idanu tayi sosai tana jin yarda jijiyon kanta da na cikin idanuwanta ke wani irin murɗewa da tashin hankali tana jin yarda wani irin raɗaɗi da zafi ke samun mazukunni cikin idanuwanta mikewa tayi daga kwance da take tana buɗe idanuwan nata hannaye bibbiyo ta zabga tagumi tana kallon yanayin DUHUN DARE da ya mamaye cikin dakin bata ganin komai ko jikinta bata iya hangowa sake runtse idanu tayi kafin ta sauke kafafuwanta a gefen gadon tana kai hannunta wajan fitilar dake girke gefen gadon kunnawa tayi haske ya wanzu sosai ta ko ina dakin ta shiga bi da kallo kafun ta mike saman kafafuwanta da take jin su kamar za su watsar da ita zuciyarta na ta karanto mata huɗubobin da suke kara caza mata kwanya.

Maganganunta da Alhaji Abdulwahaab ne suke dawo mata a jiya da rana inda yake kara karfafa mata gwuiwa amma tana zillewa.

*****

“Ban san mai zan ce miki ba kuma Areefa da farko na dauko za ki zama jaruma mai dakakkiyar zuciya wajan cimma fata da burin da kike dashi a zuciyarki amma gabadaya duk wannan fatar da burin naki ya rugeje lokaci guda ban san mai yasa ba Areefa ban san mai yasa kike kaunar jinkiri a wannan lamarin ba dama ce sau daya take zuwa in kuwa ta kubuce da wuya WATA DAMAR ta sake zuwa”.

Cire hannayenta tayi daga tagumi tana mai runtse idanu kafun ta buɗe su sosai tana dubansa zuciyarta na kara narkewa da lamarin Aurenta da Dr.Erena.

“ba wai na cire burin fata na bane akan Dr.Erena ba ba abin da ya canza…”.

Ta fadi dakyar tana jan numfashi kafun ta dauki Glass Cup mai dauke da sanyayyan ruwa ta kai bakinta ta kurba ba wai don jin dadi ba a,a domin kuwa ji take yi kamar ta kurbi maɗaci a dandanon da harshenta ya bata runtse idanu tayi ta hadiye shi dakyar kafun ta buɗe tana dubansa shima idanuwansa na kanta.

“ina son fatana a kansa ya tabbata amma wannan lamarin da aka kawo min ne nake jin kamar zuciyata ba zata iya hakura ya tabbata ba”.

Mikewa yayi kan kafafuwansa yana binta da wani irin kallo kafun yayi taku kadan ya goya hannayensa a bayansa.

“ko RIGAR SILIKI haka ta ganki ta barki Areefa ana taroki ta nan kina watse wa ta can ban san mai yasa ba…ko da yake shikenan amma ki sani auren ki da Dr.Erena shi ne mafita kuma ita ce hanyar da zaki bi domin cimma burinki kamar yarda Hajiya Layla ta fadi bana tunanin zata cutar dake ko da cikin rashin sani ne ki sani baki da wata a duniyar nan ita ce uwarki da ubanki baki da mai kaunarki kamar ita ba zata taba yin abin da zai taba miki rayuwa ba kuma kema kin san haka don haka ya kamata ke ma ki yaki ce duk wani k’i da zuciyarki take nuna miki ki koya mata hakuri da juriya”.

STORY CONTINUES BELOW

*****

Wani huci ta saki tana mai cusa hannayenta cikin gashin kanta zuciyarta taji tana sauya bugu da sauri-sauri a hankali ta zube kan gadon tana kwanciya gami da runtse idanu so take yi ta koyi hakuri da juriya domin ganin tabbatar wannan lamarin amma ta kasa amma ya zame mata dole ya zame mata tilas! Ta koyi jarumta da juriya a zuciyarta domin ganin komai ya tabbata yarda ya kamata tayi alkawarin yin abinda Maama take so a gareta da wannan tunanin barci barawo yayi awon gaba da ita ba ta farka ba sai wajan shidda da rabi shima Maama ce taji ta shiru ta shigo dakin sai da kare mata kallo cikin yanayin tausayawa domin daga ganin kwanciyar barcin bata yi shi tadadin rai ba kuma ba da wuri ba a hankali ta zauna kusa da ita ta shiga shafa mata goshi a hankali Areefa ta buɗe idanuwanta mai cike da barci ganin Maama ya sanya ta kara buɗe tana ya mutse fuska cikin muryar barci tace.

“Maama!”.

Murmushi tayi mata kafun tace.

“bakiyi barci da wuri ba ko Areefa kin sakawa kanki damuwa ko?”.

Girgiza kai tayi kafun ta mike zaune tana mai duban agogo ganin karfe bakwai saura ta ware idanu da sauri.

“Yaa Allah har lokaci ya tafi haka”.

Tana kokarin mikewa Maama ta rike mata hannu ta koma ta zauna tana kallonta cikin rashin fahimta numfashi ta ka kafun tace.

“Ba zan takura ki ba Areefa domim bana son abin da zai sanya ki a damuwa amma bari zan fada miki dalilina nayin haka din yanzu na san zakiyi amanna da batuna da nake jajircewa domin ya tabbata…”.

da sauri Areefa ta kai hannunta bakin Maama tana rufe fuskarta da wani irin yanayi.

“kiyi hakuri Maama komai ya wuce na yarda komai ya tafi  yarda da kike so zan baki hadin kai daga wannan lokaci bari ki gani daga yanzu ma”.

Ta mike da hanzari ta fada toilet wanka ta sallo kafun ta zo ta tsantsara kwalliya ta sanya riga da siket ta saka wanda suka dan kamata kadan takalmi mai tsini ta saka gami da dauko wata gold-bag mai shegen kyau ta daura glass no respect sosai ta fito kyanta yakara bayyana kamar ba wani abu da ke dawainiya da ita sai murmushi take zabgawa Maama ita kuwa baki ta saki tana kallon ikon Allah kafun ta mike kan kafafuwanta ta riko Areefa ta rungumeta sosai da sosai sannan ta sake ba tare da tace mata komai ba sosai take dubanta bayan ta raba jikinta da nata amma hannunsu a tsarke.

“My Preety Areefa”.

Murmushi Areefa tayi kafin ta sake duban agogo bakwai daidai da sauri ta zare hannunta tayiwa Maama sallama ta fice daga cikin dakin.

Motarta ta dauka kirar Benz kalar Ash sai kyalli take yi domin tayi alkawarim yau zata baiwa Dr.Erena mamaki zata nuna masa kulawa ta musamman wanda sai ya raina kansa motar shine ya bata ita amma bata taba amfani da ita ba sai yau domin dai ta nuna eh tana son sa din amma da alkawari tayi bazata taba amfani da wani abu daga dukiyar da yake mata kyauta a ciki ba.

Da wannan tunanin ta fice daga gidan nasu ta dau hanyar Company din zuciyarta sai faman zillo take yi mata gani take yi abun kamar a MAFARKI ba gaske ba a haka har ta isa Company din tans yin Parking taji ana kokarin buɗe murfin hakan ya daure mata kai da sauri ta dubi glass din ganin wanda yake tsaye ya sanyata ware idanu da mamaki kafun taja guntun tsaki can kasar makoshinta sannan ta buɗe murfin tana kokarin sako kafa waje ya tokare a bakin kofar ya daura hannunsa saman murfin dayan hannun nasa rike da key yana faman kaɗawa sai murmushi yake zabgawa kamar tsohon da ya samu kyauta yar sha bakwai a bagas ko dayake a bangaren Dr.Erena yadda yake jin son Areefa a zuciyarsa gani yake yi ta fi ko wacce mace dake numfashi a doron duniyar nan so yake yi mata mai ansa suna so zai iya sadaukar da komai domin yaga ya mallake ta ko da kuwa zai rasa komai na shi na duniyar nan son Areefa ya rigaya ya gama tafiya da imaninsa sosai ya zautu akan sonta numfashi ya ja idanuwansa na kara lumshewa da wani irin yanayi da yake jin zuciyarsa na kara jefashi a ciki akan Areefa.

“Kin makara yau da nayi tunanin ba zaki zo ba har zan bi sahu”.

Gaban tane ta ji ya yanke ya fadi jin da tayi yace zai bi sahu ita dai a iyakar zamanta dashi bai taba zuwa gidan su kuma bata taba jin yace ya sani ba yayi nacin ta kai shi amma ta kiya wani yawu ta haɗiye mai tauri kafun ta dube shi da murmushin yake a fuskarta.

“to da kake cewa zaka bi sahu ina zaka kai da baka san gidan mu ba”.

Daga kafaɗa yayi yana mai kara juya idanuwansa akanta.

“wai shin me kika mai dani ne kin dauka son da zan miki zai zauna a raina haka ba tare da na san gidanku domin zuwa kai ziyara ba to ko jiya naje gidan ku lokacin kina nan wajan aiki ba tare da kin sani ba”.

Wani irin dokawa taji gabanta yayi da tashin hankali runtse idanu tayi lokaci guda kanta taji yana sarawa shikenan asirinta ya tonu ta gama yawo in har Dr.Erena ya ga Hajiya Layla ta tabbata kashinta ya bushe zuciyarta ta shiga kara mata kwarin gwuiwa akan cewa ‘ke kin fiye karaya da yawa ki bari ki ji wani gida yaje mana kuma inda yaje gidanku ai da hajiya Layla ta fada miki tun jiya din’.

Wani numfashi taja gami da buɗe idanu tana mai kakalo murmushin dole don bata son ya gane halin da ta fada aiko tana daga idanuwanta ta dube shi wani kallo taga yana yi mata kamar na tuhuma.

“Uhmm ban yarda ba ai in da kaje da an fada min”.

Murmushi yayi yana kara gyara tsayuwarsa kafun ya nuna ta da hannu kamar zai lakace mata hanci.

“Bosso Lowcost gida mai lamba 112 gidan Alhaji Saifullahi Suraj”.

Wata irin ajiyar zuciya tayi lokaci guda jin sunan da ya fadi tabbas ta gane sunan da ya ambata gidan da za su zama iyayenta ne da Alhaji Abdulwahaab ya zo ya sanar da Hajiya Layla ajiya tabbas tayi mamakin amma da ya san gidan cikin nuna mamaki ta dube tana kara fara’arta.

“Amma nayi mamakin yarda akayi ka sani fa”.

“Abu mai sauki ne a gareni kin ga tashi mu shiga daga ciki nan yayi hanya da yawa bana so a zo wuce wa ana kalle min kenan wannan hadaddiyar kwalliyar da kikayi mani domin na tabbata don ni akayi mata kuma zan saye ta da farashi mai tsada ke dai meke mu shiga daga ciki”.

Mamaki sosai ya kama Areefa ganin yarda yake rawar jiki ba tare da nuna isa da izzar nan tashi ba da yake da ita kamar bashi ba ko da yake kadan daga makircinsa ne zai iya fiye da haka don ganin ya cimma burinsa akan abin da yake so a hankali ta zuro kafafuwanta ta mike bayan ya matsa ta dauko jakarta tana kokarin dauko wayarta taji ya anshe jakar da sauri ta dago ta dube shi ba tare da tace dashi komai ba tana kokarin mai da kofar motar ta rufe nan ma da sauri ya sanya hannu ya rike yana mai sakar mata tattausar murmushi yana girgiza kai matsawa tayi sannan ya rufe kofar  kafun yayi mata nuni da hannu su tafi amma ta kiya ta mika masa hannu ya bata jakarta da ya rike kamar wata uwargijiya da bawanta sai da tayi da gaske tana nuna rashin amincewarta sannan ya bata suka jera don cewa yayi bata isa ta taka ita kadai ba ba yarda ta iya haka suka jera din kamar wasu mata da miji shi kuwa sai rawar jiki yake yana faman yashe baki yana zuba surutu.Duban juna suke yi cikin tsanar da zuciyarsu take mika su akai ji suke yi kamar su shaki juna da kunci da takaicin da suke ji a tsakanin junansu sai faman huci suke yi kamar wasu mayunwatan zakuna.+

Dr.Karami ya ja wani dogon tsaki kafun ya juya ya dubi kofar gidan su Mariya da wani irin yanayi mai girman gaske yana jin yarda zuciyarsa ke harba da sauri-sauri komai yake ji ya jagule masa gabadaya tunaninsa ya tsaya cak! Kwanyarsa sai kamawa take yi da wuta tana kokarin

babbakewa numfashi yake ja yana jin yarda kirjinsa ke wata irin kartawa da tashin hankali mafi girma a filin duniyarsa juyawa yayi da idanuwansa da suka fara kaɗawa ya kalli Dr.Aqeel dake ta faman hura harci kamar zai ci babu.

