YAR MAKIYAYA CHAPTER 16
Cikin nutsuwa yake tuk’i idanuwan sa na kan titi yana ganin yanayin hark’allan mutane wasu su bashi dariya wasu kuma su bashi haushi. Wayar sa ce tayi k’ara don haka ya yi parking a gefe sannan ya d’aga wayar + “Habeeb bro! I can see you are already missing me, ai na fad’a maka you can’t do without me!” Suraj ya fad’a cikin yanayin zolaya. Daga d’ayan b’angaren Habeeb yace “Hah! As if kai ma zaka iya rayuwa ba ni! Anyways ina gari fa yanzun haka amma ina da wasu y’an ayyukan da zan yi , but gaskiya you will pick me up when am done coz ba mota a waje na”. “Ok toh ba matsala yanzun haka ina kan hanya I’ll take care of some business ,let me know in ka gama sai in d’auko ka”. Daga nan suka yi sallama kowanne ya ajiye waya Suraj ya tada mota yaci gaba da tuk’i….. Hirar su suke mai dad’i ita da umma hauwa k’ararrawar k’ofa ta yi k’ara hakan ya sa Layla ta mik’e cikin sauri ta nufi k’ofa a zaton ta Suraj ne ya dawo amma wanda idanuwan ta suka nuna mata mutum ne da bata yi tsammanin ganin sa ba kwana kusa
Zaro ido tayi baki na b’ari tace “Yarima SAEED!” Wani shu’umin murmushi ya sakar mata sannan yasa hannu ya ture ta gefe guda har ta kusa fad’uwa, cike da k’asaita ya shigo falon se k’aran takun takalmin sa kake ji yana k’are wa katafaren falon kallo kafin ya juyo ya dubi Layla daga sama har k’asa se faman gyara mayafin kan ta take yi kanta a k’asa. Umma hauwa ba tun yau ba ta san halin shi sarai don bashi da mutunci tasan in har ta sa baki tayi magana kashin ta ya bushe dan haka ta ja baki tayi gum ta d’auki waya a hankali ta fara k’iran Suraj. Matsawa ya soma yi kusa da Layla duk da ta k’i had’a ido da shi tana iya kallon yanda yake takowa kusa da ita saboda haka ta fara taking steps baya baya har saida ta ci karo da staircase (matakalar bene) hakan yasa ta zube k’asa ,nan da nan hawaye ya fara gangaro wa diga idanuwan ta. Hannun ta ya chafke yana dariya kafin nan take yanayin fuskar sa ta chanja “me kike nufi kenan? Ohhhhh nagane , so gudu na kike yi, i should have known yanzu y’ar makiyaya is not that piece of crap! Kin waye kina rayuwa a mansion of course dole ki ja baya in kin gan ni ko da yake kin saba since wannan ba shine first encounter d’in mu ba, Really Soooraj yayi k’okari dubi yanda ya chanja y’ar makiyaya ta zamto mutum kinga ya sauk’ak’a min aiki”
Cike da firgici Layla ta fisge hannun ta gami da ja da baya tace “ni ban fahimce me kake nufi ba don Allah ka kyale ni kar ka cutar da ni, babu abun da nayi maka na shiga uku !” Umma hauwa tayi ta k’iran Suraj amma shiru babu amsa baya d’aga wa hankalin ta ya tashi ta ajiye wayar ta nufi inda Layla ke zube a k’asa tayi k’ok’arin d’ago ta Saeed ya hankad’e ta nan ta zube a k’asa wanwar abunka da y’ar tsohuwa. A tsorace Layla ta saki k’ara ta mik’e zata nufi inda Umma hauwa take ya dakatar da ita ta hanyar damk’o hannun ta yana kallon yanda duk ta birkice kafin yace “ya kamata ki gane cewa ke tawa ce ni kad’ai! You are mine! Saboda mai martaba ya kawo ku nan ya b’oye hakan ba yana nufin yayi min katanga da ku bane ,babu wanda yanzu ya isa ya shiga tsakani na da ke ko da jarumin naki suraj” Kuka Layla ta saki cikin d’aga murya take k’iran Suraj kamar ranta zai fita Wata dariya Saeed ya saki kafin ya ce “ki yi ihun ki yanda kike so babe shout all you can babu abunda zai sa na rabu da ke!!”. Jiri ne ya kwashe ta nan da nan ta sulale ta zube a jikin sa ganin haka ya shimfid’ar da ita ya k’ura mata ido yana murmushi kafin ya juya yayi ficewar sa daga gidan…… “Habeeb pls enough of your shopping, ni fa na gaji hutu kawai nake so” Tab’e baki Habeeb yayi kafin yace “ohhhh suraaj! Matsala na da kai takura, nifa ban taho da kaya ba daga gida haka na taho saboda unexpected ne tafiyar gashi ba kwana kusa zan koma ba , anyways muje kawai don nasan in bamu tafi yanzu ba se ka had’iye ni babu shiri.”
Dariya ya bawa suraj suka fice daga shopping mall Suraj na jan mota ya d’aga wayar sa don yin k’ira sai yaga missed calls daga umma hauwa har sun fi sha biyar “what the jahannam! Ya Ilahy i hope all is well.” ya fad’a da k’arfi. Habeeb ya dube shi yaga kamar ya shiga damuwa yace “what’s up dude? what’s with that face i hope ba wata matsala?”. Ajiyar zuciya Sooraj yayi yace ” i dunno Habeeb, Layla was recently ill sannan umma hauwa tayi ta k’ira more than 15 missed calls that doesn’t seem normal Habeeb normally Umma Hauwa bata k’ira na a waya in babu matsala i think i should call back” Kai habeeb ya jinjina yace “amma ya kamata ka nutsu in sha Allah babu matsala yanzu bari in yi driving se kayi making call d’in , besides kai da kanka kake fad’a min rigimar Layla this days.” Jin haka suraj yayi murmushi kafin ya yi parking ya fita Habeeb ya dawo shine mai jan motar Suraj ya yi ta k’ok’arin k’iran wayar su duk basu d’auka ba sannan ya k’ira wayan cikin gida ma babu answer. “Kai Habeeb pls speed up am sure akwai matsala”………….. Relax dude! ai gashi muna shiga gidan” cewar Habeeb yana kutsa motar cikin gidan daidai lokacin ne Saeed ke fita da nashi motan kuma da gangan ya sauk’e gilashin motar sa ido cikin ido suke kallon juna da Suraj har motocin suka yi clear, saeed ya fice shi kuma motar su ta shigo. + Ko numfashi da kyar Suraj ya fitar, wayar hannun sa ma zame wa tayi baki a bud’e ya dubi habeeb shima habeeb kallon nasa yake, da kyar ya saki nannauyan nufashi kafin yace “REALLY??! …….. Habeeb did you just saw what i saw? I mean….. How on earth is this possible? Habeeb what if he hurt my wife…….. I …..i can’t …” Suraj bai k’arasa maganar ba ya bud’e motar da gudu ya nufi main entrance na gidan. Yana shiga ya fara kwalla k’iran Layla kafin ya hango ta shimfid’e a k’asa ko k’afafun sa ya kasa d’aga wa balle ya motsa, Habeeb na ganin haka ya taimaka wa umma hauwa ta tashi sannan suka kama Layla zuwa mota bai bi ta kan Suraj ba suka nufi asibiti. “How could this be? I can’t believe he had the gut to showoff just like that and humiliate my family” Saida suraj ya maimata hakan sau uku a yanda yake tsayen kafin ya ce “Oh God LAYLAH!!” Sai lokacin ya dawo senses d’inshi ya laluma jikin shi kaf babu waya , a fusace ya yi wurgi da jacket d’in shi ya bugi couch da k’afar sa “Yeah OF COURSE! well done Soooraj! well-done! You left the God damn phone back in the car , Layla’s been taken to the hospital and what are you doing?…. You are fucking Standing like a statue doing nothing” Ya fad’a da k’arfin gaske biting on his fist kafin ya haura stairs da sauri ya nufi Bedroom inda ya samu wayar Layla ya k’ira Habeeb. “what on earth are you doing dude, I’ve been calling ur phone baka d’aga wa look what ever you are up to set that aside and come to the specialist hospital right now” Suraj bai ce qala ba ya kashe wayar da sauri ya d’auki key d’in mota ya fita…….
Isowar Suraj asibitin ya iske Habeeb yana waya da mai martaba, yasan tabbas ya sanar da shi abunda ya faru , wafce wayar Suraj yayi Habeeb ya juyo a fusace yace “what d heck are you doing man?! Magana nake da His royal highness regarding abunda ya faru ya zaka katse wayar?” Had’e rai Suraj yayi kafin ya mik’a wa Habeeb wayar yace “i know, amma if you had asked da bazaka fad’a masa komai ba regarding this issue” “WHAT??!! what exactly are you trying to say? I mean Suraj , this man has crossed all limits, he walked into your mansion with head held high and insulted your pride how could you stay calm without taking action? Like seriously? Ina ga baka da lafiya kaima kaga likita”. Murmushin dole Suraj yayi kafin ya dubi Habeeb ya dafa kafad’ar shi yace “look bro, ba wai na hana ka fad’a bane it’s just that Now it’s time to stop whining and take a step foward, bana buk’atar protection d’in mai martaba anymore, i will do whatever it takes to deal with Saeed and that Hypocrite Aamir by myself, sun gama kaini mak’ura let mai martaba be, I’ll make sure i make their lives a living hell”. Habeeb kasa magana yayi yana kallon shi, kafin yace “well! You know. If kana ganin hakan will quench your thirst of ……” Kafin habeeb ya k’arisa Suraj ya wuce ya shiga d’akin da Layla take. Habeeb ya furzar da iska ya dubi Umma Hauwa dake zaune tayi jugum “Ya Ilahy i hope this guy is not trying to do something stupid.” ………. BELEL……… “Ahmadu tun kafin rai na ya b’aci ina buk’atar ganin Saeedu nan da kwanaki biyu! Na jima ina yafe Laifukan sa amma wannan karon he has exceeded za limits”. Kai a k’asa Uncle Ahmad ya ce “Allah ya huci zuciyar mai martaba In Sha Allah zan yi yadda kace, Saeed ya tafka babban kuskure duk hukuncin da kayi masa daidai ne”. Ko kallon inda yake Mai martaba bai yi ba Haka Uncle Ahmad ya fice da takaicin Saeed ya nufi sashen sa yana bambami
“Unless i die, yaran nan baza su bari na samu peace of mind ba, Yaya za’a yi Saeed ya aikata hakan, da matar ka har ma da y’a! How disgusting! Farko Aamir yanzu kuma Saeed, sun sa mai martaba ko kallon fuska ta bai son yi but I’ll soon put an end to this” “ashe kuwa baka d’auko hanyar kashe wannan wutar ba” Uncle Ahmad ya ji murya daga bayan shi tana magana, nan take ya juyo ya k’ura mata ido Maryam ce matar sa Mahaifiyar su Saeed tsaye. “me kike nufi da ban d’auko hanyar kashe wutar ba?” Ya tambaya yana mai nutsuwa don jin amsar da zata bayar “mak’e kafad’a tayi sannan ta zauna kan doguwar kujera ta d’aura k’afa d’aya kan d’aya tace “kada ka hukunta su akan d’an wannan laifin domin kuwa duk abunda ya faru laifin ka ne kai da mai martaba, komai SURAJ! SURAJ !SURAJ. ….. Ina nufin shi kad’ai ne d’a a gidan nan? An d’auki tsana an d’aura musu komai sukayi ba a daidai yake ba nashi ne daidai ,suraj ya zama tamkar lu’u-lu’u na kohinoor mai daraja ai yau da gobe dole su ma a ga sauyi daga wajen su saboda haka ni kar a tab’a min martabar y’ay’a na!” Tamkar gunki haka Uncle Ahmad ya k’ura mata ido cike da mamakin sauyin halin da tayi……….Kai Uncle Ahmad ya jinjina yana murmushin takaici kafin yace “ban yi mamaki ba ko kad’an, sam sam kalaman ki basu bani mamaki ba. Daman kullum nakan tambayi kaina cewa me yasa ni y’ay’a na suka fita daban? Me yasa halin su ya banbanta da nawa? Se yanzu na samu amsa ingantacciya! Ashe na manta jinin ki ma yana yawo a jikin su, of course! I’ve been wondering me yasa ni abunda ban yi wa iyaye na ba na rashin d’a’a su kuma suke aikata wa? Se yanzu kalaman ki suka nuna min dalili but just remember duk bak’in halin ki you can never change the fact that Suraj tamkar d’a yake gare ni ba kuma jini na ne tunda d’an uwana shi ya haife shi kuma, i will not let your mistakes ruin this family!” Yana kai nan ya juya yayi ficewar sa daga sashen yayin da Maryam ta ja balance ta gyara zama tana bambami F.C.T…. Suraj ne zaune gefen gadon da take kwance yana waya habeeb na zaune chan gefe kan couch yana shan tea “Ok then Mom se kin iso” shine abu na k’arshe da Suraj ya furta kafin ya katse wayar gami da maida duban sa ga Layla ya sakar mata murmushi yace “kina buk’atan wani abu ne? Abinci? Ruwa? Anything!”. Murmushi tayi tace “babu abunda nike buk’ata, ban jin yunwa”. Kai Suraj ya jinjina kafin yace “Layla ina son zan tambaye ki” juyo wa tayi tana kallon sa kafin yaci gaba da cewa “Saeed!, me yayi miki? Ya buge ki ko? Nasan dole ya……….” bai k’arisa maganar ba Layla tace “Nifa babu abunda yayi min kawai de ya tsorita ni ne” tana kai nan tayi shiru ta kawar da kan ta gefe, nan take Suraj ya mik’e ya fice daga d’akin Habeeb na gani haka ya ajiye kofin shayin ya bi bayan shi. “Bro! What the heck was that!! Me kuma ya saka b’acin rai all of a sudden? ” “Habeeb kai baka gani ne? Baka ganin k’arya take yi? Me yasa Layla zata kare shi? Cewa fa tayi babu abinda yayi mata alhalin k’arya take yi, bakaga ta kasa ko had’a ido da ni?”
Kai Habeeb ya girgiza kafin yace “Wai me kake fad’a ne haka? Kasan cewa har yanzu bata gama farfad’o wa ba sannan she’s in pain and shock kuma Layla ko da bata fad’a maka gaskiya ba ya kamata kayi mata uzuri zai yiwu tana da dalilin ta give her some time” Shiru Suraj yayi ya jingina da bango kafin ya ce “Ban san me yasa ba Habeeb when it comes to Layla ina rasa nutsuwa ta , in wani abu ya same ta bazan iya yafe wa kaina ba”. Habeeb ya dube shi yace ” na fahimce ka Suraj amma ni ina ganin ya kamata ka ajiye komai a gefe guda abunda ya faru ya faru, Saeed ya yi kuskure kuma ya tafi amma Layla! Layla is you present and future don haka yanzu tana buk’atan ka kusa da ita fiye da komai , ka manta da Saeed ka d’auki matar ka kawai kayi nesa da ita out of his reach, nesa da Saeed, Ameer and thier wrath! Ku sake rayuwar ku cikin farin ciki da soyayya”. Ba tare da ya amsa ba Suraj ya mik’e ya koma d’akin inda ya tarar da Layla har ta yi barci, wuta ya kashe ya zauna gefen ta ya k’ura mata ido hannun sa cikin nata. Habeeb ya dad’e zaune yana waya da mai martaba kan yanda sukayi da Suraj da kuma shawarar da ya bashi, mai martaba yayi amanna da shawarar sannan ya jinjina wa Habeeb bisa k’ok’arin shi na ganin ya tsaya wa d’an uwan shi a ko wanne hali yake ciki “Nasan in nayi magana da Surajo bazai k’i bin umarni na ba dan haka kar ka damu Habeebu in Allah ya kai mu gobe zan k’ira shi dare yayi ya kamata kaima ka huta” Da wannan maganar Mai martaba ya k’are maganar sa suka ajiye waya. Daidai lokacin ne Suraj ya fito jiki ba kwari ya zauna gefen Habeeb sannan yayi ajiyar zuciya yace “Habeeb in na tuna wani abu se inga a rayuwa ban yi wa Layla adalci ba ko kad’an! Komai da ya faru a rayuwar ta na bak’in ciki duk nine sila, nayi zaton in na aure ta zan k’ara ninka mata farin ciki ne amma abun ba haka yake ba from a positive view”…….. Habeeb ya dafa kafad’ar shi yace “Bro what are you trying to imply by saying so? Me kake nufi kenan?” Hawayen shi ya share kafin ya dubi Habeeb yace “The Layla I’ve met a wancan lokacin yarinya ce wanda iya rayuwarta babu abunda ta sani face kiwo, duniyar ta karama ce amma farin cikin ta mara misaltuwa ne, bata san wata duniya ba, banda tsaunika, dabbobi, bishiyoyi, da koren ganyayyaki babu wani abu a rayuwarta, bata san firgici ba, she was innocent, hardworking, and beautiful in all aspects, zuciyar ta farinciki ta sani sannan cikin ta babu komai se k’aunar mahaifin ta. Habeeb kwatsam se na shigo rayuwar ta, from day one na fara k’aunar ta sannan zuwa na Belel shine mafarin matsalolin ta, ga takurar Ameer da Saeed ,ga nesanta ta da nayi da duniyar ta mai cike da haske na kawo ta cikin duniya ta mara daidaito, Habeeb komai da ya faru keeps haunting me , they are like nightmares, ina so in saka wa Layla da farinciki iya rayuwar mu, but how? Yaya zan yi in yi hakan in har Saeed da Ameer are out there? Kaga ni fa babu inda zan sake tafiya, in fact zan d’auki Layla mu koma Belel in ta haihu.” Zaro idanuwa Habeeb yayi ya mik’e yace “WHAT?!! Me kake nufi da cewa zaka d’auki Layla ka koma Belel? Ka manta yanda ka zo nan ne? Besides me zamu ce da mai martaba? Suraj please ka saurare ni ka bar k’asar nan kai da matar ka in komai ya lafa kuka yi settling se ka dawo it will be better”. Kai suraj ya girgiza yace “Noooo Habeeb! Bro ka fahimce ni! Ni fa ba kwallon garawan su bane da zasu dinga gara ni, sannan da kace in bar k’asar nan ina zan je inda Ameer da Saeed bazasu kai ba? I have to fight back saboda ina so in sama wa Layla farin cikin ta da ta rasa, Habeeb don tana murmushi ba yana nufin tana farin ciki bane kawai tana iya k’ok’arin taga na gefen ta yana farin ciki ne so I’ll do the best i can to make her happy” Habeeb yasan babu yanda za’a yi Suraj ya saurare shi don kuma yasan bazai tab’a sauya ra’ayin shi ba don haka ya fuskanci Suraj yace “in that case , my brother ina so ka sani duk inda kake duk abunda zai faru ina tare da kai 100% ko da kuwa hakan na nufin zan rasa rai na” Rungume shi Suraj yayi yana masa godiya……..