YAR MAKIYAYA
CHAPTER 5
Daga k’arshe Mun gano d’an giyan nan mai takura wa Laila ba kowa bane Illa *SAEED BIN Ahmad* D’an uwan Ameer , Mun ji yadda a dalilin *Y’AR MAKIYAYA* suka doki junan su har saida Ameer ya taho to the rescue, Amma tambaya a nan shine ,shin Saeed zai hak’ura kuwa? Me zai faru Idan suka yi ido hud’u da juna?.
Don samun amsoshin wad’annan tambayoyi sai mu garzaya shafi na gaba +
***** ***** *******,
“Suraj?” . Laila ta k’ira sunan shi tana zaune ta had’a kai da gwiwa
Ba tare da ya amsa ba ya d’ago yana kallonta na wasu dak’ik’ai kafin ya taso ya zauna gefen ta yace
“Fad’a min me yake damun ki, tun d’azu kin yi shiru kin had’e kai da gwiwa , wannan shirun naki har yasa na fara jin bacci”
Murmushi tayi sannan ta ce “Tsoro nake ji, duba da yadda kuka yi fad’a kai da d’an uwan ka, a dalili na, ina tsoro kar nayi silar tarwatse war zumunci tsakanin ku, ina kuma jin tsoron zak’ewa a kan soyayyar ka kasancewar ka yarima gashi ni kuma y’ar makiyaya wanda bata saba da irin rayuwar ku ba, iyaka abinda na sani a rayuwa shine rayuwa da dabbobi, da safe in na tashi bayan gabatar da ibada zan taho kiwo, kiwo shine tushe na, bani da aikin da ya wuce na kula da dabbobi, na basu abinci na gyara muhallin su ,kullum aikin kenan ,rayuwa a wancan makeken gidan Sarautar zata zamo bak’uwa kuma zan kasance cikin takura. Tun ina k’arama inna ta rasu tun a lokacin zuciya ta ta tarwatse, amma na tattara ina manegi da shi saboda wani b’angaren zuciyar na babana ne , rayuwa babu mahaifiya akwai wahala shekarun da nayi babu ita sun kasance masu wahala a gare ni duk da Baba yana iya k’ok’arin sa, har yanzu ina buk’atar Mahaifiya wanda zata d’aura ni a kan hanya daidai , sannan Suraj wata gaskiyar ita ce, duk da wad’annan matsalolin ina matuk’ar k’aunar ka, ka samu b’angaren zuciya ta da ban tab’a bawa wani ba, Suraj ina ji a jiki na nan gaba akwai matsalolin da zasu tun……”
Bata k’arasa maganar ta ba Suraj ya rufe bakin ta da hannun sa yace
“Shush! Kada na sake jin kina irin wad’annan kalaman. Daga ni har ke babu banbanci Laila, banbancin kawai shine ba’a waje d’aya muka tashi ba, nima na taso ne k’ark’ashin kulawar Oummi na, na taso ne tsakiyar ahali masu k’aunar junan su , duk inda naga dama zan je babu takura zan yi yawo da abokai na kuma ban damu ba don kai talaka ne domin abota tafi min kud’i muhimmanci, banbanci na da ke ni nawa Uban na rasa, yana raye amma he’s good as dead! Bashi da banbanci da matacce, bai tab’a furta Kalmar da zata faranta min ba komai nayi ba daidai bane, har yanzu ina buk’atar wanda zai maye min gurbin mahaifi. Kinga tun da na shigo wannan gidan komai ya chanja , na had’u da y’an uwan da basu damu da ni ba kullum burinsu su aibanta ni , su tozarta ni ,bani da sakat sun tsane ni ban san dalili ba. Gidan chan shi da kurkuku babu banbanci.”
Ajiyar zuciya Suraj yayi sannan yaci gaba da cewa
“Laila in har duk wannan tsananin bai sa na karaya ba Ke me zaisa ki karaya? Oummi na ta dad’e tana muradin samun y’a mace dan ahalin ta ya kammala Idan kika amince na Aure ki zaki cike gurbin y’a ga Oummi na yayinda ita zata maye miki gurbin mahaifiya da kika rasa, ni kuwa daga Baba zan samu gurbin mahaifi da Dad ya kasa cike wa. Bazaki takura ba,bazan bari ki cutu ba sannan bazan tab’a samun sukuni a wancan gidan ba har sai kin zamto haske ga duhun da ya yi mamaye a zuciya ta.”