“ka rubuta ka ajje bar ganin abotar da ke tsakanina da kai wallahi sai na shayar da kai ruwan mamaki a filin duniyar nan wallahi kayi kadan ka wulakanta ni a gaban wacce nake so har kake ikirarin ban isa ba to ka jira lokaci zai zo zaka ga yarda zan rabaka da wacce kake cewa kai kafi cancanta da ita”.

Ya karashe yana nuna Dr.Karami da dan yatsa cikin tsananin bacin rai mara yankewa da sauri ya juya yana kokarin barin wajan amma jin Dr.Karami yayi gyarar murya mai sauti ya sanya shi juyowa murmushi ya gani dauke a fuskarsa mai ma’anoni masu yawa.

“karka manta da abotarmu domin ban sako ta a ciki ba amma tun da kace mu ajje komai a gefe to nima zan dauko makaman yaƙi na kuma za a buga ni da kai a ga wanda rana zata rigashi faduwa”.

Kallon na raina wayon ka Dr.Aqeel yayi masa ya ja kwaɓa.

“Ok Hakan na da kyau ina tsumayenka”.

Yana karasa fadin haka ya juya da sauri ya faɗa cikin motarsa ya fizgeta kamar wanda zai tashi sama.

Sosai tashin hankali ya bayya a fuskar Dr.Karami duk juriya da kai zuciya nesa da yake yi akan sabon halin da Dr.Aqeel ya kirkira ya dorawa kansa abin da bai taba zato ko tsammani ba bai taba kawowa kansa Dr.Aqeel zai iya katse ABOTA dake tsakaninsu ba ya sha mamaki sosai akan haka zuciyarsa ta jima tana ciwo akan hakan yayi hakuri ya kau da kai amma sai da ya sanya shi tsayawa ya dube shi har suka fara SA’INSA a tsakanin su.

Tun ranar da aka sallamo Mariya daga asibiti gabadaya ya ga ya rikice masa musamman da yaga Mariyar sam taki kula kowa a tsakanin su ko kallon banza ba su ishe ta ba amma shi ya danne zuciyarsa bai nuna komai ba sai shi ne zai dinga ajje masa bakaken maganganu ba tare da laifin sa ba domin shi dai bai ga abin da ya aikata masa ba har da zai din ga daukarsa a wani macuci har yake ikirarin haduwar su ba tayi kyau ba.

Jingina yayi da  bayan motarsa yana harɗe hannayensa a kirji sosai ya runtse idanuwansa jin yarda zuciyarsa ke kartawa kamar zata yayyage komai yake ji yana zama kunci gareshi komai ya sauya masa sosai yake jin yarda so yake wahalar dashi bai san so haka yake ba bai san ana faɗawa har haka a cikin so ba bai taba tsammanin zai ganshi a

DUNIYAR SO yana gararamba ba amma yau shi yake yawo a ciki kamar wani wanda bashi da mafadi ya fado duniyar nan.

Numfashi ya kuma ja kafun ya haɗe wani yawu mai tauri ya dubi kofar gidansu Mariya na ba dadi yau cikin satin sa na uku kenan yana zuwa amma Mariya taki kula shi ko

fuskarta taki bari ya gani tun ranar da suka dawo da ita gida aike goma zai amma ba biyan bukatar ko daya daga ciki tashin hankalin sa na daduwa abun ya zame masa goma da ashirin ga lamarin Mariya ga wannan shi kuma yana masa hayaniya akai can kuma gida Hajiya ta saka shi gaba bai san me zai yi ba kansa kara kamawa da wuta yake yi ya kasa yin wani tunani ma na kirki ko zai samu mafita.

STORY CONTINUES BELOW

Ya jima tsaye a wajan kafun ya yanke hukuncin barin wajan domin ya tabbata ba fitowa za tayi ba shikuma ba iya shiga gidan zai yi ba domin kuwa gabadaya bai son su hadu da Umma kwata-kwata.

Yana kokarin shiga motarsa ya hango Mu’azzam ya fito da gudu yana waige da alamun biyo shi akayi da sauri ya dakata yana mai da kofar ya rufe kamar daga sama ya hangota ta tunkaro kofar fitowa tana ta faman kiran Mu’azzam amma ina sai kara wutar gudun sa yake yi wata irin mutuwar tsaye yayi ganinta ta canza sai yaga ta kara masa kyau da haske sai dai ta kara ramewa sosai harɗe hannayensa yayi a jikinsa kirjinsa da yake faman dokawa da sauri-sauri a daidai lokacin Mu’azzam ya iso

gareshi ya kankame shi yana neman ya ceceshi amma shi ina fuskarsa da komai nasa na kan Mariya a daidai lokacin ita kuma ta dube she wata irin razana tayi kafun idanuwanta su yo waje sosai da sauri ta juya ta fada cikin gida cikin wani irin hali mai ciwo a zuciya.

Ya shafe lokaci kafun ya ja wani gwauron numfashi mai sauti ya durkusa ya dafa kafadar Mu’azzam yana kallon sa abin mamaki fuskar Mariya yake ganin tana yi masa gizo tana mai sakin tattausar murmushi a gareshi sai da Mu’azzam ya taba masa fuska sannan ya dawo hayyacinsa yana dubansa kafun ya ce dashi.

“Me kayi aka biyo ka da gudu haka hala rashin ji kayi ko?”.

Juyawa yayi ya kalli kofar gidan kafun ya dubi Dr.Karami da ya kureshi da idanu.

“Yah Mariya ce ke kuka a daki shine na fadawa Umma kuma ta hanata kukan to shine don Umma ta shiga bandaki shine ta biyo ne don ina ce mata mai kukan banza”.

Dariya Dr.Karami yayi amma cikin zuciyarsa ji yayi wani zafi na kawo masa farki sosai tashin hankalinsa na daduwa kalmar ‘kuka’ da yaji Mu’azzam ya ambata tana yi ita Mariyan sake daga kai yayi ya dubi kofar gidan yaji kamar ya mike ya fada cikin gidan ya lallashe ta.

“je kace ina kiranta”.

Ya fadi yana dubansa cikin idanu shima Mu’azzam din dubansa yake kafun ya shiga girgiza kai.

“a,a dukana za tayi kuma ko an aika ta zo ba ta fitowa kullum”.

“Me yasa?”.

Ya fadi bugun kirjinsa na sauyawa da sauri-sauri

Girgiza kai yayi kafun ya sake kallon kofar gidan.

“nima ban sani ba kawai dai kullum a daki take zama ba ta fitowa ko Umma bata tayawa aiki”.

Runtse idanunsa yayi jin wani abu ya tokare masa zuciya kafun ya sake fadin.

“Ba ta da lafiya ne”.

“Tunda ta dawo daga asibiti shikenan ina ganin kila bata ji sauki bane”.

Mikewa yayi ya saka hannu cikin aljihunsa ya zaro kudi masu auki ya mikawa Mu’azzam girgiza kai yayi alamun ba zai ansa ba sai da yayi dakyar sannan ya ansa.

“kace ina gaida Umma da Ita Mariyar kaji yi maza ka koma gida ba wanda zai dakeka”.

Da gudu kuwa ya juya yayi gida shikuwa jin gina yayi da mota yana faman mai da numfashi sosai yake jin zuciyarsa wani iri jin halin da Mariya take ciki ji yake kamar ya kakkare mata damuwar ya dawo da ita kansa ya sani har da laifinsa wajan sanyata ko wani hali ta fada yana da kamasho in da ya san haka rayuwar zatayi

STORY CONTINUES BELOW

musu inda ya san ALKALAMIN KADDARA haka zai rubuto musu wannan rayuwar da bai yi SAKE wajan bayyana mata yana son ta ba da ya furta mata tun lokacin da yake ganin bata cancanta ba ya san komai daren dadewa zata koyi son shi kuma zata ajje kalmar so da ya fadi mata tun lokacin baya har zuwa lokacin da za ta gane meye SO.

Da wannan kuncin zuciyar ya shiga motarsa ya bar kofar gidan kwanyarsa sai wuta take kokarin kamawa da ita gabadaya ya rasa me ke masa dadi a rayuwarsa dole ya san abin yi dole ya fuskarci wannan kalubalin dole ya nemi mafita a gareshi.

********

Tana zaune ta na aikin Cake wanda ya zama yanzu ita ce take yinsa Mariya ta zama abin da ta zama sosai lamarin na Mariya ke sha mata kai ta rasa mai ke damun ‘yarta ta yau

kusan wata guda kenan tun da aka sallamota daga asibita ta rasa gane kanta kullum cikin kuka take kullum cikin damuwa bata da aikin yi sai kuka abin na taba mata zuciya tayi faɗan tayi rarrashin amma bata sauya zani ba har ta zurawa sarautar Allah ido ta sani suna cikin yanayi na rayuwa duk yarda ta zo musu dole su anshe ta duk wani abun dake faruwa dasu na dadi da rashin sa ALKALAMIN ƘADDARAR su ce a haka ba yarda za suyi…

Tunanin ta ya katse lokaci guda da hanzari ta dawo hayyacinta jin an kwaso da gudu anyo waje gabanta ya yanke ya fadi daga idanuwanta tayi cikin fargaba da tsoro duk a

tunaninta Mariya ce amma sai taga akasin haka Hafsat ce ta fito da gudu daga dakin Goggo Marka ta zube tana ta faman amai da kakari kamar wacce zata amayar da ‘yan hanjin cikin ta amai take yi wanda ba komai a cikinsa sai ruwa da majina sosai ta rike cikinta tana faman nishi tana murkususu kamar wacce akayiwa dukan shan gishiri.

Da sauri Umma ta zare hannunta cikin kwabin da take yi ta dauraye hannayenta  ta mike kan kafafuwan ta da sauri ta karasa inda Hafsat take wacce ta gama galabaita rikota tayi tana mata sannu gabadaya jikinta ya saki sai faman nishi take yi kamar wacce rai ke kokarin ficewa daga jikinta sosai Umma ta tauyasa mata ganin irin halin da take ciki lokaci guda duk ta zurma kamar wacce take amai da guda.

Ruwa ta debo ta bata ta dauraye bakinta sannan ta wanke mata fuska ta taimaka mata ta mike ta raka ta daki ta kwantar kafun ta dubeta ganin ba kowa a dakin.

“Dama baki da lafiya ne ina Goggo din take?”.

Banza tayi da ita jin yarda cikinta da kasar mararta ke kartawa da wani irin azababben ciwo kamar yan hanjinta zasu zazzage sai faman juyi take tana cizon laɓɓanta idanuwanta a runtse sosai zuciyar Umma ta karyewa da yanayin da ta ganta a ciki sai faman sannu take mata jin ta kasa bata ansar tambayar da tayi mata sai da ta jima a tsaye ganin Hafsat ta lafa da murkususun ya sanyata juyawa

tana kokarin fita har ta daga labule sai ga Goggo Marka ta sanyo kai ita da sauri ta ja baya Goggo Marka ta shiga dubanta da wani irin yanayi na tuhuma kafun ta leka cikin dakin ta hango Hafsat a kwance sake dubanta tayi.

“Lafiya me ya shigo dake dakina”.

Ta fadi cikin tsawa tsawa da nuna bacin rai.

“A,a Hafsat naga ta fito tana ta kalaya amai shine na taimaka mata ban san bata da lafiya ba”.

“Ba ta lafiya fa ? Kika ce injiwa ya fada miki lafiyarta kalau sai dai in wani abu taci yake tayar mata da zuciya har ya kaita ga amai”.

Yanayin da take maganar kawai zaka kalla ka gane bata da gaskiya da sauri ta shigo dakin har tana bangaje Umma kayan da suke hannunta gabadaya suka watse Umma tabi kayan da kallo lokaci guda gabanta ya yanke ya fadi ganin kulin maganguna har su mataccen ƙadangare da sauri ta ja da baya ita ma Goggo Marka kayan tabi da kallo kafun ta dubi Umma a dan tsora ce ta shiga tattare kayan tana cewa.

“to ki fita mana ko kin tsaya kina kare min kallo ko da kwai wani abu ne?”.

Tana magana jikin ta na rawa da sauri Umma ta fice daga cikin dakin gabanta na kara tsananta faduwa sai sunayen Allah take kira sosai zuciyarta ta shiga zargin abin da tagani fata take yi Allah yasa hakan kar ya tabbata kar dai ace wani abun

Goggo Marka take aikatawa domin sosai ta ji a jikinta akwai wani abu a boye dangane da abin da ta gani a yanzu ta jima tsaye a kofar dakinta tana tunani kafun ta isa wajan aikin da take yi gabadaya taji ya kuma sure mata kwasar kayan tayi ta fada cikin dakinta…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *