RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 29 BY HALIMA K/MASHI
Shatima yace,
Yarinyar da ba ta taba rike
babbar waya ba bare computer?”
Safwan yace Wannan duk laifinka ne, in
mun fita yanzun muje a sai mata waya da laptop Shatima yace
-To kin ji”.Salma ta ce,Na gode”
Shatima ya ce,Ki masa dai godiya, shi zai
sai miki Salma ta cube shi, “Yaya na gode sosai Safwan yace Kar ki wani damu”
‘ Salma ta yi murna sosai da ganin wayarta
dankareriya da laptop, Shatima ya ce,
“Ko dai in
miki canji ne don wannan laptop din ta fi tawa kyau da tsada Salma tace To ka dauka mana”
Yace Wasa nike, ga shi ya kashe mik kudi
duka fa kin ga rasist din
Ya bude ledar wayar ya ciro su duka biyun.
dubu dari shidda da talatin. Salma ta zaro ido tana kallon Shatima;
*Yaya ya aka yi ka bari har ya kashe
irin wanna kudin?”
Yace Gurin Safwan wannan karamin kudi
Ne Ta ce,
“To na gode, don Allah Yaya ka yi
masa godiya”.Ya ce,
“Bari in kira miki shi ki masa, ni tuni
na yi masa-godiya
Safwan ya daya wayar Shatima tare da fadin,
“Na yi nisa, amma ban kai gida ba
Yaa ce, “Na kawo sako tace nayi maka
godiya. Ya ce, “Haba babu damuwa
Salma ta amsa tayi sallama, ya amsa tare da
cewa, ” Sun yi miki ko? Tace
“Sosai ma, na gode sosai Yaya, Allah
ya kara arziki” Yace
“Zan iya yi miki komai Salma, a cikin
ledar laptop din nan za ki ga sakona, sai na ji
kiranki”Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. Salma ta kalli Shatima sai tana ganin kamar ya ji abin da Safwan din ya fada.
Ya ce, “Mu je duk ki hada su
Ta saka layinta a waya, randadau gwanin
shi’awa, Shatima ya ciro laptop din yana kunnawa. Salma ta duba cikin ledar katin Safwan din ta gani,
ta dubi Shatima, hankalinsa yana kan laptop din dayake dubawa. Ta dubi katin an rubuta, Safwan EL Nasir, ga lambobinshi nan. Ta juya bayan katin ya
rubuta, “Ina jiran kiranki Salma ta yi saurin maida katin tare da
tambayar kanta abin da Safwan yake nufi. Sai ta ji duk ta tsani wannan kayan, tana fa da aure ya sani, to
ita abin duniya ba zai rude ta ba. Shatima yana nuna
mata yanda Za ta sarrafa computer, amma yaga duk ranta a jagule ya ce,
“Ya ya ba kya murna ne?”Tace Ina murna mana, kaina ne ya kama ciwo
Yace To bari na aje gobe na nuna miki”
Ta ce,To
“. Yana fita ta shiga tunani. “Bari dai kada ta yanke masa hukunci har sai
in ya bayyana nufinsa, kuma babu damar ta dada ma Shatima don ba za ta zama sanadin lalacewar zumuncinsu ba.Har sati ya zagayo ba ta kira ba, kuma bata da niyya, illa dai ta yi wa katin boyo na gaske. Salma
Dankasa an shiga KASU university ta Kaduna. Ita dai English take karantawa, sabanin Salma da ke karantar Mass Communication. Burin Salma jarida, amma in ba ta samu ba komai ta samu za ta yi, sai ga
shi ta samu tana ganin za ta iya cinma burinta. Tana girki ta jiyo kukan wayarta, tana zuwa ta ga bakuwar lamba. Ta dan yi shiru tana son tuna ko ta taba ganin
lambar, kiran yana daf da tsinkewa ta daga da sauri, yar siririyar murya ta ji an ce, “Salma?”
kafin mu yi nisa wacece don
Allah?”
Ta ce, “Ni ce Sa’ida daga G.R.A”
Salma tace
“Ah Sa’ida abin mamaki, ina ki
ka samu lambata?”Ta ce,
“A gurin wata yarinya Saddika S. Tata
Tace min department dinku ta ke”
Salma ta ce,
“Na santa, muna shiri sosai, S.
Tata yar G.R.A ce ita ma?”
Sa’ida ta ce,
“Nima ai nan nike, amma ni
Hausa nike karantawa Salma ta ce,
“Wuuu a languges ki ke, sannu
fa da kokari, kuna shanta Sa’ida ta ce, ‘
“Kuma da yake ina son Hausar bana ganin wuyarta Salma ta ce,
“Haka ne”
Suka dan yi hira, sannan suka yi sallama da
alkawarin sai sun hadu a makaranta, ta yi kamar tace ta gaida mata Safwan, sai kuma ta ga rashin dacewar hakan.
Aliya an yi arba”in an dawo, kuma an koma
bakin aiki. Sai dai ita ma ta sa Shatima ya daukar mata mai aiki, dawainiyar gidan Shatima ta yi yawa
har ta sa albashinsa yana neman ya gagari rike gidan.
Ko da ya yi batun da Aliya, sai ta ce, to tunda haka ne kawai ya rage abin da yake kashe musu. Ya yi
batun da Nafisa don so yake ya ji ta bakin kowa. Sai ta ce, tunda Aliya tana aiki ta dauki nauyin wani abin nata, ni ma tunda na fara yin kayan yaran nan da
zannuwan gado kuma suna tafiya a Zaria sai na rage maka wani nauyin. Amna ma haka, ita ko Salma saita dakata da karatu
Ya samu Amna da zancen, ta ce,
“Ni dama ban dora maka nauyina dari bisa dari ba, don haka wannan ba zancena ba ne”
Kamar kada ya yi batun da Salma, don yana
ganin har yanzún ba wai tana da hankali bane. sai Kuma ya ga ya dace ya ba ta hakkinta ita ma. Tana karatunta ya shigo har uwar dakinta, ba za ta tuna rana
Ta karshe da Shatima ya shigo dakin baccinta ba. Har
a ranta tana cewa, in dai har Yaya hakkinshi ya kawo shi dakina, to yau kuwa zan sauke wa kaina nauyi Ya zauna bakin gado, “Kina karatu ne?” Tace
“Eh Yaya, ya gajiyar hanya? Ina su
Ashraf?”Ya ce,
“Suna lafiya. Salma’ ina son za mu yi
magana, amma ban sani ba ko za ki fahimta?”
Ta ce,Yaya mai zai hana ni fahimta in dai
Ka fahimtar da ni?”
Ya yi dan murmushi tare da fadin, “Haka ne.
wato Salma abin da ke faruwa dawainiyar yau da kullum din nan ne yanzu haka bana iya samun rara a cikin asusuna wannan watan har sai da mai kayan abinci ya bi ni bashi fa” Salma ta ce,”To yaya a rage abubuwa Kamar me?”TaCe,
“Farko ni maimakon direba ana biyanshi a wata, kullum dubu daya zai isa in je makaranta in dawo nawa ne Zaria? Dari uku ne, ko
Ka koya min kamar yanda ka ce, ka ga an samu sauki. Nama da sauran abin da bai zama dole ba sai a
rago, sannan da za ka yarda Yaya ka hada da
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe