DR MUHSEEN CHAPTER 7 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝………………Bayan wasu shekaru Allah ya Kara ba Ummeey ciki,Wanda ya Kara haddasa kiyayya tsakaninta da Hajiya Mariya domin karara take nuna batasan cikin dake jikin Ummeey.
Amma da yake Ummeey ma’abuciyar hakurice sai bata damuba,illa dagewa da tayi tana Kara neman tsari daga makircin Hajiya Mariya.
Lokacin da cikinta ya isa haihuwa ta haifo santaleliyar diyarta mai kama da Muhseen,ranar suna aka radamata Lailah.
Sosai Muhseen yake kaunar Lailah dukda lokacin Yana karatu a Sudan a shekarar shi ta farko kenan.
Tun Muhseen yana yaro ya riga daya fahimci Hajiya Mariya da mahaifiyarta Balaraba basu kaunar wannan family nasu,tundaga lokacin ya saka buri a ranshi na yanaso ya zama soja .
Haka ya dauki Karan tsana ya dorawa Ameerah dan tun farkon zuwanta gidan yake bala’in kaunar Muhseen,shiko gano hakan da yayi yasa yake Kara tsanarta Wanda kowa dake cikin wannan estate yasan da tsanar da yake yimata.
Ameerah tasha sanar da Hajiya Mariya ita dai tana kaunar Muhseen ta taimaka Mata dan ganin ta aure shi.
Haka Hajiya Mariya zata kontar Mata da hankali akan komai runtsi komai wahala saita mallaki Zuciyar Muhseen.Haka yasa Ameerah take jin kanta Yana Kara girma,Dan tasan inharta mallaki Muhseen to ta kerema kawayenta a komai,domin Muhseen miji ne na nunama sa’a.
Tun bayan Muhseen ya kammala karatun shi na secondary School anan wata pravet dake cikin garin katsina.sai Alhaji Muhammad ya nema mai Admition a University of Sudan, Makaranta ce da take tafe da tsarin addinin Musulimci,sannan Kuma ga tsantsar ilimin tsamani.a bisa Alfarmar da Hajiya Aishatu ta nema na abata Muhseen ya zauna tare da su har zuwa lokacin da zai kammala digreen shi na farko.haka kuwa akayi abinka ga masu abu dandanan cikin lokaci kalilan aka kammala komai Muhseen ya daga Kasar Sudan inda zai fara karantar fannin theater,Amma a kasan zuciyar shi ra’ayin aikin soja ne a ranshi.
Haka duk matasan gidan suka dukufa a fannin karatun addini dana zamani,domin Hausawa nacewa ilimi gishirin zaman duniya.
Muhseen hankalin shi konce a kasar Sudan karatu yake yi babu kama hannun yaro.Dukda yana fuskantar tsangwama daga bangaren Gimbiya Zulaihat Amma hakan baisa yayi wasa da damar sa ba.dan gimbiya Zulaihat akwai wulakanci ,shima sarki Abdulkareem zaman hakuri yake da ita,bayan ka kammala digreen sa inda dakyar su Hajiya Aishatu da sarki Abdulkareem suka bar Muhseen ya dawo kasar shi ta haihuwa.Domin ranar da zasu karasa karatunsu saida Yan Nigeria Suka je,kama daga Dadyn shi da Ummeey, Jabeer da Faruk da kanwar shi Lailah.Bayan sun je aka Sha hidimar yaye dalibai kafin Suka tarkato suka dawo gida Nageria.
Bayan dawowar shi da wasu watanni results dinsu ya fito haka ya amso,sosai result yayi kyau.anan ya nunama Dadyn shi ra’ayin shi nasan zama sojan sama.da farko Abba ya nuna rashin amincewa,Amma ganin yadda Hajiya Kaka ta cije akan ya barshi yayi yasa ya hakura.
Watanni tara Suka dauka a Kaduna suna gudanar da treaning,wani lokacin Muhseen sai yayi kamar zai gudo saboda tsabar wahalar da ake basu,Amma idan ya da burin shi sai yaji zai iya jure kowace irin wahala ce.
Cikin ikon Allah bayan dawowar su Muhseen da wasu watanni,aka fito da list na wadanda Suka sami aikin soja.sunan Muhseen shi ne a farko.sosai yayi farinciki har bazai misaltu ba.
Farkon fara aikinshi Abuja aka kai,shi kafin daga baya a shekarar 2017 bayan an kammala gina bareak ta Daura aka dawo da wasu nan cikinsu kuwa harda Muhseen.
*BACK TO STORY*
Tunda Muhseen ya figi motar shi a guje yabi ta gaban su Faruk da yake rike da hannun Seeyerma Yana faman rarrashinta.ganin irin gudun da yake yi yasa hankalin Faruk ya Kara tashi Dan yasan an tabo soja,tunda yaga bai tanka ba yasan ranshi yayi mugun baci.faruk a zuciyar shi ya ce “tabbas akwai matsala dan idan har Ameerah tayi gigin zama da Muhseen to wataran Yana iya hallakata.suna shiga part din Hajiya Kaka ya zaunar da Seeyerma saman kujera Yana sharemata guntun hawayen dake saman fuskarta.
Wayar shi ya ciro daga aljihunshi ya fara kokarin Kiran wayar Dr muhseen.jin ance a kashe take yasa yayi saurin duban inda Hajiya Kaka take zaune tana Jan casbaha.
Itama dubanshi tayi ta girgizamai Kai.
Shiru yayi Yana tunanin irin matsalar da take kunno kai a wannan ahali nasu.
Shiko Muhseen tunda ya haura da motar shi saman titin unguwar kwado yayi saurin kashe wayar shi.dan yasan tunda Faruk yaga fitar shi to ba makawa saiya Kira wayar shi.
Derect gidan su abokinshi ya nufa Lameer ya nufa.
Da sauri yake faman Danna horn Wanda ya saka mai gadin saurin bude gate din ba tare daya shirya ba.ganin Abokin Lameer ne yasa ya daga mai hannu,shiko gogan naka baisan ko Yana yiba ya danna hancin motar cikin farfajiyar gidan.koda ya bude da sauri ya nufi part din lameer saboda jin wani zazzafan zazzabi Yana neman rufeshi,cikin dauriya yake ya kamo lebenshi na kasa Yana taunashi da karfi dukdan ya samu sassauci,Amma ina.
Ko knowking bai tsaya yiba ya shiga.
Baya falo dan haka ya wuce bedroom,ganin Yana kallo a system yasa ya fada bisa gadon Yana mayar da numfashi,Dan saboda bacin rai ya manta ashe ko murfin motar bai rufe ba.
Ta kasan ido Lamerr ya kalleshi Yana jin wata dariya tana kamashi.dukda baisan damuwar abokin nashi ba,Amma Yana bukatar taimako.
Jinjina kanshi yayi Yana addu’ar Allah ya toni asirin masu hada munaficci a cikin wannan family.
Ruwan gora ya dauko masu sanyi ya mikamai.
A hankali ya amsa Yana mikewa zaune.saida ya jingina da jikin gadon kafin ya bude murfin robar,tinda ya kafa Kai saida ya shanye tas kafin ya collar da emptyn goran Yana dafe kanshi jin yadda yake saramai kamar zai fita daga jikin shi.
“Haba my Friend ka natsu mana,kaifa soja ne,duk soja kuwa ansanshi da juriya,kada fa kasa na hanaka auren Seeyerma”
Yana danne dariyar shi Dan yasan ya taboma kanshi masifa.
Dakyar ya bude kwayar idonshi yana yima Lameer kallon kasan ido.
“Mtsssssss banza Kaine Dan akuya dakaga mace sai kahau mazari kamar kaga nama,Ni kasan wannan kwailar yarinyar bazata iya daukata ba,Kai wallahi wacce ta fitama zan iya ballata ballantana ita,mtsssss”ya Kara Jan tsaki Yana kokwakarin konciya.
Sosai Lameer ya saka dariya saida ya dara sosai jin maganar da Muhseen yayi, kafin ya ce “wallahi ni haryanzu banga dan ‘iska irinka ba,ehee Naga Kai rashin akuyancin ne yasa kake kasa iya control din kanka sai kayi ta faman taune lebe kaman wani tsohon maye,Ni wallahi duk wacce tsautsayi yasa ta aureka to kawai tasan ta zama sorry”.
Cikin takaici da jin haushi Muhseen yakaima Lameer naushi a jikin hannun,Amma Lamerr yayi saurin kocewa Yana cigaba da dariya.
Da gudu ya biyo shi,ganin ya nufi falo yasa ya kyaleshi.
Dakin ya dawo ya sakama kofar key ya cire rigar jikinshi ya rage daga shi sai dogon wando da singlet ya konta Yana tunanin tun ranar daya fara ganin Seeyerma da zuwa ranar data dawo estate dinsu da zama,baya da wasu shekaru da bazasu gaza biyar ba.
Wata rana ne Muhseen ya zo hutu suna hira da Kaka Yana Kara bata labarin Sudan da gidan mai martaba sarki Abdulkareem da yadda Hajiya Aishatu take kula da shi.
Sosai ya mayar da hankalin shi ga Hajiya Kaka ya ce “Inaso na fadamaki wata magana,Amma Ina jin tsoro domin nidai a iya sanina Dady ya taba sanar da ni Baku da family a Sudan,shima aiki ne ya kaishi harya auro Ummeey”.
Kaka cikin kula da jikan nata ta fahimci da gaske yake wannan maganar,Dan haka itama ta mayar da hankalinta gareshi kafin ta ce “maigidana ko wasu ka gani masu kama da wannan Family shiyasa kake wannan maganar”
Saida ya kontar da kanshi bisa cinyar kakar tasu kafin ya lumshe idon shi tamkar mai son tuno da wani abu ya ce “Kaka idan har idona ba gizo yayiman ba to tabbas naga wata yarinya mai kama da Aunty Aliya sosai,kullum idan za’a kaini school sai naga yarinyar itama Driver ya kawota school dinsu saboda ba nisa a tsakaninmu da su,Amma idan na sanar da Aunty Aliya sai ta ce ba kowa kawai kamanni ne na Dan Adam,Barima kiga na nunamaki hoton dana saka aka daukoman na yarinyar ba tare data sani ba”Yana kokarin binciko hoton daga cikin wayarshi.
Mikamata wayar yayi Yana cewa “kinganta ko?wallahi ranar dana fara ganinta sai Naga kamar Lailah ce,Amma ta dan dara lailah hasken fata”
Amsar wayar tayi tana dubawa,cikin razani da tsoro ta zabura tare da ture Muhseen daga saman cinyarta tayi saurin cewa…………cikin razani da tsoro ta zabura tare da ture Muhseen daga saman cinyarta tayi saurin cewa