Mik’e wa Laila tayi gami da share hawayen fuskar ta tana Murmushi.
Junaid ya dad’e da zuwa wajen basu sani ba, sosai kalaman Suraj ya bashi tausayi babu alamar k’arya ko yaudara a tattare da shi dan haka Junaid ya matso kusa yace
” Yanzun nan wani tunani ya fad’o min, Yaya zakiyi da kiwon naki Laila kamar fa zaki bar wa Baba nauyi” ya kashe mata ido.
Mik’e wa Suraj yayi ya naushi cikin Junaid cikin raha yace “Wannan bazai gagara ba tunda baba ya samu d’a, ka sani Junaid wai don na d’auke Laila ba yana nufin zan hana ta yin rayuwar da ta saba bane, sedai muyi rayuwar tare, ina nufin nima sai na zama *d’an makiyaya*” sosai Suka fara mishi dariya Junaid yace “dan haka zan nema maka sanda.”
Ita de Laila dariya take musu sai hirar su suke.
Kusan sha biyu na rana Suraj ya mik’e yana karkade jiki
“Zan tafi yau nayi alk’awarin da Oummi na zan ci abinci bana so tayi ta jira na”
Laila ta Zaro idanuwa baki na rawa tace “yanzu da fashashen baki zaka tafi? Wancan ranar goshi yau kuma….. Gaskiya.”.
Dariya Suraj yayi gami da kashe mata ido d’aya kafin yace
“Ki shirya yau da yamma akwai wani wajen da zan kai ki, kada Nazo kuma baki shirya ba akwai wanda nake so ku had’u , mutum ne mai muhimmanci a rayuwa ta kawai ki shirya”
Kai kawai ta girgiza shi kuwa ya juya ya bar wajen .
Shigar sa mota wayar sa tayi ruri ,ba tare da b’ata lokaci ba ya d’aga gami da kara wa a kunne
“Suraj ! Nine Habeeb, kana lapya de ko?”.
Murmushi Suraj yayi kafin yace
“Habeeb! Ya naga numbern nija ko de kana K’asar ne?
“Eh kuma the biggest surprise is gobe in shaa Allah zan shigo Adamawa, I have a lot to tell you”
Naushin stirring Suraj yayi yace
“YES!!!! Allah ya nuna mana goben, ni kaina ina da labarai da nake son fad’a maka can’t wait to see you tomorrow!”
Sun d’an jima suna hira kafin daga bisani suka yi sallama da juna kowa ya ajiye waya. Motar sa ya ja bai tsaya ko ina ba sai gurin ajiye motocin sashen su , fitowar sa ke da wuya bai ankara ba yaji sauk’ar naushi hakan yasa saida ya Sunkuya yana k’ok’arin self defense daga harin naushin da *Saeed* ke aiko mishi, tun ya iya hak’uri har ya kai mak’ura ya dunkule hannun shi ya bawa Saeed lafiyayyen naushi har saida yayi juyi kafin yakai k’asa Ameer ya rik’e shi sannan ya hankad’e Suraj cike da zafin rai yace
“Why can’t you stay away from us! Ka dena shiga hurumin mu!!”
Wani mugun dariya Suraj yayi kafin ya dubesu daga sama har k’asa yace ” *stay away from you guys?* wait a minute! Ni da ku waye yake shiga rayuwar wani? Waye yake tsoma kan shi cikin hurumin wani? Har kuna da bakin furta wad’annan kalmomin? Am impressed! For the first time ever na tab’a ganin players irin ku! Impressive!” Yana kai nan ya Hankad’a su gefe ya wuce cikin gida yana mai kare fuskar shi don gudun kar mom ta ga ta’asar dake cikin ta.
Bin shi sukayi da kallo Saeed ya cije baki ya ja Ameer yana fad’in “Oh damn it! Can you imagine har wancan d’an gidan kod’add’iyar balarabiyar ne zai d’aga hannu ya buge ni? Ashe kuwa ya tab’o match don yanzu aka fara ni gaba d’aya ma naji chaji na ya yi d’ub I need a drink”.
“Shaye shayen giya? Not good for your health me zai hana kayi wani abun instead?” Cewar Ameer fuskar sa d’auke da shu’umar Murmushi. Saeed ya harare shi sannan ya bar wajen aka bar Ameer shi kad’ai yana Murmushi…….Suraj! Suraj!! Son! Kamar ba k’iran ka nake ba?” +
A tsanake ya juyo kai a k’asa yace “Na’am Oummi”
“Huh? Ya ilahi! Habeeby miye kuma Wannan nake gani? Did you engage in a fight? I mean look at you! Yanzu kam bazan d’auki ko d’aya daga cikin karayrayin da kake min ba, waye ya maka haka? Dubi yadda fuskar ka tayi purple da ita wato ka fita ne don ka takalo fad’a ko?”.
Hannun ta Suraj ya rik’e yace “Oooooh Oummi Nah you seem so over protective yau d’in nan , kwata kwata ma baki dace da act d’in ba , ki bar batun ciwon nan muyi magana akan wani abun na daban Yawwa daman ina son sanar da ke gobe Habeeb zai zo, finally zan samu company!”
Gira Mom ta d’aga tace “are you trying to divert our discussion? Na riga ka sanin Habeeb yana hanya saboda haka mu koma topic d’in da muka baro wanda ka kasa bani amsa and am going to ask you for the last time ,don’t lie to me saboda sam k’arya bata karb’e ka ba.”
Kawar da duban sa yayi daga gareta jiki a sanyaye yace ” Sorry I lied to you Mom, ba dan son raina nayi ba su suka tunzira ni ,kawai na taimaki wata yarinya daga fad’awa tarkon sa na mummunar ak’ida shine ya hau ni da fad’a ya fara kai min naushi I can’t stand him kawai na mayar masa da martani”.
Fuskar sa Mom ta duba a karo na biyu tace
“Sanin kanka ne y’an uwanka ba son ka suke ba, basa k’aunar ka shiga harkar su me zai dame ka da abun da suke yi da har zaka sa kanka a hurumin su?”
“Mom magana fa ake akan yarinya, a lone girl , that too my girlfri……..”
Da sauri yasa hannu ya rufe bakin sa yayinda mom ta saki one of her finest Murmushi tana kallon shi baki a sake. Juyawa yayi da sauri ya nufi hanyar d’akin shi yana Murmushi.
Ba kamar yadda ya bar d’akin ba komai tsaf yake sai daddad’an k’amshin lavender da ke tashi rigar sa ya tube sannan ya fad’a gado rigingine ya lumshe ido yana Murmushi.
Pat!! Ta make shi a cinya har saida ya mik’e tsabar razana
“MOM!!” Ya fad’a cikin firgici yana shafa wajen da ta doke shi. Had’e rai tayi ta fisgo shi ya zauna gefen ta kafin tace
” so daman fad’an naku is all about boy girl thing ko? Sannan a matsayi na na Ummin ka bazaka iya fad’a min komai ba akan ta, kawai na gane you don’t need me here anymore zan koma Cairo”.
“Mene?! Mom? Ki koma Cairo kuma? Daman so nake kawai in baki mamaki ,kasancewar kullum kina cewa bazan iya zab’ar mace tsarar ki ba ,gashi yanzu kin b’ata min shiri kawai ba zata nake son miki fa, Toh kawai ma barin fad’a miki gaskiya ta ” I so much luv her Mom ta kasance the most intelligent being I’ve ever met after you Oummi Nah.”
Zaro ido Mom tayi cike da mamaki tace ” wai da gaske? Tell me more about her”.
Nan Suraj ya cigaba da labarta wa Mom had’uwar su da Laila har zuwa yau d’in nan ,ita kuwa cikin nutsuwa ta zuba masa ido tana sauraron sa cike da kulawa, ta tabbatar d’an ta ba k’aramin son Laila yake ba saboda tasan Suraj sosai abunda yafi so shi yake bawa muhimmanci tabbas wa Suraj se Laila kad’ai!
Sedai Suraj ya lura yanayin ta ya chanja. Murmushi yayi ya mik’e yana duna fuskar shi a madubi yace
“Nasan kina tunani ne a kan Dad, amma ni halin Dad da duk fad’an da zai yi bazai sauya min ra’ayi ba coz I love her, ban damu ba ko miye zai faru don bazan tauye wa zuciya hakkin ta ba”
Murmushi mom tayi kawai ta mik’e zata fita, daidai bakin k’ofa ta juyo ta kalle shi sannan tace “ka shirya ka sauk’o mu ci abinci.” Kai ya jinjina kawai ya fad’a bathroom don yin wanka ,duk jikin shi yayi tsami, ga gajiya, dan haka da ya fito ya manta da zancen cin abinci kwata kwata don yana idar da sallar azahar ya kwanta a nan kan sallaya bacci ya sace shi.
Mom ta gaji da jira ta koma d’akin don ganin dalilin rashin sauk’o war shi taga har ya 6ingire yana bacci , Murmushi kawai tayi ta fice gami da Jan k’ofar.
*Laila*
“Ban san wanne irin yanayi na shiga ba yau, gabana fad’uwa yake yi.” Laila ta fad’a idanuwan ta cikin na Zubaina.
Daga nan babu wanda ya sake fad’in komai.
Daddad’an k’amshi na jiyo wanda ko a barci na shaqe shi nasan waye ma’abocin k’amshin nan ballantana ido na biyu. Cikin muryar sa mai sanyaya ra yace
“Haba MASOYIYA ta! Me kuma zai baki tsoro bayan gani nan? Inda zan kai ki ba waje ne da zaki cutu ba, wanda zan had’a ki da ita mahaifiya ta ne kina muradin mahaifiya ita kuma tana k’aunar d’iya mace,tun da taji zan kai ki wajen ta take ta murna ta kagu ta gan ki, kada ki k’i zuwa don ina so in tabbatar mata na san irin surukar da take so”.
Murmushi tayi sannan tace “ban tab’a shiga wancan gidan ba, tun da na taso kiwo ya fi min komai amma ka sani yau zan shiga ne saboda in tabbatar ban bawa Inna kunya ba”
“Dakata! Me kika k’ira Oummi Nah?”
Baki a sake Laila tace “Inna mana!”
Wata muguwar dariya ya sa harda rik’e ciki, “Wallahi kar ki soma, Ki k’ira ta Oummi ko Mom ,zo mu tafi kuma ki sake fuska dan bana son tafiya da mutum yana had’e rai! Wai ma tsaya tukunna! Miye naga kina shan k’amshi.”?
K’in kula shi tayi ta bi bayan shi tana Murmushi, ita da Zubaina suna zaune a back seat. D’agawa Junaid hannu yayi tuni ya runtumo a guje ya bud’e k’ofar motar ya shiga da kyar.
Suraj ya ja mota babu wani cikin su da yace k’ala, tun Suraj na musu magana har ya gaji. Tinted glass ne a jikin motar saboda haka babu wanda ya ga da wad’anda Suraj ya zo ko motar sa ma a bakin k’ofa daf yayi parking. Tun daga nan Laila da su Junaid suka fara juye juye da kalle kalle tun Suraj yana jin takun su a bayan sa yaji d’ub babu takun su.
Tafiya take amma kamar ba yi take ba sam bata ganin inda ta nufa bata ankara ba taci karo da wani figure kai kace dutse, a firgice ta ja da baya zata matsa tsantsin tile ya ja ta har ta kusa kaiwa k’asa ya rik’o ta yayinda Junaid da Zubaina suka zuba musu ido baki a sake.
Bud’ad’d’en k’irjin sa ta kalla sannan ta d’ago kai ta dubeshi ,Murmushi ya sakar mata kafin ya d’ago ta yace
“Ku k’araso, ga wajen zama bari na k’ira Mom d’ina.”
Dukkanin su kowa ya nemi wuri ya zauna har aka kawo musu drinks da snacks babu wanda ya sani kowa bawa idanuwan shi abinci yake.Mom, na kawo ta, she’s downstairs, please Mom tell me I’ve made the right choice”
Murmushi mom tayi yayinda ta mik’e tsaye ta dube shi yadda ya zama desperate tasa ta dariya tace +
“Haba Babana, ai se ka bari na ganta tukunna kafin in baka amsar irin choice d’in da kayi, yanzu de ka k’ira Dad naka tun jiya yake fad’a wai tun da ya tafi baka k’ira shi ba” Mak’e kafad’a yayi sannan yace , zan k’ira maybe anjima nidai mom mu tafi ku gaisa har aboki na nakawo miki ku gaisa” kai Mom ta jinjina ta fice tana Murmushi ya bi bayan ta.
Duk da cewa Suraj ya ce su zauna kan kujera kafin ya dawo duk suna takure a k’asa ,ko da ya hango su Gaba d’aya sai suka bashi dariya bai tsaya second taught ba ya kwashe da dariya har yana rik’e ciki al’amarin da ya sa duk suka zuba masa ido babu wanda yasan dalilin dariyar, y’an aikin dake kai kawo ma duk suka tsaya kallon sa don tun zuwan sa bai yi dariyar da ta kai haka ba galibi sai Murmushi, harara Mom ta watsa masa hakan yasa ya gimtse dariyar har saida suka k’arisa falon, zubewa yayi kan lallausan kujerar dake gefen Mom ya cigaba da dariya ,da kyar ya bud’e baki dan dariya
“Hhh. Mmom Wannan shi ne Junaid aboki na ne sosai kuma ai na baki labarin shi.”
Cike da rusuna wa Junaid ya gaida Mom ta amsa da fara’ar ta sannan ta dubi matan biyu dake rakub’e da juna tace
“Ku saki jikin ku mana ai nan gida ne” daga Laila har Zubaina had’a baki suka yi wajen gaida ta. “Lafiya lau” ta amsa cike da raha sannan ta nemi waje zata zauna.
“Wait Mom! Ai baza ki zauna ba sai kin yi guessing cikin su biyun Wacece Laila ta!” Kai ta girgiza tana dariya ba tare da tace k’ala ba taja hannun Laila ta zaunar kan kujera sannan ta juyo rik’e da kunkumi tace “Idan na kintata daidai Wannan ita ce wanda tayi nasarar sace zuciyar Suraj”
Zama tayi gefen Laila tana jira taji me zai ce ganin ya zaro idanuwa waje ya bud’e baki tace “miye kuma haka?”
Kai kawai ya girgiza ya mik’e ya ja Junaid suka nufi flat nashi aka bar mom da su Laila, ai kuwa da kyar Mom tayi nasarar sa Laila magana Zubaina kuwa sai kalle kalle take hankalin ta kwance.
Mom ta sha hira da Laila duk da bata cika magana ba Amma mom ta alak’anta hakan ne da rashin sabo, basu jima ba wata hadima ta shigo cike da ladabi ta ce “food is ready ma’am” kai kawai Mom ta d’aga Mata sannan ta aika matar da ta tafi ta k’ira Suraj.
“Yanzu Abokki na kana zaune cikin Wannan duniyar amma ka zab’i ka wuni cikin daji inda ko ina cike da had’ari yake ga muggayen Kwari” Cewar Junaid dake ta fama da taunar crunches. Dariya Suraj yayi yace “Idan da ace zaka zauna a matsayi na kawai na kwana biyu Toh ina mai tabbatar maka kwana d’aya zaka yi ka bar gidan nan, saboda Mom nake zaune a nan, ina so naga na cika gidan nan da soyayya, in basu abun da suke lacking a rayuwa, musamman Dad ,na sani cewa baba na ne shi amma sam……..Kawai a bar maganar Junaid, abunda ya wuce ya wuce.
Knock suka ji a k’ofa, mik’e wa Suraj yayi ya bud’e k’ofar,bai jira abunda maid zata ce ba yace ta tafi yana zuwa don yasan tabbas k’iran na abinci ne.
Wannan yini ya zama Mafi soyuwa ga kowanne daga cikin su Musamman Mom da ta kwallafa rai a kan Laila duk da cewa har yanzu damuwa bata bar zuciyar ta ba ,damuwar yadda soyayyar Suraj da Laila zata kasance with Dad in between. A b’angaren Suraj kuwa ji yake no matter the consequences no retreat no surrender! Haka zalika Laila, ji take bata damu ba koma me za’a fad’a soyayya yanzu ta fara. Sun tafi bayan Mom ta cika su da kyaututtuka ,sannan Suraj ya nuna musu wasu sashen gidan inda suka kashe kwarkwatotin idanuwan su. Abun burgewan shine babu d’aya daga cikin Saeed ko Ameer da ya ankara da zuwan su ballantana tafiyar su, their journey to the palace was quiet adventurous and amazing.
Washegari.
Bak’ar mota k’irar Mercedes-Benz Brabus g.800 ce tafe , baka iya kallon wanda yake ciki don tinted glasses ke da ita, bata tsaya ko ina ba se sashen su Suraj, budewar k’ofar ke da wuya ya sauk’o da k’afar sa wanda ke sak’ale cikin black shoe sannan ya fito yana mai k’are wa gidan kallo, ba yau ya fara zuwa ba, don Kusan kuruciyar sa a nan yayi ta tare da Suraj da Ameer, sosai yasan halayen kowanne daga cikin su, musamman Ameer duk da cewa rabonsa da ganin shi ko jin muryar sa ya kai shekaru sama da sha hud’u don sai Hutu yake zuwa kamar dai Suraj kuma tunda Suraj ya daina zuwa shima ya d’auke k’afa.
Komai de yana nan kamar da” ya fad’a yana Murmushi sannan ya nausa cikin gidan kai tsaye.
Mom tana zaune tana waya ganin shi yasa ta katse wayar gami da k’iran sunan shi cike da fara’a “Habeeb!” Da y’ar dariyar sa ya zauna gefen ta gami da kwantar da kanshi a kafad’ar ta yace “Mom, finally na dawo that same old place, I was surprised babu abunda ya chanja daga waje” Murmushi Mom tayi kafin ta ce
“Welcome home son, naji dad’in zuwan ka , yanzu ka shiga ciki Suraj yana nan ,freshen up kafin a kawo maka abinci don nasan baka wasa da cikin ka. Dariya yayi yace “Yawwa Mom kamar yanzu ma kin san yunwa nake ji ” yana kai nan ya suri bowl d’in fruit salad na mom da gudu ya nufi Upstairs yana dariya.
A hankali ya tura k’ofa ya lek’a d’akin ,kwance yake yayi d’add’aya yana sharar bacci ,dariya Habeeb yayi ya kutsa kai cikin d’akin ya haye tsakiyar gadon gami da nad’e k’afa ya fara shan fruit salad d’in cikin kwanciyar hankali saida ya gama ya ajiye bowl d’in sannan ya takarkara ya maka wa Suraj duka wanda hakan saida yayi sanadiyyar da Suraj ya firgita ya mik’e kamar zai gudu shi kuwa tsakani da Allah dariya yake harda kwanciya ,Saida Suraj ya kai k’ofa tukunna ya tsaya chak cike da takaici , juyowa yayi rik’e da kunkumi ya Furzar da iska daga bakin sa sannan ya dubi Habeeb dake ta dariya yace “BRAVO ALAIKA! Well done Habeeb !” K’arasa wa yayi bakin gadon ya zauna yana shafa k’asumbar sa yana Murmushi kafin ya mik’e ya zari pillow ya wurga wa Habeeb, chafke wa yayi yace “you missed”.
Dariya Suraj yayi ya ce “not yet!”.
Ya mik’e ya nufi inda Habeeb ke zaune ganin haka Habeeb ya rufa a guje ya fice Suraj yabi shi, sai karo suke da ma’aikatan gidan har suka sauk’o downstairs, kad’an ya rage su kada Mom.
“Ah ah! Me kuke yi haka? Suraj! Habeeb ku nutsu mana!”
Kai Suraj ya girgiza yace “barni dashi Mom da kin ga abinda yayi min nasan bazaki hana ni ba Mom”.
Habeeb da ke lab’e bayan Mom ya girgiza kai yace
“Mmom Ni ban masa komai ba ,wai daga tashin sa daga barci kawai ya firgita ya fara neman k’ofa kamar wanda ya ga aljani mom daman I have a surprise for you barin je mota in kawo miki amma kafin nan ki rik’e shi Mom” Habeeb ya nufi k’ofar fita da gudu Suraj ma ya zame daga hannun mom ya bi bayan shi suka bar Mom tana ta dariya ita kad’ai.
Dukkanin su basu ankara ba suka yi karo da juna sanadiyyar abunda suka gani tsaye bakin k’ofa , iya k’ok’arin su sun yi dan ganin sun daidaita numfashin su saboda haki da suke yi, ita kanta Mom cike da mamaki take kallon k’ofar dukkanin su babu wanda yayi magana……