SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 29

SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 29

  Zaman su sukeyi lafiya lau abun gwanin sha’awa se Wanda yagani, mansur yasan he’s very lucky da ya sama Nazeefa a matsayin abokiyar rayuwarshi, cos batada Qiwa, Komai tanamai, balle wajen girki, tanamai duk abincin da yakeso, da kungansa kunsan yai kiba Masha Allah, he gat no worries Bangaren Mubeen kuwa soyayya da shakuwa me karfi ta shiga tsakaninsa da ameerah, kullun yana kofar gidansu suna soyayya, sau tari Dr bashir na ganinsu sedai zuciyarshi da yake ya mutu akan ameerah Sam beganin soyayya sukeyi Har rannan yana ganinsu suna tsaye suna hira, yazo musu yai sallama, Ameerah ta amsa a zuci, shi kuma mubeen ya amsa da waalaikumus Salam hade da Dan tsuke fuska! Dr bashir ne yace malan wai me kake zuwa yi nan ne? Mubeen da ya kalleshi yace me idonka ya ganema? Yace Be ganemum komaiba Dr Bashir yace to Kadena zuwa wajenta har gobe Ina Sonta Smiling Ameerah tai tace Kai Malan dakata, kar insake ganin kafar ka anan wajen, in bahaka ba wallahi sai nasa an tarama gajiya, Sannan kaga Mubeen, he’s My fiance shi Zan aura Mubeen yace Masha Allah Ina fatan kaji da kunnanka? Kaje chan ka gyara halayenka kagani idan ba’a soka ba, Sannan yacewa Amirah sweet heart zo mubar wajen, Matsawa sukai suka barshi a wajen, ya sororo kamar ya kwala ihu Gida ya nufa ya zauna yai nazarin gaskiyane, ya chanza hali Dan yasan tabbas har yanxu halinshi na nan na Neman Mata! Mik’ewa yai a daki ya Fara zagaye ina tino abubuwan da da sukai shi da Mubeen, kenan shima it’s not too late ya tuba, cos Allah na amsan tuban mutune, Kwalla masu zafi ya zubomai ya daga Hannu yace inshaa Allah daga yau na chanza halina, I change for good, Ya Allah na tuba, Allah ka yafemun Kalmar shahada yayi, sannan ya shiga toilet ya sake Wanka ya tsarkake jikinshi, yazo yai Salatul tasbihi ya ruka Allah ya Kara shiryashi da sauran yan uwa musulmai baki daya, _muma ga wani sirri zan bamu mudinga yawan kalmar shahada saboda bakunan mu sai Mu fada abunda zai fitar damu a musulunci bamu saniba_ Allah ya Kara shiryamu ya kuma tsaremu…Ameen Ameerah ne suna tsaye da mubeen tace please dear karka damu, yace haba bakomai, wai ko kinje gidan Amarya Nazeefa kuwa? Tace wallahi banjeba amma cikin satin nan nakeson zuwa, yace OK inkinje ki gaisheta, Jiya su faeeza da faeez sukaje, Tace Ayyah sun kyauta sosai! **** Bangaren Maihaifiyar Mansur kuwa, A yaune zataje gidan beloved son dinta, Dan haka Nazeefa tai abinci kala Kala na tarban Sirikarta, Wajen 11 na safe Driver yakaita ita kadai, Nazeefa na ganinta Ta tashi da gudu taje tai hugging dinta tana mata sannu da zuwa Mansur ne ya fito daga daki sanye da track suit yamai kyau sosai duka black ita kuma Nazeefa Tasha atamtarta tayi kyau sosai Nan Nazeefa ta kawo mata kayan fruits da drinks da abinci, taci kadan taji dadi sosai, tace Dan Allah kuzauna lafiya, Nasan yarona beda problem idan kuma ya Fara maki wani abun Ki sanar dani kinji, kaima kaita hakuri da ita, kasan zo Mu zauna zo Mu sabane! Yace hakane 1st love, Tace Masha Allah, Allah ya Kara muku kwanciyar hankali tace Ameen, Zata tafine taba Nazeefa 500K tace ko akwai abunda zata siya tace Tagode sosai Har bakin gate suka rakuta, Driver ya kaita gida tana Mai farin ciki da kara son Nazeefa Hajiya mum Mansur nadawowa, Ta sanar da Alhaji tace harga Allah tanason yarinyar akwai kirki, yace haka akeso, ke ko dan kunyar nan na uwar miji bakijiba? Tace to Alhaji ya za’ai Ina missing Mansur ne, Dariya yai yace yanzu kuwa Mansur ya zama na wata, tace to yazanyi *** Bayan Hajiya tabar gidan, Nazeefa tace kaji dadi kai kadai aka Haifa, dariya yayi yace see you kema ai hakane KO Ku biyune a gidanku bansaniba, laaa tace Ashe nikadai ne, yace you’re not seriously, kinsan what do I like most about you? Ta girgiza Kai Tace a’a yace sometimes se kidinga behaving Kamar wata karamar yarinya, Tace LOL, Yace Lolli pop ne ba lol ba Dariya sukai Call din hassan ne ya shugo wayarshi, ya amsa yace bro, Hassan yace bawani bro Kai haka akeyi daga aure se mantawa damu Mansur sosa kai yayi yace afuwan Dear, yasu Hajia? Yace lafiya lau! Nandai sukaita hirarsu ya kawomai gulman Suhailat ta koma gidansu, Mansur yai dariya yace Hassan bakaji wallahi, Hira sukai sosai sannan Sukai sallama! *** Bangaren ummie Kuwa, yau kusan 1 week kenan kota Kira number Mansur be zuwa, bakin ciki ya addabeta, Ita ta kosa ya aureta dan bata ganin kowa a matsayin namiji se Mansur cos irin namijin novel ne da take karantawa, yau taganshi kuma bazata taba ya wuceta ba, gani take shine daidai da ita Dan mansur nada duk wani Abu da mace take bukata gun namiji Dan haka she’s drying for him, and she’s praying Allah yasa ta zama matarshi Kiran wayarshi takeyi Sam baya shiga Dan haka washe gari nayi ta sanar da kakanta zataje gidan ya Mansur taga Amarya, Kakus tai na’am tace sai kindawo, ni badan kafa yadan matsamun ba da tare zamu tafi Ummie ne ta tashi ta Fara shiri Riga da siket na less tasa matsattsu, se flat shoe da jaka ta dakko, se kitson attached da tasha ya zubo har gadon baya, Sannan ta fito se yanga takeyi, Samun adaidaita tayi taimai kwatancen inda ze kaita, Maza dukda tana cikin motar se kallonta sukeyi Dan tayi kyau Har kofar Gidan ta me adaidaita ya kaita, Sannan tai knocking, Mansur yaje ya bude Kallonta yai sama da kasa yaji duk wani farin ciki ya gushemai, Itakam tana ganinshi taji wani dadi sosai Shugowa har falon Nazeefa sukai, Kallonta tai ta shugo ko sallama Da yake nazeefa Nada hankali tace Ina kwana, ummie ta amsa a yatsine, Hade da wurga Mata harara, Aran Nazeefa tace too waye wannan Mansur kuwa na zaune Shi sam beson ta harareta ba Tashi tai tace yaya yunwa nakeji tun safe banci abinciba, Kallonta yai yace to kije kitchen ki dafa Indomie dakwai da Irish duk akwai, Aranta tace chab baga matarkaba! Tana tinanin maganar ne Mansur yace Sweetheart zo muje ciki Lol, Nazeefa dirarriyar mace haka ta mik’e cikin yanga ta rike hannunshi suka shiga dakin Ummie na tsaye na kallon ikon Allah, haushi ya isheta kamar tai Ihu Kwaikwayon tafiyar Nazeefa tai tace shegiya se kace Me jikin roba Tsaki tai tace nifa ba zuwa gidan amaren nan ba se su wani shige daki su barka Kitchen ta nufa, ta kunna gas ta dafa indomie da kwai abunta taci ta koshi Shuru shuru basu fitoba, zuwa tai ta buga musu kofa, Sai gasu sunfito Kallon mansur tayi tace yaaya Zo ka kaini gida bazan iya hawa napep ba, Kare mata kallo Nazeefa tai, Taji haushin maganar kawai setasa ma zuciyarta hakuri tace my love kaje ka kaita din please Dan batarai yayi cos nasan Matsalar Ummie, Key ya dakko yace mu tafi Nazeefa kuwa suna fita ta gyara dakin ta dakko littafan addua tai abunta, Ita Sam bata kawo komai game da ummie ba Hmmmmm Mansur ne yadau ka key, ya fita zekai ummie gida, ahanyarsu ta tafiya ta fashemai da kuka, Lafiya yace kuwa? Kallonshi tai tace bakai bane+ Hmm yace, Zaro ido tai tace hmm ma zakace? Kamanta maganar mune? Ni wlhi I so much love you! Daga ta yace mata, yaci gaba da driving dinshi Shagwaba takeyi mai a cikin motor, text din Nazeera ya shugo kamar haka Mijina abun alfaharina, Ina matukar kaunarka I love you, Allah ya dawomun dakai lafiya, cos Dan fitar nan dakai jinai kamar kakai shekara bansaka a ido na ba…I love yoi Budewa yayi, all this thought alert ne ashe beloved wife dinshine, budewa yai ya Fara karantawa ummie ta matso tagani Dan gulma, da ya lura tana karantawa, Kara karkata wayar yayi yanda zata gani dakyau jitai zufa ya Fara keto mata, Aranta tace matar nan da alamu tanason mijinta Tsaki taja tace saukeni anan! Yai murmushi yace ai bamuzo gidan ba, tace eh din ka barni nace maka Samun waje yai parking ya ajiyeta ta nema adaidaita sahu ya karasa da ita gida, aranshi yace kyaji dashi, Shi kuma yace tunda ya fito bari yaje gida ya gaishe da iyayanshi dama yanason zuwa Yana zuwa ya taddasu a falo, marhaban sukai mai Hajiya tace Ina amaryan? Yace tana gida Hajiya “tace in gaisheku Tace Allah sarki, muna amsawa, Dad dinshima nasiha ya karamai akan hakuri, yace kaga badan hakuriba da yanzu bama tare da mahaifiyarka, Tai dariya tace tabbas, Hakuri shine ginshikin rayuwa Sun dan taba hira Kadan ya tashi ya koma gidanshi Dad dinshine ya kalle Matarshi yace kinga yanda yaron nan yai kiba KO? Tace bana fadama ba Dad yace Masha Allah, Allah ya Kara basu zaman lafiya da zuria dayyaba tace Ameeen *** Tunda ummie ta koma gida taji ta tsana kanta meyasa ma ta nunawa mansur tana sonshi? Wata zuciya tace kinyi gaggawa balle yanada sabuwar amarya ai ba samun shiga zaki ba lol tundaga ranar tasha alwashin bazata Kara zuwa gidan ba se an kwana biyu Bangaren Ameerah kuwa dama yaune tace zataje gidan Nazeeda Dan haka ta shirya ta tafi, Koda taje gidan knocking tai akaqi budewa, Kiran Nazeefa tai a waya tace ganinan fa a bakin gate, da sauri taje ta bude mata ta kulle gidan tanamai farin ciki! Ameerah kallon Nazeefa tai tace kingankine kuwa kinyi kyau abunki kodai ciki gareki? Nazeefa ce Tace kin manta ba ciki gareniba goyo nakeyi, Kwashewa da dariya sukai, Ameerah tace uhmm kindaiyi kiba wlhi Nazeefa tace kyaji dashi, da zuwanki zakimun sharri! Ameerah tace to shikkenan, Suna cikin hirane saiga Mansur ya dawo, Shugowa yai yana sweet heart dina nayi missing dinki hade da bude hannayenshi yana shirin tazomai oyoyo, Ameerah ce tace hoo ango ina ganin love, Kunya yadanji yace lalle yau kece a gidan Namu? Tace wlhi kuwa gaisawa sukai sosai sannan yace Bari na Shiga daki karna hanaku hira Nazeefa tace aikuwa Shigewa daki yai yana tino da al’amuran ummie, yarinyar nan inbe mata da gaske ba rainashi zatai, yana cikin tinanin ne bacci ya kwasheshi Ameerah da Nazeefa kuwa kasa kasa sukai da murya suna ta hira, Ameerah tace ya amarci? Nazeefa tace ba sauki har yanzu wajen ciwo yakemun, ameerah tai dariya, Nazeefa tace Zaki sanine kema ay, wai Ina mubeen me yasa bakuzo tareba STORY CONTINUES BELOW Tace bakomai wlhi next time zamuzo yace ingaisheki sosai, tace Ayah bakomai Hira sukasha sosai kamar karsu rabu, Dazata tafi Nazeefa ta hada Mata sha tatara ta arziki, cos tana son Ameerah, the girl is is unique, duk cikin friends dinsu, su 2 ne jininsu yafi haduwa, saboda Ameeeah time din na tausayin nazeefa sosai, Dan sau tari gidansu yake zuwa cin abinci, rayuwa kenan! tashi sukai ta rakata har waje ta sama napep yakaita gida Nazeefa kuwa, tana dawowa falo ta dakko wayarta ta Kira iyayanta tace tana missing dinsu sosai tace tananan zuwa, umma hafsatu tace indai kuna zaune lafiya bakomai, munanan muna maku addua Allah ya Baku zaman lafiya tace Ameeen Shuru taji Mansur be fitoba Dan haka tasan bacci yakeyi Dan jiya sallar dare yayi sosai be sama enough bacci ba Dakin ta shige taje ta bayanshi ta rungumeshi, tana Kara mannewa da jikinshi, Yanajin motsinta yai kamar yana bacci Itama bata dadeba tai bacci Dan yasan baccin safen yau bataiba saboda Ummie tazo gidan Tasama bacci kusan 1½ hour sannan ya juya akan gadon yana kare mata kallo, shidai yana son matarnan Romancing dinta ya Fara tundaga Kai, firgigit ta bude ido, zatai magana kenan dama already akwai sweet a gefen gadon shi ya dakko yasa a baki, Kai bakinshi kan nata yayi ta kasama magana sedai kallon juna sukeyi! Sunkai kusan 15mins yana kissing dinta hade da romancing, nan ta gigice, suka ci gaba da love dinsu Bayan sun gama suka tashi sukai wanka sukai sallah tare sannan suka shiga kitchen tare, Yace sweet heart har gobe Ina Kara gode maki, you’re my type I love you so much Murmushi tayi tace love you more sweat heart sannan ta rungumeshi Yace kee hmm mudaici gaba da abincinmu Dan yunwa nakeji Tace OK sweet heart *Bayan wata biyu* Haka rayuwarsu taci gaba abun gwanin sha’awa Mansur ya koma bakin aikinshi, itama ta Fara zuwa company din da mahaifinta ya bata ta rike, wanda zata dinga samun kudi a koda yaushe Sannan alkawarin da dad dinta yai mata, yasai Mata mota Matrix taji dadi sosai Da yamma idan Mansur ya dawo shi yake zuwa koya mata moto saboda bata iyaba! Duk safe kafin Ya tafi aiki shi yake kaita wajen aikinta sannan idan yadawo ya biya ya dauketa! Kowa na fita aikinshi hankali kwance, Shakuwa kuwa kamar tun suna kanana sukeson junansu, Dan Ko ina idan ana hiran best couple sune kan gaba! Akwai wata rana da dare suna zaune suna hira sweet heart yace dama akwai maganar da zamui ta gyara zama tace OK inajinka love Yace maganar school ne ya kamata Ki koma please, murmushi tayi Tace tabbas zan koma amma nafison na islamiya love! Banyi nisa sosaiba, yace wow Yar Aljannah, na Tina ma lama fa na aura lol Jefamai trowing pillow tayi tace zaka Sani, ya tashi ya shige daki ta bishi da gudu suna wasan love lol Tana shiga ya kulle kofar yace kinkawo kanki lol Shagwaba ta faramai tana kayi hakuri please, rike mata hannu yayi yace wayace ki shugomun daki To? Tace yanzu zanfita ka budemun Daukanta yayi Yakaita kan gadonshi yace let’s sleep yau bazamui komaiba nasan kingaji my manager! Gwalo tamai tace yeee yau se hakuri, yai dariya yace zaki sani, kashe wuta yai yace let’s sleep muyi addua Allah tashemu lafiya Tace Ameeen Lol kowa ya juya yai baccinsa A cikin baccinsune, Nazeefa tai mafarkin wai ga Wata matanan zata tafi da Mansur wata kyakkyawa! Ita kuma tanata jan hanunshi tana karka bita please Ina Sonka Firgigit ta tashi tade da addu’a tana sharce zufa Shima tashi yayi yace love what’s wrong? Cemai tai wlhi mafarki nayi, yace fadamun! Nan take ta fadamai, Yace karki damu bakomai kawai mafarkine! Ki taashi mui sallah, Tashi sukai sukai nafila sannan sukai addu’oi Sosai yasa karatun qur’ani ya rungumeta kamar zata shige cikinshi bacci ya kwasheta! Addu’a ya dinga tofa mata, A zuciyarshi yace Hmm kaga Nazeefa kamar me aljanu Shima bacci ya kwasheshi, Asuba nayi Suka tashi sukai Sallah, sukai addu’a Nazeefa ta koma baccinta Allah yasa weekend ne, Shi da kanshi ya shiga kitchen, ya fere Irish ya tafasa sannan yazo ya hada da Irish da kwai ya soya! Sannan ya soya kwai daba yasa musu ruwa a flask ya ajiye komai a dining table sannan yazo yai wanka ya gyara kitchen din Na Nazeefa ta tashiba se kusan 9:AM tashi tayi da sauri tace sorry love yau nabarka da yunwa ko? Tana magana tana kokarin tafiya kitchen Janyo Hannnunta yayi yace Noo karki damu na riga na gama komai! Kallonshi tai cike da mamaki tace badai breakfast Kai ba? Yace Lol, falo ta fito taga komai ready a dining Sannu da kokari tace, yace yauwa, muje ki brush ko sweet Heart tace OK Toilet ta nufa ta wanke fuska tai brush suka taho kan dining Tea ya hada musu ta gutsura bread, wani dan kwano ta bude taga Irish da kwai, ta soma ci sosai, tace love naji dadin abincin nan, kaman kasan inason Irish da kwai, yai smiling yace ba dole nasaniba naga kusan kullun se kinci irish ai Tea ta kurba ta ajiye cup din tace Wow thank you I love you so much yau ka cikamun tunbina da yawa! Yace it’s my duty ay, Bayan sungama Kwashe kayan wajen sukai suka nufa kitchen suna hira suna wanke wanke har suka gama……… _Agurguje_ Bayan wata 3 Soyayya me karfine ta shiga tsakanin Mansur da matarsa Nazeefa, kullun suna cikin farantawa junansu rai, basu taba samun misunderstanding ba saboda suna kiyaye duk abunda zai bata musu rai.. Sannan kuma yasakata islamiya tana zuwa Saturday and Sunday, motar da yake koya mata itama ta Iya sosai, idan basa komai haka suke fita kan hanya suyi tsere, Mansur na bala’in son matarshi itama haka!+ Bangaren Su Ameerah kuwa suma shan soyayyarsu sukeyi gwanin sha’awa Dan har mubeen ya turo gidansu an amince ansa bikin bayan Karamar Sallah, Da nazeefa taji labarin tayi farin ciki sosai kuma tana musu fatan alheri, Sedai har yanzu Mubeen naji ajikinshi kamar Nazeefa bata hakura da abunda yai mata ba, Dan harga Allah yana bala’in son Nazeefa, Dan haka ya tashi ya kudira yau zaije Gaisheta da ganan ya bata hakuri Dan duk sanda ya tino Da abunda yai mata hankalinshi be kwanciya, Shiryawa yayi ya tafi gidanta, Koda yaje Mansur benan dan haka yai sallama, Jin muryanshi datai tai sauri ta bude tanamai karemai kallo, Tsayawa sukai a harabar gidan ta Nazeefa kuw kallonshi take aranta tace yau naga ikon Allah Ya kelleta yace kiyi hakuri nasan ke matar aurece amma Dan Allah nazo baki hakuri ne, Kiyi hakuri ki yafemun, yafiyarki shi zai Kara samun natsuwa a zuciyata, nasan ba da son ranki bane Kika amince mun na aura Ameerah kawai dan kina sontane bawai Dan saboda niba! Idonta ne ya cika da kwalla tace tabbas kuwa hakane amma Meya kawoka gidan nan ka fita bansan ganinka, sannan ta fashe da kuka! Tace Wlhi ban hakuraba Yace yeah dama nasan AI baki hakuraba sai yasa nazo Dan girman Allah kiyi hakuri ki yafemun ko zanci gaba da ganin haske a rayuwata! Hakkinki bina yake bazaki ganeba! Kuka ta Kara fashewa dashi, sannan Ta juya zata shiga dakinta ya Rik’e mata gefen hijab dinta a daidai lokacin Mansur ya shugo, Nazeefa tsayawa tai chak, shi kuma Mubeen yaqi sakin hijabin Kallon yanda mubeen ya rike mata hijab yai yace what is this? Nan ma ka biyota ne ka Kara Mata…….be karasa maganar shiba Nazeefa ta juyo cikin jajayen idanuwanta tai maza ta rufemai baki, tace karkace komai, AI ahankali ya matsar da nazeefa gefe Ran Mansur ya baci sosai yace” uban me kazomun yi gida? meya kawoka, ko kwartoncin ne naka ya tashi kuma akan Mata ta!!! Mubeen Yace Allah ya kyauta, kaga malan ka Iya bakinka! Nazeefa kuwa tsugunnawa a kasa tayi tana kuka sosai tana shikkenan, yau na shiga uku, kuyi hakuri Sun dade suna musanyar magana da Mansur da mubeen, shidai mubeen in banda hakuri ba abun da yake bashi kuma yai kokarin ganar da mansur din abunda ya kawoshi Mansur yace naji dai ka fitar mun a gida! Mubeen yace fadama bata lokacine mezanyi anan gidan? Kaima kasan matarka tana sona KO? Wani Yunkuri Mansur yayi kafin ya chapke Mubeen tuni ya fita da gudu yabar gidan Wani zufa Mansur ya ketomai, yana Mai kallon matarshi data tsugunna tana kuka! Daukarta yayi yakaita kan gado shi kuma yadawo yanata zagaye A tsakar gida, Shin mubeen wani irin mutun ne? Shi kuma mubeen ya fita da gudu, sedayai nisa da gidan Yace Oho dai inkaga dama ka kaini court nidai burina ta yafemun, Sannan ya kwashe da dariya irin gudun da yasha yau ya dade be yishiba Lol Gida Mubeen Ya karasa, yana shiga toilet ya nufa! Yai wanka, shi sam yama manta da Wayarshi a gida ya barta Missed call din Ameerah yagani sannan ya kirata sukafa Fara zancen soyayyarsu STORY CONTINUES BELOW *** Gidan Mansur kuwa Nazeefa kuka tasha sosai, Sannan mansur yazo yana bata hakuri, taqi haqura, lallashinta sosai yayi Tace kantane ke ciwo! Taba jikinta yayi yaji yai zafi rau!! burgima a gado ta fara tace cikinta na murdawa Subhanallah yace da sauri ya dagota zai kawota falo saita fadi kasa loooo, jini ne ya Fara zubo mata ta kafa da sauri Ya kaita asibiti, Aka tabbatar mai da miscarriage tayi, Yace sweet love dama kinada cikine baki sanar daniba? Tace love ni kaina bansaniba saboda banji wani changes a tare dani ba ko kadan, Yace OK To bakomai Mansur yadanyi baki ciki kadan saboda yanason yara, amma daya Tina Allah ne Mai badawa duk lokacin da yaso sai yace Allah yasa hakan yafi zama alheri tace Ameen Kwananta biyu aka sallamesu saboda tana dan jin jiri kuma batajin karfin jikinta, Aka Kara mata ruwa! Zuwa sati daya ta sama sauqi sosai Sannan sukai agreement da cewa karsu sanar da kowa tayi miscarriage! Mansur kuwa zuwa Wajen aikinsu yayi yace yanada uzuri sosai, ya yarda adinga cirewa a albashinshi, bazai dinga zuwa wajen aiki 8 ba se 10, sukace sun yarda, saboda mansur me kwazo ne yasan aikinshi, idan suka rasahi, Tabbas zasu sama chikas dan haka suka hakura da ya dinga zuwa 10 din Wata rana suna zaune Nazeefa tace dan Allah love kayi hakuri, abunda ya wuce ya wuce Yace hakane, tino da Rikon Hijab din da Mubeen yaiwa Matarshi yayi yaji bakin ciki sosai yace love dolema Mu tashi a garin nan in ba hakaba da matsala! Kallonshi tai tace wani irin matsala? Yace bazaki ganeba Tace lna zamu koma? Yace yobe, Gidan Sarki Kinsan da chan zamu zauna! Shuru tayi tana kallonshi Ya cigaba Da magana yace kinsan asalinmu yan Chan ne aikine yadawo da dad nan suma very soon zasu koma Chan! Tace yes kafadamun AI Yace yeah, kinsan last week akaba dad Commissioner na chan so dole mu koma, tace hakane but ita tinaninta daya Zatabar iyayanta, Sannan ya Kara da cewa I hate mubeen dama Sai yasa naga a bikinmu, yanata daukarki hoto Hmmm tace Kadena tinanin wannan, koba komai he’s my brother Dan Allah mubar maganar kaji please Dear Yace munbari amma zakibar zama gida ke kadai duk inda zani zaki bini KO kuma kije gidan Hajiya ki zauna ko Umma, kwanciya a kirjinshi tayi tace angama my love duk yanda kakeso haka za’ai nidai please ka dena tina baya! Kiss yai mata sannan ya kashe mata ido, Kara shigewa jikinshi tayi, nan jikinshi ya aikamai da sako cikin kwakwalwa nidai na fita dakin na barsu lol *** Dan zaman da mansur yakeyi a gida sun bala’in Kara shakuwa da Nazeefa, Komai sunayi In a fashion way, love kuwa se abunda ya Karu Dan ji sukeyi kamar zasu hadeyi junansu! Soyayya salo salo Nazeefa ta kara iyawa saboda *zauren Ummie xeey* da take ciki suna turo abubuwan daya shafa Mata ga topic Ana kawowa a tattauna so she learn alot, uwa uba ga shi ta Kara hakuri sosai Ga kawayen data saba dasu irinsu Nana Firdausi, Zainab Bose, Meelat, Nazeefa, Momin nasirin, Dr Ayoush, Zee complete, Mmn Ilham, Khadija harun, Kai kusan duka yan group din Dan sunada mutunci So Nazeefa najin dadin group din saboda suna bata shawarwari masu kyau, group din is the best gaskiya saboda minti minti take duba group din saboda akwai abubuwan karuwa sosai ga ban dariya Washe gari, kasancewar weekend ne kuma beson barin nazeefa a gida saboda sunada meeting a wajen aikinsu Dan haka yace ta shirya zekaita wajen ummanta, tsalle tayi sosai tace are you serious? Yace love kiyi fa ahankali qila munsama wani Cikin wannan irin tsalle, rufe idonta tayi tace love Allah ya shiryamun kai yace Amen Shiryawa tai cikin wata less tayi kyau sosai, suka fito yakaita gidan yace seya dawo zai shugo tace bakomai Xuwa gidan su tayi tun a bakin gate take Umma, Umma, ummanta fitowa tai tace yau kece a gidan? Tace wallahi kuwa umma, Daki suka Shiga suka Fara hira Sosa kamar wasu kawaye! Nan nazeefa kece mata ai tayi Bari, Umma tace Alhamdulillah dama inata tinani nace shuru Yar nan! Tace umma karki damu, tace to Allah ya kawo masu albarka tace Ameen, Sannan tace Bari na tashi na shiga kitchen na dafa maki Abu Nazeefa tace a’a umma a koshe nake Wlhi, ni ya kamata ma nashiga, Umma tace aa Ki zamarki Suna cikin maganar ne babanta ya shugo! Tamai sannu Da zuwa! Yace kece yau a gidanmu? Tace Wlhi kuwa Zama dukansu sukai suna hira tace dama Zan fada muku bayan Sallah zamu koma yobe state gaba daya amma bansan rabuwa daku Umma tace Yar nan kiyi hakuri aure ba inda bekai mutun bare ke da kikasha gwagwarmaya na tabbata ba inda bazaki zaunaba, kedai KO Ina kika tsinta kanki ki kasance me hakuri da kauda da Kai Dan Allah, Tace to Umma inshaa Allah Hira sosai sosai, Sannan tace amma ya kamata aneman maki me aiki KO Umma! Ga azumi na zuwa! Wanda zasuci arziki saboda arzikin nan ya mana yawa Babanta yace sai yasa nakesonki, Ya ta, Yanda kike da zuciyar nan Allah ya saka miki da alheri za’a nemo, Ko a kauyen mune bare baza a rasa yan uwa baa! Se chan yamma Mansur yazo daukar matarshi Ya shigo gidan suka gaisa, Sannan suka tafi Ahanyarsune mansur ya ce love muje chicken republic muyi orden abinci Dan yamma tayi kuma I don’t want you to suffer, Tace OK dear Shiga yayi ita kuma tana mota, ta jirashi ya fito, yana fitowa taga Ya tsaya gaisawa da wata Mata Dan ba budurwa bace! Idon nazeefa kyar akan matar, tace wanene wannan kamar Yar duniya! Karasowa kusa da motar sukai taji matar nan tace M.T kenan kana Duniya Ashe! Yace Wlhi kuwa nayi aure ga matar nan! Ya nuna mata Nazeefa suka gaisa tace wow she’s beautiful nima nayi aure ina Ya kalleta yace seema kenan! Ayimun hakuri, Tace lol karka damu, you have a beautiful wife, nan dai suka gaisa yace yananan kawo Mata nazeefa har gida tace OK Nazeefa kishi ya tashi shin wacece wannan? Yana shiga mota yaga fuskarta ya sauya yasan da magana! Yace karki fishi please love tadai ce uhm Gida suka nufa yanata mata hira itakam se sham kamshi, shikam dama yasan batason yana kallon mata boobs Aiko ya kura musu ido, yana driving yana Dan lashe baki, ta morrow ta ganshi tai maza ta janyo gyalenta ta Kara rufe jikinta, murmushi yayi yace my queen kenan Gida suka karasa, Koda sukaje nazeefa se jan aji take tayi, Sunci abinci sun koshi dukda kadan taci saboda ba yunwa takejiba, Sundan yi kallon tarkon kauna, inda Zerah ke kwana a gado omer kuma a kujera, tace yauwa, yau a gidan nan jaka za’ai kuwa Zuwa yai ya sureta se bed room yana mata chakukuli yace ki sake ranki nasan fushin da kke Seemah da kika gani mun gaisa she was my ex tasoni sosai kamar ba gobe, yarinyar Former commissioner of Education ne, hajiya ce naga batai na’am da itaba sai yasa na kyaleta, But she loves me sosai, Gata halinku kusan daya akwai tausayi tinowa abubuwan daya shiga tsakaninta da mubeen tai kuma still Mansur ya amince ya aureta beyi fushiba, so bekamata itama ta nuna bacin ranta ba Tace sorry I don’t knw what comes over me dazu kayi hakuri, I love you till eternity smiling yayi yace love you more!! Daki suka Shiga sukai alwala sukai sallah sukai addu’oi akan Allah ya azurtasu Da zuria dayyaba Ameen Sannan ta tashi ta Fara cire kaya zatasa night gown, binta da kallo yayi yace bari nazo na tayaki Lol……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *