MAFARIN SO CHAPTER 1
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tafiya take cikin nutsuwa, burgewa, da takun Isa, Sanye take cikin doguwan rigan material, kalan brown da milk, saita yafa k’aramin mayafi akai, tana rik’e da wasu littafai a hannunta.
Bata ankara ba sai dai taji abu ya dakar mata goshi harta kusa faɗuwa, kafin ta ɗago kanta kawai taji an kwashe da dariya, cikin k’unar zuciya ta ɗago da kanta tana k’arema wurin kallo, gaba ɗaya cike wurin yake da ɗaliban jami’ar kuma kusan duka hankalinsu na akanta. Dariyarshi tafi shigar mata kunne, juyawa tayi ta watsa mishi harara.
Dariya yayi irinta gogaggun en iskannan,
“zo mana” ya kirata da hannu, yana zaune saman motah da en korenshi zagaye dashi, taso ace zata iya komawa ta sauke mishi duk masifan dake ranta, anma jin kanta da tak’ama bazai taɓa barinta ba, kuma shi bai kai ajin da zata tsaya gaban mutane tana maida magana dashi ba. Juyawanta kawai tayi taci gaba da tafiyanta,
Batasan sanda ya diro daga saman motan ba, sai dai kawai taji yana neman rik’o hannunta, cikin zafin nama ta juyo ta wankeshi da marin da yazo mishi a bazata, ɗaga kanshi yayi yana kallon mutanen da sukayi cincirindo suna kallonsu, sannan kowa ya fara k’ok’arin riƙe dariyanshi don babu wanda baisan halin Abdallah ba.
“Ni kika mara?”
“an mareka ɗin, wannan shine gargaɗin dazan maka na ƙarshe akan shiga harkata da kake”
“ke kinsan waye Abdallah, wallahi sai kinyi dana sanin marina da kikai”
“Anma bakasan wacece Rabi’ah ba, kuma ina mai baka shawaran karka zaƙe akan saika sani ɗin”
Nunata yayi da ɗan yasha, “zan ramane a inda zaifi miki ciwo, kuma ki sani ban taɓa son abu na rasa ba, ko bakiso dole kiyi soyayya dani”
Tofar da yawu tayi a k’asa, “Allah ya kiyayemun soyayya da ɗan shaye-shaye” ta juya ta barshi wurin a tsaye yana huci yama kasa maida mata magana, ya watsa ma mutanen wurin kallo ba shiri kowa ya ɓace, ya shige motanshi ya jata a guje.+
Hankalinta kwance ta gama lecturenta suka fito tare da Aminiyarta Amrah, hannunta taja suka koma gefe,
“Faɗamin Rabi’ah meye gaskiyar abinda naji wai kin mari Abdallah”
“toh meye naga duk kin wani ruɗe kaman wani babban abune ya faru?”
“haba Rabi’ah, naga hankalinki kwance kaman bakisan halin Abdallah ba”
“ni mamaki kike bani wallahi, siyasa ne kawai zai nunamun, anma kuɗi kam har ke kinsan Yayana yafi mahaifinshi sosae, don haka duk abunda zaiyi nima zan iya, ban taɓayin abunda nayi dana sani ba”
“hakane fa, anma ni dai duk a tsorace nake”
“kinma warware,”
Tun daga bakin gate, ma’aikatan gidan ke kawo mishi gaisuwa anma ko kallo basu isheshi ba, ganin motoci da yawa ya tabbatar mishi Daddyn nashi na a ciki, don haka kai tsaye falon Mai girma mataimakin Governor ya wuce,
Zaune yake yana amsa waya, bodyguards nashi zagaye dashi, yana ganin yanayin da Abdallah ya shigo dashi, ba tare da yaa gama ba ya katse wayan.
“Yadai Son?” cikin sham ƙamshi ya kalli bodyguards ɗin, sannan ya maida kallonshi kan Dad din nashi, alama ya musu da su fito, cikin bin Umarni duk suka fita.
“waye kuma ya taɓomin kai?”
Saida ya ƙara ɓata fuska sannan ya fara magana, “Haba Dad! Ni bansan me yasa baka damu da abinda nakeso ba, ba ruwanka dani sai harkan siyasarka kawai”
“akwai abinda ka taɓa nuna kanaso banyi maka bane?”
“A’ah kawai dai wannan ne nake tunanin bazan samu ba”
“babushi, indai Kuɗi da Mulki na iyayin komai a duniya babu abinda zaka nema bazanyi maka ba”
“I know Dad, but uh should promise me”
“promise”
“thank you Dad, i love you”
Sannan ya fara fara’a, jinsa yake wasai kaman yama riga da yaa rama abinda Rabi’ah ta mishi.
Hankalinta kwance ta k’arasa gidan, tama manta da wani abunda ya faru tsakaninta da Abdallah,
Kai tsaye ɗakin ƴaƴan yayan nata ta wuce, en biyune mace da namiji Hayra da Hayran, hankalinsu duk yana kan laptop saboda Game ɗin da suke.
Tsaye tayi tana kallonsu, da taga dai basusan da shigowanta ba ta musu gyaran murya duk suka juyo a tare, har suna rige-rigen zuwa mata Oyoyo,
“har an gama Home work ne, aka zauna ana Game?”
Hayra tace “nidai na gama nawa”
“ni nama rigata gamawa Aunty”
“Awwah Gud, bara in dawo nima ayi Game ɗin dani”
“Awwah Auntie, daman sai cheating yakemun”
“itace bata iya bafa, tun ɗazu nake kasheta”
“mortal combat ne? Bara in dawo in muka fara kasheka ko motsi bazaka iya ba”
“Kai kai, waye zai kashemun ɗa?” sai dai suka jiyo muryan Matar yayansu tana hargowa,
“Momie a Game ne fa” inji Hayrah
“ke yimun shiru, tun yanzu za’a fara koya muku maganar kisa?”
Murmushi kawai Rabi’ah tayi, don indai akwai sabo
ta saba da halin matar yayan nata, “Aunty deejah Sannu da gida”
“yauwa” tana taɓe baki,
Ta raɓa ta gefenta kawai ta shige, ɗakinta ta shiga, sai da ta watsa ruwa sannan ta saka kaya mararsa nauyi, ta haye gado saboda gajiyar da takeji.+
Rabi’ah kenan, er gatan Yayanta Alhaji Ibraheem Naira, su biyu ne a wurin iyayensu, an mishi aure ba daɗewa Allah ya amshi rayuwansu, shiyasa ya maida ita gidanshi yana kula da ita da karatunta, akwai shaƙuwa sosae da soyayyar juna a tsakaninsu, bai haɗata da kowa ba shiyasa matarshi ma take kishi da ita, shine ya zama uwa da Uba a wurinta, saboda yanda yake tausaya mata da rashin iyayensu.
Rabi’ah yarinyace mai son gayu da nuna harkar girma, babu abinda tafi so a duniya kaman yayanta, babu kuma abunda tafi tsana kaman soyayya, shiru-shiru ce ga wanda bai santa ba, anma masifaffiyace ga wanda ya taɓota ko kaɗan bata jiran saita kwana.
Tun ranar data mari Abdallah ya daina shiga harkarta, ko a makaranta ma ta daina ganinshi, ita daman bashi gabanta, sai murna takeyi taa koya mishi hankali.
Suna tare a ɗakin su Haiyran tana nuna musu Home work wayanta tayi ringing, tana ganin mai kiran tayi saurin ɗagawa,
“Hallow sis, ya naji ki shiru fa”
“maganar me fa?”
“kin manta zamuje a mana lallen bikin Stylish ne?”
Tayi dariya, “wallahi fa sis, nina ɗauka zata zo gidane ta mana”
“idan tayi mana lallen a gida, gyaran jiki da gashin fa?”
“komai sai tayi mana, ko nawane basai mu biyata ba, kinga ni banson jirannan”
“kinga ni sai kinzo” ta kashe wayanta,
A shirye take, mayafi kawai ta ɗauko a ɗaki da mukullin mota ta fito, ɗakin Matar yayanta ta shiga mata sallama,
“Aunty deejah na tafi wurin lalle”
Ta taɓe baki tana kallon gefe, “aifa, abunda kika iya kenan, kullum kina hanyar makaranta, in kun dawo kuma babu zama sai shegen yawo, shi kuma ya saka miki ido”
Murmushi tayi murya k’asa-k’asa tace, “amfanin ilmin kenan ai, babu mai sanin daɗin karatu sai wanda yayishi”
“me kikace, daman ba tun yau ba nasan kin gama rainani”
“bance komai ba” ta fito ta biyo bayanta, su Hayra na tsaye suna jiran fitowarta,
“Auntie nima za’amun lallen” inji Hayra
Hayran yace “nima zan raka ki Auntie”
“tohh kuje ku shirya”
“bazasu je ba, ku wuce ɗakinku binto ta kunna muku kallo” ta daka musu tsawa, ba shiri suka wuce.
Rabi’ah ta ɗaga kafaɗa, ta juya tayi tafiyanta.A hankali take tafiya, ta kunna wak’an Zara larsson (So Good) ta k’ure ƙaran sosai tana bin waƙan cikin jin daɗi, tana cikin tafiya wayanta ta sake ringing, ta duba Zahran dai ce, ba tare da taa rage k’aran wak’an ba ta ɗaga da yake hanyan ba mutane sosae.
“Hey sis” sai magana take bataji sannan ta saka hannu zata rage k’aran,
“ke kinga nama kusan gidan, bara na k’ara taka motan” ta faɗi tana k’ara gudu ba tare da tana kallon gabanta ba, sai dai taji an take wani wawan burki, ae batasan sanda ta saki wayan ba tayi gefe da motanta saura kaɗan su buga ma juna,
Sunyi tsaye da motan sai maida numfashi take tayi matuƙar tsorata, saida ta gama dawowa hayyacinta taga shiru mai motan yaƙi ya janye gashi dole saiya matsar da motar zata wuce.
Sai cika take ranta yayi matuƙar ɓaci, gashi bata ganin ko waye a cikin motan an rufeta da (tin tet), saida taja tsoki cikin ɓacin rai ta fara matsa horn, anma ko gezau baiyi ba, ranta ya k’ara ɓaci,
Kusan fiye da 30mnts suka kwashe a haka, gashi jin kanta ya hanata fita ta mishi magana, tana ganin kiran Zahra na shigowa taƙi ta ɗauka, saima ta jefar da wayar cikin ɓacin rai tace,
“anma fasa lallen, bazanyi ba” ta kwantar da kujera tana karkaɗa kafa, awa huɗu suka kwashe a haka, saida taga magriba na niyyar mata a wurin, da alama kuma idan ta biyewa mai motan sai su kwana a wurin, ta buɗe mota kaman zata fita, kuma sai ta fasa, tayi haka yakai sau biyar sannan dai ta fita,
Dai dai motan nashi taje, sannan ta ƙwankwasa, tana riƙe da ƙugu taa juyar da fuskarta donma karsu haɗa ido damai motan ta sassauta daga masifan data rik’o,
Tana jin an buɗe motan daddaɗan ƙamshin turaren da taji ne ya tabbatar mata da fitowanshi, sannan ta jiyo da fuskarta cike da masifa,
“wannan wane irin wulak’an…..?” kasa ƙarasawa tayi saboda cin karo da tayi da kyakkyawar fuskarshi mai cike da ƙwarjini, ɗauke da kyakkyawan murmushin daya k’arawa fuskarshi kyau,
“Handsome” ta faɗa a ranta,
Ɗaga mata gira yayi cikin wani irin salo daya k’ara fito da haɗuwanshi, ya nuna mata hannu alaman, “Yadai?”
Da sauri ta girgiza kai, cikin ranta tace “A’ah Rabi’ah ba abinda ya fito dake ba kenan” ta k’ara haɗe rai, a fili tace,
“miye yasa bazaka matsar da motanka?”
“bakice bane”
Lallaima mutumin nan ya gama raina mata hankali,
“yanzu nace, yi sauri matsar mun da motannan” tana kaɗa hannu,
“Awk” kawai yace, sannan ya koma zai shiga motan,
Haushi yazo mata iyakan wuya yanda yake maida mata magana kai tsaye, yatsunta biyu ta sake kaɗa mishi, ya juyo suka haɗa ido,
“waye zai bani hak’urin asarar daka kusa yimin?” ba tare da yayi magana ba yake kallonta yana neman k’arin bayani, kaman ta haɗiyi zuciya ta huta,
“Motana daka kusan bugawa”
“na bugane?”
“sai kaa buga zaka bada hak’uri kenan”
“Yi hak’uri” ya koma zai shiga motan, ta sake mishi magana,
“hak’uri kawai? Kasan ko motan nawace da zakana bani hak’uri cikin rashin kulawa”
Murmushi yayi, “masu kuɗi babu ruwansu da ko nawa ne suka siya abu, koda ya lalace zasu siya wani ne” ya shige motanshi ya barta nan tsaye baki buɗe,+
Cikin jin haushi ta kwashi k’asa ta watsa ma motanshi data riga ta wuce ma, “Na tsaneka” ta faɗa, jin tsanarshi take fiye da duk wani abu dake duniyar nan, don ko Abdallah bata tsana haka ba, gani take tsanar ma matsayine da ita, kuma idan ka tsani mutum dole ne zai tsaya maka a rai, anma Abdallah baida wannan matsayin da zata tsaneshi, ko kaɗan bai dameta ba.
Anma wannan tunda take ba’a taɓa ɓata mata rai irin haka ba, lallai duk sanda ta k’ara ganinshi koda a mafarkine sai ya raina kanshi…..Lokacin data isa gida har an gama Sallahn Magrib, idanunta cike da ɓacin rai ta shiga gidan, a babban falo taci karo da Yayanta su Hayrah sun zagayeshi.
Idanunshi na kan k’ofar da zata shigo, nan da nan tayi saurin kauda damuwarta, ta faɗaɗa fara’arta da gudu ta tareshi.
“Oyoyo Yayana” sai kuma ta ɗan ɓata rai ta juya gefe,
“ni namayi fushi, kawai koma ka faɗamun yau zaka dawo, kuma fa ko da safe munyi waya”
Murmushi yayi yana ɗago da fuskanta, “bara inga k’anwar dake fushi da yayanta”
Dariya tayi kawai, “Baki duba wayanki ba halan? Tun ɗazu nake kiranki harna daina k’irga missed calls yanzu haka zaman jiranki nake anan”
Sai sannan ma ta tuna da wayanta, batasan ma inda ta shige ba, “Ayyah! Sorry yayana, U did’nt told me yau zaka zaka dawone, da bazan fita ba”
“kawai naso nayi Suprising naki ne”
Fitowan Aunty Deejah ne ya katse musu firan, “ka ganta nan ba, kullum ina faɗa maka tana fita gantalinta in baka k’asar anma kak’i ka yarda, yau kaa gani da idonka ba”
Cikin takaici take kallonta, “Aunty deejah gantali kuma?”
“eeh gantali, idan ba can ba ina kikaje?”
“na taɓa fita ban faɗa miki ba? Yauma aena faɗa miki inda naje”
“kincemun zakije lalle dai, idan da gaskene ina lallen?”
Cikin bak’ar magana tace “tun a gantalin ya goge”
“ni zaki faɗama bak’ar magana? Kana jinta take maidamun magana son ranta?”
Ɗaga kanshi yayi tana kallonta, “kinfi kowa sanin banson Hayaniya, daga dawowana zakimun tsaye akai, ko tarbar kirki ban samu daga wurinki ba”
“shikenan, daman ya za’ayi tayi laifi wurinka? Sai kacemun gatanan in ringa kula da ita, toh ni daga yau na fidda hannuna a kanta, don karma ta lalace a ga laifina”
“Subhanallahi, Allah ma ya kyauta mata da lalacewa” bata tsaya saurarenshi ba ta juya ɗakinta tana kumburi,
Girgiza kai yayi sannan ya juyar da kanshi daga binta da kallon da yayi, murmushi Rabi’ah tayi, “Bara nayi Sallah Yayana, me za’a girka maka?”
“haba nasan kin gaji da yawa, zan fita inci k’anwata”
“kwana nawa kana cin na wajen? Nidai faɗamun”
“komai k’anwata ta girkamun zanci, anma fa mai sauk’i”
“an gama Yayana” ta wuce ɗakinta tayi Sallah.
Tana idar da Sallah ta shiga kitchen ɗin falon daman ita tafi amfani dashi indai yayanta na gari, daman Deejah babu ruwanta da cinshi, ita dai in en aiki sun girka taci kawai, kitchen ɗin tsaf da yake kullum sai an gyarashi, ta ɗauka tukunya ta ɗauraye nan da nan ta ɗaura girki, Cocunut rice ta girka mishi, da miyan kaji sai k’amshi ke tashi, ta markaɗa fruits ta mishi drink dashi, ta ɗauka a tire sai ɗakinshi, ta shiga bayan ya amsa mata sallama,
Tana ajewa ta kama hannunsu Hayran, “ku taso muje muci namu, kun cika Daddy da surutu”
“ina zakuje? Ku zaunanan muci tare”
“A’ah Yayana, ka dawo da gajia, ka huta sai da safe”
Yayi murmushi “tohm Allah ya kaimu”
“Ameen”
Suma suka mishi “Good nyt” sannan suka tafi. Sai da ta tabbatar sunyi Sallah, sannan ta raka kowannensu ɗakinshi, ta kunna musu kallon Tom and Jerry,
“idan anji barci a kashe, kar kuma a manta da Addu’a”
“tohm Auntie” itama ta dawo ta wuce ɗakinta,
Tana kwanciya kaman a T.V, hotanshi ya ringa dawo mata, yanda yake mata kyakkyawan murmushinshi, cikin Izzah da nuna isa, da yanda yake bata amsa da idanu kawai ko da hannu, ta ringa jan tsoki kawai tana juye-juye, tsawon lokaci sannan barci ya ɗauketa.
Yayan nata na gama cin girkin, yayi shirin barci, bai zame ko ina ba sai ɗakin Deejah, ya ɗan k’wank’wasa shiru ba magana yama ɗauka tayi barci, sai da ya murɗa k’ofan ya shiga, can ya hangota gefen gado ta bashi baya, shi sai lokacin ma ya tuna da wai laifi aka mata,
Girgiza kai yayi, Deejah ko rigima, hakanan ya k’arasa kutsa kanshi cikin ɗaki yana tunanin ta inda zai fara rarrashi.Washe gari tana duba wayanta, misscalls 99+, da messages ɗin Zahra duk dai tana mata mitar rashin zuwan da tayi ne, kaɗan kaɗan zata daki Zuciyanta, saboda anan ne takejin Zafin abunda ya mata, koda second ɗaya ta kasa mantawa dashi, kyakkyawan murmushinshi sai yawo yake mata a k’walwa,
“I hate him” ta faɗa da k’arfi, ko breakfast ta kasayi har kusan 1pm. Sai da yayanta yayi kiranta sannan ta fito daga ɗakinta ta nufi sashenshi,
Bayan sun gaisa ya nuna mata wata haɗaɗɗiyar k’atuwar jikka mai kyau,
“ko kinma manta da sak’onki ne?”
“Ina fa? Kawai nabar Yayana ya gama hutawa ne” ta fara buɗa jikkar cikin farin ciki.
“Wow Yayana duk wannan nawane? gaskia Yayana ngde….”
“Shhht!! Idan ban miki ba wazan mawa? Duk duniya kina da wanda ya fini ne?” murmushi tayi, taɗanyi hugging nashi,
“Allah yabarmun kai Yayana”
Ta ɗauka tsarabanta, a bakin k’ofa suka haɗu da Deejah sai shan k’anshi take, tana duban jikkan hannunta taja tsoki, murmushi kawai Rabi’ah ta mayar mata,
“Aunty deejah An tashi lafiya??”
“eeeh” kawai tace da ita, bata k’ara cewa komai ba itama ta wuce.
Kayan da zata saka wurin Dinner ne na yau, anko ne komai kalan da za’a saka, anma nata is more expensive, sai da ya haɗo mata da er k’aramar jikka mai ɗaukan ido, da takalminsu da agogonsu mai haɗe da necklace da earrings nasu, komai dai da zata buk’ata masu tsada sosae.
A ɗakin Yayanta, Aunty deejah ce ta haɗe ranta wuri ɗaya sai cika take, da yayi kaman ya mata banza don yasan k’orafinta bai wuce kan Rabi’ah, sai kuma ya ɗago kai,
“Yadai deejahna na ganki cikin farin ciki?”
“na maka kama da wadda take farin ciki ne?”
Saida yayi k’asa da murya sannan yace “toh aike kullum ma haka kike”
“me kace? Yanzu idan nayi magana kace na cika tsegumi, anma kuma ko kaɗan kasan baka kyautamun”
“Yau kuma me nayi?”
“tun jiya nace ka nunamun tsaraban Rabi’ah kaqi, sai yanzu ka bata saboda kasan nata yafi nawa ko?”
“Cikin dare ko hutawa bazaki barni nayi ba zanta faman nuna miki tsaraba? Saboda Allah deejah miye bana miki? Anma gaba ɗaya kin saka idonki akan er k’anwarki”
“Naji babu abunda bakamun, anma ai kana banbantani da ita”
“itafa k’anwatahce, ke kuma matata, kinga kuwa akwai banbanci sosae a tsakaninku, kina dasu Umma da Abba, kina dasu Hayrah da Hayran, gani nima naki ne, anma itafa Rabi’ah ni kaɗai take da, meyasa zamu barta tayi kukan maraici?”
“nidai koma……” ɗaga mata hannu yayi, “don Allah ya isa haka Deejah, ki barni na k’arasa aikin lissafinnan gobe nake son fara fita aiki”
“kenanma daga zuwa na harna isheka?” dafe kanshi kawai yayi, yama rasa mezaice mata. Ko kaɗan baison Hayani da yawan magana, anma deejah abunda tafi iyawa kenan fiye da kula da miji.+
Waya suke da Amrah tana bata labarin guy ɗin data gani, ita kam sai dariya take mata,
“idan kin gama dariyan kinmun waya”
“Srry dear, na daina”
“ke ɗince wlhy, hw many times shld i tell uh dis? Dnt start a fight dat uh ddnt knw hw it will end”
“yama k’are insha Allah, coz all i wish is not to saw him again”
“da alama bakinki na faɗin abinda ba shine a zuciyarki ba”
“har a zuciyana hakanne”
“nikam daman nice na ganshi, don yanda kike faɗan haɗuwarshi…”
“da kinsha kayan haushi kam, don ɗan rainin hankaline na qarshe” suna gama waya, ta koma barcinta, ba ita tashi ba saida aka kira la’asar.1
Da wuri ta shirya tafiya wurin dinner tun duhu baiyi ba, sai da tayi Sallama ya amsa mata sannan ta shiga, sai kuma tayi baya zata fito.
“Yadai?”
“ba komai naga kana aiki ne”
“idan ina aiki ba’amun bankwana?”
“Sorry Yaya, na tafi”
“haka zaki tafi babu kuɗin lik’o?”
“ba komai Yaya, akwai kuɗi wurina”
“idan ya qare fa? Kinga ni zoki amsa” ta shiga tana murmushi.
Bandir na 1k ya bata guda biyar, ta amshe ta saka jikka, “sun isa ko a k’aro?”
“sunmayi Yawa Yaya, kaga jikkar ma ta cika sai dai na rik’e wayoyina a hannu, Allah dai ya k’ara buɗi”
“Ameen Ya rabbi, a dawo lafiya”
Tayi tsaye tana gyara zaman mayafinta, ya ɗago yana murmushi yasan akwai magana,
“ehheen!”
“daman keys ɗin motarnan”
“ba kinsan inda suke ba?”
“wannan bak’ar fa”
“tohm ki ɗauka mana”
“sabuwarnan fa Yaya”
“ita ɗin, idan kinji daɗinta ki rik’e kawai”
“Da gaske Yaya? Wayyo daɗi,” ta faɗa jikinshi tana murna, “thank uh so much Yaya” ya ɓata rai,
“bana hana godiyarnan ba?”
“Sorry broz, saina dawo”
“tohm a dawo lafiya, kar dai kiyi dare sosai”
“Insha Allah, bye” ta biya tama su hayran Sallama, sannan ta wuce gidansu Zahra, a can ta iske Amra ana musu makeup, ana gamawa itama aka mata, anan suka shirya, wurin 10 suka wuce wurin dinner kai tsaye.
Suna isa wurin kallo ya koma sama, don kowacce ba k’aramin haɗuwa tayi ba, ga wani taku da suke a tare na burgewa, suna sanye da pink ɗin riga, da mini-skirt baqi, ankon da kowacce ta saka wurin, sannan suka zubo dogon gashinsu bak’i mai santsi, sai Zarah da tayi k’ananun kalba mai kyau, ba k’aramin haɗewa sukai ba, wurin da aka bari musanman donsu suka zauna, daman already an fara suka shigo.
Ko kaɗan Rabi’ah bata ɗaga fuskanta ta kalli inda su Zahra keta firan wani haɗaɗɗen guy ba, da alaman duk samarin wurin babu wanda ya haska kamanshi, shine Babban abokin ango zaune a hightable, ita kam haushin wanda ya dameta kawai ya isheta,
Sama-sama take jiyo daddaɗar muryar Abokin Ango yanda yake bada tarihin Ango cikin yaren Hindi, kaman ba indiyen Asali, cikin taushi yake magana sosae ya burge mutanen wurin, sai da ya gama sannan yayi da turanci yanda kowa zai fahimta, cikin barkwanci yake magana.
Tananan tana tunani har aka kira Amarya da Angonta su taka, sannan aka kira k’awayenta da nashi suma suyi rawan, Amrah sarkin son rawa kusan ta riga kowa mik’ewa, Rabi’ah tace “nidai liƙi kawai zanyi” suka jera a tare zuwa filin.
Taja tsoki, “kunsan da zanga mutuminnan a wurinnan zan shak’eshine kawai in huta da haushinshi”
Har suna haɗa baki “wa kenan?” su sunma mnta
“guy ɗin dana baku labari mana”
“da alama ya dameki da yawa” inji Amrah
“bazaki gane yanda nakejin tsanarshi bne”
Zahra tace “want another reason to hate him?” kafin ta maida ma Zahra amsa sai dai taji ta taka abu suna dai dai isa filin rawan, ta zame ta tafi suuuu tana niyyar faɗuwa sai dai taji tayi karo da mutum, da sauri ya rik’ota ta faɗa k’irjinshi.
Yanayi biyu ne ya ziyarceta, na farko faɗuwar gaban ta kusa faɗuwa, na biyu kuma k’irjinta ne ya buga, wani irin yanayi da bata taɓaji ba sanadiyyar haɗuwan jikinsu, kunya ta sanya ta kasa ɗaga kai ta kalleshi, tayi kwance saman lallausan k’irjinshi, tama manta duniyar da take.
Tafin da aka farayi a wurinne ya dawo da ita, da sauri ta ɗaga kai suka haɗa ido, ta waro dukkan idanunta cikin kaɗuwa da mamakin ganin kowaye,
“kaine?” ya ɗaga mata girarshi, cikin salon dayake saurin rikitata.
Ko waye Rabi’ah ta gani??